Auren huce haushi complete - Chapter 50
Auren huce haushi complete Chapter 50: Auren huce haushi complete Chapter 50. ........... Cikin kankanin lokaci mahmud yaji ya Dan samu nutsuwar Daya rasa,…
4,446 words
........... Cikin kankanin lokaci mahmud yaji ya Dan samu nutsuwar Daya rasa, yarinya karama ta saka shi sakin layi a gaban mutane, ita dai Aishat sai jijjiga Afnan takeyi wadda har lokacin take 'yar mita, tashi Mahmud yayi da nufin barin gurin, Ya Abbas ne ya riko Masa hannu Yana girgiza masa Kai. "Dawo magana zamuyi ta fashimta, baiyi gaddama ba. "Kana ji yanzu ka Bata sarari ta huta ta Kuma Huce daga fushin da tayi da kai, idan so Samu ne ka koma gidanka ka kame kanka, kada ka Bari ta Kara ganinka Nan kusa har sai an Kai wani limit da zata nemeka ruwa a jallo ta rasa yanda ko kun hadu babu saura fishi sai dokin ganinka dole ba Zama very strong a fannin soyayya Kaine namiji kada ka yarda ta gane itace rauninka, sannan dole ka koyi takatsantsan kasan inda na dosa idan ba haka ba za"ayi amfani da wannan damar a cutar maka da ita Koda ta furucin Baki ne". Shiru mahmud yayi Yana saurarensa wato shi kansa zaman takewar auren sai an shirya mata, Dan rausayar da Kai yayai yana fad'in. "Anyway shike nan,Amma da so nake ta yarda muje asibiti su dubata tukunna sai na wuce din". Wani kallon me yake damunka Ya Abbas yayi Masa. "For God sake! Ashe bazaka Zama Mai karfin ba kenan? Tunda nace ka kame kanka ai sai kayi yanda nace ko, tashi mu fita ja rakani na dubo patient din namu ma ida discussion din a hanya tunda Naga alama ka rifta da yawa". Ya fada Yana Masa dariya, sumar kansa ya shafa shima Yana murmushi. Bayan fitarsu Aishar Goya Afnan tayi so take tayi barci, Bata Kara bi takan Zahra ba ta shige kitchen ta Dora ruwa ta dauko kaza ta Fara gyarawa ta Dora a wuta ta debo fresh fruits ta wanke ta Fara hada fruits salad ta saka a fridge tayi lemon kankana da Madara pepper chicken tayi da chicken rice sai coslow data hada ta dafa ruwan tea Mai hadin spices masu Dadi na dafa tea kafin magariba ta Gama komai, Babban tray ta hadawa zahra kayan bude Baki ta aje a gefe sannan ta ringa fita da nasu zuwa dinning tana jerawa Saida ta Gama komai ta dauki na zahra lokacin har duhun magariba yayi, knocking Daya tayi Zahra ta bude Mata ta matsa gefe tana fad'in. "Sannu Aunty da aiki Aunty". Ta fada tana karbar kayan Amma taki yarda su hada Ido. "Zanje nayi sallah idan na Gama zamu zauna dake Ina so mu tattauna wasu abubuwa". Aishat ta fada tana juyawa. "To Aunty zanzo basai kin dawo ba". Dan dakatawa tayi da tafiya ta waiwayo. "Kiyi zamanki ai Amare 'yan lalashi ne, ni zanzo on behalf of my beloved brother". Ta fada tana dariya, itama zahra murmusawa tayi.
******Daga gida direct Asibiti su Mahmud suka nufa, sun samu Habib da Abubakar, Ya Abbas yayi mamakin ganin Abubakar a gurin sosai Amma baice komai ba kenan da wadanda mahmud yayi hijirar dasu. Lokacin Baba malam Yana zaune suna Hira, har gabansa su mahmud suka karasa suka gaishe shi da Kara suba shi, sannan su Habib suka gaishe dasu mahmud, Ya Abbas ne ya kalli Abubakar Yana fadar. "Wato har Kai gurin kufe Mana gaskiya ko? Kana ji ana ta Fadi tashin nemansa kayi fumfurus kana kallon kowa daga karshe ma akace ka canza gurin aikine". Sadda Kai yayi yana Dan sosa gefen wuyansa, gyaran murya Baba malam yayi Dan duk da bayanin matsayin Ya Abbas da mahmud yake basa baisa ya dauke hankalinsa daga maganar da Abbas din fada ba. Jin gyaran muryar Malam yasa suka juyo gaba Daya suna kallonsa. "Ayi Masa Afuwa shima Mai bin umarni ne,sai yanda akayi dashi kada aga laifinsa amanar kenan da baya da Amana baze yarda dashi irin haka ba. Allah yayi albarka ya kiyaye gaba, ai karfin addu'a ne yasa komai ya Zama tarihi naji dadin ganinka sosai Malam Abbas Dan Allah kayi min aikin Dana kasa ka maida min Dana gida tare da iyalinsa ka bawa mahaifinku hakurin karambanin da mukayi musu wallahi nagarta muka duba ba komai ba tunda Bamu San gaibu ba, in Sha Allah idan lafiya ta Samu Ina Nan zuwa sokoton da kaina". Waje su Habib suka fice, ya Zama daga Malam din sai su Ya Abbas. "Babu komai Malam Allah ya baka lafiya, muke da godiya ya fada min duk dawainiya da kayi dashi tunda kuka tsince shi har kawo yanzu ai kaima ubane ka Isa kayi yanda kaga dama dashi, Allah ya Kara lafiya da sutura yasa kaffara akeyi in Sha Allah amanarka Zan idata, ai mu bamu da Bakin godiya sai dai ubangiji ne ze biyaka". Sun Jima suna tattaunawa anan Malam yake farawa Abbas yanda kayiwa mahmud makaru abinda Bai taba fada Masa ba sai yanzu yakeji, har wasu hawayen gefen Ido Mahmud yaji sun taro Ashe haka akaso a kassara Masa rayuwa Allah yayi Masa gada da Rahama ya kawo Habib ya gashi a gurin da yake a yashe a kasa. Anan sukayi magariba sukayi insha'i sannan sukayiwa Baba malam sallama, mahmud ne yace suje su duba jikin Alhajin su Aunty surayyar uncle Mustaphan Shima Yana nan. Shima sun samu 'ya'yansa maza biyu sunzo duba jikin nasa, sun gaisa tare da jajanta musu, shima Alhajin jikin da sauki sosai Dan har Yana takawa shima da karfe. Gida suka koma mahmud yayi dinner tare dasu, haka Nan yayi ta maza bai nemi zahra ba Suma babu Wanda yayi maganar ta har suka gama, Mahmud Bai wani zauna ya shiga dakin da ya mayar nasa tun ba yanzu ba ya dauko laptop din da wayoyinsa ya fito. "Ka Bari na saukeka Nima Ina son fita ne". Ya Abbas ya fada. "No, ka barshi kawai nayi waya da Mr salahuddeen Yana kusa da isowa, kawai dai Alfarma za'ayi min twins zasu shiga Nigeria a tsakanin kwanakin nan harna Fara musu processing na visa harda yaran duka". "Ba damuwa Nima Ina son suje Nigeria din to saboda makarantar Abulkhairi ne, Amma yanzu dole suje tunda ta Kama amma naji kana fadar kana nemar musu visa Kai kana Nan kenan?". Kai ya girgiza Yana fadar "A'a akwai dalilin raba tafiyar ne jikina Yana bani wani Abu da bansan ko menene ba". "To Allah ya rufa asiri, Zan fadawa sweetie ka wuce tana can gurin 'yar daru ita da dare take tata rigimar amma da Rana lafiya kalau za'a wuni da ita". Dan murmushi Mahmud yayi Yana ayyana Wai babyn su ce da zahra suna tarairayarta. Yana fitowa harabar gidan motar sayyid tana shigowa, dai dai gurin Mahmud ya tsaya ya kashe motar ya fito da sauri ya rungime Mahmud Yana fad'in .
"Ina ka shiga a duniyar nan ka barmu da tashin hankali? Munyi nema har mun godewa Allah kasan Umma cewa tayi a saka nemanka a jaridu da mujallu da kafafen sada zumunta na zamani,Su uncle Mustaphan ne suka Hana sukace abun ze zama tonon sillil Wanda Bai sani bama ze sani". Dan zare shi daga jikinsa mahmud din yayi Yana fad'in . "Ai gashi Nan dawo sayyid ya karatu ace ka koma PhD ko?" "Wallahi kuwa". "To Masha Allah. Allah ya taimaka, Nima Zan wuce ne matar abokina na kawowa Aishat su zauna a Nan asibiti sukazo zataga likita". Ya mika Masa hannu yayi gaba, sayyid Yana da kirki amma fa gurin lamarin Mata sai a hankali, ko baya Zina ta zahiri akwai 'yan tabe -tabe. Yana fita ya turawa Aishat text message a waya. Amma fa karfin Hali kawai yakeyi Sam zuciyarsa Bata nutsu ya tafi yabar zahra da wannan Karen farautar a gidan ba, amma dole ya kauda Kansa yayi kawaici da Kara kada Ya Abbas yaga Bai dauki maganarsa ba. Koda ya koma su Habib suna gida Suma sun baro asibitin, coffee ya bukac Mr Ajey ya kawo Masa ta wuce ciki Saida yayi wanka ya bude laptop dinsa Yana aiki Yana sipping din coffeen, ya Kai kusan biyun dare Yana Abu Daya Saida ya tabbatar da komai ya dai daita sannan ya kwanta zuciyarsa da gangar jikinsa suna mararinta, filo ya rungime a haka barci yayi awon gaba dashi. Bayan sun sallar Asuba barci mahmud ya koma knocking din da ake a kofar bedroom dinsa ya tashe shi daga barcin da yake Mai Dadi Wanda ya saka shi nishadi. Umarnin budewa ya bada Yana daga Cikin blanket dinsa. Mr sunny ne Mai yin share share da goge goge.
" Good morning Sir" Ya fada Cikin ladabi daga Bakin kofa sannan ya Dora da fadin. "Akwai Baki daga Nigeria". Wani smile yayi Yana tashi zaune yasan za'a Rina sai yanzu ya gane hikimar ya Abbas na cewa ya dawo nan shi kansa baze so zahra taga dabin da za'ayi ba". "Kaje ayi musu duk abinda ya kamata, Mr Ajey ya Basu abinci kafin na fito". Toilet ya shige yayi suk abinda zeyi sannan ya fito Yana tsane sumar kansa da Karamin towel a nutse ya Gama shirinsa ya fito a Mahmud dinsa, ya riko wayoyinsa hannu ya nufo main parlour. Da uncle Mustaphan ya Fara yin tozali kafin ya sauke idanunsa a Kan uncle saminu, nan da nan ya hade girar sama data kasa tamkar yaki ya rigshi kofar gari. A ciki ya gaishe su duk da shafi ce ta shafi uncle Mustapha sai yayi musu kudin goro, neman guri yayi ya zauna Bai Kara cewa komai ba, uncle saminu ne yazo iya wuya Dan ba haka yayi zaton zega Mahmud ba l,Dan an Bashi assurance na ya Gama lalacewa,dan a yanda a kayi Masa aikin rigar sawa ma sai tafi karfinsa, bare wani arzikinsa sai dai komai ya lalace masa, sai ya Zama abinda zeci ma saiya fi karfinsa, sai Kuma yaga sabanin haka Dan yanda yake da kyawun gani a yanzu ko kafin faruwar matsalar da suka Zama asasin fatuwarta Bai Kai haka kyaun gani ba. A zuciye ya taso yana fad'in. "Kai din banza har yaushe kayi arzikin da zamu tako har inda kake ka wulakantamu eyeh? Ka maida mu 'yan iska Wanda Basu San ciwon Kansu ba ko a Nan ma halin akuyancin kake tabawa shi yasa ka makale kana gyallin goshi?' Uncle Mustapha ne ya taso da sauri yana fadin. "Meye haka kakeyi saminu? Daman abinda ka shirya kayi kenan? Amma kaji kunya wallahi Dan zumunka? ko abinda kuka kitsa kaida munafukarka kuka lankaya Masa sharrin da gaske Yana yinsa ai ka rufa Masa asiri ba kazo kana wannan shirmen ba Wanda Allah ya daga ya daga shi sai dai mahassada suyi kuka, dai dai gwargwado meka nema ka rasa da yawa ta taka suke nema Basu samu ba wace irin sutura ce Ubangiji baiyi Mana ba Amma ka tsaya kana yiwa dan Dan uwanka hassada saboda Allah ya daukaka shi a cikin family din kace ya auri 'yarka yace baya so to nuna kin jini na me Kuma wani ya taba auren matar daba tasa ba ka ragewa kanka wannan walahar Dan babu inda zata kaika sai fagen Dana sani, Ashe 'yar burumburum kayi min ka nuna komai ya wuce muzo mu tafi dashi gida". Sadda Kai saminu yayi baiyi zatom Mustapha zeyi masa haka ba Dan Saida ya shirya ya taho da zummar duk abinda yayi babu Mai iya tanka Masa. Maganar Mahmud uncle Mustapha ya tsinkayo daga bayansa. "Ka daina Bata Bakinka uncle Wanda yayi nisa baya Jin kira,ni Mahmud ta zamar Masa kadan garen bakin tulu ya barni na Bata ruwa a karni a Kar tulu, babu abinda ya Isa yayi min tinda bashi ne ya halicceni ba Kare ya canza min kaddarata kuma har abada Bazan taba auren wannan karyar 'yar tasa ba, yaje yayi bincken wacece ita kafin ya samu bakin fadawa mutane maganar suna Zina aje asibitin tugar barau ka nemi solomon kaji sau nawa ya zubarwa da 'yar taka ciki? Ko an fada maka bamu San haka ba Dan anyi shiru an kyaleta ba' a fasa maganar a family ba idan kace karya ne yanzu na nuna maka hujjata Mai karfi, kaci gaba da abinda kake kada ka fasa Dan Allah mu Zuba sharri dai Dan aike ne kada ka rufe kofa ze dawo Komai Daren dadewa, uncle Mustapha kayi hakuri wallahil azim Bazan bika ba yanda na fito ni kadai haka Zan koma indai da wannan mutumin zamu tafi Saida na mutu ban koma ba, bani da wani Hadi dashi Wanda ze shige min gaba a dukkan lamurana. Uncle Mustapha baiyi yunkurin Hana shi ba saboda yasan irin bakin Cikin da yaron ya kunsa a wancan lokacin. Juyawa mahmud yayi ze fice daga parlourn, uncle Mustapha ya riko hannunsa. "Ina zaka tafi?". Idunu jajur ya kalli uncle din, yana girgiza masa Kai, wallahi bazan zauna dashi ba idan ka matsa min za'ayi Dana sani, yanzu babu abinda ze hanani nayi abinda banyi a wancan lokacin ba, uncle kana da daraja da qima a idanuna to ka fada masa ya fita faga sabgata idan Yana so ya tsira da Dan sauran mutumcin Daya yage Mana to ya kiyaye shiga duk abinda ya shafeni, mu hadu a Sokoto two thirty flight dina ze tashi duk abin bukata a kwai shi a nan, idan ka shiga asibiti Faisal ze rakaka gurin malamina ka duba shi anyi Masa aikin spinal cord ne".. Ya kada ya fice abinsa. "Yanzu irin wannan Ina ranar ta ka zubarwa da kanka qima da girma saboda sakawa Rai hassada a banza, shima ya juya ya fice daga gurin zuciyarsa babu Dadi Dan ko kadan baiga laifin yaron ba an Bata Masa fiye da kima. ya bar uncle saminu ya kasa ko kwakwjwaran motsi.
* AUREN HUCE HAUSHI*
AISHAT ISAH MUSAH. (Maman Fateemah)
Bismillahir Rahamanir Rahim.
P. 73
........... Tunda Zahra ta farka daga barci taji Sam Bata Jin Dadi jikinta ita ba Mai zazzabi ba duk jijinta ciwo yake Mata, ta Kuma kasa fita Dan Bata son su hadu da Dan gidanta kada ya Kara Bata kunya Dan taga alama tasa tayi kaura daga idanunsa sai ya iya yi Mata abinda yafi hugging ma ga Kuma uwa uba tana Jin bala'in nauyi Ya Abbas tunda ko banza yayan mijinta ne ya wani kwakumeta ko kunya babu, agogon waya ta duba karfe Tara saura kwata na agogon kasar, tattaunawrsu da Aunty Aisha ta ringa dawo Mata tiryan-tiryan. Tasha mamakin halin da aka saka mahmud Ciki yaga masifa da tashin hankali ace kowa yayi maka naqi, kuma dadin dadawa kowa ya kasa fashimtarsa, ta yarda kamar yanda Aunty Aishat din ta fada abun an Dade ana shirya shi Saida aka Sha Kan kowa sannan aka fasa maganar, kuma tayi wani irin tasiri Banda taimakon Allah da wani labarin akeyi ba wannan ba. Yunkurawa tayi ta tashi sai taji tana bukatar kasancewa kusa dashi ta lallashe shi, abin tausayi be kuma abunda ya fada gaskiya ne, sai yanzu ta gane gundarin me maganarsa take nufi duk da na gari dole yabi iyayensa, kawai shedan ne ya tunzura ta ta hau dokin zuciya Mai mmakon ta Zuba Ido taga yanda abun ze kasance sai ta kasa ta hau fushin fari, ai dole ma hakan ce zata kasance tunda Yana da magabatansa, idan sun amince da auren da akayi Masa laba'asa idan Basu amince ba shikenan. Tana zuwa wannan gab'ar taji wata irin faduwar gaba, kada fa iyayensa Suki yarda da ita a matsayin mararsa. "No!!!. In Sha Allah mutu ka raba takalmin kaza.". Ta sauko daga gadon gara ta fita ko tayi arba dashi tayi yanda tayi ta Shawo Kan kayanta. Wanka ta shiga shaf-shaf ta fito ta shirya ta saka rigar cotton lace marar nauyi tana baza kamshinta, bata daura dankwalin lace din ba karamin gyale ta Dan rufe gashinta dashi ta sako plat shoes ta fito zata shiga kitchen tayi musu abin break fast kada ta Zama cima zaune sai dai ayi a Bata. Parlourn ba kowa shiru sai karar a/c kakeji kawai sai Kuma sansanyan kamshin turarukan daki tunda gidansu akazo, kitchen ta nufa Kai tsaye saboda tana da yakinin masu gidan Basu tashi ba, da sauri tayo baya ganin mutum tsaye Cikin kitchen din daga shi sai boxer short da singlet, shima Jin motsi daga bayansa ga wani scent Mai shegen Dadi ya bakunci hancinsa yasa shi juyowa babu shiri. "Ya subhanallahi!". Ya fada lokacin daya Dora idanunsa Kan fuskar Zahra, da wani mahaukacin sauri ta juya fit ta fice daga Cikin kitchen din, shima sayyid da sauri ya aje cup din Daya dauko ze Zuba coffee din daya dafa. Ko duriyarta sayyid Bai gani ba sai dai kamshin da tabar Masa. Zahra na shiga daki ta Danna Masa key tana maida numfashi. "Waye wannan Kuma da yake da irin wannan freedom din a cikin gidan matar aure irin haka? Gaskiya wannan rayuwar da sake, dole meu amor yazo su bar shi ai da matsala sosai gidan musulmi Kuma matar gidan Matashiyar mace Mai jini a jika, shaidan ake gudu gaskiya. Wayarta ta dauka tana neman Aunty Hassana su gaisa.
______
Mahmud yana fita kofar baya ya koma ya shiga bedroom dinsa ya dauko abokiyar tafiyarsa jakar laptop ya shiga mota sai tashin motar uncle Mustapha yaji Dan ya fita har waje baiga mahmud din ba Bai Kuma kawo Yana Cikin gidan ba. Da sallama ya shiga dakina da aka kwantar da Baba Malam din Yana zaune shi kadai Yana lazimi ga kayan break fast Nan an kawo Masa Bai Kai ga cinsa ba. Sallamar Baba malam ya amsa Yana fadin. "Sannu da zuwa mahmudu, Amma yau kayi sakko, ya Naga ran naka babu Dadi lafiya dai ko?"
Dan murmushi yayi duk da iyakarsa fuska. "Babu komai kawai dai bana Jin dadin jikina ne". Ya fada Yana karasawa kusa dashi ya gaishe shi ya Kara duba Jikin nasa, abinci ya dauko ya hada Masa yaci sosai sannan ya fada masa Yana son yaje Nigeria a yau in Sha Allah, addu'a yayi Masa sosai tare da Kara bashi Baki yayi hakuri ta koma ga iyayensa, sadda Kai kasa yayi kafin yace. "A karayi Mana addu'a can na nufa idan Allah ya amince Mana". "Kai! Masha Allah kazo min da abinda ya faranta min Raina mahmudu ubangiji yayi maka albarka ya Kara Kare ka daga dukkan sharri abin halitta Dan isar Manzon Allah s a w.w, kaje babu abinda ze faru da yardar ubangiji,Ina Kuma Fadimar ko ba tare zaku tafi ba?". "Eh su sai jibi zasu taho da Hasanata wadda Dan uwana da mukazo dashi ya dawo ya kawota ta duba ka". "Ikon Allah ai Bai min bayani ba yace dai ga iyalinsa tazo ta gaisheni, yanzu mahmudu daman takwayene Kai? Koda Wai ban taba sani ba, ko danma Kai ai saidai hamdala Amma me kake fada". Murmushi yayi Yana Dan shafa sumar Kansa wadda Tasha gyara. "Ayi hakuri yanayin ne yazo a haka". "Babu komai hakan shine dai dai Allah yayi yagora ya Kara arziki Mai dorewa". "Allahumma Amin". Nurses ne Wanda suke bada maganj suka shigo, suka gaisa da malam Cikin harshen turanci sannan suka gaisa da mahmud da yarensu, magunguna suka bashi ya Sha sannan suka fice,Hira sukaci gaba dayi inda Baba malam ya dinga bawa mahmud Addu'oi masu karfi na tsarin jiki sanan ya Kara bashi wata yace ya dunga karantawa duk bayan sallar farilla in Sha Allah badai sihirin Dan mutum ba. BISMILLAHI WA BILLAHI BISMILLAHI MASHA ALLAHU BISMILLAHI WALA HAULA WALAQUWWATA ILLABILLAH ÷ QALA MUSA MAJI'ITUM BIHISSIHIR INNALLAHA SAYUBDULUHU INNALLAHA LAYUSLUHU AMALAL MUBSIDIN FAWAQA'QAL HAQQU WA BADALA MA KANU YA'AMALUN FAGULIBU HUNALIKA WQNQALQBU AAGIRIN. Godiya sosai mahmud ya yiwa Malam yace masa ze tafi Amma baze wuce sati daya ba ko biyu ze dawo tunda ya fadawa doctor kada a sallamar masa patient sai tafiyarsa ta nuna kukunna. Yana fita ya Kira Mr salahuddeen yace su hadu a Airport ze dauko mota. Karfe biyu da mintuna flights din su Mahmud ya dago Nigeria text kawai ya turawa Ya Abbas, itama Aishar ya tura Mata nata da bayanin komai.
Sayyid ya Jima a tsaye a parlour ko zaga ta inda Zahra zata bullo Amma yaga Shiru dole ya koma ya dauko coffee dinsa ya wuce dakinsa. Bai Jima da barin parlourn ba Aunty Aishar ta sakko Cikin gayunta kitchen ta shiga ta Fara aiki tana tunanin irin yanda Hussein ya gindaya Mata dokoki akan matarsa tana ganin soyayya Amma sai take ganin Dan uwan nata yayi zurfi da yawa. Tana Cikin aiki Sayyid ya shigo yayi Shirin fita school. "Aunty Ina kwanq?" Ya fada Yana shigowa ciki. "Lafiya kalau Sayyid har an fito yau da wuri haka? Gashi ko break ban Gama hadawa ba". "No Aunty I am ok, Nasha coffee tun dazu, Wai Ni Aunty bakuwa kikayi a gidan Nan ne ko Kuma gamo nayi da safiyar Allah wata"Ala?". Dariya tambayar ta bawa Aunty Aishar,duk yanda akayi yaga Zahra kenan, Amma sai tace masa. "Meta faru Kuma kake wata magana irin haka?" "Wallahi Aunty ba maganar jocking Naga yarinyar India ko larabawa a gidan Nan har fa Cikin kitchen din nan ta shigo muna had a Ido ta fice kamar walkiya ko dana fita ko Mai kama da ita bangani ba wallahi". "Eh bakuwa ce nayi Baku San juna bane shi yasa ita ma Bata San da zamanka a gidan bane shi yasa inaga itama tsorata tayi gaskiya". "Wow! Amma daga Ina Kika samo irin wannan Mai zafin haka? Gaskiya za'a da ita Dan Allah Ina kamu wallahi daga wannan Kuma kallo ya Kare ki Fara min campaign Dan Allah". Ya fada Yana hade hannu irin ba 'yan kabilar Hindi na nan Indian din🙏🙏. Anzo gurin tab Allah kiyaye da mijinta baya nan da a gabansa zeyi wannan kwabar da kuwa sun kwashi 'yan kallo. "Wai kana nufi sonta jakeyi kenan?" "Kwarai kuwa". Ya fada da tabbatarwa. "To ai matar Aure ce". Dafe Kai yayi Yana fadin. "Oh my God! Waye wannan Mai sa'ar da yayi min shigar sauri Dan Allah?". "Wanda ya fika sonta ne ya dauke abarsa". Langabar da Kai yayi Yana fadin. "Shikenan na wuce school, Amma fa I really loved her". "Matar Auren?"
Baice komai ba ya saka Kai ya fice daga kitchen din ransa babu Dadi. "Allah ya kyauta, wato mahmud ya yiwa Sayyid wani irin farin sani kenan, yasan matukar zeyi arba da ita sai an samu matsala gashi kuwa ya kasa ba marad'a kunya". Sai da ta Gama komai ta dauko abincin data Zuba musu ita da zahrar a wani guri ta aje basket din ta koma ta dauko wani Abu kaman story mat da table mat ya shinfida sannan ta koma sama lokacin sweet heart din ya fito daga wanka, taimaka Masa tayi ya shirya tunda shi azumin litinin da alhamis yakeyi itama Aishar lalurar mu ta Mata ta hanata dauka, fita zeyi Yana da wasu ayyuka da Mahmud ya turo Masa Wanda zeyi masa su, tare suka gangaro Aishar ke fadar . "Bari na kirawo Zahra ki gaisa tunda ba lallai yau ku hadu ba naji kace sai dare sosai zaka dawo aikin da yawa". Dan janyota yayi jikinsa. "Kyaleta ai Dan uwanki ya dasa Mana 'yar kunya a tsakaninmu tunda yayi mata irin wannan wawar rungumar a gabana kamar ze bude aiki kinji yanda jikinsa yake tsuma kuwa a lokacin?"
"Kai sweet heart Banda fa... Dan kaga baya kusa, shida abarsa har zakace Wai jikinsa Yana tsuma Kamar wani sabon shiga". "Ni dai abinda naji nake fada Miki bawai Qage nayi masa ba, Kika sani ko farin shigar ne koma Bai shigan ba". Ya fada yana dage Mata girar idonsa Daya. "Wallahi Kai dai Yaya Babba ne, Banda irin haka da gani kasan ai Yana shanawa dubi fa yanda ya damu daga Dan turza shi da tayi yanzu ma kaji yanda yake jaddada min na kular masa da ita kamar wata jaririya". "Ke dai mubar maganar lokaci ne ze nuna". Har gurin mota tayi masa Rakiya tana fada Masa zasu fita fa.
Sama ta koma ta dauko Afnan wadda ta koma barci tun da akayi Mata wanka Dan kada ta tashi suna can bazajiyo kukanta ba. Dakin Zahra ta Dan buga kadan tana fadin. "Pls open the door" . Jim muryar Aunty Aishar yasa Zahra tasowa da sauri ta bude kofar tana sakin murmushinta Mai kayatarwa. "Ina kwana Aunty?" Ta fada tana karbar Afnan dake barci, can tsakiyar gado Zahra ta kaita ta kwantar. " Ki fito muyi break fast tun dazu na kawo na koma na sallami sweet heart ne shi yasa". Tare suka jera zuwa gurin da tayi musu shinfida, abincin gargajiyar ba bahaushe tayi musu kunun tsamiya ne da kosai sai pepper soup din cow legs. Suna gamawa Zahra ta kwashe kayan ta mayar kitchen ta wanke su ta aje komai a muhallinsa, taso ta yiwa Aunty Aishar magamar guy dai data gani sai wata Zuciyar ta kwabeta, Bata sani ba ko kaninta ne shaqiqi muharraminta. A gurin ta dawo ta Sami Aunty Aishar tana amsa waya daga ganin yanda take amsawa kasan ba wayar sawa bace Mai wayar Yana da girma da kima a idanunta. Zahra Bata zauna ba ciki ta shige tana shiga taga Afnan tana daddaga kafa tana Wasa ta tashi, daukarta tayi tana fadin. "My Afee Babyyy.." Yarinyar na ganinta ta Fara dariya shaidar ta ganeta kenan.
Saida Aunty Aishar ta Gama wayar ta shigo tana fadin. "Au Kice mutuniyar ce ta tashi? Sai ki shirya fita zamuyi yanzu guri ya kure sosai kinsan Hussein shi komai nasa baya fada sai guri ya kure, sosai jibi fa zamu wuce Nigeria shine yace muje kasuwa kiyi tsaraba shi ya wuce Nigeria". Da madaukakin mamaki Zahra ta dago ta kalli Aunty. "Ya wuce Nigeria?" Sai idonta yayi kwal-kwal ta tabbata abinda ya fada gaskiya ne, shikenan ita Kuma haka tata kaddarar take. Girgiza Mata Kai Aunty Aishar tayi. "Haba Banda shagwaba Mana, keda kike fushi dashi, yasan ko yazo bazaki saurarasa ba shi yasa ya tafi tunda baisan laifin da yayi Miki ba kike dafa shi da naki salon, Dan Allah a rangwanta Masa shi bako ne a cikin soyayya Bai taba yinta ba ke Kuma Naga taki da zafi ta kamashi batayi Masa da Wasa ba". Da kyar ta iya mayar da hawayen, da suka so zubowa ta rasa dalili itama tata zuciyar Bata da wani karfi a Kan lamarinsa. "Shike nan Aunty inda sabo na Saba yayi tafiyarsa Bai fada min ba". Aunty Aishat ji tayi yarinyar ta Bata tausayi, kenan shima Yana gwada Mata halin miskilancin nasa, nata ne baya iya jurewa. "Ki rabu dashi tafiyar ce tazo masa ba zato kiyi hakuri dole zamu zauna ya daina Miki irin haka tunda ke ba sanin halin yawonsa kikayi ba, inaga duk duniya Amminsa kadai yake bude Baki ya fada Mata duk inda zaya a cikin duniyar nan kafin yayi fushi kenan".