Auren huce haushi complete - Chapter 49
Auren huce haushi complete Chapter 49: Auren huce haushi complete Chapter 49. Sun Dade suna Hira da Aunty Aishat har barci ya Fara Kama Zahra sannan tayi…
4,346 words
Sun Dade suna Hira da Aunty Aishat har barci ya Fara Kama Zahra sannan tayi Mata sallama ta nufi inda akayi Mata masauki, bayan ta wuce Aishat da Dade tana auna Lamarin Zahra a zahiri Sam batayi Kama da yarinya marar tarbiyya ba ko masu budedden idanu Amma tayiwa tafiyarsu da Dan uwanta Question mark, idan ta tuna da irin warning din da yayi Mata kafin ya bar gidan. "Gata Nan amanace a gurinsa shi yasa na kawo ta Nan inda zata zauna safe, ki kula sosai nasan halin sayyid a Kan mata duk da kince yayi tafiya to Koda za'a samu akasi yazo bana nan, to ki fada masa yarinyar nan da mijinta Dan muna komawa za'ayi bikinta ya dauke idonsa daga kanta idan Kuma ba haka ba za'a iya samun matsala. "Maji ma ganj, an binne tsohuwa da Rai" Ta fada a fili. A Nan taci gaba da Zama tana jiran ta inda Dan uwanta ze bullo, wurin Sha Daya da minti goma ya bude ya shigo gidan, ya yi mamakin ganin Aisha Ido biyu. "Ashe dai Hali yana nan, yanzu Dan Allah bakiyi barci ba". "Naka wasa ne kana tunanin Zan iya barci banji komai daga gareka ba Nima ban Amayar maka da abinda ya faru bayan baka nan ba". "To ai shikenan Bari nayi wanka na fito inaga kwanan zaune zamuyi yau". Ya shige ainihin dakin da yake sauka idan yazo wani aiki kasar bata yarda ya sauka a hotel ko Daya daga cikin gidajensa, inda Allah ya taimakesu Abbas Dan kanwar Abbie ne Kuma sa'anni suke da yayunsa gashi tasu tazo Daya da mahmud sosai Dan kusan tare suke aiwatar da ayyukan kamfanonin Abbie. Bai Dade ba ya fit Yana baza natural kamshinsa ya zauna yana fadin hada min coffee sai zance yafi tafiya dai dai". Ta tashi ta nufi kitchen tana fadin. "Bari na hada coffee maker yanzu na kawo maka". Tashi yayi ya nufi dakin da Zahra take, a hankali ya tura kofar a kwance a tsakiyar bed din ya hangota da wayar ta a yashe a gefe da gani batasan lokacin da barci yayi awon gaba da ita ba. A hankali ya tako har gaban gadon Yana Kare Mata kallo a cikin dim light din dake dakin, Dan sunkuyawa yayi daidai lips din ta ya Bata light kiss ya shafa gashin kanta a hankali, wayar ya dauke ya Dora Kan bed side ya gyara Mata blanket din ya rage karfin A/Cn ya tofa Mata Addu'oi ya ja Mata kofar ya fice yana Jin wata irin kewarta. A tsaye ya samu Aisha da kallon tuhama ta bishi, yana kallonta Sarai yayi Mata fuska. "Bani idan ya Zama ready". Ya fada yana Mika Mata hannu. Kada hakuri tayi ta kalleshi idi cikin ido. "Wai wacece wannan yarinyar a gurinka? Kuma meye dangantakarka da ita Naga ka shiga inda take alhalin ba muharraminta bane Kai?". Ta fada tana tsare shi da Ido amma zuciyarta sai dokawa take Bata fatan abinda take sak'a Mata ya kasance gaskiya. "Ple Aisha zauna ki nutsu ki tambayeni duk abinda ya shige Miki duhu". Bataki tasa ba zaman tayi tana Kara jaddada Masa tambayarta akan dangantakarsa da Zahra. "Wai meye damuwar ki da ita ne na fada Miki 'yar uban gidana ce, daga haka me kike son ji Kuma?" Lokacin da suke wannan maganganun ita Kuma Zahra kishirwa ta tasheta Karamin fridge din cikin dakin ta duba Babu ruwa a ciki Wanda Kuma Auntyn ta shigo Mata dashi dazu ya huce bazeyi Mata dadin Sha ba. Kofa ta bude ta fito da niyyar zuwa kitchen ta dauko ruwan ta saka ma a fridge din dakin, maganganu ta rinka jiyowa kasa kasa da farko har tsoro ya kamata sai daga baya ta ringa jiyo maganar Mahmud ne da 'yar uwarsa. Abinda taji ya masifar daga hankalinta. "Na fada miki babu komai a tsakanina da yarinyar nan kina ganin Zan iyayin gaban kaina nayi Aure ba tare da sanin iyayena ba? ki rubuta ki aje duk abinda Ammi ta yanke a kaina na karba ita zata nemar min matar aure da kanta, idan kin tuna ta taba fada tayi min Mata a Niger,Wadda har aka kawota tayi sati biyu a lokacin Abbie ya Hana maganar to yanzu zanje natsuguna a gabanta na nemi yafiyar abinda nayi Mata Kuma ta zabar min duk wadda tayi Mata Zan karba da hannu biyu tunda ni dai babu Wadda na gani ta kwanta min da sunan Aure, Kinga gara ita ta zabar min da kanta".. Ai jikin Zahra karkarwa ya fara me yake nufi duk abinda yake Mata pretending ne ba gaskiya ba kenan? Da kyar ta Kai kanta dakin Dan tana shiga ta zube a kasa tana fadin . Naga ta kaina Ni Zahra Ashe ni kadai nake kidin girbina bani da wata kima da daraja a idanun Dan tahalikin nan?.
* AUREN HUCE HAUSHI*
MAMAN FATEEMAH.
09061432330 Or 09055362975
Page 71 ..….... Sai da Zahra tayi kukanta ta bawa uku Lada sannan ta share hawayenta tana hakurkurtar da kanta, lallai irin wannan cin fuskar da ciwo ita meta rasa da yake gudun nunata a matsayin matarsa? Wai 'yar ubangidansa, To ita Kuma zata Kama Kanta in Sha Allah ba Kuma zata nuna taji hirar nan tasu ba. "Ya ubangiji ka shiga cikin lamarinta ka Bani hakuri da dangana bisa jarabawar da kake jarantata da it's Dan isar fiyayyan halitta Annabin Rahama Muhammad s.a.w.w.". Ta fada a fili tana tashi daga inda ta zauna tana kissima abubuwa da yawa a wannan karo. Amma dole ta nemi tudun dafawa dole ta iya Kanta tunda abun yazo da cin fuska har ze ringa gudun hada kansa da ita. Ranar barci dai sai barawo, kwana tayi tana nafilfili da rokon ubangiji mafita.
Bayan tayi sallar Asuba ta koma ta kwanta lamo batajin zata iya fadawa kowa wannan maganar zatayi hiding din kayanta taci gaba da addu'ar samun mafita a gurin lillahil wahidul Qahhar ya shiga duk lamuranta. Da safe kin fitowa tayi har Aunty Aishat ta biyota daki, Tana ganinta Zahra ta tashi zaune tana fadin. "Ina kwana Aunty, Ina Afnan da Abul?" "Lafiya kalau, ya bakunta Kuma? Afnan Kuma Bata tashi ba sai takai twelve tana barci in dai ta farka da Asuba, shi kuma Babana ya tafi school" "Ok. Allah sarki". Zahra ta fada tana Dan Jan blanket din zuwa jikinta saboda yanda rigar barcin take sai a hankali. Dan zama Aunty Aishat din tayi gefen gadon. "Ki tashi ki shirya kiyi break yau zamu shiga Asibiti a duba ki,tun jiya nayi Mana booking na ganin doctor din, kinsan Hussein sai a hankali idan yaso Abu to babu sauki bare Naga ya dauki lamarinki ba Nan kusa ba". "Nifa Aunty ki fada masa na warke tun a Nigeria fa,na biyoshi ne kawai saboda na duba jikin Baba Malam,Kuma wallahi azumi nakeyi yau". Tsare Zahra tayi da Ido sai taga yanayin yarinyar ya canza ba kamar jiya ba, Amma dai batace komai ba ta tashi tana fadin. "Bari na fada masa". Ta fice duk zuciyarta babu Dadi da gaske yarinyar tayi wani irin collapse Wanda Bata San dalilnsa ba. Tunda Aishat ta wuce yace duba tsadedden agogo Rolex dake hannunsa, shifa jiya da kyar ta iya barci ba tare da ita ba a jikinsa sau uku Yana zuwa kofar yana jinta bam da key a rufe. Sai Zuba Ido yake yaga ta bullo, Maimakon ya gansu su biyu sai yaga Aishat ita kadai ta dawo. Kasa hakurin ta karaso yayi ya tashi ya nufi inda take. "Tana Ina Kuma? Lokaci fa Yana tafiya nifa tun seven thirty na shirya". Wani kallo tayi masa ganin duk ya wani rude. "Tace ita babu inda zata ita ta warke, kuma da azumi ta tashi bazatayi break ba". "What!! Bata da hankali ne? wane irin ta warke duka last week fa tayi ta fama da bleeding duk ta daga min hankali, shine yanzu zata fadi haka, salon mu koma Kuma wata matsalar ta taso, tasan halin Dana shiga a wancan lokaci Bari naje na sameta".
Ikon Allah Aishat ta tsaya tana kallo, lokaci Daya ya daga hankalinsa ya wani birkice, Wai me taji Yana fada ne? Me kalamansa suke nufi idan ba Rami me ya kawo zancen Rami. Da sauri ta rufa Masa baya duk ya wani susuce lokaci Daya ita ba taga abin daga hankali ba tace Bata so Amma lafazinsa sun sakata a kokonto ba Dan kadan ba. Da zafinsa ya Kama handle din kofar sai dai tayi locking dinta, a zafafe ya Fara dukan kofar Yana fadin. "Precious me kike nufi da baza kije Asibitin ba? kina son ki tayar min da hankali ne ko? maza bude ki fito mu tafi tun jiya aka Gama komai". Tsayawa Aishat tayi turus Jin kalaman da yake fada Wai ko ya manta a Ina yake ne?. "Previousss...." Ta fada a hankali tana girgiza Kai komawa tayi tunda Allah baisa ya ganta ba. Ita Kuma Zahra tana jinsa yanda ya ambaci precious sai taji wani irin bacin Rai ya lullibeta wata harara ta zabgawa kofar tana gunguni a ciki. "Saina shayar da Kai ruwan mamaki saika karyata kanka da kanka Wallahil Azim, Ni Zahra nafi qarfin cin fuska gurin 'yan uwanka saina saiwa kaina kimar daka Zubar min sai ka nunawa duniya ni wani bqngare ce ta rayuwarka". Toilet ta shige taba iska ajiyarsa. Kasa hakuri Aishat ta dawo, Bata karasa inda yake ba daga dan nesa dashi ta tsaya tamkar a yanzu ne ta biyo shi. " "Wai menene na tada jijiyar wuya, tace bataso ka qyaleta Mana ba lafiyar jikinta bace, ka wuce kawai Nima Ina son na shiga kasuwa saboda wasu Abubuwan amfanin sunyi kasa". Wani duban Baki da lissafi yayi mata. "Wai kinsan wahalar da Tasha kuwa, Kinga yanda ta daga min hankali kuwa? Kin..." Ai baisan lokacin Daya ci wani burki ba shaf ya manta Aishat fa Bata San komai dake tsakaninsu ba.
Tahowa yayi ransa a hade ta rufo Masa baya, Zama yayi ya dafe Kansa. Daga sama ya tsinkayo maganar Aishat. "Wai meya jawo dacin rai haka daga fadin Bata zuwa Asibiti,Kuma sai sakin magana kake kamar da wani Abu a tsakaninka da wannan yarinyar ni ka fada min kamanta bama rufewa juna damuwa ko farin ciki tare fa muke sharing". Bai dago ba Bai Kuma tanka Mata ba. "Miskili kawai". Ta fada a zuciyarta. Itama Bata Kara tofa tata ba tayi wucewar ta sama. Da Ido ya rakata Yana ayyana subul da bakan da yayi. Lokacin da Zahra ta fito daga wanka Bataji motsinsa ba, ta kuduri aniyar sai dai wani tsautsayin idan ya gotta ya ganta Amma ta haramtawa kanta haduwa dashi. Yafi zaman awa Daya da rabi ko motsinta Bai Kara jiba ya koma kusan sau uku, amma babu canji dakin dai a rufe. Dole da yaga Babu sarki sai Allah ya hakura ya wuce Asibitin gurin Baba malam.
Yana ficewa Aishat ta sauko kasa ta nufi dakin da Zahra take knocking tayi Tana Kiran sunanta. Lokacin tana chart da sajida tana fada Mata next week zasuyi graduation, taji kiran da Aunty Aishat din ke Mata, tsam ta taso ta bude kofar arba tayi da Afnan wadda akayi Mata gayu sosai sai kamshin Bom-bon tajeyi zallo ta Fara tana dariya, hannu Zahra ta Mika ta amsheta tana matsawa daga hanya. "Sannu Aunty,ko fita zakiyi ne?" Zahra ta fada tana Zama a gefen gado ita Kuma Auntyn ta zauna a Kan sofar dake dakin, kallon Zahra tayi Ido Cikin Ido. "Me yasa Kika rufe daki kina Jin bro Yana Miki magana kikayi kunnen uwar shegu dashi ko da wani Abu a tsakaninku dashi?". Girgiza Kai tayi. "Ba komai Aunty Ina wankane Kuma na rufe jacuzzi din shi yasa ban jiba, Kuma maganar asibiti mijina ne yace na Bari ba sai naje ba tunda an tabbatar da narkewar ciwon kada a jogalo min wani Abu daban, lokacin da muka taho Baya nan sai Abbana ya hadoni da Ya Mahmud tunda Shima zezo India din, sai a dubani sosai to jiya bayan na shigo ya kirani yace sunyi magana da doctor Hajara tace babu komai kawai dai nazo yawo ne, shine yace to kada naje wani asibiti zeyi magana da Ya mahmud din Ina ganin ya manta ne ko sai yau ze fada Masa". Ta karasa maganar kamar Dade duniya haka akayi ta.
Kallonta Aishat keyi tunda ta ambaci mijinta ita fa nema suke su caza Mata Kai kowa da nasa salon, shi yana wani furuci dake nuni da ita din kamar suna da wata alaka da daf da daf Dan yanda ya ture dazu ita ya saka Mata shakku a cikn furucin nasa, itama kuma gashi tayi wata magana wadda tayi karo da zarginta kuma. Nisawa tayi tana fadin "Allah ya rufa asiri". "To Zaki zauna a gida ne keda Afnan ko kuma Zaki bini muje kasuwa? To ai Kuma kina azumi kada ki kwaso kishirwa". Zubut Zahra ta Mike da Afnan a hannu tana fadin. "Muje Aunty Nima Ina son nayi sayyaya Naga gari Kuma". "To kin fadawa mijinki zakiyi yawo ko?"
Dan murmushi tayi tana wasa hannun Afnan. "Ai ban tare ba, Kuma yace duk inda ya Kama naje yasan bazanyi rashin gaskiya ba". "A'a Kice aikin gyaran amare ya sameni kinzo inda ake bidi'ar gyaran aure". Dariya tayi tana fadin. "kaji Aunty Ni wane gyara za'ayi min kawai ki Bari". Ta fice daga dakin bayanta Aunty Aishar ta biyo. Ita ke driving din motar Zahra na gefenta rike da Afnan. Basu Dade a kasuwar ba suka dawo Zahra laffaya ta dauko tsaraddu masu kyau da tsada a gurin biya Aunty Aishar ta hanata ta biya ta biya Mata. Ba zato suka tarar da mahmud a parlour Yana ibadar kallon ball ana Asian cup, Zahra you tayi kamar Bata San Allah yayi ruwan tsirarsa a gurin ba ta wuce da Afnan a kafadarta Wanda tayi barci, har ta kule ganinsa Yana kallonta a zuciyarsa ya Fara tunanin Wai to meya shiga Kan yarinyar Nan ne haka totally ta canza Masa yanda ta nuna tamkar Bata taba saninsa ba ko gaisuwar Daya Raina ta Hausawan baici arzikinta ba. Remote ya dauka ya kashe kallon Yana fuskantar Aishat. "Shatu Wai me yake damun yarinyar Nan ne ko magana fa batayi min ba ta wuce, kota fada Miki wani Abu da nayi Mata, wato Naga alamar raini ya Fara shiga tsaninmu. Zama tayi daura dashi tana fad'in. "Toni Ina Zan sani ne dazu dai ta fada min mijinta ne ya hanata zuwa Asibitin Wai yace kada a jankwalo Mata wani Abu tunda a Nigeria sun Basu tabbacin babu sauran ciwon". A zabure ya gyara Zama Yana wani kankance idanu. "Kikace menene ? Mijinta kome?"
Gyada Kai tayi tana bashi assurance na abinda ta fada. "Mijinta fa kikace? Haka ta fada Miki?". "Eh haka ta fada min dazu kafin mu fita kasuwa, harma tace min Bata tare ba sai ta komai gida, gaskiya mijin yarinyar Nan yayi Dace da mace ta gari Naga alama tana jida mijin nata...." Bai jira yaji abinda zata fada ba ya nufi dakin data ke. Yanzu ma ta b'ame dakin Yana zuwa yaji shi a rufe, baiyi knocking ba dawowa yayi ya zauna Yana huci, Nan da Nan Yana yinsa ya canza har abun yaso yaba Aishat tsoro.
Ita ta rasa wane irin lamari ne haka idan ma da wani Abu a tsakaninsu to a Cikin gidan Nan ya faru Dan jiya harta kwanta lafiya kalau suka rabu da ita, Amma wayewar garin yau aka tashi da wannan sabon canjin daga gareta.
Har tausayi ya Bata da gani Yana Cikin damuwa.. "Dan Allah Dan sonka da Manzon Allah ka fada min meke tsakaninku da wannan yarinyar dazu naji kana fadar maganganun da suke nuna kamar Kaine ke Jan ragamar rayuwarta wacece ita? Wace irin alaka ce a tsakaninku? Yarinyar Kace? Ko matarka ce? Ka fada min Kona samu nutsuwar zuciyarta,wallahi duk duniya babu Mai Jin wannan maganar".
Bai dago ba harta Gama fadar abinda ke bakinta, yasan Dole ya fuskanci tuhuma daga Aisha dan ya kasa controlling Kansa tun lokacin Daya fuskanci tana fushin da baisan Kona menene ba da Kuma ma'assasar yinsa ba. Motsin bude kofa yasa mahmud dagowa yaga waye, yasan dole ya kasance ahalin gidan ne. Abbas ne ya shigo rataye da jakar laptop dinsa, kallon kallo aka shiga yi tsakanin su Mahmud yasan ko rantsuwa yayi babu kaffara Aishat ce ta gargado shi tunda jiya tace masa aikin wata biyu zeyi a Jamaica kafin ya dawo duka jiya kuma satinsa uku a can, inda yake ya tsaya Yana warewa Aishat hannu idan da sabo mahmud ya Saba ganin wannan sabgar tasu. Hannunta ya riko suka shigo ciki Yana kallon mahmud Wanda ya yi fuska. "A'a sweetie wa nake gani kamar 'yan gudun hijira?" "To gashi Nan dau". "Ammah bansan lokacin da kika Zama Mai fuska biyu ba, shine kika zagaye Mika gayyato min mijinki ko?" Hannun Aishat Abbas ya saki Yana nifar gurin mahmud, dariyar farin ciki Yana Dan doka kafadarsa. "My man kace mun ciri tuta tunda mune masaukin bakin, dan duniya wallahi Mahmud baka da dama,kayi masifar bamu kafa Wai ashe kana Bauchi state, Bari na watsa Ruwa na fito nayi welcoming dinka sosai". Harara mahmud ya Kara zubawa Aishat ita Kuma ta wani dauke Kai ai dai ta samu mataimaki tunda ita ya rainata Yana it's shata Mata layin da bazata iya tsallakewa ba gara maza su shiga. Suf ta wuce tana fad'in Bari Fara maka preparing na kayan wanka". Saida ta wuce Mahmud yace. "Ya Abbas yaushe matarka ta koyi 'yar kasa ta iya fuska biyu, nace Mata fa kada naji kada nagi shine ita Mai mijin ta tattago ka babu shiri kuzo koyi mini taron dangi, dama kayi zamanka daga Nan Sokoto nayi ayita ta Kare". Ya fada Yana huci, Abbas na ganin haka yasan da abunda ya tunzura shi. "Koma dai menene Abbie yace mu kaika sokoto dead or alive". Ya wuce shi yayi strais da sauri.
Har Abbas suka sauko Yana inda suka barshi,.bayan Abbas yaci abinci ya dawo kusa da mahmud ya zauna. "Wai me yake damunka ne ko baka da lafiya mu wuce asibiti? Ko Kuma malantar ce tasa ka zama haka? Kasan ku alarammomin nan da izza kuke". Ya fada Yana dariya, shima mahmud din dariyar yayi. "Kai Amma Aishat kin kware gurin kinibibi yanzu har kin fada masa wannan maganar gaskiya min Dena sirri dake tinda yanzu babu Aminci a tsakaninmu kina da naki ma'amincin". Itama dariyar tayi tana nufar corridor din dakin Zahra, tana tunanin wayon yarinyar da gani akwai abinda suke boyewa su duka Dan da alama horo ne take Masa a Cikin ruwan sanyi Dan ko rantsuwa tayi bazatayi kaffara ba da wata a kasa. Cikin ikon Allah tana kokarin knocking taga Zahra ta bude kofar tana sabe da Yar gidanta Wanda ta tashi daga barci. "Sannu Aunty, gata ta tashi tun dazu batayi dai kuka ba na Bata fresh milk dai sai Naga gara Tasha natural nata dai". Ta fada tana Mika Mata Afnan din, abun mamaki sai yarinyar taki zuwa gurin uwar. "Huta roro Nima na huta da tsotsa, amma kuzo muje ki gaisa da sweet heart ya dawo shine ma yake tambayar Afnan din tunda yau Abulkhairi baya Nan yaje week end gidan Dr Suraj abokin Daddynsa". "Allah sarki shi yasa banganshi ba Ashe baya gidan". Bata bukatar komai Dan ta yafa wani veil Amma karamine ta saka abaya Dubai maroon Mai adon stones kanana saita haskata sosai yarintarta ta Kara fitowa da wani sirrin kyau Dan asali ga kanshin turarenta da Kuma irin Wanda Hajiya Amina ta hada Mata masu janyo Hankalin oga duk irin kamewarsa kuwa. Tare suka Jero suna magana wadda tasa Zahra yin wani tsadedden murmushi sai akayi dace duk su biyun suna facing din hanyar. "Tabarakallahu ahasanil kaliqin". Abbas ya fada. Shi Kuma Dan gogan ya kasa dauke idanunsa daga kanta sai yaga murmushin kamar da gayya take yinsa. Cikin takunsu na matan da suka San takan gayu suka karaso parlourn, sallama Zahra tayi. Abbas ne ya samu zarafin amsawa shi kuwa mahmud tamkar an rufe Masa Baki, ai shi Abbas Bai zaci haka zahrar take ba yanda sweetie ke bashi labarin ta Sai yaga ai Sam Bata iya fasalta mutum ba. Afnan na ganin Daddy ta shiga irin rawar murnar kaga abinda kake so din nan da Yara sukeyi tana zillo gurinsa zahrar ta nufa da nufin ta kaita. Ita da duk saura ba Wanda yaga lokacin da mahmud ya diro gabanta Dan ja da baya tayi da sauri tana fad'in. "Subhanallahi! Lafiya meye faru?". Baiyi wata wata ba ya rungumosu ita da Afnan din dake hannunta. Kici kicin kwacewa take Dan Bata taba tunanin zeyi irin wannan danyan aikin ba. "Na shiga uku! Aunty ku taimaka min Dan Allah ku janye shi inaga bashi da lafiya kada yayi Mana illah Ni da yarinyar nan". Ta fada tana kuka. "Wallahi bazaki sakamin ciwon zuciya ba kin hanani sakat tun safe kin Hana ko fuskarki na gani,kinki yarda muje asibiti, me nayi Miki Mai zafi haka har kike ikirarin Wai mijinki ya Hana kije Asibiti, waye mijin naki bayan ni? Fada mini!!!..????" Ya fada Yana hargagi abinda Bata taba gani ba kenan a iya zamanta dashi,kuka Afnan ta kwallah saboda yanda ya matsesu ga Kuma hayaniya da yake musu. Da sauri Abbas ya taso yaga mahmud din kamar baya cikin nutsuwarsa. Hannunsa Daya ya kamo sai yaji jikin nasa na tsuma. Daidai kunnensa Abbas yayi magana. "Pls sakarta kaga ka saka yarinya kuka, ka nutsu ta fada maka me yasa tayi hakan kowa ai yasan taka ce Ina ga da abinda kayi Mata Mai ciwo". Da kyar ya yarda ya saketa ita da yarinyar. Zaunar dashi Abbas yayi ai Zahra na Dora yarinyar a cinyar uwarta lokacin Abbas na can Yana bashi Baki ta fice. Tana shiga tayi locking din door tana sauke numfashi tare da goge 'yan hawayenta na karya data kakarosu. "Wallahi saina rama zakayi bayani da bakinka guy ni zaka yiwa cin fuskar da ze Zubar min da daraja da kimata sai zuciyarta da Bakinka sun Fadi gaskiyar da kake boyewa, Kuma Wallahil Azim addu'ar tsamiya yanzu na Fara har FAHAZAMUHUM BI'IZIMILLAHI YA WADUDU YA JAMI'U MALIKIN NASI MALIKI YAUMIDDIN zanta zabga maka sai ka Raina kanka kasan Dan an baka kyautar zahra ba Yana nufi Zan Zama matar shige ba, sai duniya ta shaida zahrar Zahra ce, tayi kwafa ko yanzu na rage tension ko ya yake tunda kaima kaji a jikina ka Kuma karyata maganar daka fadawa 'yar uwarka jiya, Wai bakaga wadda tayi maka ba, sai kasan bayanin da zakayi musu Kuma tunda magana zarar bunu ce bata komawa.
Lokacin da Abbas ya juyo da zummar yiwa Zahra magana yaga sai filin gurin kallon Ina take ya yiwa Aishat.. "Ta gudu Ina zata tsaya ya nakasa ta yayiwa mijinta asara,kuma saboda Allah sai ka kakume Matar mutane da yammacin gari yaushe ka Zama haka yarinya da aurenta da komai wannan kasan haramun ne basai an fada maka ba, Ina cewa gida Daya kuka zauna ba diyar malaminka bace me yasa kasan kana sonta kayi shiru har wani ya aura ni Naga kokarinsa Daya amince ka taho Masa da irin wannan diamond baby din wata uwa duniya baya tsoron sharri shaidan ya gitta tunda gashi a gaban mutane ka iya rungumeta yaya idan daga Kai sai ita ne ai labarin ba irin wannan bane ki.." "Stop!!!..... Aisha, ni kike fadawa abunda yazo bakinki? to Zahra halaliyata ce matata ce ta sunna". Ya fada a zafafe tashi yayi ze fice da sauri Abbas ya riko shi. " Dawo magana zamuyi ta fashimta". Baiyi gardama ba ya dawo ya zauna, ita dai Aisha rasa ta cewa tayi wai barawo a hannun Mata. Very close dashi Abbas ya zauna ya riko hannun mahmud Yana fadin. "Munji matarka ce amma yanda sweetie ta fada min kace matar ubangidanka ce me yasa ka boye mata Bata cancanci haka ba, kasan irin wahalar Dana Sha da ita lokacin da case din Nan ya taso? yanda kasan zata zautu wallahi Amma sai ka dawo Mata da wata fuskar daba taka ba duk rintsi bakwa rufewa junanku komai, kasan ta fada min cewar wallahi matarka ce Dan ta shaida bazaka taba yarda kayi tafiya da mace irin wannan da mace kamar wannan babu alaka Mai karfi a tsakaninku". Mahmud ji yayi duk ruwa ya cinye shi yarinya karama ta dagula masa lissafin da tasa ya saki layi duk yanda yake shirya nasa planning din ta rusa a lokaci daya yayi amansa ya lashe.
"To tayi hakuri ni kaina bansan me yasa na kasa fada Mata ba Ina Jin nauyin yanda Zan tunkari Ammi da Abbie da wannan maganar ba wallahi, sai Naga nayi wani Abu Daya sabawa al'adar mu ta Malam bahaushe, Kuma ita na rasa abinda nayi mata lafiya kalau mukazo gidan Nan Amma ta sauya min na rasa abinda yake min dadi wallahi Ya Abbas yarinyar nan itace weakness dina a rayuwa ni kaina nasan hakan, itace fa wadda nake fada maka na gani da dadewa a jirgi ita da Abbanta ka tuna?". "Off cause anyi haka,Amma how comes hakan ta faru?". Furzar da iska yayi daga bakinsa. "It's long story, idan ka huta zamu tattauna akai, yanzu dai ki tashi like kiyi min Biko tunda Naga alamar kina da masaniyar laifina". Baki Aishat ta dafe da hannu Wallahil Azim ban sani ba, nifa duk abin Nan hasashe nake yi ban tabbatar ba sai yanzu, ni wannan aikin ba nawa bane Kai zaka gyaro kayanka da abinda kayi Mata tunda Naga Bata da kwaramniya Sam, Kuma ya zakayi da ita kenan? Zakaje kace ga matata nan tsaraba fushin da nayi ko Yaya za'a kayi?". "Ki Bari kawai alkawarin da nakeso kuyi min mu rufe maganar nan a nan duk da Faruq ma ya sani amma nasan tunda na kada Masa warning bazeyi karambanin fadawa kowa ba, nina taro match dina Ni zanyi playing din kayana kawai kuyi min addu'ar samun nasara kada Ammah tayi min nak'i". Ya fada Cikin raunin murya.
,
.*AUREN HUCE HAUSHI*
MAMAN FATEEMAH
09062432330
Or
O8055362975.
Page 72