Auren huce haushi complete - Chapter 12
Auren huce haushi complete Chapter 12: Auren huce haushi complete Chapter 12. Su Habib ya tarar a falon Yana karatun Alqur'ani, Abubakar Kuma Yana ta faman…
4,430 words
Su Habib ya tarar a falon Yana karatun Alqur'ani, Abubakar Kuma Yana ta faman hada Nile sat. Su duka suka amsa Masa sallamar Nan falon ya aje jakar laptop dinsa abinda bai taba kwatanta zuwa da ita ba kenan Dan duk aikin da zeyi sai dai yayi acan hotel din ya barota, amma yau dole tasa ya taho da ita nan saboda so yake ya raba dare Yana aiki shi yasa ma Kai tsaye ya nufo gidan da ita yasan bashi da matsala dasu duka biyun. Abubakar ne ya tsaya da aikin Yana kallon Mahmud Yana fadin "Dan Allah Ina ka shiga Wai bakasan kana dagawa Baba malam hankali ba? shifa yafi son daya juya ya ganka, gashi ka Kama ka rufe wayar ana ta Kira a rufe". Girarsa ta daman ya dan shafa kadan kafin ya zauna Yana fadin "cool down Mana my man Ina kake tunanin zan tafi? Wallahi aikine yayi yawa na wannan NGOs din bakaga har kayan aiki suka bani ba tun zuwan da sukayi wancan karon, yanzu haka ana koya min yanda zanyi amfani da ita laptop din ne yanda zanji dadin aikin, Bari nayi wanka sai muje gurin Baba malam din nayi Masa bayani yanda ze fashimta, sunce ma nan da sati daya ko biyu zasu kiramu zuwa babban taro da za'ayi". Tunda ya Fara magana Habib ya dakata da karatun da yakeyi yana bin Mahmud da kallo haka nan kawai yaji Kamar ba gaskiya Mahmud din ya fada musu ba, Kamar yana boye wani Abu, shifa tun lokacin daurin aurensa ya lura da yanda Kamar yake baiwa Sameer umarni a wasu lokutan sai idan ya farga ne yakan yi maza ya canza taku, sannan a watannin baya ya taba jin yana waya a kusa da dakin da suke taron abinda ya shafi makaranta lokacin yana duba wasu sabbin forms da aka kawo na Enterprinuership da za'ay a gurin Sam baisan Yana ciki ba tunda kofar a rufe take ji yayi sosai Yana bada umarnin yanda abin ze kasance harda makudan kudin da za'a kashe gurin sawo kayan sana'ar da za'a koyar harda kudin da za'a participants din tunda program din harda matasan unguwa a cikinsa duk za'a Kuma bada kayan sana'ar da mutum ya koya kyauta, tun lokaci yayi masa alamar tambaya sai dai ba wata kafa daya Bari wadda za'a fashimci komai. Bai tabbatar da abinda yaji ba Saida akayi komai Kamar yanda ya bada umarnin, ga Kuma lokuta yawa sai yayi batan dabo ka nemeshi ka rasa Kuma har yanzu baisan takamaiamai Ina yake zuwa ba duk kuwa iya kwakwarsa. Jakar ya dauka yayi gaba Yana fadin Bari na Dan watsa ruwa na fito. Da ido suka bishi har ya shige corridor din daze kaishi bedroom dinsu,kowa Yana ayyana wani Abu a zuciyarsa. Ya dauki Kamar minti hamsin kafin ya fito cikin Riga da wando na shadda Fara tas, a gaggauce ya fito ganin lokacin sallar magriba ya kawo jiki.
*** Da dare Zahra tana dakin Ammah suna Hira da Inna maimuna tana Kara nusar da ita yanayin rayuwa Sajida ta shigo da waya a kunnenta ta gaishe da innar ta Mikawa Zahra wayar tana fadin "Baffan Rimi ne yake son magana dake" Amsa tayi tare da sallama, cikin daki Inna ta nuna Mata da hannu ma'ana ta shiga ciki tayi wayar, Dan sajidar tana Mika Mata ta juya ta koma, haka Nan ta tashi duk da Bata San nufin innar na hanata waya a falon ba. Gaishe da Baffan tayi tunda Daman ya Santa tun suna makarantar kazaure sunje masa ita da Sajida lokacin da Zahrar ta zauna a kano gidansu sajidar sanda akayi musu hutun midtrem break maimakon taje Azare sai umman sajidar ta nemi Alfarmar Ammah ta barta tayi hutun a gurinta,to kafin su koma ne sukaje Rimin sumailar gurin kakan sajidar, tun lokacin ya baiwa Zahra magunguna sosai yace tayi amfani dasu har Sajida na mita ita Bai Bata irin na Zahra ba, a lokacin murmushinsu manya yayi Yana fadin "yanda aka saka rayuwarta a gaba ke ba Wanda ya damu da taki rayuwar ita akwai tarnaki Mai yawa a kanta Kuma Naga jikin nata ba wani abun azo a gani na tsarin jiki. Gaisuwar Baffa ya amsa Yana fadin "Ashe haka lamura sukayita faruwa ko Fadima? Dazu Babar taku tazo min da bayanin abinda ya ringa faruwa dake akan aurenki, yanzu haka tana Nan zata kwana saboda akwai abinda nasa ayi Miki gobe in sha Allah zatazo Miki dasu da yanda zakiyi amfani dasu in sha Allah ba abinda ze Kara faruwa dake, lallai akwai shedancin mutane akan lamarin Amma mu dauka Daman haka Allah yayi nufi, wanin Allah Bai Isa yayi maka komai ba face da izinin Ubangiji, ga Uwar taki ku gaisa". Ya mikawa Maman Sajida wayar. Bayan ta gaisheta ta Kara da yi Mata nasiha sosai itama, sannan ta fada mata gobe in Sha Allah daga Rimin Nan zasuyo ita da Babban danta Wanda some times shine direban ta idan zatayi doguwar tafiya, kafin sukayi sallama. Dakin Ammah Zahra ta shiga ta fada Mata yanda sukayi da kakan Sajida, godiya sosai Ammah ta ringa yi tana Kara jinjina kaunar da bayin Allah nan.suke yiwa Zahra dalilin 'yarsu gashi saboda matsalar Zahrar zata taso tazo har Azare. Washe gari tunda wuri Zahra da Sajida suka Gama gyaran dakin Ammah sukayi wanka sannan sukayi breakfast gurin karfe Sha daya Maman su Sajida da yayanta Ya Abba suka karaso murna gurin Sajida ba magana, dakin Ammah suka nufa da Maman Zahra tasonsu Fara shiga gurin Mama su gaisa Amma Sajida ta Hana tana fadin "A'a ki Bari mu shiga inda ya kamata idan min Gama abinda ya kawo ta sun gaisa da kowa so kike azo a zaune Mana a hana ruwa gudu". Tarba ta girma Ammah tayiwa Maman Sajida itama ba wata babba bace Dan Bata Kai sa'ar Ammah ba, an sauki Ya Abba a dakin da suke sauke bakinsu yayin da magaji ya shiga shidima dashi. Bayan Maman su sajidar ta Gama cin abubuwan da aka kawo Mata suka sake gaisawa dasu Ammah da Inna maimuna ta jajantawa Ammar abubuwan da suka ringa faruwa, ta Kuma Dora musu da bayanin da mahaifinta yayi Mata akan matsalar Zahrar inda ya bada tabbacin ko waye yake wannan shegantakar a kusa dasu yake sosai, Kuma dashi ake faduwa da tashi, kuma yace kada Wanda ya kawo wani Abu da sunan naci kona Sha yace a baiwa Zahra da sunan tsarin jiki ko na gyaran aure a barta taci sannan a kula da Koda abincin cikin gidan ne in dai ba ita Ammar ta dafa da hannunta ta Bata ba daga Nan har tabar gidan. Wata babbar leda ta dauko wadda sukazo da ita ta bude ta Ciro jarka da ruwa a cikin Mai kalar yellow na za'afaran ta dauko wani garin magani Mai laushi ta hadasu da jarkar ta mikawa Inna maimuna tana fadar. "Ga wanna ruwan addu'a ne da garin magarya zata dibi ruwan addu'ar ta zuba garin magaryar ta Sha ta shafe jikinta safe da yamma,wannan Kuma kafa da hannu kawai zata Riga turarawa sai Addu'oi da ya bada a Bata zata ringa karantawa safe da yamma". Godiya sosai su Ammah suka shiga jerawa Maman Sajida Kamar ba gobe har sai da ta ringa fadin "Haba Hajiya meye amfanin taren abinda ya shafi Zahra ai ya shafi sajida wallahi shekaranjiya data Kira ta fada min hankalina ba karamin tashi yayi ba wallahi na dauka abin ya kwaranye tunda an dauki dogon lokaci kafin a Kara maganar Auren". "Wallahi kuwa muma mun dauka na bayan da aka fasa ko matsalar namijin Aljani ne ya aureta Amma duk inda akaje da ita sai a ce ba wani iska a jikinta". Inna maimuna ta fada. Sun tattauna sosai da Maman Sajida Saida akayi sallar Azahar Sajida ta raka mamanta dakin Mama su gaisa, sun Sami kawar Mama Asabe sun hada Kai suna kus-kus bazaka taba cewa da mutane ba. Sun gaisa sajida ta fadawa Mama mamanta ce, Basu jima ba suka fito Mama ta biyosu har kofar part dinta Nan godiyar ziyarar. Sai kusan karfe uku su Maman Sajida suka juya Kano Sajida tace ita saita raka Zahra gidanta zata dawo. Tun da Mahmud ya Kira Zahra sau daya Bai sake kiranta ba, yau yaji ya kamata ya Kira yaji lafiyar ta ko banza fa yanzu tana karkashin ikonsa ne cinta da Shanta da duk lamuranta suna wuyans Kuma ai Bai kyauta ba gaskiya ace yayi burus da lamarin ta abun sai yayi Mata yawa. Sai gurin Tara na dare ya lalubo numbarta ya Kira, harta gama ringing ba'a dauka ba sai kawai ya share ya tura Mata text massage ya fada Mata Daman ya kirane yaji lafiyar ta. Tun bayan tafiyar Maman Sajida Ammah da Inna maimuna suka shiga hasashen abinda kakan Sajida ya fada na hasashen Mai yiwa Zahra bita da Killin nan duk iya nazarain su Basu gano ba sai suka.barwa Allah amma dai innar ta soke kwanan Zahra a can gurinsu tace su dawo dayan bedroom din Ammah suna wanna ita da Sajida da ita innar ya ishesu ita ko katifa sai a saka Mata a kasa ta kwanta. Hakan akayi su Zahrar suka tattaro suka duk wani Abu na amfaninsu suka dawo dakin. Kafin su kwanta Saida Inna maimuna ta saka Zahra tayi amfani da duk magungunan da Maman Sajida ta kawo Mata, wanna ne dalilin dayasa innar tace su dawo nan tunda komai na duniya Yana son sirri, duk da Hameeda ce kawai ke kwana a tare dasu Zahra Dan Salma tunda suka dawo ma Bata taba kwana a part din nasu ba. Tun Hameeda na jiransu Zahra su shigo har tayi barci. Saida Zahra ta Gama amfani da duk abubuwan da aka kawo Mata sannan ta dauko wayarta rabon data dauko ta tun bayan sallar Azahar data hau online ta duba sakonnin whatapps. Sajida da Inna maimuna Kuma sunta hirar duniya abunsu. Missed calls ta gani har hudu uku na mujiba ne sai Kuma wani daya number ce amma kallo daya tayi Mata ta gane ta waye, ji tayi gabanta ya fadi to neman me yake Mata da wanna tsohon Daren haka kawai ya dagula Mata sauran lissafinta. Fita tayi daga call history din sai Kuma taga envelope alama massage ya shigo budewa tayi sakonsa ta gani a hankali ta furta ta "Ya salam". Allah da gaske fa take jin wani irin lamari a tare da shi. Da safe ma innar ta saka Zahrar gaba Saida tayi duk abinda ya kamata kafin ta fice tabar dakin dan tun kafin ta Fara Sajida tayi waje ta Basu guri. Saida tayi wanka kafin ta fito yin break bayan sun gama ne Ammah tace Zahra taje Abbansu na kira, gyalen rigar ta yafa a kanta ta nufi gurin Abban, lokacin data shiga ya Gama break Shima, guri ta Sami ta zauna kusa da kujerar da yake Kai tana fadin "Abbana Ina kwana?" Jaridar dake hannunsa ya aje Yana fadin "lafiya kalau uwata, Ina fatan ba wata damuwa ko?" Kai ta gyada kafin tace "ba komai" "Masha Allah ya fada. Kafin yayi gyaran murya ya Fara fadin "Uwa inaga in sha Allahu jibi da yamma Zaki tafi gidanki Dan dazu ne malam Bukar ya roki wannan alfarmar saboda shi Mahmud din ne zeje wani taron da kunyar da suke aiki dashi suka shirya to Kuma yace baya son ya tafi Baki tare acan gidan ba kada abin ya Zama na magana ace ko ya gudu ne ya barki a nan, to Nima din na karbi nasa hanzarin tunda Masha Allah jikin naki yayi sauki sosai Kuma Baki bani kunya ba kin kwantar da hankalinki". "To Abba"abinda ta fada kenan tayi shiru, Mamace ta shigo dakin itama Tasha wanka sai baza kanshi take Kamar Kullum. Da barkwwnci ta shigo tana fadin "A'a bamu Gane ba, irin wannan kebewa tsakanin 'ya da uba mu ba'a neman ayi shawara damu". Ta fada tana fadada murmushinta. Gaisheta Zahra tayi kafin mamar ta gaisheta da Abban tunda ba itace da girki ba. Bayan sun gaisa ne yake fadawa mamar "Ba wani shawara muke ba wadda Bata shafeku ba Ina fada Mata ne jibi in Sha Allah zata tafi dakinta tinda Allah yasa ta warrare Kuma shi mijin nata ne zeyi tafiya shi yasa nake son ta tafi dakinta". Nisawa Mama tayi kafin tayi magana. "Kamar Yaya zeyi tafiya daga Kai masa yarinya basai ya tafi da ita ba salon ya cuci yar mutane ya lallaba ya budu ya barta tunda tsintacciyar mage ai Bata mage, gaskiya Abban Yara ka tsaya ka duba lamarin nan Mana kada fa azo ana Dana sani kaga masu iya magana na cewa keyace". Abban ne yace "ba abinda ze faru sai Alkhairi Amma Jibi da izinin Allah uwata zata tafi dakinta, tashi kije Uwata Allah yayi Miki Albarka yanda Kika yi min biyayya Ubangiji ya Baki 'ya 'yan da zasu yi Miki biyayya kema". A zuciyarta ta amsa da "Amin" Saida Abbai yaga ta fice gaba daya sannan ya dawo da dubansa gurin Mama yace "haba Rabi'a har yaushe Zaki dinga magama irin wannan a gaban kankanuwar yarinya Kamar Zahra ai Bai kamata ba ki duba kiga yanda aka dunga walagigi akan auren yarinyar nan a baya yanzu Kuma anyi aure Zaki ringa fito da maganganun da zasu iya sakata a wani Hali ai kwantar da hankali uwata take bukata ba irin haka ba, mu bita da addu'a in sha Allahu Alkhairi na hada Wanda a gaba duka sai sun gode min koda kuwa bana duniyar ne". Tunda Zahra ta shigo ta kwanta a kan sofa a nan falon Ammah na kallonta tasan kan zance dan tunda Abba ya dawo daga masallaci ya fada Mata, zancen da suke da Inna ma kenan ta shigo suka bar zancen. Da hantsin Ammah ta Kira Aunty Hasana ta fada mata. Zuwa Sha biyu tana gidan suna zaune a falon Ammah Mama ta shigo ita da kawarta ta amana Asabe wadda kwanan Nan ta mayar da gidan gurin zuwanta sabanin baya da sai a share watanni Bata zoba, Nan suka zauna akaci gaba da tattaunawa akan tarewar Zahra har Asabe ke fadin zata saka wata 'yar gusau da suke makwaftaka ta yiwa Zahra hadin kazar amare da daka shine nata Gudunmawar. Da yamma Aunty Hasana ta umarci Sajida da Hameeda da zilai Mai aiki suzo suje gidan Zahrar a gyara abinda ya kamata tunda jeren ya dan jima da yi. Sun fito zasu tafi ne Abdul Hakeem ya tsayar da Auntyn Yana fadin "sai Ina Kuma Aunty mu?" "Gidan Zahra zamuje a Dan Kara gyarawa jibi Abba yace za'a kaita kaga kuwa ai dole a shiga a duba ayi abinda ya kamata". Komai tsab suka sameshi da gani ana gyarawa Kullum dan har wani hadaddan kamshin freshner ke tashi a falon haka bedroom din Shima komai neat yake a toilet ne abin ya bawa Aunty Hasana mamaki an zuba kayan wanka masu azabar tsaba Bata Kara tsinkewa da ta janyo locker ta jikin mirror taga wasu designers din turaruka na Mata Kuma da yawa na kamfanin Al -haramain ne harda irin Wanda Zahra take amfani dasu. Ita dai Hameeda Yar kauye ta Zama a gidan Dan ko a mafarki Bata taba kawo Wanda aka aurawa Zahra, ze Kama hayar gida irin wannan aljannar duniya haka ba. A kitchen ma Nan Hameeda da zulai suka lalace komai na gurin saiya burge mutum, Nan ma Saida Auntyn taga wani fregde ash colour a cikin Dan ack din jikin kitchen din irin Mai kofa Kamar ta wadroof ko ba'a fada ba kasan kudi sunyi kuka a gurin. Burner Auntyn tasa aka jona aka zuba turarikan wuta Wanda aka hadowa Zahra daga Saudi Arabia tun wancen lokacin tunda basa komai saima Kara kamshi. Basu baro gidan ba sai kusan magariba. Aunty Hasana taso ta wuce da Zahra gidanta amman Ammah tace A'a ba inda zata so suke ace Mata tsohuwar banza idan so suke su tafi to ita zahrar ta Kira ta fadawa mijinta idan ya amince ita nata Mai sauki ne ita kuma Zahra tace lahlah a barshi kawai. Wajen goma saura aunty Hasana ta dauki yaranta suka wuce gida. Da safe Saiga Asabe da dahuwar kazar amare da jarkar zumar Mata da ta tsimi tayiwa gidan tsinke, part din Ammah ta shigo direct, bayan sun gaisa ne ta mikiwa Ammah babbar ledar data zubo kayan tana fadin "Ina Amarya tazo gashi na cika Alkawari tazo ta cinye ta bani kashin tace a koma Mata dashi zata hada Mata wani Abu dashi. Inna maimuna ce tace "ai kuwa yanzu taci abinci ta shga daki saidai a aje zuwa anjima sai taci ko gida ne sai a aika Miki da Qashin, mun gode kwarai madallah Allah yabar zaman tare". Asaben ta amsa da "Amin ai bama sai an tashi mutum ya kaiba Nima saina jira taci din ko Nan da yamma ne" ta fada tana mikewa tayi musu sallama ta nufi dakin Mama. Bayan fitarta ne Ammah ta dubi Inna maimuna tana fadin "nifa jikina Bai bani ba akan taci wanna abun Dan ni tunda ta fada jiya naji abin Bai kwanta min ba,mutuniyar da gaisawa ma sai ta kure akeyi da ita Amma fa ki duba sai wani rawar jiki take akan abinda Bai shafe ta ba ko alama, Kuma kar nice wani abun arziku sukeyi da zahrar Dan ko gaisawa saita kure, Amman ki duba ki gani yanzu sai haba haba take da Zahra. Dakin Ammah aka shiga da kayan ammar tace zata cire tsokar tabar musu kashin, hakan ne ya kasance tayi komai ta baiwa auta ya kaiwa Asaben dakin Mamar. Saida Asaben ta tabbatar auta ya fito ta kwashe da dariya tana fadin "wallahi Maman yara kinsan ta kan mugumta, yarinya har yarinya amma ta Kare a auren marar asali Wanda ko danginsa ba'a sani ba" Kwafa Maman tayi "barni kawai Asabe wallahi tun lokacin da aka dauko yarinyar nan hankalina ya kasa kwanciya, saboda babu ta inda Allah ya rageta duk abinda ake so jikin 'ya mace to Allah yayi Mata ga uwa uba yanda mazan zamanin nan suka jarabtu da son Mata irinta nasan ba karamin mutum ne ze dauke taba Ina zaune sai dai na Zama 'yar kallo ga nawa 'ya'yan a gabana, wallahi baze yuwu ba ai hankalina Bai Kara tashi ba Saida na raka Aunty Ladi gurin wani Mutum a can jos nayi Masa maganar Asma'u to cikin binciken ne maganar yarinyar ya Fado yake fada min na kyale maganar Asma'u don ba yanda zanyi da ita jikinta a shirye yake haka Shima Alhajin ba abinda zeyi tasirin da ze rabashi da ita, Amma ga wata yarinya Nan duk gidan ba 'yar da zata wuceta a sa'ar rayuwa a gurin aure Dan mijin da zata aura ba karamin mutum bane Kuma dai..... Sai kawai bawan Allahn Nan yayi shiru da bakinsa nayi nacin duniyar nan Amman yaki karasa mana zance, haka muka tasho Aunty Ladi nata zugani kada na kuskura na Bari ta auri Mai maiko duk yanda zanyi nayi Naga hakan Bata faru ba. Nayi ta fama duk Wanda zezo gidan Nan gurin yarinyar nan zezo duk kuwa da Fadi tashin da nake akan su Salma amman a banza, maganar dai daya ce Zahra, ni Kuma nayi Alkawarin badai Zahra tayi aure ta barmin Yara a gida ba,Kuma badai ta auri Mai rufin asiri ba, gashi kuwa ta Kare a Wanda ko asalin kirki bashi dashi Abu daya ya tsaya min a Rai yanda Naga gidan da zata zauna da abin yaso razani sosai Dan ba haka na zata ba, amman duk da hakan ma yayi tunda ai gidan ma Malaminsa ne ya bashi aro su zauna, Kinga kuwa karshe sai dai a Kare a yawon haya cikin Yama yamar matan alarammomi, Kuma wannan kayan da ake qafafar an saka a gidan karshen wasu kayan saidai a sayar Dan Babu abinda za'aci dasu Dan an sawo da zimmar su tafi Abuja sai gasu sun Kare a gidan Alaramma". Ta fada cikin izgilanci. ** Duk yanda Zahra taso ta kwantar da hankalinta abin ya faskara dan da gaske zulumi takeyi na yanda zata fuskanci wannan sauyin da yazo Mata a bazata Wanda Bata tab'a tunanin hakan ba ko cikin mafarki, lallai tayi zaton daga kan Mushahu komai ya kwaranye Amma sai wata matsalar ta taso wadda tafi ta baya. A kwance ta wuni duk ta tsangwami kanta Sajida sai tausarta take duk da itama tata zuciyar a kusa take Dan da gaske tana tausayin zahrar ba kadan ba. Gurin karfe biyu ne sukaji alamar Kamar anyi Baki a gidan da alama ma da dan damarsu. Sajida ce ta fito ta gaishesu zata koma cikin ne Ammah tace taje ta Kira Mama tace tazo su gaisa da Baki Iyayen Musbahu ne daga kano. Ta fita tana mamakin to meya kawo su Kuma. Tare suka shigo da mamar Dan sajidar na fada Mata ta nufo dakin cikin rawar jiki. Ciki Sajida ta wuce yayin da mamar ta zauna tana gaishe da bakin nasu Kafin Inna maimuna ta Fara Mata bayanin Maman Musbahu ce tazo da 'yan uwanta ta bada hakurin abinda ya faru Wanda ita kanta Bata San yanda akayi ba sai daga baya ake fada Mata shine tazo taji ko da yanda za'ayi a gyara matsalar tunda ta dawo hayyacinta take cikin damuwa domin kwata kwata Musbahun baya cikin nutsuwarsa tun bayan samun labarin an Aurar da zahrar, ganin lamarin nasa ba sauki ne yasa suka nufo nan Ashe har da yaron sukazo sun jima a gurin Alhaji ma kafin su shigo nan din, hakuri kawai ya basu akan aikin Gama ya Gama tunda yanzu matar wani ce ita. Kallonsu Mama ta karayi tana tambayar "Ina mamar tasa take" Hajiya Nafisa kanwarta ita ta nuna Maman Musbahun tana fadin "gata nan" "Ayya Allah sarki Hajiya sai hakuri Allah Bai nufa matarsa bace ba sai dai yazo ya duba wata tunda da sauran yaran a gidan". Mama ta fada tana kafe Hajiyar da ido. "Kayya a yanzu dai bana tunanin haka zata yuwu sai ko a gaba tunda ban taba ganin abinda Musbahu ya kwallafawa Rai ba Kamar auren yarinyar nan tunda kuwa ya rasa ta bansan Kuma lokacin da ze Kara maganar wani auren ba". Sun Dan Jima kafin Ammah ta tashi ta shiga gurin su zahra tace ta fito su gaisa da Baki zasu tafi. Jiki ba kwari ta nufo kofa doguwa rigace a jikinta kirar Bahrain Mai duwatsu har kasa blue black gyqlenta kwai ta Dora a kanta Dan Sam Zahra Bata fiye son saka hula ba a kanta Dan Sam santsin gashinta baya Bari hular ta zauna ta dunga zamewa kenan. Cikin takunta na nutsuwa ta shigo falon hade da sallama Kanta na kallon kasa ta karaso cikin nutsuwa ta zauna gefen Ammah a kasa kan carpet, tunda ta shigo suka bita da idanun kowa da abinda yake ayyanawa a zuciyarsa. "Masha Allah! tubarakallah 'yata matso kusa dani dole my son yayi kamar ya zauce da labarin rasaki ya riskeshi" abinda Aunty Nafisa ta fada kenan tana nunawa Zahra kusa da ida, jiki ba kwari ta karaso ta zauna tana gaishesu. Suka amsa jiki a sanyaye su kansu sun San dansu yayi wani babban rashin da maida shi sai nufin Allah, tunda Daman shiya hada shi da Zahrar kuma shiya raba lokacin daya so. Nan sukayi sallama suka fita cikin matukar jimami Dan da gaske sunyi rashin sirika. A daki Zahra kwanciya bayi ta rufe fuskarta da hannu biyu Batasan lokacin da hawaye ya zubo Mata ba, Wai shike nan komai ya Zama past tsakaninta da Musbahu duniya ba tabbas. sajida na kallonta Bata hanata ba Dan itama Saida ta matse, lokacin zahra na falo Mushahun ya Kira wayar ta, sajidar ta dauka yanda taji maganarsa ko rantsuwa tayi bazatayi kaffara ba kuka yake shima da idanunsa Dan abinda ya fada kawai ya karya Mata zuciya, kalamai ne na bankwana ga masoyi da da given off akan Abu, da kyar ta iya fada Masa ba zahra bace itace magiya yayi Mata dan Allah ta fito Masa da zahra yayi Mata sallamar karshe Amma hakuri kawai ta bashi tunda yanzu Zahra matar aure ce bashi da hurumin yin magana da ita.
Sun Dade a haka kowa da abinda yake sakawa a zuciyarsa nkafin su jiyo maganar Magaji Yana fadin "Ammah ga Ya Mushahu zaku gaisa yazu tafi ne". Su biyu suka shigo suka gaishe dasu Ammah a nan Inna maimuna ke fadin "kayi hakuri da hukuncin Allah kaji kada kayi fushi da mahaifiyar ka itama bayin kanta bane duk uwa bataqi ace danta yafi kowa sa'ar abokiyar Zama ba, irin wannan matsalar ta Jima tana bibiyar yarinyar Nan to munyi zaton daga kanka abun ya Kare sai Kuma ya canza salo akan mahaifiyar ka, kayi hakuri ka fawwalawa Allah komai shi ze baka wadda tafi Zahra daman Allah hukunta kai ba mijinta bane ayi hakuri". Kansa Yana kasa tunda ta Fara maganar wani Abu ya tsaya masa a makogwaro yaji Sam ya kasa magana sai Aliyu ne ya amasa da "ba komai Mama haka Allah ya nufa, Allah ya Basu zaman lafiya mu zamu koma". "To Allah ya tsare ya baka mace ta gari wadda zata maye maka gurbin Zahara'u" Inna ta fada ita kuwa Ammah kasa magana tayi dan da gaske yaran tausayi suke Bata sun kwallafa Rai da juna Amma akayi musu karan tsaye, a zuciyarta ta ayyana "Allah ka biwa yaran Nan hakkinsu duk Mai hannu a cikin Bata lamarin Nan kayi Mana sakayya da gaggawa Dan isar Annabin Rahama Muhammad s.a.w.w." Ta window zahra ta leka lokacin da suka fito daga falon kamar ance ya juyo sai ganin zahrar yayi tana kallonsa da sauri ta juya ta rufe fuskarta da hannu ta saki wani marayan kuka ta zube a gado. Su Kuma suka fita zuciyarsa Kamar zata Kama wuta dan ganinta ba karamin fami ya zamar Masa ba, har ji yayi Yana wani layi Kamar ze fadi. Magaji ne ya shigo falon Yana fadin "Sun tafi, wallahi Ammah naji tausayin Ya Musbahu sosai kinsan har gurin Baba malam yaje Amma magana daya dai kowa yake fada masa yayi hakuri, bayan mun fito ne yace na nuna Masa mijin Aunty zahrar na fada Masa ai shine suka Fara gaisawa dashi bayan sun gaisa da malam, shiru yayi sai kawai Naga ya dafe kansa Yana girgizawa, yace na hakura da zahra nasan wannan baze taba sakin zahra ba. wallahi Ammah sai Naga yana goge hawaye gaskiya Allah saiya saka musu wannan ai zalunci ne Kullum idan Aunty zahra ta samu miji sai an samu matsala". Ya fada Yana Jan tsakin takaicin.