Kenza eBookz

Auren katin kasa complete - Chapter 13

Auren katin kasa complete - Chapter 13

Auren katin kasa complete Chapter 13: Auren katin kasa complete Chapter 13. Ganin tayi nisa a baccin yasa baibi ta kanta ba ya nufi hanyar futa, daidai…

6,031 words

Ganin tayi nisa a baccin yasa baibi ta kanta ba ya nufi hanyar futa, daidai bakin kofar ya juyo ya sake kallonta ganin kamar kwanciyar da tayi zai iya sawa ta fado don tana gab da jikin gadon a ringine, kamar bazai motsa ba daga inda yake ba Chan kuma ya juyo ya koma gaban gadon, tsayawa yayi daidai saitin fiskarta dake fuskantarshi,kallonta yake sosai wanda shine kallo daya taba mata na kurulla, kyakyawar cute baby face dinta ya zuba Ma ido wadda curly gaban gashinta ya soma rufe fiskar tata she look so innocent, Jan dan numfashi tayi kamar wadda a ka tsungula, ta dan turo redish lips dinta alamun kwanciyar bai mata dadi ba, juyi ta soma yi cikin bacci, aykuwa kamar yanda yayi tsammani yanda ta mirgino dinnan zata iya faduwa,bai gama tunanin ba ta gangaro da sauri ya dan rankwafa sosai ya tallabota jikinsa, gaba daya bata da wani nauyi amma yanayin yanda take da jiki da kayan alatu zaka dauka zatayi nauyi, wani irin sanyin niima ke shiga cikin kashinsa da jikinsa, tare da yanda take dan juyejuye acikin kirjinsa daya saqala ta Sai abin yayi mashi kamar tana goga mashi kirjinta ne, daurewa yayi ya miqe da ita a jikinshi ya kwantar da ita akan gadon asibitin yanda bazata fado ba saida ya gama ya juya zai fita kenan idanunshi suka sauka kan rigar jikinta da sauri ya gyara mata rigar donta yaye sama Santala santalan cikakkun lallausan fatar cinyoyonta da suka bayyana, yana gama wa ya fuce bai sake Waiwayon ta ba.
Wurin doctor dayayi operating dinta ya nufa inda ya shaida mashi nan da gobe za a sallameta don ta ji sauki saidai abinda baza a rasa ba saikuma dingishin da takeyi shima within 2days zata dawo normal, Sai kuma yanayin cin abincinta da Har yanxu ba komai mai nauyi zata ke ci ba, godiya yayi ma doctor ya fuce wajen da yayi parking motar shi, office ya wuce direct yayi wasu few ayyuka don Ana saka rai dawowa hutu very soon.

Hammam…..
Kallon mahaifin sa yayi wanda ke zaune kan kujera da mamaki dauke a fiskar sa,yanayin yanda yake mashi magana kadai zai tabbatar maka this time around da gaske yake akan kudiriri kan sa, sauke idanunsa yayi wanda sukayi jaa suka rine sakamakon maganganun da yake fada mashi da kuma tunatar dashi tushen sa da asalinsa "karka manta, nine na maidakai mutun lokacin da kake ba kowan kowa ba, ni na suturta ka nina ilimantar dakai sannan na baka Duk wani kin dadi na rayuwa, so this should be the last time dazan umarce ka akan abu kamin gardama"

Dagowa Hammam yayi ya kalli mahaifin nashi wanda ya hade fuska babu imani ko kadan acikinta, anatse ya soma furta "in sha Allah bazan Kara maka gardama ba za ayi yanda kake so, sannan ka bani number Zan yi kokari akai,daman badan komai Nace a jinkirta ba saboda yanda yanayin abubuwan suka zo ne kuma ban boye maka da wata manufa ba saidan na bari Saina Tara Duk wani evidence da zaka ji dadin samu" duk wannan zancen nasu cikin harshen larabci suke yi, saida suka gama magana kafin ya Tashi ya fuce daga gidan ma baki daya kamar zai Tashi sama,tuki yakeyi Amma idanunshi sunyi jaaa sosai,bai tsaya ko Ina ba Sai wani kebataccen waje saida yayi parking ya kutsa futo anatse ya shige ciki, maqabarta ce cike tam sosai wanda tasha tsafta ko'ina tsaftsaf babu dogon datti anatse ya Taka Har gaban wajen da aka rubuta Fatima bint malawi, tsungunnawa yayi daidai wajen idanunshi na kawo qwalla, saida yayi mata addua sosai na samun yafiya wajen Allah sannan ya miqe "umm I'm successful now, amma Duk bana ganin amfani komai saboda bakya raye, nayi maki alqawarin baki jindadin duniya saidai rai yayi halinsa,Allah ya jiqanki ya gafarta maki"…yana kaiwa nan ya juya ya koma cikin motar shi, zaman kusan Rabin awa yayi idanunshi na kawo qwalla sosai, deep down yana jin abubuwa da dama dayake yi kamar ba daidai bane ba amma tunawa da kalaman mahaifiyar sa wadda ke tinasar dashi koda yaushe Duk wanda ya daraja rayuwarsa ya daga shi ya maidashi mutun kada ya sake yayi butulci sannan ya kasance mai hallaci agaresa. Kallon wayansa yayi yana wasu Yan danne danne kafin daga bisani ya Kurama number da mahaifinsa ya tura masa ido yayi kafin ya aje wayan, tsaki yayi duk haushi ya gama kamashi Duk shi yayi sakacin mantawa baiyi copy din evidence din ba gashi yanxu komai ya tabarbare mashi don mahaifinshi yayi tsananin fushi kuma yana ganin kamar yaqi fada masa ne don wani dalili daban wanda shi Sam ba haka bane ya bari ne komai yadan lafa sannan ya bullo ta bayan fage, tsaki yayi ya kunna motar ya fuce daga harabar wajen.

Abu Dhabi hospital…
Sai wajen magrib ta farka, ahankali take lumshe idanunta wanda sukayi mici mici ta sauke su kan couch din dake facing gadon da take kwance, ganin baya wajen yasa tayi miqa bakinta dauke da salati sannan ta fara kokarin sauko da zara zaran kafafunta, ahankali hancinta ya fara jiyo mata kamshinsa, mamaki ne ya cikata don baya cikin dakin amma yanda take jin kamshin kamar yana kusa da ita, sannin yanda komai nashi kamshin yake hatta kujera Idan ya zauna ya Tashi kamshinsa na maye wajen yasa ta Kawar da tunanin ta miqe, harta wuce toilet ta dauro alwala ta fito jin kamshisa take sosai, ahankali ta jawo kasan rigar ta don goge don ruwa daya shiga mata ido, tsayawa tayi kyam ba tare da tayi abinda taso yi ba jin kamshinsa tarr ajikinta ahankali ta gangaro da hancinta zuwa gaban rigarta, mamaki ne ya cikata ta yanda akayi kamshinsa yazo jikinta, Kawar da tunanin tayi don Duk zatonta lokacin daya tallabeta ne data kusa faduwa kasa. Saida tayi salla ta idan kafin ta cire hijabin ta koma kan gadon ta doka uban tagumi wayan take so ayanxu don ta sake Kiran su salima ko za a dace amma babu hali, wasu siraren hawaye ne suke saukowa daga idanunta zuwa kan fuskarta tun bayan ta farfado Sai tayi kukan don babu abinda ke fado mata arai Sai tunanin yanxu da ta mutu fah shikenan kannen ta basu da wani basu da kowa ita kadai ta rage masu,lokaci guda taji karatun da komai ya fuce mata, hankalinta Duk ya koma gida don gani take kamar idan Har ta cigaba da zama ba tare da tasan halinda suke ciki ba wani abun zai iya samunsu koya cutar dasu,Amman sanin cewa babu wanda ke rayuwa kuma ya tsare Sai allah Hakan yasa ta fawalla Ma allah komai ta kai kukanta wajenshi don yanxu bata da kowa wanda zai tsaya mata saishi.


Washe gari wajen karfe biyar na yamma Amar ya iso asibitin, saida ya gama clearing Duk wani bills kafin ya wuce cikin dakin da aka kwantar da ita, lokacin daya shiga yayi mamaki ganin babu kowa a cikin dakin, jin alamun saukan ruwa acikin toilet yasa ya samu waje ya zauna kan couch din dake facing patient bed din, zaro wayanshi yayi yana diban time don yana sauri ne sbd Kiran da Hammam yayi mashi akan wani aiki da zasuyi urgently a office, bai jima da zama ba ya bude kofar toilet din ya futo, sanya take da kayan daya kawo ta asibitin dashi wanda tasa aka wanke mata a laundry din asibitin, batama lura da mutun a cikin dakin ba saida tazo tsakiyan dakin ta hango shi idanunshi kyam akanta, da sauri ta sauke nata ta soma magana a hankali "Ina wuni yaa..ya".. bai amsa ta ba daman tasan hakan ce zai biyo baya,saidai tsintar hard voice dinshi tayi yana cewa "I hate people wasting my time, na baki minti biyu ki sameni a waje " yana kaiwa nan ya sa kai ya fuce, da idanu ta bishi saida taga fucewar shi ta tabe baki, daman bata dade da Tashi ba tayi wanka ta shirya don already doctor dake ganin ta ya shaida mata sun sallameta, shiganta toilet kenan zatayi alwala don bata samu tayi sallan asr ba sakamakon baccin da tayi sosai tun bayan sallar dhur, hijab dinta ta zura sannan ta sanya takalmin asibitin don kwata kwata babu takalmi aka kawo ta, ficewa tayi daga dakin anatse don Har yanxu tana dan digisawa sakamakon gefen inda akayi mata aikin cikin data dafe don tundaga kan wajen aikin Har zuwa kafanta na daman tana jin kamar ba a jikinta suke ba.
Daidai gaban kofar shugowa cikin asibitin ta tsaya ganin mota guda a gaban wajen sannan ga horn dataji daga motar yasa tadan qara saurin kafar ta don tun fitowar ta ya hangota, cikin hanzari ta bude kofar gaba ta shiga da sauri wanda hakan yasa tadan fama cikin nata, rufe kofar tayi ta runtse idanunta sosai hawaye na zubo mata, baima tsaya bi ya kanta ba ya fizgi motar ya fice daga harabar asibitin, shuru ne ya biyo baya baka jin komai Sai ijjiyar zuciya da take sauke wa Sai kuma sanyin ac cikin motar tashi da kuma kamshin turarensa wanda yanzu kam itama ji take kamar kamshi ya fara bin jikinta, sanyin ac ne ya soma shiga cikin kasusuwanta, ganin yanda ta takure yasa yayi mata kallon daya ta wutsiyar ido yace "lafiya?" Kallon sa tayi wanda idanunta suka sauka cikin nasa da sauri ta dauke nata "uhm..daman sanyin ne yayi yawa".. kamar bazai yi wani abu abun ba don saida ya dauka kusan minti biyar kafin ya rage gudun ac, ahankali ta sauke ijjiyar zuciya tana mamaki halayenshi, shi ba a isa a saka shi abu ba Sai yayi niyya idan kuwa zaiyi saiya jaa aji, lumshe idanunta tayi wanda suka rine sosai dalilin dan kukan da tayi da kuma yawan koke koke da take Duk dare akan qannenta.
Direct apartment dinshi ya wuce suna isa yayi parking, baiko kalle ta ba yace "kije" jin haka yasa ta bude motar ta fuce abinta, shima yaja motar ya fuce daga cikin compound din, ahankali take tafiya harta karasa gaban lift ta danna floor din da zata sauka, tana karasawa gaban kofar ta tuna bata san pin key dinba gashi ya tafi, ga magrib na dosowa, komawa gefen jikin kofar ta tsaya don babu abinda zata iya, gashi babu waya a hannunta ganin tsayuwa bazai yiwu ba ga yanayinta yasa ta danyi gaba wajen lobby inda Aka aje wasu Yan kujeru a wajen ta zauna, Har kusan karfe Tara tana nan zaune, ga yunwa dake nukurkusarta ga cikinta dake neman kullewa ga shi wani irin bacci ke fusgarta ga ramuwar sallah don ko sallar asr bata samu tayi ba don lokacin data so yi ya iso asibitin ya dauketa, kuka ne ya kubce mata don ta galabaita sosai, runtse idanunta tayi gam ta dan yi relaxing bayanta akan kujeran Har wani irin wahalallen bacci ya kwasheta, kusan baccin awa biyu tayi a zaunen nan wanda Duk a wahale tayi shi, ga wani irin futsari daya matsota sosai wanda dalilinshi ya farkar da ita, miqewa tayi azabure ta koma gaban kofar apartments din, wasu irin hawayen wahala take,babu abinda take aranta sai rokon Allah ya kawo mata dauki,karshe dai a galabaice ta zauna anan kasa,tunanin yanda zatayi ne ya fado mata arai, yanxu idan tace zata tafi babu waya a hannunta bare tayi requesting taxi, bayan wannan Ma babu kudi hannunta kuma Duk wani transaction da wayanta Take yi.

11pm na dare daidai ya iso cikin harabar compound din saida yayi parking kafin ya fito ,zagayawa bayan motar yayi ya bude ya kwaso ledoji guda biyu sannan ya rufe motar ya wuce ciki, anatse yake tafiya Har ya shiga cikin lift ya danna floor din da zai kai shi apartment dinshi, yana fitowa tun daga kan corner din da zai sadashi da nashi apartment din, daga nesa ya hango ta zaune a kasan, mamaki ne ya cikashi don baiyi tunanin ganin ta a wajen ba, anatse ya tako ya karaso gaban kofar ya kalleta, kamar bazai ce komai ba ya soma magana cikin nutsuwa "zaman me kike anan?" Amra wanda tun dosowarsa wajen kamshinsa yayi mata sallama tare da maganar karshe da yayi yasa ta dan gumtse rinannun idanunta ta bude akan shi, Kawar da nashi idanun yayi don lokaci guda yaji bazai iya jurar kallon idanuun nata ba, babu abinda ya hango Sai wahala da galabaitar da tayi, wani irin tausayi ta ne ya ziyarce shi ba tare da dalili ba, saida yazo danna pin alamarin ya fado mashi, wato bata san pin din kofar bane ta zauna tun wajen 6 daya aje ta a wajen, runtse idanunshi yayi a zuciyar sa yace "why I'm I causing her so much pain".. shigewa ciki yayi ya aje ledojin a kitchen, ganin ya bude kofar yasa ta fara kokarin miqewa Amman ina babu kuzarin yin haka, da sauri ta koma ta zauna ta fashe da wani irin matsanancin kuka ahankali gadan gadan zazzabi mai zafi ya tunkarota, jin shuru kusan minti biyar babu alamun shugowarta yasa ya Ankara da tunanin daya tsunduma,ahankali ya tako Har gaban kofar,ganin yanda take kukaa wiwi yasa ya karaso Har gabatan ya tsugunna ya daukota gaba dayanta, ya shugo ciki da ita ya rufe kofar, Duk wannan dramar akan idanun hafiza wadda tun lokacin daya sauke amra take bibiyarsu Har lokacin da amra ta karaso ta tsaya gaban kofar apartment din, lokacin data koma lobby yasa hafiza gane cewa bata san pin dinba wanda haka yasa taga dama ce mai girma a gareta, Duk wannan abubuwan da take bata ganin fuskarta don tana nesa da ita sosai,wayanta ta jawo ta fara video tun lokacin da amra ta galabaita Har lokacin daya iso ya shige ciki ya barta dukda yaga ta galabaita saida hafiza ta dauka daidai lokacin daya dawo ya zo daukanta zai shiga ciki da ita ne yasa tayi stopping video din don bata buqatan wannan scene din Iyakacin wanda ta dauka ya wadatar don wannan kadai zai tabbatar da babu so ko wani alamun auratayya a tsakaninsu, murmushin mugunta tayi don wannan Ma evidence ne mai karfi, wanda idan Har uae marriage consent group suka gani dole za a fara zarginsu, saidaga baya ta fara jin gajiyar tsayuwar da itama tayi dukdan samun biyan buqatarta, anatse ta tattara ta fuce daga apartments din gaba daya sannan ta tafi.

Bai sauketa ko'ina ba Sai cikin bedroom dinshi, anatse ya kalleta yace "go and freshen up" ya fuce zuwa parlor, ahankali ta fara bin bango harta wuce cikin toilet dinshi, saida ta rage mararta kafin ta sakarma kanta hot shower saida ta dade sosai ta gasa jikinta kafin ta fito da kayan jikinta, hijab dinta ta maida sannan ta fara takowa ahankali har ta futo parlor, idanunta ne suka sauka kan nashi daya tsaya gaban fridge hannun shi rike da ruwa alamun ya gama sha, ledan daya aje a kitchen lokacin daya shigo wanda daya maganinta ne daya kuma abincine ya kwaso ya tako Har inda take ya aje agabanta , karba tayi tare da mashi godiya, baiko amsa ta ba ya wuce cikin bedroom dinshi don shima yana buqatar warm shower sosai.

Ganin ya koma daki yasa tayi saurin tube kayan jikinta ta saka mara sa nauyi sannan ta sauya hijab dinta ta tayar da salla domin Rama wanda suka wuceta.

Bayan ta idar ta zauna tayi adduoi sosai sannan ta jawo ledojin daya aje mata ta fara budewa daya bayan daya, kamshin brown veggies pasta ne ya fiki hancinta, anatse ta soma ci Har ta samu taji ta koshi don Lkita yace ta takaita cin abinci sbd aikin da aka mata, mikewa tayi da sauran abuncin ta wuce kitchen ta aje sauran a fridge sannan ta bude drawers ta dauka glass cup ta Debo warm wata a cikin dispenser tasha kadan sannan ta koma parlor da cup din ruwan, zama tayi a kan couch din parlor ta jawo ledan magungunan ta balla wanda ya kamata tasha sannan ta aje agefe, anatse ta gyara kwanciyanta taja hijab din jikinta ta kukaje idanunta don tunda ta soma cin abinci baccinta soma fuzgarta, Ringinawa tayi don karya fama aikin da akayi mata acikinta. 87-88 Washe gari bata tashi da wuri ba don wani irin bacci ne mai dadi ya dauketa tun bayan sallar asuba datayi sai wajen karfe 11am na safe ta tashi daga bacci, wanda karar bude kofar fita da yayi ne ya sata farkawa, ganin ya fice yasa kamar kullum ta miqe ta wuce bedroom tayi wankanta a bathroom hankali kwance tayi brush da alwala ta futo kai tsaye, shiri tayi cikin baqar abaya wadda tasha stones masu kyau sosai, parking gashinta tayi wanda yake buqatar kulawa ta musamman sannan tayi rolling veil din abayar, wani irin sihirtaccen kyau tayi na musammam, rigar ta zauna dam a jikinta, tayi mata masifar kyau, red lipstick kawai tadan Mirza a lebbanta sai dan kohl data shafa a idanunta ta sannan tadan fesa turaren ta na hermz wanda yawan ci bata rabo dashi,agurguje ta karasa shiri ta kafin ta kashe tv dake Kara ta tattara parlor saida ta kammala kafin ta zari wayan ta ta saka flat shoes baki na Zara dake cikin akwatin ta sannan ta fuce, anatse ta rufo kofar sanin babu buqatar saka wani pin yasa ta wuce gaban lift cikin natsuwa ta shige ciki, dannan grown floor tayi within seconds ta iso ground floor, saida ta tsaya gaban compound na Yan mintuna kafin motar haifa ta kunno kai,saida ta tsaya daidai gaban ta kafin ta daga kafafunta ta karasa cikin motar murmushi kwance a fuskarta na kewar aminiyar Tata, tana zama tayi facing haifa tace "babeeee I missed you so badly" kallonta haifa tayi fuskarta dauke da murmushi tace "bridey Ay na barki ne kisha honeymoon bfr mu samu baby sainazo na kula Dake da babyn" dariya haifa ta kyalkyace dashi ganin yanda maganar da tayi yasa amra tabe baki murmushin nata ya dauke lokaci guda tace "in your dreams that's impossible my dear ay badan hakan akayi auren ba ko har kin manta"…ganin dariyar Haifar taqi karewa yasa ta saurin cewa "wallah Zan koma idan bazaki bari ba mu wuce"…, anatse haifa ta ja motar suka fuce daga harabar compound din saida suka hau kan babban titin dar jamal kafin haifa ta kalleta "babe yanxu da Ina zamu fara, ni inason zuwa shopping na karba black card din Abu Ma"
Latsa wayanta take bata dago ta kalli haifa ba tace "no babes mu fara zuwa saloon Ina buqatan hair treatment Kinsan yanda natural hair dina ke bani wahalaa Wallahi kamar na aske"…
"Okay tohm, but kema nace maki just relaxed the hair kinqi kin tsaya gayuu, anyway yanxu na gane dalilin gayun da kikeyi it's because of…."
Bata Bari ta karasa ba tace "haifa please!!!! Don't spoil my mood"… dariya haifa ta dunga mata Har suka iso saloon, as usual Yauma saida aka fara Gyaran gashin nata kafin aka fara masu pedicure da menicure, Sai full body polish wanda haifa tayi requesting suyi, kusan awa biyu suka dauka kafin aka gama masu gaba daya, dakyar amra ta yarda haifa tayi payment din wanda bata so hakan ba, saida suka fito suka shiga mota amra ta fara jin yinwa, Sai alokacin ta tuna batayi breakfast ba gashi almost 2pm, da sauri haifa ta jasu zuwa wani cafe suka dan rage yunwa kafin suka wuce mall, basuyi wani sayayyya sosai don amra pir taqi yarda haifa ta kashe mata kudi wanda ganin hakan take yanxu bai daceba wanda akayi mata a baya Ma ya wadatar don babu mai maka irin wannan abun Sai mai sonka sosai, lallai haifa ta zama mata yar uwa wanda ta shigo rayuwarta babu sani babu tsammani, Duk yanda amra tayi kicin kicin haifa saida ta saya mata wasu kayan bacci Sai Yan abubuwan da zata buqata nan kusa kamar turare dasu sabulai wanda itama haifa din ta dauka Ma kanta, saida suka shafe wajen awa uku a mall kafin suka fito, lokacin wajen karfe 5 na yamma, tsayawa sukayi wajen grocesy shop wanda amra tadan saya kayan abinci don kwanakin da take duk a wahale takeyin shi ga kudin saving dinta yana neman yin kasa sbd yanda take kashewa tana ordern abinci ba kamar lokacin da take apartment dinta ba, bata yawan order lokacin sbd babu amfani indai har zata girka, few abubuwa ta saya hardasu fruit da vegetables sai shinkafa dasu pasta da seasonings da meats duk wani abun buqata saida ta sayo sannan tayi payment suka nufa mota, tafiyar 20mins sukayi suka iso lokacin wajen karfe bakwai na dare daidai compound din haifa tayi parking, da kyar ta lallaba amra ta karba sayyayan datayi mata a mall kafin tayi mata godiya sukayi sallama ta fito haifa kuma ta wuce, karasawa tayi cikin building din apartments din, agajiye ta karasa gaban kofarsu, saidata zo daidai kofar ta tuna bata san pin din ba hankalinta atashe tunawa da tayi last time da irin haka ta kasan ce mata kuma tana ta Allah Allah ta tambaye shi sai kuma ta manta,tunawa da ya rigata fita yasata tunanin maybe ya dawo, cikin hanzari ta soma danna door bell din, saida ta dauka Kusan 30mins tun bayan ta danna Sai uku shuru, hakan yasa tayi tunanin bai dawo ba sanin baya dawowa Idan ya fita wani lokacin ma harsai tayi bacci yake dawowa da daddare, aje shopping bags din da Haifa ta bata tayi da sauran kayan abinci data saya a Kasa sannan ta fara laluben wayanta dake cikin aljihun abayar dake jikinta, tana zaro wayan ta fara tunanin yanda zatayi laluben contact din haifa tayi, bata kaiga danna call din ba aka bude kofar, da sauri ta dago ta kalli fuskarshi don ta tsorata sosai batayi tsammanin yana nan ba tsawon lokutan data shafe a tsaye, idanunshi ya soma lumshe wa da alamu bacci yake mai nauyi sosai,white shorts ne kawai a jikinshi wanda ya kamashi sosai guntu don daidai wajen ma'ajiyar dic** dinshi ne kawai ya samu rufuwa cikin shorts din, bai saka rigaba wanda haka ya same mashi kamar alada idan yazo kwanciya yakan tube ta sometimes, bin kirjinshi tayi da kallo wanda yake afafade ga fadi ga kwantaccen gashinsa da suka kwanta lub a kirjin zuwa ga damtsen hannunshi wanda yanda ya damke kofar karfaffen hannunshi hade da jijiyoyin wajen suka bayyana sosai, da sauri ta fara kokarin sauke idanunta saidai akan six packs dinshi suka sauka da sauri ta runtse idanunta lokacin da suka sauka kan tiny tight short dun jikinshi wanda suka ka mashin sosai kuma suka bayyanar da manhood dinshi sosai kamar a fili da yanda gabanshi ya ciko sosai Har wajen na yin tozo kamar zai fiddo kasa, gabanta ne ya fara bugawa pat pat, da sauri a dfe kirjinta tayi saurin kawar da idanunta bakinta na karkarwa tana furta adduar fargaba kawar da idanunta tayi daga shi gaba daya, ganin ta tsaya sototo yasa shi Jan dogon tsuka ya juya afusace ya koma daki don ta katse mashi daddaen bacci da ya daukeshi bayan ya dawo daga wani private meeting da yayi da wasu private investigators baimayi tsammanin ita ke knocking ba dukda lokacin daya dawo bai ganta ba kuma bai damu ba don ba shiga harkar ta yake ba sbd baya son raini ko kadan and shi bamai son mutane bane. 
Yana shiga daki ya wuce toilet yayi wanka ya dauro alwala don gabatar da sallolin da bai samu yayi su ba, yana idarwa ya cire jallabiyan ya sauya zuwa nighties masu laushi don garin ya soma sanyi sosai cikin Yan kwanaki, wanda idan sanyi ne to fah sanyi za ayi sosai idan kuwa zafi ne shima haka za ayi zafi sosai don wether din uae babu sauqi, anatse ya lalubo wayanshi ya kunna lokaci guda yaci karo da messages da yawa wasu daga doctor shi wanda reminder ne yake mashi akan de-freezing sperm dinshi da ya kamata ayi tun last week don daman due date din 3 months ne yana gama duba message din doctor ya bude na Hammam shima dai akan aiyukan office ne wanda za ah koma monday gaba daya, Sai last message daga private investigator daya saka yayi mashi bincike akan amra, qurama message din idanu yayi yana maimaita abinda mutumin ya rubuta "good day sir, I have a new update,both the children are been admitted yesterday night, which one of them is brutally injured I want to confirm if I should keep digging about their sickness"
Saida ya gama karantawa tsaf kafin ya tura mashi message "go ahead, keep a close eye on them,if there's need of any help go to them anonymously"..yana tura mashi ya aje wayan, tunani da yawa na yawo a kanshi, tabbas yarinyar nan rayuwar ta da kanneta abin dubawa ne, dukda ya gane cewa kamar bata da sanayya akan matsalar da qannenta ke ciki, yana nan zaune tayi knocking a natse saida ya dauka kusan minti biyar kafin yace "come in",budewa tayi ta shugo Har lokacin tana sanye da abayar data futa , anatse ta dan karasa nesa dashi tace "ina wuni" bata jira amsa shi ba don tasan da wuya ya amsa, hakan kuwa ta kasance don ko kallon inda take bai sake yiba saima gyara zama da yayi akan gadon yana latsa tsadaddiyar wayarshi that is worth of dollars, wucewa toilet tayi saida ta tabbatar ta kulle daga ciki kafin ta soma tube kayan jikinta don Duk sun takureta sabd wuni datayi dasu, wanka tayi da sabulunshi mai kamshi na royy soap shidai komai nashi is expensive don ta sha ganin soap din idan taje sayayyan kayan skincare dinta wurin packaging dinshi ma da slot din sabulun is different from general soap da ake saida wa, alwala kawai ta dauro, saida ta mayar da rigarta kafin ta bude kofar ta fito, yanda ta barshi haka ta same shi ahankali ta soma takawa zata fuce daga dakin saida ya tabbatar tazo tsakiyan dakin kafin ya dago ya kalleta daga sama Har qasa tunanin iri iri na yawo a ranshi, kwata kwata bai ga alamun damuwa a tattare da ita ba amma sanin irin kukan da take Duk dare da yanda tayi pushing kanta to marrying stranger don ta samu katin kasar uae don wani kudiri nata daman don har yanxu bai yarda da dalilin da suka bashi ba akan katin kasar nata amma yanxu yake ganin komai is making sense nunfasawa ya danyi kafin ya soma magana Adan fadace cikin kakkausar muryarshi "where have you been"?
Da sauri ta dago ta tsaya chak bata juyo ba, juyawa ta soma yi kanta a Kasa kafin ta dago tayi mashi kallo daya don batayi tsammanin jin tambayar daga bakin shi ba,anatse ta soma motsa bakin ta tace "uhm..daman naje Gyaran gashi ne nida haifa"…. Shuru yayi kafin cikin dabara ya soma magana "Kinsan halinda Yan uwanki suke ciki" mamaki ne ya cikata don bata gane wani Yan uwan yake nufi ba, ganin yanda tayi da idanu ya sashi cewa "you can go" juyawa tayi ta fita daga dakin tana maimaita tambayar, ganin ta Kasa gane inda ya Dosa yasa ta kawar da zancen ta shirya cikin kayan baccinta ta daura dogon hijabinta ta tada sallah tana idarwa tayi kwanciyarta don baccin dake fusgarta, shima Sai wajen karfe uku ya koma ya kwanta bayan ya tube rigar jikinshi sannan ya shige cikin lumtsentsen duvet dinshi,
Amra wanda wani mummunan mafarkin datayi ya sata kwala uban kara tana innalillahi arazane ta zauna tayi zaman dirshen babu abinda take furtawa Sai innalillahi, wani irin mafarki tayi akan su salima wanda yayi mata zuwa kamar zahiri, don ta tsorata sosai da yanda yanayin mafarkin yazo idan Har badan tanada imani ba zata ce abin da ke faruwa kenan da kannenta, Salim ne ta gani yashe a kasa duk jikinshi jini kamar matacce Sai salima wadda itama tana kwance jina jina dukta galabaita, babu abinda take Sai kuka tana cewa shikenan Salim ka mutu innalillhi adda shikenan nima mutuwa zanyi, adda yunwa nake ji adda kizo ki taimake ni yunwaa" bata kaiga karasawa ba ta yashe itama ta kasa matatta take zuciyar ta ta buga, wannan munmunan mafarki ya tayar Ma da amra hankali sosai ba kadan ba, wanda a mafarki tana kallonsu salima amma ta Kasa taimaka masu don tayi nisa sosai don ko muryarta salima bataji saidai ita tanajinta sosai saida taga salima Ma ta mutu yasa ta kwala karar data sanya ta Tashi itama afurgice, zufa ne ke tsatsofi mata Sai hawaye kamar famfo, Duk ta burkice Sai addua kawai datazo baki ta take kamar zautacciya, 
Amar wanda bai dade da lumshe idanu ba bacci ya dan fisgeshi jin wannan razananniyar karar yasashi saurin miqewa ya sauko ya fito daga dakin, da sauri sauri ya karaso gaban parlor ganin ta zaune ta daura hannu aka tana rapka kuka ya sashi bin parlor da kallo, saida ya duba ko'ina don duk a tunanin wani abun ne ta gani dazai cutar da ita, takowa yayi har gabanta ya tsaya ya mata kallo daya hannayenshi nade a kirjinshi kallo daya ya mata ya kawar da kanshi kafin ya soma Magana cikin kakkausar muryar shi mai amo ''keeee ihun me kike yi a cikin daren nan, are you sure bakida matsalar kwakwalwa kuwa''… saida yakai karshe maganar tashi ya zuba mata kyawawan idanunshi masu kwarjini da haiba, jin saukar muryarshi ya sata dawowa cikin hayyacin ta, maimakon ta daidata saita kuma daburcewa ta guntse bakinta wani irin matsanancin kuka na ambaliya a fuskarta ta sukuyar da kanta, ''hey look up'' ya fada chan kasan makoshi, dagowa tayi Ta zuba mashi eyeballs dinta da sukayi jaa sosai gwanin ban tausayi, takawa yayi gaban kujerar parlorn ya zauna ya dora kafa daya kan daya yace ''zo'', anatse ta miqe, silk riga da wando ne na banci wanda suka lafe a jikinta masu santsi, wandon yayi mata kyau dukda bai dameta ba ammam yanda yake da santsi ya lafe a jikin fatar jikinta, kawar da idanunshi yayi daga kanta ganin yanda rigar ta shafe da kirjinta da babu bra sai tsayyayun bobby dinta wanda suke looking so puffy daga cikin rigar ga shatin nippy dinta dayayi tsini ta gaban rigar wanda kallo daya zakayi ma gaban rigarta zasuyi welcoming dinka, bai sake kallonta ba yace ''whats wrong with you, kinada matsala ne?'', shuru ta danyi tana share hawayen dake zubo mata masu zafi, wani irin radadi take ji acikin zuciyarta, bata ko kalleshi ba ta ahankali karamin bakinta wanda ya zubama ido ta soma Magana ''nayi mafarkin kanne na ne, sun mutu'', nazari ya soma yi kafin y ace ''mafarki gaskia ne?, girgiza kai tayi alamun ah ah, kafin ya cigaba ''da kikayi mummunan mafarkin meya kamata kiyi?,'' shuru ta danyi kafin ta soma Magana cikin shshekar kuka ''Addua'', jinjina kanshi yayi yace ''kinsan da hakan shine kika zauna kina yin ihu kamar bakida ilimi,ko ihun da kikeyi ne zai kawo maki kannenki?, I will warn you this is the last time hakan zai sake faruwa idan abu ya sameki, ba shirme zaki tsaya yiba, kukanki zaki kai wajen allah'', zuba mashi ido tayi wanda shma ita din yake kallo, wani irin sanyi ne a cikin maganganunshi wanda saika natsu zaka fahimci Magana yake cikin natsuwa da kamewa, share hawayenta tayi tass sannan tace ''in sha Allah bazan sake ba'', ''good for you'' yana kaiwa nan ya mike ya wuce cikin dakinsa ya barta anan tsaye, ganin kusan karfe hudu da rabi yasa ya shiga toilet kawai ya dauro alwala ya futa ya sanya farar jallabiyanshi mai kamshi ya tada kabbarar sallah, yana cikin salla ta shugo dakin itama ganin dakin da dan haske yasa ta wuce toilet din ta dauro alwala ta futo, bata kalli inda yake ba ta fuce zuwa parlor ta zurma hijab dinta ta fuskanci kibla ta fara gabatr da salla dakai kukanta wajen allah ta dade sosai har aka kira sallar asuba tana nan zaune bayan ta idar ta soma azkar, har wajen karfe takwas tana gaban sallaya ta kasa mikewa don gani take idan ta mike kamar zata rasa su ne gaba daya, tana nan kishingide har bacci ya kwashe ta mai nauyi sosai, daidai karfe tara ya futo daga dakinshi sanye da riga da wando na gyming, yana isowa parlor ya zuba mata idanuwanshi takowa yayi gabanta, tausayinta ne ya darsu a cikin zuciyarshi, baice komi bay a fuce daga gidan gaba daya, yana sauka ya wuce wajen parking ya dauki motanshi ya wuce penthouse din, don kwana biyu baijeba yayi motsa jiki shiyasa ya tashi da wuri. 89-90 Rayuwa juyi juyi wasu najin dadi wasu na cikin wuya, rayuwa dai ta gama juyawa su salima, don cikin wata uku abubuwa da dama sun samesu ciki kuwa shine azabtuwar da suka sha wajen rita, wadda ta gano wayan ta da salima ta dauka watannin baya da suka shude, yanda ta ganota kuwa akwai ranarda cutar salim tayi tsananin kamar zai mutu hakan yasa ta burkicewa ta zaro wayar hankalinta baya kanta ta nufi dakin rita arikice, tana zuwa ta fara dube duben charger ko zata samu, rita wadda futowanta kenan daga toilet din cikin dakinsu na masu aiki, idanunta ne suka sauka akan salima dake barbaza maka kayanta ganin yanda salima ta burkita mata katifarta kayyaakin data sato da yawa daga dakunan yan gidan duk sun zuba a kasa yasa ta dago kallonta ga salima, ganin tsohuwar wayrta a hannun salima yasa ta tako gadan gadan ta kwashe ta da maruka wajen hudu ajere, salima kuwa wadda yunwa ta gama busar da ita ta dago ta kalli rita, ganin yanda take kallonta yasa rita cewa ''ke dan uwarki barauniyace ke dama, kece kika sace min waya, to yau kuwa saina nuna maki ni cikakkiyar yar bariki ce mai lasisi, fadowa tayi kan salima saida ta mata dukan tsiya kafin ta kwace wayar ta hankadata gefe, dakyar salima ta rarrafa zuwa kofar dakinsu dukda bakinta bai mutu ba babu abin take cewa sai Allah ya isa, tun daga ranar rita ta dunga gana masu azaba, yanxu takaiga har line din wutar dakinsu gaba daya tasa mai gyaran wutar gidan wanda suke soyayya dashi ya kashe ta bangaren su salima, haka zasu kwana cikin zafi ga duhu, abinci kuwa yanxu kamar dabbobi haka take basu, wani sa'in zata zuba masu shinkafa banda miya ko mai haka zasu ci suna kuka, wani sa'in kuwa abincin da take diga masu ko salim baya koshi balle ita ta samu taci,duk wannan wahalar da suke sha basu taba attempting guduwa ba, to ko sun gudu ma ina zasuje? Duk wannan rayuwar da suke babu wanda ke lekensu daga yan gida gaba daya dukda yanxu suma abubuwa sun fara juya masu, don akwai wani tashin hankali da gaba daya gidan suka shiga wandalabarin kamawar ya Ibrahim ya riskesu na safarar mugayen kwaya da yake yi daga manyan kasashe daban daban, wanda haka ya mugun tayarma da dai hankali, ya kashe maqudan kudi sosai akan belin Ibrahim har ta kaiga ya sayarda gidan su salima don sunanshi ne akan takardun gidan as their guardian dukda sune masu gadon gidan, saida ya dauke wata uku a kulle duk ya jeme ya lalace yaci uwar wahala kafin alhaji Mustapha yayi yan cuku cuku aka samu aka fito dashi don da kyar aka samu aka danne zancen don case din yaje har gomnati kasar nageria don abin ya shafi sauran kasashe da taimakon wani abokin alhaji Mustapha babban general of police aka samu zancen ya kwanta don o su manyan government din bazasu so zancen ya fitaba don zai zame masu babbar matsala tsakanin kasashe da akeyin safarar don ayanda report din yazo daga Nigeria ake futar da kwayoyin meaning daga nan ake hadata da wasu sinadarai da anan Nigeria kawai ake samu haka zalika idan gomnatin kasashen suka gane zai iya jawo matsala sosai wanda gomnatin Nigeria bazata so haka ba kwata kwata. Tunda aka fito da ya Ibrahim aka fito da Ibrahim babu wanda yasan inda yake, hajiya kareema tayi kuka tayi magiya akan dadi ya fada mata inda danta yake amma fir yaki fada mata, karshe ma yace ta cire dan da ya jawo mashi bal'in da bazai iya saukewa ba daga duk kudin shi daga jerin yayansa, don ya sallama shi.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull