Kenza eBookz

Auren huce haushi complete - Chapter 9

Auren huce haushi complete - Chapter 9

Auren huce haushi complete Chapter 9: Auren huce haushi complete Chapter 9. Ta Fara karatu cikin nasara Bata da wata matsala ta zahiri saidai sau da yawa…

3,054 words

Ta Fara karatu cikin nasara Bata da wata matsala ta zahiri saidai sau da yawa tana shiga dogon tunani akan al'amuranta ta rasa Gane daga Ina ne ake samun irin wannan akasin? matsalar dai iri daya ce, Kuma salon tafiyar iri daya ce sai Dan banbancin da baza'a rasa ba. Suna yawan waya dasu Ammah da mutanen Jordan, lokacin data Kira Hameeda mita ta ringa yi Mata akan tana boye Mata wani Abu tunda gashi Saida ta bar kasar kana ta Kira ta. Da kyar ta fashimtar da ita abun ne yazo da gaggawa itama Bata sani ba Saida komai ya Zama ready, Kuma tayi ta try din ta sameta Bata Samu ba lokacin ana fama da matsalar network a area dinsu.

Zahra najin dadin Zama a kasar duk karshen sati a gidan uncle Haisam take yin weekend din ta, sai Monday da safe motar Embassy take dawo da ita. Tsakanin syprus science University din wadda take kyrenia city a arewacin syrups din da capital city din dake Nicosia tafiyar kilometers talatin ne, kawai daga Baya ma da uncle din cewa yayi ta baro cikin makarantar ta dawo gidansa kawai da Zama sai a ringa kaita kullum itace taqi tana ganin Kamar abun da wahala yau da gobe sai Allah daga nesa nesa dai. Yau ma Monday da wuri motar Embassy din ta kawo ta, tayi gaba da wasu daliban zuwa mabanbantan makarantu inda suke karatunsu.Ganin da saura Kamar awa aya da rabi kafin su shiga lectures yasa ta wuce hostel Dan ta aje kayan da tazo dasu. Tana cikin tafiya tazo gota wani hostel Kamar a mafarki sai taji Kamar ana hausa a dakin abin ya Bata mamaki tayi Kamar ta koma ta duba sai dai tayi gaba tunda bin kwakwkwafi haramun ne. Lokacin da suka Gama lectures din Bata koma hostel ba, karatu suka zauna sunayi da wata course mate dinta 'yar kasar Lebanon Asseyeh tasu tazo daya sosai saboda itama akwai nacin karatu ga Kuma kwanyar Allah ya hore itama, uwa uba ga rikon addini tunda su dai kasar sai a hankali kawai culture din ta rinjayi addinin, Dan wasu Ma sai kaga suna sallah zaka Gane musulmi ne. Yamma likis su Zahra suka nufi hostel, haka nan Zahra taji tana son karabi ta wurin inda taji ana magana da Hausar nan, can ta nufa bayan sun rabu da Aseeyeh. Very lockly kuwa tayi Dace da wata daga ciki ta fito tana waya bahaushiya sosai.A shape ce a jikinta ta atamfa sai karamin hijabi a jikinta da alama Kamar fita zatayi.Dan tsayawa zahra tayi har ta karasa wayar, cikin nuna zallar farin ciki zahra ta nufeta tayi Mata sallama. Da sauri ta juyo Jin an Mata magana da Hausa cikakkiya. "Wa'alaiki Salam" yarinyar ta amsa Mata tana kallon zahrar da murmushi itama a fuskarta. "Masha Allah wallahi naji dadin ganinki kema daga Nigeria kike". Zahra ta tambaye ta. "Eh daga Nigeria muke muna da Dan yawa zamu Kai goma". Mamaki ne ya Kama zahra ganin Bata taba ganinsu ba Koda wasa. "Ikon Allah! Amman dai baku Dade ba ko?" Kai ta gyada "Mata gaskiya Kam ai ba school daya muke ba mu a Nan mu hudu ne, sauran suna different Universities ne on transfer mukazo nan daga Sudan tunda can rikici ya d'ai d'aita Qasar. Zo mu shiga ciki ki gaisa da sisters Dina kafin na dawo zan fita na samo Ko fizza ne yau bamuyi girki ba". Ta fada tana juyawa ciki, bayan ta zahra tabi suka nufi ciki. "Khadijah ! Fatima,! Sajida! Kuna Ina ku fito gashi mun Samu qaruwa". Kowacce barin abinda take tayi ta nufo kofar tana fadin "Anisa menene?". Ai kafin tayi magana Zahra tayi Arba da sajida Musa, sajidar ta ta FGGC KAZAURE. Cikin wani irin farin ciki suka rungume juna Zahra sai kuka Dan wani abune da Bata taba zata ba robonta da sajidar tun suna cikin bala'in Sudan kafin wayar sajidar ta salwanta shi kenan suka daina Jin juma Amma kullum zahra da fargaba take kwana har zuwa lokacin da ta Samu labarin dawowar su sajidar a bakin Maryam Suraj wata kawarsu. Kallo saiya koma sama Wai shaho ya dauki giwa ita Mai kawo bakuwa sai duk suka Zama 'yan kallo. Hannun zahra sajidar ta Kama ta nufi bed in ta da ita tana fadin "wannan wace irin ranar farin ciki ce bestie wallahi ranar nan tana daga cikin ranekun da bazan taba mantawa dasu ba cikin tarishin zamana a syprus, pls bestie talk ya akayi haka ta faru Dan Allah kece ko gizo idona yake mini ne Dan Allah kiyi magana". Ita dai zahra ba baka sai kunne, ai ita nata mamakin yafi na sajidar sau dari idan da Wanda Allah ya yiwa gyadar dogo ai ita ce, ba zato ba tsammani Allah yayi Mata irin wannan suturar bama 'yan Nigeria ba A'a aminiyar ta sukutun ya kawo Mata kasar, ba abinda zata cewa mahalicci sai godiya take a Nan tayin sujudushshukur ga Allah. Sai da ta goge hawayenta sannan ta Samu damar magana suka gaisa da sauran yayin da Anisar ta cire hijabin tana fadin "Ai Kuma saidai kowa ya hakura da cin fizzar Dan na fasa fitar kawai ayi abinci tunda Naga bakuwar tamu ce ko sister" ta fada tana kallon sajida. "Kwarai kuwa ai dukkanku kowa ya kwana da sanin Zahra Muhammad sani ko?". Gaba daya suka zubawa Zahra idanu suna fadin sosai ma kuwa, niba har gaisawa munayi ba some times idan Kuna vedio call lokacin muna Sudan" inji Khadijah. "To ai ita ce gata a gabanki zahiri" Khadijah ta Dade tana mamakin abun ita sai taga Kamar canza Zahra akayi tasan dai yesss ba karya zahra Mai kyauce na a bugi kirji a fada, amma sai taga wannan Kamar ma Bata taba hada dangantaka da 9ja tamu ba, komai nata classic ne. Nan suka baje hajar hirar yaushe gamo, har kusan karfe goma na agogon kasar suna tare anan su sajida suka fada Mata gwamnatin tarayya ce ta dawo dasu Nan tunda suna under scholarship ne shine aka rarrabasu kasa kasa su Allah yasa suka shigo cikin daliban da aka kawo Nan din. Har daki suka raka Zahra a Nan ta Basu fizzar tunda Daman tazo da ita daga gidan uncle Nan ma sun jima kafin su koma. Ai tun daga ranar wata nutsuwa da kwanciyar hankali suka Samu kyakykyawan muhalli a zuciyar Zahra, haka itama sajidar duk da Daman ita tana da masu dauke Mata kewar gida, Suma su sajidar sau da yawa suna bin Zahra a wasu weekend din zuwa gidan uncle Haisam din Amma su basa kwana duk da irin nacin da zahrar ke musu. A haka karatunsu ya Mika har sukayi exams, Mama Hanifa taso Zahra taje Mata tayi hutu Amma Haisam yace tayi hakuri sai hutun karshe session. A haka suka Kare hutunsu suka Dora da karatu, ba Sajida ba hatta su Khadijah suna Jin dadin Zama da zahra gashi Sam abin duniya Bai rufe Mata ido ba, Dan ta ko'ina kudi ne ke sauka a Account din ta ba daga 9ja din ba, ba daga Jordan ba, ba daga turkey ba, kowa kokarin farantawa zahra yake zuwa lokacin tayi wani irin mahaukacin kyau na ban mamaki ga wayewa da wayon zaman duniya ta Kara Zama 'yar gayu Kamar me Dan ba karya matar Uncle Haisam Yar gayu ce sosai kamar Auntyn ta Hasana tasan yanda ake tattalin jiki matuka. Har zuwa lokacin ba ruwan Zahra da saurayi bil hasal ko aboki namiji Bata dashi, akwai wani Dan Syria Omer yaso Zahra Kamar kaddara Amma ta shafawa idanunta toka tace ba wannan maganar yace to su Zama friends Nan ma tace lah lah. Dole ya hakura saindai duk inda zasu hadu sai yayi Mata magana idan abu ta saya duk yawan kudin shi ze biya.

Lokacin hutun karshen shekara Zahra taso zuwa Nigeria tunda taga su sajida nata Shirin tafiya, ta kwallafa Rai sosai akan zuwan Amman sai Ammah ta hanata zuwan tace taje Jordan idan hutun ya kusa karewa ta dawo Nan gurin Mama Hanifa ta karasa Abdul Hakeem zezo ya ganta. Ba haka taso ba da har tayi niyyar Kiran Abban ta fada Masa sai Kuma tayi tunanin kada Ammah tace ta Kai Kara dole ta hakura tunda Bata San nufin Ammah din ba data hanata zuwan. Taji dadin zuwa Jordan din sosai, dan Ummee na Shirin zuwa Saudi Arabia ne ma zuwan Zahrar ne ya kawo Mata tsaiko, tare suka tafi bayan ta huta, a can suka tarar da Aunty Nawwara wadda taje zuwa na musamman tunda lokacin ana daf da bikin aurenta inda za'a kaita Bagdad (Iraq). Sunyi sati daya zuwa suka nufi makka sukayi Umara, sosai Zahra ta mayar da hankali gurin addu'a akan matsalolinta na yanda rayuwa ke walankekuwa da ita Bata rasa komai ba Amma aure Yana neman yafi karfinta dah kudi ko kyau ke sawa mace ta auru tasan da yanzu ba wannan zancen ake ba, sai dai tasan duk Dan Adam baya wuce tasa kaddarar sai dai neman sauki gurin Allah s.w.a. Madina suka koma da suka Gama umarar,basu Dade ba suka koma Jordan. Lokacin da hutunsu ya taho garewa zahra ta koma syprus. Gidan uncle ta Fara Zama kafin daliban su dawo tunda ana saura one week ayi resuming ta dawo. Karatu suke ka'in da na'in ba Kama hannun yaro, amincin ta da Sajida ya Kara karfi tamkar uwa daya uba daya suke, Dan lokacin da sukaje hutu sajidar har Azare taje ta gaishe da Ammah ta karbowa Zahra sako. Duk lokacin da za'a yaye dalibai makarantar tana hada gagarimin taro tana baiwa best student na kowane department award. A karshe semester din ne aka hada taron Wanda ya Tara al'umma daban daban daga kasashen duniya masu Taya 'ya'yan su da 'yan uwa murnar gama karatu, celebration ne ake na gasken gaske, su zahra dai suna kallon abubuwan tunda wannan shine na farko da akayi suna Nan lokacin da akazo bada award ne ba zato ba tsammani aka Kira zahra Muhammad sani daga Nigeria aka Bata award na overall a department dinsu akan kowane subject. Wayyo murna gurinsu ba'a magana Dan Zahra kuwa har mukan Dadi tayi data duba taga yawan daliban da suke a department din nasu Amma ace ita ta karbi best ai abin murna ne Kam. Sun Sha hotuna da mutanen mu na africa more especially 'yan Nigeria. A ranar Zahra tayi takaicin karatun nesa da ace a gida ne da Abbanta ko Ammah ko wani daga cikin yayinta zata danqawa kyautar su sharing happiness din tare Amma Nan kuwa fa sai da friends da wasu tsirarun mutane Wanda ma ba saninsu tayi ba sukayi farin cikin, ga Uncle Haisam ma a matarsa da yaran duka sun tafi turkey. Sai ta waya sukayi murnarsu da jama'ar gida ta tura musu hoton award din ta waya hotunan da suka dauka.

-----------------

AZAREN KATAGUM

Alhaji Jafar ne da Malam Bukar sai Habibu dan kanwar malam Bukar dake aure a suleja malam din yake rikonsa tun yana karami mahaifinsa ya rabu da mahaifiyar sa acan gida Yobe da tayi auren a suleja din ne baban Habibun yace baza'a tafi Masa da yaro gidan wani ba yayi agolanci, rigima sosai aka kwasa da shi saboda itama tace bazata bar danta a inda za'a kashe Mata shi ba. Shine mafarin malam din ya dauko shi tunda ba wasu 'ya'ya yake dasu da yawa ba, a hannun malam ya girma shi yayi karatun boko har matakin HND. Jikamshi malumfashj zasuje Daurin Auren 'yar abokin Alhaji Jafar din sannan zasu shiga Jikamshi dubiyar malamin malam Bukar din daya kwanta kwanakin baya a Asibitin Ibadan nisa yasa shi majiyyacin ya Hana masu zuwa dubiya sai yanzu daya dawo gida ne malam zeyi amfani da wannan damar yaje dubiyar. Tafiya ce mikakkiya Dan tsakanin Azare da malumfashi tafiya ce ba kadan ba Dan haka sukayi sakko Habibun ne ze tukasu malam Bala anyi Masa Rashi acen garinsu Itas gadau Yana can. Cikin ikon Allah Basu rasa Daurin auren ba Dan Sha buying Mai kyau suna cikin garin malumfashin. Basu Bata lokaci ba suka dauko hanya sun biya jikamshin sun duba malamin Alhaji yayi masa kyau ta girma. Suka dauki hanya sosai Alhaji Jafar ya yaba da tukin Habib Dan baiyi zaton ya kware irin haka ba. Sunzo kachako lokacin sallar la'asar yayi guri suka Sami inda akayi wani Dan masallaci dan matafiya. Suka firfito Dan gabatar da sallar, malam ne ya Fara gewayawa yayi dahara sannan Shima Alhajin yayo sukayi alwala suka shiga sallah Saida suka Gama suka fito sannan Habib Shima ya nufi gurin you daharar Amma shi saiya nufi wani bangaren daban, Bai jima da tafiya ba sai gashi da sauri Yana Kiran" Baba malam! Kuzo ku gani". Da sauri suka nufi inda yake harma da wani mutum da suka Sami a gurin Kamar Mai kula da gurin ne Dan daga gefe da 'yar tiredar shi suka rankaya Habib na gaba suna bin shi tun kafin su karasa suka hango mutum a kwance Kamar marar Rai. "Subhanallahi "abinda suka gada kenan suna karasawa kusa dashi sai da suka matsa sosai suka Gane da ransa Amma Yana cikin wani yanayi, dako dako sukayi aka rasa ya za'ayi dashi matashi ne ba zefi sana'an Habibun ba saidai a yanayin yanda jikinsa yake ba alamar wahala a tare dashi. Habib ne ya matsa kusa dashi sosai ya tsuguna Yana dudduba jikinsa ko akwai alamun duka ko makamancinsa amma babu komai, shawara sukayi su daukeshi kodan ceton Rai su tafi dashi idan yaso sai su dauki hotonsa a Dora a social media wata kila a Dace. Lokacin da suka shigo Azare ana sallar insha'i directly asibiti suka nufa dashi ma'aikatan nan da Nan suka duqufa a kansa, sai gurin Sha daya Allah ya taimaka ya kawa kwakwkwaran numfashi. Sai lokacin suka nufi gida malam ya turo dalibansa guda biyu ya fada musu dakin da aka kwantar da Wanda suka tsinta din, ya basu kudi saboda abun bukata. Haka su Abubakar suka kwana da shi sai gurin hudu da rabi na Asuba ya bude idanunsa Yana kallon bakon gurin da yake ciki ga bakin mutane a gurinsa, yukurawa yayi ze tashi yqji ya kasa kansa Kamar an Dora Masa dutse, bakinsa ya bude zeyi magana yaji kwata kwata ya kasa yayi yayi Amma Sam maganar taki yuwuwa sai hakuri yayi ya zuwa bawa sarautar Allah ido.

,💋❤️

💋❤️

AUREN HUCE HAUSHIN

💋❤️ 💋❤️

✨ MAMAN FATIMAH ✨

✨PAGE THIRTEEN ✨(13)

__________Washe gari daga gidan Alhaji Jafar Abdul Hakeem da magaji suka kawowa su Abubakar abinci Asibiti, sun tausaya bawan Allah nan sosai Dan zuwa lokacin sun fuskanci baya magana Kuma jikin ma baya motsuwa yanda ya kamata, toilet ma sai da sukayi Kama Kama suka kaishi, a haka su malam suka shigo Asibitin tare dasu Malam Mudi, Basu Dade da zuwa ba likitoci suka shigo round sun tambayi menene Asalin ciwon to su dai sun fada musu Yan suka hadu dashi Dan Basu da masaniyar komai akai. Gwaje -gwaje suka rubuta ayi Masa Dan binciken lafiyarsa. Basu Dade ba suka koma gida saboda a ranar Alhaji Jafar ze shiga Bauchi suna da meeting da gwamna Amma ya bar kudade a hannun Abubakar saboda magani da sauran hidimar Asibitin. Da yamma Habib ma ya shigo ya duba marar lafiyar nasu, Wanda har lokacin baya magana. Likitoci sunyi iya nasu binciken basuga komai ba a tare dashi, sai dai rashin maganar kawai Amma Kuma Yana Jin komai da ake fada. Bayan sun Gama bashi taimakon daya kamata suyi Masa suka sallame shi, Magaji ne ya dawo dasu gidan malam, Nan dakin malam na waje aka ajeshi tunda aka dawo dashi gida malam ya dukufa da Yi Masa addu'a Dan yayi bincike akan lamarin ya fashimci inda matsalar take, har Taraba ya tafi gurin malaminsa da yayi karatu a gurinsa ya fada Masa matsalar yaron, kwanansa biyu ya dawo Azare aka dukufa da rokon Allah da maganin hausa, haka zalika Alhaji Jafar ma Yana taho Masa dashi daga wani Islamic chemist da yayi musu bayanin matsalar yaron a can Abuja. Cikin ikon Allah ba'a rufe wata hudu ba ya Fara magana sai dai idan yayi sau daya sai a wuni bai sake wata ba. A haka aka dunga bashi taimakon har Allah yasa ya dawo normal Yana magana. A lokacin ne malam ya zauna dashi da Habib suka fada Masa inda suka same shi da halin da yake ciki a lokacin shiru yayi kafin yace musu shi dai yasan wata Rana Yana gida ciwon Kai ya takura masa har ya kasa fita, jzuwa dare yasha magani ya kwanta, to tun daga lokacin bazece ga yanda akayi ba shi dai ya farka ne ya ganshi a Asibiti tare dasu a hankali Kuma ya Gane a wani garin ma yake daban ba garinsu ba. Lokacin da Alhaji Jafar yazo garin malam ya fada Masa komai yanda sukayi da Mahmud din, Alhajin yasa aka Kira shi ya Kara jajanta Masa sannan ya nemi ya fadi garin nasu a mayar dashi Dan da gani Dan manyan mutanene. Nan fa ake yinta Dan kekashe kasa yayi yace shifa ya manta sunan garin nasu akayi juyin duniya yace sai dai ko Nan gaba idan Allah ya nufa ya tuna, abinda ya tuna ma daga baya tunanin yazo Masa, haka suka hakura badan sun amince ba bayan ya tafi sun tattauna da Malam din akan lamarin inda Suke hasashen ko bacin Raine ya baro shi da gidan ya gwwmmace yayi zaman sa a Nan kafin ya huce ya nemi komawa gidan. Nan yaci bada da Zama da Malam Yana kwasar ilimi kala kala. Nan da Nan ya Zama Dan gida suka dinke da Habib duk da ze iya girmar Habib din da Kamar shekara biyu dan yayi Kamar sa'an Abdul Hakeem. Bai cika wata shida ba Allah ya kawo aikin NGOs din Nan Wanda aka sakewa makarantar fasali da tsari suka sayi wani katon fili na makudan da sunan makarantar akayi gine ginen hostel din Yara suka dauki ma'aikata suka gyara tsarin karatun saboda kwazon Mahmud har co-ordinator din Shirin Muhammad Sameer ya dauke shi aika a shiyyar Katagum local government din ya Zama shine idon su a Nan, tunda ya iya rubutu da karatu. Habib ma Yana bada gudunmawa sosai a aikin duk da Shima nasa aikin da ma'aikatar ruwa ta Nan local government din tasu. Wannan kenan.

____ Syprus.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull