Auren huce haushi complete - Chapter 4
Auren huce haushi complete Chapter 4: Auren huce haushi complete Chapter 4. *****A bedroom din ammah Zahra ce da Sajida suke tattaunawa akan abinda ya…
4,373 words
*****A bedroom din ammah Zahra ce da Sajida suke tattaunawa akan abinda ya faru,sunyi iya nasu hasashen amma sun kasa gano bakin zare Sajida ce tace "nifa Zahra Ina hasashen wani Abu akan lamarin ki" "Kamar me kenan?" Dan Jim tayi kafin tace "Anya ba asiri ake yiwa duk wani Wanda yazo da niyyar aurenki ba? Ki tsaya kiyi nazarin abun Mana ko mafarkan da kike yi duk lokacin da maganar aurenki ta taso abin dubawa ne" Dan murmushi Zahrar tayi "kin jiki kema bestie wane irin asiri Kuma,ana zaune lafiya to waye har ze bata lokacinsa da kudinsa gurin yi min wani Abu kawai daga Allah ne kinsan kowa da yanda Allah make jarabtarsa ni tawace tazo a haka". "Eh na yarda daga Allah ne bana inkari Amma akwai sanadi, inaga gobe ma zan wuce duk da nacewa Umma sai Wednesday Amma na fasa wallahi Rimi zanje gurin Baban Umma na fada Masa ai kinsan shi farin sani Kuma zeyi duk abinda ya kamata tunda ke wani lokacin kanki ba Maths". Kwarkwar tayi da ido Dan Allah Saji kada ki tafi ki Bari a Gama komai saiki tafin". Wani kallo tayiwa Zahra "tafiya dole na tafi Amma zan dawo kwana kusa in Sha Allah, kinsan Zama da Baffa yasa Ina Gane wasu abubuwan tunda Yana fadw min ire -iren abubuwan da suka shafi sihiri Kinga yace min duk wani ciwon da yake da lokaci misali ace kullun sai dare mutun yake kasa barci kinsan da matsala, ko ace mace duk ranar girkinta Bata da lafiya ko duk ranar girkinta tana zubar da jini amma idan ta Gama aikin shike nan sai ya dauke babu, ko kamar taki matsalar sai an saka Miki ranar aure sai ana gaf da biki abun yake lalacewa, Kika sani ko Abban naku ma ya Fara irin wannan tunanin ne yasa ya yanke wanna hukuncin cikin sirri ki tsaya kiyi tunani Mana" Sosai magungunan Sajida sun sakata a tunanin da Bata tabayi ba. Sauke zazzafan numfashi tayi tana fadin "Allah ya kyauta ni duk kin sakani a tunani wallahi" Haba "Bestie ai kinsan ruwa baya tsami a banza me ake nema a gurin mace Allah Bai Baki ba Amma sai an Yi abu kama-kama ya lalace zance da muka Dade munayj da Aunty Hasana kenan jiya Kuma ta bain go ahead na naje na faduwa Baffan rimin, tace ma zata fadawa Ammah, ma". Kiran da Aunty Hasana tayi wa Sajida ne ya katse musu tattaunawar, ta tashi ta fita.
Washe gari duk bakin Ammah suka tafi, Inna maimuna kadai suka Bari sai Amarya taje dakinta zata koma gida. Part din da bakin suka zauna Ammah tasa su Zilai suka gyara sosai tunda Daman nasu Zahra ne, kafin yamma gurin yayi tas kamar ba'ayi wata dabdala a cikinsa ba. Bayan sallar insha'i zahra da Sajida suka koma part din. Suna zaune a kan gado Autan Ammah musaddiq ya shigo dakin da sallama hannunsa rike da leda fara Mai kyau ya mikowa Zahra yana fadin "gashi Aunty inji wannan na gidan Baba Malam din yace a kawo Miki Kuma yana duba ki, Kinga Nima ya bani". Ya Mika nata 1 k din dake hannunsa.". "To angode madallah". Ledar Sajida ta dauka ta bude waya ta gani sabuwa kar a ciki. "Wow gaskiya ba karya ke! Irin wannan babbar harka haka, Dan Allah Yi min bayani naji yace wannan na gidan Baba malam din waye ko angon namu ne da ake Raina mana ya Fara tsula Mana abun arziki haka?". Baki ta Zahra ta zunbura. "Nace Masa Ina bukatar sabuwar waya ne da zai kawo min, ni wallahi a mayar Masa". Ta fada tana kokarin amsar ledar faga hannun sajidar. "Ke tsaya da Allah yi min bayani yanda zan gane, Ina taking wayar naji kina wata magana".
"Tana gurinsa tun safe ya karba ni bansan abinda zeyi da ita ba, ya dai ce na bashi kawai ni kuma na bashin shine Kuma maimakon ya bani tawa shine ya Aiko min da wannan".
Musaddiq Sajida ta kalla 'kai auta maza kaje kace tace ta gode Allah ya Kara nudi" Sai da ya fita sannna ta juyo gurin Zahra. "Amman wallahi kin bani mamaki Allah ya tarfawa garinki nono ki nemi ki Bata rawarki da tsalle to kici gaba har ki nuna b'araka a gaban 'yan uba, Koda wasa kara ki Kara ba'a yiwa miji haka ko bakaso Abu baka nunawa a gabansa, kika san da Yaya yayi sawo Miki danya faranta Miki Rai Amma Zaki wani kwasale shi kice a mayar Masa kina son tun yanzu ki kashe Masa Gwiwa ko". 💋❤️ AUREN HUCE HAUSHI💋❤️
JINJINA TA MUSAMMAN GA MALAMAN MAKARANTA ALLAH YAYI JAGORA YA QARA BASIRA DA JURIYAR SAUKEN NAUYIN DA AKA DORA MUKU NA AMANAR YARA QANANA👫👫👫👫👍👍👍✍️ ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ This page is deducted to you Families of late Alhaji Isah Musa Bakin kasuwa kazaure jigawa state. 🔷PAGE SEVEN🔷
_______Mika tayi tana salatin ma'aiki s a.w.w sannan ta Zoro kafafunta kasa, tunda ta farka tasan tabbas karfe biyu tayi na sulsulin dare har ya zamar Mata jiki. Dubanta ta kai inda Sajida ke kwance barcinta take sadidan cikin kwanciya hankali, sai taji Ina ma ita ce haka, wasu hawayen ne suka ciko idanunta a hankali tace "Ya Rabbi ga baiwarka Mai rauna ka jibinci lamarina dan Isar Manzon Allah s a.w.w. kada ka barni da iyawata ka iya min da iyawarka kada ka Bari makiya su yi min dariya ka bani rinjaye ka dorani akan duk Wanda yake son Hawa kaina". Ta Mike tsam ta nufi toilet din cikin dakin sai Kuma ta fito saboda shaf ta manta kafin su kwanta taga famfon ya dauke Kuma da alama ba'a kunna layinsu na tanki ba. Cikin rashin tsoro ta bude kofar ta fita zuwa bayan part din Mama don ta kunno ruwan, gurin ta dosa gadan gadan sai Kuma tayi turus, magana take jiyowa daga wurin da sauri ta koma baya dan bata San abinda zata gani ba. Tana tsuma ita fa duk da Bata da tsoro amma tana tsoron ganin abinda yafi karfin idonta ko Kuma wani mugun abun. Dole tayi hakurin yin sallar a koma ta kwanta tana ta sake-sake har kusan Asuba, ba Kuma taji motsin wani na tada hankali ba. Saida Sajida ta tashe ta lokacin har an Fara sallah a masallacin gidan nasu. A gurguje tayo alwala da alama Sajida ce ta shigo da ruwan. Bayan sunyi sallah zaman Azkar sukayi har lokacin da gari yayi shahhh alamar wayewa, sannan suka koma suka kwanta. Dukkan su ba barci suke ba, Zahra ce ta danyi tsaki kadan ta tashi zaune. Kallonta Sajida tayi. "Yaya Bestie akwai damuwa ne?" Dan juyowa zahrar tayi tana kallon sajidar tana Kara wani tsakin "nifa wallahi na fada Miki tsoron mutumin nan nakeji tun ranar Dana Fara ganinsa a gidan Baba malam nake Jin wata irin shakkarsa. Dan Allah a haka zamu rayu bana ko son kallon idanunsa? Kinsan wani tarin abin haushin jiya fa hannu yasa ya dago fuskata Wai dole saina bude idona na kalle shi ko Kuma ya bani mamaki, Kuma fa ranar Nan a asibiti har wani shafar min fuska yayi Yana fadar nayi hakuri da wannan hadin shima ba so yake ba, kawai yayi biyaya ne tunda baze iya yiwa su Abba musu ba, amma ni Ina iya fada musu bana so". Baki Sajida ta rufe tana kunshe dariyar ta. Kai ta shiga girgizawa tana fadar Babbar magana ki fadawa su Abba bakyaso! Wato ke ga marar ta ido ko? Shima har yasan kimarsu da baze iya yin musu dasu ba saike ce marar kunya Zaki Fadi Baki so, ki rabu dashi kwaai abinda nake so dake yanzu ki koyi dakewa a gaban nasa sannan ki daina tsoron idanun nasa, Wai tsaya fada min menene a cikin idon nasa da yake firgitaki duk girmanki da wayonki da wayewar ki?" Wani shagwabe fuska tayi kamar Mai Shirin fasa kuka. "Bazaki gabe ba, ni kaina bansan ya zanyi ba saboda shi fa na daina zuwa gidan Baba malam tunda lokacin kullum Yana tare da shi kuma sai yayi ta kallona yana tsareni da wadannan idunuwan nasa kamar Mai jin barci". Yanzu dariya sosai Sajida keyi harda kwalla tana fadar Babbar magana tab kice abin asali ya Samo shi ai kaya ne suka tsinke Masa a gidin kaba kece dai kike bulayi" "Kamar yaya?" "A'a bazakiji mutuwar sarki a bakina ba ai tunda an hada anyi Mai walahar...". Sautin kiran waya ya dakatar da shegantakar da sajidar ke mata. Wayar da aka kawo Mata jiya ce ta dauki kida, Sajida ce ta Mika hannu ta dauka M.M DANGE ta gani Yana yawo akan screen din. Zahra ta mikawa tana fadar oga ne da alama a Sha soyayya lfy. Tayi waje tana fadin Bari naje nayiwa Ammah shara. Bata daga Kiran ba har Saida ya kusa katsewa kana ta daga tasa a kunnenta. Daga can taji Yana fadar "Assalamu Alaikum warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu". A zuciyar ta a amsa Dan da gaske in dai zata ganshi ko taji maganarsa kasa samun nutsuwa take. Sake maimaita sallamar yayi, da kyar ta amsa masa tare da fadar " Ina kwana?" Shiru taji ba'a amsa ba kamar ma an sauka daga layin, amma ga mamakinta tana dubawa sai taga Yana nan, itama shirun tayi kudin sunata tafiya saita saka handsfree ta aje wayar kusa da daga gefe tana kallon ikon Allah. Saida ya mula Dan kansa "yace ya jikin naki I hope kin shan maganinki?" "Eh" ta fada a takaice. "Fine"yace shima a takaicen. Ita mamaki ma yake Bata har wani turanci yake jefawa a magana kamar gaske. "Sai an jima ta fada tana kokarin katse Kiran. "Kada ki kuskurs ki kashe min Kira" ya fada in serious tongue. Shiru tayi tana mamakinsa sai wata izza yake Mata kamar wani abin azo a gani. Muryarshi ta tsinkaya Yana fadin ki bude data na turo Miki sako idan da abinda kike bukatar ayi ko a Kara sai ki fada min, take care". Kit ya kashe kiran. "Kutt!" Ta fada "amman gayen nan yama Raina ni wlh Wai kada na kashe Masa waya" Kwafa tayi "zakaga na kiraka ganin idon ka" ta Jafar da wayar tana mita. Taso yin barci Amma ta kasa dole ta hakura, wayar ta Kara daukowa tana kare Mata kallo. Number din Hameeda ta Fara sakawa tunda taga sabon layi ne ya dauke natan, ga mamakinta sai taga sunan Hameedar ya bayyana ba bata lokaci ta kira. Tana ta ringing kamar baza'a dauka ba sai Kuma ta daga da sallama ai tana jin muryar Zahra ta Fara mita "yanzu Dan Allah kin kyauta tun jiya nake neman layinki Amma shiru na Kira Mama nace ta Baki tace min bakya Jin Dadi kina barci, wallahi Kinga yanda hankalina ya tashi kuwa ki Bari lokacin da Sajida ta fada min halin da ake ciki wallahi daba final muke ba Allah da barinta zanyi c/o na taho gida har fada mukayi da Salma Wai ai sai inje na baiwa Mushahun hakuri ya dawo ya aure maganganu dai gasu nan ki Bari kawai ai jibi zamu Gama in Sha Allah komai dare a gida zan kwana". "Allah ya yarda ki Bari kawai wallahi Ina cikin yanayi akwai damuwa Dan Allah kizo ko naji sauki abubuwan". Ta fada tana share hawaye, sukayi sallma Dan it ma Hameedar kukan take. Wai ita Mushahu ya yiwa haka, duk wadanda suka fasa aurenta Bata taba Jin Wanda ya Bata Mata Rai ya Kuma tsaya Mata kamar wannan ba ai ko wace irin matsala ce ita ya kamata ya Fara fadawa ba ya yanke mu'amala da ita ba a lokacin da take matukar bukatarsa ya manta shakuwar dake tsakanin su da alkawarirrikan da suka yiwa juna.
Kwantawa tayi tana tunanin baya a haka wani wahalallan barci yayi gaba da ita.
**********Tun Yana tsammanin ganin ta bude data ta duba sakon har ya cire Rai da hakan. Lambar Abdul Hakeem ya Kira sun jima suna waya kafin suyi sallama. Laptop dinsa ya janyo yaci gaba da aiyukansa sai kusan azzahar ya Gama. toilet din cikin dakin ya shiga ya dauro alwala,a masallacin hotel din Yaya sallah lokacin daya fito Kiran Habib ya shigo Masa "Wai Dan Allah kana Ina ne tun dazu muke nemanka kazo masu aikin hada furniture's din Nan ne suka Gama da cabinet din kitchen". "Ok gani Nan inaga kada kayi nisa zuwa an jima su Aunty zasuzo suga gurin" Ya fada. Yana nufar gurin da ya saba aje lifan din Habib. Wayar Ammah Abdul Hakeem ya Kira ya fada Mata Mahmud yace a turo a gano gidan an Gama gyaran, dakin Mama Ammah ta shiga ta fada Mata sannan Kira Aunty Hasana ta fada Mata kafin ta wuce gurin Alhajin ta fada Masa tunda shiya dawo daga gidan gonar sai su Abdul Hakeem ya baro suna yiwa shanu Allura da Basu magunguna. Wurin karfe biyar Aunty Hasana ta debesu a mota harda Sajida suka nufi Hayin bankin cikin jagorancin Habib, lokacin Inna Bata Nan taje MIYA gurin wata aminiyar ta da sukayi aikin Haji shekara daya.
Duk cikinsu ba wadda Bata kadu da ganin gidan ba domin ba karaya an narka mahaukatan kudi a gidan bazaka tab'a cewa renovation akayi Masa ba, bedroom's ne guda uku biyu suna kallon juna dayan Kuma daga gefe da alama yafi sauran girma Kuma shi kadai ne a rufe, sun zagaya ko Ina sai santin gidan Sajida tace tana ta daukar video, falon kadai abin kallo ne duk da ba komai a cikinsa sai fitilu da aka kunna sai Kuma AC da aka ware. Hajiya mama ce ta kasa hakuri ta leka ta Kira Habib Nan falon ya shigo Yana fadin "gani Mama" Yana Dan rankwafawa. Aunty Hasana mama ta kalla "Hasana Dan Allah ki tayani tambayar yaron Nan tunda shi namu ne na gida baze cucemu ba, Wai wannan yaron sana'ar me yake daya iya Kama hayar wannan uban gidan"?" Kara risinawa yayi Yana fadar "ba haya ya Kama ba Baba malam ne ya bashi kyauta, sai Kuma kungiyar yake yiwa aiki suka kawo masu aiki suka yiwa gidan 'yan gyare -gyare harda kayan daki ma suka zuba masa, Bismillah Bari na bude muku ku gani yanzu ba dadewa zuka Gama hadawa da kitchen din suka tafi". Dakin ya bude musu ba Hajiya mama da take ta kwana biyu ba, ko Aunty Hasana da Sajida Saida suka Zama 'yan kauye Dan tunda suke Basu taba ganin irin wanna gadon a zahiri ba, ita kanta aunty Hasana lamarin Yana neman ya gagari tunaninta fa ance Almajirin Baba malam to Amma idan aka saka mizanin hankali abin yafi karfin yanda aka fada to wane irin NGO's ne da suke irin wannan aikin akan daidaikun ma'aikatan su haka?" Gaskiya abin akwai abin dubawa. Lokacin da suka fito harabar gidan ne wata Hilux ta shigo da kaya a bayan motar mutane uku ne a motar bakar fata biyu fari daya Kamar balarabe Kamar kwara. Kameme Hajiya mama ta hanasu tafiya sai da aka sauke kayan ta gani abinda da suka Gane irin katuwar plasima din Nan Mai cin Rabin bangon Nan ne kawai amman sauran tarkacen Basu Gane komai ba, haka suka kada suka tafi mama nata mitar "A'a da sake Alhaji ya titsiya yaron Nan saiya nuna Iyayen shi kafin a Kai Masa yarinyar Nan haka kawai aje ayi kitso da kwarkawata mutanen yanzu ba abin yarda bane sai kaga mutum har mutum Amman a Baki malam a ciki Kuma Fir'auna". Maganar data Basu Aunty dariya kenan.
💋❤️ 💋❤️ 💋❤️ AUREN HUCE HAUSHI
💋❤️ 💋❤️ 💋❤️
STORY AND . WRITTEN BY MAMAN FATIMAH
PAGE EIGHT
Lokacin da suka shigo gidan ana ta kokarin daura alwalar sallar magariba. Sai bayan sallar insha'i ne Mama ta shigo dakin Ammah suka hadu da Aunty Hasana suna fadawa Ammah yanda suka gano gidan da Kuma yanda abin ya daure musu kai. Nisawa Ammar tayi tana fadar "Mama ki Sami Abban kiyi Masa bayani yanda ze fahimta kinsan yanda suke da malam bana tunanin wannan abun ze saka ya canza ra'ayinsa duba da yanda ya yanke hukuncinsa Bai nemi shawarar kowa ba". "Aiko dai ya kamata ayi wani Abu gaskiya Nima lamarin ya tsaya mini a cikin zuciya". Aunty Hasana ta fada. Sun jima suna tattaunawar kafin Mama ta koma daki tabar Autty Hasanar da Ammah. Zama Aunty Hasanar ta kyara ta fuskanci Ammar ta Kira sunanta "Anya wannan Mahmud din ba abinda yake boyewa kuwa Ammah Kinga gidan kuwa ga wannan uwar wayar daya canza Mata kinsan kudinta kuwa ? gaskiya I doubt much, ni dai kiyiwa Abban magana da kanki Kamar zefi daukar abun serious akan na Mama". Can Kuma sajida ce tasa Zahra a gaba tana ta faman zuba. "Innalillahi! Kinga gidanki kuwa? Allah ya bamu ya taku wallahi Zahra ki godewa Allah. Wallahi Allah ya Gama miki duk wata ni'ima ta ko Ina kinyi gaban da Nan kurkusa dai kafin a fiki za'a Dade ana lalube. Zahra Naga mijinki har mun gaisa ada Ina adawa da auren Amma tunda na ganshi Naga Yana yinsa nasan yanzu ne kikayi aure da mijin daya Dace ke.Kawai dai matsalar za'ace ba Mai kudi bane,amma a yanda gidan da zaya ajeki yake wallahi ko minister ne sai hakan, akwai abinda na gani a gidanki wallahi ban taba gani a gidanki kowa ba duk yawona sai dai a film amma dai a zahiri A'a ban taba gani ba Allah Bai kaini gurin ba". Tunda ta Fara zuba Zahrar ke bin sajida da idon lokaci daya duk ta wani rude sai zuba take Kamar 'ya 'yan kanya. "Kin Gama?" zahrar ta tambayi sajidar. "Eh na Gama aini an ma yanka ta tashi na fasa tafiyar zanyi waya da Mom taje can Rimin sumailar gurin Baffan kawai, tunda Daman zatazo nan din ba suna kwantagora". "Ke Kika sani dai tunda Naga kina nema ki Zama wata daban ko dai an canza min ke da wata ne ko Kuma wani abun ya fada Miki ya goge Miki hadda ne?". "Eh da alama Kam Dan ya fiki iya lafazi gaskiya inaga na Zama 'yar team dinsa fa tunda Naga ke Baki da wayo".
Ta fada tana dariya.
Washe gari tun safe Abba yasa aka Kai furniture's din Zahra gidan Daman Aunty Hasana sunyi magana da Wanda zasu hada musu kayan, kayan kitchen da sauran kayayyakin duk suna gidan Aunty Hasana daga can aka ringa daukowa, masu aikin su suka hada komai na gidan hatta kitchen su suka gyara komai, gidan ba karamin kyau yayi ba, ba karya duk Wanda yaga gidan yasan na 'yar gata ne.Dan wasu irin mahaukatan Turkish furniture's ne wanda kakanninta ta gurin uwa sukayi Mata duk wani abun more rayuwa akwai shi a gidan Nan, bangaren electronics ma sai a cikin lockers aka zuba wasu, komai yayi. Lokacin da aka Gama gyaran Aunty Hasana da sajida ne sukazo gani ba karamin burgesu gidan yayi ba Dan sai yanzu ne ya fito a asalinsa na kyau da kayatar da Mai gani, komai na gidan unique ne Masha Allah.
A waya sajida ta daukowa Ammah komai. Ita kanta Ammah Kai Kawai take jinjinawa Dan ba karamin burgeta abin yayi ba, sai dai can kasan ranta rudani ne kala-kala domin abin ne duk yazo a hagunce. Tana tsoron lamarin sosai sai da har abada baza iya jayayya da Alhajin ba Dan da gaske ubane tsayayye Wanda baya nuna banbanci tsakanin abinda ya Haifa da Wanda yake bashi ya Haifa ba, amma harga Allah tana zulumin wannan AUREN HUCE HAUSHIN da Alhajin yayiwa 'yar marainiyar Allah, mazan yanzu sunce suna sonka ma ya kukan kare idan Zama yayi Zama ballantana matar cushe ta San komai Daren dadewa ranar da yaga irin matar da yake so Sai dai zahra tayi hakurin zama Kawai, duk da tasan Bata da haufi akan yarinyar Tata Dan macece har mace abin alfaharin kowa ne namiji ace ya mallaki Kamar ta, to Amma shi lamarin so daban yake duk kyan mutum da asalinsa ba lallai ne ace yana burge kowa ba domin shi dai so makaho ne. Ajiyar zuciya ta sauke a hankali duk jikinta yayi Mata wani irin Sanya ta kalli Aunty Hasana tace "Hasana Ina jin wani irin rauni a zuciya ta game da lamarin nan Ina tausayin yarinyar nan rayuwa tana ta walagigi da ita sai nake ganin Kamar laifi nane Dana kafe a barmin yarinyar Nan na hana kakanninta ita ni Kuma nayi sakacin da aka maida rayuwar ta Kamar kwallo ana ta dokata daga Nan zuwa nan". Ta karasa maganar hawaye na zubo mata. Abinda tunda Allah ya kawo Aunty Hasana duniya Bata taba gani ba a zahiri gurin Ammah Nan da Nan hankalinta ya tashi sajida ma kukan ta Fara duk da batasas takamaimai man abinda ya saka Ammah kukan ba, tashi tayi ta fice daga dakin jin an Fara Kiran sallar magariba. Aunty Hasana ce tace "Haba Ammah duk yanda Kika jure bakin cikin baya na abubuwan da suka faru Baki taba zubar da hawaye ba sai yanzu da Allah ya nufa akayi ai godiya Zaki yiwa Allah daya kawo karshen wahalar ba kuka ba". Gefen zani tasa tana goge hawayen. "Hasana Ina hango abinda ke bakya hangowa ne,masu iya magana suna cewa matar shige Bata daraja ba irin wannan rayuwar na sowa Zahra ba to sai dai kana naka Allah Yana nasa Kuma nasan ne gaskiya. Ba komai haka Allah ya tsara komai mukaddari ne daga gare shi, naji Alhaji Yana maganar zuwa juma'a za'a kaita".
*******Tun bayan kammala karatunsu na bayan insha'i da suke na littafin iziyya yake zaune a kusa da Baba malam har kowa ya watse ya rage saura su biyu tunda malam yaga haka yasan da magana a bakin Mahmud ne. "Ya ya akayi ne Mahmuda?" Malam ya jefo Masa tambayar, Kara dukar da Kai yayi kafin yace "Daman maganar kayan lefe ne dazu Oga Sameer ya kirani yace ya hado tasa gudunmawar kenan, shine nace Bari na fada maka Dan kasan da zuwansu". "Ikon Allah shi wannan yaron baya gajiya ne Kamar baisan ciwon nema ba tunda yazo ya riski maganar Nan yake Yi kan jiki kan karfi. Allah ya saka Masa da Alkhairi yabar muku zumunci". "Ameen" ya amsa. Harya Mike ze tafi sai malam din ya dakatar dashi, dawowa yayi zauna. Gyaran murya malam din yafa kafin ta jefo Masa tambayar. "Sai zuwa yaushe ne kake ganin zamuje ga mahaifan naka kaga dole muje musu tunda wannan lamarin ya faru". Kai ya sadda kasa Yana fadin "zamuje in Sha Allah Amma Dan Allah a Kara min lokaci da kaina zanyi maganar ayi hakuri". "To ba laifi Allah ya iya Mana kaje ka Samu su Habibu kuje acan gidan ku kwana kaga sun zuba dukiyar kasan yanzu mutum ake kiwo ba dabba ba". "To in Sha Allah za'ayi hakan amma ni Ina Nan sai dai su Habib din suje". "To ai hakan ma yayi Allah yayi Albarka". Saida ya dudduba dakunan yaran ya tabbatar da komai lafiya lokacin sha biyu ta wuce, dakinsu ya nufa wanka yayi ya saka kayan barci sannan ya hau gado ya bude laptop dinsa. Email dinsa ya shiga Yana duba sakknnin daya samu sakon daya shigo ne ya dauki hankalinsa. "Ya Salam!". Abinda ya iya ambata kenan sai Kuma sautin daddad'an ringtone dinsa ya karade dakin. "Sameer!" Ya fada a hankali yasan za'ayi haka, ya haga wayar Yana fadin "Ta Yaya hakan ya faru?"
Daga can bangaren Sameer din yadan furzar huci Mai zafi Yana fadar "wallahi nayi duk yanda zanyi Amma abun yaki yuwuwa dole ka daura ka kawar da komai muje gaskiya Dan kasan tunda akaje Nan zuwan nake ne Kawai mafita". "Amman ai kasan halin da ake ciki so kake ace na gudu nabar 'yar mutane Eyeh?". "Cool down Mana my man abin Bai Kai nan ba aikin daine ya taso na gaggawa Kuma dole sai da Kai za'ayi Dan haka suyi hakuri su aje maka ita zuwa sanda ka dawo ko Kuma ka dauko abarka ku tafi, kaga ai tafiyar tafi yi maka armashi ko?" Ya fada cikin zolaya. "Dan Allah ka Zama serious mana, kayi duk abinda ya kamata a Nan goben ka hakura da zuwan ka turo wannan friend din naka tunda yasan gurin ya kawo kayan kawai, Kai Kuma ka Kira Baba malam ka fada Masa daga can sun nemi ganin wakilansu na kasa da jahoshi da kananan hukumomi nasan dai kome ake ciki baze wuce kwana buying zuwa uku ba kaga lokacin na tare a gidana nafi son na barta a Nan gidana akan na tafi Bata tare ba".
"Ko dai.......?" Sameer ya fada Yana dariya. "Allah ya shiryeka ko dai me? kasan ni salihn ne ba ruwana da wannan sabgar sai ku". Kit ya kashe wayar sannan yayi switch off dinta.
Misalin karfe Sha biyun Rana wata tamfatsetsiyar mota Parker a kofar gidan malam. Akwatuna Yara suka dunga saukewa suna shiga falon malam saida suka Gama sannan baki nufi falon malam din bisa jagorancin Habib sun gaisa sosai da malam suka gabatar Masa da kayan daga Sameer. Malam yayi godiya ya saka Albarka ba adadi. Falon malam ya bar musu sukaci abinci suka huta sannan Habib ya rakasu can gidan suka gaisa da Mahmud din. Sai bayan Azahar suka tafi malam yayi musu Sha Tara ta arziki. Kayan malam yace suje su duba su gani saboda da an jima za'a Mika musu can gidan Alhajin. Kaya ne na gani na fada an zubasu Kamar ba gobe, an shigarwa da iya Abu ciki ta gani malam yace ta turawa makotanta na kusa suzo su gani anjima za'a Mika musu. Bayan fitowa daga sallar la'asar ne Malam Bukar ya fadawa Alhaji yanzu su malam Mudi da Alaramma malam Haruna zasu kawo kayan Zahara'u. Fada Alhajin yayi akan kayan da za'a kawo Yana fadar "Haba malam Dan me za'ayi min haka ko wancen da aka fasa auren Kai sheda ne ban karbi lefe ba da suka matsa cewa nayi suje da kayan idan tazo saiya ba matarsa". Kai malam yanjinjina Yana fadin "Anyi hakan Kam amma wannan shima bamu muka hada ba wannan yaron Sameeru ne ya turo dasu dazu yace gudunmawarsa ce aba Amarya" "Ikon Allah shi baya gajiya da dawainya haka daga wannan sai wance Allah ya saka da Alkhairi ya bar.zumunci na jima banga yaro mai karqmcinsa ba abin duniya Bai rufe Masa ido ba".