Kenza eBookz

Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature - Chapter 15

Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature - Chapter 15

Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature Chapter 15: Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature Chapter 15. "Ai kuwa ba zuba mashi ido za'ai ba k'ato dashi…

4,210 words

"Ai kuwa ba zuba mashi ido za'ai ba k'ato dashi yay ta zama ba mata yakamata a nema mashi tunda shi baida Niyya, Akwae k'anwar wadda D'an uwan nashi zai Aura ita yakamata a nema mashi" duk suka yi murmushi sai lokacin Sameer d'in ya d'aga ido ya kalli Senator da yay Maganar bakin shi ya d'an d'aga kad'an wai a hakan murmushi yay shima na mamakin jin shi za'a had'a da mata, can sai ma ya mik'e don baison kallonshi da ake d'agowa anayi ya nufi upstairs yana taka staircases d'in cike da isa suma sunga ta kansu, duk bin shi sukai da ido Haisam dae d'an murmushi yay cikin ranshi yana imagining yadda zaman Aure zai yiwu tsakanin Sameer da Farha, kuma abunda basu sani ba shine yana da yan mata kawae ra'ayin Auren ne baida shi, bayan sun gama shima Haisam upstairs din ya haye part d'inshi nan ya iske Sameer d'in kan gado yana latsa waya dama duk in yazo a part d'in Haisam yake sauka yana shiga wayarshi ta fara ringing Amarya tay kira bayan ya d'aga tace tana son suyi Video call ya amsa da Ok kafin yay connecting da laptop d'inshi dake kan bedside suka fara magana akan program d'in gobe da za'ayi a Lagos duk abun nan ko kallonsu Sameer bai yi ba tamkar bai ma jin abunda suke can Fanan tace waye a bayanshi yace mata Sameer ne tace bari su gaisa, d'an janye jikinshi yay ya juya yace zasu gaisa ko tanka shi bai ba har saida Fanan d'in tace"Hi Sameer!" sannan ya d'an juya ba yabo ba fallasa ya bita da ido saidae yanayin fuskarshi ya d'an canja a hakan wai murmushi ne yay mata tana murmushi tace "hope u'r coming to Lagos 2morrow" D'an jinjina mata kai yay kawae daga haka ya maida kanshi kan wayar Haisam ya juya suka cigaba da Magana kafin daga baya sukae sallama ya juya ya kalli Sameer ya kai hannu ya kwace wayar yana fad'in bari yaga abunda yake da ya janye attention d'inshi ya kasa sakin jiki ya gaisa da bride d'inshi sosae, d'an d'age bakin dae yay Haisam ya kai idonshi kan screen d'in wayar da sauri ya d'aga kai yay mashi wani kallo Sameer d'in ya d'age mashi gira sigh Haisam yay yace "Bro stop decieving people and ur self Just get married" wani guntun murmushin gefe yay ma sha Allah ashe k'ilan yasan kyaun da yake in yay murmushi shiyasa bai cika yi ba shima dae yana da dimples kaman Haisam d'in saidae nashi biyu ne mik'ewa yay ba tare da ya ce mashi komae ba walking majestically ya nufi hanyar toilet, aje mashi wayar yay ya d'aura kanshi akan pillow yana son ya kira Fatuu yaji halin da take ciki amman yana ganin kaman dare yayi can dae ya kai hannu ya d'auki wayarshi yay sending mata kira baiwar Allah lokacin tana kwance kan gado tayi lamo don ta kasa bacci sai tsumayen kiranshi take don kwana biyu kullum da wayarshi take bacci tana haka taji ringing alamar kira da sauri ta kai hannu tana ganin shine tay murmushi kafin tay picking ta kifa wayar a Kunnenta,

"Zaraah" a hankali tace "na'am ina wuni" amsawa yay yace ya akai batayi bacci ba tana murmushi tace hakanan baccin ne bai zo ba, d'an murmushi yay kawae ya tambayi ya take tace mashi lpy lou daga haka suka ci gaba da wayar yana cikin yi Sameer ya fito k'ugunshi d'aure da towel ya nufi press sai lokacin ya juya ya kalli Haisam lokaci guda ya gane da mace yake Magana jin ya ambaci Zaraah cikin husky voice d'inshi don ba irin muryarsu d'aya ba yace "U what do you think u'r doing, ain't u deceiving??? Wani kallo Haisam d'in yay mashi shi kuma ya ta6e baki ya juya yana kokarin sa short da sauri Haisam ya juyar da kai don yasan ba kunya ta ishe shi ba kimono yasa iya gwuiwa ya d'auki laptop d'inshi ya fice daga bedroom d'in ya nufi Parlor, sosae suke fira har yake ce mata gobe su Abbas zasu zo he isn't happy da batare da ita za'a zo ba saidae tay murmushi kawae daga baya yace ta kwanta gobe akwae skul sukae sallama sai gashi kuwa tayi bacci bada jimawa ba.

Ana kiran sallan Asubar farko wayarta tay ringing har saida gabanta ya fad'i ganin lokacin da aka kiratan gashi bata san lambar ba, can dae ta d'aga tay shiru tana son jin waye ya kira on the Other hand taji an kirata da Zarah lokaci guda ta gane Abbas ne cikin muryar bacci ta amsa ta gaidashi yace gasu nan kopar gida a bud'e ma Feenah da sauri tace to ta saukko daga gadon, d'akin gwaggo ta nufa ta fad'i mata suka fito tare gwaggo ta nufi wajen taje ta bud'e Abbas ya fito yazo wurinta suka gaisa yace zai wuce Masallaci gasu Feenah nan zasuyi salla in ya dawo sai su wuce tace to ya juya Feenah ta shigo tana ruke da hannun Abdul ta rungume Nasreen gwaggo ta kar6eta Fatuu kuma taje ta kama hannun Abdul suka nufi d'akin gwaggo gaba d'aya bayan sun zauna suka shiga gaisawa Fatuu ma ta gaishe da ita tace "Allah sarki Zarah banji dad'i ba dake za'a ba wllh" Abdul ma yace "nima haka momy" ita dae d'an murmushi tay haka gwaggo ma Feenah ta sake cewa "Amman dae ba gida zaki zauna ke kadae ba ko" gwaggo tay saurin cewa "eh zata zauna a makwabta ne gidan kawarta da suke Makaranta d'aya" Feenah tace yauwa hakan yayi daga baya suka tashi jin an kira salla, bayan sun gama gwaggo tace kota dafa masu wani abu Feenah tace a'a bata iya cin abu yanzu amman akwae Abinci a Mota a hanya sai su ci, su Abbas da Amadu na dawowa daga Masallaci Amadun ya shigo ya fara fita da kayayyakinsu ba 6ata lokaci suka fito don tafiya gwaggo tace ma Fatuu ta d'aukko jakarta da uniform sai a ajeta gidansu Haulat, da tace zata zauna in safiya tayi saita shirya ta tafi Makaranta in ta dawo sai ta wuce can amman gwaggon ta k'i amincewa don gaba d'aya ma don ba yarda zatayi ne yasa zasu tafi su bartan, bayan ta daukko komae suka fita Amadu ya kulle gidan gwaggo tace ya ciri makullin guda yaba Fatun yace to, Amadu ne ya shiga gaba sai su kuma suka shiga baya Abbas na ganinta yace da ita za'a kenan gwaggo tace a'a za'a ajeta can gaba gidan da zata zauna yace Ok yayinda a ranshi yake jin wani irin tausayinta in ba so da rashin Adalci ba ya za'ai ace Mom Zarah bata je bikin Haisam ba da ranta da lafiyar ta, a daidai bakin lungunsu Haulat aka ajeta duk jikinta yay wani iri gwaggo tace taje ganin tayi tsaye rungume da jaka cikin breaking voice tace " Allah ya kiyaye hanya ya kaiku lafiya...." Da sauri ta juya jin tana niyyar fashewa da kuka Abdul ya kwala mata kira ta juya ya fito da hannunshi yana mata bye bye itama ta d'an d'aga mashi sai kuma Feenah da gwaggo har da Amadu suma suka d'ago suna yi mata kawae sai ta juya ta fashe da kuka saida suka ga shigarta gidan sannan suka tafi, kopar Marusa low-cost suka wuce aka d'auki Nana kaman yadda Haisam ya ba Abbas sak'o sai fatan a sauka lafiya.

Tana shiga d'akinsu Haulat ta aje jakar gefe ta kwanta kan katifa ta rufe fuskarta da bakinta tana ta kuka, haulat dake gefenta tana ta bata hak'uri itama kaman zatayi kukan har saida wata k'anwar haulat taje ta gayo ma innarsu ta shigo tana fad'in "Fatima ya da kuka kuma da girmanki don an tafi unguwa an barki ai kaman gobe ne zata dawo ko haba daina kuka k'annenki nata kallonki sai suyi maki dariya ma" jin hakan yasa ta sassauta kukan, da gari ya idasa wayewa da k'yar haulat ta samu tasa ta tashi suka fara shirin tafiya Makaranta bayan sun gama aka kawo mata abun kalaci biredi da kosai da tea don Haulat ta fad'i ma innarsu Fatun bata shan koko, bata wani ci da yawa ba tace ta k'oshi haulat taitai da ita ta k'ara ta kafe akan ta k'oshi amai take ji dole ta kyaleta da aka kai ma innar tasu tace suje su ci, k'arfe bakwai da rabi suka fito suka iske innar a yar barandar da take sana'ar koko haulat tace zasu tafi har ta k'irgo kud'i zata basu cikin disasshiyar murya Fatuu tace ta barshi gwaggo ta bata kud'in da zasu rink'a yin break innarsu haulatun tace kuma dae banda wanda ta bata, godiya tay tayi masu a dawo lafiya kafin ta k'ara ba Fatuu hakuri suka tafi, jikinta sukuku suka nufi bakin hanya wai kuma sai take jin dama ta bisu don kwata kwata ta rasa mike mata dad'i a haka suka k'araso bakin titi bada jimawa ba sai ga School bus suka tafi.

Tafiya yankin Azaba,Amadu sai dae ya d'anyi bacci ya farka ya kalli hanya yayin da cikin ranshi yake ta Murna yau dae Allah yayi zaije Abuja, akan hanya suka samu wuri acikin wani gidan mai da bai aiki suka yi breakfast don Abdul nata kukan yunwa harda Nana don bata wasa da cikinta shiyasa gata nan tubarkallah, bayan sun gama suka sake d'aukar hanya aka dasa baka jin komae sai muryar Nana da Abbas dake ta hira abunsu don ita Feenah tafiya galabaitar da ita take sai jefi jefi take saka masu baki, Alhamdulillah Allah yayi an iso a Abuja wuraren Azahar, sakin baki Amadu yay yana kallon ikon Allah da kafin su shigo Abujar a garuruwan bakin hanya har yana ce ma Abbas dama haka Abujar take Abbas na dariya yace ya jira tukun kafin ya yanke hukunci, sakin baki yay sai faman kalle kalle yake kaman d'an kauye yazo birni Abbas na ta faman yi mashi dariya gwaggo ma dae bata ta6a zuwa ba amman bata nuna k'auyanci kaman Amadu ba don shi fa tsakaninshi da Allah a k'asar waje yake ganinshi ba kaman shimfidaddun tituna masu girma da bai saba ganin irinsu ba, ko ina titi haka yake ta fad'i can kuma yace wai ba Keke Napep ne da babura sai motoci kawae yake gani Abbas dae dariya kawae yake yace mashi akwae bangaren da keda akwae su nan dae inda suke babu, saida suka sake 6ata kusan awa Saboda go slow na Motocin ma'aikata kafin suka iso gidansu Haisam d'in, "Ya ilahi ya rabbil alamen" haka Amadu ya fad'a acikin zuciyarshi saidae baisan ya fito fili ba Nana ma cewa tay "kan uban nan!,wai anan Zakee ke rayuwa shine don cutar kai ya koma Katsina ya tsugunna" gaba d'aya ta basu dariya, gwaggo ma dai ta yaba ba abunda take fad'i sai "Ma sha Allah" da alama fa Amadu yay mutuwar tsaye don mamaki ya gama cikashi tunda uwar data haifeshi bai ta6a ganin gida irin wannan ba nan take ya fara jinjinawa hali irin na Haisam harma da yan uwanshi yadda basu d'auki Duniya da zafi ba, bayan Abbas ya parker Motar a wagegen parking spot d'in gidan mai d'auke da jerin jigunannun motoci duk suka fito Abbas ne ya hangi Nameer yana nufar Mota dake can gefe ya k'wala mashi kira ya juyo yana yin arba dasu ya washe baki ya nufesu, yana zuwa ya shiga gaishe dasu yana yi masu sannu da zuwa duk suka amsa Nana tace "yauwa mai kama da Zakee" still dariya yake ya kai hannu ya dafa shoulder d'in Amadu yace "Mutumina barka da zuwa" murmushi yay mashi wanda yafi kama dana yak'e yace mashi yauwa, Nameer d'in ya kuma cewa "Ya banga yar gidan ya Haisam ba mai kumatu?" Dariya duk suka yi gwaggo ta sanar dashi bazata samu zuwa ba Saboda jarabawa da zasu fara yace baiji dadi ba, Abbas yace "zaka wani wuri ne?" Yace "No bakin gate zanje akwae wadanda zan shigo dasu wai security sun hanasu shigowa" Abbas na dariya yace "Ok muma saida aka tantance mu, amman ya naga ansa security sosae lafiya dae ko?"

"Eh lafiya lou akwae na Momyn Nasarawa ne" D'an bud'a ido Abbas yay "kace her Excellency na nan ashe" kai ya d'aga alamar eh yace yaje bari ya shiga dasu Nameer d'in yace bari ya kai Amadu d'akinshi sai ya dawo ya d'aukar mashi jakar goyonshi Amadun na cewa ya bari ya d'auka yace ya bashshi ai shi bak'on shi ne suka nufi part d'inshi dake saman bene, ta baya suka bi don akwae benen da zai kaika saman Amadu dai na biye dashi zarare zarare tamkar rakumi da akala,

Suna akan hanyarsu ta shiga mai Entrance na gidan Nana ke tambayar Abbas wacece Her Excellency d'in data ji suna Magana don Mutum yay taka tsantsan, sosae Abbas yasa dariya kafin yay mata bayaninta harda alak'arsu da Haisam ita gwaggo dama tasan labarinta, suna shiga parlon sukae kacibus da Jidderh cike da Farinciki ta nufosu tana masu sannu da zuwa ta gaishe su duk suka amsa suna mata Murmushi Abbas yace ta kaisu wurin Hajiya tace to tay gaba suka bi bayanta har part d'in da Hajiya take, lokacin da ta gansu sosae tay murna sai sannu da zuwa take masu harda rungume gwaggo bayan sun gaggaisa da Mutanen dake a parlon nata ta jasu cikin bedroom tace su huta duk suka ce salla zasu yi, kafin su gama sallar an jere masu Abinci da abun sha suna gamawa suka hau cin Abincin don suna buk'atar shi, saida suka samu natsuwa sannan Hajiya tay masu jagora part d'in Mahaifiyar Haisam d'in lokacin duk suna zaune a k'ayataccen parlonta harda Hajiya Zainab da Auntynsu Haisam nan su Nana suka ga ikon Allah sun rasa gane wacece ma Mahaifiyar Haisam d'in har saida Hajiya tay masu bayani suma Matan gidan ta gabatar masu dasu gwaggon duk da sun santa Feenah ma ta ta6a zuwa sau d'aya wani zuwa da sukai da Abbas ya kawota suka gaisa Nana ce dae ba'a sani ba duk ta wani natsu sai kace ba ita ba, faram faram suka amshe su sunata godiya da Addu'ar Allah ya bar zumunci ita dae First Lady d'an murmushi kawae tay masu daga baya Hajiya ta koma part d'inta dasu,

Abbas na fita part d'in Haisam ya wuce anan ya iske shi da Sameer da Saleem dama shi yana a gidansu na Abuja, duk sunyi mamakin ganinshi don bai gaya masu sun iso ba last wayar da sukai da Haisam basu kaiga isowa ba hannu ya ba kowannen su suka gaisa harda Sameer don sun san juna ta dalilin Haisam daga baya yay joining nasu cin Abincin, Nameer na shiga da Amadu part d'inshi duk ya k'ara shan jinin jikinshi ganin kyawawan yan gayun samarin dake ciki harda yan Ethiopia bedroom ya wuce dashi nan ma dae ya iske wasu kyawawan guda biyu kan gado suna game a laptop cikinsu d'aya d'an Hajiya Zainab ne, Nameer ya kallesu da murmushi yace "Guys meet my Friend from Kt" d'aya ne ya d'ago yace mashi an zo lpy shikam d'an uwan Sameer d'in ko ci kanka bai ce ba da alama duk haka suke, Nameer ya lura da yanayin Amadu hakan yasa ya dafa shi yace "just feel at home" d'an murmushin yak'e dai kawae yay ya kai jakarshi cikin press kafin ya nuna mashi toilet yace ko zaiyi amfani dashi bari yaje ya shigo da mutanen yanzu zai dawo yace to Nameer d'in na fita ya shige toilet, farko jigum yay saman seat dake rufe hakanan duk sai yaji ya raina kanshi can kuma ya mik'e yay abunda zaiyi ya d'auro Alwala ya fito, yana fita cikin sa'a yaga basu saman gadon ashe yana shiga toilet Ashraf k'anin Sameer yace su koma d'akinsu nan ana interrupting nasu dama ba anan suke da zama ba shine suka fita, wani sanyi Amadu yaji ya fara kokarin gane inda gabas take saidae ya kasa dole ya zauna gefen gado har Nameer ya dawo d'auke da tray d'in kayan Abinci bawan Allah shi yaje ya amso mashi, tambayarshi gabas yay ya nuna mashi ya zauna ya jirashi har ya gama sannan yace ga Abinci nan yaci ya k'oshi bari yaje ya dawo aikuwa wa Allah ya had'a da Abinci ba Amadu ba sosae ya saki jiki ya kwashi gara ganin shi kadae ne a d'akin yana gamawa cike da karfin hali ya d'auki tray d'in ya fita bayan ya sauka k'asa ta baya cikin sa'a yaga d'aya daga cikin ma'aikatan dake aiki a babban Kitchen d'in dake bayan ta amsa tray d'in shi kuma ya juya ya koma upstairs yana shiga bedroom ya haye gado nan da nan kuwa bacci yay awon gaba dashi. Ana gama sallar la'asar masu tafiya Lagos suka fara shiri duk Abokan Haisam ne banda iyaye ko su Jidderh baza'a dasu ba sai dae Laila da Amal k'anwar Sameer itama kusan sa'ar Lailan ce da wasu daga cikin yan Ethiopia, haka Nameer ma banda shi da alama sha'anin na manya ne Jidderh harda kukanta taje ta fad'i ma Mom dinsu tana son zuwa don Allah tasa aje da ita tace tay hak'uri tunda ance baza'a da ita ba Hajiya Zainab tasa baki tace yakamata aje da ita itama ai yan mata ce da kanta ta kira Haisam tay mashi Magana akan a sama mata ticket itama sannan akace za'a tafi da ita, kusan su goma sha biyar harda Nana aka kaisu Airport wasu dama already suna can Najeeb ma acan ya sauka don bai k'asar, ba 6ata lokaci jirginsu ya tashi.

THIS IS LAGOS........

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 da 3 Naira 400 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wannan no 09013804524._

*ASM Bk2019*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

........Tuni jirginsu yay landing har an daukesu Matan na gidansu Fanan angwayen kuma na a Guest house d'in Dad dinsu Fanan nan da nan aka fara shirye shiryen event d'in da za'ai wato Indian Night, Misalin k'arfe Goma na dare aka fara d'aukar Mutane zuwa inda za'ayi wanda katafaren Hall ne acikin wani tsadaddan Hotel wanda na Mahaifin Fanan ne had'in gwuiwa da wasu Abokansa turawa, Wow! Wow!! Wow!!! Just Speechless abun ba'a cewa komae sai wanda ya gani Hall d'in ya k'awatu matuk'a kai kace a India ne koda yake indiyawan ne sukai decorating Hall d'in da taimakon Mommyn wata Friend d'in Fanan da suka yi karatu tare suma indiyawa ne amman a Lagos suke zaune duk ita ta tsara komae furanni kota ina, zuwa k'arfe 11 na dare duk an hallara Matan sun sha sari kala kala wasu masu wando wasu dogayen riguna wasu na nad'awa yayinda mazan ma ke sanye da nasu wanda yawanci fakistan ne na Maza, Farar fata kawae kake gani a wurin bak'ak'en yan k'alilan ne irinsu Abbas suma sai sukai kaman bak'ak'en indiyawa gashi dama Lagos badae fararan fata ba sun taru wurin sosae dama suna da wannan had'in kan sai dae basu ji ba har turawan duk shigan kayan indiyawan sukae can Ango da Amarya suka shigo Tubarakallahu ma sha Allah har saida Alk'alami na ya su6uce ba tare dana ankare ba saida zan ci gaba da rubutun na fahimci hakan, gaba d'ayansu shigan Red sukae Haisam na sanye da Pakistan riga red sai wandon golden brown haka takalmanshi ma red ne anyi masu adon golden brown tamkar na sarauta sumar nan tasha gyara sai salki take wuyanshi rataye da scarf irin wanda indiyawa ke sawa shima golden brown wohoho ba ka ta6a cewa ba ba'indiye bane tabbas da Fatuu tazo wurin nan zuciyarta na iya bugawa ganin ta rasa zuk'ek'en miji kamar Haisam yayin da Amarya Fanan aka sha rantsattsan Sari ja tun daga kafarta har wuyanta gwala gwalai ne ta fito sak ba'indiyyar Amarya masu Arziki don kuwa ba kananun kud'i bane a jikinta to d'iyar Hajiya Maryam face yar kasuwa ta kirki data san kaya masu daraja, su kansu kayan Haisam d'in da wad'anda Abokansa su Abbas suka sa duk daga India aka kawo su aka rarraba masu different colours and designs, a bayansu Haisam d'in su Hajiya Maryam ne dasu Laila harda kakarsu Fanan ta wurin uba baturiya da wasu daga cikin danginsu, su Farha ansha sari riga da wando yellow da fari sai faman yauk'i take, fuskar Haisam a sake suka shigo Fanan kuwa sai fara'a take fuskarta cike da tsantsan farinciki komae yayi mata yadda take so suna shigowa Friends d'inta suka hau watsa masu furanni, bayan duk an zauna an natsu MC wanda yake ba'indiye ne amman yana jin turanci sosae ya fara gabatar da abunda aka zo yi in yayi da indiyanci sai ya fassara da turanci, babbar kawar Amarya wadda mamanta ta tsara wurin ita ta fito tay ma kowa sannu da zuwa ta bada tarihin Amarya da indiyanci bayan ta gama sai khairat data sha sari maroon ta fito tayi da turanci bayansu sai aka bukaci babban Abokin ango Abbas ya fito cike da shak'iyanci ya bada da turanci yana yi yana kwa6awa da indiyanci gaba d'aya yaba Mutane dariya bayan ya gama aka kira k'awayen Amarya indiyawa harda khairat don da ita akai rehearsal d'in rawar da za'ayi aka sakar masu wak'ar indiya suka fara cashewa cikin gwanancewa ba tare da suna missing steps ba abun ba k'aramin nishadantar da mutane yay ba bayan sun gama aka bukaci Amarya da Ango su fito su taka Fanan ta mik'e dama ta shirya ma hakan amman sai Haisam d'in yak'i tashi don shi baya rawa balle kuma rawar indiya shi gaba d'aya program din ma baiso ba kawae don yaga tana so ne ya biye mata amman kuma shima abun ya k'ayatar dashi, ita kadae aka kunna ma wak'ar ta fara rawa a nutse tana yi tana zagaye haisam wani lokacin ta duk'a gabanshi ko ta sak'o kanta ta gefen kanshi kota d'aura fuskarta saman gashinshi yadda take bin wak'ar kai kace ita ta rairata sai k'arar sarkokinta ke tashi kowa sai murmushi yake saki hardae sarkin jin kai saida ya d'an murmusa wato Sameer, wak'ar na zuwa k'arshe ta kama hannuwan Haisam alamar ya mik'e ta rungume shi gaba d'aya aka sa tafi da sowa, haka aka ci gaba da gabatar da abubuwan nishad'i ana raba ma Mutane lemuna, har Abbas da Najeeb saida sukae rawa da yan Matan da sukae, oh su Abbas an yada mata a Abuja anata fantamawa🙄, can bayan wani lokaci aka bada damar cin Abinci kowa abunda yake so za'a zuba mashi yawanci duk Abincin indiyawa ne 6angare 6angare, Bangaren shinkafa akwae su chicken Briyani,Veg Briyani,Briesd beef rice,Butter chicken rice, bangaren kaji kuwa akwae su, Chicken Masala,finger chicken,chicken grilled,chicken prame, haka bangaren Salad akwae su Antipasto salad,chicken salad,crispy salad,ponir mix salad da sauransu dae haka lemun ma akwae su Orange juice,Apple,grape,pine apple juice da sauransu kowa saida yaci yay hani'an nima dae ba'a barni a baya ba naci na sha Alhamdulillah😋,wadanda suka ce bazasu zo ba kun ma kanku ai ☹️

Sai wurin biyun dare aka tashi kowa ya koma masaukinsa masu bacci sukayi masu hirar abunda akayi suka dasa, Washe gari kuma aka hau shirin komawa Abuja, kai Jama'a masu kud'i na abunda suka gadama dama iya abunda yasa aka zo Lagos d'in fa kenan🤔, Wuraren sha biyu wasu suka tafi yawanci Haisam ne da Abokansa dasu Nana da wasu daga cikin k'awayen Fanan d'in su kuma sai da akayi La'asar dasu Hajiya Maryam da dangin mahaifinsu lokacin sun gama duk wani shiri suka tafi don a Abuja hidiman take.

Suna komawa ranar aka hau shirin yin Ethiopian Night wanda Laila ta matsa sai anyi har Mahaifiyar Haisam d'in ma tana so ayi dole Haisam ya bada had'in kai ba yadda ya iya, bayan sallar Isha duk an gama shiri danginsu na Ethiopia dasu Laila su Jidderh harda su Amal Amarya Fanan da wasu daga cikin kawayenta duk sunyi shigar kayan gargajiya na Ethiopia wato habesha khamis kala kala duk dogayen riguna Matan suka sa farare masu adon golden mazan ma riga da wando ne farare sai gaban rigunan anyi adon golden, wasu adon maroon, green da sauransu har iyaye su Mahaifiyar Haisam d'in da Hajiya Zainab da sauransu ba'a barsu a baya ba abun ya matuk'ar bada citta su Fanan dasu Jidderh har iyayen duk anyi masu irin gyaran gashinsu ya bud'e d'innan kaman fanka, ba wani wuri aka je ba a cikin gidan akai program d'in anata d'aukar hotuna a wurare daban daban har a saman staircases suka jere abun gwanin k'ayatarwa daga baya aka ci aka sha, Washe gari Alhamis Arabian night akayi a tsadaddan Event center nan ma da taimakon danginsu Laraba aka tsara komae ya tafi daidai su Ango da Amarya dasu Abbas an sha shigan larabawa anci dabino ansha tea an kuma sha Fruit dasu Alkubzu can na hango wasu daga cikin yan Comment section su Bahillot,husnarh,Ma'ulee,munah bature,Boss bature,Bajatu,sis Asma,Maman Amir,habibty, shafa adili,Angel love,Aisha da sauransu dae anata kwasan saura ana ci ana zubawa a jaka wasu harda dabinon k'asa suke tsinta an fake da ba'a murna da bikin kuma anzo ana k'walama lol🤣,

FRIDAY.....

Readers Also Read