Kenza eBookz

Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature - Chapter 23

Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature - Chapter 23

Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature Chapter 23: Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature Chapter 23. "A'a basu nan k'asar suna America" da k'yar ta…

5,035 words

"A'a basu nan k'asar suna America" da k'yar ta bata amsar ta d'ukar da kanta k'asa jin kwalla na niyyar zubo mata girgiza kai yadikko tay tace "Allah bai k'addara mijin ki bane don ni da nayi tunanin son ki yake wllh koda kika ce man ba haka bane wancan lokacin kawae na jiki ne na zata yana son ki ne ya bari sai kin k'ara girma don hidimar da yake tayi yawa yawanci zaki ga irin hakan ba hakanan mutum ke yi ba da dalili ashe shi don Allah yake yi" a sanyaye Fatun ta d'ago tace "shine ma ai ya turo kud'i aka siya wancan kayan" hannu yadikko tasa ta ruk'e ha6a tace kai don Allah Fatun ta d'aga mata kai alamar eh,

"Kai amman dae wannan mutumin d'an Arziki ne wllh ni bamma ta6a jin mutum mai Alkhairi irin nashi ba, ace daga makwabta ka ya dinga hidima haka ni fa wllh nayi mamakin kayan can don ko banza sai sun yi miliyan ko ma fi" dakatawa tay tana maida numfashi kafin da d'an murmushi ta dafa kafad'ar Fatun tace "amman da gaske bai son ki kuwa?" D'agowa Fatuu tay ta kalleta idanunta sun k'ara sauyawa a hankali tay shaking kanta tace "bai ta6a so na ba, dama yana tare da wadda ya auran yar uwarshi ce" cike da zolaya yadikko tace "to amman ke nasan ai kina son shi ko?" bin ta da ido Fatuu tay ta kasa ce mata komae kawae sai ganin kwalla yadikko tayi tana zubo mata zaro ido tay Fatun ta kifa kanta a jikin kafafun yadikkon ta sa kuka, wani irin sanyi jikin yadikkon yay ta kai hannu ta d'ago ta ta zaunar da ita gefenta ta rungumo ta ta gefe cikin kuka Fatun ke fad'in "ina son shi sosae yadikko nayi tunanin shima yana sona ne ashe ba haka bane bai ta6a so na ba ina ji ina gani yayi auren shi ya tafi ya barni" har idanun yadikko sun ciko da k'walla ita dama tayi mamakin saurin amincewa da Fatun tay ai mata auren ashe ashe ciwo ne da ita a zuciya sosae ta bata tausayi ta shiga rarrashinta tana bubbuga bayanta tace "kiyi hakuri Fatuu na fahimci yadda kike ji ki bar ma Allah komae in har shi rabon ki ne Allah ya k'addaro zaku rayu matsayin mata da miji ko ba dad'e ko ba jima hakan sai ta faru don in dae abu rabon ka ne kana zaune zai iske ka har inda kake har kai ta mamakin yadda hakan ya kasance wannan kad'an daga ikon Allah ne don ni kaina shaida ce na so Mahaifin ki kamar mi muna cikin soyayya aka ce an bayar dani ga wani abokin mahaifina ina ji ina gani aka man Auren dole kaman zan yi hauka naje gidan shi sam ba kwanciyar hankali ga wulak'anci dama shi bai d'auki mace a bakin komae ba tamkar riga haka yake canja mata shima Baffana harda kwad'ayi yasa ya bashi aure na k'arshe ya yi man sakin wulakanci lokacin yunwa duk ta k'arar dani abun bak'in cikin lokacin Mahaifin ku har yayi auren shi koda na tuntu6e shi Bayan na gama idda sai ya bani hak'uri ya nuna man bai da ra'ayin mata biyu, ya dae fad'a man haka ne kawae amman nasan kawae ya daina so na ne dama na samu labarin irin son da yake ma matarshi wato mahaifiyar ki gata yar birni mai ilimin boko a lokacin ne na samu aka man hanya na tafi aikatau Abuja nayi nisa da garin to ashe Allah bai kaddaro zasu rayu tare tsawon lokaci ba wllh lokacin na girgiza da jin labarin mutuwarta don lokacin ni nama fidda ran auren nashi na nemi number d'in shi ta hanyar wani Yayana na kira don yi mashi gaisuwa to anan muka samu lambar juna mu ka d'an rink'a gaisawa ina d'an kwantar mashi da hankali ana haka Bayan wani lokaci watarana sai kawae yayi man Maganar Aure yace in ba damuwa lokacin na k'ara gasgata girman ubangiji don kuwa in nace ban son shi to fa nayi k'arya Saboda son gaskiya nike mashi wanda bai k'arewa, ba 6ata lokaci na nuna mashi na amince sanin yana cikin hali ga marayun yara kuma duk da ina jin dad'i a in da nike aikatau haka na baro Abuja na dawo mu kai Aure" lamo Fatuu tay yayin da cikin ranta ta ke kokonton anya Ya Haisam zai zama mijinta ita tama fidda ran hakan, to yaushe ma ita da zata auri wani shima kuma yana can yana auren wata, Yadikko taci gaba da cewa "ina so ki sani Al'amarin mumini dukkan sa Alheri ne, in samu yay Alheri ne in ya rasa ma Alheri ne, acikin wani hadisi aka fad'i mana hakan lokacin ina zuwa islamiyya a Abuja don haka ki sa a ranki duk abunda ya faru dake mai kyau ne ki daina damuwa don duk abunda zai faru da bawa an riga da an rubuta ki ci gaba da Addu'a muma kuma muna yi maki" kai Fatun ta d'aga mata ta d'ago da fuskarta tana share mata hawayen da d'an murmushi akan fuskarta bayan ta gama goge mata tace ta tashi tayi sallar Isha sai ta ci Abinci ta amsa da to, bayan ta ci Abincin wanka tayo ta saka kayan bacci ta haye gado ta fara tunanin gwaggo tana son kiranta amman kuma tana zullumi don tasan in da Lafiya lau bata fushi ba yadda za'ai ace har yanzu bata kira taji ya suka iso ba tana cikin hakan wayarta ta fara ringing ta d'auka ta duba Kawu Amadu ne mik'ewa tay zaune ta kara wayar a kunne bayan ta d'auka, gaisawa sukae yay mata anje lafiya ta amsa kafin ta tambaye shi gwaggo yace tana d'aki shiru tay bata ce ya kaima ta ba shima bai ce zai kai Matan ba, yar hira suka yi yawanci dae lallashin ta ya k'ara yi kafin daga baya sukae sallama ta cire wayar, zaune tay bata koma ta kwanta ba gaba d'aya ta rasa ma tunanin da zata yi komae bai mata dad'i tana cikin hakan wayarta ta sake yin ringing ta kai idonta kan screen d'in sunan Ya Haisam ta gani lokaci guda ta saki murmushin da ita kanta bazata tuna when last da tayi irin shi ba don taji dad'in kiran nashi ko ba komae ta fahimci ya damu sosae da halin da take ciki, picking tay ta kara kunne kafin a hankali tay mashi sallama ya amsa mata a sake ya tambayeta ya suka isa tace mashi lpy Lou, shiru suka d'an yi sai kuma taji yace "kin daina kukan ko?" tana murmushi tace eh yace "dat's gud ki yi hakuri haka rayuwan yake we plan but God plans d best for us and all tests from Allah are Alkhair" jinjina kai tay ta d'an had'e lips d'inta sosae take jin dad'in yadda yake mata Magana bayan d'an shiru cike da zolaya yace "kin had'u da groom d'in naki ko?" Tura baki tay kaman yana ganinta, yace "ba tura man baki zaki ba ki ban amsa" waro ido tay jin ya gane abunda tay a hankali tace "a'a ni har yanzu ban san shi ba" d'an murmushi yay sai kuma yace "Ok in kun had'u sai mu gaisa in bashi amanar ki" d'an murmushi tay bata ce komae ba yace "ko baki so?" Da sauri tace "ina so" shiru suka d'an yi can tace mashi ya Aunty Fanan yace yana wurin aiki itama tana wurin aiki tace to, "baku da Network mai kyau da na maida vedio call in ga sore eyes d'in ki" zaro ido tay da yar dariya kawae yace "ko idanun basu kumbura ba?" Tura baki tay tace "sun kumbura" lallashinta ya shiga k'ara yi suna haka yadikko ta shigo dama tana falo ita da yaran ta hana su shigo don kar su takura mata har saida tay mamakin ganin Fatun zaune tana waya kuma harda murmushi akan fuskarta ganin kallon mamakin da take mata ne yasa tace ma Ya Haisam d'in ga yadikko zasu gaisa yace Ok ta cire wayar ta mik'a mata ta fad'i mata ko wanene da sauri ta amsa ta zauna a bakin gado tana ta washe baki suka gaisa kafin ta hau yi mashi godiyar abun Arziki yace ba wani abu sosae tay mashi Addu'oi kafin ta mik'a ma Fatuu wayar tana amsa yace bari ya kyaleta ta huta sukae sallama, bayan sun gama firar Haisam d'in ta shiga yi ma Yadikko ita kuwa ganin sakewar da tay yasa ta biye mata, Washe gari tana cikin yin karin kumallo don bata tashi da wuri ba Baffanta ya shigo duk suka gaishe dashi da fara'a yabi Fatun ya samu wuri kan kujera ya zauna yana amsa gaisuwarta yadikko ma ta gaishe dashi ganin ya shirya tace har zai fita ne yace "Eh ina son zan je can jumeta ne wurin masu kayan gadon" yadikko tace "za'a d'aukko ne?" Shiru ya d'an yi kafin yace "tukunna dae kinsan har yanzu akwae sauran kud'i da zan cikashe masu dubu 200, da nayi tunanin zan samu wasu kud'i ne to amman tunda lokaci k'urewa yake zan k'ara kai shanuwa guda kasuwa sai a basu kawae" da yar damuwa yadikko tace "amman shanayen ba biyu ne suka rage ba kuma kace zaka sayar da d'aya Saboda hidimar bikin yanzu in ka saida wannan shikenan fa sun k'are" yar dariya yay yace "to ai biyan buk'ata yafi dogon buri sai a gode ma Allah da ya sa akwae" shiru kawae tay acan k'asan ranta kuwa haushi ne ya turnuke ta na Ard'o duk shi ya tattago hidimar ba tare da an shirya ba, shi yakamata ace ai yay kusan duk hidimar amman ya k'ame hannu duk tulin Arzik'in da ke gare shi, shiru Fatuu tay tana bin su da ido can kuma sai ta mik'e ta nufi cikin uwar d'akin bada jimawa ba ta dawo ta nufi gefen baffanta ta zauna da d'an murmushi ta mik'a mashi abunda ta d'aukko, bin yan kunnan dake a tafin hannunta yay da kallo kafin ya maida idanun nashi kanta cikin alamun rashin fahimta tace "Baffa wannan zinari ne kuma 200k aka siye shi in kasan in da ake sayarwa sai ka saida kayi amfani da kud'in" ba shi ba har Yadikko waro ido sukae cike da Al'ajabi baffan ya tambayeta ina ta same su ta fad'i mashi da Ya Haisam makwabcin su zai yi aure ne ya bata kud'in shine Gwaggo ta siya mata yan kunnan, jinjina kai duk sukayi a tare suka shiga yabon Haisam d'in baffan yace "to inna wuro abu mai daraja haka ai bai kamata a sayar dashi ba" yar dariya tay tace ai don ajiyar kudin aka siya tunda yanzu ana buk'ata ba sai a sayar ba, duk yadda tayi K'in Amincewa baffan yayi da a saida yan kunnan yace ta bar abunta zai mata amfani ba abunda zai gagara in sha Allah, bata ji dad'i ba ta yamutsa fuska cike da wasa yace ko tayi kuka ba zai amsa ba gwara ta adana hawayenta, can ta tuna da kud'in da ya tura mata ta siya kayan kitchen ta mik'e da sauri tace to tana zuwa, bayan ta dawo ta d'aura mashi kud'in kan cinyarshi tace "to ga wad'annan su dae dama kai ka tura man kud'in kayan kitchen to kuma an siya komae sai kai amfani dasu sannan ga Atm d'ina akwae dubu 70 a accnt d'in sai ka cire su ka had'a" baki bud'e suke kallonta ganin haka yasa tay mashi bayanin inda ta samu kud'in cikin account d'in nata 50k da Abbas ya tura mata sai dama akwae 20k cikin sauran kud'in Graduation da Haisam ya tura mata,

"Amman inna wuro ke ba amfanin da zaki da kud'in ki ne da kin bar su dama na ta6a sadakin ki" da sauri tace "a'a ba abunda zanyi da su Baffa kayi amfani dasu kawai" yace zai cire dubu 50 ta bar 20k d'in ta mata wani amfanin, sosae suka shiga yi mata godiya shida yadikko harda yar k'wallar shi yace in sha Allahu yadda ta za6i farin cikin shi fiye da nata ita ma Allah zai faranta mata haka ya shiga jera mata Addu'oi tana amsawa da Murmushi daga baya ya mik'e yay masu sallama ya tafi.

JUMETA

babban Parlor ne mai d'auke da set d'in dankara dankaran Sofas da kayan kallo irin dae falon da daka kalla zaka shaida na masu hannu da shuni ne, a kowanne 6angare na bangon d'akin akwae hotuna wanda yawanci duk na yan siyasa ne kama daga d'an majalisa, governor harda na shugaban k'asa, zaune a saman 3 seater Alhaji lawal ne yana sanye da farar jallabiya idanunshi sanye cikin glasses yana kallon labarun yamma a kai akai yake juyawa gefenshi ya kalli Matar shi Hajiya Rabi'atu dake gefenshi tana mashi hira, babbar mace ce saidae bata manyanta ba sosae kana kallonta zaka fahimci hutu ya zauna mata sosae, tana da kyau ba laifi gata jajir da ita sannan tana da k'iba ba irin mai muni ba jikinta sanye da had'addan lace ta kashe d'auri kana kallon ta kaga wayayyar bafullatana, da yar sallama ya shigo cikin parlon duk suka d'aga kai suka kalleshi, matashi ne wanda a k'alla zai iya yin shekaru 35, dogo ne sosae sai dai sam bai da jiki kuma ja ne irin kalar fatar Mahaifiyar shi har kama suke ga sumar kan shi da ta k'ara bayyana shi a matsayin bafullatani don a nad'e take amman bata da yawa, jikin shi na sanye da bak'in silk wando da blue riga mai dogon hannu da ma6allai ya yi zanzaro hakan ya bayyanar da had'addan bak'in belt d'in dake d'aure a k'ugunshi haka hannun shi na sanye da wrist watch silver, saman kujerar dake opposite da su ya zauna fuskar shi sam ba annuri ya gaishe da su duk suka amsa Alhaji lawal yace "Khalid ka dawo?" Amsa mashi yay da "Yes Dad" "To ya aikin?" yace "Alhamdulillah" ita dae Hajiya Rabi'atun kallonsu take tana murmushi,

"Dama dalilin da ya sa na kira ka don in sanar da kai Amaryar taka ta iso tun jiya don haka sai ka samu kaje ku gana da juna, sannan duk abunda ya kamata kayi in kaje sai ka tabbatar kayi ma'ana ka sallame ta da abunda zata yi hidimarta don kasan 2 weeks ya rage so we need not to waste time" wani irin k'ara d'aure fuska Khalid d'in yay har saida Dad d'in yace bai ji bane sannan kaman an masa dole ya ce "Ok" kallon Hajiya Rabi'atu yay yace "Ke wurin ki ina fata kin kammala komae" tana murmushi tace "Eh an kammala had'a lefen dama abunda ya rage akwae kayan da za'a d'inka mata already na fitar dasu suna ma wurin d'inkin to amman ba'a d'inka ba Saboda rashin measurement nata tunda ba saninta mu kae ba amman tunda ta zo yanzu ko zuwa gobe sai Sadeeya taje da driver su taho tare aje a d'auki measurement d'in nasan ba 6ata lokaci zai d'inka" jinjina kai yay alamar gaisuwa sai kuma ya maida kallon kan Khalid yace "kai yaushe zaka je d'in?" shiru ya d'an yi sai kuma ya watsa hannu yace "ko Next tomorrow tunda naji zasu wurin d'inki goben" shiru Alhaji lawal d'in ya d'anyi yana d'an tunani can yace "kai yakamata kaje goben ku ga juna zuwa wurin d'inkin sai a bari sai Next tomorrow d'in" d'an yamutsa fuska yay yace Ok daga haka ya fara kokarin tashi ya tambayi shikenan Alhaji lawal d'in yace eh zai iya tafiya yay masu sallama ya nufi hanyar fita................

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268._

*ASM Bk2028*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

.........Bin Khalid da ido Mahaifiyar shi tay har ya fuce fuskarta d'auke da d'an murmushi a ranta take ayyana in ba don yarjejeniyar dake tsakanin shi da Mahaifin shi ba tasan ba yadda za'ai ya yarda da wannan Auren had'in saidae ta wani 6angaren taji dad'in hakan don rashin Auren nashi na damun su tana fatan kuma ya zama silar canzawar shi. Bayan Fatuu ta gama breakfast d'in gyara d'akin ta fara yi yadikko na ta bari tace zatayi, sosae ta gyara su Mino duk sun tafi Makaranta tun kafin ta farka da sun nuna basu zuwa yadikko ta ce in dae don Adda d'in tasu ne ta zo kenan Saboda a garin zata zauna a cikin gidan Gonar Chairman shi kan shi yana zuwa Hutu da iyalan shi wani lokacin amman Khalid d'in ya fi su zama a gidan, bayan sallar Azahar Fatuu tayi wanka ta shirya cikin riga da skirt na atampa da sukai mata cif a jiki dama duk haka kayanta suke sai yan k'alilan d'in dogayen riguna, ganin ta shirya yasa Yadikko matsa mata kan ta daure taje ta gaishe da su Ard'o da Yaya ba don ta so ba ta yafa mayafi mahad'in kayan ta tafi, a nutse take tafiya ta shiga shashen Yaya lokacin da ta shiga ba kowa a filin wurin sai su K'anwar Altine dake wanke wanke a gefe, kallonsu kawae tay ta wuce kaman daga sama taji sun sa Dariya k'anwar Altine tace ma d'ayar mai suna zakiyya "Yar uwata ki bar wani yanga da ji da kai wai ke zaki auri mai kud'i duk fa munsan kalan mijin da zaki Aura" Fatuu na jin hakan ta dakata don sai taji tana son jin wani irin miji ne zata auran dama kuma da biyu suke Maganar shiyasa ma suke yi da hausa,

Zakiyyar tace "Bai kamata fa in rink'a yanga ba kuka yakamata in yi zan auri mashayi wanda har giya yake sha ya shigo gari yana niyyar taka mutane da Mota" sosae k'anwar Altine ke dariya kafin tace "dama iya hakan ya tsaya ai da sauki kin manta da d'ayan aika aikar da kowa yasan yana yi...." Da sauri zakiyya tasa hannu ta rufe mata baki tana fad'in kada aji mutuwar sarki a bakin su, wata irin mutuwar tsaye Fatuu tay mi take ji haka game da wanda zata aura, Mashayi kuma! Kuma miye d'ayan abunda yake aikatawar, a hankali ta juya ta kallesu sai tik'ar dariya suke suna kashe wa, wani irin nauyi k'afafunta sukae mata taji tamkar bata iya taka su ga jikinta tamkar ana zare mata laka take ji da k'yar ta daure taci gaba da tafiya, lokacin da ta je kopar d'akin Yaya ji tay kaman ta koma kawae ganin takalma tasan ba ita kadai bace da wasu mutanen kuma a halin da take ciki tsoron k'ara jin wani abun da zai iya tarwatsa mata zuciya take sanin sun iya ya6a bak'ar Magana, shahada kawai tay ta cire takalmanta ta shiga da yar sallama duk mutanen cikin d'akin suka d'ago suna kallonta hakan yasa ta sadda kanta duk suna zaune a k'asa su hud'u sai Yaya d'in na zaune a bakin k'aramin gadon k'arfe idon ta akan Fatuu har ta k'arasa gefenta ta tsaya, d'aya daga cikin Matan ta mik'e tana fad'in bari ta bata abun zama tasan yan birni basu zama a k'asa, darduma ta shimfid'a mata Fatun ta hau ta zauna tay shiru kaman bazata ce komae ba can ta d'aga ido a hankali ta gaishe da Yayar dake ta faman bin ta da ido, d'an ta6e baki tay tace "Amarya Sai yanzu aka ga damar zuwa gaishe dani kenan" shiru bata ce mata komae ba innar su Altine tay yar dariya tace "Yaya kin san Amaryar ta Manyan Mutane ce" d'an guntun murmushi yayar tay tace "haka fa ai na manta mune ma Yakamata muje mu mik'a gaisuwa, an zo lafiya Amarsu?" K'asa k'asa tace lafiya lou, innar su Altine tace "to muma bari mu mik'a gaisuwa ga Amaryar manya, ina wuni Amarya an zo lafiya?" Kafin Fatuu ta bata amsa wata tace "aikuwa saidae mu d'in mu gaishe da itan tunda Yaya ma da k'yar ta samu gaisuwar ballantane mu" ita dae Fatuu shiru tay masu can Yaya tace "sai kuka ji abun arzik'i kwatsam abun farinciki, ai dashi Baffan naki har zai maki bakin ciki Allah ya baki miji d'an Arziki muka dage kai da fata tunda da Arziki a garin wasu ai gara a naku a gidan ku ma, ko ba haka ba?" Banza Fatun tay mata ita dama tasan duk zugar Su ce tasa Ard'o ya tursasa ma Baffanta kan Maganar, tsam ta mik'e tace masu sai anjima Yayan na ba ta bari tasha ruwa ko don kar su je gidanta suma ta basu, bata tanka ta ba ta yi wucewarta tana jiyo yadda su innarsu Altine ke dariya suna fad'in ai kuwa dole a basu ruwa harda Naman kaji ma su da sukae ruwa sukae tsaki za'a auri mai Arziki, bayan fitar ta wata mai suna Hasiya ta kya6e baki tace "Sai wani d'aure fuska take don a ga bata so" a harzuk'e Yaya tace "aikuwa ko mutuwa zata yi sai an yi auren nan badae ita ga mara d'a'a ba bata ganin kowa da gashi an d'aure mata wutsiya ta raina kowa dama nace sai nayi maganin ta ai shiyasa Ard'o na yin Maganar Auren ta da d'an gidan chairman d'in na nace sai abun ya yuwu, inda lafiya lafiya ai wllh cikin yaran ku zan sa wata ta Aure shi a k'yaleta to amman gwara ita ta aure shin yadda zata kwashi kashin ta a hannu waye bai san rashin Mutuncin d'an gidan Chairman ba Mutumin dake taka kowa yadda ya ga dama kinga daidai da ita kenan sai taje tayi mashi rashin kunyar da ta saba ma Mutane" kyalkyacewa da dariya innar su Altine tay tace "ya kuwa sassa6a mata kaman ni wllh, wannan wa zai so yaron shi ya aure shi banda shaye shaye ga lalata yaran Mutane yanzu ji bi yarinyar nan Danejo yadda ya d'irka mata ciki hankalin shi kwance k'arshe kuma ya zubar mata tak'amar shi likita ne" Hasiya ta amshe "yo ai ba itace farko ba mata kala kala yake kawo wa a gidan Gonar nan aka ce harda arna" haka suka cigaba da tattauna mugun nufin su kan Auren Fatuu. Har wani duhu duhu take gani ta nufi sashen su lokacin da ta shiga falon su Mino ne zaune suna cin Abinci hakan yasa ta wuce cikin uwar d'aki ba tare data tanka ma kowa ba, Mino na kiranta ko jin ta bata yi ba, tana shiga ta haye saman gado can k'arshe tayi rubda ciki tana numfashi da k'arfi da karfi tana zare ido waye wanda za'a aura mata? Da gaske mai shaye shaye ne? Ita da a rayuwarta ta tsani mashayin mutum shine yanzu zai zama mijinta, shin miye d'ayar aika aikar da taji su zakiyya sun fad'a? Tana haka Mino ta shigo ta zauna a bakin gado tana kallon Fatuu ganin tak'i ce mata komae yasa a sanyaye tace "Adda Fatuu" shiru bata amsa mata ba bata kuma kalleta ba Mino ta sake cewa "Adda Fatuu miya faru kin yi shiru?" Sai lokacin ta kai idonta kanta amman still ta kasa tanka mata ganin hakan yasa ta mik'e ta fita bada jimawa ba sai gata sun dawo tare da Yadikko, a bakin gadon ta zauna ta kai hannu ta ta6a jikin Fatun da harshen fulatanci ta shiga tambayarta lafiya Mike damunta can ta yunk'ura ta tashi zaune idonta akan yadikko cikin karyayyar Murya tace "Don Allah waye za'a Aura man??" Da mamaki yadikkon tace "dama Baffan ki bai fad'i maki wanda zaki Auran ba?" da sauri tace "Ya fad'i man d'an Chairman ne amman ina son ki fad'a man wane irin Mutum ne?" Dam k'irjin yadikko ya buga ta hau had'iye miyau ganin ta kafe ta da ido alamar jiran amsa take yasa tace "Mutum ne kamar kowa kuma likita ne...." Katse ta Fatuu tay "ba wannan nike son sani ba wane irin hali gare shi?" Shiru yadikkon tay tana kallon Fatun ganin haka yasa tasa mata kuka ta kama hannuwanta tana fad'in "ki fad'a man yadikko don Allah da gaske Mashayi ne?" Zaro ido tay cikin rawar murya tace waye ya fad'a mata hakan nan take ta kwashe firan da ta ji su zakiyya nayi ta fad'a mata, shiru bakin yadikko ya mutu don bata san mi zata ce mata ba Fatun ta hau rok'onta kan ta fad'a mata, juyawa yadikko tay tace ma Mino da ke yin hawaye ta fita ta ce to, bayan ta fita yadikko ta juya kan Fatuu ta kama hannuwanta tace "haka ake cewa amman ni ban san ko gaske bane tunda ban ta6a gani da ido na ba na dae san shi tunda yana yawan zama nan gidan Gonar bayan ya gamo karatun likitancin da yayi a K'asar waje..." Tun kan ta rufe baki Fatuu ta tari numfashin ta "to bayan shi naji sun ce akwae wani abun da yake aikatawa miye?" Wani abu Yadikko ta had'iya a ranta take raya taya zata ce mata yana neman Mata ko shaye shayen ta san da gaske yana yi don kada ta tada mata hankali ne yasa ta nuna mata bata san ko gaske bane, ganin tayi shiru yasa Fatuu d'an girgiza hannunta tace "Yadikko ta don Allah kar ki 6oye man ki fad'a man" sauke ajiyar zuciya tay cikin rawar murya tace "k...kin gane w..wai ana zargin yana neman Mata ne a gidan gonar da yake zama....." Zaro ido Fatuu tay a kidi'me tace "Neman Mata kuma kenan Mazinaci za'a Aura man!!" ganin yadda ta rud'e yasa da sauri yadikkon tace "a'a fa kawae ana zargi ne wai ana ganin shi da mata amman kuma ai zai iya yuwuwa Abokan aikin sa ne tunda ba wanda ya ta6a shiga ya kama su suna aikata ba daidai ba kinsan irin Wannan baka saurin gasgata wa" girgiza kai Fatuu ta shiga yi cikin kuka take fad'in "ai yadikko in dae aka cika Maganar abu to tabbas akwae alamar gaskiya, mi zai sa ya rink'a zuwa da mata gidan gona in Abokan aikin nashi ne suyi aikin acan wurin aikin su mana, ni dae na bani na lalace k'arshe na ya zo za'a lalata man rayuwa taya zan yi rayuwar Aure da Mashayi kuma Mai neman mata, Ya akai Baffana ya amince a jefa man rayuwa cikin had'ari yadikko ya akai kuka amince bacin kun san halin shi haka yake so kuke ya lalata man rayuwa ne??" Itama Yadikkon kukan ta sa tana fad'in "a'a Fatuu kar ki ce haka Don Allah kin fi kowa sanin yadda muke son ki muka damu da rayuwar ki hakan ne ma yasa lokacin da Ard'o ya sanar da zancen Auren naki Baffan ki ya shiga mawuyacin hali har yay sanadin kwanciyar shi ciwo duk Saboda jin Mutumin da za'a aura maki k'arshe dae har zuwa yay wurin Chairman ya rok'e shi kan a hak'ura da had'a ku Aure koda ya tambaye shi dalili bai 6oye mashi komae ba game da halin yaron nashi da ake fad'a kuma ya nuna mashi ke karatun likita kike son yi anan ya nuna mashi ya kwantar da hankalin shi in dae wannan ne damuwar shi to saida ya tabbatar da d'an nashi ya shiryu ya daina komae sannan kuma har yarjejeniya sukae kan ko bayan auren ya kama shi yana aikata wani abu ba daidai ba sai ya sa6a mashi don dama a bisa sharad'i ya nema masa auren kuma ya tabbatar ma Baffan ki cewa da kunyi auren zaki cigaba da karatun ki don ya fahimci kina da kokari sosae tun lokacin da ya fara ganin ki tun sannan yaji kin burgeshi har yayi sha'awar D'an nashi ya aure ki, wannan ne dalilin da ya sa har Baffan ki ya gamsu sanin chairman d'in Mutumin Arzik'i ne ba zai ta6a had'a aurenku don son zuciya ba" shanye kukan Fatuu tay sai taji hankalin ta ya d'an kwanta ganin haka yasa Yadikko cigaba da lallashin ta tana k'ara kwantar mata da hankali had'i da nuna mata wani abun da biyu suka fad'a dama don su tada mata hankali su k'untata mata, ganin ta d'an samu natsuwa yasa ta d'agota ta tambayeta taje ta gaida Ard'o ta girgiza mata kai alamar a'a ta ce to ta daure taje in Baffanta ya dawo yaji bata je ba bazai ji dad'i ba a sanyaye tace to ta sauka daga saman gadon ta fita idon yadikko akan ta cike da tausayi take kallonta tana d'an girgiza kai. Koda taje iske shi tay da Mutane hakan yasa ba yabo ba fallasa ta gaishe su ta juyo ta dawo ta koma kan gado tay lamo. Sai bayan Magrib Baffanta ya shigo d'akin lokacin duk sun gama salla suka gaishe shi da fara'a ya amsa kafin ya zauna a nan yake sanar da yadikko game da zuwan wanda Fatun zata Aura gobe in Allah ya kaimu da yamma ta amsa da to ya nuna mata k'atuwar ledan da ya shigo da ita yace ga cefane nan sannan a yanka kaza ayi amfani da ita wurin shirya mashi Abinci ta amsa da to Fatuu dae tay tsit kanta a k'asa don wani irin bugu kirjinta ke mata jin wanda aka ce zai zo d'in, ganin yanayin ta yasa Baffan tambayar ta lafiya ta d'ago da d'an murmushi tace mashi lafiya lau daga baya ya fita, da daddare bayan ta kwanta duk kewar gwaggo ta dame ta don har yanzu basu yi waya ba can ta d'auki wayarta ta kirata tana jin ta fara ringing ta tashi zaune har kiran ya kusa katsewa bata yi picking ba har Fatun ta fidda ran zata d'auka sai gashi gab da zai tsinke ta d'aga tay yar sallama wani kalan lumshe ido Fatuu tay da d'an murmushi ta gaidata gwaggon ta amsa mata suka d'an yi shiru can gwaggon tace "anje lafiya, koda yake mun yi Magana da Kamalu yace kun isa lafiya" Fatun ta amsa mata da lafiya lau daga haka tace mata ta kwanta sai da safe bata jira cewarta ba tay cutting kiran, cire wayar tay daga kunnanta ta bita da ido kawae.

Readers Also Read