Auren huce haushi complete - Chapter 10
Auren huce haushi complete Chapter 10: Auren huce haushi complete Chapter 10. Zuwa lokacin su zahra karatu ya Mika, tun tana saka Rai da zuwa Nigeria har…
4,224 words
Zuwa lokacin su zahra karatu ya Mika, tun tana saka Rai da zuwa Nigeria har ta hakura Kuma abinda ya Kara Bata mamaki sau biyu Abba da Abdul Hakeem suna zuwa ganinta idan harkar kasuwanci ya kawo sun Istanbul.Amma Koda wasa Basu taba ce Mata ga lokacin da zataje gida hutu ba. A haka har suka hada shekara biyu a kasar, da gaske gida take son zuwa shi yasa lokacin da hutunsu ya gabato batayi shawara da kowa ba ta kama shirin barin qasar, online tayi komai Kamar su Sajida sai da komai ya Zama daidai sannan ta fadawa Uncle Haisam Shima bai hanata ba yasan tayi hakuri, Mama Hanifa ma ta waya ta fada Mata Nigeria zata wuce kawai, haka Ummee ma ta wayar itama ta fada Mata taso ta hanata Amma sai tayi wani tunani kawai tayi shiru kudade dai to tura Mata masu yawa Wanda har saida Zahrar ta Kara kiranta tana tambayar kudin ma meye haka da yawa? Tace ta turo Mata ne kawai ko idan take zatayi wani abun, godiya tayi Mata sosai hakan Kuma dabi'ar Zahrar ne komai kankantar Abu idan akayi Mata alherinsa zatayi godiya Kuma ko waye ta Bata Bata duba ai iyayene. Kwana biyu suka Kara da akayi hutun shima visa din su Khadijah ne Bata Zama ready ba. Lokacin da jirginsu ya dauka a Aminu Kano international airport taji ta sauko ta shaqi iskar Nigeria ji taji Kamar a Aljanna take lallai kowa yabar gida gida ya bar shi, saukar safe sukayi wurin karfe Sha daya ba yanda su zahra da Khadijah Basu da zahra ba akan ta zauna ta Dan huta kona awa daya ne a gurin sajida Amma tace A'a Azare tayi Kira su Anisa ne da Fatima suka bi Sajida Su dan huta kafin driver dinsu ya karaso tunda ba nisa tsakanin kazaure da kano, Kuma Gwammaja kan hanya ne. Shatar taxi Zahra ta dauka ta kaita Kano line Dan direban taxi din ta tambaya Ina zata samu motar zuwa Azare ya fada Mata akwai gurare Amma ita Kano line yafi Mata kusa. Har cikin Tasha Mai taxi din ya shiga da ita gurin motocin arear Bauchi, tayi Masa godiya sosai ta kuma Kara Masa kudi akan yanda ya bukata. Away biyu da rabi Mai kyau matarsu zahra ta shiga Azare tun shigowa su ta Fara ganin 'yan canje canje a garin Kamar sabbin titina street light na solar sai gine gine masu kyau. Masha Allah ya dunga fada a zuciyar ta, Mai adai daita ta Sami ta fada Masa inda ze kaita, tunda suka tinkaro unguwar naji want irin nishadi ya mamaye ilahirin zuciyar ta, unguwar tasu ma an Sami cigqba sosai ga wasu gine gine sabbi masu kamar makarantar kwana har da gate a gurin gidan malam Baba gidansu ma gaba daya ya canza anyi Masa mahaukacin gyara tamkar sake sabo akayi. Lokacin da Mai adaidatan ya sauke ta dai dai lokacin ya Hamza ya fito da alama wani gurinzeje Nan kusa. Da madaukakin mamaki yake kallon zahrar shi dai Koda Wasa baiji ance zatazo ba Kuma yasan da ansan da zuwanta ai Bala driver ko su suje su daukota a kanon. Da sauri ya karasa Yana Mata sannu da hanya ita Kuma tana gaishe shi, shi ya biya Mai Dan sahun yace ta shiga ciki za'a shigo mata da kayan. Tunda ta shigo gate din tasan eh lallai gidan ya lashe makudan kudin Dan gaba daya an canza fasalin gidan, tunda ta shigo gidan Mai gadin ke kallon zahra Dan shi dai sabo ne Bai Dade ba ta dai gaishe shi tayi gaba Nan ma wani mamakin ya rufe shi Jin tayi hausa radau Dan shi dai ze iya rantsuwa da abinda ze kashe shi wannan ko zo Bata sani ba da Hausa. Ai mamakinta Bai karu ba Saida ta shiga cikin Nan dai ko rantsuwa tayi ba kaffara sabbin gine gine ne dam kwata kwata inda parts din su na da yake gurin ba komai sai filing da shuke shuken flowers. Lokacin data shigo gidan ba motsin kowa kamar ba mutane a gidan kowa ne kofar part Yana rufe Ido ta lumshe tana shakar iska Mai Dadi ta gidan. Idonta na nufen Nan tana tsaye Dan ita batasan wane dakin zata nufa ba tunda da gaske ta Zama bakuwa a gidan, maganar Ibrahim taji Mai bin magaji Yana fadar "kai!" Da karfi ya juya a guje Yana fadin Ammah! Ammah! Kizo ga Aunty Zahra a tsaye a kofar part din Mama". Magaji ne dake zaune a falon yana kallon wani series na 'yan Lebanon ya dago Kai da sauri daga kallon T.V Yana tsaki Yana fadin Amma Kai ba karamin soko bane dallah Banda tsabar hauka zaka wani ware murya Kama kwala Mata akan shashancin Kawai Wai zahra A'a wat......" Maganar ce ta makale Masa lokacin da zahrar ta kunno Kai ciki da sallama a bakinta, dan a bude yabar kofar saboda zumudin ya kawo labari. Ammah ce ta fito da sauri tana fadin Wai Kai har abada Ibrahim bazaka giirm..." Idonta ya sauka akan Zahra wadda tayi tsaye ta langabar da Kai tana kallonsu,kafin Ammah ta dawo daga duniyar mamaki sai Jin zahrar tayi ta rugumeta ta saki shashhshekar Kuka. "Ikon Allah!" "Ikon Allah!" Abinda bakin Ammah ke fada kenan, ita Kuma zahra ta riketa kamar zata bace Mata. Mamace ta shigo dakin da sauri tana fadin "Ina zahrar yanzu sahura ta shiga ta fada min taga Zahra ta shigo yanzu". Ta fada tana kokarin Zama idanunta suna kan Zahrar. "Wallahi kuwa Mama kin ganta Nan yanzu Ina daki Ibrahim ya shigo a guje Yana fadin gata Nan a waje nayi zaton shashancinsa ne Saida na fito na ganta kwatsam ba zato ba tsammani ba wani bayani". Ammar ta saki da Dago kanta tana goge hawayenta tana fadin. "Haba Ammah an kaini wata uwa duniya an manta Dani idan nace zanzo ace A'a ni Kuma wallahi na gaji gida nake so shi yasa naki fadawa kowa na tasho kawai na gaji da ganinku a waya ni zahiri nakeso". Ta fada tana maida kanta jikin kafadar Ammar. Tunda ta Fara magana Mama ta kureta da ido dan wani irin mahaukacin kyau taga Zahrar ta kara, ga wata irin gogewa da wayewa tamkar ba Zahrar data sani ba komai nata ya canza har ma salon yanda take magana. "Ai kodai ki daina irin wannan kasadar ta tahowa daga uwa duniya irin wannan ke kadai sai ki fada ko addu'a ayi Miki sannan aje a daukoki daga Kano, Amma fa Ina tunanin a motar haya kikazo garin Nan ko?" Mama ta fada. Kai Zahra ta gyada alamar eh, dai dai lokacin Yara suka shigo da jakunkuna ta guda biyu. zaunawa tayi tana gaishe dasu Ammah, sannan magaji yayi Mata sannu da hanya Yana fadin "irin wannan surprised haka uktiy? kin ganki kuwa kin juye Balarabiyar ki sak kodan kina cikin 'yan uwa dangi farare irinki" Dariya Zahra tayi Masa kawai. Ibrahim ne ya shigarwa da Zahra jakunkunan ta dayan bed room din Ammah, ya fito ya nufi kitchen ya kawo Mata ruwa da lemo, ya koma ya dauko warmmers din abinci sai Ina yaka saka yake da zahra har Mama na Masa Dan biki. Saida tayi wanka taci abinci sannan suka zauna da Ammah bayan sallar insha'i, hira sosai Suke Amma duk yawanci korafin Zahra ne na hanata zuwa.da Ammah tayi, a haka Abdul Hakeem ya samesu Shima yayi mamakin ganin.zahra kamar a mafarki Dan lokacin da ta dawo baya nan yaje Darazo ganin ganin wasu gonaki da Ya Hassan ya saya a can. Sun raba dare suna Hira da 'yan uwanta a falon Mama sunyi waya ma da Abban tunda lokacin Yana aAbuja, Shima yayi fada sosai lokacin da Ammah ta Kira shi ta fada Masa ga zahra tazo. Sai da ta kwana biyu tana huce gajiyarta, tana jikin Ammah kullum kamar kamar wata 'yar yaye, duk 'yan uwan kowa nan nan yake da ita, kowa kokarin kyautata Mata yake yi. Sunyi waya da Aunty Hasana tace Mata tana nan tafe Jos zatayi Mata sati Amma sai Abba ya dawo, haka kusan Kullum sai sunyi waya da Hameeda. Ranar data kwana biyar ne Ammah ta takura Mata akan ta leka makwabta ta gaishe wasu da yawansu sun shigo, wasu Kuma sun turo yaransu suyi Mata sannu da zuwa harda abin hassafinsu. A waya Zahra ta Kira mujiba akan ta Shirya ta rakata Nan gidajen su shishhiga a gaisa. Doguwar Riga ta saka kirar Dubai blue black Mai duwatsu tun daga sama har kasa ta saka plat she dinta fari tas ba wani makeup da tayi powder kawai ta saka sai lipsglow turarenta na Alkawari ta fesa Mai sanyi kamshi, Kota sa ko Bata Saba komai na sutarata kamshin yake. Ta fito Kamar wani dawisu Dan da gaske zahra mai kyauce komai nata Kamar ita ta zabarma kanta. Tunda ta shiga bedroom din Ammah ke kallonta data ita sai halicinta suka San abinda zuciyar ta ke ayyana Mata a fili Kuma sai tace "Masha Allah! Har kin shirya?" Kai ta gyada Mata tare da fadin "Eh Allah Dan dai kin matsabe Ammah Allah da Babu inda zani sai nayi sati biyu ko gate ba leka ba". Wata leda Ammah ta Miko Mata tasa hannu ta karba tana tambayar "na waye?" " Idan kunje gaida Baba malam saiki bashi tasa tsarabar turarika ne". Murmushi Zahra tayi har fararen hakoranta suka bayyana tana fadar "wace irin tsaraba Kuma Ammah nida ba Hajji naje ko Umara ba daga makaranta fa na dawo hutu". "To Miko min kije hannu sake ki gaisa ki taso tunda Zama da turawa ze saka ki koyi rowa" ta Mika Mata hannu alamum ta Bata ledar. Dariya tayi Zahrar tana fadin "Allah ya Baki hakuri Ammah Ina ni Ina koyo rowa a garin wasu alhalin na gaji kyauta gaba da baya Allah qara lfy". Ta nufi kofa tana fadin "saina dawo" "Allah ya tsare Kya gaishe da Malam din. Gidan su mujibar Zahra ta Fara shiga suka gaisa da Mamanta sannan suka shishhiga gidajen suka gaisa, gidan Malam ne na karshe, a hanya Zahra ke tambayar Mujiba ginin da taga anyiwa Almajiran Baba Malam? nan ta fada Mata iya abinda ta sani akai. A cikin rumfar canopy din da Malam yake bada karatu Zahra suka tarar da Malam din suna magana da wani matashi sukayi sallama a bakin rumfar a tare malam da Wanda Suke magana suka amsa sallamar, Yana fadin Bari naje na karbo yanzu in Sha Allah. Juyowar da zeyi sukayi ido hudu da Zahra wallahi ita dai batasan lokacin data rufe idanunta ba Dan wallahi wani Abu ta gani a idonsa Wanda Bata taba gani a idon kowa ba take zuciyarta ta wani harba a cikin girjinta. Ga wani mayen kamshi daya cika Mata hanci ita dai Bata San ya wuce ba Saida Mujiba ta tabata tana fadin ki bude idonki "Zahra menene?". Ajiyar zuciya tayi a hankali tace "ba komai muje" Cikin rumfar suka shiga suka zauna daga gefe suna gaida malam din. Amsawa yayi Yana fadin Masha Allah da bakin turai ne Fatimah yaushe Kika shigo ban sani ba kodon Alhaji Yana Abuje shi yasa bani da labari". Sunkuyar da Kai zahra tayi tana fadin. "Ban Dade ba Baba Malam yau kwanana biyar da dawowa, Saida na huta nace Bari nazo na gaisheka" "To Masha Allah! Allah yayi Albarka ya bada sa'ar abinda akaje nema, ai ba'a Gama karatun ba ko?". "Eh da sauran shekara daya karatun ne da banbanci da namu na nan tunda su basa yajin aiki". "Wannan haka yake, Allah yayi jagora ya bada sa'a" "Amin" suka amsa tashi zahrar tayi ta karasa gaban malam din ta aje Masa ledar turarikan dake hannunta tana fadin "gashi Baba ba yawa"
Godiya yayi sosai kafin yace "ku shiga ku gaisa da zainabu batajin Dadi tana fama da masassara tun jiya". "Allah ya sauwake"suka fada suna fita faga cikin rumfar. Tunda suka shigo gidan suka sallama Amman gidan shiru a falon ma ba kowa uwar dakin Zahrar ta nufa tunda gidan ba bakonta bane, can tsakiyar gado ta hango Iya Abun jikinta yana ta kadawa tana ta rawar sanyi da sauri Zahra ta karasa kusa da ita tana Mata sannu Amman Sam ta kasa amsawa hannunta Zahrar ta Mika ta taba jikinta sai taji Kamar wuta. "Ya Salam". Ta fada tana nufar falon inda tabar mujiba tana fadar "Bari na fadawa Baba Malam jikin Kamar ya matsa gaskiya". Tayi waje ba tare data jira taji abinda mujibar zatace ba. Tafiya take cikin sauri burinta ta Isa gurin malam ta fada Masa abinda kenan. Ita dai Batasan yanda akayi ba sai ji tayi ta bugi kirjin mutum da kanta abinda yayi sanadiyyar ta tafi taga -taga zata Fadi taji an fusgota da Dan qarfi kafin ta Kai kasa sai ganin ta tayi rungume kane kane a jikin koma wannene an saka hannu biyu an zagaye bayanta. Kici kicin kwace jikinta ta shiga yi data Samu ta Sami kanta coming fishing ta daga ido taga wane Mai tarar aradu da fadin Kaine ya kwakumeta haka da yammcin Allah wata'ala ta sauke Masa zallar rashin mutunci duk da ba halinta bane, tana daga Kai sukayi arba dashi ya kafeta da idanunsa masu wani irin kaifi da mugun kwarjini a cikin nata idanuwan Wanda a ganinta dashi na farko ya yamutsa duniyar ta
.AUREN HUCE HAUSHI MAMAN FATIMAH
Page Fourteen 14. -----------kusa da ita ya matso sosai Kamar ze Kara rungumo ta, da sauri tayi baya tare da rufe idanunta ruf zuciyarta na Kara speed, a hankali yayi magana saitin kunnanta "ki rinqa duba gabanki idan kina tafiya Mana kada kiyi Mana asara pls". Ya fuske yayi wucewarsa ciki Bai Kara bi ta kanta ba. Nan inda ya barta Bata iya motsawa ba, wani Abu ilahirin jikinta keyi itafa ji take kamar kafarta bazata iya daukar ta ba wallahi,.shi Kuma wanene wannan a tare da malam haka? A Ina ya Samo shi Dan a gaskiya baiyi Kama da kolo ba Sam to waye shi?". Tambayoyin dake Mata Kai kawo kenan a kwakwalwarta daga ganin mutum haka kawai ze nemi yayi Mata shiga hanci da qudundune,ga wani irin kwarjini a cikin idanunsa da Bata taba gani a gurin wani namiji ba. Bata ankara ba taji maganar malam Baba Yana fadin " A'a Fatimah ya Kika tsaya a Nan ko wani Abu kike jira?" Da sauri ta bude idanun tana kallon malam da wani yana binsa a bayan. "A'a ba komai Daman gurinka zani jikin Iya Abun ne Naga kamar ya Dan matsa tana ta rawar sanyi". Ta fadan kanta na kallon kasa kamar marar gaskiya, dan ji take kamar malam din Yana Jin mayen kamshin turarensa da ilahirin jikinta keyi. "To Babu laifi muje ciki, yanzu Mahmud yaje ya dauko abokinsa don ya kara dubata tunda jiya sunje Asibiti da Halima matar malam Mudi ance zazzabin typoid ne yake damunta, to da jikin yaki Dadi ne za'a Kara bincike ko na cizon sauro ne zazzabin".. suka wuce ciki sannan zahrar tabi bayansu zuwa falon Iya Abun Kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki. Yana tsaye daga bakin kofar ta waje ya harde hannuwansa a kirji kamar Mai tunanin. Ganin malam din da salahuddeen sun shigo ya daga kansa Yana amsa sallamar su. Mujiba ce ta leko tana fadin" ta tashi din gata Nan fitowa". Bai shiga falon ba Saida malam ya Fara shiga sannan suka biyo bayansa. Sannu salahuddeen din yayi Mata ya dauki jinita take a Nan yayi Mata gwajin maleria ai kuwa ita ke damunta har ta Kai || +. Allura ya dauko Yana fadin " malam allura za'a yi Mata emal, idan Allah yasa an dace shi kenan idan Kuma Bai sauka ba sai ayi Mata Attusunate, amma muna fatan Allah yasa a dace ma".
"Allaumma amin ya Rabb". suka fada su duka. Magunguna ya rubuta Mata na ulcer da tayi masa complain na ciwon girji da gefen kafadar ta, sannan yayi Mata Allah ya sawaqe suka fita. Har magariba su zahra suna gidan Baba malam, tun bayan fitar su malam ba dadewa Iya Abu ta koma daki ta kwanta Zahra ta rufeta da wani qaton blanket barci Mai nauyi ya dauketa. Nan falon suka zauna suna Dan tattaunawa da junansu, da tafiya zasuyi Majiba tace su zauna zuwa wani lokacin tunda ansan suna Nan Dan lokacin da zasu shigo mujibar taga kaninta Mubarak tace ya fadawa Mama suna gidan Baba malam. Duk hirar da Mujiba ke yiwa Zahra Sam hankalinta baya tare da ita ta tafi duniyar tunanin abinda ya faru dazu da Wanda aka Kira da Mahmud wai ita Zahra ce kwance a kirjin wani namijin daba muharraminta ba, Kuma ba wani mataki data dauka Koda kuwa na kad'a Masa warning ne yanda gobe baze Kara marmarin rungumar wata ba, Amma Wai sai gata ta b'ige da shakkar idanunsa abinda kaf tarihin rayuwar ta hakan Bai taba faruwa da ita ba, ga wata faduwar gaba ta ba gaira ba dalili data sameta yanzu, ganin nan biyu da tayi Masa duk Abu daya takeji a kansa. Wani wawan tsakin Zahrar tayi Wanda ya tabbatarwa Mujiba Bata tare da ita duk zubar da takeyi kamar 'ya'yan kanya. "Keda waye kike tsaki haka kuma?". Majiba ta fada. "Kedai kawai bari kawai ba komai. Ta fadar tare da you kwafa ta tashi tsaye tana fadin "Tashi mu wuce gida tunda Naga wannan barcin na Iya Abu bana Kare bane, inaga har da allaurar barci yayi Mata gaskiya". A kofar gida suka yiwa malam sallama Yana ta Sanya musu Albarka. Tun daga ranar Zahra Bata sake fita ba tana gida saidai lokaci-lokaci Mujiba na shigowa, a ranar data cika sati daya Abbansu ya dawo murna ba'a maganarta gurin Zahra, duk da tana ganin shi a can syprus din idan yaje Amma hakan bai Hana sun Kai wani lokaci ba suna tattaunawa irin ta d'a da mahaifi. Saida Zahra tayi sati biyu sannan ta nufi Jos gurin Aunty Hasana. Taji matukar dadin zuwanta Jos din. Dan har gidan Aunty Jana sukaje da Yara tunda lokacin da akayi bikin Bata Nan. Duk inda ya kamata taje taje har gidansu Mama taje haka ta kaiwa jannifer ziyara lokacin sunyi hutu tana karatu a Nan University ta Jos. Maganar samari da gaske ta sakata side idan ka ganta tana magana Mai tsawo da namiji to ka tabbatar dan uwanta ne ko wani Mai qirma a idanunta. Satinta daya a Jos suka taho tare da aunty Hasanar da Yara Wanda a satin sukayi hutu, bayan dawowar ta daga Jos ne su Hameeda sukazo hutun semester. A lokacin ne Salma ta fito mata a mutum sak, ta nuna da gaske Bata yin zahra abinda yaso ya kawo b'araka Mai girma kenan tsakanin Mama da Ammah Dan da gaske an Kai hakurin Ammar karshe, maganganu Salmar ta ringa saki kamar lokutan baya, sai dai a wannan karon Zahrar ta nuna Mata jiya fa ba yau bace, idan da tayi tolerating na nonsense din ta a yanzu Kam dai dai take da ita tunda Bata Jan girmanta a gurinta, abinda ya Kara harzika Salmar lokacin da Zahra ta kalleta tayi tsaki tace "Wai wannan ce mace,kina duba mirror Kuma kina ganin kanki kuwa?gara ni da har kike min gorin ana saka aurena ana fasawa, Ina laifi tunda har ana ganina ana sona, kaddarar Babu mijina a cikin su ce take rabani dasu, kefa ko Kare Bai taba zuwa yace Yana sonki ba, baga kanwarki Nan ba Ina cewa har anzo tambayar aurenta? kije kiji da abinda ya dameki Zaki zauna kina fada da kanwar bayanki". Tana Gama fada Mata maganar ta nufi hanyar ficewa daga dakin. Cikin fushi salmar tayo kan Zahrar ta fardota baya saura kadan ta Fadi dai dai lokacin Kuma sahura ta shigo zatayi musu sharar yamma ta tarar da wannan badakalar, da sauri ta shiga tsakanin tana Basu hakuri ta Kama salmar ta fita da ita daga dakin tana faman zagin Zahrar abinda ya janyo hankalin Amma dake main kitchen din gidan tana yiwa Abba gas meat saboda Yana sonsa sosai yawanci idan Yana gida kusan duk dare sai anyi Masa shi. Da sauri ta fito tana tambayar "me yake faruwa ne?" Sahura ce ta fada Mata abinda ta shiga ta gani tsakanin Zahra da salmar, juyawa kawai Ammah tayi ta koma taci gaba da aikinta Bata Kara lekowa ba tanaji Mama ta fito tana fadan daman ai ba tun yau ba ta fuskanci Zahra ta Raina Salma, Kuma komai runtsi dai Salma ai gidan ubanta ne Nan ba Mai hanata sakewa. Zahra ce ta fito zata wuce zuwa part din Ammah,har ta gota Mamar batace komai ba, Mamar tace. "To fiqe kafi qaya tsini da Kika Samu guri kina yanda kikeso a gidan wallahi duk rintsi bazaki Kai matsayin 'ya'yan gida ba, tunda har abada ba'a canzawa tuwo suna" Har zahra tayi kamar ta maida Mata martani sai taji bazata iya ba babba babba ne, kawai ta shige part dinsu. Har Mama ta juya taji maganar Ammah daga bayanta, dan harga Allah batasan Ammah ta fito main kitchen din ba, Sam duk da tana jiyo kamshi ta dauka a can part dinta take aikin. Bata juyo ba Amman ta tsaya. Ammar tace "Haba Mama ban zaci haka daga gareki ba wallahi, cewa nake da Zahra da su Hameeda dauka daya ne a gurinki, ai saiki tambayi meya hada fadan?kiyi musu fadan gaba daya ba wai ki nuna Salma itace taki ba, kina fadin maganganu irin haka ai na dauka ni duk binda lauje ya yayo a gidan Nan ya kamata ki dauke shi ciyawa ne na gode amman ki sani Banda komai nufin Allah ne Zahra tafi karfin ace Mata 'yar karere tunda Mai gidan ne da kansa ya karbo rikon lokacin da aka nemi tafiya da ita kema Kuma sheda ce kinsan su waye kakanninta ba bakinki bane, dukiya idan ana gadonta kinsa Zahra 'yar mun gada ce, ko shi Wanda kike takama da dukiyar tasa yasan tazarar da nisa a tsakaninsu da kakanninta idan kina tunanin karya ne idan yazo ki tambaye shi ze Baki cikakken bayani". Bata jira taji abinda mamar ke kokarin fada Mata ba tayi gaba abunta ta nufi part dinta. Tun daga ranar Ammah ta daukewa Mama wuta gaisuwa kawai ke hada su, a kwana na biyu da Mama ta karbi girki ta kasa hakuri ita abin yafi damunta ta fadawa Abban Ammah Bata Mata magana, yayi mamaki matuka da gasken gaske Dan wannan shine karo na farko da irin haka ta faru da matan nasa duk tsawon shekarunsu. Bai taba rabasu akan sun Sami matsala ba Koda wasa, dan haka ya Kira Ammah a waya yace tazo part dinsa Yana son ganinta. Batayi mamakin ganin Mama a zaune ba tasan za'a Rina tunda kaf tasan halin Mama na zahiri. Gaishe da Abban tayi suka Kuma gaisa da Mama, tambayar ta Abban yayi ko akwai abinda ya hadasu da Ammah ne?. Ba wani kwana kwana ita Daman tun can baya Bata da munafurci ko kadan. Dan haka ba wani ta fadawa Abban duk abinda ya faru tunda Saida ta tutsiye Zahrar akan ta fada Mata abinda ya hadasu da Salma da kuma abinda mamar ta fada, shi kanshi Abban yayi mamakin abinda Salma tayi sosai, itama Mamar ya nuna Mata kuskurenta na fadar wannan maganar ya Kara da cewa. Ban tabi yiwa zahra kallon ba nine na haifeta ba, bil hasal ma shine dalilin da yasa ban aura Mata Daya daga cikin 'ya'yana ba, ita kadaice ba uwa ba uba tun batasan inda kanta yake ba, mu ta sani a matsayin iyaye sauran yaran Kuma 'yan uwanta. Idan na aura Mata wani a cikinsu ba zata Zama feel free tare da ni ba, idan damuwa ta shiga ba Wanda zata fadawa kinga ai anyi adoh badan kyau ba". " Haka ne suka fada. "To karna Kara Jin makamanciyar irin wannan maganar, ba Wanda ze kawo min rarraba kan iyalin gidana. Zahra 'ya tace kawai na saka sunan mahaifinta ne Dan haka shari'ar musulunci tazo dashi, badan in nunawa duniya bani na haifeta ba, a kiyaye kodon gaba". "In Sha Allah". Suka fada. Bayan tafiyar iyayen yasa suka turo yaran yayi musu fada sosai sanan ya Kare da nasiha. Tun daga lokacin abubuwa na zahiri sukayi sauki sosai. Kusancin Zahra da Hameeda ba abinda ya taba shi saima Kara shakuwa sukeyi a kullum suna Jin dadin butun, Zahra suna waya sosai da Ummee da Mama Hanifa harma da uncle Haisam a wasu lokutan.
Lokacin da hutunsu ya kusa karewa duk sai Zahra ta nemi walwalarta ta rasa ko da yaushe kamar marar lafiya ana saura kwana biyu ta tafi Ammah ta matsa Mata taje Kiran da Baba malam yake Mata, dan sau kusan uku yana turo Yara tana cewa gata Nan Amman sai tayi burus da zancen. Har dai ta Kai Ammah karshe tayi magana. Hameeda tace ta rakata suje tare, yau gurin malam din ba kowa ba Kuma rumfar karatu tunda ranar basa karatu. Gurin ganawa da mutane suka sameshi su Habib suna ta gyaran Shirin kantar littafai. Da sallama suka shiga suka gaishe da malam din sannan suka gaishe dasu Habib, sai sukayi shiru. Malam ne yace "Zahra'u Ashe lokacin komawar taki har yayi ko?" Kara risinawa tayi tana fadin "eh lokacin yayi yayi Baba gobe zan tafi in Sha Allahu amma a Istanbul zan tsaya sai wani satin zan wuce syprus din".