Kenza eBookz

Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh - Chapter 37

Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh - Chapter 37

Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh Chapter 37: Asanadin makwabtaka book 1 by zee laluh Chapter 37. Washe gari ya kama saura kwana biyu salla, tunda ta…

4,376 words

Washe gari ya kama saura kwana biyu salla, tunda ta farka ba walwala a tare da ita komae sukuku take yinshi don Maganar ta tsaya mata arai, taci burin cin gayu suyi yawan salla tare dashi ya kaita wurare, gwaggo ta lura da yanayinta kaman akwae abunda ke damunta ba kamar data zauna gida bata je gidan hajiya ba hakan yasa ta kirata a d'aki ta tambayeta mike damunta ne (har an shirya kenan🥰) da farko ce mata tayi ba komae gwaggon tace ai in ba komai bazata ta6a ganinta haka ba dole akwae abunda ke damunta hakanne yasa ta fad'i ma gwaggo Hajiya ce zasu tafi Abuja ba anan zasu yi salla ba, "To dama wannan karonne ta fara tafiya Abuja salla" gwaggon ta tambaya da mamaki, "A'a nasan tana zuwa, amman wai fa harda Ya Handsome za'a tafi kuma da shi naso ya kaini yawon salla" ta fad'a fuska a kwa6e, jinjina kai gwaggo tayi jin wani karfin hali awurin fatun tace "to tunda bawanki ne ai sai ki hanashi tafiya gidan babanshi yin salla ya tsaya ya bauta maki tunda ke shashasha ce" turo baki tayi kaman zatayi kuka, can bayan wani lokaci a marairace tace ma gwaggon wai ko tace ma Hajiya zata bisu, aikuwa tun kafin ta rufe baki gwaggo ta hau zazzaga mata fad'a tana fad'in ahirr dinta karta sake taji hakan in ba haka ba ranta zai 6aci ne, duk da da hajiyar ke tafiya da ita dama ake zuwa ne, sosae ta 6ata ma gwaggo rai k'arshe ma tace ta tashi ta bata wuri kuma da taji ance za'a Abuja da ita to tasan ita tayi Maganar atafi da ita kuma wllh daga can tana dawowa Yola zata tafi tunda ita komae sai tasa rashin hankali, lokacin data koma d'aki kan gadonta ta fad'a tana share kwallar da suke zubo mata ita dae hakanan bata son yin salla ba tare dasu ba. Da rana Wuraren karfe sha biyu Hajiya ta kira waya tace Fateema tazo ga Balaraba nan ta kusa gama mata kitso sai ayi mata itama, lokacin da gwaggo ta sanar mata tana tura baki tace ita dae bata son ayi mata kitso tunda an gyara mata gashi gwaggo na jin hakan tace to taje da kanta ta fad'i ma hajiyan hakan, lokacin da ta shiga falon Hajiyar har angama mata kitson tana ganin yanayin Fatun ta tambayeta lafiya ko duk azuminne tace mata a'a bata jin dad'i ne, hajiya na jin hakan ta yarda don duk ranar sai lokacin taje gidan wanda lafiya lafiya tasan bazata k'i zuwa ba, tace to anma yi mata kitso kuma bata jin dad'i fatun tace a'a abarshi tunda Ya Handsome ya kaita an gyara mata gashin, daga haka tayi mata sallama ta nufi hanyar fita hajiyar nayi mata Allah ya sawak'e harda Saude dake jiran itama ayi mata kitson da Balarabar ma,

_____________

"Zaraah" taji an kirata lokacin har ta kai gate d'in gidan tana niyyar fita, a hankali ta juya ta kalli haisam dake fitowa daga cikin corridor d'in part d'inshi da alama Masallaci zaije don an fara kiran salla, d'an matsawa tayi kafin taja ta tsaya ya k'araso gabanta yana kallonta, "Ina wuni" ta fad'a asanyaye, shiru bai amsa ba sai cewa yay "mike damunki ne" ya tambaya ganinta sukuku kuma yasan ba azumi ne yasata hakan ba don yanzu sam ta daina korafin azumi har ukku ukku take yi ma, "Am i not talking to u?" ya fad'a da d'an d'aga Murya, maimakon tayi mashi Magana sai kawae tasa mashi kuka hakan kuma yasashi Fahimtar tabbas akwae abunda ke damunta, "Kije part d'ina ki jira ni" ya fad'a yayin da yake wucewa ya nufi Masallaci, "Baki ji bane" ya sake fad'a bayan ya dakata ganin bata tafi ba, a hankali ta wuce part din nashi, ana gama sallar ya dawo yana shiga falon ya isketa tana yin salla dama hijab ce ajikinta kuma d'akin da ta ta6a zuwa yin fitsari taje tayo alwala, zama yay kan kujera ya d'auki remote ya fara canja Channel, zaune tayi kan Carpet bayan ta gama ta sunkuyar da kanta kasa,

"Unhum am all ears, miye ne?" taji ya fad'a idonshi akan tv, shiru tayi tana wasa da yatsun hannunta don tsoron fad'i mashi take saboda gargad'in da gwaggo tayi mata, aje remote d'in yay ya maido hankalinshi kanta a hankali ta d'ago suka had'a ido ganin kallon da yake mata ne yasa ta fara motsa baki amman ta rasa mi ma zata ce mashi, "Kina sani abubuwan da bana so Zarah, i think i ave told u since banason maimaita mgn right?" ya d'age mata gira, d'aga mashi kai tayi alamar eh, "Ok ina jinki" Cikin en ina ta fara Magana "da..daman naji ba anan zakuyi salla ba Abuja zaku tafi" Shiru kaman bazaice wani abu ba sai kuma yace "yea, akwae matsala da hakan?" girgiza mashi kai tayi "a'a, kawae dai nayi zaton anan zakuyi saboda ina son muyi yawan salla tare da kai", bud'a ido yay jin wata Magana mai nuna tsantsan yarintarta, d'an Murmushi yay gently yace "ni ai bani yawon salla Zarah"

"Eh ina nufin ka kaini wurare dama, don duk salla ba inda nike zuwa in ba nan cikin Unguwar ba sai gidan wasu yan uwanmu yan kad'an" jinjina kai yay "Ko zaki bi mu Abujar ne?" ba zato ba tsammani taji ya fad'a aikuwa arud'e ta d'ago tana girgiza mashi kai alamar a'a, ya lura da razanar da tayi da jin abunda yace hakan yasashi tambayarta dalilin k'in bin nasu, farko shiru tayi sai kuma ta tuna da baison maimaita Magana hakan yasa kaman zatayi kuka ta fad'a mashi yarda sukae da Gwaggo harda rantsuwar da tayi na daga can tana dawowa sai Yola, shiru yay yana nazarin Maganar tabbas bai kamata ya gifta rantsuwar da tayi ba don yasan tana da dalilin hakan wanda bai wuce k'ok'arin da take yi na saita Fatun,

"Owk tunda ta rantse shikenan ba sai kin bimu ba but ki daina damuwa kan yawon sallan zan sa akai ki duk inda kike so in ma ta hana i will talk to her" d'agowa tai ta kalleshi ya d'age mata gira "are u Happy now?" jinjina mashi kai tayi alamar eh, "To baki smile ba" ya fad'a fuskarshi a sake, da bud'ar bakinta sai cewa tayi "dama ina wannan ne?" wato abunda yace mata rannan itama ta fad'i mashi aikuwa ya jefo mata throw pillow yana fad'in kin raina ni da yawa Zaraah, duk'ewa tayi tana dariya hakan kuma ba k'aramin dad'i yay mashi ba don shi sam bai son yaga Mutum na k'unci duk sai yaji ya damu shiyasa in dae yana da iko yin yadda zai sa Mutum farinciki sai yayi, shiru su kai na wani lokaci can ta kalleshi idonshi akan tv, "Naga an kawo man dinkin jiya" kai ya daga ba tare da ya kalleta ba, "Nagode" jinjina mata kai yay sai lokacin ya kalleta tana ta wasa da yatsun hannunta, "Baki yin kunshi ne da salla" taji ya fad'a, Turo baki tay "da gwaggo ke yi man irin na hausa nan da ake d'ansa Salatef ni kuma yanzu banson tayi man irinshi nafi son irin wanda ake yayi a yayyanka salatef d'in ayi design mai kyau da kuma bak'i da ake zanawa" ta k'arasa tana kwatanta mashi wanda take nufi a hannunta, d'aga mata kai yay alamar ya fahimta ya maida idonshi kan tv, bayan wani d'an lokaci ya d'auki wayarshi yai dialing kira ya karata a kunne, wadda ya ta6a kira mai suna Nana lokacin da zai kaita saloon ita ya k'ara kira, yar wurin aikinsu ce zatayi tsararshi sai dae bata yi aure ba har yanzu amman ba zaune take ba tana ta aikinta da bussiness kuma tana jiran Allah ya kawo mijin (da duk masu neman mijin aure Allah Ubangiji ka albarkace su da mazaje na gari masu wadatar zuci wadanda zasu sosu su kuma ruke su saboda Allah ba don wani abu ba haka ma mazan, masu aure kuma ka kara zaunar damu lafiya da mazajenmu ka k'ara rufa mana asiri ka Albarkaci zuri'armu, Amin ya hayyu ya kayyum, ban mance da masu neman haihuwa ba Allah ubangijin samai da kasai mai ikon akan komae wanda da yace kun faya kun (kasance sai ya kasance (wani al'amari) ka albarkace su da samun zuria d'ayyiba Amin),

suna mugun yin good time dashi dama kuma ita d'in yar barkwanci ce tana d'aya daga cikin Mutanen da ke sashi dariya ba tare daya shirya yin ba, kai tsaye take fad'i mashi itafa Mugun sonshi take ya taimaka mata ya shige da ita mana wato ya aureta, bayan ta d'aga kiran sun gaisa yace yana son ai ma Sister nashi henna ne tace ba matsala in zai yuwu ya kawota gidansu da safe mai kunshi zata zo yi masu sai ayi mata, amsa mata yay da owk daga haka yai rejecting call d'in, kallon Fatuu yay da ta k'ura mashi ido bayan ya aje wayar yace ta tambayi Grandma d'inta zai kaita k'unshi gobe da safe around 10 tace to, mik'ewa yay yace mata yana jin bacci ta d'aga mashi kai ya nufi Bedroom dinshi ita kuma ta koma kan kujera ta d'auki remote ta canja channel zuwa Bollywood ta kishingida tana yin kallon ahaka bacci yay awon gaba da ita, sai da akai la'asar ya fito don zuwa Masallaci ya ganta kwance tana baccin ta dukunkune cikin hijab d'in jikinta, babbuga kujera yay ta bud'e ido yace ta tashi taje gida tayi salla daga haka ya fuce bayan yaga ta mik'e itama.

Washe gari jajibirin salla kaman yadda su kai dashi karfe goma tazo part d'in nashi tana sanye da riga da skirt na atamfa ta yafa gyale dama tun jiyan ta sanar ma gwaggo ba 6ata lokaci suka fito don tafiya gidansu Nanar, lokacin da suka hau hanya zasu wuce k'ura ma lungun gidansu Haulat ido tai Haisam din na kallonta ta Mirror "ko zaki je da ita ne" taji ya fad'a lokacin har sun wuce lungun, kallonshi tay ta d'an d'aga mashi kai alamar eh ba tare daya ce komae ba ya juya Motar suka nufi lungun gidansu Haulat din, abakin lungun ya tsaya bai shiga ba don ba tanan ne hanyarsu ba, ce mata yay taje ta kirata ta amsa da to ta fito, lokacin data shiga gidan ba kowa a tsakar gidan sai yan kannenta k'anana suna wasa hakan yasa ta nufi d'akinsu Haulatun, akwance ta isketa kan yar katifarsu ita da kannanta guda biyu da suma suke yin azumi sunata bacci, gefenta ta durkusa tasa hannu tana tada ita bayan ta farka ta tashi zaune Fatuu ta gaya mata ta taso za'a kaisu kunshi yanzu, tambayarta tayi wanda zai kaisu tace Ya Handsome, d'an jimm tayi tana tunanin anya za'a barta kuwa don da yau da daddare zasuyi na salatef, tana cikin tunanin taji muryar innarsu tana k'wala mata kira hakan yasa ta mik'e ta fita Fatuu ma tabi bayanta, gaishe da ita tayi ta amsa mata da fara'a cikin in ina haulat ta sanar da ita batun zuwa kunshin, da farko k'in amincewa tayi tace in ta tafi waye zai tayata aiyuka tunda tasan karshenta sai yamma koma dare zasu dawo don dole su iske layi sosae saida Fatuu tayi mata bayanin cewa ba gidan kunshi za'a kaisu ba gidan wasu yan uwan Hajiya ne nan mai kunshin zata zo, d'an jimm tayi haulat din ta marairaice fuska tana rokonta kan ta barta bazata dade ba in ma taga za'a kai yamma to zata dawo Fatuu ma ta tayata rokonta sannan ta amince suje, cike da farinciki sukae mata godiya haulat din ta nufi d'aki kaya kawae ta canja don ba lokacin yin wanka suka fice,

Lokacin da suka isa gidansu Nanar dake a Kopar Marusa lowcost wanda da gani suna da hali ba laifi, kiranta yay a waya yace mata sunzo ba tare da 6ata lokaci ba Nanar ta fito, yar gajera ce mai k'iba bata da haske sosae saidae baza'a kirata da bak'a ba don akwae yanayin hutu a fatarta, daka kalleta zaka gane wayayyar yar boko ce tana sanye da kaftan ta atamfa ta yafo gyale asaman kai don bata da kallabi, cikin fara'a sosae ta tarbesu bayan ta gama gaisawa da haisam din ta jasu ciki tace in an gama zasu yi waya, sosae ta shiga haba haba dasu haka ma yan gidansu harda Mahaifiyarsu a mutunce suka kar6esu don tun kafin suzo tayi masu bayanin wadda za'a kawo kunshin saboda ba wanda baisan Haisam ba agidan sosae yake yi masu Alkhairi don wani lokacin shi ke maido Nanar gida in sun tashi daga aiki in bataje da Motarta ba suna ganin Fatuu suka yanke cewa itace kanwar tashi duk da Haulat ma sam ba mummuna bace sai dae yanayin fata, batare da 6ata lokaci ba bayan angama ma wadda suka iske anayi mawa aka fara yi ma Fatuu bayan an gama mata akai ma Haulat lokacin har azahar tayi, ba k'aramin had'uwa kunshin yay ba na salatef da kuma zane dayake ba mutum d'aya ce keyi ba akwae mai kama mata nan da nan aka gama, sosae suka rink'a yaba kunshin ba kamar na Fatuu daya fito sosae kasantuwarta fara, har kitso Nanar ta tambayeta in tanaso ayi mata don da ana kunshi kallabinta ya cire sunga gashinta sosae suka rinka santinshi cikin ransu tace mata bata son kitson dama ita Haulat ta riga tayi kitson sallan, bayan sunyi sallar Azahar a d'akin Nanar Fatuu tace mata ta kira ya handsome ta fad'i mashi yazo ya daukesu an gama tace bazasu bari su sha ruwa ba a gidansu ta fad'i mata ance haulat ta koma kafin yamma ne, bayan ta kirashi ta sanar dashi ba'a d'auki wani dogon lokaci ba sai gashi ya kirata yace yana waje, kayan shafa harda turare dasu Popcorn da gullisuwa irin wanda Haisam ke ba Fatun ta basu kowa ledarshi daban daman a wurinta ne Haisam din ke siya, a tare suka fito falo sukai ma yan gidan sallama har mamarsu Nanar na cewa basu tsayawa su sha ruwa Nana tayi mata bayanin ana jiran d'ayar ne kafin suka wuce ana tayi masu bye bye,

Suna fitowa Nana ta nufi gaban Motar ta kwankwasa Haisam d'in ya bud'e kopar har yayi wanka ya canja kaya jeans da t-shirt, zuro kafarshi yay guda fuskarshi a sake suka sake gaisawa, juyawa tayi ta kalli su Fatuu da sukayi tsaye gefe tace tazo ta nuna mashi kunshin mana, matsowa tayi ta hade hannuwanta tana nuna mashi harda na kafafunta, dan Murmushi yay yace mata ya gani yayi kyau ita dae haulat na tsaye tana ta Murmushi, maida kallonshi yay kan Nana ya tambayeta nawa ne kudin aikin, " Ka barshi ni zan biya" girgiza mata kai yay alamar bai yarda ba, d'an farr tayi da ido tace "kaji zakee baka son na biya ma k'annen nawa ne?" Murmushi yay yasan halinta sarae in ya biye mata sai taita jan Maganar hakan yasa ya kai hannu cikin Motar ya d'aukko wallet dinshi, kud'i ya kirgo yan dubu dubu sabbi fill (da alama dae haisam bai kashe tsoffin kudi), mik'a mata yay amman sai taki Kar6a tace "tunda baka son na biya masu to ka rike na biyo ka bashi zan amsa", Cikin Cool voice d'inshi cike da tsokana yace "naki ne boyfriend dinki ya baki ki biya henna dinki kema" yana rufe baki ta saki wani k'arajin Murna ta zube kan gwuiwowinta, d'aga hannuwanta tayi sama tana fad'in " Allah Amin, Allah ka bani balaraben nan dama wani jinkirin alkhairi ne, kun ya Allah" tunda take mashi Maganar soyayya sai dai ya d'anyi mata Murmushi kawae yau ne kadae yayi mata Maganar data danganci hakan tunda ya bata kudi yace nata ne saurayinta ya bata duk da tasan wasa yake itama kuma kaman Comedian take ta cika ban dariya, su kuwa su Fatuu mi zasuyi in ba dariya ba ganin yadda ta durkusa k'asa dama gata yar 6asukuta shi ma Haisam Murmushi yake ta yunk'ura ta mik'e tsaye, mik'a mata kudin yay tasa hannu da sauri ta kar6a tana fad'in "dole in kar6i wannan babbar kyauta daga Muradin Zuciyata, kasan fa Zakee in dae ka aure ni sai nayi wata ina azumin godiya ga Allah sannan kuma inyi kyauta da duk abunda na mallaka, to mi zanyi dasu Allah na tuba na samu miji d'aya tamkar da miliyan" juyawa tayi ta kalli su Fatuu tace "ko baku so ya aure ni?" waro ido Fatuu tayi tana dariya Allah yaso dae bata ce komae ba don tana ganin wasa Nanar take, itama haulat dariyar take, girgiza kai Haisam yay ya furta "Nana u are too much" daga haka ya maida kafarshi cikin Motar yay ma su Fatuu alamar su shigo da hannu, tana ta d'aga masu hannu ya tashi Motar har zai tafi tai mashi alamar ya tsaya da hannu, sauke glass yay bayan ya dakata ta d'an lek'a tace ma Fatuu tana jiransu su zo mata yawan salla suka amsa mata da to daga haka tace ma Haisam masoyi asha ruwa lafiya, saida suka bar kopar gidansu sannan ta shige gate din gidansu.......

ALBISHIRUNKU MATAN AFRICA DA KEWAYE SHAHARARRAR MAISAIDA KAYAN MATAN NAN WADDA KUKAFI SANI DA MAMAN HAIDAR TANA YIMAKU ALBISHIR DA CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE AFADIN NIGERIA DA NIJAR, KARKU MANTA MACE MAI GYARA BATA BORANCI💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃08040448621 Akwai zafafan kayan mata masu matukar kyau da arha cikin sauki zamu aika miki da kayanki cikin aminci da yardar Allah su isa har inda kike ba cuta ba cutarwa karku bari abaku labari. Muna kawo kalolin ingantattun kaya kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇 1-Maganin sanyi 2-Maganin gyaran nono 3-Maganin hips 4-Akwai gumba kala kala 5-Maganin matsi masu ciko da gaba ki koma kamar budurwa 6-Kalolin garirrika masu bawa mace ni'ima da jimawa ajiki yana aiki 7-Akwai tsumi sha yanxu magani yanzu 8-Akwai jigidar sirri kala kala Sannan kuma muna dahuwa kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇 1-dahuwar kaza 2-yan shila 3-ciccibi Dadai sauran su.Abubuwa dayawa gaskiya bazasu lissafu bah saboda lokaci maiso ta bini PC don ganin Kalolin kayan da muke dasu 08040448621,

ALLAH YAYI MAKI KIMA DA DARAJA AMATSAYINKI NA MACE👰,KADA KI WOFINTAR DA KANKI A WURIN MIJI SABODA RASHIN GYARA KAI, BURIN MAMAN HAIDAR KO WACE MACE TA ZAMA TAURARUWA⭐YAR LELE AGUN MIJINTA😍 SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI🤝

*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖*

_A heart touching story of Love and Destiny_ 💔

*Mallakin* ⬇️ *🌹ZAINAB LALUH*📲✍ _~(Oummu imam)~_

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

6️⃣1️⃣

.......Saida suka hau hanya ne ta nuna mashi abubuwan da Nanar ta basu ya jinjina kai kawae daga haka kuma suka yi tsit ba wanda ya k'ara tankawa don rana tayi Azumin ya fara bugu, lokaci bayan lokaci take d'an d'aga hannunta ta kalli k'unshin da aka yi matan, a daidai lungun gidansu Haulatu aka sauketa tayi ma Haisam godiya ya jinjina mata kai kawae tace ma Fatuu sai sun had'u anjima daga haka ta tafi, a kopar gidansu ya parker ta juya ta kalleshi tana Murmushi tace "thank u so much Sweetheart Ya Handsome", sigh yay kafin slowly yace "U'r Welcome Sweetheart Yar Fillo" waro ido tay tasa tafin hannunta guda ta rufe baki alamar mamaki don tunda take ce mai Sweetheart bai taba maido mata ba yace mata hakan sau yau,

"Ya Handsome nima inada kirki ne kace man haka?" ta kafe shi da ido alamar jiran amsa take, shiru ya d'anyi kafin ya furta "U'r my sis", "kana sona kenan tunda na zama kanwarka?" lumshe mata ido yay alamar eh, yar Dariya tayi tace "Nima ina sonka Ya Handsome" jinjina kai kawae yay yace ta shiga gida, bud'e Motar tai ta fito bayan ta rufe kopar ta fara d'aga mashi hannu tana yi mashi bye bye har saida taga ya tafi sannan ta shige gidan, a tsakar gida ta iske gwaggo nata aiki ga kwandon cefane da kaji an aiko masu daga gidan Hajiya dama tana basu sai dae basu kai yawan na wannan karon ba wanda ba sai an fad'a ba kowa yasan aikin Haisam ne, basu kadai bama har makwabta tana basu kaji da Sallah don suna da k'atuwar gona mai suna ZAKEE's FARM wadda Mahaifin Haisam d'in suka gada awurin mahaifinsu Gen. Adamu, an zuba ma'aikata sosae dake kula da ita banda dabbobi, kaji tsuntsaye har kifi ake kiwatawa aciki dasu zuma Allah yasama gidan gonar Albarka, duk wani kwai da suke amfani dashi suke rabawa kuma da azumi da kaji daga gonar suke,

Lokacin da gwaggo taga k'unshin bayan Fatuu ta nuna mata sosae ta shiga washe baki tana yabawa har zolayarta tayi tace itama da zata samu da an zana mata Fatun na jin hakan tace wai bari tayi ma Ya Handsome Magana aikuwa ba arziki gwaggo ta kwa6eta tace ita wasa take yau da daddare zata k'unsa abunta yadda ta saba, hutawa ta d'anyi sai can bayan la'asar ta fito kama ma gwaggo aiki saboda da ta dawo ta isketa tanata uban aiki don ma tuwon shinkafa kawae zatayi da kanta sai waina da alkubus wanda ta bada ayo mata kaman yadda ake yi yanzu a sauk'ak'e akwae wad'anda sana'arsu ce da hidima ko sallah sai ka kai kayan abincin da kake so ayi maka ka biya kai kuma sai kayi miyarka da kake so, itama gwaggon miya kala d'aya zatayi wadda za'a iya cin duka abincin da ita,

ba abunda Gwaggo ke fad'a a fili da kuma cikin ranta face ALHAMDULILLAHI dama kuma kullum bakinta bai gushewa da fad'in hakan koda kuwa ba yadda taso abu ya kasance mata ba, kuma fad'ar Allah (SWT) ce idan ka gode mashi zai k'ara maka haka idan kayi takawa ya kasance ka kiyaye dokokin shi, yayi alkawari zai baka mafita a kowane irin al'amari sannan ya azurtaka ta hanyar da baka ta6a tunani ba, shiyasa ake so bawa ya kasance mai mik'a dukkan al'amuranshi ga Allah kuma ya kasance mai yawan gode mashi a koda yaushe to tabbas kuwa zai rink'a ganin bud'i kala kala (Alhamdulillahi ala kulli halin), gaba d'aya Azumin nan Gwaggo zata iya k'irga nawa ta kashe kud'inta don kuwa ba wasu kud'i masu yawa bane, ko su d'inkin salla da sauran siyayyar da ta yi masu duk cikin kud'in da tay niyyar siya ma Amadu freezer ne, ga Amadu yayi cinikin k'ank'ara sosae a haka ma don makwabta kyauta ake basu kuma sam basu cika mata kud'i ba kamar yadda wasu Mutane ke d'aura buri kan kankara cikin Azumi suyi ta saida ita da mugun tsada sai kace suma ba Musulmai bane suna yin azumin sun kuma san yadda mai azumi ke tsananin bukatar kankara, A maimakon su saukaka sai su tsawalla, A nan nike son jan hankalin masu saida kankara da suke tsawwalawa acikin Azumi da kuji tsoron Allah, kusani duk wanda ya ji tausayin Mutane ya rangwanta masu shima Allah zai tausaya masa akasin haka kuma kaima Allah bazai tausaya maka ba hadisi ne ingantacce, ba kuma iya masu kankara ba harda masu hali wannan ma ya shafe ku, wani sai kaga yana da hali amman har ya iya barin makwabcinshi ya kwana da yunwa wa'iyazubillah, saboda ba kyakkyawar alakar da d'aya zai iya sanin halin da d'aya ma ke ciki, sam wasu basa kiyaye hakkin makwabtaka wani ma ko cikakkiyar gaisuwa bai iya tsayawa yayi da makwabcinsa don yana ganin yin hakan tamkar alfarma ce yay masa, akwae hadisai da dama da sukae magana kan makwabtaka, Misali akwae wanda Manzo (SAW) yace, Mala'ika jibrilu bai gushe ba yana man wasiyya akan makwabci har nake tunanin idan na mutu makwabcina zai gajeni, haka akwae hadisi ingantacce da yay Magana kan duk wanda yay imani da Allah da ranar tashin Alkiyama to ya karrama makwabcinsa, amman sai kaga an koro yaran makwabci daga Makarantar da suke saboda littattafai ko Uniform kodae wani abunda bai kai ya kawo ba amma makwabcinsa nada hali bazai iya taimaka masu ba suna ta gararan ba acikin unguwa ko ajikinshi bai damu ma da ya tambayi dalili ba balle har ya taimakesu shi nasa yaran suna a Makarantu masu tsada har takai ta kawo wani fa ko rage ma yaran makwabcinsa hanya a Motarsa bai iya yi ya kaisu Makaranta yana kallo uban zai kama hannunsu yakaisu bakin titi don hawa abun hawa amman k'arshe saidae ya sakar masu horn ya wuce, ko kuma yaga yaran kan hanya suna d'aga mashi hannu alamar gaisuwa bazai iya tsayawa ya daukesu ba, abubuwan takaici dai da yawa wanda in nace in bayyanasu to fa har sai littafin nan ya idasa k'arewa ba tare da angama fad'in komae ba, Yakamata mu gyara masu hali ku rinka jin tausayin maras hali duk min yadda kake akwae wanda bai kaika ba so ko d'an yaya Allah ya bud'a maka kaima ka taimaki wani sai kaga an rage ma juna radadin talauci ba kaman a halin da muke ciki yanzu da babu tayi ma Al'umma yawa, kowa ya rinka kokarin ganin yasa farinciki ta hanyar yaye ma wani damuwarsa matuk'ar kana da halin hakan, kowa dae karshensa Mutuwa ce ko Mutum ya k'i ko ya so, duk kuma abunda ka mallaka dole anan gidan duniya zaka barshi su zama mallakin wasu, wad'anda suka aikata ayyukan Alkhairi Fisabilillah da dukiyoyinsu ne kadae zasu cigaba da cin moriyarsu ko bayan Mutuwarsu, ALLAH Ubangiji kayi mana Arziki mai amfani ka bamu ikon taimakon juna Amin.

Sosae Fatuu ta taya Gwaggon aiki saidae bata yarda tayi aikin da zata ta6a ruwa ba sosae wai kada lallenta ya fice tun kafin sallan, zuwa dare sun kammala komae har kajin sun soya anyo markad'en miya an tafasa shi sai zuwa da Asuba za'a idasa had'a miyar ta kuma tuk'a tuwon, ana gama Sallar isha aka sanar anga wata don haka baza'ai sallar asham ba hakan yasa fatuu ta nufi part d'in Hajiya don ta nuna mata lallenta, suma sosae sukae santinshi ita da Saude anan kuma Fatun ta tambayi Hajiya ya akai basu tafi Abuja ba gashi gobe salla tace mata Haisam ne yace su tsaya sai sunyi salla gobe sai su wuce, dama ita hajiya tana son yin sallar anan Senator ne ke matsa mata take tafiya daren sallah ko saura kwana biyu sallah, sosae Fatuu taji dadi don tasan tare zasu je sallar idi Gobe.

GOBE SALLA, GOBE💃💃

Readers Also Read