Auran bazawara complete by ummuh hairan - Chapter 6
Auran bazawara complete by ummuh hairan Chapter 6: Auran bazawara complete by ummuh hairan Chapter 6. Ita kuwa qoqarin janyewa takeyi tana fadin “Naseer…
4,242 words
Ita kuwa qoqarin janyewa takeyi tana fadin “Naseer don Allah ka bari kagafa a gda muke kadasu Hajiya sujika..." Rufe mata baki yayi da hannunsa yace “to saime ne matata ce ke ni mijinki ne kuma dama ai don ayi wani abun akayi auran" dora bakinsa yayi saman nata ta janye ta miqe daga ruwan ta bude qofa da sauri ta fice daga bathroom din ya bita da kallo yana murmushi yace “zakizo hannu ne sai kinyi bayani da Hausa Allah ya hadamu anjima" Wanka yayi ya fito ya tarar da ita ta tayar da sallah yasa rigarsa ya dauki wayarsa ya fice da sauri ya nufi masallacin dake kusa da gdajen nasu, a masallacin suka hadu da iyayen nasu da yayansa Jafar yace “amma yau baa gda ka kwanaba ko nass naje inata buganka qofa mu fito masallaci naji shiru"
Shafa kansa yayi ya harareshi tare da satar kallon Abba yace “eh a gurin matata na kwana" kallonsa Abba yayi yace “ya jikin nata?" Shafa kansa yayi yace “da sauqi sosai na barota ma tana sallah" basu kuma mgn ba suka tayar da sallah bayan sun idar suka fita daga masallacin amma banda Naseer ya jima yana azkar yana nemawa matarsa abar qaunarsa lfy me dorewa tare da neman Allah yayi musu maganin duk wani dazai zama matsala a cikin zaman aurensu. Bai koma gdansu Nafeesah ba gdansu ya shiga inda yana shiga dakinsa ya nufa, ana ya tarar da ummah mahaifiyarsa yana shiga ta miqe ta nufosa a zafafe tsayawa yayi yana kallonta ta daga hannu ta sharara masa mari tare da damqar kwalar rigarsa tace “Naseer meyasa bakajin mgn ne meyasa bakada kunya dan ubanka kanka aka fara aure waima a gdan ubanwa ka kwana" bai damu da riqon da tayi masa ba yace “to waike ummah Ina ruwanki danine matata ce batada lfy shine naje na kwana a gurinta ko nayi laifi ne".........
~_Sai anjimanku yasin bacci nakeji over ina typing idona na lumshewa_~
More comments More typing
*Mrs Dr M.A...✍🏻* [4/22, 9:58 AM] UMMUH HAIRAN CE...✍🏻: *_A B_*
*17*
Numfashi taja ta share hawayen idonta ta miqe ta dauki mayafinta zata yafa Aunty Amina ta warceshi tace ke dama abinda take hadani dake kenan bakison gsky kin wani zari mayafi zaki fita to mijinki yace komai dare kada na barki ki fita ki jirashi zaizo ya daukeki" komawa tayi ta zauna dabar tana huci ta hade kanta da gwiwa tana sauke ajiyar zuciya ta rasa meyasa danginta suka kasa hasko abinda take hangowa ta lura da tarin qyamatar da Ummah mahaifiyar Naseer takeyiwa tarayyarta da danta bayan hakama ita a kankin kanta bataga dacewar gamayyarta da Naseer ba. Haka Aunty Amina ta rinqa rarrashinta tana nusar da ita amfani da alfanun aurenta da Naseer amma ta kasa hangowa jinta kawai takeyi, sai shidda da rabi ya dawo gdan yazo ya dauketa daga yanayin yanda taga fuskarsa tasan akwai matsala amma batama saurareshi ba bare ta tambayeshi haka sukayita tafiya yana huci har suka shiga unguwar tasu yaja yayi parking a wani guri ya dago ya zuba Mata manyan idanunsa da suka kada sukayi jawur yana kallon yanayinta yanajin wata qaunarta da tausayinta na fusgarsa yace.
“Zan batawa uban kowa rai akan mgnr aurena dake Nafeesah wlh zanyi rashin mutuncin da baa tabayin ba a family dinmu kowanne munafiki zai gane kurensa babu wanda ya isa yasani nayi abinda yake ba raayina ba" keda bakya gurin idan kin tanka masa Nafeesah ta tanka saima cigaba da tayi da danna wayarta saboda iya wuya take dashi zata iya zaginsa ma nan gaba kadan, fuzge wayar hannunta yace cikin qaraji “wannan matsalar fah bani kadai ta shafa ba hardake ki bani hankalinki mu nemo mafita kafin abin ya rikice Feesah tun jiya Ummah take kuka wai an cuceta an hadani dake kiji wani shirme irin naku na Mata kamar ita zata zaunamin dake to wlh ni babu abinda ya dameni narantse da Allah yau saina saukewa kowa aljanun kansa harni zaayiwa iskanci ita uban waye yayi Mata d ba Wanda takeso ta auraba saini zata rainamin wayo saboda tanayimin kallon yaro har wani tana cewa Idan na kusanceki bata yafemin ba to wlh saidai ta tsinemin sex dake yanzu na fara"
Yamutsa fuska tayi tace “kaine yadama ni babu wani abuda ya shafeni ai dama tsuntsun da yaja ruwa shi ruwa kanyiwa dukan tsiya dama yana daya daga cikin abinda yasa nace banson wannan mahaukacin auran amma kaida su Abba kuka nace aiga irinta nan dama yau nasan cewa mahaifiyarka bata qaunata Naseer kaine kasani yau, to bari kaji na fada maka bance inason dantaba liqamin kai akayi a dole saboda haka babu wanda ya Isa ya qetaramin kara ban karya ba kuma da take cewa kada ka kusanceni aini gata tayimin ubanme zanyi dakai wanne dadi zanji a abinda na wankeshi tunba jijiya a cikinsa" Sosai kalamanta sukayiwa qwanyarsa lugude bawai wanda ta fada akan mahaifiyar sa ne suka bata masa raiba aa wadanda tayi akansa sune suka caccaki zuciyarsa wai me zatayi dashi? Dukan sitiyarin yayi ya danna mata wuta yaja da gudu ya qarasa gaban gdansu Nafeesah ya danna horn megadin yazo ya bude masa ya shiga yanayin parking ya zare key dinta ya cilla mata yace.
“Na gde Nafeesah na gde tukuici qaunar dana nuna miki kenan Abu daya dazan fada miki shin iya wuya muna jorne babu abinda zaisa ki taba samun abinda kikeso na rabuwa daga gareni dukkanku zan iya daku" banko qofar motar yayi da qarfi ya juya ya nufi get din ya fice ya nufi nasu gdan qwafa tayi ta bude motar ta fito tanajan qafarta da tayi mata tsami ta nufi cikin gdan. Koda ta shiga gdan tana ganin su Hajiya da Mama a parlour harda Hajiya babba mahaifiyar su Aunty Amina a parlourn amma babu wanda ya samu arziqin tayi masa mgn ta haura saman da sauri ta kulle qofar ta fada bathroom saboda mugun zafin da takeji saida ta qara gasa gabanta daya kumbura sosai saboda gurzar azabar da taci har yanzu idan ta tuna wai yau yaron data rainawa wayo Naseer shine ya kwanta da ita har yakeyi mata ihu wai dadi kawai sai taji wani hawaye ya zubo mata na takaici.
Fitowa tayi tasa kayan baccinta ta dauki magungunan ta tasha sannan ta kwanta ta jima a kwance kafin ta samu bacci yazo ya dauketa, cikin baccin taji kamar ana tabata ta bude idonta da sauri gabanta ya fadi ta miqe zaune da sauri tace “ A'UZUBILLAHI" jikinta yana rawa saboda ganin Anwar yau a siffarsa ya tsaya akanta yace “ana neman rabani dake saboda wannan dan tatsitsin yaron haihuwar jiya abinda basu saniba shine su sunyi sammako ne nikuwa a tafe na kwana kinyi ganganci Nafeesah da kika bari qanqanin yaronnan yayimin wasa a gonata tabbas kinyi ganganci kuma zaki gane kurenki bazanyi miki komai ba amma zakigani sakamakon cin amanar dana baki Nafeesah wacce dama na hanaki ina kusantarki an hanani na hqr na sanya miki sha'awar jima'i na hadaki da wanda zaike rage miki zafi amma duk da haka saida kika ha'inceni kika bari aka aura miki yaronnan to dagake harshi zaku gane kunyi kuskure" Hannu yakai zai kamota tayi saurin janyewa shima ya janye hannunsa ya saki wata qara ya bace bat daidai lkcn data saki wata qara data tashi kowa dake gdan sukayo dakinta suna shigowa suka tarar da ita a qarshen gadon sai rawar jiki takeyi idanunta sunyo waje tanata riqe wuyanta tana jijjiga kanta..........
_Marnege wlh_
More comments More typing
*Mrs Dr M.A...✍🏻* [4/22, 9:58 AM] UMMUH HAIRAN CE...✍🏻: *_A B_*
*19*
Sakinsa tayi cike da mugun mamaki wai ita Naseer yake kallo yake fadawa a gurin Mata ya kwana tab lallai yaron ya tafaso dole ta dauki mataki kafin ya qone idan ba hakaba saita kirashi yace bazai zoba shigewa yayi cikin bedroom dinsa ya banko qofar yana mita ya fada gadonsa ya kwanta ya rungume pillow yana tunano kwanansa na jiya a jikin Feesansa kwanan dabai tabayin irinsa ba a rayuwarsa.
Feesah kuwa bayan fitarsa ta dade a zaune saman sallaya tana mamakin tsageranci irinna Naseer amma bata isa tace zata tanka ba ita gaba dayansa tsoro yake bata ta lura neman zautata yakeyi idan ta biyewa halinsa gefe guda kuma abinda ya faru a jiye shine yake dawo mata tsakaninta da Anwar. Haka ta miqe daqyar ta koma kan gadonta ta kwanta taja bargo ta rufe jikinta bacci ya dauketa me dadi bata tashi ba sai goma da rabi tayi wanka ta fita parlourn a kunyace takeyin komai iyayen nata suna binta da kallon mamakin yanda duk ta tsargi kanta tadaiqi basu damar su fahimci wani abu amma duk da haka saida Hajiya juwaira ta fahimci wani abu ya faru tsakaninsu duba da yanda take taka qafarta da qarfi ita wai a dole saita boye tsamin da gurin yayi mata.
Zama tayi a parlourn tayi tagumi ta tusa kofin tea din a gabanta ta kasa sha saboda zafin da zuciyarta takeyi mata gabanta ya fadi saboda tunawa da tayi da cewa sati biyu kafin auranta da Naseer wani abu ya shiga tsakaninta da Habeeb duk da tayi period a bayan hakan amma to meye matsayin aurenta da Naseer yanzu? Miqewa tayi da sauri ta shigs dakinta ta dauki wayarta ta kira number Maryam ta daga tace “Kinsan an daura aurena da Naseer kuwa?" Wani ihu ta saki tare da kabbara tace “yaushe wannan abin arziqin ya faru?" Numfashi taja muryarta na rawa tace “kwana hudu kenan amma ni abinda yake damuna sati biyu kafin aurena da Naseer munyi tarayya da Habeeb meye matsayin aurenmu yanzu?" Shiru Maryam tayi na dan wani lkc sannan tace “kinyi period?" Amsawa tayi da eh nayi period sau daya kuma ai jini biyu shine istibra'ih to shima wannan tsageran yaron ya kusanceni jiya yanzu ya kenan?"
~_Kar Wanda yacemin komai ehee_~
More comments More typing
*Mrs Dr M.A...✍🏻* [4/22, 9:58 AM] UMMUH HAIRAN CE...✍🏻: *_A B_*
*21*
Kallon juna sukashi shida Mama yayi wani ihu ya rungumeta yace “kingani ko kinga rabo ko Mama ciki fah Mama cikina ne a jikin My millon Allah na gde maka da qananun shekaruna ka azurtani da mata gashi harda ciki" sakin Mama yayi da tayi mutuwar tsaye saboda tsananin mamaki tanabinsa da kallon mamakin yaron “shi wannan dan abun shine har yayiwa mace ciki?" Ta tambayi zuciyarta cikin mamaki wai Nafeesah take dauke da cikin Naseer abunda ta kasa samun da sauran mazan data aura dama ashe rabon na Naseer dinne.
Shiga yayi dakin ya tarar da ita tana bacci ya zuba mata ido yana kallonta sai yanzun ya gano hasken data qara sosai ta rame kuma murmushi yayi yace “zakiyi qiba kwananan zanyi miki kiwon da baa tabayi miki ba" qarasawa yayi gabanta ya sunkuya ya daga rigarta yayi kissing cikinta yana jin wani farin ciki a ransa, turo qofar Mama tayi yayi saurin janyewa ya tsaya sosai kallonsa Mama tayi tace “amma Naseer kayi shiru da bakinka kada ka fadi a cikin gda tunda kun kusa tarewa kasan abin mgn ba kadan gareshi ba" kallon Mama yayi yace “au Mama yanzu saboda nayiwa Mata ciki sai ayi surutu?" Ji Mama tayi kamar qasa ta tsage ta shige amma dole tayi masa bayani yanda zai gane.
Bayani tayi masa sosai har saida taga ya gamsu sannan ta qyaleshi ya fita ya siyo mata magunguna ya dawo kafinnan Feesah ta tashi tana zaune ya matsa da sauri ya riqo hannunta ta janye yayi murmushi yace “kada dana yaga kina gudun babansa fa akwai matsala kinsani ko" shareshi tayi ya zauna kusa da ita ya dauko fruit ya fara bare mata ayaba yana bata da farko qinci tayi saida taga ya hade rai yana neman fashewa sannan ta karba yana bata yana murmushi ya dauko Apple ya bata taci kadan ta kawar da kanta yace “kada ki horamin baby na da yunwa don Allah nafison ki haifamin qaton da wanda da anganshi ansan yaron nan yana qoqari kuma yana kaiwa har maqogoro" Harararsa tayi yayi dariya yace “Allah cikine dake sati biyu dayan kwanaki kai likita kwai jarababbe wai har ya gano abinda akayisa a sirr..." Juyowa yayi ga mamakinsa kuka takeyi tana girgiza kai tana fadin innanillahi wa innah ilaihirraji'un ciki kuma ciki Naseer wanne irin ciki kuma ana zaune qlau" kallonta yakeyi baki a sake yace “ciki na haihuwa kuma na sunnah" gabanta ya sake faduwa tace “aa Naseer kada muyi haka dakai wlh banaso Allah ya kiyaye kaima nawa kake rainonka fa aka bani sannan kacemin wani ciki aa nikam banaso wlh tun muna mutunta juna ka canza zancenka bazan iya haihuwa da yaro kamarka b..."
Rufe mata baki yayi yace “kada kuma ki shegantamin ciki wlh wannan kadai idan kinada hankali ya isheki ishara ki gane cewa ba yawan shekaru ne girma ba kinga cikinnan na jikinki Nafeesah wlh ko ciwon kai yayi kece saboda haka ki kiyayeshi ki tsaremin shi sonsa nakeyi fiye da yanda nakeson kaina" Ficewa yayi daga dakin ya nufi motarsa ya zuba kayan nasu a ciki Mama ta kuma diban wasu ta fita dasu ya dawo ya matsa ya kamota ta miqe tare da tureshi ta nufi hanyar fita yabita a baya yana mata fadanci da bambadanci takaici ya cikata sosai, ta rasa irin Naseer da baya da zuciya akan duk abinda ya shafeta baya ta bude ta shiga yana zuwa ya tsaya yace “gsky baki isaba fitowa zakiyi aini ba drivenki bane" kwanciya tayi ma a bayan dole ya qyaleta Mama ta shiga gaban sunajin Jan zuciyarta alamar kuka takeyi shareta sukayi har sukaje gda tun kafin ya gama daidaita parking dinsa ta bude ta fice ta shiga gdan, binta yayi da sauri yana Kiran sunanta har yana tuntube amma tamaqi sauraronsa dakinta ta shige ta datse da key bugun duniya taqi bude masa.
Dole ya haqura ya qyaleta ya juya ya fita nufi gdan yana shiga a parlourn ya tarar da Ummansa kasancewar yar tsama sukeyi jam'u yayi musu sannu zai wucce ta daga murya tace “Kai nake jira Naseer" sake tsare gda yayi yace “to lfy?" Yanda yayi mgnr yayi mugun bata mamaki tace “zan samu arziqin ka zauna muyi mgn ko kuwa a tsaye zaka tsayamin akaina kamar ubana?" Jan qafarsa yayi kamar bazai takaba ya zauna a hannun kujerar ya fito da wayarsa yana dannawa yace “inajinki" Takaici ne ya cika Ummah ta yarda har zuciyarta an gama mata dada an shanye kurwarsa dubi yanda yake mata mgn a gadarance kanar wani ubanta dan da abaya duk tsagerancinsa yana daga mata qafa amma Wai yanzu shine yakeyi mata abu isa² dole ta dauki mataki akan Hayatu da zuri'arsa bazasu rabani da dana ba, dubanta yayi yace “inason zan shiga ciki idan bakida abin fada nasan dai bai wucce kice Ina naje ba to kafinma ki tambaya bari na fada miki matata ce batada lfy mukaje asibiti ashe ma qaruwa muka samu cikine da ita kin kusa daukan jika"
Wata zabura tayi ta miqe ta qunduma ashar tace “Billahil lazi qaryane Naseer ciki kai yanzu dan ubanka yaushe ma ka tafasa da har zaka qone inama abin yake dahar zakace wani wai matarka cikine da ita ina matar take? Tsohuwar guzumar kaini banma yarda cikinka bane wannan kawai dai liqa maka akeson yi ni dama nasan da wata a qasa cutata akeson yi aka qaqaba maka auren wannan tsohuwar yarinyar kusan saata" miqewa yayi yace “haba haba Ummah ki rinqa tsoron Allah ai kema saida kika tsufa kika auri Abbanmu don Moddibo ya fadamin rasa me aurenki kikayi a Adamawa har saida kikayi shekara talatin sannan aka bawa Abba sadakarki balle Nafeesah yarinya qarama ni wlh ganima nakeyi batan lissafi kukayi na girmi Nafeesah nesa ba kusa ba, ke komadai menene nidai inason matata kuma wlh zan sabawa kowa akanta sannan dole ne idan anason a zauna lfy dani a daina yimin shisshigi akan iyalina domin yanzu lkcna na Nafeesah ne da dan tayin dana dake cikinta yauwa" yana fadin haka ya juya nufi dakinsa kare da waya a kunnensa yace “My millon ina sha'awarki sosai Allah yau bazan iya bacci..."
Iya abinda taji kenan ta toshe kunnenta saboda kalaman Naseer din sun wucce tunaninta, miqewa tayi tana zagaya dakin zuciyarta cunkushe da damuwa da kuma tunanin yanda zatayi da Naseer duk inda ta biyo masa zillewa yakeyi, wayarta ta wawura ta danna number aminiyarta tace “Talatu akwai matsala fah duk inda kike tunanin tsagerancin yaron nan Naseer ya wucce haka wlh an busar masa da zuciya baya ganin kowa da gashi sai yarinyar nan bansan daya zanzo masa da mgnr auran Lateefah ba bama zai taba yarda ba nasani balle kuma babansa" wata muguwar ashar Hajiya Talatu ta saki tace “wlh baki isaba Nafi dolene kiyi amfani da power ki ta uwa ki tursasawa Naseer ya auri yata Lateefah wato bakeson bacin ran danki nikuma tawa yar ta mutu ko? To baku isaba wlh" Qasa Ummah tayi da muryarta tace “ba haka nake nufi ba Talatu kaina ya kulle bakiga diban albarkar da yaron nan yayimin ba harda cemin wai nima tsohuwa babansa ya aureni garama Nafeesah ita yarinya ce wani kayan takaici duk da dokar da malam ya bani ta kada ya kusanci yarinyar nan nima na gindaya masa dan banzan yaron nan baiji ba saida ya kusanceta yanzu yake fadamin wai asibiti sukaje cikine da ita..."
Salati Talatu tasaka ta fashe da kuka tace “shikenan ta faru ta qare kinyi sake danki ya zama ba naki ba kinajin abinda malam yace laqaninta a jikinta yake indai ya kusanceta to yariga ya gama mallakuwa sai yanda tayi dashi amma dake ke wawuya ce baki kishin danki kika sake har ya kusanceta, Uhmmm! Hmmm!! To nidai koma menene indai akwai malamai da bokaye a duniya ko zanyi yawo babu dan kamfai zan tsayawa yata ta samu cikon burinta wato Naseer kuma saina wulaqanta Nafeesah a duniya tunda ta shiga gonar yata" Kit ta kashe wayar tabar Ummah da “hello! Hello!! Talatu..." Sauke wayar tayi ta zabura ta miqe tana zagaya parlourn ta koma ta zauna tace “qarya kake Naseer ni na haifeka bakai ka haifeni ba dole nima kayimin biyayya" miqewa tayi ta shiga dakinta ta dauki mayafinta ta fito ta nufi gdansu Nafeesah, tun daga qofar parlourn ta fara kiran sunan Hajiyan Nafeesah tana fadin “Zuwairah kike ko Juwairah to koma me kike bai dameni ba kashedi nazo nayi miki tun dare baiyi miki ba ki koma gurin bokanki kice ya kwance asirin da yayiwa dana wlh ban haifawa guzumar yarki da taqi zaman aure miji ba Naseer yafi qarfin auran bazawara na riga nayi masa mata kuma ki fadawa yarki ta nemawa shegen cikinta uba amna ni dana burarsa batayi qwarin da zaiyiwa mace ciki ba yaushe ma aka haifi Naseer din da har yayi balagar da zaiyiwa wannan tsohuwar yar taki ciki?"
Hajiya ce da take saukowa ta cafe da cewa “Haba Nafi ai duk abin baikai na hakaba da Naseer da Nafeesah duka yayanmu ne kuma dukkansu ikonmu ne ba dole akayiwa danki ya auri Nafeesah ba hasalima ita akayiwa dole duk da itace take da yancin zabar mijin aure kasancewarta bazawara..." Mama ce ta cafke da cewa. “Kuma da kike wannan babatun waye ya gaya miki baikai ba aini tun ba yau ba nasan danki ya isa burarsa ta cika wandonsa idan kinada ja kije ki duba ai danki ne ya kamata ace kin riga kowa sanin hakan kuma ma da kike cewa an liqawa danki auran bazawara wlh bani na haifi Nafeesah ba Amma tafi qarfin a liqawa namiji ita balle harijin danki ke bandama dabbancin ki ai taimakonki akayi don da ace baa daura masa auranba memakon dan sunnah da zaki goya da shege zaki goya a matsayin jika, shashasha kawai da batasan ciwon kanta ba wlh Nafi ki fita idona idan ita wannan sullutuwar bazata iya qwatarwa yarta yanci ba toni zanyi yaqi dake akan Nafeesah dama danda kike iqirarin nakine shege ka fasa ni dake"
Sosai suka rinqa musayar kalamai ita da Mama itadai Hajiya Juwaira hqr take basu da taga abin yaqi saita kira Baffa a waya ta fada masa shikuma ya kira Abba tunda shi baya gari a fusace Abba ya shigo ya zafga mawa Ummah Nafi mari ya nuna mata hanya yace “kika qara second talatin a gdannan a bakin auranki ki wucce Adamawa" juyawa yayi ya kalli Hajiya Juwaira da Mama yace “kuyi hqr matar nan batada hankali saina nutsar da ita Ina Feesahta" daki Hajiya ta nuna masa tace “tana ciki batada lfy" numfashi ya sauke yace “ku hada mata kayanta yanzu Naseer zaizo ya dauki matarsa su wucce kawai ayi bikin daga baya idan ta haihu"………….
More comments More typing
*Mrs Dr M.A...✍🏻* [4/22, 9:58 AM] UMMUH HAIRAN CE...✍🏻: *_A B_*
*20*
Numfashi Maryam ta sauke tace “bansan komai akan wannan harkar ba amma zan tambayi limamin masallacin unguwarmu duk abinda yace zakiji amma kiyi hqr don Allah ki kwantar da hankalinki zakiji dadin wannan auren insha Allahu Naseer dan'uwanki ne kuma qaninki da yafi kowa sanin darajarki idan kika kwantar da hankalinki zakiji dadin aurensa kuma zakiyi alfahari da aurensa..." Cike da masifa ta katseta tace “dakata Maryam ba nasiha nidai na kiraki nace kiyimin ba saboda haka ki adana wa'azinki a gaba zaiyi miki amfani" kashe wayar tayi ta koma ta kwanta zuciyarta cike da tunani kala² tanata tufkawa da warwarewa har zuwa wani dogon lkc ta tashi ta sake fitowa parlourn turus taja ta tsaya saboda ganin iyayen akwatinan dake zube a parlourn har guda sha biyu ta zuba musu ido cike da tunanin lefen wa aka kawo?.
Muryar Aunty Amina taji tace “yawwa gatanan ma sai tazo ta gwada idan sunyi mata yawa sai a mayar a canzo tunda baa fita da kayan ba" gabanta ne ya fadi daidai lkcn da Jameelah tazo ta ruqo hannunta tace “matar yaro ga lefenki nan an kawo kizo ki duba ki gani" wani abu taji ya tokare mata maqogwaro ta zare hannunta daga na jameelah ta juya zata shiga kitchen idanunta na zubar da ruwa Jameelah tayi saurin riqota tace “ki duba mana" zame hannuta tayi tace “basai nagani ba sunyi" kitchen din da bata shigaba kenan ta shige dakinta ta fada gadon ta sake fashewa da kuka tana fadin “Allah na gode maka nikam wai da gaske yaronnan ne mijina ni Nafeesah?" Kukanta taci me isarta sannan ta tashi tayi alwalar azahar tayi sallarta a dakin ta sake kwanciya sosai takejin yunwa amma ta kasa sake sauka saboda ko kayan batason gani, duk da bangarorin zuciyarta suna bata shawarar ta hqr ta rungumi qaddara ta karbeshi a matsayin qaddararta wannan rana taci kuka ta gode Allah.
Duk yanda yan'uwannata sukaso ta fito cikinsu a parlourn taqi ko abinci da Jameelah takai mata yin duniya taci taqici Allah ya sani da zata iyayin jayayya da mahaifanta da tayi akan aurennan musamman da taji hirar dasu Jameelah sukeyi dasu Mama a parlour na diban albarkar da Ummah takeyi akan auren dannata da Nafeesah take ta qarajin tsanarshi musamman da taji yanda wai take cewa Hajiyanta ce ta tsaface danta aka mallakesa kan aurensa da Nafeesan hakan ya qara mata tsanar auran a ranta tare da qudurcewa a ranta duk yanda zatayi saitayi taga auren ya wargatse. A bangaren ango Naseer kuwa komai ya rikice masa musamman ta bangaren mahaifiyarsa da take kullum cikin yi masa bala'i da jawa auran nasa mugayen alkaba'i kala² tana dorawa auren nasa inda shikuma ya qara qaimi wajen ganin ya samo kan iyayen nasu maza sun bashi matarsa hakan kuwa akayi a baya wata biyu akasa zaayi bikin amma saboda baqin nacinsa saida Baffah yace ya rage sati biyar ya dawo dashi sati uku, murna gurinsa baa cewa komai.
Hidima akeyi sosai a gdan nasu duk wani abuda Nafeesah take buqata Naseer ya bata Maryam da Aunty Amina sune suka zama jakadu tsakaninsu sai Jameelah da komai ita take tsarawa kasancewar itadai Nafeesah duk shirin da akeyi taqi saka baki a ko daya ko kasuwa da suka matsa sai taje sun zabo ashobi dinsu su hudu cewa tayi ita bai Isa ta tambayeshi zata fita ba gashi shikuma Baffah cewa yayi komai takeso ta tambayi mijinta Aunty Amina ce ta kira Naseer ta tambayeshi zasuje kasuwa da Nafeesah aikuwa yace “dawa zaku Aunty Amina aa wlh ban yarda ba koba yanzu ba ban aminta matata taje kasuwa ba kuje kawai zan turo muku da kudin da zaku siyi komai ma" yana fadin haka ya kashe wayar suka kalli juna Jameelah tace “tabdi lallai yaronnan yayi nisa wato har yasan kishin matarsa" tabe baki tayi ta miqe ta shiga bathroom tayi wanka ta dawo lkcn sun fice daga gdan.
Sai magrib suka dawo suka zube kayan a dakin nata suka fara dubawa kayan sunyi kyau sosai suna tsaka da dubawa Naseer yayi sallama ya shigo dakin idonsa ya fada kan matar tasa da take zaune a gadon tanata danna wayarta Aunty Amina ce tace “meya kawoka dakinnan rasa kunya?" Murmushi yayi ya shafa kansa ya taka a hankali ya zauna a gefen gadon lkcn jikin Feesah yasha gyara na dole da Mama ta dage akeyi matashi daqyar, hannunsa ya dora saman sangalalin qafarta wani taushi da danshi yaji fatarta tanayi ga wani qamshi fitinanne da yake tashi a jikinta ya hadiyi wani yawu ya sanya hannunsa ya dago fuskarta yayi mata kasalanlen murmushin sa yace “kin hanani ganinki wifey tsayin sati biyu wato ke babu ruwanki da halin dazan shiga saboda rashinki ko?"