Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh - Chapter 35
Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh Chapter 35: Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh Chapter 35. A daidai wata k'atuwar Plaza ya juya kan Motar ya…
4,227 words
A daidai wata k'atuwar Plaza ya juya kan Motar ya shiga, can gefe guda ya parker Motar bayan ya kashe yace mata ta fito, wani katon shago mai d'auke da sunan Zee's Collection ya nufa tana biye dashi sai faman kalle kalle take, suna shiga wata wayayyar mata fara mai d'an jiki ba sosae ba kuma tana da dan tsawo jikinta sanye da bakar Jallabiya tayi rolling veil dinta ta nufo su da fara'a hakanne ya bayyana hakorin makkan dake bakinta, " The Big CoE, U'r welcome" fuskarshi da d'an Murmushi ya furta "thanks Zee" hannu ta mik'a ta nuna masu 2 seater leather sofa dake a shagon wanda yake dankam da kaya su laces, Atampopi, Materials harda dinkakku wato ready-made da kayatattun dogayen riguna, nufar kujerar yay ya zauna ta maida kallonta kan Fatuu dake ta bin shagon da kallo tace "Beauty ave a seat" kallonta tayi sai lokacin ta gaidata da fara' a ta amsa mata tace ta zaune, acan gefen Haisam ta zauna, "H,Zakee ya ibada" ta tambaya tana ta faman fara'a, "Alhamdulillah, Ya bussiness" " Alhamdulillah gamu munata kokartawa" jinjina mata kai kawae yay, Kallon Fatuu tayi tace "What's ur name?" "Zaraah" ta bata amsa "Sannu Fateema Zahra anata Azumi balle kisha ko ruwa" da sauri tace "ai banayi" d'an bud'a ido Zee tayi tace " bakya yi why?" "Ai bai zamar man dole ba saboda ban...." cakk ta kasa k'arasawa ta juya tana kallon Haisam da ya dan kishingida ajikin kujeran, lokaci guda Zee ta fahimci abunda zata ce hakan yasa tayi d'an Murmushi tace "to amman dae kinayi ko?" d'aga mata kai tayi "Eh, inna yi biyu sai in huta kwana d'aya" jinjina kai tayi tace gud, juyawa tayi ta kwala ma wata Esther kira sai gata ta fito yar matashiya ce da bazata wuce shekara sha biyar ba kuma tun daga kan shigarta da sunanta zaka gane ba musulma bace, tana zuwa ta d'an rankwafa ta gaida haisam da turanci ita kau fatuu sakin baki tayi cike da al'ajabi tana kallonta, abunda ya d'aure mata kai shine ganin kanta a aske kwal ga ba d'an kunne hakan yasa da farko tayi tunanin namiji ne sai kuma idonta ya sauka kan kirjinta dake dauke da breasts, Umarnin amso cake da lemu ta bata awani shago ta nufi hanyar fita Fatuu ta bita da kallo baki sake tace "kai! Wannan Namijine ko mace, kodae irin tane mata maza!" duk atunaninta acikin zuciyarta ta fad'i hakan bata san a fili tayi ta ba, Murmushi Zee tayi "ba Namiji bane Mace ne haka al'adansu yake" bin ta da ido kawae tayi lokacin esther d'in ta dawo ruke da leda mai dauke da abubuwan da kace ta amso, d'an durkusawa tayi taba zee tace mata ta kawo plate cikin inda ta fito ta koma sai gata ta dawo rike da plate d'in ta bata, fiddo cake d'in Zee tayi ta d'aura asaman plate d'in da lemun, da d'an Murmushi ta mik'a ma Fatuu ta amsa tace ta gode, a hannun kujera ta d'aura plate d'in ta fara ci bayan ta bud'e lemun, yar hira Zee suka ci gaba da yi da Haisam don kawarshi ce tare sukae Secondary school da ita sai dae ta d'an girmeshi, jefi jefi yake tanka mata Fatuu dai nata cin cake d'inta tana kurbar lemu, bayan wani lokaci ya duba wrist watch ganin lokaci ya tafi yace ma Zee ta duba mata kayan da sukae Magana ta amsa mashi da to kafin ta kalli Fatuu tace mata tayi sauri tazo ta za6i kaya, jin hakan yasa tai saurin tura sauran cake din gaba daya ta kwankwad'e lemun da sauri ta mik'e tace ta gama, Zee na murmushi ta mik'e suka nufi bangaren laces tace mata ta zabi wanda yay mata nan fa Fatuu ta zaro idanu tana tsuke baki ta fara bin kayan da kallo zee dae na tsaye agefe tana Murmushi, "Should i help u?" girgiza mata kai tayi tace "zan iya za6a" can ta nuna wani hadaddan swiss lace,
"Wow, gaskia kin iya za6e" Zee ta fad'a yayin da takai hannu ta ciro mata lace din, sosae Fatuu ta shiga washe baki tana juya lace din a hannunta can idonta ya kai kan price d'inshi dake manne ajikin ledan lace din, kura ma kudin ido tayi cikin rashin fahimta tace ma Zee "Wannan kudinshi ne?" kai ta d'aga mata alamar eh, " To..Naira nawa ne naga ansa 64..,dubu shidda da dari hudu yake kenan?" tana ta Murmushi tace mata "No, ki duba sosae dai how many zeros are there?" K'ara k'ura ido Fatuu tayi tana kallon kudin can ta dago a d'an firgice tace "zero ukku ne, kenan dubu sittin da hudu yake?" "Yea, haka ne kin fad'a daidai" tana rufe baki ta tura mata lace d'in sai kace wani mugun abu, cikin rashin fahimta Zee ta tambayi miya faru ne tana tura baki tace " banson shi yay tsada da yawa, ace kudinshi har yayi kudin dan shanu wannan ma ai Almubazzaranci ne" sai yanzu Zee ta gano dalili kuma Maganar shanun da tayi tasa ta fahimci bafullatana ce nan take ta yanke aranta k'ilan cikin yan'uwan H,zakee ne na Daura, cikin d'an lallami tace "ai isn't an extravagance, in kana da hali ba laifi bane don ka siya abu mai kudi sosae, kuma ai kinga lace d'in is very fine and unique" turo baki tayi tace ita dae bata sonshi,
Girgiza kai Zee tayi ta maidashi kafin tace to ta za6i wani, tambayarta tayi wanda basu kaishi kud'i ba ta nuna mata gabansu, wani Golden yellow mai sak'a Coffee brown ta nuna shima yay kyau sosae amman tun kafin aciro ta tambayi nawa yake, saida Zee ta d'anyi jimm kafin tace dubu 42, shima sai cewa tai yay kudi a nuna wadanda basu kaishi ba Zee ta nuna mata, wani blue mai kwalliya golden brown ta nuna tana washe baki alamar yayi mata don dama tana son blue har saida Zee ta sauke yar ajiyar zuciya don duk atunaninta shi zata d'auka amman koda ta ciro mata taga kudinshi dubu 34 sai tace shima bata so yayi tsada, lallashinta ta fara yi tace ta daukeshi kawae tunda tana sonshi kuma shi ai baiyi kudi sosae ba tunda kudinshi ma rabin na farkonne amman ta kafe akan yayi tsada shima, jagub zee tayi tana kallonta tana ta tura mata baki can ta tambayeta kaman na nawa take so ne tace kaman na dubu goma irin wanda gwaggonta ta siya mata waccan sallar, jinjina kai tayi tace to bata da irinshi gaskiya don ita laces d'inta masu kananun kudi duk sun kai 20k, tana jin hakan ta juya tana fad'in "bari in ma Ya Handsome Magana babu wanda nike so sai mu tafi wani wuri", Zee na jin tana niyyar yi mata asarar ciniki ta d'aga murya tana fad'in ya zatace ba wanda take so bacin duk gasu nan ta nuna, aikuwa tana yin Maganar sai a kunnan Haisam d'in dama hakan take so, tsam ya mik'e ya nufo su ya tambayi abunda ya faru Zee tayi mashi bayani, wani kallo yay ma Fatuu data tamke fuska, kallon Zee yay ya tambayi wanne ta nuna da farko aikuwa tana jin hakan tasa mashi kuka tana fad'in "Ni wllh bazansa wannan leshin ba don Almubazzaranci ne an fad'a mana a islamiyya, kudinshi fa sun kai na d'an shanu kuma ko gwaggo taji kudinshi wllh sai tayi fad'a, nidae banson shi don Allah Ya Handsome kar ka siya man shi" still sukai suna kallonta har fuskarta tayi sharkaf da hawaye gaba daya gyalenta ya zamo tana goge fuskarta yayinda Zee ke fad'in Masha Allah acikin zuciyarta ganin gashin kan Fatun, Sigh Haisam yay yasan halinta sarae tunda ta nuna bata so to fa yasan bata so d'in, umarnin suje su zauna ya basu ya fara duba kayan da kanshi, lace d'in data nuna tana so blue d'an dubu 34 shima shi ya d'aukko, sai atampa Chiganvy Gold mai shegen kyau, kiran Zee yay ta taso ya nuna mata kayan yace suje ta samo mata takalmi da veil da duk abunda yakamata kar ta k'ara tambayarta ta amsa mashi da toh, umarnin biyota taba Fatuu suka shiga kopar nan da wadda ta kira da Esther ta fito, suna shiga nan ma Fatuu sakin baki tayi tana kallo wurin don wani katon shagonne shake da takalma, jakuna, gyaluluwa, sarka da yan kunnaye, Undies Cosmetics harda English wears, akwae babbar kopar glass ta shigowa daga waje banda ta cikin d'ayan shagon, takalma golden da gyale guda biyu da jaka daya da zasu shiga da kayan ta d'aukko mata ta bata takalmin ta gwada wanda mai tsini ne amman heel d'in nada kauri kuma takalmin nada mad'auri, Jama'a kuzo kuga Fatuu cikin takalman sun mugun yi mata kyau ita kanta sai Murna take sai kace ba wadda ta gama kuka ba dama kuma tana son takalmi mai tsini amman gwaggo bata so shiyasa bata siya mata su sai mai tudu, sam bata ma tambayi su nawa suke ba saboda d'oki, sark'a da yan kunne da yan hannu gold plated ta daukko mata sai agogo, juyowa tayi don ta tambayeta ko akwae abunda take so kuma sai taga ta k'ura ido tanata kallon d'an mutum mutumin da aka sanya ma wasu had'addun wando jeans da riga sai kyalli suke ,
"Ko kina son su?" Zee ta tambayeta, maido idonta tai akanta tace "inaso amman fa ni ina jin tausayinshi ne banson sashi kashe kudi sosae saboda sai yayi wahala yake samunsu" ta k'arasa a marairaice, jinjina kai Zee tay da mamaki tace "ke waye ya fad'a maki sai yayi wahala yake samun kudi?" "Eh mana, ai ya fad'i man shi engineer ne rannan dana tambayeshi kuma yace man a filin jirgi yake aiki kinga kenan suke gyara jirgi in ya lalace in ma yak'i tashi su suke tura shi har ya tashi", bud'a ido Zee tayi sosae alamar mamaki sai kuma tasa Dariya tace "Yaushe H,zakee ya zama injiniyan jirgi kuma?" wuri wuri tayi da ido sai kuma tace "ko bashi bane?", girgiza mata kai tayi "yea bashi bane, shi Kwararran Computer engineer ne, he knows both the hardware and software da duk abunda ya danganci computer dae sosae, kuma yana samun kud'i sosae don yanzu we're in a Digital world so kullum cikin samun kud'i yake gashi Dad nashi ma mai kud'i ne sosae ke baki san Babanshi bane, ba yar'uwarsu bace?" da sauri Fatuu ta girgiza mata kai "a'a ni ba yar'uwarsu bace bafa makwabciyarsu ce",
" No wonder dat's why kike cewa kina jin tausayinshi, to bari kiji in zai siye maki kayan shagonnan duka ba abunda zaiji kuma dukiyarshi bazatai ko gezau ba, a Abuja fa baki ga tangamemen gidansu ba gari guda in kika shiga zaki manta kina a Nigeria ne kuma bashi ne kadai gidansu ba don ko anan garin a GRA suna da wani katon gidan hadadden gaske..."
"Ke kin ta6a zuwa gidansun ne?" Fatuu da tayi kasak'e tana sauraronta ta tambaya, " Yea sosae, don nasan yan gidansu suna siyan kaya awurina kuma wani lokacin ni ke kai masu in naje Abujar, yanzu haka akwae Sisters dinshi a Whatsapp group dina kuma suna fallowing handle ena na instagram da sunga kaya suna so zasu siya ne, akwae ma Stepmom dinshi da suke ce ma Aunty ita bata dad'e da auran dad dinshi ba, ita dama to tun kafin ta auri Senator d'in nasanta don yar Daura ce yar'uwarsu ce itama sosae take siyan kayana kuma wasu kyauta kawae take dasu, so su haka suke, yin babban Alheri ba wani abu bane a wurinsu, in ke kin k'i suna yi ma dubban Mutane gara ma kiyi amfani da damanki ki d'auki duk abunda ranki ke so" sauke ajiyar zuciya Fatuu tayi tace to ta bata kayan, juyawa zee tayi tana d'an girgiza kai ganin yadda tasata uban bayani kafin ta amince, wasu riga da skirt na jeans masu kyau ta daukko mata, rigar fara ce tana da ta sama kalar skirt d'in ta nuna mata wata kopa tace ta shiga change room ne ta sanya sai aga in sunyi mata, ba wani 6ata lokaci ta sanyo kayan don dama doguwar riga ce ajikinta,sosae kayan sukai mata kyau kuma sunyi mata daidai dama skirt din irin wanda bai kaiwa can k'asa ne, wasu riga da wando ta sake daukko mata har sunfi na jikin mutum mutumin kyau tace ta gwado su suma, cike da zumudi ta amshi kayan ta nufi dakin, suma bata dau wani dogon lokaci ba wurin sa su, lokacin data fito cikin jeans da shirt d'in har saida Zee ta furta Tubarkallah a fili ba tare da shiri ba don ba k'aramin amsar jikinta kayan sukai ba, babban abunda yaba Zee mamaki shine ganin yadda k'ugun Fatun ya fito sosae cikin wandon duk da kananun shekarunta amman hips ne da ita sosae, da alama dae Maganar gwaggo ta tabbata da tace da alama irin jikin mahaifiyarta gareta,
Cike da Murna Fatuu ta nufi hanyar fita d'ayan shagon tana fad'in bari ta nuno ma Ya Handsome ba tare data jira mi Zee zata ce ba ta fice saidae tabi bayanta, tunda ta fita ta kwala mashi kira ya d'ago daga kan wayar da yake latsawa ya kalleta, tana ta washe baki ta nuna mashi kayan jikintan da hannu, bud'a ido yay ya d'age gira alamar mamaki, "Nayi kyau ko?" ta tambaya cike da zumud'i, jinjina mata kai yay alamar eh ai sai ta fara d'an tsalle gashinta dake zube a bayanta yana d'an watsowa har ta gefen fuskarta ita dae Zee na atsaye gefe tanata Murmushi, can tace mata tazo suje su ko sa gama don an bar Haisam d'in nata zaman jira, bin ta Fatuu tayi suka koma ciki suna shiga taci gaba da Murna tana ta ta6a jikinta,
" I think u also need dis" Zee ta fad'a yayin da takai hannu ta ciro wata yar k'aramar bireziya ta mik'o ma Fatuu, ai koda idanunta sukai arba da ita da sauri kamar wadda shock ya ja ta matsa baya tana zare ido, "Kina bukatarta itama" Zee ta fad'a, da sauri ta girgiza mata kai "a'a ni bani sa ta, kawae so kike ace man yar iska", yar dariya tayi "to mu da muke sawa duk yan iska ne kenan?" turo baki tay "ai ku abunku manya manya ne" "To ai muma da kaman nakin ya fara mana kuma tun lokacin ake fara wearing nata",
" to ai dana isa sawa gwaggota zata siya man ne", "Inaga ita gwaggon naki bata san yakamata ki fara sawa bane tunda baki sa irin wannan dress din ba agabanta, look at ur nipples yadda suke showing fa, haka kika je gaban Ya Handsome din naki da naji kina fad'a har kina tsalle" shiru tayi tana ta turo baki ita ala dole bata son sa bra d'in hakan yasa Zee ta kama hannunta ta kaita gaban katon mirror dake a shagon, "Look at ur chest very well, ko da breasts d'in basu da girma kiga yadda nipples dinki suka bayyana sosae" tayi Maganar tana nuna mata abunda take magana akai ta cikin Mirror d'in, aikuwa da sauri tasa hannu guda ta rufe bakinta alamar al'ajabi d'ayan hannun kuma ta kare kirjinta dashi alamar kunya,
"Yanzu kin gan abunda nike Magana ko, in kina sa bra din baza'a rinka ganinsu ba", Fuska akwa6e Fatuu tace " to kuma gwaggota fa, kar ta bugeni in ta ganni dashi fa", da sauri Zee tace "No bazata yi maki komae ba, kice mata mai shagon da aka kawoki ce tace kina bukatarta", jinjina kai tay "to amman in bata yarda ba zansa Ya Handsome ya kawo ni in maido maki abunki" d'aga mata kai tayi alamar ta yarda daga haka ta shiga nuna mata yadda zata sa bra d'in har ta fahimta sannan tace taje ta gwada, tana shiga d'akin gwadawar Zee ta girgiza kai a fili ta furta "in kana sana'a kaga Mutane kala kala ( haka ma Rabiu Mai kayan marmari ya fada🤣),
" Aunty a wane karfe ne kika ce zan makala ma?" Fatuu ta tambaya da d'aga murya, d'an matsawa tayi yadda zata jita tayi mata bayani yadda zata sa tace in taji ta matseta ko ta mata yawa sai tai adjusting karshe ta tambayi ko ta gane, da sauri tace "Nagane karki shigo" dariya Maganar taba Zee ta girgiza kai kawae ta koma kan stool d'in data taso ta zauna can sai gata ta fito ta maida rigar sai faman kakkare kirjin take, mik'ewa Zee tayi ta nufota tace ta cire hannun don taga intayi mata, da farko k'iyawa tayi saida tace mata to ba kina da riga ba sannan ta cire hannun, dubawa tayi taga tayi mata das ta kuma tambayeta lafiya lau breasts d'in sun zauna aciki batayi mata yawa ba, cike da jin kunya ta d'aga mata kai hakan yasa ta kamo hannunta ta sake kaita gaban mirror ta nuna mata yadda yanzu ba'a ganin nipples d'in nata ita dae dan Murmushi tay don duk jinta take wani iri ta takura, umarnin taje ta cire kayan tayi mata, bayan ta curo harda bra d'in ta saka jallabiyarta ta kawo mata kayan duk aka zuba su acikin k'atuwar leda, wata bra d'in Zee ta k'aro mata tace ta saka ta hannunta aciki don dama tana ahannunta ta dunkuleta, k'in sakawa tayi saima ta d'aukko d'ayar da aka saka tace wai bata so Ya Handsome ya gani, Zee tace to ai inta ruk'e a hannune zai ma fi gani sai kawai ta cusa su can cikin hammata ta mak'alesu, ba yadda Zee bata yi ba akan ta kawo a saka acan k'asan kayan amman tak'i wai ai zai iya duba kayan kuma ya ganta, k'arshe dole ta kyaleta suka fito d'ayan shagon,
"Allah ya yi mun gama" Zee ta fad'a yayin da ta tunkaro Haisam da Murmushi, d'ago kai yay ya kallesu fuskarshi a sake, agabanshi ta aje kayan tana kokarin bud'a mashi ya dakatar da ita ta hanyar mik'o mata card yace ta cire kud'in kawae, saman wani d'an table dake d'auke da littafi da wasu yan takardu ta d'aukko Pos machine tasa card d'in, tana kokarin mik'o mashi don yasa pin kawae sai taji ya fad'i mata Pin d'in yace ta k'ara 20k sama tasha ruwa har saida ta d'an ware ido kafin tayi mashi godiya, Fatuu kuwa sakin baki tayi tana kallon yadda take fidda kudin ga kuma mamakin ance ta k'ara har dubu ashirin duk uban cinikin da akayi mata, tana sake da baki har bata san lokacin da bra guda ta fad'o ba, jin abu ya sauka kusa da kafarshi ne yasashi kai idonshi kasa ya d'an janye kafar kawae sai ga yar bireziya ta fito daga kasan rigar Fatun, kauda kanshi kawae yay ba tare da yace komae ba ita kam bata ma san abunda ke faruwa ba, kaman ance Zee ta kalli k'asan taga bra d'in yashe k'asan tiles bud'a ido tai ta kalli fatun suka had'a idanu, da kai tai mata alamar ta kalli k'asa hakan yasa tai saurin duk'ar da kai, ai koda tay arba da yar bra dinta sai ta wani zabura ta kwalalo ido ta d'ago tana kallon Zee dake yar dariya ta d'an rufe bakinta, juyawa tay ta kalli Haisam dake still azaune ta k'ura mashi ido duk ta sha jinin jikinta sai zare ido take, a hankali ya d'ago ya kalleta suka had'a idanu aikuwa a rude ta ida sakin d'ayar bra d'in ta nufi hanyar fita da gudu.........
ALBISHIRUNKU MATAN AFRICA DA KEWAYE SHAHARARRAR MAISAIDA KAYAN MATAN NAN WADDA KUKAFI SANI DA MAMAN HAIDAR TANA YIMAKU ALBISHIR DA CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE AFADIN NIGERIA DA NIJAR, KARKU MANTA MACE MAI GYARA BATA BORANCI💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃08040448621 Akwai zafafan kayan mata masu matukar kyau da arha cikin sauki zamu aika miki da kayanki cikin aminci da yardar Allah su isa har inda kike ba cuta ba cutarwa karku bari abaku labari. Muna kawo kalolin ingantattun kaya kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇 1-Maganin sanyi 2-Maganin gyaran nono 3-Maganin hips 4-Akwai gumba kala kala 5-Maganin matsi masu ciko da gaba ki koma kamar budurwa 6-Kalolin garirrika masu bawa mace ni'ima da jimawa ajiki yana aiki 7-Akwai tsumi sha yanxu magani yanzu 8-Akwai jigidar sirri kala kala Sannan kuma muna dahuwa kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇 1-dahuwar kaza 2-yan shila 3-ciccibi Dadai sauran su.Abubuwa dayawa gaskiya bazasu lissafu bah saboda lokaci maiso ta bini PC don ganin Kalolin kayan da muke dasu 08040448621, ALLAH YAYI MAKI KIMA DA DARAJA AMATSAYINKI NA MACE👰,KADA KI WOFINTAR DA KANKI A WURIN MIJI SABODA RASHIN GYARA KAI, BURIN MAMAN HAIDAR KO WACE MACE TA ZAMA TAURARUWA⭐YAR LELE AGUN MIJINTA😍 SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI🤝
*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖*
_A heart touching story of Love and Destiny_ 💔
*Mallakin* ⬇️ *🌹ZAINAB LALUH*📲✍ _~(Oummu imam)~_
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
5️⃣9️⃣
.......Bayan ta gama fitar da kud'in har ya mik'e sai kuma yace yana son atampopi guda ukku, Zee ta tambayeshi kaman wane kala yay mata bayani ta d'aukko mashi, sunyi kyau sosae tasaka mashi biyu a leda daban sai d'aya ma a leda daban kaman yadda ya buk'ata, bayan ya k'ara bata card d'in ta fitar da kudinsu atare suka fito daga cikin shagon yana ruk'e da babbar leda guda ita kuma ta ruko mashi guda saida ma tace ya bari Esther ta kai mashi yace ba wani abu, suna fitowa bakin shagon yace ta bashi d'ayar ledar ta koma, duk yadda taso ta kai mashi yace ta barshi kawae, sallama sukai tana tayi mashi godiya har tana cewa ya isar da sak'on sallamarta ga Zarah yace Ok, lokacin da ya iso bakin Motar back door ya bud'e ya saka ledojin kafin ya rufe, d'aga kanshi yay yana d'an kallon wurin da alama Fatuu yake nema, ganin bai ganta bane yasashi tunanin k'ilan ta shige cikin Motar, zagayawa yay da nufin shiga ciki kawae sai ganinta yay a duk'e jikin Motar, tana jin motsinshi ta d'ago suka had'a ido aikuwa da sauri ta sunkuyar da kan tana turo baki, d'an ta6e baki yay ya bud'e Motar zai shiga ganin bata tashi bane yasashi dakatawa yace mata "kina son in take ki ne?" jin hakan yasata mik'ewa sumi sumi ta zagaya d'ayan side d'in maimakon ta bud'e kopar ta shiga sai kawae tai tsaye a bakinta, ganin bata shigo ba bayan ya shigan yasashi sauke glass d'in kopar gefen nashi da d'an d'aga murya kad'an yace "zan fa barki a wurin", jin hakan yasa takai hannu a hankali ta bud'e kopar ta shiga tana ta sussunar da kai takai hannu ta rufe kopar, tashin Motar yay suka bar cikin Plaza d'in, tunda suka hau hanya batace uffan ba a hankali take satar kallonshi yanata driving idanunshi akan hanya, jin shirun nata yay yawa yasashi d'an juyawa ya kalleta daidai itama ta saci kallonshi suka had'a ido, kasa janye idanun nata tayi tana ta yamutsa fuska kaman zatayi kuka hakan yasashi d'an sakin Murmushi aikuwa kaman tana jira ta fara fad'in "Wllh Allah bani na d'auka ba fa, itace ta bani tace wai ina bukatarta kuma saida nace mata ni bani sawa amman ta matsa in d'auka kuma dama nace mata in gwaggota ta hana zaka kawo ni in maido mata kayanta" d'age gira yay kafin ya juya ya kalleta itama lokacin kallonshin take yadda ta wani kwa6e fuska ne yasashi sakin kayatacciyar dariyar dake Matuk'ar k'ara mashi kyau ba kamar daya kasance hakoranshi na gefe gefe sun d'an yi tsini daga k'asa, tana ganin dariyar da yake kawae sai ta fashe da kuka ta fara rantsuwar Allah ba ita tace tana so ba, ganin da gaske ta tashi hankalinta ne yasashi daina yin dariyar Calmly ya kirata "Zaraah" amsa mashi tai "uhhuym" cikin muryar kuka ba tare data kalleshi, "Is Okey, ai ba wani abu bane taga kina bukatan ne dat's why ta baki", Wani kallo tayi mashi baki kumbure kaman zata kai mashi bugu, d'an juyawa yay ya kalleta suna had'a ido sai kawae gani tai yayi mata Murmushi aikuwa sai ta k'ara kware baki tana fad'in " ni wllh ba yar iska bace bani nace ta bani ba ko"
"Who said dat? Kinji na fad'i hakan ne?" Cikin muryar kuka tace "ba gashi nan kanata min dariya ba" "Owk, na bari calm ur mind" d'agowa tay don da ta d'age kafafunta sama ta cusa kanta ne, " isn't something to worry ur self about, kin reaching stage na amfani dashi ne so ba wani abu bane ai" "To ai na baro su kuma" ta fad'a da disashshiyar murya, juyowa yay ya kalleta fuskarshi sake kaman zaiyi Murmushi aikuwa sai ta fara yayyarfa hannuwa tana fadin "ni ka daina man dariya to" daure fuska yay yace "kinga yanzu na maki wannan ne?" kallonshi tayi ganin fuskar a daure yasata girgiza mashi kai alamar a'a, maida idonshi yay kan hanya yaci gaba da driving, "Ya Handsome to mu koma a daukko kar muyi nisa" ta fad'a a d'arare, shiru yai kaman bazai ce komae ba sai kuma ya daga ido ya kalleta ta cikin mirror suka hada ido, "an saka maki a kayanki " taji ya fad'a wai kuma sai ta sunkuyar da kai alamar kunya, d'an Murmushin gefen baki yay ya dan girgiza kanshi yaci gaba da driving dinshi ba tare daya k'ara ko kallonta ba itama bata k'ara cewa komae ba.