Kenza eBookz

Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature - Chapter 16

Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature - Chapter 16

Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature Chapter 16: Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature Chapter 16. Juma'at babban rana Allah ya kawo mu Abuja ta…

4,065 words

Juma'at babban rana Allah ya kawo mu Abuja ta kar6i bak'uncin Manyan Mutane na gida da kasashen k'etare don halartar d'aurin auren jarumin mu, hidima ta kacame acan cikin gidan bak'i ta ko ina sai zuwa suke banda wad'anda dama sunzo tuni, tun safiyar ranar aka fara sanya anko, Abokan Haisam gaba d'aya na a wani apartment na Senator dake a cikin layin nan aka sauke su har shima Haisam can ya koma yayin da Senatorn kuma da bak'inshi na a katafaren Guest hause d'inshi, Ana gama sallar juma'a a Central Mosque dubban Mutane suka shaida d'aurin auren ENGR. HAISAM ALEE ADAMU ZAKEE DA DR. FANAN MOHAMMED ABRAHAM akan sadaki Naira 500k, Haisam yaga kara Al'umma ko ta ina ba K'aramin dad'i yaji ba, su babansu Haulat duk sun zo haka yan wurin aikinsu babbar Mota suka yo mata da maza har yan gym dinsu ma ba'a barsu a baya ba mata da maza harda Anah duk sun zo kai wasu ma shi kanshi Haisam d'in bazai tuna inda ya sansu ba sai zuwa ake ana gaisawa dashi ana mashi fatan Alkhairi fuskarshi cike da annuri yasha babbar rigar Farar shadda haka sauran Angwayen ma duk Farar shadda suka sa, to a can gida ma dae duk farinciki ake kar ma Fanan taji sam bakinta ya kasa rufuwa kamar ta zuba ruwa a k'asa tasha ba wata kunya da take ji sai faman godiya take ga Allah daya nuna mata wannan rana cike da murna ta kira Haisam lokacin sun nufi Hotel da za'a yi reception yana d'auka ta fashe mashi da kuka tana fad'in at long last ta zama matarshi Murmushi kawae yake saki kafin yace mata shima yana farincikin hakan su Abbas dake gefenshi suka fara mashi tsiya yace zai kira later, daga cikin manyan bak'in dake zuwa yin Allah yasa Alkhairi harda Hajiya Kubra ta Comment section dama Abuja tasu ce can na hangota cikin shiga ta Alfarma ta zo harda iyalinta aka kar6esu hannu bibbiyu ba kamar data gabatar da kanta a matsayin Fan d'in Haisam, bayan wani lokaci tace zata tafi Hajiyar Sanata tace ya kamata ta tsaya aje dinner dasu anjima tace to zasu je anjima zasu sake dawowa ta bukaci sanin time d'in da za'a yi dinner d'in aka fad'i mata,

Jama'a wai ya Fatuu????

Gaba d'aya ranar ta k'ara harmutsewa sanin yau ne d'aurin auren Haisam k'arfin hali kawae take a Makarantar amman ko daga yanayin fuskarta zaka fahimci ba daidai take ba, ba abunda haulat ke gani kan fuskar tata face tsantsar tashin hankali, bayan an tashi suna zuwa bakin lungun gidansu Haulat tace mata gida zata anjima zata zo kasa dakatar da ita haulat d'in tay ta bita da ido har tay nisa, tana zuwa ta bud'e gidan ta maidashi ta datse tun a bakin kopar daki ta saki jakar ta fizge hijab dinta ta nufi gado da gudu sai lokacin ta samu damar sakin kukan dake ta cinta, sosae ta shiga rizgar kuka tana cikin kukan ta mik'e taje ta jawo drawer chest ta mirror d'inta ta curo IV d'in bikin ta koma kan gado tana kallo tana cigaba da rizgar kuka har time d'in da akasa za'a d'aura Auran yay tana a hakan sai ma abunda ya k'aru ma daga kukan duk ta fita hayyacinta fuskarta tay jajir can kuma a fusace ta fara Magana tana fad'in "nasan na rasa ka yanzu bazan ta6a samunka ba Ya Haisam kayi Aurenka ka barni cikin mawuyacin hali ko kirana ma ka daina yi to nima na daina sonka,na daina na daina na daina.......".

Haulat na komawa gida ganinta ita kadae yasa innarta tambayarta Fatuu tace mata ta wuce gida ta d'aukko abu, bayan tayi wanka tay salla taje wurin innarta a d'aki tace a bata Abincin Fatuu zata kai mata tana kallonta tace "to ba zata dawo ba?" Yan kame kame ta fara yi tace "eh amman tace sai anjima" shiru innar tayi sai kuma tace "wai kodae wani abu na damunta ne naga duk ta canza kamar tana cikin damuwa ko?" Yan kyafcen kyafcen idanu haulat ta hau yi murya na d'an rawa tace "a'a... ba wani abu kawae dae har yanzu tun ciwon data yi kwanaki bata ida warwarewa ba ta koma kaman da" gyad'a kai innar tay tace Allah ya bata lpy da sauri ta amsa mata da Amin, bayan ta zuba Abincin haulat tasa Hijab ta nufi gidansu, tana isa kopar gidan ta iskeshi a rufe ta fara buga kopar shiru shiru ba'a bud'e ba kuma tana da tabbacin Fatun na ciki, can ta aje yar warmer d'in a gefe taci gaba da bugawa amman shiru har gabanta ya fara faduwa ta fara tunanin kar dae wani abu ya samu Fatun wata zuciyar kuma tace ko dae ba gidan ta dawo ba, ta kuma raya mata to ina zata tabbas tafi tunanin tana ciki, cigaba da bugawa tayi da k'arfi can ta tuna da Fatun nada waya ai da sauri ta fara kokarin kiranta har saida ta kira sau biyu tana niyyar tura kira na ukku taji ana bud'e kopar har saida taji wani sanyi a ranta a hankali ta d'an bud'e kopar ta lek'o da kanta suka had'a ido da Haulat ganin itace yasa ta idasa bud'e kopar haulat din ta d'an waro ido tana kallonta da Al'ajabin ganin yadda fuskarta ta koma idanuwanta sun kumbura gaba d'aya ma fuskar ta kumbure da gani ba d'an k'aramin kuka ta sha ba, a sanyaye haulat ta shiga bayan ta d'aukko Abincin ta tsaya tana kallonta tace "Fatuu ya zaki lahanta kanki akan..." Bata k'arasa ba Fatun ta fad'a jikinta tana fad'in "Haulat na daina son Ya Haisam daga yau, yayi Aurenshi ya manta dani inata wahala" nan da nan idanun haulat suka kawo kwalla cike da k'arfin hali ta d'ago ta tace shikenan su shiga ciki hannunta cikin nata bayan ta rufe gidan suka nufi d'akin Fatun, a gefen gado duk suka zauna Haulat ta aje Abincin k'asa kafin ta d'ago ta kama hannuwan Fatuu tace "Haka yakamata, ki daure ki daina sonshi tunda kinga yanzu yayi Aurenshi yana can yana farinciki shida matarshi ke kuma kina nan zaki ma kanki illa kuma ki sani duk abunda ya sameki kece a wahala iyaka kawae nasan bai wuce su kira ki a waya suyi maki sannu an k'ure ya turo kud'in magani, ki daure ki cije Fatuu ki raya mafarkin ki na son zama Doctor kinga jarabawa ke tunkaro mu bada jimawa ba kuma tattare da ita ne zaki raya burinki ko ki kashe shi ki duba irin d'awainiyar da gwaggo ke maki Fatuu kan karatunki Saboda rayuwarki ta inganta ta baro ki da garinku ta kawo ki nan ya kike tunanin zata ji in kika kashe mata kwarin gwiwar da take da a kanki? ki yi hakuri ki bar ma Allah komae kinji?" Kai ta d'aga mata duk tayi sanyi sai kace ba Fatuu ba, hannu Haulat ta kai ta d'aukko kulan Abincin tace "ga Abinci na kawo maki zaki ci ko?" Kai ta d'aga mata alamar eh, tace "to kin ma yi salla kuwa?" girgiza mata kai tayi cikin disasshiyar murya tace "banyi ba amman yunwa nike ji sosae" yadda tay Maganar gwanin ban tausayi, bud'e mata kulan haulat tay tace to taci in ta gama sai tayi Salla tace to haulat na kokarin zuwa ta d'aukko mata spoon a Kitchen taga ta sa hannu ta fara ci ta koma ta zauna tana kallon yadda take tura Abincin da gani ba k'aramar yunwa take ji ba dama ko da akayi break a makaranta bata ci komae ba wani irin tausayinta ne ya kama haulat ta mik'e taje ta daukko mata ruwa ta kawo mata saigashi ta cinye Abincin tass cikin d'an lokaci Haulat na d'an murmushi don taji dad'in yadda ta ci Abincin ta mik'a mata ruwan shima ta shanye shi tass haulat tace to taje tayo Alwala suka mike tare tana kokarin daukan kulan Haulat tace ta barshi ita ta d'auka suka fita, bayan ta gama sallan da kanta tace bari tayo wanka har saida haulat ta rakota bakin toilet kafin ta koma d'aki tana ta juya abun a ranta tana kuma Addu'ar Allah ubangiji yasa ta daina jin son nashi ko kuma ta rage tunda tasan ba abune da zai yuwu lokaci guda ba sai a hankali, bayan ta fito ta shirya cikin riga da skirt na atampa ta d'an fad'a daka kalli wuyanta amman dirin ta na nan yadda yake, falo suka koma suka kunna kallo saidae ita Fatun idonta ne akan tv d'in amman zuciyarta na duniyar tunane tunane sai faman imagination take akai akai Haulat ke juyowa ta kalleta su had'a ido ta sakar mata murmushi itama sai ta d'an yi mata na yak'e.

Bayan isha aka shiga shirin tafiya Dinner zuwa k'arfe tara aka fara kwasan Mutane, wohoho Jama'a kuzo Kuga tsaruwar wurin dinner d'in Naira tasha kashi a wurin iya decoration d'in wurin abun tsayawa kallone, Ango yasha tsadaddun suit bak'ak'e yayin da Amarya Fanan ke sanye da wedding gown fara tun daga kunnanta wuyanta hannunta da yatsunta duk Diamond ne mai d'an karan tsada haka takalmanta da yar jakar hannunta masu d'auke hankalin Mutum ne, Angwayen ma duk shigan suit sukae haka k'awaye da yan'uwan Amarya ansha ankon rantsattsan leshi jama'a ina masu sana'ar lalle da d'inki ku zo ku dau style iri iri wani d'inkin sai kace na Aljanu gaba d'aya an watse karamar leshin, ina ganin Farha na hau tunanin yadda akai tasa fitted gown d'in jikinta k'arshe dai na yanke a raina k'ilan a Jikinta aka d'inka ta, Ma sha Allah an ci an sha an kuma nishadantu can na hango Hajiyar Sanata da Hajiya kubra suma duk sun sha leshi ashe dae ta dawo da gaske to Momy muna godiya Allah ya bar zumunci, su Fanan a banza an kadaddabe Haisam balle yanzu da igiyan Aure ya shiga tsakani sam bata barshi ya wataya ba tabi ta k'ank'ame abunta amman banga laifinta ba mijinta ne halak malak, sai wurin d'aya aka tashi Haisam duk ya gaji da hidindimun don shi ba mai son hayaniya bane, Washe gari Asabar akai Mother's eve wanda yazama tamkar Walima don a cikin gidan akayi shi ranar ankon shadda aka sha abun dae sai dae ace ma sha Allah, sai bayan isha taro ya watse masu tafiya suka tafi Misalin k'arfe goma da wasu mintuna Haisam na tare da Abbas a gaban parking lot basu dad'e da shigowa ba daga wurin sauran bak'in su da basu kaiga tafiya ba don wasu duk sun tafi tun jiya Sameer ma sun tafi yau da safe, zaune suke a saman boot duk suna sanye da shadda dinkin sen style duk basu da huluna akan suna cikin fira wayar Haisam dake ajiye gefe ta fara ringing ya kai idonshi kanta Amarya ce tay kira hannu ya kai ya dauka kafin yay picking call d'in ya kara a kunne tun kafin yace wani abu ta riga shi da tambayar inda yake taje part d'inshi bai nan ya bata amsa da inda yake daga haka tay cutting call d'in ya maida wayan inda take Abbas na murmushi ya tambayi Amarya ce ya d'aga mashi kai kawae, bada jimawa ba sai gata ta 6ullo ta baya jikinta sanye da wata matsiyaciyar fitted gown ta atampa super daga k'asa ta bud'e sai tay kaman kifi mermaid kanta tayi fav d'aurin kallabinta wato Zaraah buhari tana sanye da fashion d'an kunne da yan hannu hannunta ruk'e da wayarta yayinda kafarta ke sanye cikin flat shoes sumarta ta linkata ta yadda ta dawo daidai tsakiyar bayanta, wani kalan fitinannan kamshi mai narkar da zuciyar wanda ya shaka take saki ba a kayanta ba ba kuma a Jikinta ba don ba k'aramin gyara tasha ba tun daga cikin jikinta zuwa kan fatarta ita kanta tana jin canji a jikinta sosae ta tsumu da yawa, tunda ta tunkaro su idon Haisam na kanta haka Abbas ma sai sakin murmushi yake tun kan ta k'araso kamshin ta ya rigata isowa tana zuwa gabadaya ta fad'a jikin Haisam ta d'aura kanta a saman shoulder d'inshi don a zaune yake, wani kalan lumshe ido yay ya d'an juyar da kai yana kallonta daga yadda take ta gaishe da Abbas dake zabga murmushi ya amsa yace "Amarya ya gajiyar hidima?" K'asa k'asa tace "akwae shi don am completely exhausted" d'ago kan tayi idonta akan Haisam sukae ma juna kallon cikin ido seductively ta furta "I ave been looking for u since nayi trying no d'inka bai shiga ba sai yanzu" kallonta kawae yake yadda take Maganar underneath his breath ya furta"What's it, do u have any problem?" K'ara kwantar da kan tayi ba tare data ce komae ba, Abbas yace "baka ji tace she's exhausted ba I think she needs some fresh air ko ta rage gajiya ya kamata ta d'an ga gari ai ansha hidima da yawa?" daga yadda take tace "u'r right Abbas" wani kallo Haisam yay ma Abbas d'in ganin dariyar da yake yasa ya fahimci da biyu yay Maganar da yayi sigh yay yace "aiki ya sameka sai ka shiga kai driving muje" wata yar iskar dariya Abbas yay yace "aiki ya same ni ko ya same ka ko kana nufin mun gama ma hidiman bikin Matan ma mu zamu yi maka dawainiyar ta in zaka tashi kai aikin matarka ka tashi ni wllh ba in da zani zuwa ma zanyi in kwanta don nima a gajiyen nike" daga haka ya diro ya aje mashi car key d'in yay gaba yana dariya yana fad'in sai sun dawo, Abbas na tafiya ya kai hannu ya d'ago da face d'inta suka k'ura ma juna ido Fanan sai faman lumshe ido take shima nashi a d'an lumshen suke duk sun cika juna da k'amshi, dirowa shima yay ya kama hannunta ya zagaya other side d'in Motar ya bud'e mata ta shiga ya kai bakinshi ya manna mata kiss a cheek d'inta ta wani kalan lumshe ido bayan ya rufe Motar ya zagaya driver side ya bud'e ya shige bayan ya tashi Motar ta kai hannu ta kama hannunshi guda daga haka yaja suka nufi hanyar gate suna isa aka bud'e masu suka fice..............

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 da 3 Naira 400 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wannan no 09013804524._

*ASM Bk2020*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

........Suna hawa hanya wayar Haisam tay kara alamar shigowar message a hankali ya janye hannunshi daga rik'on da ta yi mashi ya d'auki wayar yana k'ok'arin dubawa,

_Take it easy on her sabon shiga._

Abunda aka turo kenan kuma ba kowa bane ya turo fa ce Abbas, d'an guntun murmushin gefe yay ya fita daga wurin ya maida wayan ya ajiye suka cigaba da tafiya, Abbas na komawa part d'in Haisam bedroom ya nufa ya fad'a saman gado nan take yaji kewar matarshi ta rufe shi wanda in ba don hidima ba ba yadda za'ai suna wuri d'aya har yaji kewarta can ya yunk'ura ya tashi zaune ya kai hannu ya d'auki wayarsa dake gefenshi ya shiga call log, lambar Feenah ya kira saida ta kusa katsewa tay picking yadda tay Magana daga jin muryarta ta fara bacci, bayan sun gaisa ya tambayeta yara tace duk sunyi bacci yace Ok yana son ganinta ta tambayi inda yake yace ta biyo ta kopar baya yana nan ta amsa da ok, saida ta d'aura hijab a kayan baccin dake jikinta sannan ta fita, tana zuwa bayan ta hango shi a tsaye d'an can nesa ta nufeshi tana zuwa gabanshi da murmushi tace mashi "Dear bakai bacci ba" d'an ta6e baki yay yace "yea na kasa shiyasa na kira ki ki taya ni fira" a d'an shagwa6e tace "kai dear wani irin fira yanzu bacin k'asan inda muke hakanan ka tado ni ina bacci na..." bata k'arasa ba ya janyota jikinshi ta waro ido kafin tace wani abu ya rigata fad'in "Wato kin manta dani ko har kina iya yin bacci hankalin ki kwance" tana ganin yadda yay Maganar ta fara k'ok'arin raba jikinta da nashi tana fad'in kada wani ya gansu, K'in sakinta yay ya riketa gam yace "to a gammu mana zunubi muka aikata ko me" d'an yamutsa fuska tay ya fara kokarin janta yace suje tay mashi massage k'ilan yay baccin turjewa tay a marairaice tace "amman Dear kasan fa a inda muke yanzu fisabilillahi a ina zan maka wani massage" ya bata amsa da part d'in Haisam idanu waje tace "ya hakan zai yuwu cikin Abokanka!" d'an murmushi yay yace mata ai ba kowa shi kadae ne Haisam d'in ma ya fita da Amaryarshi tana jin haka ta d'an bud'a ido Abbas d'in yay dariya yace su je mana, to dae itama tana kewan mijin nata hakan yasa ta bishi suka nufi kopan baya mai stairs da zasu kai ka parts d'in sama ta baya, suna shiga kopan ya sungumeta yana taka staircases d'in sai yan nok'e nok'e take don gaba d'aya a d'arare take Allah yaso har suka haye ba wanda ya gansu ya tura kopar ya shige da ita, to dae Allah ya kyauta jin kunya ko tashin yara,

Suna hawa hanya sosae ya tambayi Fanan ko tana jin yunwa tace a'a just abu mai sanyi take buk'ata ya jinjina kai still hannunsu na cikin na juna a gaban wani cold store ya parker motan yace mata yana zuwa ya fita, after some few minutes ya fito hannunshi ruke da Leda mai d'auke da tambarin wurin ya zagaya ya shiga Motan bayan ya mik'a mata ya rufe kopan kafin yaja suka tafi, bud'e ledan tay Manyan robobin ice cream ne guda biyu ta curo d'aya ta bud'e ta fara sha cike da salon jan hankali ta rink'a d'e6owa tana kaiwa bakinshi ba tare daya ce komae ba ya rink'a d'an bud'e bakin yana sha, zagayawa yay da ita gari bayan wani lokaci ya tambayeta is she calm su koma gida sai ta wani langa6ar da kai cike da marairaicewa tace "I know su khairat aren't sleeping yet suna can suna shouting and it caused me headache" nodding kai yay idonshi akan hanya can ya tambayeta yanzu ina take so suje ba tare da ya kalleta ba, tace "somewhere very quiet and calm" d'an juyawa yay ya kalleta idonta akanshi ta d'an d'age mashi gira, d'an murmushi yay ya maida idon kan hanya can kuma sai ya taka burki a gefen hanya tana kallonshi yace ta fito tay driving d'in zai yi wani abu ta amsa da Ok ta bud'e kopan lokacin shima ya fito saida ta d'an shafi gefen fuskarshi yay mata Murmushi kafin ta zagaya ta zauna a driver seat shi kuma ya shiga inda ta tashi ya zauna bayan duk sun rufe kopopin kafin ta ja Motar ya kai hannu ya d'auki wayarta dake ajiye a gaba lokacin ta tambayeshi ina zasu yace mata yana zuwa hakan yasa ta dakata bata ja Motar ba, Google map d'in wayarta ya shiga ya rubuta inda zasu sannan ya aje mata inda zata rink'a gani ta kai idonta kan wayan tana ganin wurin daya sa ta d'an juyar da kanta gefe ta saki wani kayataccen murmushi kafin taja Motar tana bin Map d'in suka tafi shi kuma yanata latsa wayarshi da alama yana wani abu ne, kusan 30 minutes sannan suka iso harabar katafaren Hotel d'in ta nufi inda aka tanada don ajiye Motoci ta sama ma tasu wuri a cikin jerin rantsattsun Motocin dake wurin, juyawa tay ta kalleshi tace sun iso ya d'aga mata kai sai kuma ya d'ago daga kallon wayar yay mata alamar suje da kai tana k'ok'arin bud'e Motar taji cool voice d'inshi yace "Are u going like this?" Dakatawa tay ta langa6ar da kai shi kuma ya d'age mata gira alamar jiran amsarta sam ta manta ta d'aukko mayafi can ta tuna da kallabinta babba ne ta curo shi ta bud'e ta rufa saman kan ba laifi ya saukko har kusan k'ugunta sannan ya bud'e Motar itama ta bud'e ta fita, suna zuwa reception ba 6ata lokaci aka basu key d'in d'akin da tuni ya kama masu online suka nufi VIP inda d'akin yake ya bud'e yay mata alamar ta shiga kafin shima ya shiga kopan ta rufe, babban single room ne mai d'auke da had'addun Furniture d'akin ya k'awatu ga ni'imtaccen sanyin Ac had'i da sanyayyan kamshi na tashi, gefen gadon Fanan ta tsaya idonta akan shi har ya k'araso ciki ya aje wayoyinsu da keys kan bedside drawer ya d'ago shima ya tsaya a gabanta suka cigaba da kallon juna, wani kalan kallo da basu saba yi ma juna irinshi ba suke bin juna dashi kasa jurewa Fanan tay ta d'an sadda kanta don wani irin kwarjini yay mata, d'an murmushi ya saki ya kai hannuwanshi ya dafa shoulders d'inta da sauri ta d'ago ta kalleshi ya jata jikinshi yay hugging nata ta wani kankameshi sosae kawai sai jin sobbing d'inta yay alamar kuka take slowly ya d'ago da ita ya ga da gasken kukan take tak'i had'a ido dashi, da wata irin murya ya kirata"FANAN" yarrr taji tsigar jikinta ta tashi don rabon da ya kira sunanta har ta manta ganin tak'i dagowa yasashi sa hannuwanshi ya d'ago da face d'inta ta kalli cikin idanunshi da idonta jage jage da hawaye underneath his breath yace "what for??" Motsa baki ta fara a hankali tace "ba komae Ya Haisam am just feeling dat am d happiers person on earth now, nagode ma Allah burina ya cika mun zama married couple" murmushi kawae yake saki yana kallon yadda take Maganar, ya sani tana matuk'ar kaunarshi shima kuma yana jin sonta a ranshi, Cupping face d'insu yay suka cigaba da shakar kamshin juna gaba daya she's irresistible ga lafiyayyan Namiji at dat moment a hankali ya d'ago da face d'inta ta yadda har tsinin hancinsu ya had'u slowly ya had'e lips dinsu wuri guda without wasting time suka shiga ba juna deep French kiss kasa daukarsu kafafunsu sukae suka kai gadon suna cigaba da bawa juna very hot romances na wani lokaci ba k'aramin kokari Haisam yay ba ya iya controlling urge d'insa a lokacin ganin suna niyyar kaiwa wani mataki da bai shirya ma hakan ba, da k'yar ya d'an ja jikinshi breathing rapidly Fanan na ganin hakan ta kalleshi da idanunta da tuni sun canja daga sufar su ta ainihi shima kallonta yake ganin yanayinta yasashi d'an jawota ya kai bak'inshi saitin kunnanta cikin trembling voice ya furta "am sorry isn't proper in a Hotel room" da sauri ta runtse idanunta all she needs at dat Moment was for him to do it with her don ba k'aramin tsumuwa tay ba shi kanshi dauriya ce kawae don kuwa bacin kasancewarshi lafiyayye Abbas da Najeeb sai da shima suka gyare shi tsabb, kasa cewa komae tay ta kife kanta a chest d'inshi tana ci gaba da breathing quickly a hankali kuma wasu siraran hawaye suka fara zubo mata amman bata bari ya gani ba, jin yadda take numfashin yasashi kai hannu yana rubbing soft skin d'in bayanta dat's opened alamar rarrashi ta lumshe ido a hankali numfashinta ya fara daidaituwa bayan wasu mintuna ya d'an d'agota jin tayi tsit ya ga tayi bacci ashe bin face dinta yay da kallo kafin ya kai hannu ya goge yan guntun kwallan dake mak'ale a idanunta wanda bazai tantance na miye ba kafin ya gyara kwanciyarshi ya daurata kan chest d'inshi sosae, shiru yay duk jinshi yake wani iri don abunda ya faru tsakaninshi da ita abune da bai ta6a aikatawa ba shi ko had'a jiki da mace ma in ba ita ba da yan'uwanshi ko Farha bai ta6a had'a jiki da ita ba sai dai ya dafata ko ya kama hannunta in ta kama SAI KUMA ZARAAH zuciyarshi ta raya mashi hakan lumshe ido yay ya fara tunaninta kwana nawa bai ji ya take ba Saboda hidima lokaci guda yaji yana son ya kirata yaji ya take a hankali ya mik'a hannu kan side drawer ya d'aukko wayarshi saidae yana duba time yaga dare yayi sosae shi kanshi baisan dare yayi haka ba kusan d'aya saura na dare, shiru yay yana kallon wayar sai kuma ya shiga messaging ya rubuta mata sak'o kamar haka,

_Hope u'r doing gud Zaraah._

Readers Also Read