Kenza eBookz

Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature - Chapter 62

Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature - Chapter 62

Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature Chapter 62: Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature Chapter 62. A tare suka fito parlon Hajiya da Saude na zaune…

4,479 words

A tare suka fito parlon Hajiya da Saude na zaune suna kallo, tana ganin su ta fara k'ok'arin mik'ewa Saude ma haka, Hajiya tay ma Fatuu saida safe tace taje ta jira Mijinta yazo daga haka ta nufi k'opa, kallon juna sukai ita da gwaggo ganin idanunta sun ciko yasata girgiza mata kai alamar kada tay kukan had'i da yi mata d'an murmushi da k'yar itama ta d'an yi mata gwaggon ta nufi kopa har zata fita ta juya ta kalli Fatuu da tay tsaye tay mata alamar ta koma ciki a sanyaye ta d'aga hannu ta d'an yi mata bye bye ta jinjina mata kai daga haka ta fuce, bin parlon ta shiga yi da kallo har ta kai idanunta sama kan chandelier taga an canza wata da ta fi ta da k'awatuwa, d'an murmushi tay ta sauke idanunta ta juya har zata shiga corridor sai kuma ta juya ta nufi Dining Area tana tafiya kaman mai yin sand'a, tsaye tay tana bin wurin da kallo ya burgeta sosae can ta nufi wurin table d'in ta kai hannu ta fiddo Warmer guda ta bud'e farfesun yan ciki ne sai zuba uban k'amshi yake, fiddo d'ayar tayi wadda tafi girma itama ta bud'e taga Fried Spaghetti ce da tay brown tasha vegetables daga gefe manyan soyayyun tsokokin nama ne a jere, maida murfin tay ta rufe ta jera su kan table d'in kafin ta d'auki basket d'in ta wuce, Kitchen ta shiga don ta aje nan ma ba k'aramin burgeta yay ba fuskarta d'auke da d'an murmushi take k'are mashi kallo, daga baya ta juyo ta fito ta koma Bedroom.

***** *****

Bayan Abbas ya aje su inna Zaliha direct G.r.a ya wuce, Haisam zaune acikin Bedroom d'in shi saman 3 seater ya d'an kishingid'a ya cire rigar shaddar jikin shi daga shi sai farar singlet da wandon shaddar, Video call yake da Fanan ta cikin computer d'in dake ajiye saman c-table sai faman zabga mashi shagwa6a take kan ya koma tana missing d'in shi sosae shi kuma yana rarrashin ta kan ta kwantar da hankalin ta ya kusa komowa, daga ita sai wasu yan fingilallun half vest da wandon ta wanda da kad'an ya d'ara ma pant sai faman yin abubuwan jan hankali take yanata d'an murmushi don ya gane mata sam bata da Sauk'i ta wannan 6angaren don in dai yana a kusa da ita hana mashi sakat take, suna cikin haka Abbas ya turo kopar Bedroom d'in ya d'an juya ya kalli wurin kafin ya juyo kan screen Fanan d'in ta tambaye shi waye can k'asan makoshi ya furta Abbas aikuwa da sauri ta tashi ta sauka daga saman gadon da take kwance tayi ruf da ciki ta nufi closet, Zama Abbas yay gefen shi yana sakin murmushi ya tambayi da wa yake Video call ne slowly ya furta mashi Fanan,

fad'ad'a murmushi Abbas yay yace "kace da uwar gida kake ganawa, to in ka gama ga Amaryar ka can mun kai maka tana jiran ka" wani kallo Haisam d'in yay mashi mai kaman harara, ba don Fanan d'in ta mik'e ba da tabbas sai taji abunda Abbas d'in yace, dariya sosae Abbas ke yi yana fad'in ya gama boye boyen shi dole asiri ya tonu, Haisam d'in bai tanka mashi ba saima ya maida idon shi kan Screen, lokacin Fanan d'in ta dawo ta zura doguwar riga kanta tasa hula sa6anin da babu hulan sai brown sumar ta da ta zuba gefe da gefen fuskarta duk da haka yanzun ma ta fito daga gefen wuyanta, tambayar ina Abbas d'in yake tay Haisam ya juya laptop d'in ta kalli Abbas dake dariya yace "gani nan uwar gida",

itama yar dariya take tace "uwar gida and also Amarya" wata yar iskar dariya Abbas yasa har saida haisam yay mashi wani kallo suka had'a ido hakan ya k'ara bashi dariyar da k'yar ya tsagaita Fanan d'in tace mashi ko ta fad'i ba daidai bane da sauri yace "No, no daidai kika fad'a kawae yanayin yadda kikai Maganar ne naga kaman akwae son kai a ciki, da sai ki tsaya a uwargidan ita kuma Amaryar sai tazo" wani kallo ta watsa mashi ta had'e giran sama da ta k'asa tace ashe bai k'aunar ta har haka bata sani ba, da sauri ya d'aga hannu yana fad'in tuba yake, cikin d'an d'aure fuska tace to ya daina mata irin wannan mummunan fatan ita kad'ai ce ba k'ari wannan Alk'awari ne Until death do them part itama d'in tare zata d'auke su, jinjina kai Abbas ya hau yi yana k'ok'arin danne dariyar dake ciyo shi yace to ya bari Allah ya bada ikon ruk'e Alkawari tace Amin ai yasan waye mijinta tunda ya d'auka zai ruk'e da sauri Abbas yace gaskiya ne,

"To amman wai ya akai kika k'yale shi yay zaune anan ne naga ma kaman bai da niyyar dawowa nan" d'an 6ata fuska tay "nima na k'osa ya dawo bana jin dad'in rashin shi a kusa dani duk na takura, amman yace man wani aiki ne ya ruk'e shi ya kusa dawowa" d'an ta6e baki Abbas yay ya jinjina kai yace "Tabbas hakane na manta, ko yau ma ya k'ara samun wani babban aikin mai cike da Alkhairi don haka sai kin d'an k'ara hakuri kin d'aga mashi k'afa" d'an rausayar da kai tay tace shikenan ya zata yi tana yi mashi fatan nasara, da sauri Abbas yace "Yauwa, haka ake son matar kwarae duk in mijinta yazo mata da wani Al'amari ta fahimce shi ta yiwu Alkhairi ne" murmushi tay kawai tace bari ta k'yale su suyi hira yace ok, juyo da Laptop d'in Haisam yay sukai sallama cike da nuna kauna kafin ya katse, maida idon shi yay kan Abbas dake dariya ya hau jinjina kai yace "Wato har na fara tausaya maka wllh, waya fad'a maka ana ma mata irin wannan Alk'awarin? Ai koda baka da ra'ayin k'ara Aure bai kamata kai mata Alk'awari ba don bamu ke da iko da kan mu ba komai na iya canza wa just like it happens now, yanzu in tazo ta san da zancen wane kallo kake tunanin zata maka in ma ta saurare ka kenan" bin shi da ido kawae Haisam d'in yay kaman ba zai ce komae ba, can yay sigh slowly ya furta "she was already my wife then" Abbas yace "amman ai ita bata sani ba ko" d'an d'age gira yay yace zai fahimtar da ita in buk'atan hakan ya ta so, d'age kafad'a Abbas yay yana murmushi yace Allah ya taimaka bai amsa mashi ba saima ya juyar da idon shi,

"Yanzu ka tashi muje in kai ka an bar yar mutane ita kad'ai kuma kasan ba sabawa tay ba" ba tare daya kalle shi ba yace yaje kawai, still dariya Abbas ke yi can ya mik'e ya nufi hanyar fita sai lokacin ya juyo ya kalle shi, bayan wani lokaci Abbas d'in ya dawo abunka da wanda yasan gidan hannun shi ruk'e da mug d'an tiriri na fitowa alamar abunda ke ciki mai zafi ne, wurin kujerun ya nufa ya koma inda ya tashi ya zauna ya kai hannu ya kama igiyan tea bag d'in data lek'o waje yana dan tsoma ta ciki yadda zai yi Sosae, bayan wani lokaci ya mik'a ma Haisam dake kallon shi yana murmushi yace ga shi ya sha, wani kallo ya bi shi da shi kafin ya maida kallon kan cup d'in baida niyyar amsa, k'ara kallon Abbas yay ganin irin murmushin da yake yi yasa ya fahimci ko na minene tunda ko da bikin su da Fanan ya bashi irin su, d'an girgiza mashi kai yay slowly ya furta "No need" Abbas d'in yace "kai dai ka amsa don kuwa kana buk'atar shi ko an gaya maka ita ma hakanan za'a kawo maka ita ba tare da an gyara taba ba kamar yadda kai mata aika aika" kallon shi kawai Haisam d'in ke yi baida niyyar amsa, duk yadda Abbas yay dashi kan ya amsa ya sha ya k'i k'arshe dole ya k'yale shi yace yayi ma kansa shi bari yasha Allah yaso zai mashi amfani, bayan ya shanye ya mik'e yace bari ya maida mug d'in daga can zai wuce, mik'ewa Haisam yay ya taka mashi suna zuwa bakin k'opa Abbas yace yaje ya shirya ya tafi gun yar mutane tana can ita kadae, tsaye yay yana kallon shi ya fita yana murmushi har zai rufe kopar sai kuma ya dakata yace "saura ka k'ara bari ka zama uncontrollable kazo kana fad'a man k'auli da ba'adin u feel like ur life depends on it" sai lokacin Haisam ya saki murmushin da har hak'oran shi suka d'an bayyana Abbas d'in ma dariya yake yi yace makullin Motan na nan a wurin da ya zauna ya d'aga mashi kai daga haka sukai sallama ya tafi,

Wurin kujerun ya koma ya zauna kan ta farko ya d'aura kafa d'aya akan d'aya ya zuba ma gaban shi ido da alama tunani yake yi, ya d'an d'auki lokaci a haka can ya mik'e ya fita daga wurin ya nufi hanyar corridor, saida ya d'auki kusan 30 minutes sannan ya fito da alama wanka ma yayi don ya canza kaya zuwa farar shadda Sol sai salk'i take da alama sabuwa ce bata ga ruwa ba, hannun shi d'aure da agogon diamond k'afafun shi na sanye da fararan half cover, kan shi ba hula sai nad'add'ar bak'ar sumar shi da gani an gyara ta don sai shining take yana janye da d'an madaidaicin trolley, saida yaje ya kauda laptop d'in dake saman c-table sannan ya dawo bakin dressing mirror ya d'auki Car Key ya kai hannu ya kama trolley d'in da ya aje, bayan ya latsa switch hasken d'akin ya d'auke ya bud'e kopar ya fita,

Wani irin tsoro ne ya fara kama Fatuu ganin dare yayi sosae don sha d'aya ta kusa, duk ta takure kanta a saman gadon sai wuwwurga ido take ga wata irin yunwa da take ji, lokaci bayan lokaci take duba time a jikin wayar ta dake a gabanta har ta fara fidda ran zuwan Haisam d'in ta shiga tunanin yadda zata kwana ita kadae a part d'in, can bayan wani lokaci taji ana k'ok'arin bud'e kopar aikuwa a tsorace ta tashi zaune jikinta har ya fara yar rawa kanta ba kallabi ta zaro idanu tana kallon kopar, a hankali ya turo k'opar ya shigo da yar sallamar da ko Fatun bata ma ji ba, yana shigowa idanun shi suka sauka cikin nata da ta zaro ya dakata suka bi juna da kallo, ya lura da a tsorace take hakan yasa shi k'ara yin sallama a hankali sai lokacin taji ta amsa tare da sauke nata idanun saman gadon shiru ta biyo baya, jin bai k'ara cewa komai ba yasa ta d'ago ta kalle shi, still yana tsayen suka k'ara had'a idanu cikin yar rawar murya tace "Sannu da zuwa" kai ya d'aga mata kawai ya juya ya nufi wardrobe yana janye da trolley d'in ta bishi da kallo, aje trolley d'in yay ya kai hannu gefenta ya latsa sai gashi ta fara zugewa da kanta sai lokacin Fatuu ta gane yadda ake bud'e ta, bayan ta gama bud'ewa ya kai hannu ya zuge trolley d'in ya fara k'ok'arin fiddo kayan ciki tana ta kallon shi, bayan ya saka na farko ta kai hannu ta d'auki kallabinta ta yafa saman kai ta sauka daga saman gadon a d'arare ta nufe shi, lokacin data isa ya saka na biyu yana juyowa ya ganta a gefen shi ya bita da ido, saida ta had'iyi abu sannan cikin yar in ina tace "b....bari in saka.." bai ce mata komai ba sai kawai ya juya ya tafi tabi bayan shi da kallo, Laundry room ya nufa ya tura kopar ya shige, a sanyaye ta kai hannu taci gaba da fiddo kayan tana jerawa har da su underwear d'in shi, har ta gama bai fito ba ta zuge trolley d'in ta maida shi gefe wurin jakunkunan ta ta aje, komawa tay wurin gado tana niyyar zama ya bud'e kopar ya fito fuskar shi da alamun ruwa haka k'asan hannun rigar shi mai links, tsaye tay ta kasa zaman tana kallon shi tana yi tana maida idon k'asa, tsayawa yay daga d'ayan bangaren gadon yana kallon ta kaman zai yi magana, sai da ya d'an d'auki lokaci sannan taji yayi Maganar saidae bata ji mi ya ce ba ta bishi da kallon rashin fahimta, ya gane bata ji mi yace ba ya d'an maida idon shi k'asa sai kuma ya d'ago slowly da turanci yace ta samu tsarki, kai ta d'aga mashi alamar eh tare da maida idon ta k'asa taji yace taje tayo Alwala tace to, ba tare da ta kalle shi ba ta nufi hanyar Laundry room d'in sumi sumi, lokacin data fito har ya shimfid'a prayer mat guda biyu a saman lallausan carpet d'in dake a gaban gadon yana zaune a bakin gado, wurin jakunkunan ta nufa ta bud'e ta curo Hijab ta fara k'ok'arin saka wa ya mik'e ya daidaita kan abun sallar gaba ita kuma ta hau kan ta baya ya kabbara salla, Nafila raka'a biyu sukai sam Fatuu batayi mamakin jin yadda yake sakin kira'a ba don ba yau ta fara jin shi yana karatun Qur'ani ba yana yawan yi ta cikin wayar shi, gaba d'aya Allah ya bashi ilimin boko dana Addini abun saidae ace ma sha Allah, zama sukai suna lazimi tana ta kallon sumar bayan kan shi ba zato sai gani tay ya juyo har saida gabanta ya fad'i don sun yi gab da juna, had'a ido sukai ta d'an waro nata yay mata alamar ta matso da kan shi, matsawa tay dab da shi ya kai hannu ya dafa kanta ta d'an sunkuyar da kan tana kallon k'asa gaba d'aya k'amshin shi ya gama cikata, Addu'ar da Manzo (S.A.W) ya koyar mutum yayi in yay Amarya ya shiga yi bayan ya gama ya sauke hannun nashi ta d'ago suka k'ara had'a ido, bai yi tunanin tambayar ta wani abu ba don duk abunda yake son sani game da ita ya sani, juyawa yay ya d'aga hannu ya fara jero Addu'oi da sauti kad'an itama ta d'aga nata hannuwan bayan ya gama a tare suka shafa ya yunk'ura ya mik'e tana dai ta bin shi da ido, har yayi taku d'aya zuwa biyu ya dakata ya juyo ya furta akwai abu akan dining table daga haka ya juya ya nufi kopar ya fita, zugudum tay ta bi k'opar da ido tama rasa tunanin da zata yi, gaba d'aya ta kasa gane mashi duk ya canza mata sai kace ba Ya Haisam d'in da ta sani bane, in don abun da tayi ne ai taje ta bashi hak'uri kuma ya nuna ya hak'ura to miyasa taci gaba da ganin shi haka wanda ada da ta bashi hak'uri yake hak'ura kuma bata ganin canji a tattare dashi kamar yanzu, gaba d'aya jikinta ne ya k'ara yin sanyi, tunowa da Abincin da su Hajiya suka kawo yasa ta yunk'ura ta mik'e, cire Hijab d'in tayi ta linke ta mayar ta dawo ta kwashe abubuwan sallan suma ta linke ta je ta ajiye ta d'auki kallabin ta dake a saman gadon ta yafa saman kan nata ta nufi hanyar fita, d'an jimm tay a bakin k'opar tana zullumin fita can dai ta kama handle d'in ta ja kopar ta bud'e a d'arare ta fita,

Tana zuwa bakin corridor d'in ta hango shi zaune akan L-shape ya d'an kishingid'a yana kallo, had'a ido sukai da sauri ta kawar da nata sum sum ta nufi hanyar dining d'in, tana zuwa taga manyan ledoji guda biyu ta fahimci sune yay mata magana akai ta kai hannu ta fara bubbud'a su taga miye a ciki, d'aya su ice cream da Youghort da kuma snacks d'ayar kuma fruit ne, shiru ta d'anyi tana tunanin yadda zata yi dasu can ta d'auki guda ta nufi freezer ta bud'e ta saka, dawowa tayi ta d'auki d'ayar ma taje ta kai ba tare data d'au komai ba don ta ci, bayan ta dawo tsaye tay gaban table d'in tana tunanin ko zai ci Abincin ma, wata zuciyar ta bata taje ta fara tambayar shi, kamar bazata je ba sai kuma ta tafi tana tafiya kamar wadda k'wai ya fashe mawa a ciki, bata zagaya cikin parlon ba sai ta bi ta bayan kujeru ta tsaya a d'an gefen bayan kujerar da yake zaune ta bi shi da ido ta kasa cewa komai, kamar yaji ajikin shi da mutum a wurin ya d'an juyo da kan shi suka had'a ido, d'an kikkafta idanu ta shiga yi da k'yar tace mashi dama Abinci ne aka kawo daga part d'in Hajiya, shiru ya d'anyi still idon shi na akan ta sai kuma ya d'an girgiza mata kai alamar bazai ci ba, maimakon ta tafi sai tay tsaye tana kallon shi ganin haka yasa shi cewa "Dare yayi" saida ta had'iyi abu kafin a sanyaye tace "ai Abincin ba mai nauyi bane" yanayin kallon da yake mata ne ya sauya da sauri ta maida nata idon k'asa tana haka taji ya mik'e ta d'ago tana kallon shi, saida taga ya zagayo sannan itama ta nufi Dining d'in ta d'ayan side d'in da ba ta nan ya bi ba.............

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 da 3 Naira 400 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268

*ASM Bk2062*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

......... Zama yay akan d'aya daga cikin chairs d'in sai lokacin ta tuno da bata d'aukko plates ba da d'an hanzari ta juya ta nufi hanyar corridor Slowly ya juya yana kallonta har ta shige sannan ya janye idon, bada Jimawa ba ta dawo hannuwanta ruk'e da plates da bowl sai serving spoon da kuma spoons da forks duk ta d'aurayo su don da alamun lemar ruwa a jikin su, bayan ta aje ta bud'e babbar warmer d'in ta fara zuba mashi tana sa kaman rabin plate taga ya d'an d'aga hannu alamar ya isa ta d'aukko k'atuwar tsokar nama ta d'aura tana niyyar k'ara wata nan ma ya k'ara dakatar da ita ta hanyar k'ara d'aga mata hannu ta tsaya, saka mashi fork tay ta tura gaban shi ta bud'e Warmer d'in farfesun ta zuba mashi kad'an ta tura mashi, Fridge ta nufa ta d'aukko bottle water da lemu ta dawo ta aje daga gaban shi ta sake juyawa ta koma ta d'aukko glass cups daga cikin fridge d'in ta dawo, tana niyyar bud'e robar lemu ya dakatar da ita a hankali ya furta ruwa kawae yake buk'ata ganin zata bud'e nan ma yace sai ya gama a hankali ta furta to, zuba nata abincin tayi bada yawa ba tasa fork ta d'auka tana niyyar juyawa ya d'ago ya kalleta suka had'a ido ta kasa tafiya,

"zaki je ina ki ci Abinci?" taji cool voice d'in shi ya tambaya, shiru kaman bazata ce komai ba ganin ya kafe ta da ido yasa tace d'aki zata je, still yay yana kallon ta can taji yace "shi nan don me aka yi shi?" Shiru bata ce komae ba ta maida idon ta k'asa, "Sit!" cike da bada umarni taji ya fad'a, ba yadda ta iya dole ta aje Abincin ta zauna, duk da tana jin yunwa ta kasa cin Abincin sosae don duk sai taji ya fitar mata a rai sai d'an tsakura take tana yi tana satar kallon shi yanata cin nashi a nutse, bata wani ci da yawa ba ta mik'e ta d'auki Abincin yana kallonta tun kan yace wani abu tace mashi ta k'oshi zata kai kitchen ne ya d'an d'age mata gira "da kika ci mi?" yanayin Fuskar ta ne ya sauya idanuwan ta sukai rau rau kaman zatai kuka yace ta zauna ta cinye shi, komawa tay jiki a sanyaye taci gaba da ci ba don tana jin dad'in shi ba don ta rasa mike mata dad'i kamar ta fashe da kuka take ji, ya rigata gamawa amman sai yay zaune ya kafe ta da ido har saida itama ta cinye sannan ya mik'e ta bi shi da ido, Fridge ya nufa ya bud'e ya d'aukko babbar robar ice cream da wasu daga cikin Snacks ya dawo, aje mata yay gabanta da sauri ta kalle shi ba tare da ya kalle ta ba yace suma ta cinye aikuwa kaman jira take ta fashe mashi da kuka ta kife kanta a kan table d'in kallabin ta ya zamo ya baro saman kan ta, bin ta da ido yay yana kallon ta da alamun mamaki ita kan ta kawai ji tay kukan yazo mata, d'an kwankwasa saman glass table d'in yay ta d'ago fuskar ta jage jage da hawaye ta kalle shi,

"na buge ki ne?" Ya tambaya had'i da d'age mata gira ta girgiza mashi kai alamar a'a, "then miye abun kuka?" cikin muryar kuka tace "ni na k'oshi" bin ta da ido yay can yace "shine na kuka, ko akwai abunda ke damun ki ne?" Da sauri ta girgiza mashi kai alamar a'a, "Ok, kin ci wani abu ne before I came?" Kai ta sake girgiza mashi, "kuma shine har kin k'oshi?" tana d'an tura baki tace to ba ta ci Abinci ba yanzu, yanayin fuskar shi ne ya sauya kaman zai d'an yi murmushi "ai baki k'oshi ba so ki k'ara da wannan" kallon shi tay ba dama tay mashi musu don kuwa yasan yanayin yadda take cin Abinci, ganin ya kafeta da ido yasa da sigar shagwa6a ta d'an juya kai tana yamutsa fuska tace to ai sunyi mata yawa dare yayi sosae bazata ci Abinci da yawa ba tunda kwanciya zata yi, ganin yadda yake kallon ta tana Maganar yasa ta juyar da fuskar ta gefe can taji yay sigh ya furta Ok, komawa yay ya zauna duk abunda ya d'aukko ya raba biyu saidae d'aya yafi d'aya girma ya bata wanda suka fi girman shi kuma ya fara cin sauran itama ta fara ci tana yi tana d'an kallon shi har lokacin ba kallabi a kanta, kusan a tare suka gama ya bud'e mata robar ice cream d'in ya tura mata ganin yana niyyar mik'ewa da sauri tace to shi bai rage ba ai yayi mata yawa shi ma, wani kallo ya jefa mata sai taga kaman ya harareta ta d'an tura baki ta sauke idon ta k'asa, d'an guntun murmushin da iyakar shi lips d'in sa yay taji yace in ta rage tasa a fridge daga haka ya juya ta d'ago ta bi shi da ido, dakatawa yay ya juyo yace in ta gama yana buk'atar fruit bada yawa ba ta d'aga mashi kai ya juya ya tafi, sai gashi ta shanye ice cream d'in duka dama harda rashin sake mata fuska da ta ga baiyi ba yasa taji komae ya fitar mata a rai, bayan ta gama ta nufi Fridge ta fiddo ledar fruit d'in tunanin ko ta had'a mashi fruit salad tay tasan zai fi jin dad'in sha tayi ta juya tana ruk'e da ledar ta nufi hanyar corridor yana zaune a inda yake da kafin ya tashi ya d'an kai idon shi kanta kafin ya maida su kan tv, ba 6ata lokaci ta had'a mashi ba mai yawa ba sosae a cikin d'an bowl mai kyau ta bud'e fridge d'in cikin kitchen ta d'aukko k'ank'ara ta d'an kwankwatsa ta a ciki ba mai yawa ba don tasan bai son abu mai sanyi sosae, saka ledar fruit d'in tay a cikin fridge d'in nan ta d'auki bowl d'in ta nufi parlon, tunda ta fito ya maido idon shi kanta itama kallon nashi take tana isa ta d'aura saman c-table ta ja shi gaban shi ta d'ago suka had'a ido tace gashi nan da d'an murmushi ya jinjina kai tare da furta thanks, juyawa tay ta koma Dining Area ta fara kwashe kayan Abincin, wanda zata saka a fridge ta saka tay clearing wurin, saida ta wanke duk abunda suka 6ata a cikin kitchen ta maida su ma'adanar kowanne sannan ta fito ta nufi bedroom, tana shiga ta koma can bakin gado inda ta zauna d'azun ta zauna tay shiru kaman mai tunanin wani abu, gajiya tay da zaman ta kai kwance amman k'afafun ta na a k'asa, har bayan wani lokaci tana a hakan can taji an bud'e kopar da sauri ta tashi zaune suka had'a ido, rufe kopar yay ya nufo ciki ya tsaya gaban dressing mirror ya fara k'ok'arin cire Diamond Watch d'in wrist d'in shi, bayan ya cire a saman wurin ya aje ta ya juyo idanunshi suka sauka cikin nata da take ta faman bin shi dasu taga ya nufi hanyar Laundry room tana ta kallon shi har ya shige sannan ta juyo, komawa tay yadda take kafin ya shigo taci gaba da wurga ido tana tunane tunane, kusan Mintuna 15 ya d'auka sannan taji ya turo kopar ya fito tana kwancen ya zagayo wurin gadon, wani irin bugu k'irjinta yay mata don kuwa daga shi sai towel d'aure a k'ugun shi ya fito, tunda take bata ta6a ganin namiji haka ba balle shi da yake Tubarkallah, a rud'e ta juya ta yadda ta bashi baya yana jin mutsu mutsun ta bai ko kalle ta ba ya nufi gaban dressing mirror, duk mayuka da turarurrukan da yake amfani dasu suna a wurin saidae an k'ara wasu dasu kwalaben humra da turaren wuta, mai din shi ya d'an shafa sama sama bayan ya gama ya hau feshe jikin shi da turare Fatuu da tay lamo tana ta kikkifta idanu tana jin yadda yake fesa turarurruka ta d'an lumshe ido had'i da d'an yin murmushi, yana da son k'amshi sosae har da hakan ke k'ara mata k'aunar shi gashi koda yaushe zaka ji k'amshin shi na daban ne, bayan ya gama closet ya nufa ya bud'e bayan ta zuge ya fiddo sleeping dress riga da wando ya juya ya k'ara nufar laundry idon shi akan Fatuu da ta takure guri guda ya d'an ta6e baki da yanayin murmushi kan face d'in shi ya wuce, jin k'arar k'opa yasa ta d'ago da sauri ta kalli kopar Bedroom d'in sai dai bata ga alamar ita aka bud'e ba nan ta gane laundry ya shiga, bada jimawa ba taji motsin zai fito aikuwa da sauri ta maida kan yadda take da, fitowa yay ya saka kayan baccin ya nufi k'opar fita, har ya kama handle d'in sai kuma ya dakata ya juyo yana kallon ta, ta ji lokacin da ya kama k'opar amman bata ji ya rufe ba hakan yasa ta d'an d'ago zata saci kallon shi karaf suka had'a ido nan take ta kama kanta ta k'arasa d'agowa ta tashi zaune sai waro ido take tana d'an motsa baki,

Readers Also Read