Kenza eBookz

Auren huce haushi complete - Chapter 39

Auren huce haushi complete - Chapter 39

Auren huce haushi complete Chapter 39: Auren huce haushi complete Chapter 39. ______ Basu samu flight direct zuwa Kano ba Saina Abuja, karfe shida da minti…

4,189 words

______ Basu samu flight direct zuwa Kano ba Saina Abuja, karfe shida da minti hamsin da bakwai girginsu ya sauka a Abuja Namdi Azekwe International airport. Wani tickets din Sameer ya saya musu online na Abuja to Kano karfe Tara da kwata ze tashi.

Bayan zahra ta Idar da sallar insha'i ta nufo falon farko inda kitchen yake ta Fara aikin Dan kwarya-kwaryar abinci vegetable macaroni tayi tare da pepper chicken,sai tayi cocktail fruit, komai kadan tayi dai-dai cikinta drink ne da pepper chicken ne tayi da yawa tunda tana so ta bawa Aunty Zilai dasu Zayyan idan Yana Nan, komawa tayi bed room bayan ta Gama komai wanka tayi haka Nan taji tana son saka wasu fitinannun Riga da siket. English wears ne kalar sea green da ratsin fari a jikin rigar sai bandana kalar sea green din kayan ko bra basa bukata, gashin ta matse da Ribom ta saka bandanar ta saki sauran gashin baya sai tayi wani irin kyau na ban mamaki jikin Nan nata sai glowing yakeyi yarintarta saita kara fitowa sosai, ita Kanta tasan yes ba karya tayi kyau ba Dan kadan ba, tunda Aunty zila tayi Mata fada dazu da Nasiha ta samu tace Mata ta sake tayi rayuwar ta Kamar ko wace Mace a gidan mijinta tabar ganin nan a wani bakon wuri, duk inda ya kaita ta sake a gurin radin Kansa ne ya fada Mata waye shi radin Kansa ne yaki fada mata cikinsa, Amma dai a ko Ina tayi kokarin Zama matar gida bawai ki Zama kamar 'yar tsaron gida ba. Takalmi ta dauko ta saka cikin wadanda ta gani kalar fari tas, parlourn ta dawo tana baza kamshin turarenta kamar ko yaushe. Aunty Zulai ta Kira a waya tace tazo tana nemanta, Bata Dade da Zama ba Aunty zilan ta shigo, tunda ta shigo Aunth zilan take kallon zahra, daga karshe kasa hakuri tayi ta Fara fadin "Masha Allah, uwar dakina Allah ya kade hau da bala'i Ina ma yallabai Yana garin Nan da sai ya bada tukwuicin kwalliya nan, haka nake son ganinki ki nuna Masa rainon Ammah ce ke, na rasa abinda yasa Kika tsaya sanya ai ki rikita Masa lissafi da gasken gaske wani ma yayi rawa bare d'an makadi, ki dauki makaman yaki kiyi kaca-kaca da lissafinsa yasan Mata suna suka Tara yasan da gaske Zahra ce cikin taurari". Mamaki Aunty zilan ta rinka bawa Zahra. Baza kace ita ke fadar wadannan maganganun ba duba da ba ilimi Mai zurfi tayi ba iyakarta aji uku na Karamar secondary aka cire ta akayi Mata aure. Ta gane Zama da Ammah yau da gobe ne ya kawo haka. "Aunty zilai kenan ko yana Nan ba Wani yabawa zeyi ba kedai abar kaza cikin gashinta kawai, wa yasan ranar dawowarsa tinda ba fada min tafiyarsa yayi ba menene nawa na bin diddigin yaushe ze dawo". Dan murmushi Aunty zilan tayi, ."Haka kike gani wallahi nasan duk inda yake a duniya kina maqake a zuciyarsa ba irinki ake yiwa rikon sakainar juji ba ki rubuta ki aje wannan maganar Dana fada, Baya Nan Amma ta Yaya ya taso mutum tun daga TAWA Dan kawai ya daukoki, Kinga kenan ko mu"amalarki bada kowa ya aminta ba tunda gidan Nan cike yake da ma'aikata kala kala, ko Rukayya ya fadawa zata dawo dake Amma hakan be Masa ba saboda yanayin rayuwa da ake ciki gara ya kashe ko nawa ne a kawo Masa ke cikin aminci". Itama zahrar dan murmushi tayi. Aunty zilai kenan, haka kike gani? "Kwarai kuwa, Aina fada Miki d'azu"

Sun Dade suna hira da Aunty zilan kafi tayiwa Zahra sallama, da kyar zahra ta bari zilan ta koma part din da take, Wai tsoro takeji ita Daya a wannan gurin, pepper chicken din ta Bata Wanda ta Zuba Mata ta, ta Bata Kuma Wanda ta zubawa su zayyan din, ta amsa tana godiya. Karfe goma da minti minti ashirin su Mahmud suka sauka a filin sauka da tashi na malam Aminu Kano,cikin suit yake ash colour sai laptop dinsa dake rike a hannun Bilyaminu, cikin takunsa na cikakken namiji ya gangaro steps din jirgin, Zayyan ne yazo daukarsa. Sameer yaso ya raka Mahmud gida Amma sai ya nuna Masa yaje gurin iyalinsa kawai, har mota binya ya Kai Masa laptop din, ya koma Sameer ya tafi dashi tunda a nan airport din yabar motarsa.

Tunda Aunty zilai ta tafi zahra ta tashi ta nufi dining din ji tayi abincin ya fice Mata daga rai pepper chicken din kawai taci kadan ta Zuba cocktail fruit a cup ta Fara Sha, cup din na bakinta ta lumshe Ido saboda yayi Mata Dadi sosai, kawai ji tayi atmosphere din falon ya canza wannan fitinannan kamshin ya had'e falon, kasa bude idon tayi don ita tsoro ne ya rufeta ita dai tasan ita daya ce a parlourn ba Wanda ya shigo itace me bude kofar Kuma Bata bude ba, ko cup din ta kasa saukewa kuma Jin kamshinsa take Yana Kara kusanto ta, ji tayi zuciyarta ta tsinke Bata San wace kaddarar ce Kuma ke kusanto ta ba, ba alaman.shigowar mutum sai kaji kamshinsa ya cika guri. A hankali ya tako kamar me slow motion ya karaso gurinta ya saka hannu ya zare cup din, ya danyi sipping na drink din nata,sanyin ya ratsa Masa kirji, ita dai zahra ta kasa ko motsin karki, taki Kuma bude idanun taga ko wanene duk da taji shine. "Precious". Ya Kira sunanta

Shiru tayi taki magana, cup din ya aje a gefe ya Dan rankwafa daidai fuskarta Yana Kare Mata kallo Yana tasbihi ga Allah s.w.a da yayi Masa wannan kyautar. "Wai bazaki bude idanun ba?". Hannu ta saka ta Kara rufe fuskarta. Ikon Allah ya tsaya kallo,wato yarinyar nan Kullum da irin salon da Zata fito Masa dashi, idan ta murzawa idanunta toka tamkar Bata taba saninsa ba, yanzu Kuma Dan tsabar kinibibi ta Wani lullube ido, ai karya ne Bata wani Jin nauyinsa tunda Zata iya fada Masa duk abinda yayi Mata Dadi a ranta. "Wallahi ki bude ki kalleni har wata kunyata kikeji da Kika casheni tas, yanzu Kuma kizo kina Wani kinibibi". Kujerar ta ja baya kadan ta tashi tana, ta bude idon kamar yanda yayi umarni Amma taqi kallonsa. Ai Yana ganin ta Mike din ya Zuba Mata lumsassun idanunsa yana Kare Mata kallo tayi Masa wani irin kyau na ban mamaki, ga kayan wasu fitinannu ne ta saka masu motsa jam'iyya, dai ya fada Mata zuwansu da sai yace Dan ta tsokane shi tayi shirgar to be fada Mata ba, kawai radin Kanta ne sai akayi arashi Kuma ya tarar.

Hannu yasa ya juyo da fuskarta suna facing din juna. "Yanzu haka Zaki ringa yi min Idan na dawo daga tafiya? Tafiyar kwana uku Amma a kasa Yi min welcome me kyau? Da saka zuciya nishadi,saidai a bige da rintse idon ba'ason ganina". Cikin wata irin shagwaba Zahra tayi Masa warrr da ido a karon farko ta bude bakin cikin sanyin murya tace Masa. "Me nayi maka ka tafi ka barni, kofa sallama bakayi min ba meye laifina Dan Allah? Ba barni cikin tashin hankali, Bana barci,Bana iya cin abunci nayi tunani ka gudu ka barni ne kamar yanda ka taba fada min a wani dare Daya wuce can Baya". Dan bakinta yake kallo lips din ta sai glowing suke, sai ruwan hawaye Daya ciko a cikin idanunta da gaske taji ciwon barinta da yayi ba excuse. Kasa magana yayi duk ilahirin jikinsa ya Gama yin sanyi da gaske be kyauta Mata ba, duk da abinda tayi masa, sai yanzu yaji wani irin rashin Dadi ya cika Masa zuciya. Hannunsa dayan ya saka ya janyota cikin jikinsa Yana shakar kamshin jikinta Daya Kara canza Masa daga Wanda ya sani. Bataki ba ta shige tana sauke ajiyar zuciya, hannu ya zira bayanta ta cikin Riga yana shafawa a hankali Yana Mata magana a saitin kunnenta. "I am very sorry my previous, na daina wallahi na azabtu ba kadan ba da bakya kusa dani, Dan Allah ki rings respecting din maganar da zaki ringa fada mini, duk duniya idan Kika cire mahaifana babu Wanda ze fada min abinda Kika fada min na qara ma'amulantarsa a rayuwata, kin harziqani matukar gaske, ko abinda akayi min a Baya be tada hankalina kamar kalamanki gareni ba"

Kara matseta yayi a jikinsa, ji tayi jikin nasa kamar yana shaking, Bata San lokacin data kankameshi ba sosai tana fadin. "Pls! meu Amor wallahi na daina fada maka makamanciyar kalmar har abada, kayi min hukuncin Daya Dace da laifina matukar zaka huce, wallahi badan ka min shigar sauri ba da bazaka sameni a garin Nan ba da wane idon Zan Kara kallonka kalamaina sunyi Muni". Sun dauki digon lokaci a haka Zahra nata sauke numfashi. Kalamanta na karshen sun doki zuciyarsa, da me take Shirin aikatawa ke Nan? "Thank God". Ya fada a zuciyarsa. Saida yaji tsayuwar na kokarin gagararsa sannan ya zaunar dasu a kujerar dining din tana jikinsa, bandanar da ribom din ya zare yana Kara shafa gashin Daya Sha gyara. Harshensa yasa ya laso hawayen Daya gangaro Mata daga ido, Wani yarrrr taji gaba Daya a jikinta. A hankali ya furta. "Meye na kuka Kuma? gani na dawo kuka Kuma ai ya Kare, tashi ki bani abinci yunwa nakeji tun safe ta kasa cin komai". Gashin ya shiga hade Mata da ribom din Daya zare ya dauko bandanar ya mayar mata, sannan ya gyara Mata rigar Daya kusan cireta daga jikinta, Yana Kara shafar gefen fuskarta Yana manna Mata light kiss a Kan tsinin hancinta. Lumshe Ido tayi ta bude a hankali, kashe mata Ido Daya yayi Yana fadar. "Ki bani abinci kada ki maye gurbinsa fa, naga alamar son abin a cikin idanunki, Bari na Gama mu shiga ki fada min yaushe Kika Zama haka a yan kwanakin Nan da Bana Nan?". Shiru tayi Masa Dan ba karya yayi ba ji tayi kamar karta rabu da jikinsa sabanin da. A hankali ta tashi daga jikinsa Amma fa sai Wani sadda Kai takeyi. Vegetables macaronin ta Zuba masa ta Zuba Masa pepper chicken din da drinks. Ta matso dasu gabansa tana fadin. "Bismillah". Coat din jikinsa ya cire ya Miko Mata Yana fadar. "Kaita can inda na aje laptop din can kizo muci nasan ba kici komai ba". Bata fuska tayi cikin shagwaba tace. "Naci nawa fa wannan naka ne na aje maka". "Kinsan zanzo ne?" Kai ta gyada Masa. "Banda karya fa?" Dan smile tayi Wanda ya Kara Mata sirrin kyau. Saida yaci ya koshi ya Dora drinks sannan ya ja abarsa suka nufi bedroom din, Yana shiga yaga dakin yayi Masa yanda yake so. Ruwan wanka ta hada masa Bata Kai ga fiowa ba ya shigo daga Baya ya sako hannunsa akan cikinta ya Dan kwanto jikinta. Baya gajiya da shakar kamshin jikinta. "Bazaki tayani wankan ba?".

Ya fada Yana Dan shinshinar gefen wuyanta, Yana Kuma kokarin rabata da kayan jikinta. Cikin kasalalliyar murya tace Masa. "Yanzu ba dadewa nayi wanka kada nayi mura". "Bazakiyi ba ai kina da maganinta a kusa, pls ki Bari mu samu body contact Mana kinsan yanda na azabtu kuwa? Ki sassautawa Dan Husainin Ammi Mana kada fa Hajiya Inna tace kin mallake Mata jika tayi bore tace saina Miki kishiya ta uku tunda kina da uwar gida". Ya fada Yana ida zare Mata rigar da sauri ta kankameshi tana saka hannu a kirjinta, kafin ta Sami bakin korafi yayo kasa da Kansa dai-dai bakinta ya hade bakinsu. Sunfi minti biyar a haka kowa na sauke numfashi, da kyar ya iya hakuri sukayi wankan Nan ma Saida suka Bata lokaci sosai sannan ya sassauta Mata. Gurin kwanciyar ma haka ya hanata saka abin kirki sai wata nighty wadda da ita da babu duk daya. Darasin karatu yake Dora Mata Wanda ya girmewa shekarunta da wayewarta, ita mamaki yake Bata ba Wani yawan shekaru ke gareshi ba dududu baifi sa'an su Ya Abdul Hakeem ba, amma abinda yake Mata sunfi karfin shekarunsa, ya gigitata iya gigitawa, Dan Saida ya goge Mata hadda tsab ya sakata wata irin rayuwa wadda Bata taba tunanin da akwaita ba yayi mata wasu abubuwa da bakinta baze iya fada ba, ya Kai bakinsa inda Bata taba tunanin ze kaiba, Wani sabon Mahmud take gani Wanda bashi da ta Ido ko misqalazarratin, ya fada Mata wasu maganganu masu nauyin fada, Dan har ta saddaqar Mai afkuwa ce zata afku, amma sai taga ba hakan bane amma ko hakan ba sauki, dan sun Kai karfe biyu da rabi kafin su koma toilet yin wanka a can ma Saida ya Kara cakusata da kyar ya saurara mata. Bayan fito ne sun kwanta janyo yayi jikinsa yasa hannu ya zare rigar jikinta. "Na shiga goma Ni Fatimah". Zahra ta fada a zuciyarta, Dan da gaske da wata irin fitina ya dawo Mata, Bata taba zatonsa a haka ba, tana mamakin me yake dakatar dashi Dan taga fitina iya ganinta a tare dashi,wallahi tsotonsa take da gaske yake Ashe lokacin Daya ce Mata shi sadauki ne taga zahiri. "Wash!!! Allah na Dan Allah ka Bari barci nakeji". Ta fada cikin raunin murya Dan da gaske taji a jikinta. "Ba abinda zanyi Miki kiyi barcinki Mana. Ya fada Mata cikin low voice, abinda ya Kara yi Mata yasa ta rike Masa hannu da sauri tana fadin Dan Allah fa!" "Naji ki Bari na Kara Jin duminki mana precious nifa kamar jaririn Daya wuni baisha.... Ai kin gane". Yasa hannu ya Kai shafa gurin. Tanaji Tana gani yaci gaba da sabgarsa Saida ya gaji Dan Kansa ya kyaleta. Cikin ikon Allah Basu makara sallar Asuba ba, lokacin Daya dawo harta Gama Azkar dinta ta koma ta shige blanket ta Fara barci. Shima barcin ne a idanunsa fal jallabiyar jikinsa kawai ya cire ya Zama daga shi sai boxer short,ya shige jikinta ya gyara musu blanket din. Sai kusan karfe goma da kwata Mahmud ya farka, zare jiknsa daga nata ya tasheta itama. Tare sakayi wanka suka shiga kitchen,.wunin ranar haka Sukayi shi, duk inda ta saka k'afarta Yana Maida tasa har girki tare sukeyi tana bashi abubuwa Yana taimaka Mata da yankawa ko wankewa, har lokacin ba Wanda yaga duriyar Zahra Shima masallacin kawai ke fitar dashi da dare ba yanda beyi su fita ba amma ta qiya daga karshe ma cewa tayi ta daina fita dashi a garin Nan tunda anyi biyu basu dawo gida lafiya ba, baza'ayi na uku da ita ba, shi dariya ta bashi yanaji yana gani dole ya hakura da fitar. A sati Daya sukayi wata irin shakuwa ta ban mamaki wadda ta saka musu soyayyar juna kamar su cinye junansu. Babu abinda ke fitar da Mahmud sai sallah, Su duka sukayi wani irin fresh dasu, bare ma zahrar ko Ina ta cicciko kamar me yaron ciki. Gatan duniyar Nan Mahmud ya nuna Mata wani lokacin har tausayi yake Bata, bashi da lokacin Kansa sai nata Koda yaushe Yana makale da ita, tun zilai na damuwa da rashin ganin Zahra harta hakura, ba ita take musu abinci ba da gyaran part din, ita Kanta Zahra Batasan waye yake gyarawa ba ba Kuma ta damu da sanin me yin ba, bedrooms din ne dai ita ke gyarawa ta saka turaren wuta Kuma duka gidan. Satinsu biyu cur suna manne da juna, ko part din sau biyu ta fita daga ciki lokacin da yace suje lambu tayi mamakin girman gidan Dan kafin mutum yaje lambun da tafiya, kayan marmari ne sosai a ciki harda Apple dasu grapes, ta sauran su mango dasu Papaya, ranar yasha tambaya lokacin Dan kasa hakuri tayi da suka nufi bargar dawaki da bangaren da ake kiwon jimina da su dawisu. Ta jefa Masa tambayar Wai wannan gidan na waye Daya sakar maka ka Mike kafa kamar bazaka fita ba? Dariya yayi Mata Yana fadar "ba ance Hajiyar makwarari ta fada miki gidana bane tunda kinji daga bakin kakata ai inaga nawan ne tunda kike Kama maganarta wadda rikicin tsufa kawai ta iya". Shiru tayi Masa tasan tunda ya ambaci haka babu abunda ze fada Mata akan tambayar ta. Har doki ya dorata a ranar yayi Mata hotuna da yawa Dan kayan sport suka saka saita kalar fari da ja it's ta Dora hijabi a Kai da suka kebe Kuma ta cire, sunyi hotuna sosai masu matukar kyau bare na garden din sai background din yayi kyau sosai.

Da dare suna zaune a parlour tayi pillow da cinyarsa yana kallon tashar super sport ana nuna wasan realmadrid hannunsa Kuma yana. Wasa da gashin Kanta Wanda ya Sha gyara, sai kamshin hairspray ke tashi duk ya yamutsa Mata shi taga alamar da bayani a tare dashi. Wayarsa ce tayi dauki slow music na wakar wata tshowar mawakiyar America brandy. Tashi tayi tsam ta nufi wayar ta dauko sunan Habib ta gani Yana yawo akan screen din tana kawo Masa Kiran na yankewa, kiransa yayi gefe ya koma ta Zauna saboda Bata San me zasuyi tattauna ba, tana can tana kallon wani penalty da aka bawa Barcelona suka zubar, sai ji tayi ya tashi da sauri Yana fadar. "Innailaihi wa Inna ilaihi raji'un! Yaushe ne abin ya faru, subahanallahi gamu Nan zuwa Azaren da safe in Sha Allah". AUREN HUCE HAUSHI

Naman Fateemah

Page 58.

................Da wani irin sauri da sassarfa ta karaso inda Mahmud din yake tsaye rike da wayar Yana salati, hannunsa ta rike tana jijjigawa tana fad'in. Waye ya mutu a Azaren, wayyo Allah Ammah ta, shikenan Ashe munyi sallama kenan" Ta rukumkume shi sai kuka. Da kyar ya banbare ta daga jikinsa yana fad'in. "Menene haka precious Wai? Waye ya fada Miki mutuwa akayi da Zaki tada hankalinki, Nima ki tada min nawa". Zaunar da ita yayi, sannan shima ya Zauna suna facing din juna tana matse hawaye daga idonta. Hannunta ya kama ya rik'e Yana fad'in. "Ki nutsu ba Wanda ya mutu fa Baba malam ne ya Fadi dazu bayan sallar insha'i a kofar masallaci yazo tsallake kwalbatin da ake gyara ya taka slap ya zame dashi sai Kuma slap din ya biyo shi ya fada Masa a bayansa,bayan an Ciro shi daga ciki sai Kuma sai tafiya ta gagara suka nufi Asibiti to a can ne suka yiwa Su Habib bayanin ya Samu matsalar data Hana kafafunsa tafiya, yanzu haka Yana F. M. C likitoci na tsaye a Kansa Wai suna tunanin ya Samu Spinal cord injury ne". Wani irin zaro idanu zahra tayi tana fadin. "Innailaihi wa Inna ilaihi raji'un mun shiga Tara "spinal cord injury? shikenan Baba malam sai yanda Allah yayi" . Sai wasu sabbin hawayen. "Kiyi hakuri kuka baya magani sai addu'a kawai". Basu Dade a parlourn ba suka koma ciki Dan kallo dai ya tashi, ya Dade Yana lallashinta kafin ta saurara da kukan, ya sani sunyi wani irin sabo da Baba malam Yana kaunarta sosai Dan sauda yawa Yana ganin Yana saka Almajirai Yi Mata Addu'oin na musamman, itama sauda yawa Yana ganinta da Leda a hannu ta kawowa malam din. Kwana Sukayi ba nutsuwa Kota sisin kwabo a tare dasu Malam ubane na gaske Mai nuna kauna da karamci ga kowa. Dan Mahmud kusan kwana Sukayi suna waya da Habib sun Kai uku da Rabi Saida likitoci suka gama dubashi sukayi Masa Allurar barci sannan ya samu nutsuwa, zahra ma har lokaci batayi barcin ba. Bayan ya aje wayar be kwanta ba toilet ya shige ya Jima kafin ya fito da bathrobe da karamin towel a hannunsa Yana tsane ruwa, jallabiya ya zura ya Fara nafila, ganin haka ya saka Zahra tashi itama tayo alwalar ta dosa nafilar itama, suna zaune har akayi Kiran assalatu. Shi ya fice, sai kuma gashi ya dawo tana niyyar tayar da sallah, tsayawa tayi saboda gurin da take ya nufo. "Ki shirya kafin na dawo da wuri zamu wuce Azaren". "To, insha Allah". Ya juya ya fice ita Kuma ta tayar da sallah zuciyarta fal murna abunda ta cire Rai dashi kenan kwana kusa, Ashe basu sani ba a kusa zasuje garin, ikon Allah Kennan sallar ta tayar. Babu Bata lokaci ta shirya har ta shiga kitchen tayi simple Abu kamar yanda taga Ammah nayi idan Abba zeyi irin wannan tafiyar takance lusarar Mace ce ke barin mijinta ya fita neman abin breakfast a hanyar tafiya, wadda tasan kanta Bata barin mijinta neman abincin titi yayin sakakkon tafiya. Kafin ya shigo ta hada basket tsab a bedroom ya sameta tana kokarin saka doguwar rigar abaya 'yar Dubai a cikin kayan dake dakin ta ganta ba karya ta amsa sunanta, a hankali ya karaso da sallama a bakinsa Yana zuwa rigar ya karba ya saka Mata ya dauko veil din ya dauki clip din me zanen heart da stones a jiki yayi Mata rolling, ita har mamaki ya Bata ganin yanda yayi Mata dos ba Wani mistake. "Kinyi mamaki ko? A gurin Aisha na iya Ni nake Mata idan zamu fita unguwa tunda da Mace aka hadoni ai dole na iya sabgar mata". Yayi gaba da sauri ya nufi toilet. Da idanu tabi shi tasan wani wankan ze sake, ita batasan wane irin jikine dashi ba sanyin ruwa baya Masa komai a zamansu dashi ta fuskanci ma'abocin son ruwa ne shi. Handbag Mai Dan girma ta dauko ta Zuba turaruka da Dan abinda baza'a rasa ba a ciki. Yana fitowa daga toilet din ya fice Yana fadin ta jirashi a parlourn farko. Ba tafi minti biyu da Zama ba taji alamun tsayuwar mota a kusa da parlourn, tashi tayi ta shige kitchen ta dauko basket din, ta fito kenan shi kuma ya Gama gangaro steps din kenan, cikin wani yadin filtex ruwan sararin samaniya da hula itama sky-blue din Yana daura agogo a hannunsa, wani irin kyau taga yayi Mata kana ganinsa kasan yarone matashi Maiji da kuruciya ga Wani sirrin kyau da yake fita daga fuskarsa, ganinta da basket ya bashi mamaki karasowa yayi Yana fadar. "Wannan fa". Ya nuna Mata abinda ke hannunta. "Is for you". Ta fada tana nufar inda ta aje handbag dunta. "Thanks, wato so kike na koma kamar yaron goye ko?". Dan juya masa sexy eyes dinta tayi kawai. Karbar basket din yayi suka jera sun bala'in kyau Kamar ka daukesu ka boye saboda yanda sukayi wata irin dacewa kana ganinsu kasan couple ne da suke cikin ganiyarsu. Suna fita Zayyan yayo zarya ya karbi basket din daga hannun Mahmud Yana fadin. "Good morning sir". "Morning" Ya amsa masa, sannan ya gaishe da zahra. Da sauri Zayyan ya budewa Mahmud back seat ya zagaya ya budewa zahra dayan gefen itama, har ze shiga seat din driver Mahmud yace yaje side din da Aunty zilai take ya fada ta shirya zuwa goma Sameer zezo su tafi. Tare da Aunty zilan suka dawo jiki na Mata tsuma har kasa ta tsuguna ta gaishe da Mahmud sanan Zahra ta gaishe ta, zahrar tayi Mata bayanin halin da ake ciki, cikin nuna jimami ta jajantawa Mahmud din tare da Addu'ar fatan samun lafiya. Saida aka bude musu gate suka fice sannan Aunty zilan ta koma da sauri tayi abinda zatayi na abincin da take dafawa saboda hadiman gidan ta shirya kada a jirata. Saida suka bar kano sannan Mahmud ya Danna wani guri jikin kujerar gaba, take wani covering ya raba tsakaninsu da Zayyan da yake aikin tukinsa. Janyota jikinsa yayi ya kwantar da ita baice Mata komai ba itama batace masa ba sai fuskarta da yake Dan shafawa lokaci zuwa lokaci Batasan sanda barci yayi awon gaba da ita ba, Bata farka ba Saida suka kusa shiga Azare Shima wayar da sukeyi da Habib ce ta tasheta. Warrr tayi da Ido tana kallonsa. "Kin tashi?" Kaita gyada Masa tana janye jikinta daga nasa. Directly FMC suka nufa a parking space suka tarar da Habib yana tsaye Sam be gane su waye a motar data wuce shi tayi parking a nesa kadan dashi, hundred percent hankalinsa na Kan wata mota Mai shigowa, da sauri Zayyan ya budewa Mahmud kofa ya fito Yana rike da hannun zahra kamar me tsoron kada ta Bata, duk yanda taso ta zame hannunta yayi mirsisi ta qiya, gurin da Habib yake suka nufa kafin su karaso Habib ya juyo da sauri Jin turaren Mahmud daga bayansa. "Masha Allah" Ya fada a zuciyarsa, ganin yanda sukayi wata irin dacewa gaba daya gani yayi sun canza Masa tamkar masu rayuwa a kasashen Europe din nan. Da sauri ya nufo Mahmud Yana fadin "wallahi banyi zaton ku bane a waccan motar kaga wadda nafi maida hankalina a kanta Nan". ya nuna irin motar Zahra. "A'a ata yallabai mukazo tare da drivernsa, ya fada Yana tsare zayyan da Ido. Zasuyi musabiha da Habib Zahra ta samu zare hannunta daga cikin nasa, idan shi bakone ita garinsu ne yanzu da anyi dace idon sani ya gansu zance ze cika unguwa Daman ya lafiyar kusa ita da komai nata a baki yake, ga unguwar tasu ta 'yan gargajiya. Gaishe da Habib zahra tayi tare da tambayarsa Mai jiki, sannan suka gaisa da Zayyan ma. Habib yayi musu jagora zuwa dakin da aka kwantar da Baba malam vip ne Nan Abba ya saka Abdul Hakeem ya biya aka saka shi duk da Abban baya garin.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull