Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature - Chapter 71
Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature Chapter 71: Asanadin makwabtaka book 2 by zee bature Chapter 71. Bayan ta koma d'aki kai da komowa ta shiga yi ta…
4,477 words
Bayan ta koma d'aki kai da komowa ta shiga yi ta cize baki, abun ya matuk'ar d'aure mata kai yadda Hajiya ta kafe, a tunanin ta koda cewa akai Fanan bata haihuwa kwata kwata Hajiya bazata matsa ayi mata kishiya ba tunda abun na gida ne, dogon tunani ta shiga a k'arshe zuciyarta ta bata wani tunani kan dalilin Kafewar Hajiyar, A daren Hajiya Maryam ta yanke komawa lagos a yadda take ji ba don dare yayi ba da bazata ma kwana ba, a daren tayi duk wani cuku cukun tafiya saidae ba jirgin da zai je Lagos direct washe gari sai dae Kano ta yanke tafiya Kano d'in daga can sai ta hau na Lagos, a ranar baccin ta ragagge ne Saboda tsabar 6acin rai har gani tay daren yayi mata tsawo, Washe gari tana gama sallar Asuba ta hau shiri duk da bada wuri jirgin nasu zai tashi ba, Misalin k'arfe takwas na safiyar ta kira Senator take sanar dashi zancen komawar tata, tambayar dalilin tafiyar ta a yau yayi tace mashi hakanan ta canza shawara yace da yaushe jirgin nasu zai tashi ta fad'a mashi, ce mata yay in ta shirya kafin ta wuce ta same shi a G.r.a tace to, Misalin k'arfe tara da yan mintuna ta gama shirin ta tsaf cikin wani dandatsetsen leshi ruwan Madara da fulawowi maroon da golden brown, ba K'aramin had'uwa leshin yay ba idanun kansu zasu shaida maka tsadar shi don kuwa d'an dubu d'aruruwa ne, a da tazo da shirin fita taje wasu wurare kafin ta koma, gyale da jaka da takalma maroon ta saka ta fiddo wasu sarka da yan kunne da yan hannu na zinari ta saka ta fito a babbar macen ta, tana janye da d'an madaidaicin trolley d'in kayanta ta fito, Bedroom d'in Hajiya ta wuce bayan ta tura K'opar da yar sallama ta shiga, ganin Hajiyar bata cikin d'akin yasa ta kai idon ta wurin toilet nan ta gane tana ciki ta nufi bakin gado ta zauna, bada jimawa ba ta fito idanunta suka sauka akan Hajiya Maryam d'in ta nufo gadon itama ta zauna, kallonta tay ta gaishe da ita bayan ta amsa ganin tayi shiru yasa ta tambaye ta lafiya ta ganta cikin shiri da safe ko wani wuri zata ta girgiza mata kai kafin tace zata koma ne, d'an jimm Hajiya tay sai kuma tay d'an guntun murmushi tace "an 6ata maki rai shine kikai Fushi zaki tafi kenan" shiru bata ce mata komai ba idanunta na kallon k'asa, Hajiya ta k'ara cewa "shikenan bazan hana ki tafiya ba Allah ya tsare, kin yi Breakfast ne?" Girgiza mata kai tay tace in ta isa tayi ta gyad'a kai, d'an shiru sukai can ta mik'e ta kalli Hajiyar tace ta wuce, Addu'ar Allah ya tsare ta k'ara yi mata ta kama trolley d'in ta juya, har ta kusa k'opa Hajiya ta kira sunanta ta dakata ta juyo, "Kiji tsoron Allah, Kada soyayyar d'a ta tunzura ki kice zaki cutar da yarinyar can domin duk abunda kai ma d'an wani kaima za'ai ma naka ne, idan ranki ya 6aci Kada ki bari hankalin ki ya gushe, ki d'auki Al'amarin a matsayin Alkhairi sai kiga ya kasance hakan, tada hankalin ki shi zai taimaka wurin faruwar abunda kike gudu, ki gaida man Mazajena da K'awaye na" d'an jimm tay tana kallon ta kaman bazata tafin ba can ta furta mata ta gode ta juyo tana janye da trolley d'in ta fice,
Itama Fatuu a jiya bata yi wani baccin kirki ba wanda ta samu yake d'aukar ta ba wani mai nauyi bane gashi cike da mafarkin abunda ya faru tsakanin ta da Hajiya Maryam, kiran sallar farko na Asuba ta farka taje tayo Alwala, bayan ta fito ta zo ta kabbara raka'atanil fajr data gama ta d'aura da karatun Al'qur'ani har lokacin sallar Asuba yayi, bayan ta gama yin sallar kwance tay akan prayer mat d'in cikin sa'a bacci ya d'auketa, Misalin k'arfe tara saura ta farka jin jikinta duk ba dad'i yasa ta tafi toilet tayo wanka, bayan ta fito ta shirya cikin riga da wando, wandon skin tight ne bak'i sai rigar ta kai mata har gwiwa tana da gajeran hannuwa jikinta bak'i da fari ne, bata sa hula ba sai gashinta dake fake yayi tumm, bayan ta gama gado ta koma ta zauna tay tsuru, tana jin yunwa amman fargabar fita take sai kawai ta kai hannu ta d'auko wayar ta daga kan Bedside drawer ta fara dannata, bata dad'e da zama ba aka k'wank'wasa kopar ranta ya bata k'ilan Saude ce amman duk da haka saida taji tsoron bud'ewa, bayan ta bud'e taga Sauden ce suka gaisa harda ce mata tayi kyau inama Angonta na nan sai yafi ganin kyaun kwalliyar yar dariya tayi tace ita ai ba wata kwalliya tayi ba, daga baya tace mata ta fito tayi Breakfast gashi can ta kawo tace to, ce mata tayi ta fito suje taci a gabanta kaman jiya tay yar dariya tace mata zata ci Allah sannan ta fito,
Hajiya Maryam na fitowa sukai kacibus da Saude data dawo daga part d'in su Fatuu, gaishe da ita tay ta d'aga mata kai kawai ta mik'a mata trolley d'in tace ta biyo ta dashi, suna fitowa harabar gidan tay mata nuni da parking space da hannunta tace ta kai shi can ta je ta kirawo mata Tk tace mashi ya jirata anan, amsa mata da to Saude tay ta nufi parking space d'in tana tafiya tana waiwayen ta ganin ta nufi part d'in su Fatuu, Har Fatuu taje dining area d'in ta tuna da bata d'aukko cup da sauran abunda zata buk'ata ba ta juyo ta nufi Kitchen, hannunta ruk'e da plate da tea cup da spoon a saman shi ta fito zata koma dining, tana fitowa daga corridor zatai kwanar dining area taji an turo kopar parlon da sauri ta kai idonta suka shiga cikin na Hajiya Maryam, wani mummunan Fad'uwa gaban ta yay ba shiri ta saki abun hannunta nan take cup d'in yay tsalle ya fad'o ya d'aki tile ya tarwatse, tsaye tay cak ta zaro idanu zuciyar ta na wani irin harbawa ganin yadda Hajiya Maryam d'in ke jefa mata wani kallo fuskar ta ba d'igon annuri, daurewa kawai Fatuu ke yi amman jikinta har ya fara rawa daga ta ciki a yadda take ji tamkar ta watsa da gudu ta shige d'aki, cikin parlon ta k'araso tana tafiya a k'asaice ta tsaya a tsakiyar parlon, d'an d'aga murya tay tace ma Fatun ta k'araso wurinta ne ta d'an girgiza mata kai kafin ta fara tahowa cikin parlon a d'arare, a d'an nesa da ita ta tsaya murya na d'an rawa ta gaishe da ita tay mata banza still idanun ta na akanta ba alamun sauk'i a cikin su, cike da yarinta ta Fatuu tay tunanin wai ko don bata ce mata ta zauna ba yasa tay tsaye cike da k'arfin hali tace mata ta zauna aikuwa tamkar ta watsa mata wuta ta k'ank'ance ido a fusace tace "Samun wuri! Wato Ni zaki kalla ki ce ma in zauna! daga gidan ku aka kawo kujerun ko kuwa?" Da sauri ta girgiza mata kai a hankali tace tayi hak'uri....a zafafe ta amshe "Ke zan ce ma kiyi hak'uri ki tattara ki bar gidan nan don kuwa bai dace da ke ba baki samu kar6uwa ba, idan kuwa kika k'i to kuwa kin tattaro ma kan ki abunda bazaki iya d'auka ba, in ba ganganci irin naku ba k'auyawan mutane ke ko a mafarki kin isa kiyi kishi da d'iyata balle kuma a zahiri, wato har kuna da k'warin gwuiwa har haka ko? Fad'a man Asiri kukai ma shi don yaci gaba da zama dake ko??" a rud'e Fatuu ta hau girgiza mata kai aikuwa ta daka mata wata uwar tsawa "K'arya kike! dole Asiri ku kai mashi shi da Hajiya shiyasa har ta goyi bayan yaci gaba da zama dake" kuka Fatuu ta saka tana fad'in wllh su ba Asiri sukai masu ba Hajiya ce tasa yaci gaba da zama da ita, wani kallon rashin Arzik'i take bin ta da shi tun daga sama har k'asa, ada Haushin ta take ji yanzu kuwa abun sai ya juye zuwa tsana can ta buga wani uban tsoki ta d'aga yatsa tana nunata tace "To zan baki shawara tun cikin Arzik'i ki fita daga rayuwar shi, kice baki son cigaba da zama da shi idan ko ba haka ba to rayuwar ki zaki jefa a matsala don kuwa provided that am alive d'iyata bazatai kishi da ke ba da kowa ma, idan har baki d'auki shawarata ba kika fita daga rayuwar su ta lalama ba to zaki danasanin da har ki mutu bazaki daina ba don sai na salwantar da kaskantacciyar rayuwar ki, ta yadda ko kallon gidan nan aka baki shawarar kiyi sai kin zagi wanda ya baki shawarar balle ta kai ki ga cigaba da zama a cikin shi, kinsan Asirin ma mataki mataki ne iya nauyin jakar mutum iya girman wanda za'ai mashi, if u wise enough nasan zaki abunda ya dace" daga haka ta juya, har tayi d'an taku ta dakata ta juya ta kai hannu ta ruk'e kunnanta guda ta furta "idan kunne ya ji to gangar jiki ta tsira!!!" daga haka ta nufi k'opa ta fuce, Fatuu na ganin ta fita ta juya da gudo ta nufi Bedroom, Lokacin data fito bakin part d'in su a parking space ta hango Tk tsaye jikin Mota har ya saka trolley d'in nata ciki, da yatsa tay mashi alamar ya fito da Motar ta tsaya a wurin, yana tsayar da Motar ta bud'e baya ta shiga yaja suka fita su Officer na d'aga mata hannu a K'ok'arin su na su gaishe da ita don ta saba yi masu Alheri bata ba Tk Umarnin ya tsaya ba hakan yasa ya wuce, Suna zuwa gab da gidan su Fatuu ta nuna gidan tana tambayar Tk nan ne gidan su waccan yarinyar da aka kai gidan Hajiya ko yace mata eh, Umarnin ya tsaya a gaban gidan ta bashi, bayan ya tsaya ta bud'e kopar ta fito tace mashi tana zuwa, cike da isa ta nufi gidan Tk dake kallonta ta cikin glass ya girgiza kai a fili ya furta "Allah ya kad'e fitina", a bakin kopar shiga cikin gidan ta tsaya tana bin tsakar gidan da yake wayam ba kowa da kallo, Sallama tayi shiru ba'a amsa ba hakan yasa ta d'aga murya tace "ina masu gidan nan?" Amadu ne ya fito daga cikin d'akin shi yana sanye da jallabiya, wani kallon rashin Arziki ta bi shi dashi shima kallonta yake don ya ganeta, gaishe da ita yay bata amsa ba tace mashi ina take da alamun rashin Fahimta ya tambaye ta wa ya lura da yanayin ta kaman ba Arzik'i, "Kai da waye a gidan?" Ta tambaya ta yamutsa fuska, kafin ya bata amsa gwaggo ta fito daga cikin d'aki hannunta ruk'e da tsintsiya dama shara take shiyasa bata ji sallamar ta ba, juyawa Hajiya Maryam tay ta kalli Gwaggo data tsaya bakin k'opa tana kallon su don ta lura kaman ba lafiya ba,
"In k'araso ne?" Hajiya Maryam d'in ta tambaya tana kallon gwaggon shekeke, aje tsintsiyar da parker gwaggo tay ta nufo su, daga gaban Hajiyar ta tsaya da k'ak'alallen murmushi don tana kallon Fuskar ta tasan akwai matsala, gaishe da ita tay kaman bazata amsa ba sai kuma kaman an mata dole ta amsa daga haka gwaggo tayi shiru, d'an matsowa gaba tay yadda gwaggon zata jita da kyau, cikin isa ta fara Magana, "Mun ji abunda ya faru tsakanin d'an mu da jikar ki, to na zo inji cigaba da zaman su tare na minene? Taimakon ta yay to don mi zaku goyi bayan su cigaba da zama ko baku san yana da Mata bane?" Shiru gwaggo tay kanta k'asa abunda take ta fargaba game da Auren kenan don sarai tasan wacece Hajiya Maryam, cigaba tay "in dai kunsan halacci to bai kamata ku goyi baya ba, tun farko yakamata ace kun yi Magana akan ya saketa kaman yadda ku kai da shi, saidai kuma in dama akwae wata a k'asa kuna so kuyi amfani da damar don cimma wata manufa, to idan dai hakane wannan ba matsala bane ki fad'i man ko nawa kike so zan baki ta ruwan sanyi ki raba jikar ki da mijin Y'ata don bata kai tayi kishi da ita ba balle har ta zame mata matsala!" Yar ajiyar zuciya gwaggo ta sauke cikin kwantar da murya ta fara bata hak'uri tace ita wllh basu da wata manufa akan auren hasali ma itama bata goyi bayan auren ba tun da farko kawae don abun ya juye ne kuma Hajiya ta nuna tana so, a zafafe ta katseta da fad'in "tunda baki goyi baya ba sai kema ki nuna baki so, ba jikar ki bace ke kike da cikakken iko da ita!" D'an jim gwaggo tay yanayin fuskar ta ya sauya a sanyaye tace "Kiyi Hak'uri, Hajiya tana da girma ne a wuri na bazan iya musa mata ba" tamkar ta gaya mata magana taji a hasale tace "to kin mata biyayya don tana so mu kuma sauran dangi yanzu bamu so ba muyi Na'am da auren ba don haka bazamu kar6e ta ba sai ki maido abun ki in dai da gasken ba ki da wata manufa akan auren, bijire ma hakan daidai yake da bijirema Farincikin kowannan ku, zan iya k'arar da duk wani abun da na Mallaka akan bijirema hakan don kuwa ba zan ta6a zuba ido wata kaskantatta ta zama shamaki ga farincikin Y'ata, tana son Mijinta shima kuma yana son ta don haka basu buk'atar wata ta shigo rayuwar su, a shawarce sai kiyi abunda ya dace" ta k'are Maganar tana jinjina kai had'i da kanne ido,
ba K'aramin 6aci ran Amadu yay ba ganin yadda take ta gaya ma Mahaifiyar shi Magana daurewa kawai yake yana danne zuciyar shi, tana zuwa ga6ar data kira Fatuu da Kaskantatta yaji bai iya jurewa ya matso inda suke rai 6ace yace "Hajiya gaskiya ita ba kaskantatta bace, don tana talaka hakan ba yana nufin bata da galihu ba, a wurin Ubangiji duk d'aya muke wanda yafi tsoron shi yafi bauta mashi shi ya fi ba wai mai kud'i ba ko nasaba kawai mutane ne ke bambantawa, in Allah yayi mutum mai kud'i ba hakan na nufin yafi son shi ba ko rayuwar shi tafi amfani ba haka talaka ma ba yana nufin Allah bai son shi ba ko rayuwar shi bata da amfani, ki sani gaba d'ayan mu Allah yayi mu a yadda muke ne don mu bauta mashi don haka gaba d'ayan mu rayuwar kowa talaka ko mai kud'i nada amfani, kuma Maganar aure ai bamu muka sa ya aureta ba, hasali ma bamu san yadda akai ba saidai muka ji zai aureta balle kice ko dama da niyya, sannan Maganar zaman su ma bamu muka rok'a ba tun farko shi ya k'i sakin ta aka zo kuma aka buk'aci zasu ci gaba da zama tare Saboda biyayyar mu ga wadda ta buk'ata muka amince, in zaki ga laifin mu kan hakan shi miyasa bazaki ga laifin shi ba da tun lokacin bai bijire ya nuna bazai cigaba da zama da ita ba, mi yasa tun farko bai saketa ba kaman yadda akai dashi ba, Maganar hallaci kuma ai shi muka yi, ya aureta don ya taimaketa daga baya kuma an buk'aci suci gaba da zama a tare in muka k'i ai kinga mun yi butulci kenan amincewar da mukai kuma hallaci mu kai domin d'an halak shi yake maida Alkhairi da Alkhairi, Yanzu tunda baku amince da auren ba duk miye abun zuwa da tada jijiyar wuya kusa ya sake ta mana........! A fusace ta kai hannu zata wanka mashi mari ya goce Fuskar shi a tamke yana huci nan da nan Fuskar shi tay jajir kaman an watsa jini abunka da Fari, itama Hajiya Maryam d'in huci take tana mashi wani kallo mai cike da tsantsar 6acin rai zuciyarta tana boiling da burning a lokaci guda, cikin wata irin murya ta nuna kanta da yatsa manuni tace "ni kake gaya ma magana haka!!!" D'an tura baki yay yace "ni ba Magana na gaya maki ba saidai in ke kika d'auka haka amman duk abunda na fad'a ai daidai ne, ikon baro gidan nata na a hannun ku sai ku sa ta......." Tsawa gwaggo ta kwatsa mashi cikin harshen fulatanci tace ya bar wurin, wani kalan murmushin yaro bai san wuta ba sai ya taka Hajiya Maryam tayi tace "ki k'yale shi, yay man duk rashin kunyar da ya iya ai gada yay tun daga tushe, kowa ya san baku da kunya ai, bama iya hakan kuka tsaya ba gashi nan kun addabi K'asar mu" idonta da suka sauya kala akan shi tay Maganar nan da nan idanun gwaggo suka ciko da k'walla, nuna shi tay da yatsa tace "Ni ba sa'ar yin ka bace, kaff dangin ku ma ba sa'ar yi na, idan kaci gaba da yi man rashin kunya You will definitely find ur self behind BARS....!!!" A tsiyace ta furta Kalmar Bars d'in ta cize hak'ora, Shiru yay bai ce komai ba gwaggo na girgiza mashi kai alamar kar ya tanka sai huttai yake kamar wanda yay gudu da gani dai ba k'aramar zuciya gare shi ba, juyawa tay kan gwaggo ta had'e yatsanta biyu suna making sound tace "Zan yi komae don Farincikin Y'ata in kuma tabbatar bata samu wata matsala ba in kin so zaki iya yin hakan ga Jikar ki......." Tana kaiwa nan ta juya cike da tafiyar isa ta nufi hanyar k'opa ta fice........ASM Bk2069
~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
.........Tana fitowa daga cikin gidan tay ma Tk dake cikin Mota alama da hannunta nan take ya fahimci mi hakan ke nufi ya bud'e kopar Motar da sauri ya fito, bud'e mata K'opar bayan yay tana zuwa ta shige ya maida kopar ya rufe mata ya d'an d'age gira tare da bud'a ido ya koma yaja suka tafi, sai faman jinjina kai take tana cije lower lip d'in ta tana d'an huci,
Tana fita Amadu ya matsa gaban gwaggo ganin yadda idanunta sukai ja shima har lokacin ran shi a 6ace yake, kallon shi tay tace miyasa yayi abunda yayi ma Hajiya Maryam, cikin 6acin rai yace "to gwaggo sai mu zuba mata ido taci mana mutunci son ranta, miye laifin mu a ciki ko kuwa don muna talakawa" yar ajiyar zuciya ta sauke "kar ka manta ita d'in ko wacece, ko ba komai Mutanen nan nada k'ima da daraja a idon mu hakan da kayi mata bai kamata ba don kamar rashin kunyan ne, duk abunda ta fad'a ta fad'a ne cikin 6acin rai don tana ganin an mata ba daidai ba" dakata tay tana numfasawa idanunta na kallon gefe shi kuma nashi na akan ta, cigaba tay "Wllh abunda nike ta fargabar faruwar shi kenan, nasan dole irin hakan ya biyo baya shiyasa naso tun farko ace an tuntu6e su sun san da Maganar a nemi amincewar su tukun...." Dakatawa ta k'ara yi ta d'age ido sama, ganin yadda duk ta damu yasa Amadu cewa "Kar ki wani saka ma kan ki damuwa, tunda Hajiya tun farko ita ta nuna abar mata komai nasan in sha Allah zatayi abunda ya dace komai na d'an lokaci ne zaki ga ya wuce" girgiza kai tay ba tare data kalle shi ba tace dole tayi wani abu don ita bazata so silar hakan ace an samu rashin Fahimta ba yanzu na Hajiya Maryam d'in aka gani ba'a san ya sauran Yan'uwan nashi suma zasu d'auki Al'amarin balle kuma ita Matar tashi, tambayar ta yay to mi zata yi ta bashi amsa da abunda ya dace daga haka ta juya ta nufi d'aki ya bi bayanta yana ce mata ta kwantar da hankalinta ba sai tace zatayi wani abu ba yasan Hajiya bazata bari a cutar da Fatuu ba, tana shiga d'akin ta nufi gado ta zauna a baki Amadun ma ya shigo ya zauna gefen ta yaci gaba da rarrashin ta kan kar tace zata yi wani abu don anzo anyi masu barazana su yi Addu'a kawae, ce mashi tay to kawae daga baya da ya ga ta d'an saki ranta ya tashi ya tafi, Zaune tay a wurin tana tunanin abunda ya kamata tayi don ganin Auren ya rabu, k'arshe ta yanke zuwa ta samu Hajiya ta rok'e ta kawae a hak'ura da Auran, tana son ta kira Fatun taji halin da take ciki amman bata so taji abunda hankalin ta zai k'ara tashi wata zuciyar ta raya mata tunda ita bata kira ta ba k'ilan ba abunda ya faru da ita don Hajiya bazata bari ayi mata wani abu ba da wannan tunanin taji hankalin ta ya d'an kwanta.
Bayan sun iso G.r.a sun shiga cikin gidan a gaban kopar shiga ya parker, bayan ta bud'e ta fito ta nufi ciki, Parlon Senator ta wuce wanda Had'add'an gaske ne ya tsaru ta samu wuri ta zauna, ganin bai a ciki yasata kiran shi ta sanar mashi ta iso, bada dad'ewa ba ya fito yana sanye da farar Jallabiya tun bayan daya dawo daga Masallaci ya koma ya kwanta zuwanta ne yanzu ya taso shi, a kujerar gefen ta ya Zauna Fuskar shi a sake ta gaishe dashi ya amsa daga haka tay shiru kanta a k'asa tana kallon Carpet 6acin rai bayyane akan fuskar ta, tambayar ta yayi tayi breakfast ne tace mashi a'a sai ta isa yace bari dai a kawo mata tayi anan, bata ce komai ba ya matsa can daga gefen kujerar inda landline take aje saman wani table, kira yay ya bada Umarnin akawo Breakfast, after some minutes sai ga wani cook ya shigo hannun shi ruk'e da babban tray dama aikin shi kenan girka ma Senator d'in Abinci in yazo bada iyalin shi ba, har zai kai inda dining table yake Senator yace mashi ya kawo nan, gaishe da Hajiya Maryam yay ta amsa k'asa k'asa ba tare da ta kalle shi ba ya d'aura a saman c-table Senator yace ya ja mata shi gabanta, saida yayi mata Magana sannan ta fara ci shi kuma ya fara daddana wayar shi da ya fito da ita, bata wani ci sosae ba ta cire hannunta ganin haka yasa Senator yi mata magana tace mashi ta k'oshi, k'ara kiran cook d'in yay yazo ya kwashe kayan, shiru suka yi Senator na cigaba da danna wayar can ya d'ago ya ajiye ta agefen shi yay yar ajiyar zuciya a nutse ya fara mata Magana yace miyasa zata tafi, kallon shi tay tace mashi ba komai kawae ta canza ra'ayi ne, shiru yayi yana kallon ta da d'an murmushi ita kuma idanunta na k'asa tana kallon Carpet har lokaci fuskar ta ba annuri,
cigaba yay "nasan don abunda ya faru ne, ina son ki kwantar da hankalin ki abi komai a sannu sannan ayi fatan hakan ya zama Alkhairi kaman yadda Hajiya ta fad'a bamu san mi Allah ya 6oye a tattare da Al'amarin ba" kallon shi tay cikin 6acin rai tace "Kenan kaima Yaya goyon bayan auren kake?" d'an murmushi yay yace mata kawae yayi nazarin Maganar Hajiya ne shiyasa, Fuska a yamutse tace "Yanzu shikenan ya nuna bamu da iko dashi ya yi gaban kan shi sai kuma a k'yale shi hakan Yaya ai cin Fuska ne, gaskiya dole mu nuna mashi ba a komai yake da iko da kan shi ba kawai asa ya saketa" ta k'arasa tana d'an Jujjuya kai, numfasawa yay yace "ni ina ganin hukuncin da Hajiya ta yanke akan shi ya nuna ana da iko dashi, yaje yayi aure ba tare da sanin mu da niyyar zai saki Yarinyar kinga in aka sa ya sake ta shine yay abunda ran shi ke so amman matsa mashi ya zauna da itan hakan zai sa dangin yarinyar su san ana da iko dashi kuma mu ba k'ananun mutane bane, sakin ta kuma hakan gaskiya ina ganin zai zama k'aranta" idanun ta ne suka ciko da k'walla cikin karyayyar murya ta fara fad'in gaskiya ita bata goyi bayan yaci gaba da zama da ita ba duka yaushe yayi aure kuma in ma Auren zai k'ara wannan ai bata dace da shi ba ba sa'ar auren shi bace, shiru Senator yay still da d'an murmushi akan Face d'in shi don yasan dalilin da yasa duk take wad'annan abubuwan, rarrashin ta ya shiga yi yana nusar da ita aikuwa sai tasa mashi kuka tana fad'in shikenan ba wanda zai yi tunanin halin da Fanan zata iya shiga duk sun goyi bayan 6are sun za6i faranta mata da mi ake so Fanan taji ne ko don suna tunanin bazata haihu bane, nuna mata yay bai ji dad'in wannan Maganar da tayi ba sam ai yayi tunanin Fanan ta su ce da ta haihu da kar ta haihu hakan ba abun damuwa bane a gare su kuma don ance tana da matsala ai hakan ba yana nufin bazata haihu ba kawai yana son ta gane shi Al'amarin irin wannan in Allah ya kawo kamata yay a kar6a ai fatan ya zama Alkhairi ba kamar da Hajiya ta nuna tana so sai suyi mata biyayya su bi da Addu'a, hak'uri ta bashi kan Maganar da ta yin ya k'ara lallashin ta daga baya sukai sallama ta mik'e shima ya tashi don ya rakata. Bayan ya dawo inda ya tashi ya koma ya zauna ya d'auki wayar shi ya shiga kiran Haisam, picking yay tare da yin yar sallama Mahaifin nashi ya amsa mashi, bayan ya gaida shi yace mashi sun ji abunda ya aikata ya kyauta hakan ya nuna masu basu da amfani a wurin shi, hak'uri ya bashi yace mashi yayi don taimako ne, ce mashi yay to miyasa ya k'i sakin ta kaman yadda akai dashi har abu ya shiga tsakanin su, shiru yay bai ce mashi komai, sigh Senator yay yace mashi yana son ta kenan dama shiyasa har hakan ta faru don yaci gaba da zama da ita, Slowly yace mashi bada niyya bane kuma Hajiya ce tasa yaci gaba da zama da ita, d'an guntun murmushi Senator yay yace "Kenan baka son ta?" Shiru Haisam d'in yay, da d'an d'aga murya yace ya bud'e baki yay mashi magana kaman yadda yake mashi bai kira shi don yaja mashi aji ba, in bai son ta ya fad'i a raba su kowa ya huta, har saida Haisam d'in yay d'an guntun murmushi jin abunda yace dama ya saba ce mashi hakan in yana jira yay mashi magana,
"Tunda Hajiya na so zan ci gaba da zama da ita" d'an ta6e baki Senator yay da murmushi irin na ka gane Mutum ba gaskiya ya fad'a maka ba, "ita Daughter ka sanar da ita ne?" Ya tambaya yace mashi a'a,