Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature - Chapter 66
Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature Chapter 66: Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature Chapter 66. "Who told u ba Abinci bane, yanzu kaci wannan…
3,565 words
"Who told u ba Abinci bane, yanzu kaci wannan kasha ruwa bazaka k'oshi ba?" Ya tambaya had'i da d'age gira, d'an tura baki tay "Ya za'ai su kosar da Mutum, saidae in da yawa aka ci kuma ai kai kad'an ne na kawo maka ko" tana Maganar ya kafe bakinta da kallo, sigh yay ya d'an shaking kan shi "bansan ina zan sa shi ba as am stuffed, I couldn't eat another bite" bin juna sukai da kallo na d'an wani lokaci can ta kai hannu a sanyaye ta d'auki plate tana shirin juyawa taji yace zai ci wani lokacin ta juyo suka had'a ido ya d'an bud'a mata ido alamar taji abunda yace ta d'aga mashi kai daga haka ta wuce ya bita da kallo, bayan ta maida su ta fito ta wuce Bedroom, bada jimawa ba ta fito hannunta ruk'e da laptop d'inta da babban hardcover ta nufo cikin parlon ya maido idon shi kanta, a gefen shi ta tsaya a d'an marairaice tace "please, could you help me with this Assignment, ta email malamin yace mu tura mashi gashi harda drawing nayi k'ok'arin in d'aukko in saka na kasa" shiru yay just staring at her har saida tasha jinin jikinta ta d'an juyar da fuskar ta, tana haka taji cool voice d'in shi yace ta kawo ya gani ta matsa, akan c-table ta d'aura ta shiga nuna mashi yadda Assignment d'in yake bayan ta gama ta d'ago ya kai hannu ya fara latsa Computer din, can bayan d'an wani lokaci ya d'ago suka had'a ido yace mata sai ya d'aukko abu a G.r.a za'a iya tura mashi zuwa dare zai nuna mata, murmushi ta shiga yi tayi mashi godiya bai ce mata komai ba ya koma ya jingina bayan shi jikin kujerar, hannu ta kai zata d'auki laptop d'in slowly taji yace an hana ta zama a parlor ne, kallon shi ta d'an yi still da murmushi ta fasa d'aukar laptop da littafin ta koma d'ayan side d'in kujeran ta zauna, remote ya d'auka ya canza daga channel d'in da yake kallo zuwa Arewa 24 lokacin suna cikin yin maimaicin shirin dad'in kowa da yake k'arfe ukku yayi, d'an juyawa tay ta kalle shi ta d'an yamutsa baki nan take ya gane mi hakan ke nufi ya k'ara canza channel zuwa tauraruwa ganin suna yin wak'ok'i yasa ta d'an yi murmushi, voice d'in shi taji yana tambayar yayi mata ta juya ta d'aga mashi kai ya aje remote d'in dama ta dalilin ta ya san channels d'in hausa, tana kallon wakokin tana d'an bi wani lokacin har d'an juya kai take akwae wata da ya lura tana mata dad'i don sosae take bin wak'ar tana juya kai, still yay yana ta kallon ta kai kace ita ta raira wak'ar saidae kuma kunnan shi na akan wak'ar yana sauraro can kaman taji kallon ta yake ta juya suka had'a ido yar dariya tayi mashi shi kuma ya d'an yi mata guntun murmushi, ana yin wakokin kaman guda biyar suka datse suka sako tallar magunguna, juyowa tay tace mashi ya maida channel d'in da yake kallo sun gama fuskar shi a sake kaman zai murmushi ya kalle ta, tambayar ta yay ba wani da ake irin shi, ta gane wakokin yake nufi tace mashi ko an canza ba lalle ana yi ba dama nan an fi sa su, shiru yay can ya kai hannu ya d'auki remote d'in ya canza channel d'in da yake kallo farko suka cigaba da kallon American film d'in tare, gaba d'aya Fatuu ta takura don sai yin abubuwan sa kunya suke, suna cikin kallon aka nuno jarumin Film d'in da budurwar shi suna romancing juna ji Fatuu tay kaman ta nutse a wurin don abun bana Arziki bane, can abun ya kai ga an sa6ule rigar budurwar har boobs d'inta sun bayyana Fatuu na ganin hakan ta mik'e zumbur ta nufi hanyar corridor without even looking at him ya bi bayanta da kallo shi sai ma ta so bashi dariya yadda tayi, tana shiga Bedroom d'in ta nufi gado ta zauna a baki ta d'an waro ido tay shiru kaman mai tunanin wani abu, a hankali ta kwanta ta takure a guri guda tana cigaba da tunanin da take yi, bata dad'e da kwanciyar ba aka kira sallar la'asar, har tayo Alwala ta zo ta kabbara sallar bai shigo ba, bayan ta gama zaune tay kan abun sallar ta jingina da gado tana haka taji wayar ta na ringing ta mik'e ta nufi bedside drawer inda wayar take ajiye, d'an jimm tay ganin shine ke kiran kafin ta d'auka a hankali tayi sallama amsa mata yay yace mata ya je ya dawo ta yi mashi adawo lpy, tambayar ta yay akwae abunda take so tace mashi a'a daga haka yay cutting kiran, bin wayar tay da kallo bayan ta cire ta daga kunnan ta a ranta ta shiga raya shi d'in ba dai kula ba duk zai fita sai ya tambayi ko tana son wani abu, d'an murmushi tay tana jin k'aunar shi na k'ara ninkuwa a cikin ranta, tunanin tafiya part d'in Hajiya tay ta taya Saude girkin dare tunda ko ta zauna ba abunda zata yi ta mik'e, bayan ta d'aukko gyale da takalma ta k'ara gyara fuskar ta a gaban mirror sannan ta tafi, saida ta tsaya Kitchen ta d'aukko wasu daga cikin kayan da aka kawo masu Abinci don ta maida sannan ta tafi, tare sukai aikin Abincin daren kaman da rana a nan tayi sallar Magrib da isha'i sannan ta baro part d'in tare da Abincin su ta dawo part d'in su har lokacin Haisam d'in bai dawo ba, bayan ta aje kayan Abincin kan table ta wuce Bedroom, har ta zauna bakin gado zata fara latsa wayar ta Zuciyar ta ta ayyana mata yakamata tayi wanka ta mik'e bayan ta aje wayar ta nufi gaban dressing mirror ta cire jewellery d'in jikinta ta maida komai ma'ajiyar shi sannan ta wuce laundry room, after some minutes ta fito sanye da bathrobe kanta ba kallabi sai short towel tana goge fuskar ta da gefen gashin ta, gaban dressing mirror ta tsaya ta shafa mai da su humra bayan ta gama ta wuce wurin kayanta a ranta ta ayyana yakamata ta jera kayan a cikin closet ta yanke gobe tunda ba Makaranta zata je ba tayi hakan, ruwan idon kayan da zata sa ta shiga yi daga k'arshe ta yanke ta saka sleeping dress kawai tunda dare ne kwanciya zatayi ta bud'e jakar da suke ta fiddo wasu riga da wando silk cikin wanda aka kai mata rigar gajeran hannu gare ta ta d'an saukko zata kai cinyoyin ta, gefen gado ta koma ta fara saka su ba tare da ta d'aukko undies ba tunda dare ne, gaban mirror ta koma ta k'ara gyara parking d'in gashinta, bayan ta gama ta maida su bathrobe d'in ta d'aukko phone d'inta ta haye gado ta fara latsa ta, bata dad'e da hawa ba taji an turo kopar da sauri ta kai idonta suka had'a ido dashi ya shigo da yar sallama tana d'an murmushi ta amsa mashi, a gaban gadon ya tsaya tayi mashi sannu da zuwa ya d'aga mata kai, mik'a mata ledar daya shigo da ita yay ta matso ta amsa tana kallon shi kafin ta maida kallon kan ledar shi kuma ya nufi gaban mirror ya fara cire Wrist watch d'in shi, bud'e ledar tay ta lek'a sai kuma ta kai hannu ta fara fiddo abubuwan dake ciki nan taga Pop corn ne da tuwan Madara harda gullisuwa sai Chocolates manya manya with surprise written on her face ta d'ago tana kallon shi don bata tsammaci ganin su ba tunda bata ce mashi tana so ba, hanyar laudary room ya nufa ba tare da ya kalle ta ba da d'an d'aga murya tace "Thank u so much, Allah ya k'ara bud'i na Alkhairi" d'an juyowa yay ya kalleta fuskar shi a sake ba tare da ya ce komae ba ya juya yaci gaba da tafiya har ya shige, tana ta sakin murmushi da alama taji dad'in kawo mata su da yay ta bud'e ledar tuwon madara ta fara sha nan take wani dad'i ya ratsa ta harda lumshe ido lokaci guda zuciyar ta ta tariyo mata can baya irin su ne kyauta ta farko da ya fara mata da hannun shi ta dingi zuba mashi santi harda bashi labarin irin Pop corn d'in da ake kawo masu a Makaranta duk tsakuwowi da gishiri don an raina masu wayau, tunowa da lokacin yasa tay ta dariya can tay tunanin yakamata ta bashi wuri tasan wanka yake in ya fito ya shirya ta saukko daga kan gadon ruk'e da ledar ta nufi hanyar fita, tana zaune a parlor tana cigaba da cin abubuwan ta tana yi tana kallon sabon shirin dad'in kowa ya fito shima ya shirya cikin sleeping dress riga da wando tun kafin ya k'arasa shigowa k'amshin shi ya karad'e parlon, tana ganin shi ta mik'e da hannu tay mashi alama da Dining area ya nufi can ta bi bayan shi, ba wani Abinci sosae yaci ba ya dawo cikin parlon, bayan ta gama ta gyare wurin ta had'o mashi Fruit salad, a kan c-table ta d'aura mashi tace gashi nan ya sha ya furta mata thanks tay d'an murmushi ta koma inda ta taso ta zauna taci gaba da kallon ta, bayan an gama ta juyo suka had'a ido lokacin har ya gama sha tay mashi d'an murmushi taji yace zasu iya yin Assignment d'in yanzu tace eh, bud'e Computer d'in yay dama tana nan ba'a d'auke ba ya fara operating nata tana ta kallon shi can taga yay mata alamar tazo da hannun shi ba tare daya d'ago ba ta mik'e ta nufe shi, a gefen shi ta ja ta tsaya ya k'ara mata alamar ta zauna a kusa da shi still bai kalleta ba, a d'arare kaman mai jin tsoro ta raku6a gefen nashi ta zauna ya shiga nuna mata yadda zatai, tun dai bata saki jiki ba har ta washe suka cigaba da yi har ta kai ya kama hannunta yana koya mata yadda zata d'aukko zanen, tuni jikin su ya had'e da na juna gaba d'aya sun cika juna da fitinannan k'amshi, ba'a d'au wani dogon lokaci ba suka gama har an tura ma malamin tana ta murmushin jin dad'i ta hau yi mashi godiya, d'an murmushi kawae yake ba tare daya ce komai ba ta mik'e ta kai hannu ta d'auki book d'in tana shirin juyawa ta tafi kwatsam tay tuntu6e da kafar shi ta tafi gaba d'aya zata kifa aikuwa cikin zafin nama ya jawo ta tayo baya ta fad'o jikin shi gaba d'aya, tsit kake ji Wutar Fatuu ta d'auke don ba k'aramar razana tayi ba gaba d'aya ta runtse idanunta gam jikinta sai d'an rawa yake tana fitar da numfashi da sauri da sauri, still yay yana bin fuskar ta da kallo ya kasa cewa wani abu idanunta sai rawa suke, bayan wani lokaci natsuwar ta ta daidai ta a hankali ta fara bud'e idanun ta, bayan ta ware su gaba d'aya suka sauka akan face d'in shi dake gab da ta ta, sam kowa ya kasa yin kwakkwaran motsi sunyi tsit gazing in to each other's eye and inhaling each other's sweet scent, Fatuu ce tay k'arfin halin ce mashi ta gode da taimaka da yay ta fara k'ok'arin d'agowa sai dae ta kasa don ya ruk'e ta tightly, slowly ya d'ago da fuskar ta ta yadda saura kad'an su had'e Fatuu na ganin haka da sauri ta runtse idonta breathing d'in su ya fara had'uwa zuciyarta ta fara beating da sauri da sauri, numfashin ta ne ya nemi tsayawa jin ya had'e bakunan su.........
_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 da 3 Naira 400 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268*ASM Bk2065*
_Destiny may be delayed but cannot be changed...._
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
........... Kissing d'in ta ya shiga yi deeply a nutse hannun shi duka biyun talla6e da kanta da ba kallabi gashinta dake fake yayi k'asa, Fatuu kam tuni ta k'ame ta kasa ko d'aga hannunta don abun yazo mata unexpected sai numfashin ta da ke fita rapidly kirjinta na hawa da sauka da sauri da sauri, sun d'auki lokaci a haka kafin slowly ya kwantar da ita akan kujeran tayi Flat still idanunta na a rufe, had'e fuskokin su yayi ta yadda tsinin hancin shi ya had'e da nata inhaling each other's breathe wanda gaba d'aya yake fita da k'arfi, sun d'an d'auki lokaci a haka kafin slowly ya janye fuskar ya fara Moving dinta around her neck yana inhaling scent d'in jikinta, a wannan lokacin a wata irin duniya ta daban Fatuu take jinta the world around her faded away, sai faman sakin nishi take ta kai har saida ta d'an bud'e bakinta don ji take numfashin ta na neman katsewa, wani irin salo yake mata mai rikita kwakwalwa a nutse cike da gwanancewa, suna cikin haka ya kai hannu ta k'asa a hankali ya fara tattare rigar ta, Fatuu na jin haka bugun zuciyar ta ya k'aru, dakatawa yay da shak'ar K'amshin wuyan ta da yake ya fara jawo fuskar k'asa har ta sauka kan flat tummy d'in ta daya bayyana sakamakon dama iya rigar baccin ce ta rufe shi, har saida Fatuu ta d'an gantsare lokacin da taji ya kai nan jikinta ya fara d'an rawa ta fara mommotsa k'afafun ta, bin cikin nata ya fara yi yana cigaba da shak'ar Scent d'in da jikinta ke saki giving her soft kisses at the same time, she's savoring every touch and every kiss ji take tamkar zata suk'e, cigaba da moving face d'in shi yay yana yi mata abunda yake mata, a haka har ya rage da ya k'ara janye rigar boobs d'in ta zasu bayyana a lokacin numfashin Fatuu kusan d'aukewa yay, yana k'ok'arin k'ara janye rigar hannun shi ya gogi boob d'in ta, dakatawa yay da abunda yake matan tamkar an latsa mashi pause yay d'an jimm can kuma sai ya d'ago daga jikin nata, dakatawar da yay yasa da k'yar ta d'an bud'e idanun ta da sukai mata wani irin nauyi ta hango shi zaune daga gefe kan shi a k'asa yasa hannu guda ya dafe gefen fuskar tashi, k'arasa bud'e idanun ta da tuni sun canza daga ainihin kalar su da yanayin su tayi ta bi shi da kallo har lokacin numfashin ta da d'an k'arfi yake fita, sun d'an d'auki lokaci a haka can wata zuciyar ta raya mata zaman me take ta tashi ta tafi d'aki, da k'yar ta yunk'ura ta tashi zaune ta saukko da k'afafawun ta k'asa kafin ta mik'e, ko ta kan littafin ta da laptop d'in bata bi ba ta nufi hanyar corridor tana tafiya a harhard'e gaba d'aya jikinta jin shi take kaman ba nata ba sai kace na wadda ta tashi daga ciwo sam ba k'arfi a jikin nata kwata kwata, Slowly ya d'aga idon shi da suka sauya daga yanayin su yana kallon ta har ta shige d'aki sannan ya maida kan nashi k'asa yasa dukkan hannuwan shi ya talla6e shi, tana shiga ta nufi bakin gado ta zauna dabas ta kankame jikinta da har lokacin yana d'an yin rawa, gaba d'aya ji take kamar har lokacin yana cigaba da yi mata abubuwan da suka wakana tsakanin su, gaba d'aya ya tado mata da urge d'in ta dama kuma a tsume take a yadda take ji ma sai tayi wanka, ta d'an d'auki lokaci a haka can ta kai kwance k'afafunta na a k'asa tay tsuru tana ta imagination hakan ya k'ara kashe mata jiki sosae, zuciyar ta ce ta fara raya mata anya Ya Haisam na son ta kuwa, inda yana son ta bata tunanin yadda suka kai wani mataki haka zai k'yale ta, wata zuciyar ta k'ara raya mata da bai son ta zai yi mata abubuwan da yayi mata ne sai kuma ta sake raya ai k'ilan bada niyya bane kaman yadda ya faru a G.r.a dalili ne ya sa komai ya faru to k'ilan yanzu ma haka ne tunda ita ta fad'a mashi, idanunta ne suka ciko da k'walla ita kad'ai tasan abunda take ji a jikinta can ta runtse idanun ta suka fara gangaro mata, ta d'an d'auki lokaci a haka saida taji ta d'an samu sassaucin abunda take ji a jikinta sannan ta yunk'ura ta tashi zaune sai kuma ta mik'e tana tafiya a hankali ta nufi wurin kayanta ta d'aukko hula tasa, gaban dressing mirror ta tsaya tana kallon kanta kwalla na ci gaba da zubo mata daga baya ta sa hannu ta goge ta juya ta nufi hanyar laundry, d'aure da towel ta fito ta koma wurin kayanta ta curo doguwar riga ta zumbula daga haka ta nufo gado ta kwanta ta ja duvet ta lullube har kanta. Tun bayan da ta shige yake zaune a yadda yake tsawon lokaci sai daga baya ya mik'e ya nufi hanyar fita daga cikin parlon walking slowly, not too long da fitar shi ya dawo hannun shi ruk'e da wani abu har ya zauna sai kuma ya mik'e bayan ya aje abunda ya d'aukko a kan kujerar ya nufi hanyar Dining, bottle water ya d'aukko daga cikin freezer ya dawo, zaunawa yayi ya shiga bud'e ruwan bayan ya bud'e ya aje shi akan c-table ya kai hannu gefen shi ya d'aukko abunda ya aje wanda d'an kwali ne kamar na magani ya bud'e, ciro abunda ke ciki yay ya 6allo guda d'aya ya saka cikin bakin shi ya kai hannu ya d'aukko robar ruwan, bayan ya shanye ya rufe robar ya aje ya maida abun cikin kwalin wanda kaman magani ne, bayan ya rufe kwalin ya sake mikewa ya nufi hanyar fita, bada jimawa ba ya dawo ya nufi wurin Switch ya kashe hasken Parlon ya bar na wasu k'ananun fitilu kaman yadda yake yi ya koma wurin Kujerar, Zaune yay idon shi akan Corridor kaman mai tunanin wani abu, ya d'an d'auki lokaci a haka kafin ya kwanta yau ko pillow d'in babu saidae ya tada kan shi da hannun kujera yasa tafin hannun shi d'aya ya rufe fuskar shi, ta dad'e bacci bai d'auke ta ba sai tunane tunane take tana juye juye har dare ya yi sosae tana a haka, har Addu'a tay a cikin ranta kan Allah yasa tayi baccin, sai bayan wani lokaci sannan baccin ya d'auketa cike da mafarkan abunda ya faru.
Sai da gari ya fara wayewa sannan ta farka lokacin har anyi sallar Asuba tuni, bayan tayo Alwala tazo ta kabbara salla, zaune tay da ta gama cikin ranta tana ayyana Ya Haisam bai shigo bane yin Alwala da bai tashe ta ba, haka tay ta zancen zuci ita kad'ai sai bayan wani lokaci sannan ta mik'e ta cire Hijab d'in data yi sallar ta ninke ta d'auke prayer mat duk ta maida su wurin da suke, komawa tay gado ta kwanta ta kudundune taci gaba da yin sak'e sak'e a ranta, tsawon lokaci tana a hakan bacci yak'i d'aukar ta har taji ta gaji da kwanciyar ta mik'e don ta gyara d'akin, bayan ta gama gyaran d'akin tasa turaren wuta toilet ta wuce tayo wanka, bata canza kaya ba doguwar rigar jikinta ta bari haka jikinta ma iya mai kawai ta shafa sai turare data fesa ta koma bakin gado ta zauna, hakanan rashin shigowar Haisam d'in ta tsaya mata ta raya k'ilan don abunda ya faru ne k'ilan kuma ya shigo tana bacci, gaba d'aya ta rasa mike mata dad'i har wayarta ta daukka don tayi ko chatting ne amman k'arshe sai dai ta aje ta ta haye gado tay shiru, tana kwancen taji anyi knocking kopar d'akin ta tashi zaune da alamun mamaki, jin an k'ara kwankwasawa yasa ta mik'e ta nufi kopar, tana bud'ewa taga Saude ce tayi mata murmushi itama ta d'an yi mata ta gaishe da ita, bayan ta amsa tace mata dama Breakfast ne ta kawo to bata iske kowa a parlon ba kar ta aje ta tafi kuma ba'a san ta kawo ba yasa tace bari tayi mata magana, Fatuu ta d'an yi mamakin jin tace ba kowa a parlon kenan ma baya nan godiya tay mata har Sauden zata juya ta tafi sai kuma ta dakata idon ta akan Fatun tace "amman ko baki lafiya ne?" d'an fad'uwa gaban ta yay tayi d'an murmushi tace mata a'a lafiyar ta lau, Sauden tace "amman Fateema naga idanunki sun canza kaman ma kuka kikai ko?" da sauri ta girgiza mata kai "a'a Aunty Saude" tana kai Maganar ta sunkuyar da kanta k'asa don sai taji idanunta na tara k'walla, hakan da tayi yasa Saude zargin da wani abu ta kai hannu ta dafa Shoulder d'inta tace "in wani abu ke damun ki Fateema ki fad'a man in da taimakon da zan maki, barin damuwa ba abunda yake ma mutum sai haddasa mashi ciwo" da k'yar ta maida k'wallan ta kalle ta da d'an murmushin yak'e ta girgiza mata kai tace "ba abunda ke damuna Aunty Saude kawai na tashi da ciwon kai ne" kai Sauden ta jinjina ta yarda da abunda tace ta tambayi to tasha magani tace mata eh tun jiya da daddare,