Kenza eBookz

Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature - Chapter 56

Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature - Chapter 56

Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature Chapter 56: Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature Chapter 56. "To miya ke faruwa ne naga kunyi jugum jugum ga…

4,398 words

"To miya ke faruwa ne naga kunyi jugum jugum ga damuwa akan fuskokin ku ita harda kuka don Allah ku fad'a man?" Shima har yanayin fuskar ta shi ya sauya yar ajiyar zuciya gwaggo ta sauke ta fad'a mashi zancen da Hajiya tazo tayi, d'an bud'a ido yay alamar mamaki sai kuma ya washe baki yace "to shine abunda yasa maku damuwa ku da zaku yi farinciki auren zai d'ore wanda mu hakan dama muke fata" d'an murmushin yak'e gwaggon tay tace "ba wai ba'a farincikin bane kawae damuwar tamu game da dangin nashi ne da basu san da zancen auren ba ita gudun ta kar daga baya kuma azo a samu matsala suce basu amince ba" da sauri yace "ku ma cire wannan tunanin in sha Allahu ba wata matsala da za'a samu koda ma an samu Allah zai kawota da Sauk'i don haka mu mik'a komae gare shi ayi Addu'a kaman yadda Hajiyan tace, kuma kun manta ne gaba d'aya dangin na shi da matar ta shi duk tana da iko da su don haka ayi yadda tace kawae" jinjina kai gwaggo tay ya juya kan Fatuu yana murmushi ya d'an kwanta kan gadon ya kai hannu ya kamo hannun Fatuu guda yana fad'in "u should be happy Allah ya amince Romeo ya zama naki ba kuka ba" tura mashi baki tay yasa dariya gwaggo ma murmushi ta bisu da shi, sakin hannun Fatun yay ya koma ya zauna yana kallon gwaggo yace "to yanzu ya za'ai Maganar kayan d'aki gashi an sa k'urarren lokaci ko da yake ai indai da kud'i har a siya ko?" Fad'i mashi yadda sukai da Hajiyar game da hakan tay yace "shikenan ma an hutar da mu naji dad'i wllh in akwai buk'atar ayin ko nan gaba sai ayi matan in kuma zai tafi da Ita can d'in ne bama sai an yin ba" juyawa yay kan Fatuu dake ta bin su da ido yana dariya yace "Waya ga su yar fillo a jirgi za dai asha hauka nasan" k'ara tura mashi baki tay ta d'an harare shi yace "ni kike harara, kifa bar ganin wai ke matar aure ce baki fi k'arfin in kikai man ba daidai ba in zane ki ko da kin bar gidan nan ne zan iya bin ki har can gidan in maki hukunci" gwaggo dake dariya tace "shi kuma mijin nata sai ya bika da ido kai ta dokar mai mata ko",

"Wllh yadda yake tubarkallan nan ma sha Allah yace zai rama mata ai sai ya karairaya ni nasan" ya k'arasa yanata dariya itama gwaggon dariyar take Fatun dai sunkuyar da kai tay tana d'an murmushi yayin da zuciyar ta ke suffanto mata surar Haisam,

"To yanzu shikenan sai dae a jira ranar akaita ko akwae abunda zaki?" Amadu ya tambaya tace "Eh zan bada ayi mata su cin cin tunda za'a sanar da makwabta zancen Auren nasan daga baya za'a shishshiga sai ranar Juma'a d'in ayi Abinci Saboda wanda zasu zo" kai ya jinjina "hakan yayi amman fa kar kiyi su da yawa ayi daidai daidai, to su yan Adamawa fa za'a sanar masu ne naga kaman lokaci ya k'ure ko?" d'an jimm tay kafin tace "zan kira Baffanta in sanar mashi komai amman zance mashi ba sai sun zo ba su bari sai daga baya in an samu natsuwa" kai ya jinjina yace hakan yayi sai kuma yace "Yanzu shikenan haka za'ai bikin Romeo da Juliet d'in lami ba wani d'an cashewa gaskiya yakamata a d'anyi mana ko yar dinner ce mu shaida muna biki" gwaggo dake murmushi tace "aikuwa dai haka zaku yi hak'uri don ba wani abu da za'ai" gyad'a kai yay "shikenan amman fa mun biyo bashi ko daga baya ne dole ayi mana in komae ya daidaita dangin shi sun sani" ta6e baki gwaggo tay "tunda ibada ne ya zama Farilla dole sai an yi ko" k'ok'arin mik'ewa ya fara yi yana fad'in bari ya d'aukko plates su yi shagalin abun farinciki ya nufi hanyar fita, plate guda biyu ya d'aukko babba da k'arami ya duk'a ya bud'e ledar abubuwan daya saba kawo wa ne a ciki ya zuzzuba a plate d'in ya mik'a ma gwaggo ta kar6a shima ya d'auki wanda ya zuba a k'aramin plate ya mik'e idon shi akan Fatuu data takure a guri guda yace "ki saki jiki Amaryarmu dis is worth celebrating don haka ki saki ran ki kici ki k'oshi" ya nufi hanyar fita yana fad'in dole ma ya d'inka sabuwar shaddar kai Amarya daga haka ya fice gwaggo ta d'an girgiza kai da d'an murmushi ta juya kan Fatuu da tay zuru tace ga abu nan taci, girgiza mata kai tay alamar a'a ganin ta damu sosae yasa ta shiga kwantar mata da hankali tace ta saki jiki taci don jikinta na buk'atar su ko kuzarin ta ya dawo cike da tsokana tace mata ko so take a kaita d'akin miji haka sukuku da ita Amarya da ake son ta da kuzari Fatun ta duk'ar da kan ta gwaggon nata murmushi, daga baya ta d'ago suka fara ci tare da gwaggon lokacin take ce mata ta kira Fauzy ta fad'a mata don su fara shirye shiryen su k'unshi da gyaran kai har tana cewa yakamata ma in an gyara kan ai kitso ita dae Fatun shiru tay, bata wani ci sosai ba tace ta k'oshi amman gwaggo ta matsa mata saida ta k'ara ci daga baya ta bar d'akin da sauran da suka rage, tun bayan da gwaggo ta fita tay zaune zugudum ta rasa Mike mata dad'i ita dai har ga Allah zallumin zama part d'in nashi take ba tare da dangin su sun san da auren ba sam hankalinta bai kwanta da hakan ba, tana haka Gwaggo ta k'ara shigowa hannunta ruk'e da cup mai d'an girma a bakin gadon ta tsaya ta mik'a mata ta ce ta shanye abun ciki maganin sanyi ne ba tare data ce komai ba ta amsa ta kafa baki nan da nan ta shanye shi tass don dama ta saba bata tun kwanakin baya harda itatuwan tsarki da na sha duk ce mata take na sanyi ne, bayan ta shanye ta mik'a mata Cup d'in ta amsa ta juya Fatun ta bita da kallo don a yanzu ta gane ko magungunan miye take bata da sunan na sanyi, can wata zuciyar ta raya mata ko shiyasa ma lokacin da abun ya faru Ya Haisam d'in ya rikice mata tamkar bashi ba duk da rok'on shi da ta rink'a yi amman a banza, tuno lokacin yasa ta saki d'an murmushi tasa tafin hannunta ta rufe idanunta alamar kunya tana haka ta tuno da magungunan da Fauzy ta kawo mata na yar kwalbar inserting d'in shi ake bayan wasu mintuna sai a wanke da ruwan d'umi wata zuciyar ta raya mata tay amfani dashi yanzu sai kuma ta tuna da jinin da take hakan yasa ta bari sai ya d'auke sai wanda ake ci da nama gashi yanzu ta gama cin naman saidae ba dama ta sa a gaban gwaggo d'ayan kuma da peak milk tunanin ko taje shagon Kawu Amadu ta amso Madarar tay amman kuma ta k'oshi sosae gashi yanzu gwaggo ta bata wani k'arshe ta yanke gobe tayi amfani dasu kawae ta sauka don taje ta wanko hannu ta sha ruwa, tun bayan da ta kwanta bacci ya k'aurace ma idanunta sai juye juye take tana tunanin wane irin zama za tay da Ya Haisam matsayin miji kuma ta koma part d'in shi ganin abun take kaman wasa wllh, can kuma ta koma tunanin ya Aunty Fanan zata ji in taji Maganar auran na su ita da yan gidansu har saida gabanta ya fad'i tunowa da Mahaifiyar Fanan d'in wato Hajiya Maryam jikinta ne yay wani mugun sanyi don ta santa tana da kirki amman fa jarababbiya ce ta gaske a hankali tunanin ta ya koma kan yan gidan su Haisam su wannan bazata iya yanke hukunci a kan su ba kawai dae tasan suna da kirki sosae kuma tana Mutunci da wasu daga cikin yan gidan kaman Nameer, Jidderh dasu twins wannan sun ma maidata tamkar yar'uwar su haka Mahaifiyar Haisam d'in ta san ta sosae kuma duk in tazo tana zuwa ta gaishe da ita cikin sakin fuska take amsa mata bata san in suka ji zancen auren ko zasu amince ba, damuwa ce kwance akan fuskar ta haka taci gaba da tunane tunane har bata san lokacin da bacci ya kwashe ta ba, Washe gari da niyyar zuwa Makaranta ta tashi ta hau shiri ba 6ata lokaci gwaggo na cikin Kitchen ta iske ta bayan ta amsa mata gaisuwar ta ta bita da kallo ganin ta sanye da Uniform yasa tace mata ba dai Makaranta wai zata je ba tace eh ai ta samu sauk'i, girgiza kai gwaggo tay "koda kin samu sauk'i bazaki je ba gaskiya har sai shi Mijin naki ya baki izini tukun kar ai rashin hankali" yamutsa fuska tay kaman za tai kuka tace "amman gwaggo ko da ai da auren nike zuwa ko har ma in zauna a can" gwaggo dake kallon ta ta d'an d'aure fuska tace "da kika ce lokacin baki san da auren ba yanzu kuma kin sani don haka duk abunda zaki sai da izinin shi" idanunta cike da k'walla tace "to gwaggo in kika ce sai ya bada izini har sai yaushe kenan zan ci gaba da zuwa kina gani fa ko jiya bai shigo ba Kawu Amadu ya ba sak'o" tace "ba kina da waya ba ki kira shi mana ki fad'i mashi" tura baki tay tana cigaba da yamutsa fuska had'i da kikkafta idanu gwaggon ta mik'o mata abun breakfast tace taje tayi yadda sukai da shi to ta amsa ta juya, tana komawa d'aki ta aje kayan Breakfast d'in akan Carpet ta koma bakin gado ta zauna sai k'unci take ita sam bata son ta kira shi don bata san mi zata ce mashi ba da sunan neman wani izini shi da ko kiranta bai yi ba tun bayan da suka dawo har yanzu sai ita ce zata kira shi, tana ta zaune cikin 6acin rai can dubara ta fad'o mata da sauri ta kai hannu ta d'aukko jakar goyonta ta bud'e wayarta ta fiddo ta fara kiran Abbas tana fara yin ringing ya d'auka bayan ta gaishe da shi yay mata ya jikin ta amsa daga nan tay shiru jin haka yasa shi tambayar ta da wani abu ne murya kaman zata yi kuka ta fad'i mashi makaranta take son zuwa amman gwaggo ta hana wai har sai Ya Haisam ya bada izini kuma tun jiya daya maido su ma ita bata k'ara ganin shi ba tambayar ta yay har ta samu sauk'in da zata iya cigaba da zuwa School tace mashi eh har yana cewa kodae ta bari ta k'ara warwarewa amman ta kafe kan ta samu sauk'i ko ta zauna ba abunda take sai kwanciya kuma can ana ta wuce ta, sigh yay jin haka yace ta bashi wasu mintuna zai sake kira tace to, bayan sun gama wayar ta saukko ta fara yin breakfast don ranta ya bata zata je Makarantar tana cikin yi sai gashi ya sake kira bayan tayi picking yace ta zama cikin shiri ga Mijin nata nan zai zo ya kaita ya k'arasa yana yar dariya tace ta gode, cire wayar tay ta bita da kallo jikinta ne yay sanyi jin shi zai kaita aje wayar tay taci gaba da yin Breakfast d'in, tana gamawa ta jiyo horn d'in shi har saida gabanta ya fad'i ta d'an yi jimm lokacin taji ya k'ara yin wani ta yunk'ura ta mik'e, gado ta nufa ta goya jakar ta ta sa hijab dake aje saman gadon bayan tasa fararen takalman ta na makaranta ta d'auki tray d'in kayan breakfast d'in ta fita, kitchen taje ta aje su ganin gwaggo bata ciki yasa ta fito ta nufi d'akinta tana zaune kan carpet itama tana yin breakfast d'in ta shiga ta d'aura idonta a kanta Fatun tace mata gashi nan yazo zata tafi gwaggon tace "to a dawo lafiya kinga ai hakan yafi da ai abu kai tsaye" bata ce komai ba tana shirin juyawa gwaggo ta sake cewa "amman fa gida zaki dawo don zama a Makaranta ya k'are in ma kina da kaya ki kwaso su yau kin ji ni?" Kai ta d'aga mata kawai ta juya ta fita, bayan ta fito ta nufi d'ayan side d'in Motar ta kai hannu ta bud'e lokacin da ta shiga idonta ya sauka akan shi har saida gaban ta ya d'an fad'i tay saurin d'auke idon ta ta rufo kopar, juyawa tay ta d'an kalle shi yana sanye da jallabiya ta gaishe dashi ya amsa ba tare da ya kalleta ba yaja Motar suka fara tafiya ta juyar da fuskar ta gefe wani abu taji ya tokare mata k'irji wai ita Ya Haisam ke sharewa haka idanunta ne suka ciko da k'walla da sauri ta fara K'ok'arin maida su don bata son su zubo mata, har suka isa fuskar ta na gefe ya parker inda ya saba aje ta tace mashi an gode ba tare da ta kalle shi ba tana niyyar juyawa don ta bud'e kopar taji yace mata "Wait" dakatawa tay still bata kalle shi ba saida taji yace mata ta amsa sannan ta juya ta kalli kud'in da yake mik'o mata yan dubu duba bin kud'in tay da ido kafin ta d'ago a raunane ta kalle shi suka had'a ido da sauri ta kawar da nata ta furta "ka bar su" shiru bai tanka mata ba bai kuma janye kud'in ba yamutsa fuska ta fara yi tana d'an kikkafta ido a K'ok'arin ta na kada tay kuka ta sake juyawa still kallonta yake fuskar shi ba yabo ba fallasa ta sake ce mashi tana da kud'i nan ma bai tanka ba bai kuma janye kud'in ba bata da yadda zatay ba don ta so ba tasa hannu ta kar6a wani irin bak'in ciki ne ya turnuk'e ta ta shiga ayyana wato ita ga mayyar kud'i, ko tambayar ta ya jiki bai yi ba sai wasu kud'i zai bata, can k'asan mak'oshi ta furta mashi ta gode tana shirin juyawa ta bud'e taji yace mata ya jikinta har bata san lokacin data juya ta kalle shi ba kaman mai jin zancen zuci, d'auke idon tay ta ce mashi ta samu sauk'i daga haka ta juya ta bud'e Motar ta fice, saida taji ya juya Motar ya tafi sannan ta tsaya da tafiya ta juyo tana kallon Motar idanun ta cike da k'walla sharr suka fara zubowa tasa hannu tana gogewa kafin ta juya ta nufi aji, tana shiga suka had'a ido da Fauzy aikuwa ta taso da gudu ta nufo ta tana fad'in Oyoyo Bestie nah, tana zuwa ta kankame ta gaba d'aya hankalin yan ajin ya dawo kan su, sakin ta tay tana kallonta da murmushi da alamun mamaki tace mata wai har ta warke ta d'aga mata kai, kama hannuta tay suka nufo cikin ajin ana ta mata sannu da jiki tana amsawa, koda suka zauna akan seat d'in su haka a kaita tasowa ana zuwa yi mata ya jiki harda Zainab Muhammadu nan ta hau ce ma Mutane wllh su zo su nemi yafiyar ta zargin ta da sukai na tana da ciki bada aure ba aikuwa wasu sukai ta ce mata ta yafe masu su basu san ita matar aure bace tace ta yafe suna haka malamin su ya shigo kowa ya koma seat d'in shi, gaba d'aya damuwa tay mata yawa har ta kasa tsaida hankalin ta kan abunda ake koya masu saidae ta sunkuyar da kai kota kai hannu ta dafe goshi ko ta d'an cije baki Fauzy duk tana lura da ita saidae ba damar tayi mata magana, basu samu damar yin Magana ba don malamin na fita wani na shigowa har saida akai break sannan Fauzy ta tambaye ta wai mi yake damunta ne ta lura tana cikin damuwa nan ta kwashe zancen tarewar ta ta fad'a mata har Fauzy bata san lokacin data saka yar k'arar murna ba cike da farinciki tace "to keda zaki farinciki ma Allah ya cika maki burin ki Aure ya d'ore Ya Haisam ya zama naki sai kita damuwa" d'an yarfa hannu tay ta cije baki tace "Fauzy bazaki gane ba ne ina hango gagarumar matsala a tattare da hakan dangin shi fa basu sani ba haka ma Matar shi Hajiya ce kadae ta sani yanzu in suka zo daga baya suka ce basu amince da auren bafa?" Da sauri Fauzy tace "ni wllh ban ganin za'a samu wata matsala, karfa ki manta gaba dayan su Hajiya na iko dasu tunda kuma ta amince ai ta zauna na tabbatar bazata bari a raba auren ba kawae muci gaba da Addu'a" shiru kawae tay idanunta sun cika da k'walla can suka zubo sharr da sauri Fauzy ta dafa Shoulder d'in ta ta shiga bata hak'uri cikin kuka tace "Fauzy abunda yafi damu na Ya Haisam ya canza man yanzu da nike ganin ya zama mallaki na, in don laifin dana yi mashi ne na bashi hak'uri duk da in zai man Adalci ai bani kadae keda laifi ba ko, ni ina ganin gaskiya kaman gara in hak'ura da auren shi tunda na fahimci bai sona kawae nasan zai amince ya zauna da ni ne k'ilan don Hajiya tay mashi dole kinga to wane irin zaman aure zamu yi haka, koda nike son shi nafi son shima ace yana sona ko d'an yaya ne" yar ajiyar zuciya Fauzy ta sauke tace "ni gaskiya ina tunanin k'ilan akwae wani dalili da ya sa ya canza maki amman ba wannan ba kuma da dukkan alamu yana son ki shiyasa tun farko bai sake ki ba kaman yadda aka tsara, kuma in ma fushin yake Saboda rasa cikin kinga hakan ya tabbatar da yana son kine shiyasa yake son cikin har yay fushi da kika zubar, kuma da bai son ki gaskiya a ganina bazai amince yaci gaba da zama da ke ba tunda shi fa namiji ba'ai mashi dole irin wannan" shiru tay kaman mai nazarin wani abu can tace "ina ganin kaman hakurin da kika bashi bai isa ba mi zai hana ki same shi ki bashi hak'uri sosae, da kaman ki k'ara iske shi can G.r.a d'in nike gani" d'an waro ido Fatuu tay tace "in je in k'ara bashi hak'uri kuma, gaskiya ni bazan je ba Fauzy hakanan ya wulakanta ni ai na bashi hakurin ko" hannu Fauzy ta kai ta dafa Shoulder d'inta tace "k'ilan abun yay mashi ciwo ne sosae, kinsan su irin su gane masu yana da wuya amman tunda har kika ga ya nuna to tabbas bai ji dad'in abun bane kije ki same shi ki bashi hak'uri sosae ba fad'uwa bane wllh karki manta shi Mijin ki Aljannar ki na a tafin kafar shi kuskurene ace yana fushi dake haka indae fushin yake da gaske Saboda abunda kika aikata don haka nidai a gani na kije ki bashi hak'uri tun kafin ranar Juma'ar tayi" shiru Fatuu tay tana juya zancen zuwa bashi hakurin a cikin ranta can wata zuciyar ta tuno mata da lokacin data fasa mashi glass har Haulat ta bata shawarar taje ta bashi hak'uri kuma shawarar tayi mata amfani wanda itace silar komae a tsakanin su, yin wannan tunanin yasa ta kalli Fauzy tace "shikenan zan je d'in amman bansan lokacin da yake can ba gashi in na koma gida bansan yadda zan ce ma Gwaggo ba har ta barni in fito" Fauzyn ta tambaye ta yana zuwa aiki ne tace mata a'a ya bar aiki nan tunda ya bar K'asar, sake tambayar ta tay yaushe rabon data gan shi tace mata shi ya kawo ta tace "kinga da ace can ya tafi sai kiyi sauri tunda anyi break duk da ma an kusa dawowa sai kije ki dawo mai Napep d'in da ya kai ki sai ya jira ki ku dawo" d'an jimm Fatun tay kaman mai yin tunani can tace bari ta gwada zuwa k'ilan can ya wuce in kuma bai can sai ta dawo ta mik'e Fauzy ma ta mik'e tace bari ta rakata, suna fitowa waje suka samu Keke Napep Fatuu har zata shiga ta dakata takai hannu cikin aljihun rigarta ta fiddo kud'i cikin wanda ya bata ta mik'a mata tace tay break ta shige cikin Napep d'in Fauzy ta d'aga hannu tana mata sai ta dawo da fatan Allah yasa ta iske shi ta amsa da Amin yaja suka tafi ita kuma ta juya...............

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 da 3 Naira 400 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268

*ASM Bk2058*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

.........Tunda suka taho take ta faman zullumin abunda zai biyo baya in ta iske shi, wannan karon bata wani sha Wahalar gano gidan ba da suka iso don ta rik'e sunan Road d'in, a bakin tangamemen gate d'in tace ma mai Napep d'in ya tsaya bayan ta fito tace zai jirata ne su koma yace to ba matsala ta juya ta nufi k'aramar kopar a d'arare, Officer dake zaune shi kadae yana ganin ta ya hau washe baki harda mik'ewa yana mata sannu da zuwa abun har saida ya bata mamaki a hankali ta amsa mashi ta tambaye shi ko Ya Haisam na ciki da sauri ya d'aga mata kai yace eh yana nan tace zata gan shi ne yace mata ba Komai ta fito lafiya ta wuce, tunda ta shiga harabar gidan gabanta ke ta fad'uwa tana tafiya tana yan waige waige har ta isa bakin mai entrance na gidan ta turo kopar ta shige, ba kowa a cikin parlon farko ta wuce Corridor d'in da zata kaita d'akin nashi cike da fargaba har ta iso bakin dakakkar kopar dake a rufe, tsaye tay ta kasa kwankwasawa sai faman wasi wasi take a cikin ranta ta had'e hannawun ta tana cakud'a su, can dae ta kai hannu yana d'an rawa ta fara knocking a hankali, kusan sau biyar ta kwankwasa amman shiru bata ji an yi magana ba, dakatawa tay da knocking d'in tay jimm tana tunanin ko dae bai nan wata zuciyar ta ayyana mata amman ai Officer yace yana nan kuma da ya fita bazai ce mata haka ba ta raya to ko bacci yake yin Wannan tunanin yasa ta yanke ko dae ta tafi, har zata juya sai kuma ta dakata tay tunanin k'ara d'an kwankwasawa k'ilan tay sa'a yay Magana, can cikin bacci yaji knocking d'in sama sama har dai yaji shi sosae ya fara motsa idanuwan shi kafin slowly ya bud'e su dai dai lokacin ya k'ara jin anyi knocking d'in cikin disasshiyar murya irin ta wanda ya tashi daga bacci ya tambayi wanene shiru ba'a amsa ba saima k'ara yin knocking d'in da akai ya k'ara tambaya nan ma shiru, tunani yay k'ilan Officer ne ko ya kira landline bai ji ba hakan yasa ya yaye lallausan duvet d'in daya rufe rabin jikin shi da shi ya saukko da k'afafun shi kafin ya idasa mik'ewa daga shi sai farar singlet fara kal sai short da iyakar shi rabin cinyoyin shi, saida ya zura takalman da ke a bakin gadon sannan ya nufi kopar, ganin ta k'ara kwankwasa har sau ukku ba'a bud'e ba yasa ta hak'ura tana shirin juyawa ya bud'e kopar da sauri ta kai idon ta kan shi suka had'a ido, wani irin bugu kirjinta yay ta d'an zaro ido tana kallon shi shima irin kallon baka tsammaci ganin mutum ba ya bita dashi, gaba d'aya ta kame kanta ba kamar a yadda ta ganshi hannuwan ta da ta had'e sai d'an rawa suke, sakin kopar yay ya juya ba tare da ya ce mata komae ba, d'an jimm tay kaman bazata shiga ba sai kuma ta shiga ta maido kopar wani irin ni'imtaccen sanyin Ac had'i da daddad'an k'amshi mai ratsa zuciya suka tarbeta har saida ta d'an lumshe ido taja numfashi, in da kujeru suke ya nufa ya zauna kan 2 seater ta nufi can walking slowly gaba d'aya a d'arare take, a gefen wurin ta tsaya tana kallon shi ya sa duka tafukan hannayen shi ya dafe goshi alamar baccin bai ishe shi ba aka katse mashi, saida ya d'an d'auki lokaci sannan ya cire ba tare daya kalleta ba da hannu yay mata nuni da kujera alamar ta zauna jiki a sa6ule ta nufi cikin wurin ta zauna akan one seater tana facing d'in shi, gaba d'aya ta tsorata da yadda ta ganshi don bata ta6a ganin shi haka ba duk ilahirin jikin shi inda gashi ke fitowa suma ce a kwance liya liya ga farin shi gaba d'aya ya tafi bai d'aya skin d'in shi sumul da ita ba ko d'an ta6o ko bambancin kala harta gwuiwar shi ba bak'i ko tabo kamar bai yi rarrafe ba da yana yaro kawae dae skin d'in wurin jan ta ya d'an fi cizawa ga suffar k'arfin shi ta bayyana muraran gaba d'aya a murde yake, tana cikin k'are mashi kallon ya kai idon shi kanta suka had'a ido ta fara motsa baki da k'yar ta k'ak'alo Kalmar ina kwana tace mashi kaman ba zai amsa ba sai kuma ya amsa can k'asan makoshi ganin yana mata kallon da take ganin na fushi ne yasa ta sunkuyar da kanta yaci gaba da kallon ta,

"Why are u here not in School?" Bayan wasu sakanni taji cool voice d'in shi ya fad'i hakan, d'ago kanta tay ta kalle shi ta fara motsa baki tama rasa ta ina zata fara mi zata ce mashi duk ta dabarbarce ba kaman da ya kafeta da kaifafan idanuwan shi masu k'ara mashi kwarjini gathering much courage ta fara magana cikin yar rawar murya "d...dama zuwa nayi in baka hak'uri kan abunda ya faru....nasan nayi maka laifi amman ni bansan komai bane shiyasa na aikata wannan kuskuren....don Allah Ya Haisam kayi Hakuri" da k'yar ta k'arasa Saboda idon shi dake a kanta tana yi tana maida kan ta k'asa tana d'agowa, bin ta kawae yake da ido kaman ma bashi da niyyar tanka mata duk tasha jinin jikinta sai yan kame kame take,

Readers Also Read