Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature - Chapter 67
Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature Chapter 67: Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature Chapter 67. "to yanzu ai yakamata ki k'ara sha tunda ga…
4,106 words
"to yanzu ai yakamata ki k'ara sha tunda ga Abinci nan na kawo ki zo ki ci sai ki sha maganin in kuma kinji bai daina ba gara kiyi magana akai ki Asibiti, kinsan yanzu haka malaria ke sa mutane suyi ta ciwon kai mai tsanani" kai ta d'aga mata tace ta zo tayi breakfast d'in, ba musu ta fito suka shigo parlon tare Sauden tace suje tay serving nata da sauri tana murmushi tace mata lafiya lau zata yi ai ba wani ciwo yake mata sosae ba tay mata godiya ita kuma tay mata Allah ya sawak'e ta tafi, zaune tay a dining d'in ta kasa yin Breakfast sai tunanin inda Haisam d'in ya tafi take wata zuciyar ta raya mata k'ilan ma ba gidan ya kwana ba k'arshe ta yanke watak'il yana G.r.a, ta d'auki lokaci a haka kafin ta fara yin Breakfast din, bata wani ci da yawa ba ta mik'e ta koma d'aki, ji tay duk zaman bai mata dad'i ta yanke tafiya part d'in Hajiya bayan ta d'aukko gyale ta yafa ta fita, tana kaiwa bakin k'opar parlon zata bud'e taga an turo ta kalli mai shigowar da sauri, Haisam ne ya shigo jikin shi sanye da k'ananun kaya da gani wanka yayi sai sakin uban k'amshi yake, suna had'a ido ta sadda kanta k'asa da sauri, k'arasa shigowa yay idon shi a kanta ya tsaya daga gefe, kirjinta ne ya fara bugu da sauri sauri da k'yar ta bud'e baki ta gaishe dashi ba tare data kalle shi ba ya amsa, shiru ba wanda ya k'ara tanka wa balle ya motsa still idon ta na k'asa shi kuma ya kafeta da nashi idon wata irin kunyar shi taji ta rufe ta, jin bai k'ara cewa komae ba kuma yayi tsaye yasa ta d'an d'ago ta kalle shi suka k'ara had'a ido da sauri ta juyar da face d'in ta gefe ta fara motsa baki murya na d'an rawa ta fad'i mashi zata part d'in Hajiya ne, shiru bai ce komae ba hakan yasa ta d'an juyo still kallon ta yake sai kace mai nazarin wani abu, tambayar ta yay bata lafiya ne ta d'aga ido ta kalle shi sai kuma ta girgiza mashi kai had'i da maida idon k'asa, ji tay ya k'ara cewa in bata lafiya ne su je Hospital ba tare da ta kalle shi ba a sanyaye tace mashi lafiyar ta lau k'asa k'asa ya furta Ok ya fara k'ok'arin wucewa ciki, har zata fita sai kuma ta tuna da breakfast d'in da aka kawo ta juya ta koma ciki daga gefe ta tsaya ta d'an kalle shi yana zaune kan kujera tace mashi ga breakfast can an kawo ya jinjina kai yana kallonta, ganin tayi tsaye yace taje in da zata tace zatay serving nashi ne yace no problem zai yi da kan shi ta je, kallon shi ta sake yi idon su ya k'ara had'uwa da sauri ta juya ta nufi kopa ta fita, Tana tafe tana zancen zuci gaba d'aya ta kasa gane ma wannan auren nasu, tasan ana aure ne in ana son juna to su ita ce ke sonshi shi ba son ta yake ba kawae ya aure ta ne don ya taimaka mata ba don suyi rayuwar Aure ba abun kuma turns out this way, yanzu haka zasu cigaba da yin tasu rayuwar auren? Ta jefa ma kan ta tambaya, ta so ace shima yana jin son ta ya kuma nuna mata tasan da ba k'aramar rayuwar Aure mai dad'i zasu yi ba, idanun ta ne suka ciko da k'walla daga baya suka fara zubowa, saida ta iso bakin part d'in sannan tasa gefen gyalenta ta goge Fuskar sosae sannan ta shiga, ganin ba kowa a parlon yasa ta wuce Bedroom d'in Hajiya nan ta iske ta tana bacci ta fito ta nufi Kitchen ba kowa a ciki ta juyo ta nufi d'akin Saude, ciki ta isketa tana ganinta ta washe mata baki tana fad'in har ta samu sauk'i da ta fito, a gefen Katifarta ta zauna tana murmushi tace mata ai fa dama ba sosae yake mata ciwon ba yanzu ma ta samu sauk'i ta zo ta taya ta aikin Abinci Sauden tace a'a yau dae ta huta ko ta k'ara samun sauk'i Sosae tay murmushi kawae, kwanciya tay akan Katifar Sauden don tak'i yarda ta taya ta aikin bada jimawa ba kuma bacci yay awon gaba da ita, saida akai sallar Azahar Saude tazo ta tashe ta don tayi salla, bayan ta gama sallar ta nufi Bedroom d'in Hajiya ta isketa zaune akan prayer mat tun bayan da ta gama salla bata tashi ba ta nufi gefen ta ta zauna tana gaishe da ita da murmushi ta amsa tana tambayar ina Angonta ta sanar da ita ai tun d'azun tazo ta iske tana bacci shine ta wuce d'akin Aunty Saude nan bacci ya kwashe ta, tana zaune a d'akin Hajiyar sai ga Haisam ya shigo tunda suka had'a ido ta maida kanta k'asa ya zauna a bakin gado bayan ya gaida Hajiyar suka shiga d'an yin fira jefi jefi daga baya Saude ta shigo ta sanar da ita an shirya table tace ai sai su tashi suje suci gaba d'aya tunda suna nan, Fatuu ce tay Serving d'in su bayan itama ta zuba nata ta zauna saidai kasa sakin jiki tay taci sosae sai faman Jujjuya cokali take har Hajiya ta gane ta tambaye ta ko bata son Abincin ne da sauri tace mata a'a tace to taga tak'i sakin jiki taci sosae in bata son shi tayi Magana sai a samar mata wani abun tace a'a tana so dole ta daure ta rink'a turawa, bayan sun gama Haisam ya tafi dama shi ya fara tashi su kuma suka koma Parlor suna kallo, sai bayan la'asar sannan Fatuu ta koma part d'in su tana zuwa ta wuce toilet don tayi wanka, bayan ta fito ta shirya cikin doguwar rigar Atamfa A shape ta d'an shafa powder da lip glow ta fesa turarurruka, wayarta ta d'auka ta haye gado ta fara yin Azkar bayan ta gama tay tunanin kiran Haulat don tun ranar tarewar ta rabon ta da ita, ta dai san da ita aka kawo ta amman bata san lokacin data tafi ba, sai bayan isha Haisam ya dawo yau ma harda ledar su ice cream ya kawo mata tayi mashi godiya daga baya suka wuce dining area don cin Abinci, bayan Fatuu ta gama duk abunda zata yi na shirin kwanciya ta d'aukko Al'qur'ani ta zauna a saman gado tana karantawa lokacin Haisam ya shigo shima tuni yayi shirin kwanciya, dakatawa tay da karatun ta kalle shi ba laifi ta rage jin kunyar tashi Fuskar shi a sake ya nufo gadon ya d'auki pillow yace mata "Gud night" kai ta d'aga mashi ya juya ta bishi da ido har ya fita sannan taci gaba da karatun, Washe gari ana kiran sallar Asuba ta farka, tana gama yin sallar ta wuce toilet tayo wanka, bayan ta fito ta fara shirin zuwa Makaranta, Yana kwance kan kujera idanun shi a rufe ta fito sanye da Uniform ta nufo cikin parlon, daga gefen shi ta tsaya tana kallon fuskar shi ta fara tunanin ko bacci yake yi, slowly taga ya fara bud'e idon suka sauka a kanta, gaishe da shi tayi ya jinjina mata kai cikin yar inda inda tace mashi dama Makaranta take son zuwa, kafeta yay da ido ba tare da yace komai ba hakan yasa ta maida nata k'asa, tana haka taji yace tayi breakfast ne ta girgiza mashi kai alamar a'a, shiru yay ta d'ago ta kalle shi yace to zata tafi School d'in ne ba tare da tayi breakfast d'in ba tace mashi eh,
"Dama kina yin haka?" taji ya tambaya, ta gane yana nufin dama tana zuwa Makarantar ba tare da tayi breakfast d'in ba, a hankali tace "a'a, amman in na tsaya jira zan iya makara, nasan bata san da zanje Makarantar bane yasa bata yi da wuri ba" tana Maganar ya kafeta da ido, sigh yay taji yace sai tayi breakfast zata je ta kalle shi yanayin fuskar ta ya sauya, tunawa tay da ice cream d'in daya kawo mata ko roba d'aya bata sha ba tace mashi bari tasha ice cream da cin cin to, wani kallo yay mata ya d'an yamutsa fuska yace ya zata sha abu mai sanyi da safe ta yamutsa fuska a shagwa6e tace to ai lafiya lau in ta tsaya jira sai an kawo zata makara ne fa, shiru yay kaman bazai ce komai ba can yay mata alamar ta zauna da hannu, bayan ta zauna ya yunk'ura ya mik'e tana ta kallon shi ya nufi kopa ya fita, bayan fitar shi tana zaunen idanunta suka sauka akan pillow tay tunanin ta d'auke tunda tasan shi zai kai ta School d'in kuma daga can ba lalle ya dawo nan ba, mik'ewa tay ta nufi kujerar ta kai hannu ta d'aukko filon, wani abu ta ji ya fad'o akan k'afarta ta kai idanunta k'asa don taga minene, duk'awa tay ta kai hannu ta d'aukko abun, k'aramin kwali ne wanda ya d'aukko jiya ta bishi da kallo, daga yanayin sunan dake jiki da hotunan jiki ya nuna magani ne saidae ta kasa gane maganin ko na miye daga sunan shi amman daga yanayin hoton jiki ya nuna kaman na ciwon ciki ne don wani mutum ne a jiki ya daddafe cikin shi ya d'an duk'e sai kuma daga gaba gashi nan bayan yasha maganin a kwance yanata bacci harda d'an murmushi akan fuskar shi, jujjuya kwalin ta shiga yi a ranta tana raya Ya Haisam bai lafiya ne amman bata ga alama ba wane irin ciwon ciki yake yi, ranta ne ya bata ta bud'e k'ilan akwae leaflet a ciki sai ta duba k'ilan ta gane na ko wane irin ciwon ciki ne, har zata bud'en sai kuma wata zuciyar tace mata bafa kyau yin bincike hakan yasa ta fasa sai ma ta maida pillow d'in kawae ta tura maganin a karkashi don tana tunanin anan yake ya fad'o, bata dad'e sosae ba da komawa ta zauna sai gashi ya shigo hannun shi ruk'e da d'an babban tray ta bi shi da ido har yazo ya aje akan c-table, matsar mata yay da table d'in yace gashi nan ta kalli tray d'in sai kuma ta kalle shi ya koma ya zauna, hannu ta kai ta bud'e plate d'in da aka rufe wani plate nan take k'amshi ya bugi hancin ta taga indomie ce tasha vegetables harda soyayyun cinyoyin kaza guda biyu tayi gwanin kyau a ido daga gefe kuma Cup d'in tea ne an had'a shima an rufo shi, da alamun mamaki ta d'aga ido ta kalle shi ya jingina bayan shi yana kallon ta mamaki ta shiga yi a cikin ranta na badai shi ya dafa ta ba, hannu ta kai ta d'auki fork ta fara ci sosae tay mata dad'i, kasa jurewa tay tana cikin ci ta dakata ta kalle shi yana ta latsa wayar shi,
"Amman kai ka dafa ta ne?" da k'yar ta tattaro kalmomin ta tambaye shi, shiru kaman bai ji tambayar da tayi ba har ta fidda ran zai amsa taga ya d'ago ido ya kalle ta taji yace ta tambayi Abincin mana, d'an tura mashi baki tay ta maida idon ta kan Abincin, tana cikin ci taji yace shi ya dafa akwai matsala ne, har saida ta maimaita Maganar tsabar mamaki ba wai don ya dafa matan ba sai don bata ta6a tunanin ya iya girki ba koda dafa tea ne, saida ta cinye ta duka farko ta rage yace mata wa zata bar mawa tana d'an murmushi tace shi d'an murmushi yay kawai ya gane wasa take mashi tunowa da can baya, naman ne ta rage ta kwashe kayan ta kai Kitchen, saida ta wanke komae ta d'ebi su dublan don ta kai ma su Fauzy harda ice cream ta d'aukar mata sannan ta koma Bedroom ta d'aukko jakar ta da takalma dama ta saka safa tun da tasa uniform.
Bayan sun isa ya fiddo kud'i ya bata ba tay mashi musu ba don tasan ba maidawa zai ba tayi mashi godiya ta bud'e Motar ta fita, tun kan ta shiga aji wasu da suka ganta sukai shelar zuwanta, tana zuwa bakin Class d'in su Zainab suka fito da gudu suna mata oyoyo Amaryar su suka rungume ta tana ta masu dariya, bayan sun saketa ta tambaye su Fauzy suka ce bata kai ga zuwa ba suka nufi cikin ajin suna ta tsokanar ta wai k'amshin Amarci take gashi tayi Fresh ita dai sai murmushi take kawai, bata dad'e da zuwa ba Fauzy tazo tun daga bakin Class ta hango ta ta shigo da gudu tana fad'in k'awarta Amarya tana zuwa seat d'in ta rungume ta Fatun nata dariya, zama tay sai kallon Fatun take tana sakin murmushi tace "ai banyi tunanin zaki zo yau d'in ba, nayi zaton zaki k'ara kwana biyu kaman yadda na baki shawara" d'an girgiza mata kai tay alamar a'a, "wai badai duk Amarcin bane yasa baki magana" Fauzy ta fad'a baki bud'e Fatun ta sa dariya tace mata a'a,
"Amarci dad'i, Wai kinga yadda kikai Fresh duka kwana ukku, gaskiya nima na fara jin son aure wllh" ta k'arasa tana dariya itama Fatuu dariyar take suna haka malamin su ya shigo, bayan anyi break sun fito ne Fauzy ke tambayar Fatuu wai ko wani abun na damunta ta lura da suna class kaman tana yawan yin tunani a sanyaye tace mata ba komai saidae Fauzyn bata yarda ba tace in wani abu ke damunta ta fad'i mata in na shawara ne sai ta bata barin damuwa ba zai mata magani ba har da ce mata ko bata yarda da ita bane tace mata a'a, ganin yadda duk ta damu da son jin ko wani abu na damunta yasa a sanyaye tace "ba wani abu ke damuna ba Allah Fauzy, kawai dai....na rasa gane kan Ya Haisam, gani nike bai so na kaman yadda ake hasashe kawai ya yarda yaci gaba da zama dani ne ba wai don yana sona ba" idanun ta ne suka ciko da k'walla da sauri ta fara k'ok'arin maida su, ajiyar zuciya Fauzy ta sauke duk da bata san dalilin da ya sa tace haka ba ranta ya bata wani abu, tambayar ta tay dalilin daya sa tace haka tay d'an murmushi tace mata ba komai kawae dai yak'i sake mata ne, hak'uri Fauzyn ta bata tace ita tana ganin a k'ara bashi lokaci k'ilan da dalilin hakan amman tana kokonton ace bai sonta kuma ya za6i cigaba da zama da ita to miye ribar hakan, ai indae dama ya aure ta tun farko don ya taimaka mata ne to ba dalilin da zai cigaba da zama da ita Fatun tace bata ganin ko don abunda ya faru yaga bai kyauta mata ba in ya rabu da ita yasa, Fauzy ta girgiza kai tace gaskiya bata tunanin hakan koda da hakan to akwae wani dalilin wanda kuma tana ganin so ne Fatun tay shiru kawai, Fauzy na son ta yi mata Maganar magunguna amman dalilin wannan Maganar yasa ta fasa, ana tashi Haisam yazo d'aukar ta saida Fauzy ta rakata har bakin Mota ta gaisa da shi sannan ta wuce Hostel su kuma suka tafi........
*ASM Bk2066*
_Destiny may be delayed but cannot be changed...._
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
.........Tun bayan data shiga ta gaishe da shi ya amsa bata k'ara ce mashi komai ba ta juyar da kanta tana kallon gefen hanya, lokacin da suka iso Unguwar suna zuwa gab da gidan su ta juya ta kalle shi yana kallonta ta mirror ta d'an cije baki had'i da d'an yamutsa fuska, dage mata gira yay ba tare da ya kalleta ba yace "What?" A marairaice tace mashi don Allah ya bari ta shiga gida ta gaida gwaggo idon ta akan shi taga ya d'an girgiza kai alamar a'a, 6ata rai tayi idanunta sukai rau rau tana ta d'an kikkafta su bata yi tunanin zai k'i barin ta ta shiga ba, suna shiga kwanar gate tace mashi ya aje ta anan ta shiga ta k'aramar kopa ya parker ba tare da ya ce komai ba, saida ta juya zata bud'e kopar taji voice d'in shi yace ta bari wani time zata je yanzu in taje za'ai mata fad'a ne, juyowa tay ta kalle shi fuskarta a d'an kwa6e ya bud'a mata ido alamar taji ta jinjina mashi kai sannan ta juya ta bud'e, bayan ta fita yaja Motar ya tunkari gate ita kuma ta shige, tana isa part d'in a bakin kopar parlor ta cire takalmanta kafin ta wuce ciki, tana shiga Bedroom tay sensing k'amshin Haisam a ranta ta raya ko ya shigo d'akin ne, wata zuciyar ta ce k'ilan wanka yazo yayi, wucewa tayi ciki ta aje jakar ta ta cire Hijab sannan ta dawo wurin gado ta fad'a alamar ta kwaso gajiya, tana kwanciya taji k'amshin ya cika mata hanci fiye da yadda taji shi da ta shigo, hancinta ta kai jikin zanen gadon ta shinshina nan ta tabbatar da k'amshin shi ne ke tashi a jikin zanen sosae, cigaba da bin jikin zanen tai tana sunsunawa kafin ta d'ago mamaki shimfid'e akan fuskar ta, tambayar kanta ta shiga yi mi zai kawo k'amshin shi haka a wurin in dae ba kwanciya yay ba wata zuciyar ta bata kwanciyar yayi kenan, jikinta ne yay sanyi tay shiru a ranta tana raya kenan had'a gado da ita ne bai son yi, sosae abun ya dame ta don har Fuskar ta ta bayyana, ta d'an d'auki lokaci haka can ta tuna da bata yi salla ba ta saukko jiki sa6ule ta wuce laundry room, Alwala tayo tazo ta kabbara salla har ta gama bai shigo ba ta wuce Toilet don tayi wanka, bayan ta fito shiryawa tay cikin sabuwar doguwar rigar Atamfa tana tsaye a gaban mirror tana d'an yin light make up yayin da a ranta take ta juya kwanciyar da yayi akan gadon tana haka ya turo k'opar ya shigo suka had'a ido ta cikin mirror d'in, ganin yayi tsaye yana ta kallon ta ba tare daya ce komai ba yasa ta juyo ta kalle shi lokacin yace mata ga Abinci can an kawo ta fito ta ci ta d'aga mashi kai daga haka ya juya ya fita ta bi shi da ido, Bayan sun gama cin Abincin ta gyara wurin ta wanke komai a ranta ta yanke tafiya part d'in Hajiya don ta bashi wuri k'ilan ya k'ara kwanciya kan gadon in zai yi bacci, tana can har yamma suka fara aikin girkin dare da Saude, suna cikin yin girkin ne ta tambayi Sauden akan yau da safe ita ta dafa mata indomie, yar dariya tayi don ta d'ago dalilin yin tambayar tata tace mata ba ita ta dafa ba wanda ya kai mata shi ya dafa, ganin Fatun tayi d'an jimm yasa tace mata tayi mamaki ko ta d'aga mata kai tace "nima sosae nai mamaki lokacin dana fito na gan shi a cikin Kitchen yana dahuwar, na kuma rud'e don abu ne da ban ta6a gani ba, ni tunda nike da shi ban ta6a ganin yazo ko bakin Kitchen d'in nan ba balle ta kai shi da yin girki, bamma yi tunanin ko ruwan zafi ya iya dafawa ba sai gashi da yin girki kuma da ga ji Abincin yayi dadi don baki ji yadda k'amshi ya cika wurin Kitchen d'in ba" Murmushi kawae Fatuu ke yi a cikin ranta tana raya a haka kai kace Saboda yana son ta ne yayi amman kawai kulawa ce, ji tay Sauden ta k'ara cewa "ni bansan zaki Makarantar bane ai da nayi maki Breakfast din da wuri, saida ma nace ya bari in yi amma yace in bar shi kawae dai in rink'a tashi da wuri ina maki" shiru Fatuu tay still da murmushi akan fuskar ta Saude ta shiga tsokanar ta tana fad'in ai daga yau da tayi sallar Asuba bazata koma ba kar tayi ma Ango laifi kan Amaryar shi, sai bayan da tayi sallar isha'i ta koma part d'in su tare da Abincin nasu, lokacin da suka yi shirin kwanciya tana zaune akan gado tana yin rubutu ya shigo tana ganin shi ta san mi ya shigo yi da kanta ta d'auki pillow d'in ta mik'a mashi ya amsa Fuskar shi a sake ya furta mata thanks da kuma Gud night ya juya tabi shi da kallo ta d'an kwa6e fuska.
Ranar Laraba bayan ya d'aukko ta daga Makaranta sun gama cin Abinci ta gyara wurin, tana cikin Bedroom ya turo kopa ya shigo tana zaune a bakin gado ta juya ta kalle shi, daga bakin gadon ya tsaya Fuskar shi a sake itama da murmushi take kallon shi ya d'an d'auki lokaci ta fahimci kaman wani abu yake son cewa amman kuma yayi shiru, tambayar shi tay ko akwai abunda zata yi ya girgiza mata kai slowly taji yace in tana so taje gida yanzu da daddare zai zo ya d'aukko ta, waro ido tay baki bud'e take kallon shi ta kasa ce mashi komai don Maganar tazo mata a bazata, ganin yadda tayi yasa shi d'an d'age mata gira yace ko bata son zuwa ne aikuwa da sauri ta mik'e tana girgiza mashi kai had'i da yin murmushi ta hau yi mashi godiya farinciki bayyane akan fuskar ta ta nufi wurin wardrobe don ta shirya ya bita da ido, ba 6ata lokaci ta gama shiryawa da wata rantsattsar sabuwar shadda a cikin kayan da aka kawo mata ta ca6a ado ta fito a Amaryar ta sak sai k'amshi take bazawa, lokacin da ta fito yana zaune akan kujera yana lallatsa Computer ya d'ago ido yana kallon ta har ta k'araso ta tsaya daga gefen shi tana ta murmushi shima murmushin ya mayar mata tace mashi ta tafi ya d'aga mata kai ta juya, har ta fice idon shi na akan kopar sai bayan wani lokaci ya janye idon ya maido shi kan abunda yake, tana tafiya tana faman sakin murmushi sai kace wadda ta shekara bata je gidan ba, lokacin da ta iso kopar gidan shagon Kawu Amadu a kulle yake dama tunda suka wuce da aka d'aukko ta daga Makaranta taga shagon a kulle, a ranta ta raya k'ilan yana Makaranta daga haka ta shige cikin gidan, daga bakin k'opa ta tsaya tsakar gidan wayam ba kowa tana murmushi ta kwad'a sallama ba'a amsa ba saida ta k'ara d'aga murya tayi wata sallamar sannan ta jiyo Muryar gwaggo ta amsa, d'an lek'o da kanta tayi don taga waye nan tay arba da Fatuu dake tsaye tana mata murmushi, hannu gwaggo ta kai ta rufe baki sai kuma ta janye kan ta koma ciki bada jimawa ba sai gata ta fito hannun ta ruk'e da tsintsiya ta d'agata alamar bugun Fatun zatayi ita kuwa mi zatay in ba dariya ba ta nufe ta da gudu suna had'e wa ta k'ank'ame ta gaba d'aya harda tsintsiyar, dariya itama gwaggon tasa tana fad'in waya fito da ita Fatun tace Ya Haisam din ne ai yace tazo ko, d'aki suka nufa Fatun tay ma gwaggon side hug, bayan sun shiga a bakin gado suka zauna idon su a cikin na juna sai faman dariya suke ma juna, sosae gwaggo taji dad'in yadda ta ganta duk da Fuskar ta ta d'an fad'a amman wannan dama tun kafin ta tare ne Saboda ciwon laulayin da tayi amman ta k'ara haske fuskar ta sai sheki take fatar nan tayi lukui ko d'igon k'urji babu, Fatuu ce ta katse shirun ta gaishe da ita bayan ta amsa ta tambayi suna lafiya tace mata eh,
"Amman ya akai kika fito haka da wuri, bana ce banson ki rink'a zaryar zuwa ba miyasa wani lokacin baki jin magana" tay Maganar ta d'an d'aure fuska, a shagwa6e tace "Wllh shine fa yace in zo..." tunkan ta rufe baki ta katseta "to tunda kin matsa ba dole yace ki zo ba" da sauri ta ce mata wllh bata matsa mashi ba nan ta kwashe yadda akai ta fadi mata gwaggon ta gyad'a kai alamar ta yarda, tambayar ta tayi Kawu Amadu tace bai dawo ba yana Makaranta tace dama saida tayi tunanin haka, hira suka shiga yi kai kace sun dad'e da rabuwa, suna cikin yin Hiran Fatuu ke mata Maganar kud'in da suke a cikin Account d'in ta tace ana ta ajiyar su zata turo mata tayi wani abun dasu, gwaggon na yar dariya tace to ita mi zata yi da su tunda nata ne tayi wani amfanin dasu mana, tace ai ita ba abunda zata yi dasu,