Kenza eBookz

Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature - Chapter 55

Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature - Chapter 55

Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature Chapter 55: Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature Chapter 55. Bayan sallar Azahar Saude ta kawo Abincin lokacin…

4,440 words

Bayan sallar Azahar Saude ta kawo Abincin lokacin Fatuu ta farka saida ta shiga d'akin tay mata ya jiki sannan ta tafi gwaggo ta zubo ma Fatuu Abincin da aka kawo wanda lafiyayyar sakwara ce miyar egusi da tasha ganyen ugu ga ganda da kuma nama sai farfesun yan ciki wanda hanta tafi yawa a ciki sai uban k'amshi ke tashi ta kai mata d'aki itama Abincin ya burgeta tun bata ci ba, saida ta wanko bakin ta sannan ta fara ci, bayan gwaggo ta zuba ma Amadu ta mik'a mashi itama ta zuba ta koma d'akin Fatun ta zauna kan Carpet tana ci suna d'an yin fira da Fatun dake zaune a bakin gado tana cin Abincin, wurin la'asar Fauzy tazo harda Abinci ta kawo masu bayan ta shiga sun gaisa da gwaggo ta aje mata basket d'in tana ta mata godiya ita kuma tana murmushi tana cewa ba komai ta fito ta nufi d'akin Fatuu lokacin tana kwance tayi wanka ta canza kaya zuwa doguwar rigar material itama Fauzy ita ce a jikinta tayi rolling veil tana rataye da side bag suna had'a ido suka sakar ma juna murmushi ta nufi gadon Fatuu ma ta tashi zaune, hayewa gadon Fauzy tay ta yadda suke facing juna tace "sannu Amaryar mu ya k'arfin jiki?" Yar harararta Fatuu tay Fauzyn tana dariya tace "ai dai ba k'arya nayi ba ko kuma wasa da gaske amaryar ce ke, kinsan kuwa a Makaranta dana fad'a cewa ke matar aure ce akaita mamaki" Fatun tace miyasa ta fad'a tace "to ai kinga dama anata gulma gashi yau baki je ba sai tambayata ake wai badai jikin naki bane yay tsanani shine nace masu miscarriage ki kai dama ke matar aure ce mijin naki ne ba zaune yake a K'asar ba yana dai zuwa, aikuwa kinga yadda akaita mamaki kuma wllh nan da nan suka yarda har wasu na cewa wai shiyasa wani lokacin kike zama hostel wani lokacin kuma kiyi day nace masu eh har na bud'e pictute d'in ki wanda kikae tare dashi na nuna masu wasu suka ce sun ta6a gani ya kawo ki wasu kuma ya zo d'aukar ki Zainab Muhammadu ma cewa tay tabbas ta ta6a ganin shi har sukai ta yaba kyawun shi ita da su Sa'adatu nan fa ta hau shela harda hawa saman Desk tana fad'in to masu gulmar Fatima Ard'o na da ciki tabbas tana da shi kuma na halal ne don da auren ta kuma gashi nan sun ja sakamakon gulmar da suke cikin ya zube sai Allah ya saka mata bak'in k'azafin da akai tay mata, sosae ta bani dariya wllh" d'an murmushi Fatuu tay ta d'an ta6e baki tace "Auran dake lilo" da sauri Fauzy tace "in sha Allahu ba wani lilon da yake komai zai daidaita mu sha biki...." Katseta Fatuu tay "har yanzu fa Fauzy fushi yake" Fauzy tace "zai yi ya gama ne amman ni na tabbatar ya riga ya gama shigowa hannu tunda abunnan ya faru kin ma tuna man ga sak'o Aunty Mareeya ta bani in kawo maki" tana kai Maganar tasa hannu ta ciro side bag d'inta ta bud'e wata kullin bak'ar leda ta fiddo bayan ta bud'e ta ciro wata yar kwalba madaidaiciya ta mik'a ma Fatun ta amsa ta fara karanta sunan maganin da bayanin yadda ake amfani dashi ba Arzik'i tasa hannu ta rufe baki Fauzy ta kyalkyace da dariya tace "Wllh nima sunan maganin ya ban dariya lokacin da zata bani sak'on fa hana ni tay in duba aikuwa ina hawa Napep na bud'e nima saida na rufe baki nace Ya Haisam ya bani ana shirya mashi makaman da zasu tarwatsa miskilancin shi" yar dariya Fatuu tay tare da d'an girgiza kai Fauzy ta shiga fiddo sauran tana mata bayani wani da Madara zata sha wani da nama haka tay ta mata bayani ita dae tayi zuru saida ta gama sannan tace "Dama sana'ar kika fara yi kinga yadda kike bayani sai kace kece mai maganin" Fauzy ta kyalkyace da dariya Fatun ta k'ara cewa "kema yakamata Fauzy ki manta da abunda ya faru ki fara saurarar samari ko Kya samu miji kema kiyi auranki, lokaci tafiya yake muna k'ara shekaru gashi mutuwa ake yakamata muyi auren ko don mu samu masu yi mana Addu'a" idanun Fauzy ne suka ciko da k'walla cikin raunanniyar murya tace "Wllh Zarah na kasa mantawa da Mujaheed duk da irin abunda yay man ba kuma wai ace in ya dawo gare ni zan iya auran shi ba wllh tllh ko da ace misali dole sai shi zan aura to saidai in mutu ban auren ba, kawae zuciyata ce sam bata man Adalci data kasa cire man shi a rai",

Fatuu tace "matsalar daga wurin ki ne Fauzy kin k'i ba wani namiji dama da zaki daure ki ba wani da yake son ki dama a hankali zaki ga kin fara cire shi a ran ki, ki daure Pls" ta kai hannu ta kama hannunta guda, d'an murmushin yak'e Fauzy tay tace "zan jaraba in sha Allahu duk da a yanzu ba wani da zan ba damar amman k'ilan ko da bikin ki kinsan ance a bikin wata wata ke samun miji" ta k'arasa tana d'an murmushi haka Fatun ma tace "wai wane biki abunda an riga da an d'aura tuni" da sauri tace "aikuwa dole in komae ya daidaita mu sha shagali sai kace wani auren mak'iya za'a yi shi lami dole musha anko mu cashe bikin d'an Senator guda" dan ta6e baki Fatun tay can tace "Don Kawu Amadu bai had'u ba dana had'a ku" yar harara Fauzy ta wurga mata "Kawu Amadun ne zaki ce bai had'u ba santalelen saurayi dashi ga tsawo gashi fari ga kyau daidai gwargwado" dariya Fatuu tay tace "ai ba wannan had'uwar nike nufi ba ta kud'i nike nufi shi baida kud'i ke kuma na fi son ki auri wanda Mujaheed zai girgiza in yaji" d'an murmushi Fauzyn tay "Allah ya za6a mana abunda yafi zama Alkhairi a gare mu" Fatuu ta amsa da Amin suka cigaba da hira har Fauzy na ce mata ta tashi ta 6oye magungunan kada gwaggo ta shigo ta gani tace to tana k'ok'arin sauka daga gadon.

Tun bayan da Haisam ya maido su G.r.a ya wuce don yin wani aiki a computer sai da akai Azahar sannan ya dawo gidan Hajiya ya kwanta bacci, saida aka fara kiran sallar la'asar sannan ya tashi yay wanka ya shirya ya wuce Masallaci, bayan ya fito daga Masallacin parlon Hajiya ya wuce lokacin da ya shiga ba kowa ya nufi ciki ya zauna kan 2 seater ya d'auki remote yana canza channel, bai dad'e da zama ba Hajiya ta fito jikinta sanye da doguwar riga da mayafinta hannunta ruke da sandar ta haka idanunta na saye cikin medical glasses d'inta hango shi da tay yasa ta nufi cikin parlon don da gidan su Fatuu ta fito zata, tana zuwa cikin parlon ya d'aga ido yana bin ta da kallo har ta zauna a kan one seater d'in dake gefen shi itama kallon shi take bayan ta zauna tace "ashe ka tashi" kai ya d'aga mata,

"ai tun d'azu nike dakon ka bansan ma ka dawo gidan ba saida Saude ta dawo daga gidan su Fateema nike tambayarta ko taga Motar ka a parking space tace man eh" shiru kaman bazai ce komae ba sai kuma yace "ba sai ki kira ba" d'an ta6e baki tay tace ai na kira ka sau biyu ko, farko landline na kira ba'a d'aga ba na kira wayar ka itama baka d'aga ba nan nagane bacci kake" yana ta kallonta har ta gama sannan ya d'an d'age gira yace "Wani abu?" tace "kaci Abinci ne?" Kai ya girgiza mata alamar a'a, "to sai kai zaune da yunwa baka iya shiga kaman magana" tay Maganar tana d'an hararar shi d'an guntun murmushi yay "ban jin shi sosae ne" tace "uhmm kai dai ka sani wa zai zauna yay ta fama da kai kan abunda amfanin kan ka ne alhali kai ba damuwa kai da halin da mutum zai shiga ba ya mutu ko yay rai ba abunda ya dame ka" d'an murmushi yay kawae ya fahimci kan zancen ciki daya zo yay mata take Magana da alama dae abun yay mata zafi,

"Am all ears da wani abu ne?" Fuska a kwa6e tace ya ci Abinci tukun ta juya tana k'wala ma Saude kira bayan ta fito ta bata umarnin kawo mashi Abincin, akan c-table ta d'aura tray d'in kayan Abincin tana kokarin yin serving nashi ya d'aga mata hannu alamar ta bashshi ta mik'e tace aci lafiya ya jinjina mata kai, a nutse ya fara cin Abincin yana yi yana kallon channel d'in daya kamo Hajiya ma idonta na akan Tv d'in tana kallon American film d'in da ake yi tana yi tana d'age kai had'i da yamutsa fuska wani lokacin har hannu take d'an d'agawa in anyi abun tashin hankali, bai d'auki lokaci mai tsawo ba ya gama ya yago tissue yana goge baki, kallon Hajiya yay bayan ya gama yace mata "am done" ta maido idonta kan shi saida ta gyara zama ta fara magana "dama game da Fateema ne tunda an sallamo ta ina son in ji miye matsayin ta tunda bai yuwuwa a barta tay ta zama da aure a kanta ba kamar yanzu da tasan da shi" shiru yay yana kallon gaban shi har saida tace mashi kar ya 6ata mata lokaci ya bud'e baki yay mata magana don fita take son yi, sigh yay ba tare da ya kalleta ba yace "I will divorce her" wani kallo Hajiya ta bishi da shi jin bata ce komae ba yasa ya juya ya kalleta ganin kallon da take mashi yace "dama haka aka tsara ai ba Abbas ya fad'a maki ba?" a k'ufule tace "eh ya fad'a man hakan aka tsara amman bai ce acikin tsarin anyi da kai zaka rabata da budurcin ta ba" yana jin haka ya juyar da fuskar shi daga barin kallon ta taci gaba "Yanzu kai irin Adalcin ka kenan? Sai da ka raba yarinya da pride d'inta sannan zaka ce ka saketa wato k'aramar bazawara kake son mayar da ita kenan, idan k'anwar ka ce zaka so ai mata haka?" Shiru bai ce komai ba bai kuma kalleta ba a fad'ace tace "ba tambayar ka nike ba Haisam! idan Jidderh ce Fateema zaka so ai mata haka?" Sai lokacin ya d'an juyo slowly ya furta "am sorry for dat" daga haka yay shiru itama bata k'ara cewa komae ba sai da aka d'an d'auki lokaci sannan ta dasa fad'in "ko kusa ban amince wai kace zaka saketa ba yanzu ta riga ta zama Matar ka dole kaci gaba da zama da ita don haka yanzu dole ta baro gidan su akawo ta part d'in ka nan zata cigaba da zama kafin muga abunda Allah zai yi sai kasan yadda in ka koma zaka sanar ma Matar ka ni kuma daga baya zan kira iyayenka su zo harda ita ta Lagos din sai in sanar masu su kuma ganta ko don Saboda halin rayuwa bai kamata ace duk basu san da Maganar ba auren ba" shiru yay can ya kalleta yace "is dat all?" Kai ta d'aga mashi ganin yana K'ok'arin mik'ewa yasa da alamun mamaki tace "au tashi za kai bazaka ce komae ba?" Dakatawa yay yace "So What do you want me to say ba kin tsara komae ba kiyi yadda yay maki" wannan karon bud'e baki tay galala tana kallon shi ganin hakan yasa shi d'an d'age gira "ba haka ya yi maki ba so just go ahead do as u wish" ta6e baki tay tana mashi wani kallo tace "to yalla6ai shikenan" mik'ewa yay ya nufi hanyar barin parlon walking majestically Hajiya ta saki baki tana bin bayan shi da kallo har ya fuce, hannu ta kai ta ruk'e ha6a a fili tace "tabbas Yau na shaida Miskili yafi mahaukaci ban haushi kaji fa yaron nan don Allah wai ni zai ma duniyanci, in da farko ya aure ta don ya taimaketa wannan na yarda don zai iya yin hakan amman na tabbatar yana son zama da Fateema shiyasa bai saketa ba kamar yadda suka tsara" ta kai Maganar tana ta6e baki had'i da yin k'wafa tana niyyar mik'ewa Saude ta kawo mata wayarta data baro d'aki tace anata kira ta amsa ta duba mai kiran kafin ta d'aga suka hau yin wayar, sun d'auki lokaci suna wayar kafin sukai sallama ganin yamma tayi sosae yasa ta yanke barin zuwa gidan su Fatun sai da daddare.............

*ASM Bk2057*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

............. Bayan gama sallar Magrib Hajiya ta nufi gidan su Fatuu lokacin da ta zo daidai shagon Amadu ta d'an d'aga Murya tace "Ahmad ya kasuwa" jin haka yasa ya kallo wajen yana ganinta da yake akwae wuta da sauri ya fito lokacin har ta karya kwanar shiga suka had'e da fara'a ya gaishe da ita ta amsa ta k'ara ce mashi ya kasuwa yace Alhamdulillah, ganin yana k'ok'arin bin ta su shiga gidan tace ya koma wurin sana'ar shi ta gode yay mata a fito lafiya ya juya, tana shiga cikin gidan tay sallama jin ba'a amsa ba yasa ta k'arasa wurin kopar parlon ta k'ara yin wata sallamar da d'an d'aga murya lokacin gwaggo dake cikin d'aki ta ji ta amsa, tana lek'owa ganin mai yin sallamar yasa ta k'arasa fitowa da sauri ta nufeta jikinta sanye da hijab tun bayan da ta gama sallar Magrib bata Mik'e ba zaune take tana yin tasbih ta jiyo sallamar, sannu da zuwa tay mata ta gaishe da ita tana d'an murmushi Hajiyar ta amsa ta nufi cikin parlon tun ma kafin gwaggon tace mata ta shiga, bayan ta shige tabi bayanta daga d'an can gefen kujerar da Hajiya ta zauna itama ta zauna tana k'ara gaishe da ita bayan ta amsa tace "Barka an dawo" gwaggo tace "Yauwa eh wllh",

"to Allah ya kyauta gaba ya k'ara mata lafiya, ai kun auna Arziki da Allah ya tashi k'afadun ta ba tare da wata matsala ba" yadda tay Maganar fuskar ta a d'an d'aure cike da girmamawa Gwaggo ta hau bata hak'uri tace ai hak'uri ya zama dole tunda aikin gama ya riga da ya gama wanda aka cuta an cuce shi" d'an murmushi kawae gwaggon tay Hajiyar tace "Ya jikin Fateemar?" tace mata da Sauk'i bari a kira ta tana d'akinta,

"In tana bacci ne ki rabu da ita", tace "ban tunanin shi take yi kawae dai tana kwance ne tun bayan da muka dawo sai da dalili take fitowa" tana k'arasawa ta mik'e ta nufi hanyar fita Hajiya na fad'in ai dole tay ta kwanciya wannan uban jini da ta kwararar, lokacin da ta d'aga labulan a kwance ta same ta idanunta a rufe tana sanye da doguwar rigar bacci kanta sanye da hula, nufar ta gwaggo tay ta tsaya a bakin gadon ta kira sunanta jin shiru bata amsa ba yasa ta gane bacci take ta sunkuya ta kai hannu ta d'an bubbuga shoulder d'inta, a hankali ta bud'e idanun suka sauka akan gwaggo tace mata "Sannu ya k'arfin jikin?" hannu ta kai tana muttsike idanun tace mata da Sauk'i gwaggon tace "ba abunda ke maki ciwo?" Kai ta d'aga kafin tace "kawae jikin ne ba k'wari" kai ta jinjina "Wannan dama sai a hankali, ga Hajiya nan tazo ganin ki ki taso" amsa mata tay da to ta fara kokarin saukkowa, a tare suka tafi gwaggon na gaba tana biye da ita suka nufi parlon, bayan gwaggo ta shige da yar sallama itama ta shiga idon Hajiya a kanta ta mik'a hannu tana ce mata tazo ta zauna kusa da ita da yake a saman 2 seater take zaune, a gefenta Fatun ta zauna a hankali ta gaishe da ita ta amsa kafin ta kai hannu ta dafa Shoulder d'inta tana tambayar ta ya jikin tace mata ta samu sauk'i sosae,

"To Ya jinin yana zuba sosae ne?" ta tambaya sunkuyar da kai Fatuu tay tace "a'a kad'an ne kaman zai d'auke" jinjina kai tay tace "ai kin zubar da jini dole yay saurin d'aukewa" shiru Fatun bata ce komae ba Still kanta na k'asa, "Yanzu akwae abunda ke damun ki a jikin?" d'an girgiza kai tay tace "a'a kawae k'arfi ne babu sosae" tace "Wannan sai a hankali zai dawo kina dae cin Abinci sosae ko?" Kai ta d'aga mata alamar eh tace yayi kyau kafin ta sake tambayar tana shan suma magungunan da aka bata tace mata eh, shiru ta d'anyi kafin ta dasa "Fateema ina son tambayar ki kuma gaskiya nike son ki fito ki fad'a man kin ji ko?" d'agowa tay ta kalleta ta d'aga mata kai alamar to,

"Ina son inji shin zaki cigaba da zama da Yayan ki matsayin mijin ki ko kuwa baki so in raba ku?" Dammm! gaban Fatuu yay wani irin bugu ta kasa d'agowa balle tace wani abu ganin haka yasa Hajiya cewa ba shiru zata yi ba ta bud'e baki tay Magana a hankali ta saci kallon gwaggo suka had'a ido tana ganin haka ta juyar da fuskar ta daga barin kallon Fatun ta koma kallon gefe Hajiya tace "ki daina kallon ta ba abunda zata ce maki tunda ai ba ita zata zauna da shi ba dole kece zaki yanke kar Kiji wani abu ki fad'i man ra'ayin ki kan hakan" wani abu Fatuu ta had'iya ta rasa ma wace amsa zata bata duk ta rud'e kanta a k'asa sai zare ido take tana motsa hannuwan ta da bakin ta, da d'an d'aga Murya Hajiya tace mata dare nayi tayi magana d'agowa tay duk ta dabarbarce murya na rawa tace ".....Duk abunda...kuka za6a man yayi man" d'an murmushi Hajiya tay tace "To Fateema in muka za6a maki abunda bai maki ba fa tunda mu ba sanin abunda ranki zai fi so mukai ba kuma dae baso muke mu takura maki ba shiyasa aka baki dama ki fad'i abunda ranki ke so, kinga mu bamu zamu zauna da shi ba don haka kar Kiji komae ki fad'i kina son cigaba da zama dashi matsayin miji ko kuwa a raba ku" k'ara kallon gwaggo tay taga bata kallonta ta maida idon k'asa abu biyu ne suka hanata magana na farko kunya na biyu kuma tana kokonton amincewa ba kamar yanayin da take gani tattare da Haisam d'in,

"Shikenan tunda baza kiyi Magana ba bari in tashi in tafi, ni dae bazan yanke hukunci ba yazo kuma bai maki dad'i ba tunda ai harda irin hakan tasa aka fasa wanccan auren ko an za6a maki wanda baki so duk da harda k'arin halin shi" ganin tana k'ok'arin mik'ewa yasa gwaggo ta canza harshe tay ma Fatun Magana da d'an d'aga murya tace bazata bud'e baki tay magana ba, tana yamutsa fuska kaman zata saka kuka itama ta juya harshen tace mata tana so amman kunya take ji ta fad'i mata hakan, Hajiya da ta fasa mik'ewa ta kya6e baki tana bin su da ido har suka gama sannan tace "wato matsalar ka zauna cikin wad'anda ke yin yaren da baka iya ba kenan har gulmar ka sai ayi a kuma zage ka tass ba tare da ka sani ba k'arshe ma har kai ta washe baki kana tunanin abun kirki ake fad'a kaiga sakarai" murmushi kawae gwaggon tay Hajiya dake kallonta tace to mi suka ce a fad'i mata gwaggo tay mata bayani, wata irin kunya ce ta lullu6e Fatuu kan ta a sadde, d'an murmushi Hajiya tay tace "ina ruwan Fateema to miye abun jin kunya mutumin da dama Mijin ki ne kawae amsa zaki bada, shikenan Allah Ubangiji ya shige mana a Al'amarin tashi kije Allah yay maki Albarka ya k'ara maki lafiya damu baki d'aya, a hankali ta amsa da Amin ta mik'e ta nufi hanyar fita sumi sumi har lokacin bata d'ago fuskar ta ba, Bayan fitar ta Hajiya ta kalli gwaggo tace "Sai ku fara shiri ran Juma'a in Allah ya kaimu zata tare a d'akin mijinta nan part d'in shi" rasss kirjin gwaggo yay bata yi tunanin haka da wuri ba a d'an rud'e tace "to..Amman Hajiya bai yi wuri ba kuwa har a shirya ta tare a ranar?" Hajiya dake kallon ta ta cikin glasses tace "to Dije wane irin shiri ne za'ai da har nan da Juma'a bai isa a gama ba?" Cikin yar inda inda tace "dama wai Saboda kayan d'aki tunda wanccan wanda suka yi su sun fanshe su yanzu dole sai nayi ma Mahaifin nata Magana sai a siya wasu koda anan ne sai kuma sauran dae abubuwa" tana Maganar tare da yin nuni da hannuwan ta har ta k'arasa Hajiya da ta ta6e baki tana saurarar ta tace "To wane kayan d'aki kuma, ina ce a part d'in nashi akwae su kuma ba abunda sukai yanzu in an siya mata wasun su wanccan ya za'ai da su, ki bar zancen wasu kayan d'aki tay amfani da wanda ke akwae acan abunda ma nasan zaman na d'an lokaci ne Saboda karatun ta data gama ai dole ta bi shi inda yake zaune tunda ba yadda za'ai tay zaune nan mijin ta na wata uwa duniya, kuma ko bayan ta taren kina iya ganin ma ya canza mata wasu kayan d'akin tunda wanda ke akwae yanzun ma ai daga can K'asar wajen ya siyo su don haka ki bar zancen su kiyi sauran yan shirye shirye da ba'a rasa ba suma kada kice zaki wani takura kan ki tunda an riga an d'aura ba wani abu da ake buk'ata kawae ki sanar ma makwabta da Abokan Arzik'i don a shaida auren tunda abun surutu bai ma Mutane wuya kuma ma dai wani surutun dole ayi tunda yanzu tazo ta samu ciki kuma tazo daga baya ta haihu duk mutane basu san da auren ba ai kinga dole ayi surutu ko, in da wata matsala kiyi magana ina sauraren ki" godiya gwaggon tay mata daga baya tace "akwai kayan kitchen da ya siya mata na waccan auren suna nan ajiye ban san ko za'a iya kai mata ba tayi amfani dasu" tace "Eh to bai kamata aita ajiye su ba, bari muga tunda akwae d'ayan d'akin da yake aikin injiniyan cin nashi kuma an kwashe komae tunda yanzu ba'a nan yake ba sai abunda ba'a rasa ba inaga sai a jera mata kayan a cikin shi ya zama kaman kitchen dama kuma zagaye yake da table sai a k'ara gyarawa yadda zai yi Sosae, shikenan ko in kuma da wani abun sai ki fad'a don nafi son mu gama Maganar da ta danganci tarewar yanzu" d'an shiru gwaggo tay akwae abunda ke damunta a rai saidae ta rasa ta yadda zata yi mata Maganar Hajiya ta lura hakan yasa tace mata tayi magana inda wani abu ta kalleta cikin yar in ina tace "d...dama wai naga su can sauran dangin nashi da Matar shi basu san da Maganar auren ba shi ne nace...to ba matsala ta taren?" Hannu Hajiya tasa ta ruk'e ha6a "Oni Dije kin fi ni sanin abunda ya dace ne ko kuwa tsoro kike in sun sani za'a cinye maki Fateemar?" da sauri gwaggo ta girgiza kai alamar a'a ta hau bata hak'ura Hajiya ta dasa fad'in "ki bita da Addu'a kawae in sha Allahu komae zai zo da Sauk'i tunda shi ya k'addaro komae nasan hakan duk cikin hikimar sane shiyasa nima na d'auki Al'amarin da Sauk'i" kai gwaggo ta jinjina tay Addu'a tare da k'ara yi mata godiya daga haka ta fara k'ok'arin mik'ewa gwaggo ma ta tashi don tay mata rakiya,

Fatuu na komawa d'aki ta nufi gadonta ta haye can k'arshe ta zauna had'i da jingina bayanta a jikin bango sai zare ido take tama rasa shin murna ya kamata tayi ko mi, canjin da take gani a wurin Haisam duk shi ya Sagar mata da gwuiwa har take jin shakku game da zaman su tare gani take kaman shi bazai so hakan ba saboda in don laifin da ta yi ne ai ta bashi hak'uri, gani take da yana son ta ko yana son cigaba da zama da ita ai da ya hak'uri ya sake mata, tana haka Gwaggo ta shigo bayan ta dawo daga raka Hajiya, gadon ta nufa ta zauna a baki idonta a kan Fatuu da itama ta k'walalo ido tana kallon ta can tay yar ajiyar zuciya ta fara Magana "Sai ki fara shiri ranar Juma'a in Allah ya kaimu zaki koma gidan Hajiya can part d'in Yayan naki" dadamm! k'irjin Fatuu yay wata irin Fad'uwa ta zaro ido kaman zasu Fad'o a razane take kallon gwaggo jin abunda ta fad'a wanda kwata kwata bata zaci jin hakan ba, ko da ta amince ba tay tunanin da wurwuri haka ba, jin bata ce komae ba yasa gwaggo cewa bata ji abunda tace bane ta d'an yamutsa fuska kaman zatai kuka tace "Gwaggo da wuri haka kuma ya za'ai hakan bacin ba wanda ya sani a dangin shi ko ita fa Aunty Fanan bata sani ba" da alamun damuwa akan fuskar gwaggo tace "to nima nayi ma Hajiya Maganar hakan amman tace ayi Addu'a kawae Allah ya shige mana gaba" idanun ta ne suka ciko da k'walla ita tasan hakan ba k'aramar matsala za'a iya samu ba can suka fara zubowa sharr gwaggo dake kallonta tace mata ai ba kuka yakamata tayi ba suyi Addu'a kaman yadda Hajiyan tace komai sai aga yazo da Sauk'i cikin kuka tace "amman gwaggo ni ina tsoron kada azo a samu matsala fa in daga baya suka sani suka ce basu yarda bafa basu son auren tunda kinga Aunty Fanan yar'uwar su ce" shiru gwaggo tay ta sauke idanun ta k'asa ita kanta abunda yafi damunta kenan a cikin rai can ta d'ago tace "Addu'ar dae kawai zamuyi tunda ba abunda yafi k'arfin ta, koda nayi mata magana kan hakan nuna wa tay ban fi ta sanin abunda ya dace ba kin ga ai bazan yi jayayya da ita ba ko" shiru Fatuu tay tana goge kwallan dake zubo mata ana haka Amadu ya d'aga labulan d'akin ganin gwaggo yasa shi shigowa yana fad'in ashe tana nan yaje d'aki bai sameta ba hannun shi ruk'e da k'atuwar leda ya nufo su a bakin gadon ya aje ledar yace gashi nan in ji Ya Haisam yana gaida mai jiki kai gwaggo ta d'aga, ganin yanayin fuskar ta yasa shi tambayar ta lafiya ya juya kan Fatuu dake ta goge k'walla ba shiri ya kai zaune yana tambayar gwaggo jikin nata ne ta girgiza mashi kai alamar a'a,

Readers Also Read