Kenza eBookz

Auren huce haushi complete - Chapter 46

Auren huce haushi complete - Chapter 46

Auren huce haushi complete Chapter 46: Auren huce haushi complete Chapter 46. ........... Ai kukan da Salma ta fasa sai ya Zama kamar rura wutar bala'i…

4,205 words

........... Ai kukan da Salma ta fasa sai ya Zama kamar rura wutar bala'i akayi a zuciyar Mama, nan da nan tayo Kan Salma da manya manyan zagi kamar diyar maguzawa. "Kukan uban me ki kazo Kika sakani gaba kina mini ko wata jaraba Kika kwaso min Ina zaman zamana". Ita dai kukanta take ba kakkautawa. "Wallahi Zan Miki dukan bala'i yanzun nan dan kin raina ni sai ki sakani gaba kina min kukan babu gaira babu dalili". "Na shiga uku mama ciki ne daniiiiii...." Ai ita kanta mamar batasan yanda akayi ta doro gaban Salma ba jikinta kamar ana kada Mata gangi sai mazari take tamkar Wadda jaura tabi ta kanta, wata irin Shaka ta kaiwa Salma tana fadin. "Wallahi gara na kasheki na huta da inga wannan bakin cikin". Kakari Salma ta Kama nan da nan idanunta suka firfito daman ga jiki ba kwari Kullum Zazzabi. Cikin Rahamar Allah Hamza ya shigo daman ita ta aike shi tace Idan ya dawo ya shigo tana ciki ya kawo mata, badan haka ba zati iya yiwa Salma mummunan lahani. Da sauri ya nufo Mama Yana fadin. "Mama Lafiyar ki kuwa? Me tayi Miki haka? Yaushe ma tazo garin? Meta kawota?". Lokaci Daya ya shiga Jero Mata wadannan tambayoyin. Ganin kamar Bata cikin hankalinta yasa shi saka karfi ya banbare hannun Mama daga wuyan Salma. Faduwa tayi sharab a sume Nan da Nan hankalin Hamza ya tashi da gudu ya fita kitchen ya dauko ruwa Mai sanyi ya kwara mata, ya Kara Zuba Mata sannan ta kawo numfashi a wahale, har lokacin jikin mama Bari yake, kamata Hamza yayi ya zaunar yana tambayarta meya faru zata dauki doka a hannunta kome Salma tayi Mata ai bazayi Mata irin wannan danyan aikin ba da Allah baisa yazo ba da Allah kadai yasan abinda ze faru kenan. Kuka ta fasa Masa tana fadin. "Wallahi gara ta mutu da wannan abun kunyar data dauko mini, yanzu ina Zan saka kaina Ni Rabi'a shike nan duk wata fuffuka ta Kuma ta Kare a gidan nan kin tozartani kin wulakantani". Ta saki wani gunjin kuka. "Wai nifa har yanzu Baki fada min me tayi Miki ba Ni wannan zancen ba gane shi nakeyi ba fa". Ido jazur Mama ta dago ta kalli Hamza. "Cikin shege jake tayo a makaranta".. Hamza jin maganar yayi tamkar saukar aradu a Cikin Kansa. "Cikin shege Kuma how comes?" Ya fada yana kallo Salma Wadda ke fidda numfashi da kyar ga ruwan hawaye tamkar an bude lataccen famfo. "Bazakiyi magana ba Saina Ida aikin da Mama ta fara?". Cikin galabaitacciyar murya Salma tace wallahi Ya Hamza Nima bansani ba lokacin da naje Jos ne Ya Mukarram din Mama Ladi yace nazo na rakashi duba abokinsa a Asibiti da mukaje Asibitin bamu ganshi ba shine ya kirawosa a waya yace ai suna gida tun safe shine yace muje ya duba shi tunda ya riga ya sayi kayan dubiya, da mukaje gidan bamu samu kowa ba Daya kirasa a waya sai yace mu zauna yaje allura ne chemist, shine muka shiga mun Dade sosai baizo ba sai Ya Mukarram din ya Ciro Mana freshyo biyu yace musha tunda ko ruwa babu a gidan, wallahi daga lokacin Dana Sha zuwa yin barcina baifi minti biyar ba daga nan wallahi bansan meya faru ba sai tashi nayi na ganni a wani yanayin Yana ta bani hakuri Wai aikin shedan ne". Ta karasa tana sakin wani kuka. Dafe Kai yayi ya tafi taga-taga ya zauna a Kan sofar dake dakin. "Innailaihi wa innailaihi raji'un, wannan wace irin masifa ce? Shi yasa har Raina bana son zuwan da sukeyi Jos din Nan saboda gudun irin haka yanzu Dan Allah wa gari ya waya? Kin lalata future dinki totally Baki da sauran wata Qima ta Diya mace kin Bata record dinki har jikan jika wallahi". Yayi tsaki ya tashi har ya Kai bakin kofa ze bar dakin Dan idan ya tsaya saiya yi Mata fiye Dana mamar, ganin idan ya fita ba tare ta yiwa tubkar hanci ba ze iya zuwa ya Kira abbansu ya fada masa. "Kai dawo ka zauna zanyi magana da Kai" Ba musu ya dawo ya zauna yana bin Salma da Ido wadda ta takure guri Daya tana sauke numfashi kadan-kadan. "Kanaji ba wannan maganar ta tsaya iyakacin mu ukun Nan idan najita ko a bakin Abban mu ban yafe maka wallahi Dan fasa maganar Nan tamkar ka dauko wuka ne ka dabi min a cikina kaji abinda na fada ko? yanzu idan an fito sallar asuba kazo ki wuce Jos ka kaita gidan murja Zan shigo Nima zata fito ta kofar baya sai ka dauketa bana son wani yasan da zuwanta gidan nan". Sadda Kai kasa yayi yana nazarin maganganunta. Kada Abba yaji me kenan? Tana nufin baza'a fada Masa yasan halin da ake ciki ba ko me?. Take ya aro jarumta ya yafa, ta tako ya shigo ciki sosai sannan ya zauna Inda ya tashi. "Yanzu Mama menene hikimar hanawa a fada Masa wannan ba Karamar magana bace fa kiyi tunani Mana". zaburo Masa tayi tana zare masa manyan idanunta

"Wallahi naji maganar Nan sai ranka yayi bacin da Bai taba yiba yanda nace haka za'ayi, tashi ka bani guri Wanda baya kishin 'yan uwansa yanzu kai ko cewa nayi kaje ka fada ai ka nuna ba haka ba abun ya Zama sirri". Tashi ka bani wuri saura Kuma ka Bari wannan munafikin Mai gadin yaga salmar ya fadawa Abbanku ka dauki motarka ita ce me glass Mai duhu". tana Gama fada ta tashi ta nufi toilet tana zabgawa Salma harara.

*****

Cikin lafiyayyan Turkish bed Zahra ce kwance tayi lif a Cikin blanket sanyi da kamshi freshner suna ratsata, a hankali ta dauko wayarta tayi dialing number dinsa harta tsinke ba'a daga ba. Kiran ta sake Nan ma the same thing, sai taji hankalinta ya tashi ta tashi zaune ta kunna wutar dakin ta zuro kafafaunta kasa tana Kara Kiransa. Tana kokarin Kara Kiran nasa Kiran ya shigo. "Alhamdulillahi" Ta fada a hankali tana sauke numfashi sannan ta daga Kiran. "Assalamu Alaikum warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu". Ta fada Yana gyara zamanta, sallamar ya amsa Mata a kasalance sai taji hankalinta ya tashi ba haka ya Saba Mata ba. Meu Amor, meya faru? naji kamar baka cikin mood me Dadi pls menene? Dan Allah fada min ko jikin Baba Malam din ne?" Saida ya danja fasali kafin yace mata. "Precious Ina cikin damuwa sun shiga da Baba Malam za'ayi Masa aikin sunce twelve hours Amma har yanzu fourteen hours ba'a fito dashi ba, ba kuma wani information da muka samu sai dai shige da fice da yayi yawa a dakin mun tambaya sunce babu wata damuwa suna Kan aikin ne,Kinga ta Ina Zan same peace of mind ne?". "Au yau ne Daman za'ayi aikin da ba cewa sukayi sai wurin jibi zasuyi ba?". "To ai da abinda suka gani ne shi yasa suka rage kwanakin aikin". "Allah ya bashi lafiya,dan Allah kada kayi abinda ze karya masa gwiwa, you have to be very strong fa, ka ringa bashi courage akan ze tashi". "To ki tayani addu'a yanda na kawo shi Allah ya taimakani na maido shi gida lafiya, preciousss.. Baba Malam ya karya min zuciya da yawa, nayi rashinki kusa dani nasan da kina kusa dani ko dumin jikinki kadai ya Isa ya saka min nutsuwa bare nasan za'a taimaka min ai ko?" Ya fada da wata murya Wadda ta motsata. "Kaiiii... Meu amor pls ba kyau fa". "Meye ba kyau din? Lallai nayi sake da yawa fa yanzu da kina dauke da babyn mu da baki Fadi wannan maganar ba, yarinya ki shirya soon komai ze daidaita, ai kin gane?". Shiru tayi masa. "Oya Yi magana Mana". "Me kake son na fada...?". Komai ma ki fada min Ina so?" Bata Kara tanka Masa ba,yayi nacinsa ya hakura, "kina jina" "Eh..." ta amsa masa. "Gobe in Sha Allah kije gidan Ammah kiyi Mata yini sai ku dawo gida,inaga Sameer zezo kuje kano". Dan Jim tayi kafin tace " "Plssss... Dan Allah meu amor ka barni na Kwana a gurinta Ina so naji duminta?". "Ban fahimta ba? Kamar Yaya kiji duminta? Goyaki zatayi?". Ya jefa Mata tambayar. Jin tayi shiru ya sake cewa "Baki da damuwa akan wannan ki Bari kizo sai kiji Mai dalili, Amma dai maganar Kwana babu ita". "Plssss... Dan Allah fa". "Ok zuwan ma a hakura bazaki sakani a tension ba bayan Wanda nake ciki, wallahi idan na barki Kika Kwana ai ko barcin kirki Bazan iya ba kinsan riskyn dake cikin zamanki a gidan kuwa?".

"Risk! A gidan namu?". "Yessss..." Ya Bata amsa Kai tsaye. Saita rasa abin fada Kuma, duk mamakin duniyar Nan ya cikita Wai akwai hatsari a zamanta cikin gidan, to hatsarin me?. "Ok shikenan, na hakura tunda gidan namu kake zargi". "Ba gidan nake zargi ba, wasu daga cikin mazauna cikinsa nake zargi, kuma wallahi badan darajar Abba ba Saina ladabtar da duk wanda ya shiga gonarki Amma a juri zuwa rafi wata Rana za'a fasa tulu ne". Das ya yanke Kiran daga Jin yanda ya gama maganar kasan ya tuna wani Abu Daya taba dagula Masa lissai.

Ta Jima tana nazarin maganganunsa, kenan dai da gaske ne ya Kama wata rashin gaskiya daga gidan nasu Idan tayi la'akari da ranar Daya sakarmata su barbar suka hanata fita wato yayi haka ne kada taga ko wacece aka Kama a gidansa din. "Ubangijina ka Kara bani kariya". Ta fada a hankali tana gyara kwanciyar ta.

Mahmud na yanke Kiran ana fitowa da Baba Malam, a kalla ya samu good fifteen hours, da dan sassarfa yabi bayansu, wani bangare suka nufa dashi nan ma VIP section ne dakin harya fi wancan tsari da komai tamkar gida, Saida suka kwantar dashi suka kara karfin A/C sannan suka Fara yiwa mahmud bayanin yanda ya kamata a ringa yi masa sannan ze dauki kaman thirty days a haka ba tare da an daga shi ba ko kwakwkwaran motsi.sannan suka fice daga dakin, zuwa yayi ya saka shi a gaba yana jinjina Lamarin ubangiji, tsoron Allah ya Kara shigarsa ganin yanda Dan talikin Nan ya Zama sai yanda akayi dashi, idan ma fa da kwanan ya Kare shikenan, wani Abu ya gani kamar rigar roba an saka Masa a kirji ga wasu Abubuwan a kugu Suma Yana kwance baya ko motsi Nan da Nan yaji hawaye sun cika masa Idanu, Rabon da yayi kuka harya manta duk cimadadin da aka Sha a baya Bai taba zubar da hawaye ba, amma yau dai zuciyar ta karye, ya godewa Allah da yasa su Habib basa Nan ya sender su gida tunda yaga Hankalin Habib ya tashi ganin lokacin da aka ambata ya wuce da awa daya ya shiga rudu,Saida mahmud yayi masa fada sosai sannan yadan Sami nutsuwa ganin hankalinsa ya kasa kwanciya yasa dole suka bar Asibitin. Saida mahmud yayi kukansa sannan yaji Dan dama-dama, shi duk Lamarin rayuwa ya kwance Masa daga kansa, Bai taba jin abinda yayi Bai kyauta ba sai yau yayi Dana sani yafi sau shurin masaki, wani irin fushi yayi Wanda ba ragin daka sai da ya shafi kowa, a nan ya yanke hukuncin Kwana duk da lokacin Sha daya ne na dare Amma sai yaji ko Nan da can baze iya matsawa yabar Baba Malam a haka ba Yana fatan idan Allah ya nufi ya farka to ya Fara arba dashi a gabansa, tunanin Amminsa Yana damunsa kwanan nan idan da Wanda yake ganin ya batawa Bai wuce ita ba duk rintsi ai uwa-uwa ce amma sai itama ya hada yayi musu kudin goro, duk da yasan shirunta kusan shiya kawo Karin lalacewar abun Amma dai dole yaje kada alhakinta ya Fara Kama shi fa. Kiran wayar Abubakar yayi, lokacin suna zaune a parlour tun dawowarsu yake faman bawa Habib Baki akan ya dangana yayi Masa Addu'a. "Bazaka gane bane Abubakar nifa Baba Malam na sani a matsayin uwa da uba duka duk wani gata na duniyar Nan babu Wanda bai min ba, dole na shiga tashin hankali Mana idan ya mutu Yaya zanyi?". Sosai ya bawa Abubakar tausayi. Yana kokarin hada kalaman da zeyi amfani dasu gurin nuna Masa abinda ya kamata sai Kiran mahmud ya shigo. Da sauri Habib ya dago Yana kallon Abubakar. "Shi...ne yaaa kiii..ra ka ko?". Ya Fadi maganar a rarrabe kamar sabon Dan koyon Karatun hausa. Gyada Masa Kai yayi Yana amsa Wayar. "Yes sir, to shikenan Allah ya bashi lafiya, eh gani nan" Ya fada Yana mikawa Habib wayar. "My man ka samu nutsuwa kaji, sun fito dashi tun dazu anyi aikin cikin nasara in Sha Allah". Wata irin nutsuwa ta shigi Habib, Alhamdulillahi kawai yake fa.

Bayan anyone sallar Asuba Abba ya shigo ya samu Ammah ta Idar da sallah tana ninke hijabin, "sannu da dawowa" Ta fada sannan ta gaishe shi. "Yau fa barci nakeson yi sosai da safen Nan saboda na zaunu a mota yanayin hazo ya hana jirgi tashi kwata-kwata, ko Zaki tayani barcin tunda kin kawoni gurin da babu Mai takura Miki ki dama daddawarki da moda babu Mai gani, Au Kinga Zan manta danki dai ya kasa hakuri matarsa yake so, d Jiya ya kirani muna hanya yace an shiga da baba Malam aiki, sannan yace min yau Zahra zatazo ta wuni a gurinki gobe su wuce kano zata bishi India din, Amma bana Jin ya fada Mata, na fada Miki dai Koda abinda zakiyi Mata" Gyaran murya Ammah tayi tana fadin. "Yanzu Abban Yara bazaka bincko Mana asalin yaron Nan ba kadafa ya gudar mini da 'ya saboda Allah". "Kai haba Asma'u ki cire wannan tunanin daga zuciyar ma Mahmud Dan mafita ne Ina nan Ina bincken menene musabbabin abinda ya rabo shi da gida dole akwai dalilin dayasa ya baro komai nasa ya taho yayi irin wannan rayuwar". "Ban gane ba Abban Yara kayi min bayanin da Zan gane". Dan tunani yayi kadan kafin yace Mata. "Ki kwantar da hankalinki mahmud ba boyayye bane Dan cikin.garin sokoto ne a yanda aka fada mini nasan mahaifinsa farin sani, sai dai har yanzu ban Gama yarda da shine mahaifinsa ba duk da tun ganina na farko dashi Naga nasan fuskar amma na rasa Inda nasanta Saida aka fada min mahaifinsa Naga tabbas fuskarsa nake gani ata mahmud, Dan haka ki kwantar da hankalinki in Sha Allah uwata saita Zama farin wata Sha kallo duk bacin ran da aka shiga sai ance gara da hakan ta faru ki bani lokaci harna karasa nawa binciken kinje". Ya fada yana Dan murmushinsu na manya. "To shi kenan Allah ya rufa asiri, nagode da kulawar ka garemu". "Kada ki Kara yi min godiya akan al'amarin uwata yiwa Kaine Nina bada aurenta ga wannan yaro hakki nane ba binciko komar daya dangance shi, sai daga baya muka fashinci gidan ne baya muradin komawa yasa yace ya manta komai na rayuwarsa ta baya sai yanzu nake tunano maganar da mukayi ta saka hotonsa a kafafen sada zumunta na zamani ko za'a dace da wadanda suka sanshi amma kinsan yaron nan cewa yayi a''a ayi hakuri a hankali wata Rana ze tuna". "Au haka kukayi baka fada min ba da wallahi sai ya kawo danginsa sannan za'a bashi ita". Ta fada tana mokewa. "Hannunta ya kamo. Ki dawo ki tayani barcin Mana. Ba musu ta dawo suka kwanta itama barcin take ji dan Shima Abban ba Sanya ga Ammar mu da daukar gyara.

Karfe tara me kyau su zahra suka dira a famfon shanu, Aunty zilai ce ta dauko baskets guda biyu da Daya na Ammah dayan kuma na Abba ne? Suna shiga parlourn ba kowa sai buruntun Alawiyya a kitchen, Jin shigowar mutane yasa Alawiyya fitowa. "Lah sannunku da Zuwa. "Ina Kwanan ku? Ta fada tana karbar ledar hannun Aunty. "Kawo na Kai ciki"... Alawiyya ta fada tana fadin sannu da kokari. *AUREN HUCE HAUSHI *

Maman Fateemah

Page. 67.

...….........

A nan parlour zahra ta zauna suna kwasar hira da Alawiyya saboda itama 'yar shafta ce ta gaske, suna nan magaji ya shigo yana ganin zahra ya karaso da sauri yana fadin. "Kai! A gidan nan kika kwana amma?". "Eh mana da kana tunanin na sallama maka Ammar ne kai kadai? Nima ina son naji dumin uwata". Wata dariya ya saki yana fadin. "Naga wannan Allah yasa Ya mahmud ya daukeki ku tafi wata uwa duniya sai naga ta biniyar gida naga alama irin kune matan da idan kuna cikin garinku kuke raba dai dan zama rabi kuma gidan miji rabi kuna gidan iyayenku bare idan kun raina miji". Maganar Ammah sukaji ba wanda yaji shigowarta ta sha gayu sai zuba kamshi takeyi sam ba zakace su Aunty Hasana 'ya'yanta bane. "Magaji wallahi ka fita daga idona wai me zahra ta tsare maka ne? Naga alama mun kusa saka kafar wando daya da kai a gidan nan". Duka suka juya suna kallon Ammah, zahra ce ta tashi ta nufi Ammah tana fadin. "Rabu dashi Ammah wallahi duk bashi yake ci akwai ranar biya". Dariya su Aunty zilai sukayi suna gaishe da Ammar itama zahra gaishe da Ammar tayi suna zama zahra ta shige jikinta. "Wallahi kiji tsaron Allah magidanciya dake ki tsaya kina zuba tabara dan tsabar samun guri".

"Nayi din, idan fitsari banza ne kazama tayi mana, kaida wannan cinyar sai gani sai hange". Ta fada tana gyara kanta dake jikin kafadar Ammah. Zilai ce ta dauko basket daya da leda sai kuma Alawiyya ma ta sauko sauran suka kawo gaban Ammah zilan na fadin. "Ammah gashi wannan na Abban uwar dakina ne sauran kuma naki ne". "Masha Allah Allah yayi albarka, kwana kukayi kuna wannan aikin ne?". "A'a ko daya tun asuba dai muka fara kinsan uwar dakin tawa babu abinda ta aje a halinki Ammah tasan kanta". Da sauri magaji ya matso yana kokarin bude warmers din yana fadin bari mu gani nasan duk abinda ya fito daga wadannan masu two face din unique ne". Dan murmushi tayi Ammar tana son zama dasu sauda yawa saboda ko bacin rai take sai taji ta samu farin ciki tamkar Tom & Jerry haka suke. Aunty zilan sallama ta yiwa Ammah da zahra tace zataje gida, har taje kofa Ammah ta kirata, tashi Ammar tayi ta nufi bedroom dinta ganin haka yasa zilan bin bayanta, itama zahra dakin data mayar nata ta tashi ta shige dan barci takeji bana sosai, tana jin magaji wanda ya cika baki da gas meat daya diba a plate yana fadin. "Dole ma kafarki kafa ta irin wannan gara ai nan da nan zan canza, ai nasan kin fadawa ya mahmud tare akayi goyon mu". Dariya zahra tayi kawai, lamarin magaji sai shi shidai yaci nama. Sako Ammah ta bawa Zilai na ta biya gidan Hajiya Amina ta fada mata tana nemanta tun dazu take kokarin kiranta network yaki bada hadin kai sam. Parlour Ammah ta fito ba taga zahra ba sai magaji yana ta aikawa. "To acici ina zahrar kuma?". Da hannu ya nuna dakin data shiga saboda ya cika baki. Can ta nufa tayi knocking, da masifarta ta taso zata saukewa magaji sai kuma taga Ammah ce. "Kizo kije ku gaisa da Abbanku saiki tafar masa da abinda kika kawo masa tunda dama bai kai ga yin break fast ba, idan kin dawo kema kizo kiyi naki nasan ba wani abun kirki kikaci ba". "To Ammah bari na fito na dauka ya fita da naga duk su Ya Abdul Hakeem basu shigo ba". "A'a yau inaga basu da fita ko ina kamar Abban nasu". Ta juya ta koma zahra ma ta gyara rolling dinta ta fito tamkar dawisu tana tafiyar nan das-das. Basket din ta dauka ta fice bata bi ta kan dan gidanta ba dayake ta zuba mata zance, wani lokacin har mamakin yawan maganar Magaji take shi sam baya gajiya da magana. Da sallama a bakinta ta shiga parlourn kasancewar a bude ta sameshi, suna dining area sanda ta shiga, directly gurinsu ta nufa,Abba na ganinta ya fara murmushi yana fadin. "Masha Allah, uwata ba raguwa bace har kin fito? Haka akeso ki zama mai himma". Itama murmushin tayi tana karasawa gurinsa ta tsuguna har kasa. "Abbana ina kwana?". Ta fada tana aje basket din. "Lafiya kalau uwata". Basket din ta dauko tana fadin. "Yau dai abincina Abbana zaici gaskiya Ammah". "Gaskiyarki uwata ai babu wanda zaiki abincin babarsa zuba mini Allah yayi Albarka ya baki masu yi miki kema" "Allahumma Amin". maganganu yake mata masu harshen damo daga karshe ya rufe da kara jaddada mata mahimnacin hakuri, sannan ta baro sashen nasa duk jiki a mace. Lokacin data shigo mutumin ya kunna tashar restling yana kallo. Tana shigowa ya taso. "Daman ke nake jira kizo na saida miki wannan jaridar". "Jarida kuma". Tsaki yayi yana tabe baki kamar mace. "Ashe ke bakya daukar haske, to labari zan baki". "Ok. Sai yanzu naje Ghana, bani na sha". Zama sukayi nan kasa kan carpet. "Kina jina wai dan Allah me yasa kikace kada na kawo sahura gidanki? Kinga yanda Mama ta damu kuwa akan nace mata kuna kano kamar zata fasa kuka fa, ke bar wannan kada na manta abinda zan fada miki, dazu da Asuba nayi shirin masallaci na saka J/C dina a leda na nufi kofar baya na aje idan an dawo daga sallah na sulale ta baya na wuce training din ball, kinsan tun lokacin dana samu karaya Abba ya hana ball, ni kuma idan babu ita da matsala gaskiya shine nake fita ta baya har na dawo babu wanda ya sani, to dazun ina nufar gurin naga Mama da Ya Hamza da wannan 'yar rainin hankalin tana rusa kuka sun fice ta kofar bayan ita da Ya Hamzan ita kuma Mamar ta dawo ta wuce ta gefen inda nake tana shafe hawaye da gefen hijabin dake jikinta, harta wuce bata ganni ba nasan duk yanda akayi da magana a kasa tunda babu wanda yasan da zuwan salma gidan nan". Zuru zahra tayi masa tana kallonsa. "Tab Allah ya kyauta can gasu gada, wai zomo yaji kidan masu farauta, ai idan kace ruwan wani ba zai tafasa ba to in sha Allah naka ko zafi bazeyi ba, ayi dai mugani karya dai fure take bata 'ya'ya, ba dai mugun abu suka zaba ba da saura ma basuga komai ba, kace kai baka son cigaban kowa to kaima yaushe zakaga dai dai". "Haka ne kam ai so nake Abba ya gama break naje na fada masa ya kira Ya Hamzan yaji meya faru kuma ina suka tafi ko kuma nace Abban yaje makarantar da kansa ko daga can ne aka samu matsalar". "Kai magaji ina ruwanka da sagbarsu,kasa ido idan tayi wari kowa zeji ne har wani zaka fadawa Abba meye naka a ciki, ka manta hadisin Annabi Asalihissalam wanda yake cewa yana daga kyawun mutum ya bar abunda babu ruwansa? To ka kyautata musulincinka kaima, ka nuna kamar baka san anyi ba idan wani dalili yasa anzo gabar da zaka iya fadin abinda ka gani falillahil hamdu saika fada din". "To shike nan bari naje nayi wani aiki kinsan mun fara project". "Masha Allah Allah ya taimaka, ya dai fiye maka da guzirin tsegumi" . "Allahumma Amin, gaskiyarki yallabiya" Yayi waje.

Ita kuma zahra ta tashi zata koma ciki taji ana knocking din kofa ta nufi gurin, tana budewa taga Hajiya Amina mutuniyar Ammah ce sosai, tana sayar da turarika na jiki dana daki da kayan gyaran Aure dasu dilkar Amare. Jakar hannunta zahra ta karba tana bata hanya tare da fadin. "Sannu da zuwa Hajiya" "Yauwa Amarya ya gida?". "Lafiya kalau Hajiya, ina kwana?". Lafiya kalau Alhamduliahi ya mai gidan naki?. "Lafiya kalau" ta fafa tana sadda kai kasa. "Bari na fadawa Ammar kinzo" Kafin ta bata amsa har Ammar ta shigo, tana fadin. "Lale marhabin da Hajiyar kamshi, lallai kinaji da wannan 'yar taki, nan da nan haka har kinzo".

."Ai ba'a bori da sanyi jiki" ta fada tana dan murmusawa". "Haka ne kam" Ammah ta fada sannan suka gaisa. Tashi zahra tayi zata tafi ta basu guri. "Dawo ki shiga da wannan jakar, ki bude ki dauki fallan sabon zani ki cire kayan jikinki ki dauwa shi gani nan shigowa". Dauka tayi tayi gaba da jakar babu halin tambaya tunda ita dai bataga wani dalilin da ze saka ayi mata wani gyara ba tana zaman zamanta ita da ko mijin baya kusa bare yaji ko kamshin ne. Saida ta bacewa ganinsu sannan Ammah ta bawa Hajiya Amina hankinta sosai. "Kina ji abun ne yazo a gurarran lokaci wai gobe zatabi mijin india sai jiya da dare Abbansu ya fada min, shine na tura kizo kiyi mata dan abunda ba za'a rasa ba, to kuma sai a dazu Zilai ke fada min wata magana, na rasa ta inda zan bullo mata, wai sunje asibiti an tabbatar wa da zilan wai zahra har yanzu wani namji bai santa a diya mace ba, dan da farko an dauka ciki ne ya lalace sai da akayi bincike aka gani fibroid ne ya narke a sanasiyyar maganin da tasha, shine zilan tace wai ko mijin ne bashi da lafiya sukayi shiru ko asibitin da sukaje hanawa tayi a fada min wai kada hankalina ya tashi". Jinjina kai hajiyar tayi. "Babbar magana dole ayi bincike gaskiya, bari na shiga naji yanda abun yake daga bakinta"

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull