Auren huce haushi complete - Chapter 14
Auren huce haushi complete Chapter 14: Auren huce haushi complete Chapter 14. Takowa yayi a hankali har zuwa inda take zaune, har lokacin Kuma Bata daga…
4,175 words
Takowa yayi a hankali har zuwa inda take zaune, har lokacin Kuma Bata daga Kai ta dube shi ba farar ledar dake hannunsa ya aje kusa da ita ba tare daya tanka Mata ba ya juya ya nufi kofa yana juya baya ta dago da sauri ta kalli bayansa kananan Kaya ne a jikinsa sabanin dazu da yake sanye da wani lallausan yadi fari tas da hula, sai taga Kamar yafi kyau yanzu akan dazun, kananun kayan sunfi karbarsa akan manyan da yake sakawa, hannun daya saka ya Kama handle din kofar idonta ya Kai taga hannun wani fresh dashi Kamar Mai rayuwa a kasashen sanyi. Ganin Kamar ze juyo ne yasa tayi saurin kauda Kanta Dan kada ya kamata da wadannan idanun nasa tana kallonsa. Kofar tabi da kallo bayan ya fice a hankali ta sauke ajiyar zuciya da gaske fa mutumin Nan yana Mata wani irin kwarjini, ga wani tsare gida naba gaira ba dalili da yake saiya karta Abu ya wani maze Yana Shan kamshi. Karan bude kofar ne ya dawo da ita daga tunanin data shiga na wucin gadi, kusa da ita ya zauna daf da daf dan ji tayi Kamar numfashi daya suke sharing dashi, a hanakli yasa hannu ya dago fuskarta data Kama idon ta rufe, a zuciyar ta tace "na bani ni Fatima shi Kuma kome faskar Nan tawa tayi Masa? shi dai ya taba jikina kawai ya sani, muryar shi ta jiyo cikin deep voice yana fadin "Pls open your eyes and look at me mana". Kai ta shiga girgiza Masa alamar a'a. Shi abin nata ma mamaki yake bashi, a ranar da suka samu wannan arangamar da ita soron gidan Baba malam yaga ta rufe idanu ya dauka ko tsabar razanar zata fadi ne. Amman sai yaga abin na neman ya Zamar Mata jiki indai zata ganshi to kuwa sai ta rutse idanu Kamar taga wani abun tsoro, a haka zasu rayu da ita ai baze yuwu ba gaskiya dole yayi wani abun daze cire koma meye yake haddasa Mata hakan a tare dashi. "Ok Ashe zamu kwana a haka kenan tunda bazaki bude idanun ba, ko Kuma wallahi na shayar dake mamaki yazun nan". Shiru tayi Masa kirjinta Yana fat, fat da sauri kusancin yayi yawa duk ya kanainaye ta. Batayi zato ko tsammani ba taji harshensa akan fata idonta Yana lasa yana busa mata iskar bakinsa kamshin Lister mint mouthwash Yana dukan fuskarta ciki Shirin fita hayyaci tayi baya da sauri ta fada kan gadon da baya idanun nata tar akan fuskarsa da yana mata wani Yana Mata wani kallon kasa - kasa nan da Nan taji tsikar jikinta tana tashi sai hawaye zurrr... "Why! meyasa? Ai da sai ki barni na kwashe abinda yake hanawa kina kallon nawa Mana, oya tashi abinci zakici bazaki kwanta da yunwa ba kisa na Fara karya Alkawarin dana daukar Iyayena na kula dake,dan kowa amanarki yake bani da jaddadda min na rikeki da amana da gaskiya cikinsu harda bestien mu kuwa". Ya fada a kasalance Yana kashe Mata ido. Sai Kuma ya dan zamo kadan ya dauko plate Wanda ita Sam Bata San lokacin daya ajesu a gefenta ba, ledar ya bude wani kamshi ne ya doki hancinta Mai shegen Dadi kaza ce wani irin gashi akayi Mata Kamar na tsire da vegetables a ciki ya juye Yana fadin. "Oya tashi kici kafin ki kwanta kinsan yunwar dare tana kawo ciwon ulcer,kada ta kamaki ace Ina barinki da yunwa ni d'an malam gara na Kara kiwataki duk wanda ya ganki ace Masha Allah! Kamar ba matar Almajirin Baba malam ba". Ya fada da alamar zolaya a karshen maganar tasa. Itafa Yana Bata mamaki wallahi zata iya rantsewa idan aka saka Masa hannu a Baki baze ciza ba amma dubi yanda ya wani zage yana magana Kamar bashi ba. Ganin da gaske zata Bata Masa lokacin shi Kuma Yana da abinyi da yawa yasa ya matsa sosai kusa da ita ganin Yana nema Kara mannata a jikinsa yasa tayi saurin tashi zauna tana kikkibta idanu tana kallonsa. Da hannu ya nuna Mata plate din, cikin Rashi kuzari a maganar tata tace Masa "na koshi bazan iyaci ba kaina ciwo yake". Ta fada murya a shagwabe ga daman tasha kukanta. Sai yaji ta Kara bashi tausayi abun ne yayi Mata goma da ashirin. Cikin sigar lallashi yace. "To kici ko kadan ne saina kawo Miki magani kisha kinji" Ya fada yana Kara nuna Mata plate din da idonsa, kadan taci duk a takure shi har mamaki take bashi a yanda yake ganinta ai ta wuce ace tana jin irin wannan kunyar ko tsoron irin haka, tunda da gani wayayya ce ta ajin karshe, ga Kuma yanda ta ringa ta'ammali da samari kala kala, a yanda yaji labari fa sau uku ana fasa aurenta Wanda ba Wanda yasan dalilin hakan, yasan kawai rainin hankaline irin na Mata, yanda zamanin ya Zama abinda ya Zama Amma dai ai gaskiya zatayi halinta komai daren dadewa. Ba laifi ta danci tace masa ta koshi tana kokarin fitar da kwalla. A zuciya yayi yana jinjina saurin kukanta Kamar wata 'yar goye Sam yaga kuka ba wani wahala yake Mata ba, tana kuka tun abun kukan Bai Samu ba to idan ya samu yaya za'ayi kenan?. Kwashe kayan yayi ya fita dasu Bai jima ba ya dawo da p.c.m tablet a hannunsa da ruwa marar sanyi, farm fresh yogurt ya Fara zuba Mata ta karba Tasha sosai dan tana sonta sosai lokacin tana Jos har kamfanin take zuwa ta sawo musu, tayi Mata Dadi sosai sanyin moderate ba Mai cutarwa ba. Saida ya tabbatar da tadan samu relief kafin yace Mata. "Ki tashi ki canza kayan jikinki ki kwanta idan kikayi barci kan ze daina ciwon, in Sha Allah, Kuma na fada Miki tun kina Asibiti ki rage damuwa Bata maganin komai sai Karin matsala Amma idan Kika hakura komai Mai wucewa ne Zaki sameni fiye da yadda Kika tsammmata kiyi hakuri komai da Kika gani hukuncin Allah ne ba Wanda ya Isa ya canza idan Ina tunani akan kaina na duba yanda connection din ya faru nasa ba Wanda ya Isa ya tsara haka sai Allah Dan haka ki Barbi abinda ya Baki Koda bakya so kinda ance wani hanin ga Allah baiwa ne tunda gashi ya Baki Dan malami sukutum ai tsakaninki da Allah sai godiya". Ya fada Yana kafeta da idanunsa masu sakata ladabin dole. Kai kawai ta gyada Masa, ba baka sai kunne, mikewa yayi da cup da robar farm fresh din a hannunsa ya nufi kofa a hankali ya juya very lockly suka hada ido kashe Mata ido daya yayi Yana Dan murmushi Wanda Batasan Kona menene ba, sannan yace Mata "good night". Yaja kofar wasu sabbin hawayene taji Kuma ita harga Allah bada niyya ba jinsu kawai tayi hakika tana tausayin kanta, da gaskiyar masu iya magana da suke cewa cusa Kai ba kwarjini yawa ne yau ta gani ganin idonta Wai ita Amarya ce wadda zayati kwanan farko a gidan miji. "Ya illahiy!!! Wannan wace irin ranace haka? Yanzu da Musba.... Astagafirullah". Ta fada da sauri tasan tunanin wani irin haka haramun ne da aure a kanta. Ta jima a gurin tana sakawa da kwancewa Amma dai duk inda ta juya amsar daya ce aikin Gama ya riga ya gama sai hakuri da zubawa ikon Allah ido Dan shine alimil gaibi.
Tunda Mahmud ya shiga nasa bedroom din ya kasa samun nutsuwa Banda yayi namijin kokari ya kauda kansa da lallai sai ya rage zafi gaskiya idan yayi haka baimata adalci ba. Dan shi a nasa bangaren kamai ya gama zamar Masa daidai, saidai ita uwar gayyar batasan wainar da yake toyawa ba dan idan da abinda shi Kuma Bai lamunta ba yayi Mata dole yafison komai Daren dadewa taso shi da muradin kanta yafi son ya koyar da ita yanda zata soshi fiye da kowane da namiji data taba so a rayuwarta, ba Kuma ya son tasan koshi waye bama ita ba kowa ma dake tare dashi a nan, yafi son ya Gina kanshi a gurinta a wannan matsayin na yanzu. Wanka yayi ya saka pyjamas dinsa farare sol nasu laushi, yana jinsa cikin watan irin nutsuwa, maimakon ya kwanta sai ya dauko laptop dinsa ya dosa aiki sai gurin biyu da kwata ya ture computer din ya tashi ya nufi kofa ya fita dakinta ya nufa dakin zahrar yana zuwa yana turawa yaji kofar a bude Kuma dakin da haske yayi zaton ko barci ne ya dauketa tabar wutar Mai haske a kunne. Yana turawa ya ganta akan sallaya tayi sujuda Amma shashhshekar kuka take Allah kadai yasan abinda take roko tsakaninta da mahalicci ya jima a tsaye kafin yaja Mata kofar ya fita jikinsa a matukar sanyaye dan ba karamin qima ta kara a idonsa ba ya Kuma Kara godewa Allah da yayi Masa kyauta da wannan yarinyar yasan Allah sami'uddu'ai ne yasha raba dare Yana rokon Allah ya bashi mace ma'abociyar addini, sai gashi a inda Bai taba zato ba Dan gaskiya Bai taba kallonta a wata mujahida ba yafi Mata zaton bokon ya rinjayi bangaren islamar ta. Koda ya koma shima Bai kwanta ba Saida yayi nafilfili sannan ya kwanta da tunani kala-kala a zuciya. Hudu da minti arba'in ya farka ka'idarsa kenan ta tashi sallar Asuba, wanka yayi ya saka jallabiya milk colour ya bude kofa har ze wuce sai yaga Bai Dace ba gara ta tasheta ta. Sanda ya tura kofar har ta Fara raka'atanul fajri ta Riga ta tashi, lallai ya jinnina Mata gurin ibada sai yaji ya qara samun wata nutsuwa a tare da ita da sauri yaja Mata kofar ya nufi falon jin za'a tada sallah.l
✨✨ ✨✨
🔷AUREN HUCE HAUSHI 🔷
✨✨ ✨✨
MAMAN FATIMAH
💎 PAGE NINETEEN 💎 (19)
AssalamuAlaikum warahamatullahita'ala wabarakatuhu. Ina mika sakon jaje gan Alummar maiduguri bisa ibtila'in daya samesu na karyewar Alo dam, Allah ya jikan wadanda suka rigamu gidan gaskiya Wanda Kuma suke gida da Asibiti Allah ya basu lafiya, abinda aka rasa na dukiya Allah mayar musu da ninkin abinda suka rasa.
_______________Mahmud tunda aka idar da sallah Bai shigo gidan ba sai kusan karfe shida da rabi, ya Dan jima da Mai gadi kafin ya shiga ciki dakin Zahra ya nufa a kwance ya sameta akan sallaya da gani batasan lokacin da barci ya dauketaba yasan kusan kwanan zaune tayi, a hankali ya matsa daf da ita Yana karewa fuskarta kallo idanunta sun dan tasa alamun kukan da tasha da Kuma rashin barci, wayarta ce a gabanta a kunne tsugunawa yayi ya dauka Qur'an ya gani tana karantawa barcin yayi gaba da ita, baiyi tunanin tashin taba kada ya katse Mata barcinta.
Kan stool na madubi ya zauna da wayar a hannunsa Yana dubawa haka nan yaji Yana son ya shiga ya duba received calls da missed calls nata, a hankali ya ringa bi Yana dubawa yawanci kawayenta ne sai Kuma Ummee da ya gani har ze aje sai yaga Kamar number din guyn da zata aura Dan lokacin daya tafi da wayarta ya canza mata wayar da sim card din a Nan ya haddace number din tasa sai Kuma yanzu daya ga Kiran jiya dai dai lokacin suka bar gurin Baba malam, Nan da Nan yaji ransa ya sosu duk da Kiran daga gurinsa ne ba daga gareta ba. Tashi yayi tsam yabar dakin da wayar a hannunsa shima kwanciyar yayi, can cikin barci yaji alamun ana Danna door bell da kyar ya tashi ya nufi kofa, Musaddiq ne da Faruq din Aunty Hasana suke kawo break fast cikin ladabi suka gaishe dashi ya amsa yana Basu hanya suka shigo da basket din dake hannun Musaddiq ya Dora akan dining table. Musaddiq ne ya juya ya nufi kofa yayin da Faruq yayi tsaye, har Musaddiq yakai kofar fita daga falon ya juyo Yana fadin "Faruq me kake jira ne ka tsaya? kasan driver Yana jiranmu fa".. "Taya zamu tafi bamu gaishe da Aunty Zahra ba?". Mahmud ne yace "Faruq Auntyn barci take sai dai zuwa anjima sai ku dawo kaji".
*** Cikin damuwa da matsanancin tashin hankali Mama ta tashi, tunda garin Allah ya waye ta tasa kayan da Hameeda ta shigo dasu jiya a leda da envelope din kudin da mijin Zahra ya Basu a gaba ko bakasan kayan kwalliyar Mata ba kaga wadan Nan kasan ba Karabiti bane ga uwa uba kudin daya lafta musu ita abin har ya Fara Bata tsoro, dan a zahiri kowa yasan fakiri ne wanda Bai ajeba bai bada ajiya ba amma a badini abubuwan da yakeyi suna da ban mamaki. Wayar ta ta dauko tayi dealing din wata number ba'a Dade ba aka daga Bata koyi sallama ba ta Fara magana "Asabe kome kike kizo anjima da matsala babba komai Yana neman ya dagule fa kizo kiga abinda wancan tsintacciyar magen ya baiwa su Hameeda jiya harda fadin magana dan Hameeda ta fadin maganganun danace ta fada wallahi Ina kokonto akan lamarin yaron nan Dan jiya da dare Dana Kira malam na BANDE cewa yayi Wai mun kuskure wani abu shi yasa har Alhajin ya iya daura mata auren Kuma yayi duk iya yinsa ya kasa ganin komai akan mijin nata sai wani haske kawai yake gani". Daga can taji magansr mamar ta amsa da "hakane ba damuwa sai kinzo din ta aje wayar tana jan karamin tsaki ta tashi ta shiga toilet.
A bangaren Ammah kuwa bayan Sajida da zulai sun Gama aikin break fast din da aka Kai gidan zahra, sajidar wanka tayi ta Shirya kafin ta fito falo su karya, bayan sun Gama ne ta kalli Ammah tana fadin "Ammah in Sha Allah yau an tafi gida Ina son na wuce school ne daman na jira ne saina raka Zahra gidanta tun last week muka Fara lactures". Ta fada a ladabce.
"To Babu laifi hakan Allah yayi Albarka, sai Magaji ko Malam Bala wani ya Kai ki mun gode madallah, kunyi sallama da mutuniyar tun jiya kenan!" Ta tambaye ta. Kai ta girgaiza tana fadar "A'a sai anjima zan shiga muyi sallamar". ___
Zahra Bata tashi ba sai wurin takwas da rabi tayi Mika gami da salati tana Kara ware idanu tana kallon dakin da alama kamar ma ta manta inda take Sai a hankali ta dawo cikin nutsuwarta "ya Salam". Ta furta hankali tana ware sexy eyes dinta, wallahi Sam ta Manta da waifa a dakin gidan aurenta take ba a dakin Ammah ba, tashi tayi zaune kan sallayar tana Kara kallon Kanta har lokacin hijabin da tayi sallar ne a jikinta. Toilet ta shiga duk jikinta ya Mata wani irin nauyi Sam Bata jin dadin jikin nata ruwa Mai dumi ta hada ta shige ciki tayi kwance tana shakar kamshin turen wanka data zuba ta jima sosai a cikin ruwan kafin tayi wanka ta fito sabon towel ta dauko mai kalar purple Babba ta daura ta fito gurin mirror taje lotion ta dauko ta shafa a jikinta, tashi tayi ta nufi gurin wata jaka kayan gyarab gashinta ta dauko, zuwa tayi ta zubesu yanzu da a gida ne da Ammah ce zata gyara Mata tsab ta hade shi guri daya, tana kiciniyar daureshi taji alamun bude kofa da sauri ta kalli gurin, Mahmud ne cikin shigar kananan Kaya yayi wani irin fitinannan kyau, hannunsa ya nade a kirji ya jingina da kofar ya zuba Mata idon dake figitata, shi be shigo ba shi be koma ba ya kafeta da idanunsa. Tunda suka hada ido dashi tayi saurin sunkuyar da Kanta jikinta na wata irin rawa duk ji tayi ta rasa yanda zatayi daga ita sai towel din Nan a jikinta, gashin ta saki ya bazu har gadon bayanta ta matse hannunta a kijinta, sun Kai kamar minti uku a haka Yana Kare Mata kallo son ransa a cikin zuciyar sa Yana tsarkake sunayen Allah da yayi Masa kyautar bazata da wannan kyakykyawar halittar dake gabansa a matsayin matarsa ta sunna halaliyarsa wadda ba wani shamaki a tsakanin su. Cikin takunsa Mai Cike da karsashi Amma a nutse, ya doso inda take tsaye Yana zuwa ba zato ba tsammani taji ya saka hannu Yana tattaro gashin daya bazu a kafadarta yana fadar "Bari na gyara Miki tunda Naga yana neman gagararki". Bata iya ce Masa komai sai jikinta daya cigaba da tsuma, tsab ya hade ya saka ribom din daya gani a kusa mayukan gashin brush comb ya saka ya Kara gyara shi sannan yayi baya a hankali ya zauna akan sofa Yana fadar "ki shirya kizo muje ki bamu break fast gashi can Ammah ta aiko tun wurin 7:30 su Musaddiq suka kawo". Bata amsa ba Kuma ta dago kalle shi ba, d'an gunguni ta fara kasa kasa "kawai ka zauna mun a daki kana kalleni kaki fita a gabanka kake son na saka kayan ko me?". Yana kallonta gefen ido tana magana a ciki baya raba daya biyu yasan complain take akan zamansa. Tashi yayi Yana fadin "idan kin Gama kiyi min magana Ina aiki ne". Ya juya ya fice. Wata ajiyar zuciya ta sauke tana fadar "innalillahi ni Fatima Naga ta kaina Wai shi wannan waye shi? Nifa wallahi lamarinsa sun fara bani tsoro gaskiya" ta fada tana cuno Baki, sai Kuma tayi sauri har towel din jikinta na neman faduwa key ta sawa kofar, a gurguje ta saka doguwar rigar lace peach colour Mai touching din flowers green Bata daura Dan kwalin kayan ba saita rufa gyale green,Sam batayi wani make up ba powder kawai ta shafa sai lips glow turarenta ta fesa ta nufi kofa ta bude ta fice tsaye tayi a cikin corridor din saita rasa a wane bedroom din yake. Ta jima a tsaye tana saka yanda zata tunkari dakinsa Kai tsaye, cikin yin shahada ta nufi inda take zaton nan ne bedroom din nasa a hankali ta murda handle din ta tura kamar wadda za'a cewa ket ta ruga, wani sanyi da kamshin turensa Dana freshner ya shiga hancinta dakin ba wadataccen haske duk curtains din windows a sake suke can kan sofa ta hango shi da laptop a gefen sa yana ta faman daddanabawa tsaye tayi ita Bata shiga ba ita Bata koma ba, yana kallonta ta gefen ido Amma sai ya basar kamar bai ganta ba. "Assalamu Alaikum". Ta fada a darare, Bai kalleta ba Amma ya amsa sallamar. Dan Jim tayi kafin tayi karfin halin cewa "na gama shiryawar". Kansa ya dago ya kafeta da idanunsa da yake razanata dasu kafin yace "idan bazaki shigo kije kawai an fada min Ina cinye mutane ne da Kika tsaye a nan". Dan cuno Baki tayi ta saki handle din ta shigo a nutse Amma fa Babu nutsuwa Kota sisin kwabo a zuciyarta ta ayyana "waya sani ko mayen ne tunda abune a duhu". A tsakiyar dakin ta zauna an carpet Kanta na kallon tace Masa "barka da Asuba". Shiru yayi kamar Bai jiba Saida ya Mula dan kansa yace "Lafiya ya kwanan bakunta I hope ba wani damuwa ko?". Kai ta gyada masa alamar eh. Yace "good Bari na karasa wani dan aiki muje muyi break ko?" Ya fada Yana kallonta. Ganin tayi shiru yasa yaci gaba da aikinsa ita Kuma tana zaune duk sanyin dakinsa ya Mata yawa, tana son sanyi amma sai taji na dakin yana neman ya sakata rawar jiki. Baifi minti biyar ba ya rufe laptop din ya Miki, gurin da take zaune ya nufo yana zuwa ya Dan tsuguna kusa da ita Yana fadin "taso muje kada nabar 'yar amanata da yunwa na amsa query a gurin su bestie ko?" Ya fada Yana murmushi. Hannunta ya kama ya dagota tsaye suna shakar numfashin juna Amma ita kanta yana duban kasa, dayan Hannun yasa ya dago fuskarta as usual yanda ya saba. Ajiyar zuciya ta sauke a hankali Amma bata rufe idon ba kamar yanda ya hanata a jiya Bata manta ba amma ta kauda Kai gefe dan da gaske Bata iya had a ido dashi. Dan kwanto da ita yayi jikinsa Yana juyo da fuskarta yana fadin. "Wallahi kada ki rusa min budget dina kisa na kwashe kunyar nan daga idanunki tun banyi niyya ba matukar zakici gaba da irin wannan dabi'ar". Das das girjinta ya kara bugawa akan wadda yake, tana fadin "oh ni Zahra tawa ta sameni shi Wai wane iri ne haka? sai yayi ta sakin magana ko kunya babu". Saida ya matsa mata taci abincin kirki bayan sun Gama ne suka dawo parlor suka zauna Sam Babu sabo ko kalilan a tsakaninsu kallo ya kunna a Nile sat ya kamo super support suna kwallo live. Ganin ita ba wani gane kan ball din take ba yasa ta Mike zata koma daki ta kira Sajida taji ya maganar tafiyar Dan tun jiya da Abba yace a jiya zata tafi gidanta sajidar tace itama sai gida ta. Takunta biyu taji ya janyo ta ta fada jikinsa ba Shiri ta zaro ido waje hura kata iskar bakinsa yayi a fuskarta dalilin yasa ta rufe idonta kenan a hankali yace "Ina Zaki ki barni a zaune alhalin saboda na tayaki Zama yasa naki fita ko ina". ✨✨ ✨✨
AUREN HUCE HAUSHI
✨✨ ✨✨
💎 PAGE TWENTY 💎(20)
_______"ya Salam". Zahra ta fada a hankali jin yanda yake hura mata iskar bakinsa a fuskarta, yasa hannuwansa duka biyun ya tallabo fuskarta yana kallon face din very cute da ita, shifa baya gajiya da kallonta komai nata burgeshi yake yi Dan bakinta ya kalli 'yan kyawawan lips din ta pink, gdy yake yiwa buwayi Gagara misali daya mallaka masa ita a lokacin da bai taba zato ba, tunda ya kafeta da ido Bata yarda sun hada ido ba, ba Kuma tayi gigin dogowa ba. Qaran da door bell din tayi shiya kawo karshen 'yar tutsiyen da yayi Mata wani soft kiss ya yiwa gefen wuyanta Wanda har Sai da ta zabura tana fadin "wayyo Allah!". A shagwabe ta janye jikinta daga rikon da yayi mata, shi Kuma ya tashi ya nufi kofa, Bata jira taga waye ba tayi wuf ta nufi ciki jikinta kamar mazari. Tana shiga ta zube a gado tana fitar da numfashi da sauri da sauri kamar wadda tasha gudu, jin alamun bude kofar yasa tayi saurin duba gurin Sajida ta gani tsaye ta tsura Mata ido tana Mata wani kallo cikin mutukar tsantsar farin ciki zahrar ta taso tana fadin "haba bestie kin wani tsareni da ido kina min kallon qurillah irin wannan ko Kinga wani abu a jikina ne?". Ta qarasa fada tana karasowa kusa da ita 'yar madaidaiciyar ledar hannunta tana fadar "Wai meye Kika wani yi shiru kina kallona ne Dan Allah talk to me Mana pls". Biyo bayan zahrar tayi har gefen gadon kafin ta samu kuzarin fadin "Bestie Kinganki kuwa just one day Amma har kin Fara canzawa, Fadi min meye sirrin gaskiya, na tafi jiya da zulumin ki a Raina yau kuma nazo na sameki haka kin wani Kara Zama fresh dake". "Bestie tsakanin mu harda 'yar zolaya zakice Wai na Kara zama fresh?" Zama tayi gefen zahrar tana fadin "wallahi I am serious kin canza a idona gaskiya Kinga ai dole na fada ko?". "To shikenan kin fada bazan hanaki ba, wai da gasken yau Zaki wuce?" Kai ta gyada Mana kafin tace "In Sha Allah meya rage kuma ai gara naje na fuskanci karatun ko tunda na samu nutsuwa kin shigo gidan ki. Alhamdulillahi, ga sauran abubuwanki na wajen Baffan rimi kici baga da amfani dasu dazuma munyi waya da safe yace na bawa Ammah abinda ya Aiko dai ya Kara jardada Mata na a fada Miki kada wani ya kawo Miki abu kici Kuma yace a tura a karbo Miki sako Nan da sati daya". Dan langabar da Kai tayi tana Kara ganin kimar Sajida ta dauki matsalar nan tata bada wasa ba. Godiya sosai Zahra ta yiwa Sajida akan abinda suke mata, sun Dade sajidar na yiwa Zahra nasiha akan ta rike aurenta da kyau ita bataga wani abun ashsha ba gurin Mahmud idan. Nan da Nan idon Zahra ya kawo ruwa ta shiga sharewa da hannunta tana fadar "wallahi bestie na rasa dalilin da yasa nake jin wani abu a tare dashi tun ranar Dana Fara ganin shi naji abun ko kallonsa fa nayi sai naji gabana Yana faduwa heart beat Dina Yana karuwa, kinsan ma inda matsalar take?" Kai sajidar ta girgaiza tana fadar "sai kin fada". "Kinsan haduwar mu ta farko rungumeni fa yayi a cikin jirjinsa tsam kamar.wata baby amman Kamar an dinke min Baki na kasa ko fada Masa magana ne saima wani azababben kwarjini da yayi min harda fadar na ringa kula kada nayi musu asara'. Ai Sajida Bata San lokacin da wata dariya ta kubce Mata ba tana fadar. "Babbar magana kice da wata tsumammiya a tsakani ku tun tuni har kika dauki alhakina gurin hanani kwanciyar hankali tun jiya Allah barci ma ban samu na kirki ba Ina zulumin abinda kaje yazo, Dan ba kowa bane za'a aje masa mace kamar ke ya iya kauda Kai gaskiya" Wani duba zahrar tayi Mata tana fadin "ban Gane ba me kike nufi da maganganunki?.