Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature - Chapter 61
Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature Chapter 61: Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature Chapter 61. "na tuna mana har saida kay ciwon k'arya" ya…
4,407 words
"na tuna mana har saida kay ciwon k'arya" ya k'arasa yana dariya shima Tk tuntsirewa yay da dariya tunowa da lokacin, Fatuu ma dariyar take dama lokacin daga baya ta gane ciwon k'arya ne har ta fad'i ma Haisam bayan ya dawo tace bata gama yawon ba har ta rok'e shi ya idasa kai ta hakan ne silar farkon zuwan ta gidan Abbas, Amadu dake kallon shi yace "har ka kai Yayar Fauziyyar ta d'aukko sauran kayan?" d'an girgiza kai Tk yay "No tace in bata makullin Motar ta iya sai su d'aukko ni in huta shine na bata" kai Amadu ya d'aga Tk ya juya kan Fatuu dake kallon su, da murmushi yace "na taya ki murna yar k'anwar mu yanzu kuma Auntyn mu, Allah ubangiji yasa Alkhairi ya baku zaman lpy, wllh baki ji dad'in dana ji maki ba lokacin dana samu labarin auren, Ya Haisam cikakken mutum ne harda ma rabi, samun shi matsayin abokin rayuwa abun a taya mutum murna ne sam bani da shakku a kan shi don yayi 100% kuma kun bala'en dacewa wllh, zaku ji dad'in yin rayuwa tare don kun riga da kun gama fahimtar juna, shine zai iya maki don ma yanzu naga kin natsu....au tuba nike Hajiya tah su6ul da baka ne" gaba d'aya suka sa dariya ya k'ara cewa "dama ni ne mai kula da part d'in nan wurin gyara shi, to yanzu Aunty zan ci gaba da aiki na ne ko yaya?" Yay tambayar idon shi akan Fatuu dake ta faman sakin murmushi ta kasa ce mashi komae,
Amadu ne yace "ah dama ai don ba mata ne, yanzu kuma tunda gata na me kaci gaba ita zata rink'a gyarawa" da sauri Tk yace "No ka bar Hajiyata ta yanke hukunci don itama tana da iko dani yanzu" ya juya kan Fatuu yana fad'in ta yanke yadda za'ai sai Faman dariya take, da k'yar tace mashi ai ba ita zata yanke hukunci ba Ya Haisam ne yace shikenan, ya juya kan Amadu yace "gaskiya AA yakamata muma fa mu fara haramar shigewa daga ciki, ko da yake k'ilan ma sai na riga ka kai da ko budurwa nasan baka da ita, ko kayi ta Yanzu?" Amadu dake murmushi ya girgiza mashi kai alamar a'a,
"Gaskiya yakamata ace by now kana da budurwa ko kuma ka tsaida wadda zaka aura tunda nasan ba'a rasa masu son ka kaine kawae baka basu dama" Amadu dake yar dariya yace "No k'yale budurwar nan bari dae in nemi kud'i su taru tukunna in lokacin auren yayi zaka ga bazan sha wahalan samu ba tunda na gama had'uwa" dariya sosae Tk yasa bayan ya tsagaita yace "kuma wllh in dae kana da kud'i bazaka sha wata wahalan samun irin Matar da kake so ba, wai ni yanzu yan mata na soyayya tsakani da Allah kuwa? Ni kaina nan wai d'an ganin da ake ina fantamawa da motoci aka kuma ji gidan da nike kar kaso kaga yadda yan mata suke lik'e man, nan basu san Almajiri bane" gaba d'aya sukai dariya Amadu yace ai yanzu yafi k'arfin a ce mashi Almajiri shima ya zama dangin Senator d'in, suna haka aka turo k'opar duk suka kai idanun su kan masu shigowar, Abbas ne da Saleem da k'yar Abbas ya matsa mashi suka shigo don ya k'iya yace mi zai shigo ya yi, su Amadu na ganin su suka mik'e suna gaishe dasu kafin suka nufi kopar fita su kuma suka k'arasa shigowa ciki idanun su akan Fatuu da itama kallon su take da d'an murmushi haka Abbas ma murmushin yake mata, a gaban gadon suka tsaya yana kallon ta yace "Mom Zarah Amaryar mu, an daina kukan ko?" Kai ta d'an d'aga mashi alamar eh kafin a Sanyaye ta gaishe dasu suka amsa,
"haka yakamata ai kar ya haddasa maki wani ciwon muda muke so a biya mu abunda muka rasa a yau......", bai rufe baki ba daga bayan shi yaji an ce "mi kake ci na baka na zuba ai kunsan dai ita d'in bata wasa bace da kun bata zata biya ku" Aunty Mareeya ce da ta shigo ruk'e da kwalin kwalaben kayan k'amshi tay Maganar duk suka juya har da Saleem suka kalleta Fatuu kuwa wata irin kunya ce ta rufe ta da sauri ta sadda kan ta k'asa, shigowa tay cikin d'akin ta nufi wurin dressing mirror Abbas ya bita da murmushi don sai ya d'an ji kunya duk da tun a Mota wurin kawo Fatuu ya fahimci bakin ta a sake yake itama, Saleem ne ya kalli Fatuu cikin cool voice d'in shi yace mata Allah yasa Alkhairi bata amsa ba sai d'an murmushi kawae tay mashi Aunty Mareeya ce ta amsa tare da juyowa ta kalle shi kafin ta maida idon kan Abbas dake ta murmushi itama ta yi had'i da d'an girgiza kai tana a gaban dressing mirror, ta fiddo wasu had'add'un kwalaben humra da turaren wuta tana jerawa a wurin a parlor ma ta jera wasu a cikin gidajen da su tv suke sosae suka k'ara k'awata wurin, Saleem ne ya juya zai tafi Abbas dake kallon Fatuu yace mata bari su je sai ya kawo mata Angonta Aunty Mareeya tay carab tace suna jiran shi yazo ya siya bakin Amarya a wurin su tay Maganar tana dariya shima Abbas d'in dariyar yake ya juya suka fita,
bayan fitar su Fauzy ta shigo ruk'e da burner data gama turara parlor ta jona ta anan aka zuba turare Bedroom d'in ya fara turaruwa shima Aunty Mareeya da ta gama ta shiga yi ma Fatuu bayanin yadda zatay amfani da wasu daga cikin kayan kamshin ita dae kai kawai take d'aga mata, bayan an gama turara d'akin Fauzy ta hau gyara bedroom d'in duk da ba wani 6aci yay ba tana cikin gyaran Aunty Mareeya ta sake shigowa hannunta ruk'e da cup ta nufi side d'in da Fatuu take ta zauna a bakin gadon ta bata tace ta shanye abun ciki, ba musu ta amsa ta kafa baki saida ta shanyen ta mik'a mata Cup d'in tace ta taso zata nuna mata abu a kitchen tace mata to ta zuro da k'afafun ta ta mik'e suka nufi hanyar fita Fauzy nata sakin wani kalan murmushi wanda da gani da biyu take yin shi, bayan sun je kitchen d'in bin d'akin Fatuu tay da kallo an tsara shi ya koma babban Kitchen a ranta ta shiga tuna lokacin da ta fara shigowa cikin shi yin fitsari da ta zo ba Haisam hak'uri da kuma lokacin da yay mata Assignment d'in maths tuna lokacin har saida ta saki murmushi, waya ta6a tunanin wai d'akin zai zama kitchen d'inta gaba d'aya part d'in ma, wata drawer Aunty Mareeya ta jawo ta ce ta matso, nuna mata abubuwan dake ciki tay wanda sauran magungunan ta ne da aka siya mata a wurin Aunty Bee ta shiga yi mata bayanin yadda zata rinka amfani da kowanne Fatun na d'aga mata kai har ta gama, tambayarta tay ko a cikin kitchen d'in akwae abunda bata iya amfani da shi ba ta gwada mata, a sanyaye tace duk ta iya tana ganin yadda Aunty Saude mai aikin nan gidan ke amfani da su Aunty Mareeyar tace da kyau daga haka suka fito suka koma Bedroom d'in, suna komawa Feenah ta shigo tace ma Aunty Mareeya ance su fito za'a maida kowa gida tace to dama sun gama mata komae ai, ta kalli Fatuu da tay zuru jin zancen zasu tafin ta tambaye ta akwai wani abu ta girgiza mata kai sukuku da ita ta juya ta nufi wurin k'atuwar wardrobe d'in d'akin, a gefenta ta d'aukko jakar ta ta dawo bakin gadon Feenah na tsaye, zuge zip d'in jakar tay ta kai hannu ta ciro wata farar shopping bag mai d'auke da tambari ta d'aura ta akan cinyoyin Fatuu tace "Yar k'anwata Amarya ga tawa gudunmawar nan saura kuma kice zaki k'i yin amfani dasu Saboda wai kunya, ke da shi yanzu ba sauran wata kunya don kun riga kun zama abu d'aya, an san kunya abu ce mai kyau amman yanzu a wani wurin in kika ce zaki saka kunya to zaki k'wari kan ki ne da kuma shi Mijin naki don haka ba a komai zaki rink'a nuna kunya ba....." Katse ta Feenah tay da fad'in "ba kamar yadda take da kishiya kuma ma baturiya, gaskiya dole sai kin zage wllh don su ba wata kunya gare su ba don ma ita tana ruwa biyu....." Aunty Mareeya ta kar6e "kin ji dai ko, wannan nasan har yawo daga ita sai d'an pant in ma tasa kenan tana iya yi a gaban shi, don haka ki zage wllh balle ke da ma kike da surar jan hankali Tubarkallah, ki kuma dage da gyara jikin ki ciki da waje, duk magungunan da nayi maki bayani kada ki wasa da shan su sannan kuma kada ki k'asa a guiwa wurin faranta mashi irin su ta nan wajan aka fi kama su, ki sashi ya susuce ta yadda duk in zaiyi Magana sai ya ambaci sunan ki alamar kece a ran shi koda yaushe" gaba d'aya suka sa dariya harda Fauzy dake can d'ayan side d'in gadon raku6e,
Feenah ta d'aura da fad'in "Bayan wad'annan kuma sai a had'a da biyayya don itace zata k'ara taimakawa wurin siye zuciyar shi duk da nasan ke mai biyayya ce a gare shi tun ba yanzu ba, to ki k'ara akan wadda kike mashi don yanzu ne zata fi yin aiki kuma zaki fi cin ribar yin ta, a k'arshe ina Addu'ar Allah yasa Alkhairi a zaman ku ya had'a kawunan ku gaba d'aya da abokiyar zaman taki ya kauda fitina ya bashi ikon yin Adalci a tsakanin ku, ya albarkace ku da zuria d'ayyiba" su Aunty Mareeya ne suka amsa ita kuma Fatun kan ta na a k'asa, lokacin Abbas ya lek'o cikin d'akin yace su suke jira fa duk suka mik'e ya d'aga murya yana ma Fatuu sai da safe, yana shirin juyawa Feenah tace don Allah ya taimaka mata da Abdul yadda yay baccin nan ba iya d'aukar shi zatay ba ya k'arasa shigowa cikin d'akin ta kinkimo mashi Abdul d'in ya kar6e shi ya sa6a a Shoulder yana fad'in Allah ma ya taimake su da yayi baccin ai da ba k'aramar rigima za'ai dashi ba don yana iya cewa nan zai kwana ba kamar yana ganin gidan Baban shi da Momy d'in shi ne duk sukai dariya ya juya ya nufi kopa suma suka bi bayan shi Fatuu ta fara k'ok'arin saukkowa daga saman gadon Fauzy dake kallonta tace ina zata, jin haka yasa su Aunty Mareeya juyowa suma suka tambayi inda zata fuskar ta kaman zatai kuka murya na d'an rawa tace raka su zatai, waro ido tay tace a ina ta ta6a ganin Amarya tayi rakiya ta koma ta zauna kafin Angon ta ya zo, ba yadda ta iya dole ta koma ta zauna suka tafi banda Fauzy da tay tsaye ta kasa tafiya yanayin fuskar ta ya sauya itama kaman zata saka kukan, bin juna da ido sukai can k'walla suka zubo ma Fatuu sharrr Fauzy ta d'an girgiza mata kai daga inda take tsaye tace "ki daina kuka Zarah lokacin farinciki ne yanzu, Allah yasa Alkhairi ya baku zaman lafiya sai mun had'u School" da k'yar ta k'arasa Maganar, jin kuka na niyyar k'wace mata yasa ta juya da sauri ta fita, tana fita Fatuu ta d'age k'afafunta ta kife fuskar ta tana kuka a hankali.................
_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 da 3 Naira 400 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268
*ASM Bk2061*
_Destiny may be delayed but cannot be changed...._
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
.......bayan su Aunty Mareeya sun fito saida suka koma part d'in Hajiya suka k'ara yi mata Allah yasa Alkhairi sannan sukai mata sallama tana ta godiya duk aka fito harda su inna Zaliha da tun d'azu suka so tafiya Hajiya tace su bari za'a maida su gwaggo ta biyo su tace suje gida don Allah zata basu kayan biki, Motar Saleem Abbas yace su Aunty Mareeya da Feenah su shiga gwaggo ma ta shiga shi kuma ya d'auki su inna Zaliha da iyalan baba shehu sai wasu abokan aikin gwaggo da suka rage su biyu, a daidai kopar gidan su Fatuu suka tsaya gwaggon ta shiga ta d'ebo ma kowannensu su cin cin harda man shanu, bayan ta kawo masu suka yi sallama tana ta godiya tace ma Fauzy saura ta daina ganin ta tunda k'awar ta ta bar gidan tana yar dariya tace a'a zata rink'a zuwa har weekend ma zata rink'a zuwan mata, sosae gwaggo taji dad'i tace to Allah ya bada iko suka tafi tana ta k'ara godiya tare da d'aga masu hannu, saida sukai nisa sannan ta koma ta kullo gidan ta nufi gidan Hajiya don bata yi mata sallama ba ta taho, tana tafiya tana tunanin autar ta sai murmushi take wani lokacin ta d'an girgiza kai, har ta fara jin kewar ta tana son ta gan ta saidae ba dama don bazata iya zuwa part d'in ba a yanzu.
Feenah aka fara ajewa gida don tafi kusa tay ma Saleem d'in godiya sukai sallama dasu Aunty Mareeya har tana fad'in taga gida zasu rink'a zumunci in sha Allahu tace to shikenan ta gode, dama sun yi musayar lambar waya tun a gidan su Fatuu kafin akai ta, daga nan Goriba road suka nufa aka kai Aunty Mareeya, bayan ta nuna mashi gidan ya parker tay mashi godiya ya jinjina mata kai ba tare da ya ce komae ba ta bud'e kopar ta fita Fauzy dake a gaba ma ta fito bayan sun rufe mashi kopopin yaja ya tafi, tsaye Aunty Mareeya tay baki bud'e tabi bayan Motar da kallo kafin tace "da alama shima wannan lalurar gare shi" kallon bayan Motar da har tayi nisa Fauzy tay kafin ta juyo ta kalli Aunty Mareeya cikin rashin fahimta ta tambayi wace irin lalura gare shi, tace "irin ta mijin Zarah mana, daga gani shima miskili ne na gaske" yar dariya Fauzy tay "na lura da hakan don ko d'azun da za'a kai Zarah da muka hau Motar shi bai ce ma kowa uffan ba sai d'an Music da ya kunna sama sama" Aunty Mareeya dake kallon ta tace "da gani dai wani shege ne ko kuma d'an wani shegen shiyasa harda rufe lambar Mota, baice yana son ki ba?" ta kafe Fauzy da ido alamar jiran amsa, dariya Fauzy tay "taya zai ce yana sona na fad'i maki tunda muka hau Motar shi bai ce mana uffan ba, kema ba gashi kin gani ba har kin fad'a" k'wafa tay tace "Allah ya yabawa aya zak'in ta, ai da ya sake yace yana son ki har abun ya kai ga aure da an taimaka mashi an sashi ya rink'a magana shima yadda za'a sa abokin shi, Allah sarki Zarah...." Murmushi tay kawae bata ida abunda zata ce ba ta nufi gate Fauzy tabi bayanta acikin ranta tana tuna k'awarta Fatuu dama tunda suka baro ta ta tsaya mata a rai, a yanzu kuwa sai taji ta fara sha'awar yin aure itama.
Gwaggo na isa part d'in Hajiya a parlor ta same su kaman yadda ta barsu ita da Saude sai dae ita Sauden tana kitchen tana yin girki musamman don su Fatuu kaman yadda Hajiya ta bata umarni, zama gwaggon tay Hajiya tace har ta sallame su tace mata eh suka d'an ci gaba da yin hira suna kallo, can gwaggo tace bari ta tafi sai Allah ya kaimu ta k'ara yi mata godiya da Addu'oi, tana k'ok'arin mik'ewa Hajiya tace ta tsaya zasu je wurin Zarah yanzu sai suje tare tasan dae bata rasa mararin son ganin ta, cike da Zolaya tay Maganar gwaggo dai d'an murmushi kawai tay ta sadda kai, bada jimawa ba Saude ta shigo cikin parlon hannunta ruk'e da wani had'add'an basket mai d'auke da k'awatattun Warmers, a gefen kujera ta tsaya cike da girmamawa tace ma Hajiya an gama, kokarin mik'ewa ta fara yi tace ma gwaggo suje itama ta mik'e, har zasu tafi tace ma Saude taje saman gadon ta towels na nan da aka manta ba'a saka mata a kaya ba ta d'aukko a kai mata tace to, bayan ta dawo ta d'auki basket d'in d'ayan hannun rungume da towels d'in da ta d'aukko suka tafi. Tun bayan da su Fauzy suka tafi ta kife fuska tana kuka sai da ta d'an d'auki lokaci a haka sannan ta d'ago idanunta duk kwalla tay zuru tana d'an kalle kallen d'akin, can ta kai hannu ta cikin ledan da Aunty Mareeya ta bata ta fiddo abun da ke ciki, bata gane ko miye ba saida tasa d'ayan hannun ta bud'e sannan ta ga ashe rigar bacci ce orange colour ta dai had'u ba karya yadin ta gwanin santsi irin mai bin jiki d'in nan kuma bazata wuce guiwa ba tana da d'an fingilallan pant mak'ale a jikinta, ajeta tay gefe ta zazzago sauran da ke ciki guda biyu, d'aya baby pink ce shara shara wannan da k'yar ta wuce mazaunan mutum irin wadda in aka sa a naked za'a ga mutum har saida Fatuu ta d'an bud'a ido ganin rigar, d'ayar ta karshe cream ce yadinta cotton ne mai dad'in tabawa gwanin taushi daga wurin wuyanta da k'arshen hannun ta da zai iya wuce guiwar hannu duk gashi gashi ne gazar gazar yana d'an walwali harda ribbom gareta, itama tana da pant sai dai gabanta a bud'e yake kawai yan igiyoyi gareta wuri ukku da zaka daure, har saida Fatuu ta d'an sauke ajiyar zuciya fuskarta a d'an kwa6e take bin rigunan da kallo ita kam bata jin zata iya amfani dasu a yanzu gani take zai iya mata kallon mara kunya, maida su tay cikin ledan ta d'an yi jimm can kuma ta mik'e ta nufi wardrobe don ta 6oye su a ciki, saidai duk yadda tay ta bud'e wardrobe d'in ta kasa ta rasa ta ya ake bud'eta don bata ga wani handle da zaka kama ka bud'e ba a jikinta, k'arshe d'aya daga cikin jakunkunan ta dake a gefen wardrobe d'in ta duk'a ta bud'e, a can k'asa ta tura ledan bayan ta rufe ta mik'e, a gaban dressing mirror ta tsaya tana kallon kanta, ita kan ta taga had'uwar da tayi don lace d'in ba k'aramin had'uwa yayi ba kuma ko ba'a fad'a ba da ka kalle shi zaka gane ba mai k'ananun kud'i bane, ga sark'a da yan hannun ta suma tamkar gold sun yi ma hannunta da ya sha k'unshi kyau ba kad'an ba, zuciyarta ce ta fara hasasho mata Haisam tsaye a bayanta har bata san lokacin da ta d'an yi murmushi ba, bayan ta gama kallon kan nata juyawa tay jiki a sanyaye ta koma bakin gadon ta zauna ta jingina da headboard, bada jimawa ba aka turo kopar ta kai idonta da sauri kan mai shigowar, Saude ce ta fara shigowa suka had'a ido tay ma Fatun murmushi itama tana niyyar mayar mata Gwaggo ta shigo aikuwa zumbur tay ta mik'e da sauri gudu gudu ta nufo kopar tana zuwa ta fad'a jikinta ta fashe da kuka lokacin Hajiya ma ta shigo tana dogara sandar ta idanun ta sanye da glasses har lokacin lifaya d'in ce nad'e a jikinta, sosae ta k'ank'ame gwaggon sai kace zata shige cikin jikinta sai faman kuka take har kallabinta ya fad'i haka gyalen ma ya zamo daga saman kan ta gashinta da ya sha gyara baki wuluk sai salk'i yake an yi parking d'in shi ya bayyana, har cikin ran gwaggo take jin kukan hakan ya karya mata zuciya daurewa kawai take tasa hannu guda ta d'an dafa bayan ta,
"To wannan kukan shagwa6a ne ko na me, sai kace wadda zaku rabu kwata kwata, duka yaushe kika baro gidan kuma gashi har kin gan ta to miye abun kuka Fateema" Hajiya dake tsaye gefe tay Maganar Saude nata kallon su gwanin ban tausayi, d'ago da ita Gwaggo tay suka had'a ido Fuskar ta duk tayi jage jage da hawaye a sanyaye tace mata ya isa hakanan ta kamata suka nufi gado ta zaunar da ita, Hajiya ta kalli Saude tace ta kai towels d'in saman jakunkunan dake gefen Wardrobe in ta tashi ta canza masu wuri tace to, tsaye gwaggo tay a gaban Fatun tana d'an murmushi Hajiya ma ta maido idon ta kan Fatun tace "Fuskar Amarya duk tayi jage jage haka, kar kija Angon naki yazo yay tunanin wani abun mukai maki ya d'auki mataki a kan mu" cike da zolaya tay Maganar Fatun ta sunkuyar da kan ta k'asa,
"Amman Dije ya akai aka bar mata kai haka ba'ai kitso ba" Hajiya dake kallon kan Fatun ta fad'a, gwaggon tace "Wllh naso ai mata shafa'a nayi gashi yau anata hidima ban ko tuna ba" jinjina kai tay tace "shikenan bari in Allah ya kaimu gobe sai a kira Balaraba tazo tay mata" gwaggo tace to cike da girmamawa, sake kallon Fatuu tay "Fateema ga Abinci can a saman Dining table in zaki ci in kuma zaki jira Angon naki ne sai ku ci tare dama can baya ke kike sa shi yaci da yawa yanzu ma sai ki dasa don har yanzu ba wani cin Abincin kirki yake ba" gaba d'aya d'an murmushi sukai banda Fatuu da ta sadda kai Hajiya ta kalli Saude tace suje, ganin gwaggo na niyyar bin su yasa tace in bata gama da ita ba ta tsaya zasu jirata a parlor cike da jin nauyi tace to, don dama bata samu yi ma Fatuu Nasiha ba, bayan fitar su Fatuu ta kalli gwaggon ta kamo hannunta cikin muryar kuka tace ta zauna sai ta girgiza mata kai alamar a'a, magiya Fatun ta hau yi mata kan ta zauna tace bazata zauna a gadon suruki ba tay Maganar da yar dariya dole Fatuu ta k'yale ta sai kuma ta nuna mata bedside drawer tace to ta zauna saman ta, bata musa ba ta nufi inda take ta zauna Fatun taja jiki ta matsa kusa da ita ta k'ara kama hannunta tana yar ajiyar zuciya irin ta wanda yay kuka, bin juna sukai da ido Fuskar gwaggo da d'an murmushi ita kuma Fatun ta d'an kwa6e fuska idanunta sunyi raurau kaman zata cigaba da kukan, nannauyar ajiyar zuciya gwaggo ta sauke ta fara Magana a nutse,
"Ina matuk'ar godiya ga Allah daya nuna man wannan ranar gaki a cikin d'akin ki na aure hakan ba k'aramin abun farinciki bane, dad'in dad'awa kuma wanda ya kasance a matsayin mijin naki mutum ne da kowacce uwa zatay Alfahari in d'iyar ta ta samu irin shi a matsayin miji, bani haufi akan yadda zaki gudanar da rayuwar gidan auren ki don nasan wacece ke fiye da kowa, duk yadda ake son Mace ta kasance a gidan aurenta na tabbatar zaki kasance, saidai ina so in k'ara jan hankalin ki, a yanzu kin baro shek'ar da kika taso cikinta kika saba rayuwa kin dawo wata sabuwa da baki saba ba, dole zaki ga yanayin rayuwar ya bambanta sosae, kada kiga ai kinsan abokin rayuwar naki kun saba dole wasu abubuwan zasu canza, ki k'ara wasu ki kuma rage wasu don yadda kuke dashi a da da kuma a yanzu ba d'aya bane, yanzu shi Mijin ki ne wanda Aljannar ki na a tafin k'afar shi dole ki k'ara girmama shi kiyi mashi biyayya fiye da yadda kike mashi, ki bishi sau da k'afa sannan ki zama mai wadatuwa da duk abunda yay maki kada kiga yanzu kina da hakki akan shi kice zaki rink'a rainuwa kan abunda yay maki, duk abunda yayi maki ki zama mai godiya had'i da Addu'ar k'arin budi a gare shi, sannan kada kice zaki rink'a yawan kai mashi buk'atu kiga ai yana da halin yi maki in dai abu ba ya zama dole ba to ki hak'ura don yawan tambayar abu na sa ka gundiri mutum koda bai fito ya nuna ba, na tabbatar zai tsare maki dukkan hakk'in ki don haka sai ki zama mai kauda kai, sannan 6angaren tsafta nasan baki da kyuwa ko ganda, ki k'ara dagewa wurin gyara jikin ki da Mahallin ku ki hana idon shi ganin abunda zai munana mashi haka ki hana hancin shi shak'ar abunda zai 6ata mashi...." D'an dakatawa tay idanun Fatuu akan ta sun yi rau rau, bayan ta d'an nisa taci gaba "a zaman farkon nan da zakuyi anan zaki k'ok'ari ki fahimci miye yake so da kuma miye bai so ma'ana miye in kinyi zai ji dad'i ya faranta mashi rai miye kuma in kinyi ba zai ji dad'i ba ko zai bakanta mashi, in kin fahimci hakan sai ki kiyaye sai kiga kun zauna lafiya har in kin ji wasu na korafin tsakanin su da mazajen su kita mamaki, a k'arshe inason in ja hankalin ki game da abokiyar zaman ki, ki sani ku biyu keda shi Saboda haka kada ki zamo mai son kai, duk abunda baza ki so ya faru dake ba to itama kada ki so mata haka duk abunda kika so ma kan ki itama ki so mata, ki zauna da ita tsakani da Allah, nasan in Maganar auren ku ta bayyana rai zai iya 6aci kiyi hakuri da duk abunda zai biyo baya ba kamar daga gareta don tabbas an mata ba daidai ba, in Allah ya daidaita tsakanin ku ki ci gaba da daukarta tamkar Yayarki uwa d'aya uba d'aya kar kiyi mata kallon kishiya balle har zuciyar ki ta samu damar sak'a maki wani abu ba daidai ba game da ita, in abun farinciki ya faru da ita ki taya ta murna in na jajantawa ne ki taya ta jajantawa kada ki sake ki bari shaidan yay galaba a kanki game da ita in ma zaki kishi da ita to akan kyautata ma mijin ku ne, haka dangin shi ma ki d'auke su tamkar naki ki zauna da kowa lafiya sannan ki dage da yin ibada don neman dacewa, a K'arshe ina Addu'ar Allah ubangiji ya sanya Alkhairi a zaman ku gaba d'aya Amin,(Wannan Nasiha ce ba ga Fatuu kadai ba ga duk wata Amarya da ke karanta Novel d'in nan, duk abun da kika ji mai muhimmanci ki aiki da shi zai maki amfani in sha Allah).