Kenza eBookz

Auren katin kasa complete - Chapter 12

Auren katin kasa complete - Chapter 12

Auren katin kasa complete Chapter 12: Auren katin kasa complete Chapter 12. Daidai karfe 4 na dare ta miqe daga kwance a furgice, wani irin juyawa cikinta…

4,432 words

Daidai karfe 4 na dare ta miqe daga kwance a furgice, wani irin juyawa cikinta ya fara, ciwon da bata tabayi ba a rayuwar ta, da sauri ta fado daga kan couch din ta doka uban kara ''wayyo allah na innalillahi zan mutu''..da wani irin sauri amar ya miqe, saukowa yayi daga kan gadon nashi, rigarshi dake yashe kan gadon ma baibi ta kanta ba, da sauri ya fuce daga dakin daidai ta kwalla wata uwar kara ajigace ''wayyo zan mutuuuuuu…'' da masifar gudu ya karasa gabanta yace ''keee kee whats wrong menene''..ganin idanunta na neman rufewa ya sashi dan bugun fuskarta yace ''heyyy heyy wake up fadamin whats wrong''…ganin this time around ba mafarki take ba shes really in pain wanda ya kasa ganewa mainene taqa maimai matsalar nata, da gudu ya tashi ya janyota jikinshi ya zauna kan couch yace ''heyy open you eyes, tell me whats wrong with you, ganin ta sandare ya sa gabanshi faduwa, idanunta duk sun kakkafe, da sauri ya janyota gefen kujerar ya miqe daki ya wuce ya bude clost ya jawo jallabiyanshi fara kal ya saka, ya jawo keys harya kusa futa ya dawo ya janyo wayanshi ya futo, a daburce ya fara dube duben inda ya kwantar da ita, har yazo gabanta shes still d same, hankali atashe ya cicibota ya gyara zaman rigar nata ya janyo hijab din da take luluba dashi ya rike a hannu don bashida time din sanya mata a jiki, da sauri ya fuce daka ciki gidan, tsaywa yayi gaban lift allah yaso dare ne babu kowa aciki haka yasa lift din na zuwa yasa kanshi ya shige, hannunshi har karkarwa yake, yana sauka yafito daga lift din ya wuce wajen da yake parking motoci, ahankali ya danna key din ya bude ya sanya ta a baya, da sauri ya gyara mata kwanciyar ya rufe kofar ya dawo mazaunin driver ya kunna motar yaja ta da gudun balain, tafiyar 30mins saigashi in 10mins ya iso babban asibitin abu dhabi, yana iso way a bude bayan motar ya cicibota, ciki ya wuce da ita kafin ya fara Magana cikin larabci, da sauri wasu nurses sukazo da gado ya daurata suka fara turawa, kallonta ya dungayi yanda take kamar matacciya, kallonsa doc yayi wanda ya karaso yace '' are you her guardian ?I need you to register her first before we that the check up''..da sauri amar ya tafi wajen registration don anan yake ganin doctor shi, saida y agama komi ya rubuta sunanta under nashi as ''mrs amar taura''….. saida y agama rubuce rubucenshi kafin wata nurse ta karaso gabanshi tace ''come with me''..binta yayi a baya har suka tsaya gaban office din doctor, baima tsaya yaji batunda ta soma yi mashi bay a kutsa kai kawai, zama yayi yana facing doctor din, anatse doctor ya soma mshi bayani ''we're glad you bring her as quickly as possible because she might have lost her mind, she's unconscious now but we help her to reactivate her body''..nunfasawa yayi ya gyara zaman glass dinshi ya cigaba da Magana ''she has highest level of appendix in her, which was cause by the clay sand or stones she has been taking into her system, so we have to operate her to get rid of everything that's causing her so much stomach pain, you don't have to worry shes going to be fine, but she has to be operated as soon as possible okay''…kallonshi amar yayi shifa baya gane duk wani abu da yake fada mashi, da sauri yace ''just do anything to save her please, money is not a problem''…yana kaiwa nan yasa kai ya fuce, a gaban theater ya zauna gaba daya kana ganinshi kasan hes not on his right mind hankali atashe yake, babu abinda yake sai tapping kafafunshi a kasa, karshe dai miqewa yayi tsaye yana zarya, kusan zaman awa guda yayi kafin a fito da ita, fuskarta tayi fayau, kana ganinta kasan bata da lafiya, an chanza kayan jikinta zuwa na asibiti, yar gown ce blue, kanta a daure da theatre cap, zama yayi har aka wuce da ita vip daki, ganin doc ya futa ya sashi dagowa ya dan miqe, kallonshi doctor yayi yace ''it's a successful operation but shes still unconscious for now, but she will be awake by 8pm''.. murmushi hammam yayi sannan ya wuce cikin dakin, wata nurse ce a tsaye akanta tana saka mata drip da wasu allurai, tana gamawa ta fuce, ahanakli ya tako yazo gabanta, hannunshi maqale ciki aljihun wandon jikinshi, ahankali ya daga idanunshi ya sauka akan agogon dake manne, ganin wajen karfe tara na safe ya sashi tunawa da baiyi salln subh ba, da sauri ya juya ya fuce saida ya tsaya yayi instructing nurse din da take duty akan ta kula da ita sosai kafin ya dawo. Gida ya wuce direct yayi wanka ya chanza kaya, nan ya zauna jiran m5 don ya saka shi ya karbo mashi abinci wajen Pablo a apartment dinshi, futowa yayi ya zauna a parlor, koina neat neat gwanin burgewa, idonshi ne ya sauka akan akwatinan ta guda uku data jera daga gefe, kawar da kanshi yayi gefe,jin karar knockin ya sashi tashi ya yi hanyar kofa ya bude, ganin m5 yasa ya bashi hanya don ya wuce, ahankali m5 ya shige ciki wajen kitchen island ya aje luxurious woody basket din daya shigo dashi wanda cike yake da hadaddun food flask masu kyau , saida suka dan gaggaisa kafin m5 yayi mashi sallama ya tafi, kallon abincin yake tunaninta ya fado mashi, yanxu idan yace zai tafi da abinci ba lallai ta samu taci ba don anyi operating nata, haka yasa ya hakura kawai ya bari daga baya idan ta buqata ko ta fara cin abinci saiya kai mata, yanxu wani irin tausayinta yake ji, yanajinta kamar kanwarshi wadda suka fito jini daya, kwata kwata baiji dadin abunda yayi mata ba, musammam yanxu daya samu information sosai akan abinda uncle dinsu yayi masu ita da kannenta, don har raping dinta da wahab yayi saida aka kawo mashi rahoton haka, da yanda Ibrahim yayi maltreating din salima da rashin lafiyar da kannenta keyi duk wani abu na gidan su a tafin hannunshi yake gasu marayu, runtse ido yayi yana jin wani irin zafi, marainiya ce, kannenta marayu ne don basu da gata akayi masu duk wannan abun, wani irin zafi yakeji aranshi sosai, don shi mutun ne da baya qaunar rashin adalci arayuwa. Abincin ya dan yi serving kanshi,anatse ya dan deba yaci, duk yanda yaso yaci abincin ya kasa, karshe ma turewa kawai yayi ya miqe ya koma daki ya kwanta, ahankali yake sauke nunfashi da huci mai zafi har bacci ya daukeshi, bashi ya farka ba sai wuraren karfe shida, wanka ya sakeyi sannan ya gabatar da salla ya shirya cikin farar jellabiya fes wanda ta amshi karkaffan surar shi sannan ya sanya jeans baki daga ciki dan jallabiyan tadan dingile mashi, rawanin larabawa ya nada sannan ya janyo keys dinshi da laptop dinshi ya futo.

Hafiza…………………… Hafiza ce zaune cikin dakinta, dukta hargize duk wani information data nema akan amar ta samu, abu daya ne ya tsaya mata arai, ta kasa samun wanda aka hadata dasu don su hada hannu, babu yanda batayi ba akan ta gano su amma ta kasa, karshe data gaji tayi masu message kamar haka ''ina son ku bani hadin kai, inada shaida akan amar na wasu laifi daya shafi kasar nan da yayi kuma ina fatan hakan zai kawo karshensa,I can be very useful to you, all you have to do is trust me kawai''… zama tayi kusan awa guda babu reply, ganin kamar tana batama kanta lokaci ne yasa ta wullar da wayar ta miqe, hafiza irin matan nan ne da ake kira green snake under green grass, zaata iya komi akan abinda take so, kuma zata iya tarwatsa duk wanda ya bata mata koda kuwa tana son mutun, wani irin mahaukaci so take ma amar wanda dalilin haka zata iya tarwatsa farin cikinsa akan ya bujire ma tayin datayi mashi akan soyayyar ta gareshi, tana da hatsari sosai.

Toilet ta shiga tana futowa taji karan notification da sauri ta karasa wajen wayan har towel din jikinta yana neman zamewa sbd sauri ,cikin hanzari da sauri ta bude message din ''call me now!!''.. da sauri ta fara dialing number, ganin anyi picking yasa ta sauke ajiyan xuciya ta soma Magana ''thank goodness, im so happy you pick my ….'' Ba'a bari ta karasa ba akace ''what do you have against him?''..shuru ta danyi tace I have something very big and it's a secret, that can also make him fall forever''.. ''just say it'' Da dauri ta soma Magana ahankali ''he got married with illegal actions, I mean he married some girl from his country that is not emirati, and he married her because she needs uae citizenship which he agreed knwing that its illegal and it can detroy his career''.. ''do you have written document or proof of what you said''. Da sauri tace ''no I don't that's the reason I need your hands in these, I have a plan, I need to be by his side I don't care about the fake wife but I have too cos that's the only way to I can get close to him, ta wannan hanyar ne zan samu duk wani proof da zamu buqata bayan wannan ma harda wasu abubuwan da bamuyi tsammani ba''…shuru akayi daga bisani mutumin yace ''I will contact you 2morrow morning, now send me about the plans''..yana kaiwa nan ya katse wayan, aje wayan tsohon yayi, wannan batun yayi mashi dadi, lokacin da yake ganin calls dinta baiyi tsammanin abun da zai mashi dadi bane, dariya yayi irin ta riqaqqun mugaye sannan ya dauka wayan shi yayi dialing wata number da akayi saving da ''my son''..ganin kusan yyi 2 mised call ba a dagaba ya doka wani ubantsaki yace ''useless boy, dole nasan yanda zanyi na juyaka yanda nakeso, anyways I don't knw how you will feel or react idan ka gane uwar ka na raye kuma tana wajena dukda tsahon shekarun nan ka daukeni a matsayin life savior dinka, hahahahaha''..wata shegiyar dariya ya babbake yace ''you will always be my uselful stick'' Yana nan zaune wani call din ya shigo wayanshi,saida ya dauka kusan awa guda yana yi wanda duk plans ne akan yanda zasu wargazar da duk wani shirin amar akansu wanda ya zame masu kamar threat acikin harkokinsu, ''alhaji calm down,every thing is under control, hes also under my control, just focus on the transportation over there, and we need more people for tracfikking, everything is low now, I need more badges from your country, that will help out, banason ina yawan zuwa sosai don ganin yanda abubuwan suke gudana acahn''…saida ya gama wayan kafin ya kashe.

Abu dhabi specialist hospital… Yana parking ya bude moton shi ya futa, direct ya wuce ciki, daidai dakinta ya tsaya kallon kofar yayi wanda na waje kan iya hango duk wani patient dake ciki tadan glass din gaban kofar da aka rubuta vip ward 2, ahankali ya bude ya kutsa ciki ya tsaya bakin kofar, kamar kullum fuskar nan tashi babu yabo ba fallasa,dagowa yayi yana fuskantar gadonta,kallonta yyi tsaf ganinta zaune jingine da gadon idonta a lumshe ya sashi karasawa gaban gadon dan nesa da ita, kallonta yake sosai, ahankali kamshinsa wanda bata taba jin qamshin dake shiga kwanyar mutun ba kamar shi ya soma shiga hancin ta yayi mata sallama, ahankali ta soma bude jajayen idanunta tar akanshi wanda suka dan kumbura eyelid dinta duk sun dan tashi tsabar kuka, wasu siraran hawaye ne suka zubo mata, lumshe idanunshi yayi sannan ya karasa ahankali gaban gadonta, ganinshi dab yasa ta rasa dalilin sakin kukan nata da karfi nan take, ahankali ya zaune gefen gadon, abun mamaki sai ganin hannunshi tayi yana tunkarota, ahankali yasa hannunshi ya janyota kamar yar babyn roba ya sanya ta cikin jikinshi, shi kanshi ya rasa dalilin hakan da yayi, kawai ya tsinci kanshi da yin hakan ne, fashewa tayi da kuka don kamar tunda yayi hugging dinta jikinta ya kasa resisting hug din don she needs it badly sosai, ahankali ya soma dabbing bayanta yana shafawa ahankali, saida ta soma rage kuka kafin ahankli kamar bazaiyi Magana ba yace ''how are you feeling now?'' ahankali ta zaro jikinta daga nashi, ta koma gefe, wani irin sanyi jikinta yayi ga wani irin dadi dataji ya ziyarce ta, kallonta yayi sannan yace ''kinci wani abun?''..ahanakli tace ''nurse tace I cant eat sai gobe''..runtse idanunta tayi don wani irin zafi taji sbd matsawa da ta danyin nan, da sauri yace ''sorry da zafi ko''…kawar dakai tayi tace ''uhm''…zama sukayi babu wanda yayi Magana, anatse tace '' sir please zanyi wii wii ''..yanda tayi maganan saiya burgeshi, ''should I help'' Bata kalleshi tsoron abinda zatace ya dirar mata tace ''no ka kira nurse''.. baima tsaya jinta ba ya dan rankwafo ya dauke ta gaba daya, gabanta ne ya bada dam, wani irin yanayi suka tsinci kansu, tsayawa yayi yana kallon cikin idanunta, itama kallonshi take kamar zasu cinye juna, kawar dakanta tayi, anatse ya matso da fuskarshi kusa da tata yace ''daga yau sunana yaya not sir, ''..girgida mashi kai tayi sannan ya kaita toilet, akan wc ya sauketa, ganin haka ya sashi saurin cewa ''zaki iya ko…'' da sauri tace ''please sir… sorry please ya…yaa, ka kira min nurse'' jin yanda ta furta yaya yasashi lumshe idanunshi yace ''okay'' ya fuce ya barta anan zaune, yana futa ya danna emergency button din jikin gadonta, da sauri akayi knocking, bude kofar akayi, nurse din ta shugo, kai tsaye yace ''help her out'' ya nuna bata bathroom din toilet din, wucewa nurse din tayi ciki, ganin haka yasa ya fuce, saida ya shiga cikin motar shi kafin ya soma dialing number hamman, ''dude whats'up?'', jin ya amsa kiran yasa amar saurin cewa '' call your girl friend, uhm this girl is in hospital'' Baima jira amsa hammam ba ya kashe wayan ya kunna motar shi ya fuce, ahankali moment din dazu ya fado mashi, dan tsaki yayi aranshi yace ''why would you do that yanxu sai raini ya shugo tsakani'', kawar da zancen yayi daga cikin zuciyar shi, wakar maher zain for the rest of my life yake bi anatse, dan cute bakinshi yake motsawa yana dan girgiza kanshi da alamu waqan na mashi dadi, jingina yayi da kujean nashi sosai, hannun shi daya na kan steary daya kuma na kan gear.

Hammam na gama waya da amar ya soma nazarin Magana amar,idan har ba mistake din jin abinda yace bane yana nufin amra bata da lafiya tana asibiti Kenan, da sauri ya soma dialing number haifa, tana dagawa ya soma Magana ''habibty I think amra is sick, I just received call from amar that shes in hospital I just hope..anyway where are you''..haifa wanda fitowanta Kenan daga kitchen dinsu hannunta riqe da bowl din fruit call din hammam ya shigo wayanta, da sauri tayi hanzarin picking bayan ta saurari abinda yace hankali atashe tace ''wait what, meya sameta, innalillahi, ina gida ynxu amma bari ya dauko key nan a futa yanxu na wuce asibiti''..tana kaiwa nan ta kashe wayan, fruit din da bata sha ba Kenan, da sauri ta haura sama ta jawo black veil din abayar jikinta ta sakko qasa, ganin ummi zaune a sitting room ya sata cewa ''ummi zanje asibiti yanxu, amra bata da lapiyar''..fatan samun lafiyar amra ummi tayi sannan sukayi sallama ta fuce, cikin sauri take driving har taqaraso abu dhabi specialist hospital, da sauri sauri ta fara kokari shiga cikin reception din, ganin hammam daga gefe wanda kusan lokaci guda suka iso yayi parking yasa ta dan tsaya ya karaso, atare suka qarasa cikin reception din, shida kansa ya bincika masu dakinta, mamaki ne qarara a fuskarshi lokacin da receptionalist din ta nuna mashi file din amra da shi kadai ne mai sunan ta a asibiti, ganin an rubuta mrs amar, kawar da wani tunaninshi yayi kafin suka wuce dakin amra wanda ke cikin vip na manya manayan mutanen kasar, da sauri haifa ta bude kofar batama tsaya knocking kofar ba, tsaya wa tayi turus ganin amra wadda ke kwance, da sauri ta karaso idanunta na kawo ruwan tausayi don haifa ciwo kadan tage gani ya sata kuka, da sauri ta karasa gabanta ta kamo hannunta tace ''babe, subhanallah meya sameki, karaso wa shima hammam yayi ya mata kallo daya ya danyi wani nazari kafin ya kawar da kasha don shima yanson sanin dalilin kwanciyarta a asibitin, amra wadda bacci yadan soma fuzgarta don allurer da akayi mata don tanata complain din zafi tun bayan futsari ta nurse ta taimaka mata tayi ya sa ta saurin bude ido jin muryar haifa, da sauri da budesu akan haifa wadda itama ita take kallo fuskarta qunshe da tausayin aminiyarta, dan murmushin wahala amra ta qaqalo ya riqe hannun haifa don ta taimaka mata ta zauna da kyau, gayara mata zama haifa tayi kafin tace ''babe calm down daga zuwanki harkin fara damuwa, I got operated and alhamdlh komai yayi sauqi''..jin haka yasa haifa bude idanunta sosai tace ''operated for what babe, meysa baki kirani ba, why'''…jin haka yasa amra saurin kwantar mata da hankali kafin ta kalli hammam, gaisawa sukayi wanda shima duk alamun damuwa sun fito qarara a fuskarshi, nan yabar haifa bayan yayi ba amra sallama sannan ya fuce abinsa. Kallonta haifa tayi tace ''waya kawoki asibitin''..kwanciyar amra ta gyara don baccin ya soma fuzgarta sosai tace ''haifa lets not talk about its now inajin bacci sosai''…ganin haka yasa haifa ta gyara mata blanket din jikinta cikin kulawa sannan ta zauna gefenta har bacci ya dauketa.

Hammam na futowa ya wuce apartment din amar don yasan nan zai samesa, yana karasawa bai tsaya komai bay a danna pins din kofar ya bude hankali kwance, ganin light din sitting room din are dim ya sashi karasawa cikin bedroom din kai tsaye, bude kofar yayi anatse ganin babu kowa aciki dakin yasa shi karasawa gaban couch din bedroom din ya zauna, jin karar saukan ruwa ya tabbatar mashi da amar na cikin bathroom din, ahanakli ya zaro wayan shi yana dannawa don jiranshi ya futo, dagowa yayi ianunshi suka sauka kan laptop din amar wanda ya daura shi kan table din gaban couch din wanda da alamu aiki ma yakeyi kafin ya miqe ya shige bathroom din, sauke idanunshi yayi ya cigaba da danna wayanshi, after some seconds ya dago idanunshi akaro ba biyu, idanunshi ne suka sauka kan portal din headquarters da tambarin uae armed force wanda gaba dayashi id encrypted, jinjina kai amar yayi don tunda yake bait aba ganin amar yayi using irin wannan portal dinba dukda usually idan manyansu na using wannan portal din saidai idan suna aje wasu manyan bayanai wand aba kowa yasan da irin encrypted portal dinba shima ganin tambarin uae armed forced ne ya sashi gane cewa tabbas wannan secret encrypted portal ne, jin karar kofa ya sashi kawar da kanshi ya kalli amar wanda ya fito qugunshi daure da farin towel wanda yakai mashi har gwiwa, dayan hannunshi riqe da wani towel din yana goge sajen gaban fuskarshi, kallonsa amar yayi baa bin mamaki bane don ya saba ganin hammam kai tsaya cikin bedroom dinsa, karasawa yayi gaban closet dinshi ya jawo wasu kananun kaya masu shegen kyau na nike black color, baiko kalli hammam ba kuma baice mashi komai ba shima hmmam bai tanka mashi bay a cigaba da dannan wayan shi don yasan halinsa, saida ya koma bathroom ya kimtsa sosai ya futo ya tsaya gaban katon dresser shi ya soma wankan turare, saida dakin ya dauke kanshin sa kafin ya saurara ya juyo ya karaso couch din, ''tun yaushe kazo''..jawo tlaptop din shi yay ya rufe sannan ya wuce gaban gadonshi ya aje kan bedside, dagowa hammam yayi sannan ya kalleshi yace ''banfi 5mins da zuwa ba,'' ''muje parlor muyi magana''. Wucewa amar yayi shima hammam ya mara mashi baya, zama sukayi akan kujerun parlorn, kallonshi hammam yayi sannan yace ''na kai haifa asibiti dazu, amma maisa da mukaje ban ganka ba''..tabe baki amar yayi ya jawo remote ya kunna tv kafin yace ''don't I have time for my self ne? uhmm, ay nayi kokari ma dana kaita asibiti''..kallonshi hammam yayi ya jinjina kai yace ''I tot you've done it already ay shiyasa''…sanin abinda hammam ke nufi sarai ya sashi doka tsaki kawai yace ''its not that simple, bana son raini, infact bana tunani zan iya yin wani abu da yarinya kamar wannan, shes too young and small for me, anyway banason maganan for now''..dariya kawai hammam yayi yace ''okay wannan matsalarka ce, idan har sauran ruwan naka ya qare kaine kake cikin matsala, tunda na kawo maka solution kana wasa da damar daka samu anyways take your time''..banza amar ya mashi ya maida idanunshi kan tv da ake wani program, shuru ne ya biyo baya, ganin yau da yan miskilancin nasa ya sanya hammam miqewa ya mashi sallama ya fuce abinsa. Bai wani jima a zaunen ba yaji zaman ya ishesa gaba daya, daki ya koma ya rage kayan jikinsa zuwa shorts kawai sanan ya dan kwanta. 83-84 Abu dhabi hospital 5pm… Hira sukasha sosai ita da haifa bayan ta tashi daga barci allah ya taimaka jikin nata ya dan sake sosai, don tana iya tashi tana zagaye dakin don doctor ta umurce ta da hakan. Yau kusan kwana biyu Kenan tun bayan haifa tazo ta duba ta, yauma tana saka ran ganinta don sunyi waya akan zatazo da ummi don su dubata, bangaren amra kuwa ba qaramin dadi taji ba da baya zuwa don rabonta da ta ganshi tun ranar da akayi mata operation da safe bayan yaje ya dawo bai sake zuwa ba itama kuwa bata damu ba don babu abinda ta rasa anan asibitin daga kan meals dinta zuwa abubuwan buqata duk tana samun kulawa daga wajen nurses din ga haifa tana zuwa itama don ganinta. Anatse ta jawo walking stick din dake taimaka mata wajen tsayuwa, saukowa tayi daga kan gado anatse sannan ta saka cute slippers din da ake ajewa patients, gyara riganta tayi wadda ta dan karkace gefe guda sannan ta futo, ahankali take takowa har gaban compound din asibitin, wata irin iska ce mai dadin gaske ke busowa don garin yayi lumlum sakamakon danshin ruwan da akayi nay an kwanaki, anatse take zagayawa har ta dan samu waje ta zauna don jin yanda kafarta ta sage sosai, zaman minti goma tayi bayan ta huta sannan ta sake miqewa, tafiya takeyi ahankali hart azo gab da tsakanin parking space da inda zai sadaka da entrance din asibitin, anatse kamshin turarensa ya fara bade surrounding din wajen, anatse ta dan juyo ganin babu alamunshi a wajen yasa ta soma tafiya anatse ba tare da ta juyo gabanta ba, juyar da idanunta tayi gaban hanya wanda yayi daidai ta bugewanta da glass door din entrance door din cikin asibitin wanda ake turawa, da sauri tayi baya don taji zafin bugun ba kadan ba wanda dalilin yin baya yasa ta harde kafafunta, saura kiris ta zube a kasa, amar kuwa wanda tun lokacin da ta miqe daga zaune a compound din ya shigo cikin asibitin da hadaddiyar lamborgini dinshi, futowa yayi daga motar sanye da jellabiya fara kamar kullum fuskanshi sanye da bakin glass wanda yake boye mashi kamannin sa sosai, kallonta yayi sosai da yanda take dingisa kafafunta har lokacin data juyo tana waige waige, saida ta fara tafiya kafin ya mara mata baya ganin ta buge da kofa ya sashi tsayawa ya hade hannayenshi biyu a kirjinshi yana jinjina yarinta irin tata don babu babba mai hankali da zai dunga tafiya yana waige waige ba tare da kallon gabanshi ba ganin tayi tangal tangal zata fadi ya sashi saurin tahowa da sauri ya tarota zuwa jikinshi sosai, anatse ya lumshe idanunshi don jin yanda jikinta gaba daya ya sauka ajikinshi, yanayin ya bada wani irin sanyayyan alamari, ga sanyin dake kadawa, ganin idanuwa na dawowa kansu ya sashi dan janye hannuwansi wanda ya zagayo qugunta dasu duka biyun, kamar bazai cireba ya janyeta daga jikinshi sannan yace ''mind your step, kidinga abu kamar mace mana''…amra wadda salati ya kama bakinta tun lokacin data saddakar da faduwar ta, jin muryarshi wadda ko acikin bacci taji take wani mummunan farkawa don tsoronshi da kwarjini da haibarsa yasata saurin karasa sanye jikinta daga nashi, sauke kanta qasa, giftawa yayi ta gefenta, ganin haka yasa tabi bayanshi har zuwa dakinta, saida ya bude kofan sannan ya mata kallo daya yace ''get in''..wuceshi tayi sannan ta samu waje ta zauna akan gadonta, jin alamun takowan shi wajenta yasata sauke kanta kasa ta runtse idanunta saida yazo dab da ita sannan ya tsaya kyam ya fito ainahin sojansa, hannunshi biyu ya sanya cikin aljihun jallabiayn jikinshi wanda tayi mashi kyau sosai, kallonta yayi daga yanda take zaunen sannan ya dan furta ''get up''.. da sauri ta miqe har kirjinta na nemen bugawa da nashi, dan baya kadan yayi sannan yace ''dago kanki''..dagowa tayi anatse tayi mashi kallo daya, yanda idanunshi suka cika idanunta ya sata saurin sauke kanta qasa don bazata jure kallon cikin idanunshi ba ''don't make me repeat my self''..jin ya yi Magana adan zafafe ya sata dagowa da sauri amma bata hada ido dashi ba don bazata iyaba, anatse ya soma Magana ''bakida tarbiya ne? baki iya gaisuwa bane ko sai nace ki gaisheni'' jin yanda yake Magana adan fada fada ya sa jikinta fara rawa kaf kaf, anatse cikin sautin alamun kuka ya ciyo ta ya sata saurin cewa ''dan Allah kayi ha..kuri.. sir..''.. Kallonta yyi sosai saita dan bashi tausayi, anatse ya dan rankwafo don kwata kwata tsayinta a daidai kafadar shi ta tsaya,ganin yanda ya rankwafo sosai don har tana jin saukar nunfashinsa wanda ke kamshi mint ya sata saurin runtse ido, so take ta sauke kanta amma ta kasa don tsoron kar yace wani abun, don kwata kwata maganganunsh akanta basuyi mata dadi kwata kwata, ''didn't I warn you from calling me sir..'', da sauri ta kalleshi tadan tabe bakinta ashgwabe tace ''yi hkuri manta wa nayi''… matsawa yayi ya taka har gaban couch din dakin cikin izza da kamewa sannan ya zauna anatse ya daura kafanshi daya akan daya kamar basarake, dauke idanunshi yayi daga kanta sannan yadan kwantar da kanshi jikin kujerar ya lumshe idanunshi, tunda ya zauna ya dauka wajen rabin awa a zaune bai motsa ba, ganin bashida niyar tashi ya sata kame kanta tadan kwanta har bacci ya dauke ta. Shima dai baccin ne yadan fusgeshi kadan daga bisani kuma ya farka.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull