Kenza eBookz

Auren huce haushi complete - Chapter 68

Auren huce haushi complete - Chapter 68

Auren huce haushi complete Chapter 68: Auren huce haushi complete Chapter 68. Wayar taji an zare daga kunnenta da sauri ta juya Dan kamshinsa ya fada Mata…

4,001 words

Wayar taji an zare daga kunnenta da sauri ta juya Dan kamshinsa ya fada Mata shine Amma koda Wasa bataji sanda ya shigo ba. Wayar ya duba yaga magaji ne kunnensa ya Kai wayar Yana fadin "ka Adana sauran bayaninka zuwa safe". Ai kafin ya Gama fada Magani ya kashe Kiran Yana rike bakin Al'ajabin Zahra Daman Yana Nan ya zage yana ta an tayo magana. Wayar ya aje yadan matsa baya Yana Kare Mata kallon ta burge shi matuk'a Dan ji yayi kamar ya sakata gaba yayi ta kallo, hannuwa ya bude Mata alamar ta shigo ya rungumeta, sun Jima a tsaye Saida yaji kamar kafafuwansa Bazasu iya daukarsa ba sannan ya Dan zameta suka zauna a gefen gadon, da kyar ya tashi ya shiga wanka Bai wani Dade ba ya fito ya saka Riga armless da wandonta three quater na Adidas dai tunda sune best kamfaninsa gurin sport wears, tana makake a jikinsa suka fito parlourn farko na sama In da aka aje musu dinner dinsu, sakwara ce da miyar Agushi sai black tea Mai Kayan hadin star anise a ciki, Saida sukaci abincin sannan suka dawo cikin parlour na biyu suka zauna duk ya kanainaye ta ya hanata sakat, nema yake ya ruda Mata lissafi ita Kuma Alla Alla take dare yayi ya karasa Mata labarinsa. Saida ya mila ya mile Dan kansa ya Dan ragewa kansa zafi sannan ya fara fadin "Bari muci gaba ko" Kai ta gyada Masa Dan ita kam ba baka sai kunne. "Wato precious Naga gararin rayuwa kowa fa juya min baya yayi babu Mai saurarena sai uncle Mustapha da Batool kawai, abin baqin cikin Wai a tsaya nayi bayani ma abun ya faskara ta ko Ina babu sauki a haka Muka kwana uku idan Kika ganni lokacin Zaki tausaya min a lokacin dukiya ta dai batayi min amfanin ba tunda Bata Hana an wulakqanta ba, a ranar na hudun na tsunci maganar Wai a ranar za'a daura mini Aure da Safna abunda ya yamutsa min lissafi kenan cikin tashin hankali na shiga wurin Ammi wallahi precious Ina shiga Ammi ta Mike tabar parlourn da sauri nabi bayanta Ina hadata da Allah akan ta tsaya taji gaskiyar abinda ya faru Amma kinsan me tace min? Wai fa cewa tayi inje inyi abinda nake so tunda karana yakai tsaiko gani ga rayuwar Nan tunda fasadi na zaba duniya tafi Dan bagaruwa jima, wallahi a lokacin ji nayi kamar na mutu na huta nakeji,ga wani irin Abu da nake jinsa a jikina, precious wallahi Addu'oin da nake na azkar lokacin da kyar nake yinsu,Dana fito mabera na nufa naje yau dai na fada mata halin Dana tsinci kaina a ciki tunda nasan Bata San wainar da ake toyawa ba, Amma kinsan abun mamakin da tashin hankali itama sammankal duk abun iri Daya ya Zama Bata saurareni ba karshe ma maganganu ta yarfa min masu zafi ga shi Daman wani Abu na min sukuwar sallah a cikin kaina, Nan da Nan naji wani bacin Raina ya qaru ban baro gidan ba Saida naci alwashin saina Bata mamaki kuma kozan mutu saina nemoki duk inda kike a duniya Kuma a dakinta a gadonta Zan Fara saninki 'ya mace, kadafa kice Wai bani da masaniyar inda kike hummmm a'a ana bibiyar min ke ciki da waje, kinga lokacin Dana fito daga parlourn Hajiya Inna ko takalmi kafata babu banbi takan motar Dana shigo ba na Fara tafiya a kasa wani Abu Daya bani mamaki a lokacin precious wallahi Ina ganin kamar mutane basa ganina tunda konaje kusa da mutane bana ganin alamar sun San da mutum a kusa dasu gani ba boyayyan mutum ba, haka na dosa wata irin tafiya tamkar kad'ani akeyi kuma tafiyar wata iri ce Mai cin dogon zango a cikin lokaci k'alilan a cikin abinda Bai wuce minti arba'in ba ni dai sai ganina nayi a talatar mafara na fuskanci mutane suna ganina a lokacin Tunda Ina wuce Ina Jin ana fadar bawan Allah ko daga Ina? haka na dinga tafiya wlh ko gajiya banayi Dana baro cikin gari naji kamar Ina Jin barci na kwanta a wurin wata bishiya, to Ni dai daga lokacin bansan kuma Yaya akayi ba ni dai nasan na farka na ganni a asibiti ta tare da Abubakar wlh nayi zaton ko sokoto na dawo sai Kuma Naga bakin fuska su Malam Abu mafi daure Kai ganin Abbanku da nayi sai Lamarin yafi karfin Dan karamin tunanina na wancen lokacin Dan nasan wannan abun wani connection ne daga Allah Daya hadani dasu yasan abinda nake rokonsa dare da Rana, precious nayi dawafi a dakin Allah na Kai mutane suyi min Addu'a akan wani Abu da nake nema duk a kanki Dan Ubangijina kadai yasan yanda ya jarabci wannan zuciyar da soyayarki tun Baki San meye soyayyar bs, Kinsan Kuma shi maji rokon bayinsa ne Kuma mafi tausayin masu tausayi mafi jinqan masu jinkai Naga Ijaba, bana inkari da lamarinsa Amma na Kara samun yakin Dan Rahamarsa ce ta lullubeni ya kawo Habib ya ganni a wancen lokacin, ga wata sabuwa Ina Jin maganar mutane Amma Ni Kuma bana iya magana, lokacin na shiga tashin hankali ba kadan ba Dan ji nayi na koma mutummutumi, asibiti sunyi iya abinda zasu iya suka sallameni Baba malam da Abban ki su suka dunga Fadi tashi akan lafiyata Dan abun babu dadin ji na shiga wata irin rayuwa lokacin na Kara gane mahimmancin lafiya da tasirin Addu'a, su Habib su sukayi jiyyata a dakin soro na gidan malam har Allah ya bani lafiya, lokacin ne Abubakar ya fada min ai aikin da yake komai na tafiya dai dai, dan dai lokacin kina syprus to Nima ganin nesa tazo kusa saina nemi gurin Zama naje Bauchi nayi duk abinda ya kamata akan layikan waya da dasu system da credit card na bank da duk abinda ya kamata banyi kasa a gwiwa ba na Kira Sameer da Bilyaminu muka zauna dasu a dakin Dana Kama a hotel, Abu na farko Dana Fara shine kad'a musu warning akan inda nake kada naji kada na gani duk da Sameer ya fada min hankali fa ya tashi na barina gida gashi uncle saminu ya assasa daura min Aure da Safna, banji komai ba nasan suda ganina ba Nan kusa ba ko zan waiwayesu ba lokacin ba, aiki na bawa Sameer na Nemo ma'aikatan wata ngo's suzo mu zauna Ina son muyi aiki dasu a zahiri Amma ba sune zasu ringa harkar kudi ba, kinsan k'asar mu indai Zaki bada budi to kome kike nema kin samu Nan da Nan suka shigo muka Fara aiki Ni Ina gefe Sameer ne oga, ba Saina Baki labari ba Kinga yanda makarantar Baba malam ta Zama, ke kuma a can syprus din bamu barki sakaka ba sai Dana tura Omer ya shiga jikinki a can ya Zama idanuna ya Kuma yi Miki tayin soyayya sai akayi Dace kince Masa a'a sai dai kuna mutuncin da ta Kai ko siyyaya kikayi shi yake biya koba haka bane? Kuma 'yan Nigeria sai ake Baku wasu kudin scholarship daga wata kungiya MMD anyi haka? Ke naki yana ninka na sauran kunyi bincike kun rasa gano meyasa hakan yake faruwa haka ne? Kai kawai Zahra ta gyada Masa Dan ya kasheta da mamakinsa, cheeks dinta ya shafa a hankali Yana Mata smile har dimful dinsa ya Dan lotsa kadan Kinsan Allah da ban Aureki ba ina ga hummm.... Allah dai ya kyauta da dai Kam.. za'a Sami matsala Dan inaga maza biyu Zaki aura Dan Ni dai bazan hakura ba to sai Ubangijin Daya dasa soyayarki a zuciyar ya ta kaita al'amuran, Kinsan Muneeb Dan yayar mummy Badi"a ne?". Wani kallon warrr tayi Masa na nuna mamaki, ban gane ba kasan shi kenan?. Bar wannan maganar ta wuce sirrina ne bazakiji yanda aka haihu a ragaya ba, Sameer ne ya Zama Dan leken asirina duk yanda kaso aji wani Abu Sameer yaki fadin komai shima nunawa yake Yana zuwa ne Koda hasken da ake samu a Kan tafiyar tawa, Kuma duk abinda nake yiwa Hajiya Inna nace ya Dora Dan a Dan tsakanin jininta Saida yayi mahaukacin Hawa har Egypt sukaje da Uncle Mustapha da Mama mainuna surukar Aishat Ina da masaniyar komai Dan hatta bill dinsu na Asibitin Ina daga can nayi komai abinda ya darsa zargin Sameer yasan inda nake a zuciyar uncle Mustapha. Sameer ne ya kawo min labarin Ashe lokacin Dana bar gida Batool rikicewa tayi a gidan ta Hana kowa zaman lafiya ta Fadi duk abinda ya faru a Ranar da lokacin Dana kawo musu Kaya da lokacin da aka Fara fitinar sai lokacin Sajjad ma yayi bayanin shima abinda ya sani, Kuma aka shiga bincike har gurin securities Suma maganar iri Daya ce data batool sai lokacin mutane suka Fara dawowa cikin hayyacinsu aka shiga tuhumar Safna da tambayoyi na hankali Wanda ya kamata ace tun Ina Nan akayi su, inda ta kafe kaida fata ita maganarta babu canji, Kamar batool ta hakura Ashe gidan uncle Mustapha yaje ta nemi ya shige Mata gaba tana son aiwatar da wani aiki, baiki ba yace ta fada masa menene? A nutse tayi Masa bayanin kamfanin waya na MTN da AIRTEL ze rakata zata bada aiki duk da zata iya amfani da sunan family din ko ID card dinta na dalibar koyon aikin shari'a Amma tafi son suje da Babba yanda za'ayi Mata aikin a Kan Kari. Ba qaramin mamaki uncle Mustaphan yayi ba lokacin da sukaje kamfanin Dan lambobin wayar Sameera da Safna da uncle saminu da wata wadda baisan Kota waye ba ta bada tace wadannan takeso a bibiyar Mata tun daga Kira chart , messages dinsu duka daga Nan zuwa wata Daya haka sukaje Airtel ma ta bada suka caji nasu suma, shi dai uncle Mustapha Dan kallo ya Zama sai lokacin yayi nadamar Hana ma'asuma yin karatun law gasu Nan ridi-ridi babu Wanda yayi irin wannan tunanin sai 'yar cikinsu wadda take dibace ma a fagen karatun Amma harta iya irin wannan nazarin da aiki da hankali Wanda suka kasa su.

Cikin ikon Allah komai ya kammala suka Kira uncle Mustapha suka fada masa shi Kuma ya Kira Ammi yace ta turo Masa batool, tare sukaje kamfaninin kusan babu banbanci a aikin nasu sai ma na Daya kamfanin Daya Dara Daya fito da hujjojin zahiri Alfarma suka nema a Basu ma'ikacin da zeyi aikin Ranar da suke son abun ya kasance to kinsan dai yanayin Qasar indai zaka bude bakin aljihu yanzu ne zakaga biyan bukata, suna fitowa uncle Mustapha ya cewa Batool to ita nata aikin ya kare tabar sauran a gurinsa yashi Mata Albarka kamar me,ita fa batool ko Ammi Bata fadawa komai ba duk Fadi tashin da takeyi saboda haushin kowa tajeji gidan. Kwana biyu da zuwansu kamfanin taji ana maganar Abbie na Kiran meeting na duka family a Babban hall din Nan da kukayi walima. Mutane sun amsa Kiran kamar ba gobe Dan sun San da walakin goro a Miya, Uncle Mustapha ne yayi Addu'a da jawabin maraba ga jama'a sannan yace wani Abu yakeso kowa ya maida hankali ya saurara yaji sai mu yiwa kanmu adalci a ciki game da maganar Mahmud da yarinyar Nan safna, Jin haka yasa su Aunty Sameera da uncle saminu zasu tada Zaune tsaye, Abbie ne ya taka musu birki yace ko shi baisan menene ba tosu meye zesa su tada hayaniya Kan abinda bakasan menene asasinsa ba, dole suka hakura Amma zuciyar Safna kamar ta fito Dan mugun bugawar da tajeyi. *_AUREN HUCE HAUSHI_*

AISHAT ISAH MUSAH.

(Maman Fateemah).

09061432330 Or

08055362975

Page 95.

______Ba'a dauki dogon lokaci ba ma'akacin kamfanin wayar ya hada komai ya saka microphone yanda na nesa zasuji magana, cikin abinda Bai wuce minti biyu ba maganar Aunty Sameera ta karade gurin ita ta Kira uncle saminu ta nemi ganinsa a lokacin take tamyarsa yaje gurin data fada masa a Nan ya fada Mata yaje har ya bada turare Wanda safnar zata shafa taje gurina idan na shaqa ban Isa nayi Mata musun duk abinda ta buqata Koda kuwa kwanciya da ita ne, shine suka hada tazo da system tayi min wannan shishshigewar Dana kasa hanata a Ranar da uncle saminu ya samemu Ni da ita da yamma Wanda yaso tun a Ranar ya hada min gwarama sai Kuma Allah ya Kare abun ya shashance, sai kuma sauran maganganu Wanda Basu shafeni ba, haka aka dunga sauraren yanda suka ringa kulla makirci kala-kala ita da uncle din har turo min Safna daki, Ashe duk setup ne. Sai Kuma wayata da Safna a mabanbantan lokuta babu komai sai gaisawa da zumunci da Kuma requesting na kudi da dai sauransu sai Kuma wayar Safna da number din da Batool ta bada,a Nan kowa ya shiga shock Dan abin ba tsabta Dan duk abinda sukayi tun daga chart dinsu har Kira da voice note har video call ba'a rage komai ba Abu mafi tada hankali a cikin wayoyinsu sunyi maganar zubar da ciki ya Kai sau biyu, da irin yanda suke shirya haduwa a lokutan da take zuwa makaranta, a lokacin ne aka gane Ashe duk lokacin da tace ta tafi Niger state saurayin nata take bi har outside country suke fita, ta Nan aka gane tana amfani da layukan waya hudu da wayar ta yanda idan ta fita makaranta take rufe wayar tace saboda suna lectures ne. Daga karshe aka dawo kansu uncle inda aka dunga sauraren makirci abun dai babu Dadin ji, har na karshen nan Wanda suka hada karfi sukaje har okene gurin wani matsafi suka karbo abinda aka turara min a daki da wasu tsubbace_tsubbacen da akayi Dan kowa yayi min naqi, duk ta waya suke shirya komai Dan a zahiri bazaka tab'a cewa da wata alaqa irin haka a tsakaninsu ba, a Ranar da abun ya faru sun jima suna waya da hada yanda abun ze kasance Dan turaren maganin da aka saka Aunty Sameera ce ta shiga da kanta tayi lokacin yaran sun fice sallah sannan Safna da uncle saminu suka shigo dakin lokacin da uncle din yayi waya da security din gidan Hajiya Inna yace Masa mun fito da zayyan, shine fa suka shirya min wannan makircin Wanda kowa ya kasa gane meye gaskiyar Al'amarin sai batool da Allah ya tsareta ita da uncle Mustapha, tunda aka Fara wannan fallasar su Safna da Sameerar ke zufa Shima uncle sadda Kai kasa yayi, mutane kuwa Nan da Nan guri ya kaure da hayaniya masu Ala tsine nayi masu sharben hawaye nayi masu Ala wadarai nayi, cikin borin kunya Aunty Sameera ta tashi tana zazzaga masifa da hawayenta bibiyu tana fadin wallahi shirya wannan abun akayi ita ba ita bace wadda take magana inpersonate ne akayi Mata bazata yarda ba sai tayi shari'a da masu kamfanin wayar, uncle Mustapha ne yayi Mata zabu -zabu akan idan Bata yiwa mutane shiru ba ze saka a tafi da ita a sakaya masa ita ta jira ai da saura. Computer aka hada wadda akayi connecting da CCTV tiryan-tiryan aka Fara nuna duk abinda ya faru a part din su Mahmud a Ranar tun daga safe har dare,duk shige da ficen kowa gashi Nan kowa ya gani har abinda ba'a fada ba a wayar Saida aka gani in da uncle saminun ya fasa interlock din kofar shiga part din mu ya binne wani Abu da turaren da akayi da shiga cikin dakin da wayar da yayi lokacin da Mahmud ya taho da shigarsu dakin har da Wasan banza da sukayi kafin suji shigowar su Mahmud, sai lokacin akaga Ashe uncle bayan curtains ya shige ita Kuma ta tsaya gefen da kofa zata karareta idan ya bude kofar, duk abinda ya faru kowa yaga zahiri Nan da Nan hankalinsu ya Kara tashi Dan An yanka ta tashi abinda hankali da tunaninsu Bai tab'a kawo musu ba kenan, Abbie ne ya taso idanunsa sunyi jajur sai huci yake Yana fadin Sameera tazo su fice Masa daga gida ya saketa saki uku minti biyar ya Bata idan suka wuce haka sai sunga kaskancin da Basu tab'a tunanin ana yinsa ba, Nan Sameerar ta Fadi tana birgima tana tuma da fadin ta shiga uku wallahi saminu ne ya sakata yace Dan mu mallake dukiyarsa idan mukayi haka Dole sai yanda mukayi dashi da kowa ma Tunda babu Wanda ze iya bude Baki yace Mana ba haka za'ayi ba. Kan uncle saminu Abbie ya juya ya nuna Masa hanya Yana fadin ya fita kada ya Kara ganinsa a gidansa yaje yaji da kunyar tonon sililin da akayi masa, Safna kuwa a Nan da sume Saida aka yayyafa Mata ruwa ta farfado tana sambatun ita babu Mai rabata Dani Tunda an daura Aure take Abbie ya rattaba saki ga safna a madadina Tunda Daman bansan da masaniyar Auren ba. Hajiya Turai ce matar Autan su Alhaji sa'id tasa aka fita da Safna da Aunty Sameera. Saida aka wuce dasu sannan Ammi ta tashi wadda tun lokacin da aka Fara bayanin take hamdala ga Ubangiji Daya wanke Mata yaro daga zargin Zina Daya karade a cikin family. A hankali ta ratso mutane ta fito tsakiya ta Fara fadin ta godewa Allah ko yanzu ta koma ga Allah Bata da sauran bakin ciki saboda Allah maji rokon bayinsa ya amsa Mata addu'arta wadda take yinda babu dare babu Rana, saukar Al'quran ma anyi Mata babu adadi Tunda abin ya faru tana addu'ar Allah ya tona asirin duk Mai Hannu a cikin Lamarin, sannan ta juya ta dubi Abbie tana fadin daga yau kwanan gidan Nan ya qare min abinda nake jira kenan Daman gaskiyar tayi halinta, to Kuma yau Alhamdulillahi gaskiya tayi halinta Dan Haka Nima hanya kasan fita ta. Ta juya ta fice itama, abinda ya tada hankalin Abbaie din kenan ya bita da sauri ya fice shima, Dan Tunda yake a zamanzu magana makanciyarta haka Bata tab'a hadasu ba. "To fa kinji dalilin Daya mayar Ammina niger. Hakan ne ya Kara harzikani saboda anyi min rashin adalci, lokacin fa Sameer yazo min da bayanin na jinjinawa Batool matuk'a yarinyar tayi min bazata Sosai, Abu kamar Wasa Duk Wanda sukabi Ammi babu Wanda ta yarda ta biyo da suka Fara rinjar Hajja ne bayan zuwan Hajiya Inna Ammi ta dawo Damagaram gurin Yayanta kafin ya Yanke Mata hukunci dawowa sokoto dole, hummm Amma fa Ina biyiye da duk motsin Ammina Dan Yanke huldar da nayi ta zahiri ce Amma a badini Ina cikin duka lamuranta Dan Ina zuwa Yamai duk lokacin danaso ganinta sai dai su nemeni su rasa a can garin, ganin nesa ta tazo kusa yasa nayi zamana a garin ku dankwali yaja hula, sauran bayanai da yawa Kuma sirrina ne. Kinji kadan daga abinda ya sameni Dan ma na takaita Miki wasu abubuwan da uncle saminu ya ringa nuna min ke dai abar kaza cikin gashinta kawai, idan ana cin B'aure ba'a tona cikinsa Kuma idan ana sallah ba'a magana, wani sanin sirrin cikin ciki sai dai hanji kawai, Dan haka ban Hana ki gaisa da zuri'ar uncle saminu ba Amma na yanke Hulda dasu har abada kamar yanda mahaifina ya cire Shi a cikin duk sabgoginsa sai dai abinda ba'a rasa ba Dan masu iya magana na cewa hannunka baya ribewa ka yanke kayar,to kinji summary na abinda ya faru Dani ya Zama sanadin da yasa na fito a wancan lokacin sai dai ni Alhamdulillahi hakan wata Rahama ce daga Allah. Jinjina abin Zahra take a cikin zuciyarta ace duk wannan masifa ta dumfari mutum Daya ai sai Wanda Allah ya bawa karfin zuciya da imani ace duk girman family Kamar wannan duk sun maka nak'i Sai mutum biyu kawai lallai anga taskun rayuwa. A hankali ta sauke numfashi tana kallonsa Banda tasan baya son kuka ba da wallahi saita matse yanda zuciyarta ke Mata zafi, Dan ji tayi ta tsani safnar da yayarta tsana Mai zafi wadda ita dai ko Mama da Salma da suka nuna Mata qin jini bataji su kamar wadannan ba. "Me amorrrr....". Ta fada a hankali. Gyara Mata kwanciya yayi a cinyarsa Yana kallonta cikin Ido. "Umhummm.... Fadi ya akayi?". "Allah ya Kara maka juriya da hakuri kaga jarabawa ta rayuwa, lallai Ubangiyi yayi gaskiya da yace shin bazan jarabceku ba?. Amma taka dai Kam sai Mai karfin Imani Dan Mai karamar kwakwalwa sai kansa ya buga koya fada wata harkar Tunda babu ni'imar da Ubangiji Bai maka ba, Allah ya hore maka amma ya baka kariya daga fadawa mugunyar rayuwa, ya tsare min kayana Alhamdulillahi Allah abin godiya". Dagota yayi daga kwancen ya kafa Mata idanunsa da suke razanata a wancen lokacin Wanda Kuma suke tsumata a yanzu. "Kice Kayan naki ne ke kadai, to ya za'ayi da sauran dake kokowar shigowa Kuma?". Wani warrrr tayi masa da sexy din ta Wanda wani irin Abu yake walainiya a cikinsu. "Ai dagani babu wata a yanzu dai saina cinye na sude kayana tas sai dai su samu sudin kwano". Rike Baki Yayi Yana wata dariya kasa-kasa. "Kai yarinyar nan yaushe kikayi Baki haka? "Wato kin Fara gane garin ko?". Dariyarta Mai shagaltar dashi ta Fara tana nuna shi da hannu. "Ni Kuma wane garin na Fara ganewa?". Ba zato yayi Mata daukar jarirai yana fad'in Bari na nuna Miki garin".

*****Tunda su Ammah suka shiga garin Miya kukan Salma ya tsananta tamkar zata shide, Banda aikin lallashi babu Abinda su Ammah keyi daga karshe ne Aunty Hassana ta rufeta da fada ta inda ta shiga ba tanan take fita ba. Shi dai malam Bala ko tari Bai kubce Masa ba Dan yasan sakayyar Allah ce kawai ta sauka akan Mama da 'ya'yan ta Dan dashi wani Maci Amana ne da Allah kadai yasan abinda suka shuka shida ita to tun tayin farko ta taka Mata birki da barazanar sanar da Alhajin shine abinda ya kawo basa ga maciji a tsakaninsu. Ba laifi gidansu Anas din da nasu rufin asirin sai dai da alama rayuwa ake ta babu kwaba a gidan Dan yanda kannensa Mata suka ringa yatsina fuska ga babu tarbiyya Kota sisin kwabo a gidan saboda da kyar kanwarsa Haulatu ta bayar da key din dakinta a sauki Baki cewa tayi ita da kayanta kada a Bata mata, sai wani kanin Anas din yayi Mata Jan Ido sannan ta bada, aka bude suka shiga inda aka kawo musu Abinci ba laifi ta Nan sun yaba, amma dai uwar tasa basuga fuska a gurinta ba, sun dai gaisa shima ganinsu Ammah da tayi ba karya sun jiku da naira gayu ya zauna dole ta mayar da makaman yakinta ta Bari idan sun wuce ta baje kolin abinda ta tanadarwa daga salmar har Anas din tunda 'yar kanwarta yake aure Bai Kuma fada Mata ze auro Salma ba saida iyayensa maza zasu tafi daurin auren suka shigo suka fada Mata Tunda Babansu ya rasu. A dofane suka wayi gari inda tun karfe bakwai motar Kayan ta sauka a Miya Dan tun dare Abba yasa akayi lodin Kayan abinda babu yasa su sahura da makotansu suka shiga stores suka sawo, Kayan toye-toye ma gidan masu yin na sayarwa akaje aka sawo saboda Basu da matsalarsu a unguwar da Kuma can bakin kasuwa. Kafin azzuhur gida ya kankama na amarya, Ammah ta saka Salma tayi wanka wadda har lokacin kuka takeyi ga azababban Zazzabi Daya rufeta, a irin kayan da aka dinka na Zahra Wanda magaji ze tafi dasu Ammah ta debo Mata kala kusan goma ta taho Mata dasu Tunda babu Abinda aka tanada bagatatan abun yazo. Su Ammah sun Kara Kai Salma gurin surikarta sun bada Amanarta sannan suka mikata dakinta tare da yayar Baban Ana's din, tana gunjin kuka suka barota Dan abinda Bata tab'a kawowa bane ko cikin mafarki akayi Mata taci burin auren miji na kece raini ta shiryawa kanta rayuwar Jin Dadi da walwala Amma sai gashi ta Kare a auren yaron kamfanin nefa Zama a inda ko cikin hasashe Bata tab'a kawowa ba, haka su Aunty Hassana suka wuce. Saukinta Daya gidan da abunda aka zuba Mata ze kankaro Mata mutunci ko banza ta Nan fannin dai babu raini.

***

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull