Auren huce haushi complete - Chapter 15
Auren huce haushi complete Chapter 15: Auren huce haushi complete Chapter 15. Wata dariyar tayi tana fadin "A'a ba mefa nake nufi kawai dai...... " Sai…
4,330 words
Wata dariyar tayi tana fadin "A'a ba mefa nake nufi kawai dai...... " Sai tayi shiru. Wani zancen ta dauko Tana fadin "Zahra ki tsaya ki nutsu a gidan aurenki ki gyale kowa duk wanda ze raina Miki miji kada ki amince ko waye kuwa Koda ni da nake Miki wannan maganar, Kuma game da Hameeda ki kula sosai Dan a jiya ta nuna Miki jiya ba yau bace, jini kuma yafi ruwa kauri, Koda ta dawo tana neman Kara shiga jikin ki da wata manufar tazo, Dan Allah kiba marada kunya duk yanda ake son ganin lapses dinki kada ki bada damar hakan". In Sha Allah zan kula nagode Bestie Allah yabar zumunci. Zahra ta fada "Ameen" sajidar na ta fada, suna cikin hira akayi knocking din kofar ba'a bude ba Zahra ce Mike tana fadin "ina zuwa, tana kokarin yafa gyale ta rufe gashinta Sajida ta warce ta aje gefen ta tana fadin "haba ke kamar matar liman a daki na da Bata ja ba tayi gaba saboda an Kara buga kofar, budewa tayi Mahmud ta gani Yana tsaye ya canza kaya ya saka Riga da wando na wani yadi light brown dinkin buda yana baza kanshi sa na ibada. Matsawa tayi daga jikin kyauren ganin alamar shigowa zeyi Amma fa Saida yadan shafi fuskarta kadan sannan ya ida ahigewa ciki, tsaye tayi tana binsa da ido tana ayyana "Wai meye ne yake faman shafa mata fuska har a gaban mutane ko kunya bayaji tasan wlh sarai Sajida ta gani sai dai ta basar kawai gashi ta wani rike mata gyale ta wani barta tsurarta". Direct gurin mirror ya nufa ya zauna a Kan stool, Yana fadin "Bestien mu zuwa nayi muyi sallama naji Abdul Hakeem yana maganar Zaki wuce yau ko". Ya fada Yana murmushi, itama murmushin tayi masa tana fadar. ",In Sha Allah yau sai kano tunda Allah ya cika min burina Zahra ta shigo gidanta fine". "To mun gode kwarai Allah ya saka da Alkhairi sai munzo visiting idan madam zata dauki nauyin zuwan mu Kinga Nima sai Naga duniya ko madam?" Ya zubawa Zahra narkakkun idanunsa Yana Mata wani kallon qasa qasa. Shiru Zahra tayi tana yafa gyaren a kanta, Sajida ce tace "gaskiya Kam haka za'ayi". Tashi yayi ya Dan tako kadan zuwa gaban Zahra kamar ze hadeta da jikinsa da sauri tayi baya tana turo Baki yi yayi kamar Bai gani ba, envelope ya Mika mata Yana fadin ki Bata sskonta ne na jiya data Bari nayi niyya bazan canza ba sai dai idan bataso ta bayar, nizan shiga gurin su malam". A hankali tace "an gode madallah a dawo lfy".
"Amin to bestie sai munzo ko". Bai jira abinda zata ce ba yayi ficewarsa. Ajiyar zuciya Zahra ta sauke tana Zama kusa da Sajida Mika Mata envelope din tayi tana fadin "yaushe ya Baki kikace bakya so?".
"Jiya Mana lokacin da zamu tafi sanda wannan jikar marokan ta zubar da darajarta ta rokeshi, yanzu Dan Allah me Hameeda ke nema? wane irin rufin asiri ne Allah Bai mata ba. Amma ta lalace gurin roko? shi yasa na aje masa kudin sa nayi gaba kayan ma nace bana so su rike". Dan murmushi Zahra tayi tana fadin "Saji danger wato halin na Nan ko? To nidai gashi nan tunda a gaban ki ya bayar saiki karba". "Bude mu gani to" Sajidar ta fada. Stalling founds ne na ingila musu yawa a ciki kallon kallo sukayiwa juna kafin Sajida tace wallahi bestie akwai kukus a shinkafa zakice na fada Miki, Wai kuwa kin tsaya kin Kare guyn nan kallo kuwa?". Kinga ya Miki Kama da Wanda baida abinyi ko wanda ya tashi a cikin rashin wadataccen ilimi da mugu? Dubi muhallin daya ajeki, ance malam ya bashi gidan sai kungiyar da yakewa aiki sukayi renovation din gidan ki kiyasta nawa yaci gurin aikin kinsan da an kashe abinda yafi kudin ginin duk yi Masa akayi? Ki tuna Nan fa ba garinsu bane ance bako ne kuma yaki fadin garinsu anyi magana ance yace ya manta komai sai a hankali idan ya tuna hankali ze yarda da hakan? Kuma kina tunanin Abba ze daukeki ya bashi ba tare da yasan wani Abu a tare dashi ba? Kiyi nazarin abin Mana ni dai ina fada Miki kibi komai a hankali kuma yanda na fashimci wani Abu a maganar da Kika fada min kinfa kamu da son guyn Nan tun sanda kuka hadu ba tare da kin sani ba, Kuma Shima Naga yanda yake shige Miki ko kunya ta Bai jiba kinsan sai a hankali kawai kwanan Nan labarin ze sauya irinsu basayi da wasa fa". Ta garasa fada tana dariya kasa-kasa. Suna cikin tattaunawa Kira ya shigo wayar sajida "Ya Abdul Hakeem ne" ta fadawa Zahra kafin ta daga. "To" Kawai tace ta kashe Kiran tana fadin.
"To bestie ya Abdul Hakeem Yana jirana Wai a she shine ze Kaini nifa daya fada na dauka da Wasa yake lokacin da Ammah tace Magaji ko Malam Bala dureba zasu kaini sai kawai yace su Bari Shima Yana son yaje kanon Sai ya tafi Dani". Dariya Zahra tayi tana fadin "idan tayi wari munji batun, yanzu ba fa Naga Ya Abdul Hakeem Yana dama dama dake ba bai fada min ba Amma zakice na fada Miki Ina ga target dinsa kenan yau yake son ya yad'a manufarsa shi yasa yayi Riga malam masallaci yace Wai daman kanon zaya". Kin magana sajidar tayi sai murmushi kawai. Zahra tace "bestie ko dai komai ma ya kankama ne ban sani ba Ina shirme?". Kafin sajidar ta Bata amsa wani Kiran ya shigo da sauri ta dauki jakarta tana fadin "To bestie sai gani na gaba Allah ya bada zaman lafiya ya kade fitina, sai anyi ta hakuri kafin komai ya dai daita ki kwantar da hankalin ki zakiji dadin Zama dashi in Sha Allah". Har gate ta rakata babbar ledar dake hannunta ta Mika mata tana Mata addu'ar sauka lfy. Amsa tayi tana Mata godiya ta bude gate din ta fita, ya Abdul Hakeem Zahra ta gani a mota a zaune cikin mamaki tace. "Ya Abdul Hakeem daman kana Nan waje Amma baka shigo ba?". Fitowa yayi ya karaso gurinsu Zahrar ta gaishe shi, sannan ta juya ta koma ciki duk zuciyarta ba Dadi Kamar ta Hana sajidar tafiya amma ba hali.
*********
Mahmud Yana fitowa direct Famfon shanu ya nufa tunda lifan din Habib a gurinsa ya kwana, tun jiya daya karba da yamma Bai koma unguwar ba. Lokacin daya karasa yayi arba da motar Sameer wani murmushi yayi Yana fadin. "magulmaci kawai". Kafin ya shiga Saida suka dinga gaisawa da jama'a anata Allah sanya Alkhairi, Binya ya tambaya Ina Habib yace yaje Kai wani sako da malam ya tura shi ya Kai gidan sarki. Gurin Malam din ya shiga shi dasu Sameer ya samu suna magana da malam din Yana shigowa da sallama mlm din yace. "Yauwa Dan halak yanzu nake cewa bazaka jima ba zaka shigo, mutanen ku ne sukazo da wasu ayyuka gasu nan dai zasuyi maka bayani. Ya wajen iyalin naka!?"
Dan sosa kansa yayi Yana Dan sadda shi qasa yace "Lafiya kalau tace a gaisheka" . "Masha Allah. Allah yayi Albarka" Gurin su Sameer ya juya suka gaisa, kafin suka fita zuwa inda suke meeting. Stepdown training zasuyi da school base management committee Basu tunda tsarinsu ya koma sun bin tsarin makarantun government ne sai kuma officially da suka gayyaci Mahmud zuwa gurin taron da zasuyi a Lagos nan da kwanaki biyar masu zuwa. Bayan Gama taron Sameer ya dauki Mahmud a mota suka fita hotel din suka nufa a hanya Sameer ya kalli Mahmud Yana fadin "yallabai meye labari naga text dinka komai an sawo zuwa anjima motar zata karaso amma sai nake ganin kamar kayi tafiyar nan da ita tunda zaka jima a can Kuma kaga duka kwanan ta nawa zaka tafin baka ganin abin ze iya Zama na surutu ko ace ma guduwa kayi amma dai ya kake gani?". Dan Jim yayi kafin yace. Tafiya da ita ba shine solution ba na dauketa na kaita Ina ko Kuma nace Mata wanene ni Nan nace Lagos zani can Kuma taga sabanin hakan ya kake tunani ka tuna fa she's educated, zatayi saurin gane komai ni kuma nafi son na Gina soyayya ta a zuciyarta ba tare da tasan who I am ba, I hope you understand?". Kai ya gyada Masa alamar eh. Sun Dade suna tsaya yanda program din ze kasance da abinda za'a batar da abinda za'a kashe a makarantar zuwa lokacin da zasu dawo suna cikin aikin direban daya dauko kayan ya Kira Sameer ya fada Masa ya shigo Azaren ya fada Masa inda yake tattara komai sukayi suka wuce gurin da direban yake, Sameer din ne ya shiga gaba direban na binsa a baya har zuwa gidan Mahmud din. Mai gadi ya taya direban sauke kayan, kayan abinci ne da sauran tarkacen girki hatta nama da kifi daga can aka kawo kayane masu matukar yawa. Ciki Mahmud din ya shiga tararwa ya yi tayi Baki har su zulai da sahura, a tsaitsaye suka gaisa yayi gaba zuwa bedroom dinsa. Ganin idon su zilan yasa zahra mikewa tabi bayansa dai dai lokacin Kuma Yara suka Fara shigon kayan masarufin da aka kawo, ganin zahrar Bata Nan yasa su sahura shiga dasu store din kayan abincin suka hada da wanda Abba yasa suka kawo dazu da kayan gara su gireba dasu dublan da alkaki. Sunyi mamakin yanda yara ke shigo da kayan abincin basu Kara Shan mamaki ba Saida aka Fara shigo dasu Nama da kifi ga drinks Nan ko ba'a fada ba Wai ance ido ba mudu ba amma yasan kima sun San kayan na manyan kudi ne, ko wacce da magana a bakinta Amma bata furta ba. Zahrar na shiga corridorn ta waske zuwa nata dakin.
✨✨ ✨✨
AUREN HUCE HAUSHI
✨✨ ✨✨
💎 PAGE TWENTY ONE 💎 (21)
...............…... Sai da su zulai suka gyara Mata komai yanda ya kamata sannan suka gyara parlourn,lokacin da Mahmud ya fito bedroom dinta ya nufa baiyi wani knocking ba ya tura kofar a gaban gado ya ganta ta cire bedsheet din ta zubo da pillows din da alama wani Abu take nema sallama yayi mata cikin muryarsa Mai nutsuwa yana kallon ta, cikin takunsa na cikakken namiji ya karaso Yana tambayarta "lfy me kike nema ne haka Kika birkita gurin haka?". Jiki sanyaye tace Masa "wayata nake nema tun safe banganta". Dan matsowa yayi kamar ze tayata dubawar Yana fadin "Kuma tun safe Baki ganta ba Kuma Baki nema ba sai yanzu, to su waye suka shigo dakin ne?". "Shiru tayi kawai tunda tasan daga ita sai sajida ne a dakin Kuma tun bayan tafiyar ta ko Baki ne 'yan ganin daki Bata ahigo dasu Nan Dan gani take yaushe za'a dinga shigo da jama'a har dakin barcin mutum su dai dayan tunda ba a ciki take ba. Dagowa tayi ta Dan kalli gefen shi da gani wanka yayi ya canza kananun Kaya tana mamakin sa ita tunda take ganinsa Bata taba ganinsa da shiga irin wannan ba Kullum manyan kaya ne Amma daga jiya zuwa yau ya zamar Mata wani daban, Sam ba wancen bane take gani. Kamar ze wuce ta bayanta sai Jin Hannun Mutum tayi ya zagayo ta cikinta ya manna bayanta a kirjinsa ya kwanto da kansa dai dai saitin kunnenta iska yadan hura Mata kadan tare da hucin numfashinsa kafin yace. "Ki daina wahalar da kanki tana gurina tun safe na dauka, nayi mamakin da baki nemeta ba sai yanzu? Na cire sim din saboda Naga wani sakarai ya kiraki da number din to nasan ze iya bibiyarki tunda naga bashi da taushidi ko kankani Bai hakura ba da hukuncin Allah so yake da karfi saiya kwato abinda ya kubce masa". Kasa ko kwakwkwaran motsi tayi sanda yake jero Mata maganganun. Amma jin ya Kira Musbahu da sakarai marar taushidi yasa taji Zuciyarta ta wani baci, idan beji tausayinsa na abinda ya faru ba ai baze Masa bita da kullin irin wannan maganar ba, shida ya tsunci dami a kala har ya samu bakin magana irin haka. Nan da Nan taji ta samu wani courage wanda Bata San tana da shi ba, cikin muna bacin rai ta fara kokowar raba jikinta da nasa tana fadin. "Wallahi Musbahu ba sakarai bane, ba Kuma marar tauhidi bane,dan ya biyo abinda yake halalinsa amma kasan dai Banda qaddara ba abinda ze rabani dashi, dashi muka tsara planning na rayuwarmu Amma lokaci daya ka rusa Mana budget din mu ka yarda da aurena da aka baka Kuma wallahi tunda nake dashi bai ko taba rike ko hannuna ba, amma Kai kuwa fa ranar Dana fara ganinka a duniya dame ka Fara min bada rugumata ba?" Kai kenan baka da aikin yi sai tabawa mutane jiki ...... Bata karasa fadar abinda tayi niyya ba taji ya hade bakinsa da nata cikin zafin nama Yana ladabtar da bakin nata da harshensa, dayan hannun Kuma yayi Mata wani irin riko bana Wasa ba dayan Kuma yana yawo dashi a ilahirin jikinta cikin wani irin sarrafawa Mai zafi. Wata irin tsuma jikinta ya kama ga hawaye kamar na lalataccen famfo sai zuba suke ba bakin kuka sai mutsu mutsu take Amma ko a jikinsa wajen sau uku ana Kiran wayarsa tana tsinkewa, yayi biris da Kiran Kumar baya ji, sai da ya tabbatar da ya ladabtar da ita yanda yake so ya saketa, kan bed ta fada tana shashhshekar kuka hannunta daya yana Kan lebenta dake Mata zafi haka ma kirjinta zafi yake Mata ga gaban rigar ya farke Mata ita.
Kafarsa daya ya doro Kan gadon dayar tana kasa ya Fara fadar maganarsa hankali kwance kamar bashi bane ya Gama yamutsa Mata jam'iyya yanzu ba cikin mugunta. "Wallahi na Kara Jin wannan sunan a bakinki ko magana makamanciyar irinta saina shayar dake ruwan mamakina, an fada Miki ni lusari ne da har Zaki tasani gaba kina fada min rubbish ne? an rusa muku budget din sai kuyi duk abinda zakuyi, an fada Miki Nima son abin nakeyi ne? da har Zaki tsaya kina min rashin kunya akan wannan lusarin Mai karairaya kamar mace,ke yanzu wannan har wani namijin arziki ne da ze iya dake? wallahi da kinyi tsautsayin aurensa da kin Gane Baki da wayo, idan Kika Kara gigin fada min magana makamanciyar irinta zan Baki mamaki wallahi, , har kike wani zakewa kina fadawa mutane magana, kice tak akansa billahil Azeem sai kin Raina kanki a dakin Nan saina banbance Miki tsakanin namiji da muna maza". Yayi tsaki ya juya abinsa cikin takunsa na ingarman namiji ya fice daga dakin zuciyarsa kamar zatayi bombing. A yanda su zulai sukaga ya fito Saida abin ya Basu tsoro kallon kallo suka shiga yiwa juna, sahura ce tace. "Zulai bakiga yanda Mai gidan nan ya fito bane? Allah yasa ba mutuniyar taki bace ta taboshi Kinga ai ba haka ya shiga ba". Zama zilan tayi tana fadin "waya sani sahura muna Nan tare dake, nifa shi yasa nace ba zanzo ba yau amman Ammah ta matsa akan sai nazo na Gane mata lafiyar ta,tun safe wayarta idan an Kira Bata shiga". "To Kinga kuwa dole ki dubota ki gani ko Lafiya ya fito a haka kofa a dawo lfyr mu bai amsa Mana ba". Jiki ba kwari zulai ta nufi bedroom din Zahra ganin zilan ta shige cikin corridor sahura ta Ciro wayarta Nokia ta Kira Mama. Ba bata lokaci ta dauka kamar jira takeyi ta shiga labarta mata abinda ta gani tun daga kan kayan da suka Zuba store har fitowar Mai gidan yayi da alamun bacin Rai a tare dashi, to kawai sahurar ke fada alamun wani Abu mamar take fad'a Mata sannan sukayi sallama. Sai da ya fice harabar gidan ya Ciro wayar daga aljihun wandonsa ganin Sameer ne yasa ya Maida wayar ya nufi inda Sameer din yake zaune cikin mota, Bai Masa magana ba, zagaya yayi ya shiga motar yana fadin "let's go" Ganin yanayin daya fito ya hana Sameer din korafin barinsa a waje baice ya shigo ba, dan kwantar da kujera Mahmud din yayi ya kwanta yasa hannu ya dafe kansa da gaske Sara Masa yakeyi lokaci lokaci Yana Dan Jan tsaki, Sameer dai be tanka Masa ba yasan a kusa yake, sai da sukayi nisa da gidan Sameer din ya Dan juyo yana tambayar. "Ina muka nufa yanzu nifa na gaji ga yunwa Ina ji kace muzo gida muci abinci Kuma ka watsar dani a mota inaga ma sai da ka rage zafi ni in Nan Ina hamma ka shanyani". Ya fada Yana Maida hankalinsa a titi. Tsakin ya Kara yi Yana dagowa daga kishingidar da yayi Yana duban Sameer din "Allah ya shiryeka ka dauka kowa ma irinka ne Wanda baya iya kauda Kai a Kan Mata? Muje can hotel din kayi order abinci kaci tunda bani na gayyato ka ba cewa nayi ka dorowa mota kayan Kai Kuma sai gurin jibi kazo, to bansan wane kinibibin ya kawo ka ba ka bar yarinyar mutane da ciki kana gantali". Ya karasa maganar Yana hararar Sameer din. Dariya yayi Yana "fad'in easy man bani na kar zomon ba rataya aka bani, waya fada maka lamarin su da sauki? bakaji abinda Abbanta ya fada maka ba? ai da yace sai ana hakurin da gaske ne Zama dasu Saida hakuri". Wani sakaran kallo Mahmud din ya aikawa Sameer da shi. "Ka wani zaqe kana ta zuba wani Abu nace maka tayi min ne? da kaketa faman fadin maganganu haka tsabar saka ido kawai, gobe ka tattara ka koma inda ka fito tunda ba gayyato ka nayi ba da zaka dameni da kananun maganganu zan shigo da kaina kanon ba ai ba bakuwa ta bace ba". Ya fad'a da gaske Yana Bata rai. Shiru Sameer din yayi ganin da gasken koma Nene yayi touching dinsa sosai. Suna shiga harabar hotel din kafin Sameer ya Gama parking a parking lot Mahmud ya bude ya fice abinsa Yana picking din wayarsa da aka Kira.
******Tunda zulai ta doshi kofar bedroom din Zahra take jiyo Kamar shashhshekar kuka, hannunta har rawa yake gurin bude kofar Dan ba maganar knocking, rubda ciki ta sameta tana faman shashhshekar da sauri ta mayar da kofar ta rufe ta karasa gurin zahrar da sauri tana Fadin. "Subhanallahi uwar dakina me zan gani haka me kikayi masa? Dukanki yayi? Dan Allah kiyi magana Kona Kira Aunty Hasana ne sai ki fad'a mata ko na Kira Miki Ammah". Kai ta girgaiza mata alamun a'a, "to ki fad'a min ko zan iya yi Miki wani abun Mana". Saida kukan ya lafa Mata sannan ta yunkura ta tashi zaune ido zulai ta zuba Mata ita ba yarinya bace kallo daya tayi Mata tasan da wata a kasa ganin yanda take a yamutsa ga labbanta sunyi jajir abinka ga farin Mutum ga gashin kanta duk gyaran ya turje. Zama tayi kusa da ita sai a lokacin taga gaban rigarta a yage Hannun bra dinta guda a tsinke. Kai kawai zulai ta dafa tana Fadin "mezan gani haka ni zulaihatu! Haba Zahra'u me yayi zafi haka ai sai kisa ya illataki a banza, gardama kika yi Masa yayi Miki haka?" Cikin shashhshekar kuka tace "A'a maganar Musbahu yake min shine ya Fadi Abu marar Dadi a kansa shine kawai Dan na mayar Masa da amsa Nima yayi min haka". Ta karasa fad'a tana kuka.
Kasake zilai tayi tana duban zahrar kafin tace "Haba Zahra'u da wayonki da hankalin ki Zaki rinka irin wannan abun har yaushe Zaki ringa maganar wani namiji a gaban mijinki har kiyi ikirarin fad'a Masa magana marar Dadi akan shi ai yayi Miki kadan wallahi idan wani ne yau basai gobe ba saiyayi Miki kaca-kaca yanda ko sunansa ba Zaki Kara fad'a a gabansa ba, kada ki kuskura ki Kara irin haka Zaki ragewa kanki kima da daraja a idonsa, duka yaushe akayi daren da shashshawa zata Bata,Ina cewa jiya aka kawo ki amma ace an Fara da haka kinga abin baiyi kyau ba ko kadan, yanzu ki tashi ki shiga kiyi wanka da ruwan dumi zanje na cewa sahura kina wanka ne, mu tafi kawai tunda nasan halinta Abu kadan zata fara yaya tashi tunda nasan badan Allah ta biyoni ba dan Saida na fito harabar gidan ta biyoni. Sallam zulan tayi Mata Tana Kara tausarta akan ta ringa tauna irin maganar da zata ringa fada masa.
Cikin karfin Hali ta Mike ta nufi toilet da gaske ya tsumama mata jiki ta jima a toilet din tana kuka maganganunsa sun Mata ciwo matuka har wani gori yake Mata Shima ba sonta yake ba, to an fada masa ita son nasa take har yake wani Mata wulakanci, ita ta rasa a Ina ta kuskuro ne take haduwa da fitintinu daga wannan sai wancan? "Astagafirullah". Ta fada a zuciyarta, alwala ta dauro ta fito ba wani kwalliyar azo a gani tayi ba duk ranta a cunkushe ga 'yar wayar da zata debe mata kewa ma ya dauke, a ranta tace "mugu kawai wani sumumu kasam dashi Kamar na Allah Nan kuwa dan duniya ne Mai lasisi". Tana cikin saka kaya taji karan bell alamun Baki a gurguje ta ida yafe gyalen rigar ta dan fesa turare tayi gaba.
***** Sai Bayan sallar magriba su zilai suka karasa gida dai dai lokacin Magaji ya fito da manya warmers a hannunsa sai Autan Ammah da basket a hannunsa Shima, zasu kaiwa zahra abincin dare. Suna shiga zilai ta wuce part din Ammah ta fada Mata sun dawo ita Kuma sahura ta nufi nasu bangaren sai da zulan ta shige part din sannan sahura tayi wuf ta shige sashen Mama. Salma kawai ta samu a falon tana kallon series na India ko arzikin amsa sallamar sahurar Bata samu ba sai wani kallon banza tayi mata tana Fadin "lafiya Kika wani shigo afujajun haka?". Kafin sahura ta samu zarafin Bata amsa Mama ta fito daga bedroom din ta tana Fadin Kamar maganar sahura nakeji?" Cikin azarbabi tace "nice Mama mun dawo". Ta fada tana Zama a kasa kan carpet. Cikin kwarewa da munafurci ta shiga korawa mamar bayanin abinda ta gani harta Kara da cewa. "Anya Mama yaron Nan kuwa Babu abinda yake boyewa kin ganshi kuwa? Gaskiya wallahi baiyi kama da fakiri Mai neman abincin yau da gobe ba, kayan abincin da muka zuba a store din wallahi ni wani abin ma ban taba gani ba hatta madara wannan manyan gwangwwnaye sunfi ashirin Nama kuwa na kaji kawai sun Kai hamsin Banda na rago Banda na shanu Banda kifi Allah Mama Saida muka cika freezer din cikin kitchen din ga lemuka da ruwa Kamar banza ga...... Bata Bari ta garasa ba ta daga mata hannu "bar shi kawai jeki zan nemeki". Mikewa tayi tana Fadin "a huta lafiya Bari naje nayi sallah naji ana Kiran insha'i". Ta fice. Tunda ta fita Mama ke jijjiga Kai tana kwafa, Sam hankalin salma na can gurin kallon ta Bata damu da abinda su mamar suke ba, Saida mamar ta Kira sunanta sannan hankalinta ya dawo Kan mamar tasowa bayi ta dawo kusa da ita tana fadin. "Mana menene Naga kamar ranki a bace,?". Tsaki tayi tana fadin. "Anya Abbanku da Asma'u ba ninkeni sukayi a baibai ba kan auren yarinyar Nan? ni daman tunda naga daga b'angaren Asma'u da 'ya'yan ta da 'yan uwa ba wata turjiya nasan da abinda suka taka bakiji labarin da sahura tazo min Rashi ba?". Kai salmar ta girgaiza alamar bataji ba, Nan Mamar ta shiga fad'a mata abinda sahurar ta fada Mata, Nan da Nan hankalin salma ya tashi ta shiga fadar "ai laifinki ne Mama Nan nazo na fada Miki naga wani inaso a gurin Baba Malam Kika dinga zagina duk yanda naso ki fashimceni shi ba irin wanda kike tunani bane ni naga abinda na gani Amma Kika shafawa idanunki toka kikaki saurarena ai gashi nan duk fafutukar ki ta tashi a banza ko yanda kika fada min gidan yake ai kinsan da wata a kasa". Ta fad'a tana share hawaye, Nan da nan hankalin Mamar ya Kara tashi idanunta sukayi jajur, cikin kaushin murya ta Fara fadar. "Ni za'a yiwa haka wallahi sai dai kowa ya rasa Dan wannan auren sunansa matacce dole ya saketa ko baya kaunar Allah ai indai Ina raye yarinyar Nan sai dai kyanta ya Kare a banza ba dai tayi aure inda zata huta ba ita da hutu sai dai tayi nata gaji da aiki, duk wani haske na rayuwarta saina dusashe shi Bari ma ki gani". Ta yunkura ta Miki ta nufi bed room dinta tana lalubar wayarta. Ayi hakuri ba editing Naga kwanaki wata na fadar kada a karanta rubutun ba kyau.
✨ ✨ AUREN HUCE HAUSHI
✨ ✨ Story & Written By
Maman Fatimah.
Godiya da yabo sun tabbata ga Allah s.w.a, salati da daukaka da Amincin su tabbata ga shugaban mu Annabi MUHAMMAD s.a.w.w.
Page twenty two. ( 22)
📖🖋️
________Mahmud Bai bar cikin hotel din ba Saida yayi sallar insha'i, cikin gari ya koma gurin malam lokacin sun Fara karatun dare da maza manya Kamar Yanda suka Saba, shima littafin ya dauko na Riyadussalihinp ya zauna daukar karatun sai gurin takwas, bayan jama'ar sun watse ya rage daga malam din sai Mahmud da Habib. Ganin Mahmud din ya zauna malam yasan da magana, Saida Habib ya gama gyara littatafan kusan aikinsa ne shida Abubakar, bayan fitar Habib din kusa da malam din Mahmud ya matso Yana Fadin Baba barka da dare". Cikin sakin fuska malam ya amsa Masa Yana Fadin. "Ya akayi ka zauna har wannan lokacin baka koma ba kasan ba sabawa tayu ba itama ya kamata a ringa kula". Kai yadan Sosa Yana Fadin in Sha Allah yanzu zan tafi daman na tsaya ne Ina son muyi magana". "To Babu laifi ina saurarenka". Qara sadda Kansa yayi Yana Fadin. "Daman game da maganar tafiyar da zamuyi ne nace ko za'a samu wadda zata zauna da yarinyar Nan ne?". Gyaran murya malam din yayi kafin yace