Kenza eBookz

Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature - Chapter 24

Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature - Chapter 24

Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature Chapter 24: Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature Chapter 24. Washe gari tun bayan da ta gama gyara d'akunan da…

4,484 words

Washe gari tun bayan da ta gama gyara d'akunan da suka gama karin kumallo wanda bata wani ci sosai ba ta yi wanka tasa doguwar riga ta haye gado, tana kwancen yadikko ta shigo ta zauna gefen gadon da d'an murmushi tayi mata sannu a hankali Fatuu ta amsa mata da yauwa yadikkon tace "Dama shawara nazo tambaya ku yan birni kun fi mu sanin kalolin Abinci masu dad'i wanne kike ganin ya kamata ay ma bak'on naki" shiru Fatuu ta d'an yi sai kuma cikin sanyin murya tace "Yadikko kema ai kin san Abincin masu dad'i ko" yar dariya tay tace "to ai duk na manta zuwa yanzu kuma ai nasan akwae wasu iri iri da ni ban sani ba" kaman bazata ce komae ba ganin yadikkon na kallonta yasa tace "ba naji Baffa yace a yanka kaza ba kawae ayi mashi pepper chicken ba sai anyi wahalar yi mashi wani Abinci na daban ba" shiru yadikkon ta d'an yi alamar tunanin sai kuma tace "amman kina ganin shi kawae ya isa, kamar da Abincin zai fi nike gani" d'an ta6e baki Fatuu tay tace "ai ba lalle fa yaci Abincin ba fa in aka yi wannan d'in sai a had'a mashi da fura sai in ga ya isa" cike da gamsuwa yadikkon tace hakan yayi ta mik'e Fatun ma ta yunk'ura zata tashi tace mata tay kwanciyar ta zasu yi komae dasu Mino daga haka ta fita, komawa tay ta kwanta don duk jikinta a sake yake ga fargaba had'i da zullumi da suka mata yawa, Bayan sallar Azahar Baffan ya dawo ya kawo Drinks masu sanyi yace ma yadikko tasa wanda za'a bashi cikin cooler sauran sai su sha tayi mashi godiya, koda Fatuu tay salla komawa tay ta kwanta da aka mata Maganar Abinci cewa tayi ba yanzu ba saida Yadikko ta matsa mata sannan ta d'an tsakura kad'an, ganin har k'arfe ukku tana kwance yasa Yadikko ta shiga tayi mata Magana kan ta tashi ta shirya kar yazo kuma bata kimtsa ba, zuru Fatuu tay mata har saida ta k'ara mamaita abunda tace Matan sannan tace ba sai ta shirya ba ai tayi wanka d'azun,

"To ki tashi ki canza kaya ko" tsuke fuska tay idanunta har sun kawo ruwa ganin haka yasa yadikkon fara rarrashin ta ta shiga nuna mata in tayi shigar kirki hakan zai sa ya mutunta ta amman in taje mashi a yamutse zai iya raina ta, da k'yar ta tashi don ta shiryan, wanka tayo lokacin an fara kiran la'asar hakan yasa ta d'auro Alwala saida tay salla sannan ta fara kokarin shiryawa tama rasa wane kaya zata saka can dae ta fiddo wata straight gown ta Maroon lace da touch d'in golden ta saka ta sa yan kunnan zinarin ta da yan hannu tana cikin shiryawa ta jiyo Muryar Kamalu a Parlor yana fad'in "Yadikko ga bak'on nan ya iso" ta amsa mashi da to ta mik'e tana tambayar yana ina ne yace mata yana a Fadar Ard'o, shigowa tay cikin uwar d'akan ta iske Fatuu zaune a gefen gado ta rafka tagumi itama ta zauna gefenta ta dafa Shoulder d'inta tace "bak'on naki ya iso Fatuu" kallonta tay ta fara d'an ta6e baki alamar zata fara kuka yadikko ta girgiza mata kai tace "Don Allah Fatuu ki yi hakuri ki fawwala ma Allah komae, shi mai ji ne kuma mai gani yafi kowa sanin halin da kike ciki don haka ki dogara da shi na tabbatar zai baki mafita ya za6a maki abunda yafi Alkhairi gare ki" d'aga mata kai tay ta kama hannunta ta mik'ar da ita, gaban mirror ta kai ta tasa ta ta shafa powder har jan baki tace ta shafa amman ta k'i tasa lip glow kawae yadikkon ta gyara mata d'aurin kallabin ta ya zauna sosae gashin ta dama ta lankwasa shi ya fito yay tum a baya, golden brown gyale mahad'in kayan ta yafa haka takalma ma sosae tay kyau duk da ba wani make up tay ba, tun da ta fito ta nufi hanyar soron k'irjinta ke bugu tamkar ana mata luguden ta6are hakanan take jin tsananin fargaban zuwan ganin abun take kaman almara ba gaske ba wai wurin wanda zata Aura nan da sati biyu zata je, da yar sallama ta shiga lokacin da ta k'arasa ko cire takalman k'afafunta bata yi ba tun a bakin kopar kamshin turaren da ya baza a jikinshi ya d'aki hancinta, a d'arare ta idasa shiga idonta a kan shi yana zaune akan kujerar da Ard'o ke zama ya sadda kanshi yana latsa wayarshi yana sanye da shadda brown wanda ta hau da fatar jikin shi sosae anyi mashi irin fav d'inkin Haisam wato senator style saidae basu amshe shi kaman yadda suke amsar jikin Haisam ba don yanayin halittar jikin ba d'aya ba, bai sa hula ba hakan ya bayyanar da sumar shi dake a lallank'washe hannunshi sanye da brown wrist watch, ba laifi shigan tay kyau kana ganin shi kaga wayayyan d'an boko, tsaye tayi daga d'an can nesa bayan ta shigo tana kallon shi tana haka su Mino suka shigo da kayan Abinci suka nufi gaban shi suka aje had'i da gaishe dashi kaman bazai amsa ba sai kuma yace "lafiya" ba tare da ya d'ago ba balle su samu Arzik'in kallo suka juya suka fita, sun d'auki lokaci a haka sai da ya mula ya sha iska sannan slowly ya d'ago ya sauke mayatattun idanunshi tamkar na mai jin bacci akan Fatuu dake tsaye a gaban shi, kallo suka bi juna da shi tun bayan da ya d'ago Fatuu ke mashi kallon sani hakanan taji kaman ta ta6a ganin shi to amman a ina? Shine abun da take son ta gano, wani irin jarababben kallo yake bin ta dashi from head to toe tsam ya mik'e walking slowly toward her, a gabanta ya tsaya har saida Fatun tay stepping back Saboda yadda ya k'ure mata, a hankali ta kai idanunta kan fuskar shi lokaci guda k'irjinta yay wani irin bugu tuna inda ta ta6a sanin shi d'an buda ido tay sai kuma da sauri ta sadda kan ta kasa,

"Why am I having d feeling dat I know u somewhere??" taji husky voice d'in shi ta fad'a wato shima ashe yaji ya santa wani wurin, K'in d'agowa tay gaban ta naci gaba da fad'uwa wani irin mugun tashi hankalinta yay ganin shi matsayin Mutumin da zata aura, "Hey!" taji ya fad'a da d'an d'aga Murya a hankali ta d'ago duk ta kame kanta sai zare ido take ya k'ara kankance idon shi yana kallon ta da alama so yake ya tuna inda ya santa can bayan d'an lokaci kawae sai gani tay yay wani kalan murmushin mamaki ya d'an kya6e baki kafin ya furta "Wonders Shall Never End, so u'r My Wife to be!!!" bin shi da ido kawae take sai faman sakin Shu'umin Murmushi yake.........

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 da 3 Naira 400 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268._

*ASM Bk2029*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

.......Juyawa yay walking majestically ya koma inda ya ta so ya zauna idon shi a kanta,

"zaki ta tsayuwa ne?" Ya tambaya had'i da d'age mata gira wani kuka cikinta ya fara yi, kaman k'wai ya fashe mata a ciki ta fara moving zuwa gefe inda wata kujerar take ta zauna tana cigaba da kallon shi, "From all indications kema kin gane husband to be en naki ko?" wani wahalallan miyau ta had'iya bata dae ce komae ba,

"I ave been wondering wata kucakar Dad ya sama man matsayin Mata a Wannan tsukukun k'auyen ashe ba kucakar bace mara kunya ce mai zagin iyayen Mutane" still bata ce mashi komae ba yaci gaba "But duk da haka am so happy Dad has made a right Choice for me, it's nice meeting you my lovely wife" bakin Fatuu fa ya mutu murus ba kamar da ta ga irin murmushin da yake saki tasan ba har zuciya yake fad'ar abubuwan da yake fad'i ba,

"Kin bi ni da ido ko baki farin ciki da ganin husband en naki bane shiyasa ko Welcoming dina bazaki ba balle in sa ran za'a gaida ni, koda yake I know who my wife to be is ba lalle in ta iya gaida Mutane ba" d'an motsa baki tay sai kuma ta sunnar da kai katsa yayin da a cikin ranta ta furta innalillahi Wa'inna ilaihir raji'un, sam ta kasa bud'e baki tace wani abu don ba k'aramin Al'ajabi ne ya kamata ba, a hankali ta saci kallon shi taga still kallon ta yake hakan yasa ta idasa dagowa cikin trembling voice tace "ina wuni an zo lpy" d'an tafa hannu yay yace "Wow what a sweet voice, lafiya lou wife hope na same ki lpy?" tabdijan ya gama kashe Fatuu da mamaki duk yadda tay zaton zai mata ba haka take gani ba ganin tayi kasak'e tana bin shi da ido yasa ya d'age mata gira yace "Wife Kaman ke baki farin cikin gani na a matsayin wanda aka za6a maki ba ko" murya a hard"e tace "a'a nayi" jinjina kai yay yace "To ya Katsina fatan kin zo lafiya" tana d'an kikkafta ido tace mashi lafiya lau yaci gaba "dama ina ji ana cewa Katsina akwae beautiful babes masu ilimi da wayewa yanzu na shaida haka even though ke d'in asalin yar nan ce amman su suka maida man ke yadda nike son wife ena ta kasance" ya k'arasa yana wani juya yaudararrun idanun sa, sunnar da kanta tay k'asa don Maganar tashi ba wanda ta tuno mata sai Haisam Saboda shi ne ya maida ta yadda take,

"na fa san kina Magana so ki daina acting as if baki magana ko yana maki wuya, ki saki jiki ki kuma bud'a baki ki man magana kaman ranar da kika zage ni" da sauri ta d'ago ta kalle shi ya bud'a mata ido d'an yamutsa fuska tay cikin breaking voice tace "ni fa ba zagin ka nayi ba kuma Kaine ka fara zagi na ai" Shegen murmushin shi ya saki yace "kika rama kuma ko, anyway ai baki ji nace kin yi laifi ba ya wuce koma kin yi ai Amarya bata laifi if u wish yanzu ma zaki iya zagi na I won't feel offended" ya ilahi ya rabbil alamen mutumin nan nema yake ya tarwatsa ma Fatuu zuciya, shiru suka d'an yi sai faman k'are mata kallo yake can yace "Wife ina buk'atar ruwa or I should serve myself ?" a hankali ta juya ta kalleshi sai kuma ta mik'e ta nufi gaban shi ta duk'a ta fara kokarin zuba mashi lemu hannunta har d'an rawa yake, bayan ta zuba ta d'ago da niyyar bashi taga gaba d'aya hankalin shi na a wani wuri a jikinta hakan yasa ta d'an d'ukar da idonta don taga abunda yake kallo ashe saman boobs d'inta da sukae fam fatar wurin fari fat da ita ya kafe da ido yana kallo sakamakon wuyar rigar da yake a bud'e sosae, da sauri ta ja gyalen ta rufe wurin hakan ya sa shi dawo wa cikin hayyacin shi ya kalleta da murmushi kafin ya kai hannu ya amshi glass cup d'in had'i da furta "thanks my beautiful wife" mik'ewa tay ta koma ya bi bayanta da kallo har ta zauna sannan ya kai cup d'in baki ya fara sipping lemun saida yasha kaman rabi sannan ya ajiye ya kalleta ta d'ukar da kanta tana d'an wasa da yatsunta taji ya d'an yi gyaran murya hakan yasa ta kalle shi yace "Wife miye labari" d'an watsa hannu tay tace "babu" yace "What about preparations na bikin mu?" Kaman bazata ce komae ba sai kuma tace "ana yi" gyara zama ya d'an yi yace "Ok dame dame zaku yi ne?" tace "ba komae" d'an buda ido yay alamar mamaki yace "Haka zaku yi bikin ba wasu programs kaman zaki auri enermy en ki" ido kawae take bin shi da shi yaci gaba "koda yake baki da Friends anan ko?" Kai kawae ta d'aga mashi ya jinjina nashi,

"To yanzu kaman nawa kike buk'ata na abunda kike ganin zaki yi like gyaran jiki and so on" ya tambaya, tace "zanyi ba sai ka bani ba" yar dariya yay ya d'an shafi sumar shi yace "Ashe wife en nawa Hajiya ce" shiru bata ce komae gaba d'aya sai taji ta k'agara ma ya tafi kota koma ciki don gaba d'aya kanta a d'aure yake bata da natsuwa,

"Gobe sister d'ina zata zo zaku je wurin tailor zai taking measurement naki sai ki shirya" kallon cikin ido tay mashi yace "let me have ur digits so dat lokacin da zasu zo sai in sanar maki" karanto mashi phone number d'in ta tay bayan ta gama ya kira jin wayan na ringing ba anan ba yasashi tambayar inda wayan take tace tana cikin gida yace to in ta koma sai tay Saving harda fad'i mata sunan shi Khalid ya tambayi nata tace mashi Fateema yana murmushi ya furta "Fatima Zaraah" har saida kirjinta ya buga damm, ganin yana kokarin mik'ewa yasa tace bai ci Abincin ba yana wani kashe mata ido yace he's Ok bai jima da ya ci Abincin ba but next time in ya zo zai ci daga haka ya mik'e itama tana ganin hakan ta mik'e ya nufo in da take ya tsaya suna facing juna ya kafeta da mayaudaran idanunshi seductively ya furta "Hope ban yi laifi ba da ban ci ba kar next time a ki dafa man don nasan girkin ki must ba as hot as u'r" wani dam dam k'irjin ta ke yi ganin yadda yake mata Magana ba zato ba tsammani sai ji tay ya kawo hannu ya janyota ya had'e jikinsu a gigice ta shiga kiciniyar kwace jikinta saidae ta kasa a rud'e tace "Don Allah ka sake ni kar wani ya shigo fa ayi tunanin wani abu nike yi" gaba d'aya ya zuba ma lips d'inta ido yadda tay Maganar ba k'aramin tafiya tay da shi ba kokarin had'a face d'in su yake a kidi'me Fatuu ta tattara duk k'arfinta ta tura shi tay baya ta fad'a kan kujerar da ta tashi, wata yar iskar dariya ya saki yace "Wife zaki ji ma kan ki ciwo fa and miye abun rud'ewa haka kaman na aikata wani abu ba daidai ba, ko basu yi informing naki an biya sadakin ki bane?" Kasa cewa tay komae sai numfashi take fitarwa da sauri da sauri duk ya gama tsorata ta, still dariyar yake yace "I forgot wife en tawa Secondary graduate ce but at least be romantic Babe" daga haka yasa hannu a cikin Aljihun rigarshi ya fiddo rafar yan dubu dubu guda biyu ya d'aura mata akan cinyarta kafin ya sake sa hannu a aljihun ya fiddo farin glass ya sa a fuskar shi yana murmushi yace sai sun sake had'uwa daga haka ya fice, Mutuwar zaune Fatuu tay tama rasa tunanin da zata yi akan shi da k'yar ta iya yunk'ura wa ta mik'e jikinta har lokacin rawa yake ta nufi cikin gidan a kan hanya ta had'u da Mino tace mata taje ta kwaso kayan abincin da suka kai tace to, a Falo ta iske yadikko zaune tana ganinta tay mata Murmushi tace har ya tafi ta d'aga mata kai kafin ta wuce cikin d'aki tana shiga ta cillar da takalmanta ta cire gyalen shima ta wurgar ta haye gadon sai zare ido take tunani kala kala acikin ranta ba kamar akan had'a jikinsu da yay hakan yasa ta fara shakkun anya ba gaskiya bane yana neman mata in ba haka ba mi zai sa daga fara haduwar su yau ya had'a jikinsu bama wannan ba kadae har fa kusan had'a bakunan su yay ba don ta samu ta fizge ba, wata zuciyar kuma ta ayyana mata ai yace don an biya sadakin ta ne to amman ai ba'a d'aura masu aure ba ko, gashi sam ta kasa yadda da yanda ya sake mata sai take ganin kamar akwae dalilin hakan, tana ta zancen zuci har Yadikko ta shigo bata sani ba saida ta zauna ta kira sunanta sannan ta kai idanunta kan ta, tambayarta tay lafiya dai ko taga ta shigo ta kwanta ko wani abun ya faru ne ta k'ak'alo murmushin yak'e tace mata a'a lafiya lou,

"To Allah yasa dae kun fahimci juna yayi maki kuma" d'an ta6e baki Fatuu tay a sanyaye tace "koma bai man ba yadikko ya zanyi dole ai in Aure shi ko" shiru tay tana kallonta gaba d'aya tausayinta take ji don daga yanayin ta sai taga kaman bai mata ba, tambayarta tay ya akai taga bai ci komae ba Fatun tace "Yace ya k'oshi sai ya sake dawowa zai ci" jinjina kai tay tace mata to ta taso suje ta ci farko taso ta k'i tace ta k'oshi saida Yadikkon ta matsa mata sannan ta saukko lokacin ta nuna mata kud'in da ya batan na abubuwan da zata yi tace to ta ruk'e a wurinta. Da daddare tana cikin yin shirin kwanciya sai ga kira ya shigo wayarta koda ta duba bata gane mai kiran ba hakan yasa tak'i d'agawa taci gaba da abunda take sai gashi an sake kiran, zama tay bakin gado ta d'aga ba tare da ta ce komae ba on the other hand taji ance "Wife ko kin yi bacci ne" rass gabanta ya buga jin muryarshi sai lokacin ta tuna da d'azun ta bashi no dinta har ya kira yace tay Saving, sake maimaita tambayar da yayi mata yay sai lokacin tace mashi a'a yanzu zata kwanta,

"Gani na kasa bacci Saboda tunanin ki wannan shi ake kira da luv at first sight all I need in ji ki gefe na hope kema hakan?" shiru tay mashi har saida ya k'ara tambayar tata sannan ta tura baki tace "a'a" tana jiyo sautin dariyar shi yace "Don't worry Babe zan koya maki yadda kema zaki rink'a jin hakan game da ni" shirun dae ta k'ara ita duk ta fara tsorata ma da shi haka ya dingi yi mata kalaman soyayya harda tambayarta wace tarba zata mashi a first night d'in su ita dae a tak'aice take bashi amsa wani wurin kuma ta mashi shiru jin shiru shirun nata yay yawa yasa shi tambayar ko ta fara jin bacci ne tace mashi eh yace bari ya barta ta kwanta harda cewa tayi bacci mai dad'i kuma tayi mafarkin shi shima zai yi nata ita dae shiru tay mashi tana niyyar cire wayar taji sautin wani matsiyacin kiss da yay mata har cikin dodon kunnanta da sauri ta cire wayar ta k'ura ma screen d'in ido kirjinta na beating very fast can ta runtse idanunta sai ga kwalla sun fara zubowa ba kowa ne ya fad'o mata a rai ba face Ya Haisam ji take inama shine yake nuna mata so haka ba wannan ba da take tunanin duk k'arya ne da biyu yake mata hakan ba don yana sonta tsakani da Allah ba, tana ta tunane tunanenta har bacci yay awon gaba da ita,

Washe gari bayan sun kammala yin breakfast ta gyara d'akin sai ga kiran shi wai ya kira ya ji ya ta tashi tace mashi lpy Lou anan yake sanar da ita ta shirya around 1:00 za'a zo atafi da ita ta amsa da to, lokacin ta sanar ma yadikko ita kuma ta kira Baffanta a waya ta gaya mashi yace to ta dawo lafiya ta so ace Mino ta dawo daga Makaranta ta rakata, wurin karfe d'aya saura tana cikin shiryawa yadikko ta shigo cikin d'akin ta sanar da ita game da zuwan wadda tazo tafiya da ita wato Sadeeya tace to, doguwar rigar shadda sabowa dal acikin irin kayan da Haisam yayi mata Navy blue tasha aiki blue da fari yayi kyau sosae ta sa yan kunne da sark'a sai Agogo duk silver sai farin mayafi haka takalma ma high heels ne farare ta d'auki yar clutch dark blue, a saman kujera Sadeeya ta zauna ita da wata yarinya da zata yi shekara bakwae da suka zo tare tana sanye da jeans da t-shirt kanta sanye da hula da bayanta ya d'an yi tudu alamar gashin ta a fake yake, itama Sadeeyar a shekaru zata yi shekara 25 zuwa 26 itace k'anwar Khalid ta biyu, ta farkon wato Yayar Sadeeyar tayi Aure, a ABU Zaria Sadeeya ke karatu itama fara ce saidae bata kai Khalid haske ba sannan ita da Chairman take kama duk da ta wani 6angaren ta d'an yi yanayi da Khalid d'in tana da d'an jiki ba kamar khalid ba, sanye take da doguwar rigar atampa d'inkin Abuja Boubou ta kashe daurin kallabi hakan ya bayyanar da wutsiyoyin kitson dake kanta da ta tubke, da fara'a lokacin da yadikko ta fito ta sanar mata Fatun na fitowa tana k'arasa shiryawa ne itama tana fara'ar tace Ok ba damuwa, ruwa da Abinci yadikko ta kawo masu Sadeeyar na cikin shan ruwan Fatuu ta fito ba shiri ta cire cup din daga bakinta ta bi ta da kallo wanda ke bayyanar da mamaki akan fuskarta, sam bata taba tsammani ganin ta hakan ba duk da ta samu labarin ba anan take ba batai tunanin ganinta a waye haka ba ba kuma kaman da taji Secondary graduate ce, kujerar dake gefen su Fatuu ta nufa ta zauna fuska a d'an sake ta gaishe da Sadeeyar da sauri tace "Ah Auntyn mu ni ai yakamata in yi wannan" tay Maganar tana ma Fatuu dariya ita dae d'an murmushi kawae tay kafin tace sun zo lafiya Sadeeya ta amsa mata da lafiya lau, shiru sukae Fatuu ta lura da kallon da take mata hakan yasa ta d'an juyar da kanta gefe, can Sadeeyar tace "Auntynah if u done we can go driver is waiting for us outside" juyowa Fatuu tay ta kalleta sai kuma ta kalli Abincin gaban su a nutse tace "But u aven't ate d Food" d'an lumshe ido Sadeeya tay kafin tace "bamu jin yunwa ne amman tunda kin yi Magana bari mu d'an ci" tana niyyar tashi don ta zuba masu Sadeeyar tace mata ta bashshi bari ta zuba masu yarinyar da suka zo tare sai kallon Fatun take can ta d'an duk'a saitin fuskar Sadeeya tace "Aunty Sady who is she?" d'agowa tay tana yar dariya tace "she's ur New Aunty Ya Khalid's bride" waro ido yarinyar tay Sadyn tace taje ta gaida ta ta nufi Fatun tana zuwa ta tsaya gabanta ta gaishe ta da turanci Fatun ta amsa mata ta tambayi sunanta tace mata Basma, ba wani mai yawa Sady ta ci ba ita basma ma bata ci ba suka tashi don tafiya Yadikko tace ma Fatuu ta biya dasu su gaisa da Yaya ba don ta so ba ta amsa mata da to kawae itama Yadikkon gudun tsegumi yasa tace su je don zai iya zama abun Magana, kaman ko yaushe tana zaune da yan taya ta gulma su ukku lokacin da suka shiga cikin d'akin Yaya na d'aura idonta kan Sadeeya ta gane yar gidan Chairman ce hakan yasa ta nuna mata gefen gado tace ta zo ta zauna ita dae Fatuu tsaye tay Sadeeya ta shiga gaishe dasu da fara'a suka amsa suna ma Basma wasa, Yaya ce ta tambayi Sadeeya daga gidan Chairman ko tace mata eh sun zo zasu tafi da Amarya ne za'ai mata awon d'inki ta jinjina kai alamar gamsuwa daga baya ta mik'e tay masu sallama suka fita ba tare da Fatuu tace ma kowa komai ba, bayan fitar su Yaya ta ta6e baki had'i da yamutsa fuska cikin harshen fulatanci tace "Yi ma yarinyar can aure ba k'aramin rufa mata Asiri akai ba don Allah kadae yasan abunda take aikatawa a can, kuji irin yadda take saka sutura kai kace itace d'iyar Chairman d'in ma a ina ita kakar ta ta taga kud'in da zata rinka d'inka mata suturun da da gani masu tsada ne" Hasiya ta kar6e "ai fa dama da gani idonta a bud'e yake wllh" Yayar tace "kin ga an za6a mata miji daidai da ita kenan" haka suka cigaba da yi ma Fatun kazafi, suna fita kopar gida Driver ya fito ya bud'e ma Fatuu kopa bayan ya gaidata ta amsa mashi a sake Sadeeya ta zagaya d'ayar kopar ta shiga Basma kuma ta shige gaba, Tafiyar kamar Minti 35 ta kawo su a bakin k'aton gate d'in gidan Driver yay horn mai gadi ya lek'o kafin ya koma ya bud'e masu ya shigar da Motar, bayan sun fito da murmushi Sadeeya tay ma Fatuu jagora zuwa cikin gidan lokacin da suka shiga Main Parlor d'in gidan ba kowa hakan yasa tace ma Fatuu su je cika ta nufi wata babbar kopa suna shiga wani madaidaicin Parlor ne da bai kai na farkon ba, zaune akan sofa 3 seater Hajiya Rabi'atu ce jikinta sanye da doguwar rigar Atamfa a gefenta kuma wata mata ce itama tana sanye da doguwar rigar shadda kafad'arta d'aya rataye da gyale da gani bak'uwa ce tayi, suna shigowa duk suka kalle su da sauri Sadeeya ta d'aga gyale ta rufe saitin Fatuu tana dariya tace "Mom sai kin biya zaki ga face en bride d'in mu" tana rufe baki Basma ta ruga ta fad'a saman jikin Mom d'in nasu tana dariya tace "Mom she's very beautiful" d'an buda ido Mom d'in nasu tayi sai kuma ta d'aga basmar ta mik'e tana dariya ta nufi Sadeeya tana zuwa tasa hannu ta d'an tureta gefe tana fad'in sai ta ja mata rai zata bari taga Daughter d'in ta gaba d'aya harda k'awar tata sukae dariya, had'a ido sukai da Fatuu bayan ta janye Sadeeyar ta bi ta da kallo hakan yasa Fatuu ta sadda kan ta k'asa, tana sakin kayataccen murmushi tace "U'r highly welcome My Beautiful Daughter nayi matuk'ar farin cikin ganin ki" a hankali Fatuu ta d'ago ta kalleta a sanyaye ta gaishe da ita tana ta fara'a tace su je ta zauna sai su gaisa sosae tay patting shoulder d'inta suka wuce, kan one seater ta Zaunar da ita kafin ta koma inda ta taso itama ta zauna k'awar tata tace "in ce Amaryar Khalid d'in ce" ta amsa mata da itace tace "Ma sha Allah kyakkyawa da ita Allah yasa Alkhairi ya kaimu Ranar" duk suka amsa da Amin idon Momy akanta tana ta mata murmushi ita dae Fatuu sai faman sussunar da kai k'asa take, "Daughter fatan an zo lafiya" ta tambayi Fatun a hankali tace mata lpy lau ta k'ara cewa "Ya Grandma d'in taki ance a wurinta kike zaune" wani iri Fatuu taji jin an ambaci gwaggo kafin ta d'an kalleta tace tana lafiya, "Ya karatun ki ai kin gama ko" kai Fatuu ta d'aga tace eh,

Readers Also Read