Kenza eBookz

Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh - Chapter 34

Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh - Chapter 34

Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh Chapter 34: Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh Chapter 34. Saida suka gaisa da Amadu yayi mashi ansha ruwa…

3,894 words

Saida suka gaisa da Amadu yayi mashi ansha ruwa lafiya kafin ya wuce da ita har cikin gidan don yana son yi ma gwaggo barka da shan ruwa, a zaure ya tsaya yace mata ta shiga ta fad'i ma gwaggon zai shigo, cike da zumudi ta shiga cikin gidan lokacin gwaggon na kwance a tsakar gida tayi shimfida ga maganin sauro ta kunna agefe don ba wutan Nepa, a gefenta ta aje tuwon tana sanar mata cewa tare da Ya Handsome take yana zaure yace zai shigo, da sauri gwaggon ta tashi zaune tace mata tace ya shigo don a kimtse take, da gudu taje tace ance ya shigo, a tare suka shigo tana gaba yana baya lokacin gwaggo ta fito daga d'akinta ruk'e da darduma ta shimfida mashi tana ce mashi sannu da zuwa, bayan ta gama ta nuna mashi alamar ya zauna saida ya cire takalmanshi agefe kafin ya hau ya zauna ita kuwa Fatuu can gefe inda sauran kayan bud'a baki suke ta nufa ta fara bubbud'awa tana fad'in " Gwaggo Allah yasa dae baki cinye komai ba kin rage man" har saida Haisam ya d'an kalli inda take sai kace ba yanzu ta gama cin abinci ba, shuru gwaggon tayi mata suka shiga gaisawa da Haisam tace bari akawo mashi abun ta6awa, tana k'okarin mik'ewa ya dakatar da ita yace yanzu ya gama cin abu tace to ai ko ruwa yasha nan ma yace ya gode tace to ta kyaleshi yanzu amman dole yazo shan ruwa kafin agama azumin, d'an Murmushi kawae yay kafin ya d'an d'aga kai ya kalli Fatuu dake can gefe sai ta tsakura wannan ta ci wannan acikin ranshi kuwa mamakin yadda take cin abinci yake yanzu ya gano dalilin dayasa ta tashi hankalinta daya sata yin azumi dole, godiya gwaggo ta fara yi mashi game da azumin dayasa Fatuu take yi tace ita sam bata san rashin hankalin da take yi kenan ba da tuni ta tsawatar mata don duk atunaninta in tayi azumi cikakkene, nan ma dae d'an Murmushi yayi ita kuwa fatun tana jin abunda gwaggon ke cewa ta taso tazo inda suke, agefenta ta zauna tace, "Gwaggo ni ce banda hankali?", " ina kika ganshi fa" ta bata amsa cikin harshen fulatanci, turo baki tayi da hausa tace "Wllh Allah inada cikakken hankali kuma ga Ya Handsome nan ki tambayeshi kiji don shi yasan inada hankali" jinjina kai gwaggo ta shiga kafin tace " dama ai yanzu yana daga cikin wad'anda zasu fad'i rashin hankalinki Fatuu" jin hakan yasa ta fara kukan shagwa6a tana d'an tuttura kafa, girgiza kai gwaggo tayi tace "yanzu shi wannan abun da kike ai duk cikin hankalinne ko, ke sam ba ranar da zaki girma ne?" turo baki tayi ba tare data ce komai ba idonta akan Haisam daya d'an sadda kai yana kallon k'asan gidan, d'agowa yay ya d'an kalleta suka hada ido ya d'an girgiza kai kafin ya kalli gwaggo yay mata sallama yana kokarin mik'ewa, atare suka rako shi gwaggon na k'ara yi mashi godiyar dawainiyar da yake masu, suna zuwa bakin zaure ta koma ciki ita kuma Fatuu ta rako shi har waje dama bata cire hijab d'in jikinta ba, suna fitowa kan hanya yace ta koma tayi tsaye bakin hanyar tace sai ya tafi zata koma, har ya d'an wuce shagon Amadu ta kwala mashi kira,

"Ya Handsome",tsayawa yay ya juyo ya kalleta, " ai gobe dae ba Azumi ko?" shiru ya danyi da farko sai kuma ya d'aga mata kai alamar eh, kawae sai gani yay ta fara yin rawa, bud'a ido yay alamar mamaki aikuwa tana ganin hakan dayake akwae haske ta ruga tana ta dariya, girgiza kai kawae yay daga haka ya nufi gida.

Washe gari da bata yin azumi sam bata yarda taji yunwa ba,duk wani abun ci data gani sai taci, tunda safe kafin ta tafi makaranta ta cinye duk abunda suka rage haka bayan antaso data je gidan Hajiya bunu bunu taci wani abu wai daga yau sai bayan kwana biyu Saude nata mata dariya, da yamma data koma gida ma tana taya Gwaggo aiki tana cin abubuwan da aka fara na bud'a baki ba tare da ta 6oye ba kamar yadda take yi da don yanzu gwaggon tasan yau ba ranar yin azumi bace har gwaggon nace mata wannan kafin asha ruwan ma ai saita cinye komae sai da tayi da gaske ta hanata. Haka taci gaba da yin azumin duk in tayi biyu sai ta huta kwana d'aya kuma bata k'ara yima Haisam korafi game da azumin ba gudun kada yay fushi da ita sai dae in yana bata wuya tai ma su gwaggo ko Saude korafin, ana saura kwana takwas agama azumi bayan gama sallar asham yace mata ta shirya gobe karfe 10 na safe zai kaita inda za'a gyara mata kai, lokacin zai rakata gida kaman yadda kusan kullum yake rakata don yanzu da angama sallar saita koma part d'in hajiya daga baya ya rakota sa6anin da tare da Haulat suke tafiya gida da angama sallar yanzu kuwa tun a Masallacin suke rabuwa suyi ma juna saida safe, cike da murna ta amsa mashi da to sai kuma ta tuna goben ranar yin azumi ce hakan yasa ta rokeshi akan ya barta ba sai tayi gobe ba tunda fita zasuyi, da farko k'in yarda yay ganin yadda ta marairace mashi ne kuma ba wuri daya yake son suje ba yasashi ce mata in ta yarda zata rama shi next tayi ukku sai ya amince, cike da zumud'i tace to ta yarda ahaka suka rabu,

**** **** *****

Washegari tunda sassafe ta tashi don fitar da zasuyi na ranta shiyasa da tayi sallar Asuba ta kasa komawa, kuma dama tunda ya gaya mata tana isa gida ta sanar ma gwaggo tace karta tada ita sahur don bazata yi azumi ba, tana tashi shaf shaf ta share tsakar gidan tayi wanke wanke don indae bata azumi ita ke yinsu in tana yi kuma gwaggon ke kama mata wani abun kaman wanke wanke sai suyi tare in tana gida wani lokacin ma ita kad'ai ke yi ita Fatun sai ta share duka gidan don tuni anyi masu hutun Islamiyya, tana gamawa ta fad'a bandaki tayo wanka bayan ta gama ta nufi d'aki don ta shirya, Misalin k'arfe 9:30 saura ta gama shiryawa cikin jar jallabiyarta harda su makeup ga jan janbaki tasa abakinta tayi kyau sosae ba kamar yanzu da skin d'inta ta canza saboda mayukan da take amfani dasu sun fito da ainihin kalarta don bana bleaching bane, koda ta lek'a yi ma gwaggo sallama isketa tayi tana bacci hakan yasa ta fito ta tafi don tasan ta sanar da ita tun jiya, lokacin da ta fito wajen wayam ba kowa duk anata baccin safe ko kawu Amadu ma bai tashi ba dama yanzu bai bud'e shago da wuri wani lokacin ma yan kawo kud'in kankara ne ke tada shi dole, ta Gate tabi don k'aramar kopar arufe take har Officer na zolayarta cewa da ganin wannan kwalliyar bata azumi tace mashi tana yi daga haka tai wucewarta don a k'agare take da su tafi, da sallama ta shiga cikin falon nashi don abud'e ta iske kopar sai dai koda ta shiga bai acikin falon hakan yasa ta zauna don ta jirashi tunda tasan lokacin daya dibar masu zasu fitan bai idasa ba kuma koda wasa bata ta6a shiga Bedroom dinshi ba don bata ma ga fuskar yin hakan ba a wurinshi, shiru shiru har bayan wani lokaci bai fito ba hakan yasa ta gaji da zaman ta d'an kwanta a d'ayan 6arin kujerar, nan da nan sanyin Ac ya bugeta ta fara d'an gyangyadi dama jiya bata samu isasshen bacci ba saboda zumudin yau tayi, jin sanyin Ac d'in yayi mata yawa don har kafafunta sun fara rawa yasa ta mik'e ta daukko throw pillows d'in dake akan kujeran ta rufe kafafunta dasu ta linke hannuwanta akirji nan da nan ba tare da ta ankare ba bacci mai karfi yai awon gaba da ita,

Karfe goma daidai ya fito cikin falon jikinshi sanye da rantsatstsen Voile Coffee Brown haka takalmanshi da agogon hannunshi ma duk Coffee ne, Ma sha Allah shine abunda na fad'a yayin da yake nufo cikin falon da tafiyarshi ta kasaita, tsaye yay d'an nesa da ita yana kallon fuskarta fuskarshi d'auke da d'an Murmushi don ganinta da yay yasashi k'ara fahimtar yadda take son agyara mata gashin, kai idonshi yay kan kafafunta da ta jera throw pillows lokaci guda ya fadada Murmushinshi had'i da d'an girgiza kai, juyawa yay ya koma Bedroom dinshi, bada jimawa ba ya fito hannunshi d'auke da lallausan farin Duvet, saida ya cire pillows d'in sannan ya lullu6a mata shi har zuwa cikinta daga haka ya juya ya nufi dakin lab d'inshi ya fito hannunshi ruke da wata bak'ar laptop ya zauna a inda ya saba zama ya fara operating dinta bayan ya daurata kan c-table,

Bacci sosae Fatuu take yi, duk in tayi motsi sai ya d'aga idonshi ya kalleta sai kuma taci gaba, saida ta d'auki kusan awa kafin ta fara motsi sosae, a hankali ta fara bud'e idanunta kafin ta idasa ware su sosae, kuri tayi tana kallon Haisam dake ta daddana computer da mamaki tace "Ya Handsome" gira ya d'age mata kafin ya d'aga ido ya kalleta, mik'ewa tayi zaune idonta akan duvet d'in dake jikinta tace "Ya Handsome kai kasa man wannan abun?" kai ya daga mata alamar eh sai kuma yace " kina jin sanyi ne", " to munje wurin gyaran gashin ne?", shiru yay jin wata tambaya mara kan gado, can kuma tace "Wai ashe bacci nayi, to mun fasa zuwa ne" jinjina mata kai yayi ba tare daya kalleta ba yace "Yea, time d'in ya wuce yanzu ina abu ne", kaman zatayi kuka tace "to ai ba laifina bane tunda da sassafe nazo kaine baka fito ba ka ganni ba har bacci ya kwashe ni", " Yanzu laifi nane kenan tunda ni nace kiyi bacci ko?" ya d'ago ya kalleta tai narai narai da idanu har kwalla ta fara taruwa,

" Saboda ba sayar da su ake ba shiyasa da kin so sai ki zubosu without any strong reason, baki tsoron su k'are?" yay Maganar idonshi akanta aikuwa kaman tana jira kawae sai tasa mashi kuka harda shashsheka, bud'a ido yay alamar mamaki sai kuma ya mik'e ya d'auki laptop d'in ya maida ita dakin daya daukkota bayan ya fito wurin tv ya nufa ya daukko tissue box yazo gabanta, yagowa yay ya mik'a mata bayan ya kira sunanta ta d'ago idanunta sun d'an yi ja gashi duk ta 6ata kwalliyarta, fuskarshi a sake cikin cool voice dinshi yace "Wipe ur tears, ina maki wasa ne ai yanzu zamu tafi dama am just waiting for u to wake up" hannu ta mik'a ta amshi tissue ta fara goge idonta tanayi tana d'an kallonshi ganin ya kafeta da ido, " Zan sha ruwa" ta fad'a a sanyaye, " Owk " ya furta kafin ya aje box d'in kan c-table ya juya ya nufi inda fridge yake, bottle water da lemu fanta ya d'aukko ya dawo ya mik'a mata ta amsa tace ta gode, bud'e ruwan tayi ta d'an sha har zata aje yace su tafi dashi ko zata bukata ta amsa da to, daga haka yace zasu iya tafiya ta mik'e tabi bayanshi, yana gaba tana biye dashi suka fito harabar gidan, bata yi tunanin zuwa gaida hajiya ba don tasan ba lalle inta tashi ba, bayan sun hau mota sun fitane ya kira wata mai suna Nana a waya ya tambayeta wurin salon mai kyau tace zata turo mashi Address d'in mai yi masu yay rejecting call d'in bayan yace mata thanks, ba wani 6ata lokaci ta turo mashi ya duba dama bai aje wayar ba tana hannunshi, aje wayar yay ya dan juya ya kalli Fatuu da tunda suka fito batai magana ba ta kwantar da kanta tana ta kallon hanya ta glass d'in kofa, maida idonshi yay kan hanya yaci gaba da driving bayan wani d'an lokaci suka k'araso wurin wanda bene ne dauke da jerin manyan shaguna a sama da kasa, acan gefen benen ya hango shagon da aka turo mashi mai dauke da sunan MAMAN ABDUL BEAUTY SALOON, hayewa yayi sama ya parker motar acan gaban shagon tun kafin ma ya kashe sai ga wata mata mai kiba tana sanye da doguwar rigar atamfa mai gajeran hannu kanta daure da kallabi ta nufo Motar da sauri fuskarta dauke da fara'a da gani an sanar mata game da zuwan su ne, daidai lokacin da suka bud'e Motar ta k'araso tana ta faman washe baki cike da girmamawa tace ma haisam " U'r welcome sir, Nana told me about ur coming" jinjina mata kai yay ta shiga gaidashi tana ce mashi ya ibada, dama itama musulma ce amman bayerabiya ce, bayan sun gama gaisawa ne yay mata bayanin yadda yake son gashin yayi amman bai son asaka mata relaxer, da sauri tace mashi kar ya damu hakan aikinta ne zata yi mata yadda yake so insha Allahu, kallon Fatuu tayi dake tsaye jikin kopa tace su shiga ciki, saida ta gaidata kafin ta bar jikin kopar ta rufeta har zata bita ta juyo ta kalli haisam tace " Ya Handsome kai bazaka shigo ba?" girgiza mata kai yay yace "kije zan jiraki cikin mota" jinjina mashi kai tayi ta juya matar na tsaye ta kama hannunta suka nufi shagon, komawa yay cikin motar ya rufe, kwantar da seat din yay ya d'an kwanta yana cigaba da sauraron karatun Alqur'anin da dama tunda suka taho ya kunnashi, Bayan kaman minti goma sha biyar da shigar su Fatuu cikin shagon kawae sai gata ta fito da gudu kanta duk an nad'a mata rollers yayi kaman an kifa mata d'an kwando, tana fitowa matar ma ta biyo bayanta da yar sassarfa don bata iya yin gudu saboda kiba a yadda ta biyotan sai kace giwa ta biyo yar akuya, side d'in driver ta nufa lokacin idanun Haisam na a lumshe saidai yaji ana kokarin bude kopar, da sauri ya ware idanunsa koda yay arba da Fatuu ba arziki ya tashi zaune ya fara kokarin fitowa daga cikin motar don har ta bud'e kopar, tun kafin yace wani abu matar ta riga cewa "Sir, she refuses to stay in d dryer" maida idonshi yay kan Fatun dake ta hura hanci ta kumburo baki lokaci guda takaici ya rufeshi, kallon matar yay yace taje kawae ta amsa mashi da okey kafin ta juya, kallon kallo suka shiga yi da ita yama rasa mi zaice kawae sai ya juya ya tada seat d'in motar ya shige tare da jawo kopar ya rufe, tsaye tayi awurin can kuma sai ta zagaya a d'arare ta bud'e kopar ta shiga ba tare da ta rufe ba, shiru tayi tana binshi da ido ya d'age kanshi sama ya lumshe idanunshi, bayan wani lokaci ganin bai tanka mata ba yasa ta kira sunanshi "Ya Handsome" shiru bai amsa ba hakan yasa ta k'ara kiran sunanshi sai lokacin yace mata taje su cire rollers d'insu tazo su tafi, jin hakan yasa tace " Fushi kai....." tun kafin ta k'arasa a fusace ya juyo yace "A'a ba fushi nayi ba tunda ni dutse ne, an gaya maki bani da abun yi ne da zaki sa in kawo ki wuri and ki k'i yarda ayi maki, ko kuwa ance maki bana jin azumin bakina ne da zaki sa in wahalar da kaina, tell me did i brought u here ba tare da amincewarki bane da zaki nemi tozarta ni!!" zaro ido tai jin yadda yake mata Magana a kausashe daga ji ranshi ya matukar 6aci sosae don ko lokacin da ya mareta bata ga irin bacin ran dake fuskarshi ba ayanzu,

" U are wasting my time Kije su cire abubuwan su don inada abun yi" ya sake fad'a a fusace aikuwa sai ta rushe mashi da matsanancin kuka acikin kukan ta fara fad'in "to ai ba hakanan nak'i yarda ba ko, ba ji nayi abun yana da zafi ba ni kuma ina tsoron kada ya guntile man kai tunda ai ban ta6a shiga irinshi ba ko, shine za kai ta man fad'a", still yay yana kallonta sai kuma da ta yi Magana ya tuna da wacece ya kawo wurin hakan yasa ya daidaita yanayinshi calmly ya kira sunanta cikin muryar kuka tace " Na'aamm",

" look at me Zarah" a hankali ta d'ago ta kalleshi fuskarta sha6e sha6e da hawaye, hannu yakai ya bud'e glove box ya ciro mata tissue yace ta goge fuskar, amsa tayi ta fara gogewa tana sakin ajiyar zuciya, " Do u think zan kawo ki inda za'a cuceki ne?" ya tambaya bayan ta tsagaita da goge fuskar, girgiza mashi kai tayi alamar a'a, "Then miyasa kike tunanin dryer d'in zai cire maki kai ne or what?" cikin disashshiyar Murya tace " to ai kai Namiji ne baka san ya abun yake ba" d'an girgiza mata kai yay yace "Nima ina dashi ai, amman nawa na hannu ne, yana busar da gashi ne kawae bai cire kai" d'an yamutsa fuska tai irin bazaka gane d'innan ba tace "to ai kace naka na hannu ne kaga ba irin wannan k'aton bane, shifa wani iska mai mugun zafi yake busowa" d'an Murmushi yay yace "Zarah duk d'aya ne ai, kawae iskan zai drying gashi ne ba zai cutar dake ba, kuma ko ni bansan irinshi ba ai Sisters d'ina na zuwa ana yi masu amfani dashi kuma bai ta6a cire ma wani kai ba saidae ya gyara gashin ya koma irin yadda kike so", " A can Abuja" ta tambayeshi ya d'aga mata kai alamar eh, shiru tayi ta kafeshi da runannun idanu hakan yasashi cewa " in baki so kije su cire rollers d'in sai mu tafi kawae" jin haka yasa tace "to amman ai fushi zakai?" tayi Maganar fuska a kwa6e,

" bazanyi fushi ba but bazanji dad'i ba saboda kin nuna kina sone na kawo ki and bazaki k'ara nuna kina son abu ba inyi maki" yay Maganar ba alamun wasa, ta6e baki ta fara yi tace "to bari inje ayi man" shiru bai tanka mata ba saidae idonshi na akanta, "Kaji" ta fad'a ganin baice komae ba, jinjina mata kai kawae yay ta juya zata fita sai kuma ta juyo tace " zafin bazai man komae ba dae ko" gyad'a mata kai yay ta sake juyawa ta fita daga cikin motar, shima fitowa yay ya d'aura hannuwanshi asaman Motar yana kallonta, nufar shagon tayi tana yi tana waiwayenshi ahaka har ta shige.......

ALBISHIRUNKU MATAN AFRICA DA KEWAYE SHAHARARRAR MAISAIDA KAYAN MATAN NAN WADDA KUKAFI SANI DA MAMAN HAIDAR TANA YIMAKU ALBISHIR DA CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE AFADIN NIGERIA DA NIJAR, KARKU MANTA MACE MAI GYARA BATA BORANCI💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃08040448621 Akwai zafafan kayan mata masu matukar kyau da arha cikin sauki zamu aika miki da kayanki cikin aminci da yardar Allah su isa har inda kike ba cuta ba cutarwa karku bari abaku labari. Muna kawo kalolin ingantattun kaya kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇 1-Maganin sanyi 2-Maganin gyaran nono 3-Maganin hips 4-Akwai gumba kala kala 5-Maganin matsi masu ciko da gaba ki koma kamar budurwa 6-Kalolin garirrika masu bawa mace ni'ima da jimawa ajiki yana aiki 7-Akwai tsumi sha yanxu magani yanzu 8-Akwai jigidar sirri kala kala Sannan kuma muna dahuwa kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇 1-dahuwar kaza 2-yan shila 3-ciccibi Dadai sauran su.Abubuwa dayawa gaskiya bazasu lissafu bah saboda lokaci maiso ta bini PC don ganin Kalolin kayan da muke dasu 08040448621, ALLAH YAYI MAKI KIMA DA DARAJA AMATSAYINKI NA MACE👰,KADA KI WOFINTAR DA KANKI A WURIN MIJI SABODA RASHIN GYARA KAI, BURIN MAMAN HAIDAR KO WACE MACE TA ZAMA TAURARUWA⭐YAR LELE AGUN MIJINTA😍 SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI🤝

*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖*

_A heart touching story of Love and Destiny_ 💔

*Mallakin* ⬇️ *🌹ZAINAB LALUH*📲✍ _~(Oummu imam)~_

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

5️⃣8️⃣

.…...Yana ganin ta shige cikin shagon yay wani murmushi dama tun farko yadda ta fito da kan yaso bashi dariya ta wani bangaren, komawa yay cikin Motar yaci gaba da jiranta,

Bayan wasu tsawon Mintuna sai gata ta fito gyalenta a hannu da gudu ta isa gaban Motar tasa hannu ta bud'e kopar gefen driver ta shige lokacin idanun Haisam na a lumshe, "Ya Handsome!" ta kirashi da karfin gaske dama yaji shigowarta kawae dae bai kalleta bane, a hankali ya ware eyes dinshi akanta, cike da farinciki ta juya masha bayan kanta tana nuna mashi gashinta daya sha gyara ya sauka sosae don har ya kai tsakiyar bayanta da gani harda stretching akai mata sai faman salki gashin yake, gyara zaman shi yay sosae fuskarshi d'auke da murmushi ya furta "yayi kyau" washe baki tayi sam ta kasa Magana saboda tsabar murna sai faman janyo gashin take ta gaba, suna cikin hakan Maman Abdul d'in ta k'araso bakin Motar, Haisam na ganinta ya bud'e kopar tun kafin yace wani abu tana ta fara'a ta tambayeshi gashin yayi yadda yake so ya amsa mata da yayi kafin ya tambayi kudin service d'in da sauri tace komi ya bada yayi, ba tare da ya k'ara cewa komai ba ya koma cikin Motar, glove box ya bud'e ya k'irgo kudi dubu goma Fatuu nata binshi da ido ya juya ya fita, a rude ta karbi kud'in lokacin da ya mik'a mata har da d'an duk'awa, sosae ta shiga yi mashi godiya tana fad'in "Thank u sir, May Almighty Allah increases ur wealth, May God bless u....." sai faman duk'awa take don ita kanta tasan bawae kudin aikinta bane ya bata kawai kyauta ce yay mata, shi dae jinjina mata kai kawae yay ya koma cikin Motar, kafin ya rufe ta lek'a da fara'a tace ma Fatuu tana jiranta ta k'ara zuwa tunda yanzu tasan Dryer d'in bai cire kai, kai fatun ta d'aga mata kawae ta juya ta nufi shago tana yi masu bye bye, yana Niyyar tashin Motar yaga Fatun na k'okarin bud'e mota ta fita ya tambayi lafiya, " zanje in daukko abunne", "Wani abu?" ya tambaya cikin rashin fahimta, "Shi abun yin, dryer sunanshi ko?" Bin ta da ido yay kafin yace "is it ur own?" " ai naga ka bata uban kudi ba siya kayi ba?" yar harara ya wurga mata ba tare da yace komai ba ya tashi Motar suka sauka kan titi yaja Motar suka tafi,

Tunda suka bar wurin ta kasa natsuwa acikin motar, gaba daya ta aje gyalen rigar ma sai faman d'oki take tana ta6a gashinta har hannu take kaiwa ta juyo da rearview mirror bayan wani lokaci sai yasa hannu ya juya shi yadda zai ga bayanshi, da taga yana juyashi sai ta sauke glass d'in kopar da take ta rink'a lek'a madubin wajen tana ta washe baki,

"Ki rufe shi ko wanda Grandpa d'inki yace sunyi maki fitsari su k'ara" taji ya fad'a ba tare daya kalleta ba, juyawa tayi ta kalleshi tana zare ido tace "Aljanu?" kai ya d'aga mata, " To ai banda su fa, in ma inadasu yanzu sun tafi", "In kinbar kan a bud'e ai zasu ga yayi kyau su dawo ko",

hannu tasa ta rufe baki sai kuma ta kai hannu da sauri ta d'auki gyalen rigarta tasa ta rufe glass d'in don dama Gwaggo na yawan ce mata in bata son rufe gashinta shed'anun Aljanu zasu hau mata su shige jikinta,

Readers Also Read