Auren huce haushi complete - Chapter 40
Auren huce haushi complete Chapter 40: Auren huce haushi complete Chapter 40. Lokacin da suka shiga ya koma barci ba kowa a dakin sai Abubakar kadai duk…
4,545 words
Lokacin da suka shiga ya koma barci ba kowa a dakin sai Abubakar kadai duk yawanci sai bayan anyi sallar Asuba suka koma gida. Kai tsaye gurin gadon Mahmud ya nufa, ya tsaya dai dai Kan malam din, gani yayi yayi wata irin rama fuskarsa tayi wani fayau sai qananun raunika a gefen idonsa na dama da gefen kumatunsa. Kujera Abubakar ya gyarawa zahra sannan suka gaisa tayi Masa jajan jikin malam, gurin Mahmud ya karasa sukayi musabaha tare da jajantawa juna. Ya Dade a tsaye a gaban gadon daga shi sai mahaliccinsa suka San Abinda yake saqawa a cikin zuciyarsa. Juyowa yayi Yana facing din Abubakar da Habib. "A hannun wane doctor case din malam yake?". Habib ne yace. "Yana hannun doctor Omole consultant ne a bangaren Orthopedic, yanzu ma ba dadewa suka bar dakin lokacin ma inaga kun shigo garin". "Ok ba matsala, muje ka rakani na gansa". Ya fada Yana nufar kofar da wannan azamar tasa, su Abubakar suka rufa Masa baya. Zayyan ma ya bisu dakin ya rage daga Baba malam da yake barcin dole sai Kuma ita zahrar dake zaune tana duba wayarta. Office din likitan suka nufa a hanyar suka hadu dasu salisu sun dawo harda Mu'az a cikinsu, tasu batazo Daya ba da shi sam saboda yanda baya iya kauda Kai akan mata, kuma salisu ya taba fada Masa har ciki ya taba yiwa wata yarinya 'yar Mai aikin gidansu finkarfi yasa aka dannesu aka bawa wani marar gata. Sun gaisa tare da jajantawa Mahmud. Salisu ne ya kalli Habib Yana fadin. "Wai Dan Allah a Ina mutumin ya maqale ne? ko wayarsa fa na Dade ban samu ba, ka fada Masa wallahi zamu kwace kanwar mu tunda haka ze Mana gara ta dawo kusa damu yanda zamu ringa ganinsa.À Amma ka dauke yarinya kayi shiru sai wani kyallin jiki kake Kamar Mace". Dan murmushi Mahmud yayi yana fadin. "Ka dauki bashi Zan biya, kanwarku Kuma sai yanda nakeso zanyi da abata haka kawai Zan ajeta sakaka kowa Yana gane min ita, Mai tsada ce". Ya fada Yana tafiya tare da cewa. "Bari muga doctor" Har sun Fara tafiya Mahmud ya tsaya ya Dan koma baya gurin Zayyan da suka bashi 'yar tazara. "Kaje maza kafin zugarcan su Karasa dakin ka Kai precious can gidansu kace Zan kirata". Ya juyo shima Zayyan ya juya da sauri. Suna zuwa kofar doctor din wani matshin doctor ya fito da sauri sauran kadan suyi karo da Habin ya danja da baya Yana fadin. "Sorry". "Ba komai". Habib ya fada, sai Kuma doctorn ya kalli Habib sosai. "Habib Abubakar ko?" Kai Habib din ya gyada masa. "Ok. Bismillah daman kiranka zani akan issue din Babanka". Tare suka shiga ciki Mahmud da Abubakar na biye dasu a Bata. Sun samu doctors kamar biyar sun zagaye doctor Omolen Yana ta bayani sun saka hoto X-RAY a tsakiya wasu na yin jotting na abinda yake musu bayani. Matsawa wasu sukayi Habib da wannan likitan suka tsaya suma, doctor Omolen ne ya dago lokacin da doctor Hafeez yake Masa ga yaron patient din Nan harma da wasu yaran nasa ya fada Yana nuna su Mahmud da Abubakar. Umarnin tasowa doctorn yayi musu, ba musu suka taso. Bayani ya Farayi musu Yana nuna musu inda ya samu matsalar k'ashin bayansa k'asusuwan ne suka matse sakamakon fadowar da slap din yayi Masa a gadon bayansa, su suka matse spinal cord dinsa har ta samu injury Wanda ake Kira (spinal cord injury). Yanzu Abu biyu ne zuwa uku na farko ko a turasu National Orthopedic na Dala Kano ko ibadan ko Kuma su fita dashi India wani Asibitin Fortis hospital dake new Delhi ko Kuma Max orthopedic surgeon hospital shima dai a Indian. Take jikin Habib ya Kama tsuma Saida Mahmud ya zaunar dashi a resting chairs na cikin office din Yana Zama ya fasa kuka kamar mace. Abubakar ya fita da Habib waje Yana bashi magana akan ya dangana yayi Masa Addu'ar samun lafiya da Kuma mafita. Saida suka fice Mahmud ya fuskanci doctor din Yana tambayarsa wane Asibitin ne yake ganin shine best a cikin biyun Daya fada musu na Indian. Wani daga cikin doctors din ne yace abunfa ba Mai sauki bane za'aci millions of naira a Kan aikin ga kudin flight. Dan murmushi Mahmud yayi Yana fadin. "Ba komai Allah ze rufa asiri, a bani website dinsu duka zamu bibiyesu muga wanne zamuje in Sha Allah". Ba Bata lokaci aka bashi address din duka biyun da wasu sabbin magungunan da za'a saya da Allurai yayi musu godiya ya nufo kofa likitan da yayi musu jagora ne ya biyo Mahmud Yana fadin. Idan babu damuwa zanyi magana da Kai,akwai wani Dan uwana da yake zaune can Indian Zan hadaku dashi Dan ku samu saukin abubuwa" "Ok Nagode in Sha Allah zanyi maka magana idan komai ya kammala". Sukayi musabaha doctor din ya koma shi Kuma Mahmud ya nufi inda ya hangi su Habib Abubakar nata watsa hannu da alam fada yake yiwa Habib din. Koda ya karaso Baice musu komai ya zauna kusa da Habib Yana sauke numfashi. "Ya ake ciki'. Abubakar ya tambayi mahmud. Ba komai in Sha Allah za'ayi abinda ya kamata jiran zuwan oga Sameer nakeyi baze gagara ba suna aikin da yafi wannan ma ai qungiyoyin suna da kudi sosai. Dan wannan aikin ba wani Abu bane yanzu Kai Habib idan malam ya tashi ka tambaye shi inda za'aga passport dinsa kaima kaida Abubakar sai ayi muku tare da Visa tunda daku ya kamata aje". Yana Gama fada ya mikawa Abubakar takardun da za'a sawo magani tare da ATM card dinsa yana fadar a karbo wadannan magunganan. Tunda su zahra suka fito daga Asibitin ta ringa Alla Alla su Karasa gida taga Ammah. Suna shiga harabar gidan Bata jira Zayyan dake kokarin fitowa bude Mata ba ta fito da sauri tamakar zata kwasa a guje, Musaddiq ne ya fito Yana zuburar Baki da gani aikensa akayi baya son zuwa. Ai Yana ganin zahra ya kwala qara yana fadin. "Yehhhh! Adda Zahra!" Ya kwasa a guje ya koma ciki yada kwadawa Ammah Kira. "Ammah! Amma! Ammah! Ki fito ga Adda zahra tazo". Mama dake tsaye a balcony din dakinta da waya a hannu ta gangaro da sauri ta nufo part din Ammah, Mama na kokarin shiga su Kuma su Ammah da Musaddiq na kokarin fitowa Ammah na fadin. "Bana son shashanci wace zahrar Kuma yanzu ko karfe tara Bata karasa ba nasan hal......" Bata karasa ba zahra ta shigo, ai suna arba da Ammah ta jefar da handbag din ta karaso da gudu-gudu ta shige jikin Ammah sai ta saki wani siririn kuka, tana fadin. "I missed you Ammata! I really missed you, kinki zuwa ki ganni Ni Kuma ya hanani zuwa". Tunda zahra ta shigo wani fitinannan kamshi ya doki hanci Mama ta rude ga uwa uba yanda zahrar ta koma ko makaho ya shafata yasan taji dadin masauki, Dan ba karamin kyau da Wani irin fresh tayi ba. "Ke Kuma menene haka idan koroki yayi ba sai kiyi bayani ba ai kuka baya magani Daman kowa ya sayi rariya yasa zata zubar da ruwa Kuma tsintacciyar mage ai Bata mage". Mama ta fada tana kallon zahra data shige jikin Ammah. Dan murmushi Ammar tayi tana fadin. "Zahra kuje daga ciki gani Nan, ya jikin malam din ko Baku shiga can ba?". "Munje Yana barci ne, kuma gurin da maza sosai shine yace a kawoni gida zuwa dare sai muje na duba shi". "Ok, shikenan ku shiga Allah ya bashi lafiya". Ammah ta fada ta wuce main kitchen dinsu sata dauko wasu abubuwan tunda Alawiyya Bata Nan ta aiketa gidan Hajiya kaltume. Nan suka bar Mama sororo da tarin kunya wato amsa aka Bata a kaikaice. Jiki ba kwari ta koma part dinta. Su zahra suna shiga Musaddiq ya mika Mata Jakarta Yana fadin. Kai Adda kike yarda Jakarki da kudi da yawa Kuma a ciki". Kansa ta shafa tana fadin "Ni bani da wasu kudi a ciki, Wai Ina zaka Naga kana Bata rai?"
"Ba Ammah bace ta bada kyautar biscuits dina da chocolates da suka rage ba a kaiwa jikar Hajiya kaltume data aiki Aunty Alawiyya Ni Kuma Ina son All butter Kuma babu a Nan kusa sai naje store Kuma Zazzabi nakeyi". "Ah gaskiya ba'ayi daidai ba, kayi hakuri na bude opay sai na yiwa magaji transfer saiya sawo maka" "Kai! Adda ki duba da kudi fa a jakar sosai". Budewa tayi taga da gaske yakeyi to tana tunani lokacin da tayi barci ya Zuba matasu.
Jeka kirawo Amadun gidansu Aunty mujiba yaje ya sawo maka". Ya fice Yana tsallen murna. Ammah ce ta shigo da wasu ledoji a hannunta, da sauri zahra ta tashi ta karba tayi kitchen dasu, da Ido Ammar ta bita 'yar tata ta cika Masha Allah ta cicciko kamar me karamin ciki Amma idan tayi la'akari da duka yaushe suka bar garin a halin ciwo ai ko cikin ne be Isa ya nuna Kansa haka ba, kawai samun hutun Zama guri Daya ne. Kusa Ammar ta zauna data dawo. "Ki daina saka turare haka duk kamshinsa ya kashe min nawa na freshner da turaren wuta". "Wallahi Ammah Wanda nake sakawa ne na saka, yanzu Dan Allah Ammah inata rokonki jki taimaka ki saka Baki ya maidoni gida Amman Kika qiya, nasan badan rashin lafiyar Baba malam ba bazezo Dani garin Nan ba". Dan murmushi Ammar tayi Tana K'are Mata kallo. "Meyake Miki da kike son barin kusa dashi ki dawo Nan kina ganin hakan shiya fiye Miki? Ashe har yanzu Baki da wayo kada na qara Jin magana makamanciyar wannan daga bakinki,duk inda mijinki ya saka Qafa ki maida taki duk inda yace ki zauna ki zauna". "To Ammah,amma fa Kinga mahaukatan gidajen da yake kaini wallahi Sunfi Qarfin kwakwalwata Dan Allah ki taimaka kiyi min gata ki tambaye shi ya fada Miki gaskiya waye shi Kuma daga Ina yazo Kuma meye sana'arsa wallahi Ammah tsoro lamuransa suke bani. Fuska biyu gare shi wallahi ko suturar da yake sakawa a can ba irinta yake sakawa a Nan ba ki agogunansa fa Rolex ne, Kuma duk gidan daya kaini babu abinda babu hatta suturar da Zan saka da akwaita idan zamu shekara bazan nemi suturar sakawa ba shima haka, ban fada Miki ba harfa gidan Nan garin Saida na tarar da mahaukatan kayan sakawa a can". Wayar dake jakar ta aka Kira abinda ya katse Mata zubar da takeyi kenan. Tunda ta dauko wayar Ammah ke jinjina Kai da duk abinda zahra ke fada ta dauke shi rashin son Zama da Mahmud ne ke dawainiya da ita Amma ganin iPhone 16 plus yasa jikinta yayi sanyi wayar wajen 1. 46 a gurin zahra? Dole tasan waye 'yarta take aure ko kowa be mata wannan aikin ba ita zata yiwa kanta saboda akwai bukatar sanin waye shi, tunda zilai ma korafinta kenan akan gidan daya saka aka kaisu da Kuma yanda ake kawo Mata kudi ace shiya bada a Bata bayan sutura tace an Bata kusan kala goma babu na banza tace wasu ma Bata taba zaton sata samesu ko a Jace ba an Bata sabbin su. Jin Mahmud ne yasa zahra Dan kallon Amma taga ko hankalinta Yana kanta sai taga ta Mike ta nufi kitchen ajiyar zuciya ta sauke Dan wasu kalamai yake fada Mata Wanda suka girmi shekarunta kamar bashi bane ya kwana zulumin lalurar Baba malam, wato yazo ya ganshi ya samu 'yar nutsuwa ze ishetq da wannan maganganun nasa masu nauyi a kwakwalwarta. "Kina jina?" "Uhmmm ina ji, Dan Allah kayi min Alfarma na kwana gurin Ammah wallahi nayi kewarta sosai". Abinda kunnuwan Ammah suka jiyo Mata kenan tazo fitowa. Jinjina Kai tayi tana ayyana bazaki mayar Dani sakaran uwa ba kibi mijinki can ku karata". Ya koma taci gaba da abinda takeyi Daman fitowa tayi taji idan zataci fattira wadda aka yiwa Imam be Kai ga tashi ba taji ana neman mayar da ita shashasha ta barta ta kwana a Nan mijinta na can rakube kamar gwauro.
Mama ce a daki tana ta faman Kai kawo da waya a hannu ganin zahra ya daga Mata hankali ba kadan ba, a fill ta Fara fadin. "Jar uba wallahi baze yuwu ba wannan ce matar Almajirin? Da sake wallahi Alhaji munafuttarta yayi yasan ko waye ya dauko agola ya bawa ga 'ya'yansa na cikinsa be Basu ba, wato ni za'a yiwa lullubin biri ko? Wai Ina Kika shiga ne Asabe! Naje gidan,na tura babu ke babu mahaifiyarki na Kira wayarki Bata aiki Kuma mahadin cimma burina Yana hannunki tunda Kika karbo ban Kara jin ko labarin Wanda ya ganki ba" Ita kadai a daki tana ta buga sambatu kamar sabon kamu, Aunty Ladi ta Kira akace Mata wayar a rufe take jefar da wayar tayi Kan gado tana buga tsaki tana fadin. Wallahil da sake dole nayi Wani Abu yau ba sai gobe ba". _AUREN HUCE HAUSHI_
08055362975
* MAMAN FATEEMAH*
Page 59
.......... Abincin kawai Ammah ta zubowa zahra ta fito mata dashi, lokaci Ahmad din yazo zahra ta bashi kudin da za'a sawowa Auta kayan kwalam, Ammah ce ta tsawatar Jin yawan abinda za'a sawo. "Ki Bari a sawo masa kawai Ammah ba sai ya rinqa zuwa makaranta dasu ba tunda yace nasa kinyi kyauta dasu" Tana Ciro kudin magaji ya shigo da manyan ledoji a hannu Yana fadin. "Ina Ammah Bari kiga Aunty zilai yanda ta zama inaga supplement Tasha ta Zama haka naga alama harda bleaching takeyi Kinga yanda ta ... Bai karasa ba yaja birki Yana ware idanu. "Kam bala'i! Wannan yarinyar yaushe kikazo? Gaskiya kinci Amana koki nemeni duk amincin dake tsakaninmu dake har kizo garin nan ki mike kafa kiyi awanni Baki bada cigita ba,wato kin Zama DONE ko? yanzu na baro mijinki a Asibiti shima ya wani zama Jan wuya,da gani Yana Gane garin Dan ba haka yabar garin Nan ba, ku fad'i gaskiya dai ko kun danne Kan dollars din America na qungiyoyin da kuke yiwa aiki?". Pillown kujera karami zahra ta jefa Masa daga inda take zaune. "Allah ya shirye ka magaji, Kai Kullum baka girma, shi yasa nafi son Zama da Ya Imam wallahi saboda komai nasa gentle yake yinsa, amma Kai kamar rikon kauye,gaskiya da a kauye akayi ka da anga tabargaza, Wai nice yarinya ka tafi ka nemi yarinya ni yanzu yayarka ce dole kace min Adda, sauran amsar Kuma sai mun kebe Zan baka ita". Dariya ya dauka Yana tafa hannu. "Very good, inye yaushe kikayi Baki irin haka? Da sake wallahi Nima azo ayi maganar manya auren nan zanyi, kuga yarinya ta zanzare tayi bulbul sai magana fal cikinta". "Magaji! Magaji! Wallahi ka fice kada na Bata maka Rai yanzu, daga zuwanka zaka damu mutane, ka Dade bakayi auren ba mutumin musawa". Hannuwa ya hade irin yanda indiyawa sukeyi. "Sorry Ammah idan na fita dawa zatayi Hira ki Bari mu Dan cukusa kadan dan Allah". Sallamar zilai ce ta katsewa Ammah hanzari abinda zata fada. "Lah! Aunty zilai har kun karaso? Sannu da hanya". Zahra ta fada, tana kallon magajin. Yara ne suka shigo da Kaya suka sauke suna gaishe da Ammah, sannan suka gaishe da zahra. Da sauri magaji ya fita Yana Fadar. "Ina Zuwa ya fice. Wasu kayan ya dauko, zahra na ganinsu ta gane Wanda Zayyan ya aje a gidan dake BAWO ROAD ne, sai yanzu taga Ashe kilishi ne dasu dabino da cukui sai tarkacen kayan zaki dasu BAMA. Sauran Kuma suna cikin ledoji. Gurin da Ammah ke zaune Zilai ta karasa ta tsuguna tana fadin. "Sannu da gida Ammah mun sameku lafiya? Ashe Kuma Baba malam haka tsautsayi ya sameshi, Allah ya bashi lafiya, Kuma nagode Ammah Allah ya jikan mahaifa ya yiwa zuri'a Albarka a tayani godiya gurin yallabai nagode, nagode". Sai hawaye. "Ikon Allah! ku kuma da 'yan kuka kuke shigowa garin? itama mutuniyar da kukan ta shigo min, amma na fashimci kukan Dadi kukayi gaku nan kun zama wanke hannu ka taba". Yar dariya zilai tayi tana goge hawaye. "Wallahi Ammah duk yanda Zan fada Miki karamcin da akayi min Ni kaina baze misaltu ba Kinga waccan jakar wallahi duk suturu ne babu ta karamin kudi a ciki Kinga yauma abinda oga Sameer ya bani". Ta dauko envelope brown ta dora a gefen kujera inda Ammar ke zaune. "Tab Aunty zilai kice shagalinku kuke a kanon kun ninke mu a nan, da gaske Ammah wannan yarinyar ma kukan tayi Miki?". "Innalillahi! Magiya fice Dan Allah". " Kiyi hakuri Ammah, Amman fa ba inda zani nabar wannan sabgar Arzikin Kinga fa". Ya fada yana nuna kayan dake zube a tsakiyar parlourn. "Allah ya shirya" "Amin" suka fada, gurin zilan Ammah ta juya. "Lafiya kalau muke, wallahi kuwa Haka Allah ya kawo wannan kaddarar sai fatan Allah ya bashi lafiya, ki dauke abunki an gode madallah". Harta yunkura zata tashi ta koma tana fadin. "Ga kayan tsara Nan inji oga Sameer yace a kawo Niger sukaje aiki".
* * *
Baba malam bashi ya farka ba sai kusan hudu da 'yan mintina, lokacin Mahmud ne kadai a dakin Shima ya rigasu fitowa daga masallacin ne, da sauri ya taso ya karasa kusa dashi. "Sannu Baba ya jikin?" Mahmud ya fada Yana rik'e hannun malam Daya Miko Masa. "Alhamdulillahi Ala kulli halin, duk abinda Ubangiji ya yiwa bawa akwai hikima a cikinsa, Kuma bawa baya wuce K'addararsa sai dai neman sauki,Haka Allah ya hukunta tun ran gini tun ran Zane rubutaccen al'amarine baya canzuwa,ita kaddara haka take sai dai fatan Allah ya bani juriyar da dangana, inaga iyakar takawar kenan wadda akayi a baya na gode da kokarin ku naji jiya kaima bakayi barci ba, Allah yayi muku Albarka ya saka muku da mafificin Alkhairinsa, ka shigo cikin rayuwarmu ka zamar Mana fitar data haske Mana duhu, Ina hadaka da girman Allah kayi hakuri bisa abinda akayi maka ka koma ga mahaifanka nasan ba manta garinku kayi ba na dai kyaleka ne saboda halin bacin ran da nake ganinka a ciki,naso idan ka dawo na sakaka a gaba muje ga iyayenka kodan halin damuwa da nake ganin mahaifiyarka a ciki, gata da matsakaitan shekaru sai a tausaya Mata, Mahmuda ba'a fushi da iyaye kaji, sun 'yan lallabone, to sai ga kaddarar data sameni Kuma lallai naso yin wannan Alkhairn Amma bamu San abinda Ubangiji ke nufi da hakan ba shi Allah s.w.a baya da sabon aiki". Tunda Baba malam ya Fara magana Mahmud ya sadda Kansa kasa Bai dago ba Saida yaji ya saka aya a maganarsa, amma fa maganar ta doki zuciyarsa ba kadan ba. A hankali Mahmud ya dago idanunsa Wanda sukayi jajur badan Yana namijin duniya ba da kuka ze fasa kamar mace, hannun Baba malam ya Kara rik'ewa cikin nasa. "Baba ka daina fadar haka in Sha Allah saika cigaba da taka kafafunka Kuma niyyarka ta Alkhairi saika idata da izinin Allah in dai akwai inda suke magance matsala irin taka da Alfarmar Manzon Allah s.a.w.w sai an kaika, daman Nima nayi tunanin fada maka asalina idan na shigo garin sai Kuma wannan ibtila'in ya faru, kayi hakuri Allah ya baka lafiya yasa kaffara ne, yanzu ka kwantar da hankalinka ka cire damuwa in Sha Allah zaka warke, ai sunce ba wata damuwa Mai yawa bace bayan ne ya Dan bugu, harma oga sameer yazo ya gana da likitocin bansan dai yanda suyi ba, sai ya shigo muji yanda za'ayi"
Habib da Sameer ne suka shigo tare da zugar dattawan unguwa masu zuwa dubiya tun safe Dan mutum be yanke ba tafe suke maza da Mata, Dan ma iya Abu na gida tunda tazo da safe taga jikin ta Fara koke koke Habib ya mayar da ita gida. Sun Jima suna Masa Addu'ar samun lafiya sannan suka tafi tare da ajje Masa kudi masu Dan kauri. Mahmud da Habib suka Kai shi toilet suka taimaka Masa yayi alwala suka dawo dashi suka kwantar yayi ramuwar sallar da ake binsa.
* * * * *
Tunda Mama taga shigowar zilai da yanda taga zilan ma ta koma, sai hankalinta ya qara duguzuma ya tashi, nan da nan ta shige toilet dinta dole ta nemo malam na Bande. Cikin sa'a ringing Daya ya dauka Yana fadin. "Idan kin Kira ta baci kenan, yaya ake ciki!?" Babu Bata lokaci ta Fara bayanin. "Malam da matsala sosai Dan komai nema yake ya cukude, da Alama Alhaji munafutta yayi ance an bawa yarinyar nan Almajiri Qolo,amma wallahi kaga yanda ta koma kamar matar shugaban Qasa, ko Mai aikin mu da suka tafi tare ta Zama abin kallo duka a cikin 'yan satiitka Dan Allah ayi wani Abu kada bakin cikin su ya kasheni, malam ga Kuma na nemi Asabe na rasa duk komai Yana neman lalace min". Wata dariyar marasa nutsuwa yayi duk da yawan shekarunsa Yana fadin. "Ai daman na fada muku ayi duk yanda za'ayi ta turara turaren wutar nan sai kukayi sake kayan suka fada a hannun yaron mijinta, sannan Kuma Kika kasa hakuri mu karkare Kika canza guri, wannan shiya rusa duka ayyukanki na baya,maganar Asabe Kuma bana Jin zaku Kara haduwa da ita nan kusa dan naga tayi nisa sosai da nan din, naga alamar kamar korarta akayi daga garin saboda Wani asirinki Daya tuno ban dai fashimci abunba sosai gaskiya amma Yana da nasaba da ita wannan yarinyar gaskiya sai dai itama kanta yarinyar Bata sani ba". Karkarwa jikinta ya dauka ta Fara hada jibi. "Dan Allah malam ka taimaka mini kada maganar nan ta fito har abada, kayi duk yanda zakayi ita kanta Asaben a dauke Mata hankalinta daga garin dama jahar Baki Daya. ko nawa ne Zan baka fatana kada asirin ya tuno, ita Kuma kayi abinda zakayi kada ya Kara marmarin Zama da ita har abada yanda ya kawota ya tafi ya barta a nan kada ya Kara tunawa da ko sunanta dama garin gaba daya". "Ki kwantar da hankalinki, Naga tafiya Mai nisa da zeyi Kuma gaskiya banganta a kusa dashi ba, zata zauna Dan Zama kam Amma Kamar yanda nasha fada Miki Banga rabuwa a cikin aurensu ba in dai shine ze saketa to bangani ba". "Zan turo maka da sako ayi duk abinda ya Kamata kawai". Ta fada tana sauke wayar daga kunnenta, iska Mai zafi ta buso daga bakinta tana fadin. "Haba biri yayi Kama da mutum shi yasa na nemi Asabe na rasa kaura wambai tayi batan dabo, to waye ya Kamata har malam yace asiri ya tuno kenan wayarta ma ankwace tare da sauran sakonnin da zata kawo min, Kuma sakon farkon ma hannun yaron mijinta ya fada". Ta maimaita yaron mijinta yafi sau biyar. "Me hakan ke nufi kenan? Ina ga ko cikin yaran makarantar ne, amma a cikinsu waye ze budewa Asabe Ido har ya iya koreta daga garin irin haka afujajan da gaggawa?". Haka ta zauna tana faman kullawa da kwancewa babu Mai Bata amsa. Abincin kusan kala uku Ammah ta saka Alawiyya tayi tunda itama ba laifi Ammah ta horata, zilai ce ta shiga ta tayata duk da Ammah tace ta huta ita da ta dauko hanya, Amma Sam taqi Zama ta shiga sukayi tare, a manyan warmers aka Zuba abinci, magaji Ammah ta Kira yazo ya Kai Asibitin. Zahra bacin da Bata samu ba jiya ta shige bedroom din Ammah tayi kwanciyar ta daga ita sai vest da Wani wando skintight ta saka wata hula Mai budedden Baki ta zubo da gashinta baya ta Fara barci hankalinta kwance. Sai da Ammah ta Gama sallamar magaji ta shigo dakin, tsayawa tayi tana Qarewa zahra kallo, yanda ta ganta komai nata ya kara cikowa kirjinta da kasanta suka ciko sai zuciyarta ta shiga kokonton anya babu yaron ciki a jikinta kuwa? duk da bangaren ta ne da yake abin anzo Kan 'yarta ne sai ta samu confused. Abinda zata dauka ta dauka ta fice daga dakin. Sai kusan magariba zahra ta farka, wanka tayi ta shirya ciki rigar Atampha royal blue da ratsin Baki Mai manyan ganye, dinkin yaso ya matseta daga kirji abinda ya Bata mamaki ke nan dan kasa fitowa tayi Saida ta rufa da gyale sannan ta iya fitowa, sabanin da rigar har Dan yawa tayi Mata daga wurin breast cup din. Su Aunty zilai ta samu suna gyara parlourn, Zama tayi tana tana musu sannu, Alawiyya ce tace. "Aunty zahra a Zuba miki Abinci?". Dan yamutsa fuska tayi. "A'a bana Jin yunwa duk cikin ma bana jin Dadinsa, ki hado min salad kawai ya isheni sai ki hado min da fruits salad ya isa". "To Bari naje na hado miki" . Ta fada tana barin gurin. "Aunty zilai Ina Ammah ne naji shiru ba motsinta?". "Tana sabon part din Abba na bayan Nan kinsan Ammar mu Bata daukar raini ta dawo da Abba nan ta raba musu turaka ita da Mama, kinsan halin Mama har Saida takai hakurin Ammah karshe ta yiwa part din can yaji ta nuna sai dai a raba ko Kuma ta hakura ta barmata mijin duka shine ya dawo sabon nan". Baki zahra ta rike tana kallon Aunty zilai. "To ke Aunty zilai waya Baki wannan dogon labarin naga daga ni har ke bama garin Nan?". "Sahura ce ta bani labari dazu Dana shiga part din mu Zan aje kayana". Tsaki zahra tayi tana fadin "Kai Allah wadaran naka ya lalace, har abada sahura bazata daina gulma ba na tsani mutum Mai fuska biyu". Hira sukaci gaba har Alawiyya ta kawo Mata hadin salad din. Kiran sallah ya tashe su daga parlourn. Zahra na sallah Ammah ta shigo, cikin sabuwar kwalliya sai kamshi take bazawa, Abu ta dauka a wardrobe dinta ta fice, zama zahra tayi tana Addu'ointa har aka Kira sallar insha'i. Tana cikin sallar ne wayarta ta dauki Kara, sau biyu ana kira tana tsinkewa, Saida ta Idar ta dauka *Amor mue* ta gani Dan murmushi tayi. Kiransa tayi lokacin ya fito harabar Asibitin duk ya gaji so yake ya kwanta ya huta kiranta yayi ya fada Mata ga Zayyan nan ze daukota ta duba Baba malam din shine Kira biyu Bata dauka ba Yana niyyar na uku saiga kiranta ya shigo. Picking yayi tare da amsa sallamar ta. "Ina sallah ne ka kira, ya jikin Baba malam din?" "Jikinsa Alhamdulillahi, ga Zayyan nan na turo shi ya daukoki kizo ki duba shi". Shagwab'e fuska tayi kamar yana ganinta. "Nayi zaton sai gobe tunda dare yayi, pls ka kirashi kace ya dawo Dan Allah kaji". "Do what I said". Ya kashe wayar gaba Daya. Ta gumi ta Zuba tana zancen zuci. "Yanzu ko kwana dayan baze barni nayi a gidan nan ba saboda Allah shi yafi son Kullum Yana manne Dani kamar yaron goye" Dago Kan da zatayi taga Ammah tana tsaye ta Zuba Mata Ido. Karasowa tayi tana fadin. "Lafiya Naga kin hade rai?". "Ba shine yake Wai ya turo a daukeni naje ba duba Baba malam ba, nace ya Bari Saida safe yanzu dare yayi shine yace A'a". Godiya ga Allah Ammah tayi a zuciyarta yayi maganinta yarinya da muhallin ku kice bazaki tafi ba. Amman a zahiri sai tace. "Aida kinsan Baki duba shi ba da tun yamma zilai ta rakaki kunje tare, nima Abbanku ne da baya garin da tun safe naje naga jikin nasa, Amma Zuwa safe in Sha Allah Zan shiga na duba shi tunda Abban naku Yana hanya".