Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature - Chapter 70
Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature Chapter 70: Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature Chapter 70. Bayan sun gama cin Abincin suka dawo parlor nan…
4,426 words
Bayan sun gama cin Abincin suka dawo parlor nan Hajiya Maryam tace mata tunda Yayan ya dawo sai ta fad'a masu abunda yasa ta buk'aci ganin su, numfasawa Hajiya tay ta gyara zaman glass d'in fuskarta sannan ta fara Magana a nutse "Farko dai muyi ma Annabi salati" gaba d'aya suka amsa da sallallahu alaihi wa sallam, bayan kowa yayi taci gaba "dalilin kiran ku abu ne ya taso wanda dole kuna da buk'atar sani ko ba don komai ba don halin rayuwa, ta wata fuskar ba lalle ku kalle shi a matsayin abun Alkhairi ba amman ina fatan ku natsu kuyi amfani da hankalin ku ku kar6e shi a matsayin Alkhairin domin duk abunda kaga Allah yayi to mai kyau ne" dakatawa tay tana maida numfashi duk sun natsu suna sauraronta Hajiya Maryam na gefen ta yayin da Senator ke facing d'in su acan d'ayan bangaren, Maganar da tayi yasa duk suka k'osa su ji miye abun da take son sanar da su d'in, kasa hak'uri Hajiya Maryam tay tace "muna jin ki Hajjaju" sauke yar ajiyar zuciya Hajiya tay ta d'aura "Haisam ne yayi aure, kuma yanzu haka da nike maku magana Matar tashi na zaune a gidan nan acan part d'in nashi" har saida Hajiya Maryam ta d'an zabura ta d'ago sosae idon ta akan Hajiya da alamun d'aurewar kai tace "Mi kike fad'a haka Hajjaju, Wane Haisam d'in yayi AURE!!!" tace mata wane Haisam ta sani banda d'an su, da tsananin mamaki akan fuskar ta tace "To ni ban gane mi kike nufi da yayi aure ba, ai dama duk mun san da yayi aure ko" d'an ta6e baki Hajiya tay kafin tace "dana ce yayi aure baki ji nace Matar na a cikin gidan nan ba, ko dama nan yake zaune da Matar tashi da kuka san ya aura?" da alama bakunan kowannen su ya mutu, shi dai Senator bin su da ido kawai yake ya jingine bayan shi da kujera yatsun hannun shi na had'e cikin na juna, Bayanin Yadda Al'amarin ya kasance Hajiya ta shiga yi masu tiryan tiryan har ta gama ba wanda ya katse ta sannan furiously Hajiya Maryam tace "kenan don uban shi har ya isa yayi aure without our Knowledge, Saboda bamu da amfani a wurin shi bai d'auke mu da daraja ba ko mi!!!" a tsananin fusace tayi Maganar har huci take, kallon Senator tay tace "Yaya kana ji fa, wai yaron nan har ya kai yayi aure bada sanin mu ba!" d'an girgiza kai kawai yay still bai yi magana ba, "ke kuma Hajjaju ya aikata wannan d'anyen aikin har ki goya mashi baya kisa ya zauna da ita, tunda matsayin taimakon ta yayi to miyasa bazai saketan ba zaki bashi dama suci gaba da zama" a fusace idanunta akan Hajiya tay Maganar, Hajiya data kwa6e fuska tace "to miye amfanin sakin nata tunda abu ya shiga tsakanin su har rabo ya shiga tsakani...." A zafafe Hajiya Maryam ta katse ta don da ta ambaci rabo tamkar ta watsa mata ruwan zafi taji cikin k'unar zuciya tace "Don Allah ki daina wannan Maganar Hajjaju, wane rabo ba kince ya zube ba to cigaba da zama da itan na minene???"
"Amman dai kinsan in aka saketa ai ba ai mata Adalci ba, da ya aure tan ai matsayin zai taimaka mata akai dashi ba'a yi dashi wani abu zai shiga tsakanin su ba ko, to tunda har hakan ya kasance sai a rungumi Al'amarin ai fatan ya zama Alkhairi ta yuwu dama Allah ya k'addara auren ba don su rabu bane" girgiza kai Hajiya Maryam ta shiga yi tana cigaba da yin huci can tace "Impossible wllh, bazai cigaba da zama da ita ba, duka yaushe yay Aure da za'a ce wai har ya k'ara, k'arin ma na wulakanci da kaskanci, dole mu nuna mashi bashi ke iko da kan shi ba akwae masu iko dashi da zai je yayi gaban kan shi, in ba iskanci ba da ya raina mutane a ina na ta6a jin irin wannan taimakon" idanunta har sun sauya kala tsabar 6acin rai, kallon Senator tay "Yaya kana jin rainin wayau ko, dole ma a raba su wllh kawai a kira shi ya saketa!!!" tana rufe baki Fatuu ta sawo kai cikin parlon da sallama tana sanye da jallabiya ta yafa veil d'inta duk suka maida idanun su kanta, nan take ta ja ta tsaya tana bin su da ido itama, da hannu Hajiya tay mata alamar ta k'araso ta nufe su a d'arare don kuwa duk ta gane su, tana zuwa bakin kujerun ta toge duk tasha jinin jikin ta ganin yadda suke bin ta da ido ba kamar Hajiya Maryam wadda bacin rai ke kwance k'arara akan fuskarta, Hajiya ce tace "ki k'araso mana Fateema" shiga tay duk ta kame kanta, nuna mata kujera Hajiya tay alamar ta zauna maimakon ta zauna samanta sai ta duk'e saman carpet daga d'an nesa da Hajiyar, fuska a sake tace "an dawo?" Kai ta d'aga mata,
"amman ya akai baki shigo tun d'azu kin ci Abinci ba?" Cikin rawar murya tace "a..ai yanzu na dawo, na tsaya a Hostel ne wurin Fauzy mun yi Assignment" da k'yar ta k'arasa sakamakon mugun kallon da Hajiya Maryam ke jefa mata don kuwa ta santa tasan itace Matar Haisam d'in, tuni zuciyarta ta hau bugu da k'arfi da k'arfi, kai Hajiya ta jinjina sai kuma ta sake cewa "baki gaida bak'i ba to, kin gane su?" Kai ta d'aga mata alamar eh ta kalli Hajiya Maryam cikin rawar murya ta gaida ta tay mata banza, juyawa tay kan Senator dake ta kallon ta shima ta gaida shi ya jinjina mata kai kawai, juyowa tay kan Hajiya Maryam ta k'ara gaishe da ita aikuwa ta zabga wani uban tsoki ta mik'e ta nufi hanyar barin Parlon a fusace da sauri Fatuu ta fara k'ok'arin matsawa saidai ko kafin ta bata hanya ta cimmata aikuwa ta ham6are ta gefe ta wuce Fatun ta bugi kujera sosae aikuwa nan take ta fashe da kuka don ba K'aramin buguwa tayi ba, yamutsa fuska Hajiya tayi ta bi Hajiya Maryam d'in da kallo har ta shige Corridor sannan ta girgiza kai ta maido idon kan Fatuu ta mik'a mata hannu alamar ta matso ta jawo jiki tana cigaba da yin kuka tana gogewa da gyalen jallabiyar ta da ya zame daga saman kan, rarrashinta ta shiga yi tana bata hak'uri hannun ta guda a saman shoulder d'inta ta d'agota ta zaunar da ita akan kujerar kusa da ita tana cigaba da rarrashin ta, tana cikin goge k'wallan ta kai idonta kan Senator suka had'a ido kawai sai gani tay yay mata alamar tazo da kan shi, dakatawa tay tana kallon shi ya d'aga hannu ya k'ara kiranta Hajiya da ta gani tace taje ana kiranta ta mik'e a d'arare ta nufe shi, bayan ta isa gaban shi tana k'ok'arin zama akan carpet ya nuna mata kujerar kusa da shi yace ta zauna, zama tay tana cigaba da goge Fuskar ta tana yar ajiyar zuciya, a nutse cike da dattako ya fara magana,
"Kiyi hak'uri kin ji, ranta ne a 6ace shiyasa tay maki hakan amman Kada ya dame ki, nasan ba ki rasa sanin cewa in rai ya 6aci mutum na iya aikata komai ko?" Kai ta d'an jinjina mashi, d'an murmushi yayi "Good, a wani School kike ne?" Still muryar ta rawa take don wani irin kwarjini ne dashi ta bashi amsa, jinjina kai yay "da kyau, kinyi nisa a Karatun ne?" tace "Eh ina aji biyu kuma mun kusa yin Exam" nan ma kan ya jinjina yace "sai ku shiga aji ukku kenan, ai kaman daga nan ma zaku gama ko don nasan kaman karatun 3 years ne" kai ta d'aga mashi a sanyaye tace eh, "kice watarana in bani lafiya za'ai man Allura kenan, koma har kin iya yanzu?" ya d'an bud'a mata ido sak irin yadda Haisam ke yi dabarbarcewa tay don bata tsammaci ganin hakan daga gare shi ba tace eh ta iya, wani kallo yay mata irin na baka yarda da Mutum ba yace "kai, ki fad'a man gaskiya fa, ko don Kada ince baki da k'ok'ari kika ce hakan" da sauri tace "Allah da gaske nike na iya harda sa drip ma da d'inki" jinjina kai yay yana murmushi yace "kice Daughter d'in nawa mai k'ok'ari ce kenan" d'an waro ido tay baki a d'an bud'e take kallon shi ya d'age mata gira yace ko bata da k'ok'arin da sauri tace tana da shi, kai ya jinjina taji yace taje taci Abincin da sauri tace to ta mik'e ta nufi hanyar barin cikin parlon duk suka bita da ido Hajiya na d'an murmushi dama tunda suke Magana dashi take kallon su tana murmushi, Ajiyar zuciya ya sauke ya kai hannu ya shafi fuskar shi yana kallon Hajiya yace "She's so cute" Hajiya dake murmushi tace mashi haka take sai ma ya zauna da ita tana da dad'in zama sosae, nan ta shiga bashi labarin rayuwar da sukai da Haisam a baya, Maimakon ta shiga Kitchen d'aukko Abincin sai ta zille ta bi ta kopar baya ta fuce, bata bi ta 6angaren da d'akin Hajiya yake ba tabi ta d'ayan 6angaren tana tafiya cikin sauri ta d'an d'age kasan rigarta tana yi tana waigen bayanta ta nufi part d'in su.........
_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 da 3 Naira 400 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268
*ASM Bk2068*
~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
.........Har tuntu6e take yi tsabar sauri, tana zuwa part d'in su ta shiga parlor ta wuce Bedroom, tana shiga ta maida kopa ta k'ulle harda saka Key ta juya da gudu ta nufi gado ta Fad'a sai faman numfarfashi take ta zaro ido hannuwan ta har d'an kerma suke sai tuno abunda ya faru take Fuskar Hajiya Maryam na mata gizo, tafin hannunta ta kai ta rufe baki tasa Kuka, Sosae Senator yaji Fatuu ta burge shi da Hajiya na bashi Labarin ta da Haisam Fuskar shi d'auke da Murmushi, suna nan har aka yi La'asar ya tashi don yaje Masallaci yace mata daga can zai wuce G.r.a ya d'an huta, fuskar ta da murmushi tace to ba ga d'akinta ba in ya dawo ya kwanta ya huta yana dariya yace mata to ta bari zai zo ya kwana akan gadon nata itama dariyar take ta mik'e don taje tayi sallar itama, Lokacin da ta shiga cikin d'akin nata anan ta iske Hajiya Maryam aciki pacing up and down sam ta kasa zama tun d'azu abunda take kenan, sai ta zauna sai ta mik'e ranta a tsananin 6ace, Hajiya na shigowa suka had'a ido da ita ba tare data ce mata komai ba ta nufi hanyar toilet, Alwala tayo ta fito ta nufi cikin d'akin, saida ta shimfid'a abun salla sannan ta kai idonta kan Hajiya Maryam da ta zauna a bakin gado k'afar ta d'aya akan d'aya idon ta na kallon wuri guda ta cije le6en ta na k'asa tana d'an jinjina kai, ce mata tay bata ji an kira salla bane ba tare data kalle ta ba tace taji zatayi, saida Hajiya ta fara yin Salla sannan ta mik'e ta nufi Toilet, ita ta fara tashi bayan sun gama ta cire Hijab d'in jikinta ta aje a gefen gado ta koma ta zauna kaman yadda take d'azun sai faman d'an jijjiga jiki take tsananin bacin rai kwance akan fuskar ta, bayan Hajiya ta shafa Addu'a ta juyo ta kalleta na d'an wani lokaci ta d'an girgiza kai, tasan halin ta tana da d'aukar zafi sosae sam bata 6oye fushi,
a nutse ta fara mata magana "Yanzu Maryam abunda kika aikata ma Yarinyar nan daidai ne, ita miye laifin ta a ciki ne, kusan fa ita akai ma ba daidai ba ma, an aureta bada sanin ta ba kuma sannan yazo ya hakke mata tunda ita bata san da ya aureta ba abu ya kai ga har da samun ciki yazo kuma ya 6are wanda hakan yasa ta a mawuyacin hali, in rai ya 6aci ai bai kamata hankali ya gushe ba sai a bi komai a sannu asa tunani, komai ki ka ga ya faru to dama can haka Allah ya k'addara, don haka sai mu d'auka dama Allah ya k'addaro Aure tsakanin su" Tunda Hajiyar ta fara Magana bata juyo ta kalleta ba sai da tay Maganar k'arshe sannan ta juya a zafafe tace "Pls Hajjaju stop saying that, komai sai ace kaddara, Yes an san komae sai Allah ya amince yake Faruwa amman harda sa kai, don uban shi in son taimaka mata yake ai akwae hanyoyi da yawa da zai yi hakan, Why not yayi amfani da kud'i akwai abunda basu yi bane balle kuma su da suke yan k'auye ma tuni zai sa a fasa yi mata auren in yay amfani dasu, kuma ma wai miye nashi na damuwa da wanda zata auran kowa ai da kalar k'addarar sa, watak'il in ta aure shi ya canza amman Saboda ya isa da kan shi shine yay gaban kan shi shiga isasshe ko, to zamu nuna mashi haihuwar shi akai ba a komae yake da iko da kan shi ba" tana huci ta k'arasa Maganar, d'an guntun murmushi Hajiya tay "kinga dae kenan Magana ta na kan hanya, kince kowa da kaddarar sa to suma hakan kaddarar su ce kenan shiyasa komai ya juye hakan sai kowa ya rungumi Al'amarin a matsayin hakan" wani kallo take bin Hajiya dashi ta yamutsa fuska cikin k'unar rai tace "Hajjaju na fahimci goya mashi baya kike shiyasa ma har ya samu k'warin gwuiwar cigaba da zama da ita, haba! ta ya zaki goyi bayan wannan kaskantaccen Auren, Auren wulakanci, in ma k'ara Auren zai yi ai wannan ba class d'in shi bace wllh, kuma ba kowa za'a wulakanta ba face Fanan taya ma za'a had'a ta kishi da wancan abun" sai huci take tayi mitsi mitsi da idanu, d'an murmushi Hajiya tay idonta akanta tace mata ba mace bace ita Fateemar kuma miye aibunta, d'an jim tay fuska a yamutse tana ma Hajiya kallo irin na baka zaci jin Magana daga bakin mutum ba,
"Hajjaju wato na lura dae kin za6i faranta ma bare fiye da naki ko, kin sani matuk'ar auren nan aka ce ya d'ore ba wanda zai cutu irin Fanan, don Allah duka yaushe aka yi auren nasu da za'a ce har an yi mata kishiya, da mi zata ji ne da damuwar lalurar dake tare da ita ko kuwa da wannan damuwar da ake neman k'ara mata, wai ko don cikin da ta samu ne yasa kike goyon bayan auren, Saboda ance Fanan nada lalura ai ba yana nufin bazata haihu ba, tunda anata kokarin nema mata magani sai a bari zuwa wani lokaci aga in bata haihu ba sannan ai tunanin auro wata, kuma shi in ba don ya nuna irin halin nasu na maza ba da ba yan goyo bane ba har alk'awari yayi mata zai zauna da ita a halin da take ciki koda kuwa bata haihu ba shine tun ba'a je ko ina ba zai watsa mata k'asa a ido ya nemi tarwatsa mata zuciya wato ta mutu ma shi ba damuwar shi bane, to wllh bazan zuba ido ta cutu ba Saboda wata kaskantatta can" tana kaiwa k'arshen Maganar ta kai hannu ta warto wayar ta ta mik'e, har ta nufi hanyar k'opa sai kuma ta dakata ta juyo ta kalli Hajiya data bita da ido ta d'an sassauta d'aure fuskar da tay tace mata sun gama Maganar zata fita, d'an murmushi Hajiya tay ta sani duk irin zafin zuciyar ta mai d'a'a ce a gareta yanzu ma tasan Saboda tsoron abunda zai iya faruwa da Fanan yasa ta zauna tana ta mata Magana cikin 6acin rai kuma bata d'auki hakan a wani abu ba don ta san yadda soyayyar d'a da Mahaifi take, kai ta d'aga mata alamar sun gaman ta juya ta nufi kofa, cikin nuna ma kopar k'arfi ta bud'eta ta fuce,
Kuka Fatuu tasha har ta gaji tay shiru don kanta, kiran sallar la'asar ya tada ita taje tayo Alwala tazo ta kabbara salla, bayan ta gama zaune tay kan abun sallar ta langa6ar da kanta jikin gado ta shiga duniyar tunani. Hajiya Maryam na fitowa daga d'akin Hajiya Visitor room ta nufa, tana shiga ta d'aga wayarta tana k'ok'arin yin kira ba tare data zauna ba, d'an kai da komowa ta fara lokacin da wayar da ta kira ta fara ringing , Haisam zaune kan kujera a cikin d'akin da yake aikin injiniyancin shi kira ya shigo wayar shi, hannu ya kai saman desk d'in gaban shi ya d'aukko wayar, bin screen d'in yayi da ido ganin mai kiran lokaci guda ya yanke ba lafiya tasa ta kira shi ba ba kamar da yake dare ne kuma yasan tasan lokacin da suke ciki, shima abu ne ya ishe shi bacci ya k'aurace mashi yasa shi zuwa wurin yay zaune yayin da Fanan ke d'aki tana bacci, saida kiran ya kusa yankewa yay picking ya kai wayar kunne, sallama yayi mata tayi mashi banza cikin cool voice d'in shi ya gaida ita aikuwa kaman tana jira a fusace tace "Ka rik'e gaisuwar ka ban so, ai bamu da girman da zaka gaishe da ni tunda kai isashshe ne ka kai kayi gaban kanka, ashe Haisam baka da Mutunci ban sani ba! mu zaka wulakanta ka nuna bamu kai ba a wurin ka, kai ka Haifi kan ka ne ko mu muka haife ka da har zakai Aure ba tare da sanin mu ba, da izinin wa kaje kai auren???" Shiru yay bai da niyyar tanka mata aikuwa hakan ya k'ara hasala ta cikin daka tsawa tace "bazaka bud'e baki kai man Magana ba don ubanka" d'an lumshe ido yay ya bud'e, in ba ya manta ba tunda yake ba'a ta6a zagin shi haka ba, slowly ya bata hak'uri yace yayi ne don taimako, a fusace tace "then what are u waiting for da baka saketa ba kaman yadda kuka tsaran? Mi ya zaunar da ita" shirun ya k'ara yi saida tace bai jita bane sannan yace "Hajiya ce ta hana"
"Hajiya ce zata zauna da ita ko kai" d'an jimm yay sai kuma yace "I can't argue with her" shiru tay cikin ranta ta fara tunanin kenan ba don Hajiya ba zai saki yarinyar ne, d'an sassauta murya tay tace mashi shikenan zata yi Magana da Hajiyar he should be expecting her call kowane lokaci don ya saki Yarinyar, amsa mata yay da toh tace tasan Fanan bata sani ba to Kada ya sake ya bari ta samu labarin har zuwa lokacin da zai sake ta nan ma da toh ya amsa mata tay mashi sai da Safe ta kashe Wayar, bin wayar yay da kallo tun bayan daya cireta daga kunnan shi, can yay sigh ya fara latsa ta na d'an wani lokaci ya dakata ya zuba ma Screen ido kaman mai kallon wani abu...,
tana ta zaune a wurin cikin duniyar tunani, a hankali take kai hannu tana goge yar kwallan dake zubo mata daga cikin idanuwan ta da har sun d'an kumbura, wayar tace ta fara ringing ta d'aga kai ta kallo ta a saman gadon, ganin zata iya jawo ta yasa ta kai hannu ta jawo tan ta kalli screen d'in, Abbas ne mai kiran nata har saida ta d'an ji sanyi dama duk yau bai kirata ba, d'aga kiran tay ta kara wayar a kunne muryar ta can k'asa tay mashi sallama, bayan ya amsa ta gaishe dashi ya amsa daga haka tay shiru, jin yanayin muryar ta yasa shi tambayar ta lafiya nan ma tayi shiru, ce mata yay ta fad'a mashi inda matsala cikin rawar murya ta fara fad'i mashi duk abunda ya faru, sosae Muryar Abbas ta bayyana rashin jin dad'in abunda ya farun ya shiga bata hak'uri daga baya ya tambaye ta game da reaction d'in Senator nan ta gaya mashi komae tana gamawa ya furta "Alhamdulillah, dama nasan ta 6angaren shi ba za'a samu wata matsala ba, itama Momy Maryam d'in kawae tana taya d'iyar ta kishi ne ba wani abu ba, so kar kisa damuwa a ranki in sha Allah komai zai daidai ta na d'an lokaci kad'an ne" a hankali ta amsa mashi da to, "Yanzu kin ci Abincin ne?" D'an girgiza kai tay tace mashi a'a, "Ya zaki sa damuwa har ta hana ki cin Abinci hakan ai sai wani ciwon ya kama ki, ba wani Abincin da zaki ci ne?" bashi amsa tay da eh tace amman bari taje ta dafa indomie yace ta d'an jira ba sai ta dafa ba, har zai cutting kiran sai kuma taji yace bata tambaye shi Mijin ta ba, tura baki tay kaman ya gani yay yar dariya yace koda yake ai yanzu tafi shi kusa da shi daga haka ya katse, wayar na ruk'e a hannunta ta maida kan ta jingina da gadon kaman yadda take ada ta runtse idanu ta sake fad'awa duniyar tunani wanda duk na Haisam ne, gama wayar su da Abbas bada jimawa ba aka k'wank'wasa kopa ta bud'e idanunta ta kallo kopar zuciyar ta na harbawa da sauri da sauri, mik'ewa tay a d'arare ta nufe ta hannun ta har yar rawa yake da zata bud'e, tana bud'ewa suka had'a ido da Saude tana mata murmushi itama ta k'ak'alo d'an murmushin tayi mata a sanyaye ta gaishe da ita, hannu ta kai ta kamo hannunta guda suka nufo cikin parlon, akan kujera ta zaunar da ita itama ta zauna nan ta fara lallashin ta tace ita bata ma san abunda ke Faruwa ba don tana baya sai yanzu da aka kira ta a waya ai da tun d'azun ta kawo mata Abincin kuma itama ai data kirata sai tazo ta kawo mata amman zama da yunwar ga damuwa ai sai suyi mata illa, tasata gaba Saude tay saida tasa taci Abincin sosae daga baya ta k'ara kwantar mata da hankali kafin ta tafi. Bayan Hajiya Maryam ta yi waya da Haisam a bakin gadon cikin d'akin ta zauna hannunta ruk'e da wayar ta d'aura ha6arta saman shi, tunanin ta yadda zata 6ullo ma Hajiya har ta amince a saki Fatuu ta shiga yi, ta d'an d'auki lokaci a haka kafin ta idasa hayewa saman gadon ta kwanta da tunanin zata yi mata Magana anjima. Da daddare bayan kowa yayi shirin kwanciya Hajiya Maryam ta nufi d'akin Hajiya ta shiga da sallama Hajiya dake zaune a bakin gado sanye da kayan bacci idanunta na sanye cikin glasses tana duba wayarta ta amsa mata ta nufo ta, a bakin gadon daga d'an gefe ta zauna tayi mata sannu da hutawa da d'an murmushi Hajiya data d'ago kai ta amsa mata, shiru suka d'an yi Hajiyar ta maida idon ta akan Wayar ita kuma tana kallon k'asa, juyowa tay ta kalli Hajiya tace mata dama Magana take son su yi ne ta d'ago tare da jinjina mata kai idonta a kanta alamar ita take jira,
"Mun yi Magana da Haisam ya fad'a man ke kika hana ya saki Yarinyar can, kinga kenan shima ba wai son zaman yake da ita ba kawai yayi maki biyayya ne don haka ni ina ganin tunda shine mai zama da ita kuma ba so yake ba sai ki bashi dama ya rabu da ita hankalin kowa ya kwanta" d'an murmushin dattako Hajiyar tay jin abunda aka ce Haisam d'in yace, gyara zaman glass d'inta tay idonta akan Hajiya Maryam a nutse ta fara magana "Kaman yadda kika ce biyayya yay man yaci gaba da zama da ita to kema ina son kiman biyayya ki bi yadda nike so, ki yi masu Fatan Alkhairi a auren shikenan komai ya wuce" wani kallo take bin ta dashi baki bud'e alamar Al'ajabin Maganar tata rai 6ace tace "to wai Hajjaju akan mi zaki mashi dole ya zauna da ita ne, ya aureta don taimako da nufin zai saketa sai a sa ya saketan barin shi ya ci gaba da zama da ita ba komai zai ja ba sai 6acin rai" girgiza kai Hajiya ta fara yi "Ba zai rabu da ita ba Maryam dole yaci gaba da zama da ita, in kece ko Fanan a matsayin ta bazan so abunda kike so mata ba" ta k'are Maganar tana girgiza kai bakinta a kwa6e, yarfa hannu tay ta yamutsa fuska tamkar zata saka kuka cikin breaking voice tace "Wai Hajjaju ya kika za6i faranta ma bare ne fiye da naki, kin san idan Fanan ta samu labarin nan ba K'aramin mawuyacin hali zata shiga ba, dame zata ji don Allah ko so kike zuciyarta tay bursting ne, sai nike ganin kaman kin fi damuwa da ita yarinyar ma fiye da Fanan, in don haihuwa ne a ba Fanan d'in time mana kaman yadda nace d'azun duka ai ba dad'ewa sukai da yin auren ba ko" shiru Hajiya ta d'anyi still idanunta na akan ta sai faman huci Hajiya Maryam din take ta gumtse baki idanunta sun Kad'a da gani kiris ya rage ta saka kuka, cikin kwantar da murya Hajiya tace "idan aka zo Maganar Adalci Maryam baka duba bare ko naka indai Adalcin tsakani da Allah za'ai, koda Fateema take 6are ai itama tana da dangi kuma suna son ta suna son farincikin ta, sannan Maganar halin da Fanan zata iya shiga ita ai Musulma ce kuma inada yak'inin tana da cikakken imani hakan kuma na nufin ta yadda da k'addara mai kyau ko akasin hakan don haka in sha Allahu ina sa ran zata rungumi hakan matsayin k'addara kaman yadda ta rungumi ta lalurar ta ake ta neman Magani" Kuka ne ya taho mata tace "Hajiya kar azo ai dana sani, na fad'i maki har Alk'awari fa yayi ma Fanan kan bazai k'ara aure ba koda bata haihu ba kuma akan hakan suke zaune in taji ya k'ara auren nan har matar ta samu ciki mi kike tunanin zai iya biyo baya don Allah, dama kuma ga yanayin ta" cewa Hajiya tay in sha Allahu ba abunda zai faru kuma tasan lokacin da yay mata Alk'awarin ya riga ya auri Fatuu ne don haka shi yasan yadda zai rarrashe ta, a k'arshe ta tabbatar mata da indai ba yarinyar ce tace bata son zama dashi ba to wllh ba zai saketa ba, mik'ewa tay zumbur ta nufi hanyar fita Hajiya na kallonta ta kwa6e fuska.