Auren katin kasa complete - Chapter 15
Auren katin kasa complete Chapter 15: Auren katin kasa complete Chapter 15. Akwai wata ranar asabar tana zaune kusa da salim wanda ya jeme ya rame kamar…
5,156 words
Akwai wata ranar asabar tana zaune kusa da salim wanda ya jeme ya rame kamar wanda yayi shekaru yana jinya,saboda ciwon zuciya dayake fama dashi tun bayan rasuwar iyayenshi don yanxu har ta kaiga baya iya Magana sannan abu kadan ke furgitashi koda kuwa karar kofa ne sai ya zabura ya kankameta ya fara kuka, ayanxu kam ta fawwalama allah kawai don rayuwar su ta gama tagayyara, babu makaranta, babu gata, babu walwala, babu cima mai kyau sai rama da rayuwar kunci,itama kanta ciwon cikin da take ya gama maidata kamar mahaukaciya don duk dare saitayi shi, kallon salim tayi wanda ya maqalqaleta sosai a jikinta yana futar da wani irin nunfashi dakyar, tun safe yake wannan nunfashin wanda daga jiya zuwa yau ya chanza daga nunfashin da yakeyi, shafa kanshi tayi ahankali tace ''Allah ya baka lpy salim, allah yana tare damu, nasan yana kallonmu kuma yana jinmu kuma zai kawo mana dauki insha allah'', haka ta dunga surutanta ita kadai don baya iya Magana shi, ganin lokacin sallah yayi yasa ta kwantar dashi gefenta kan carpet ta miqe ta wuce toilet dinsu, gaba daya toilet din ya fita hankalinshi yayi wani irin dauda saboda baya samu gyara daya kamat da omo don rita ta daina basu koda sabulun wanka ne, fanfon toilet din ta bude wanda shima tsatsa tasa kan famfon ya balle saidai ruwa yana bulalowa idan aka kunna ta gefen wajenda bai balle ba, alwala ta dauro sannan ta fito ta jawo hijabinta wanda dauda tasa ya kode don kayansu ma ba samun wankin arziki yake ba saidai ta dauraye masu da ruwa zalla idan dattin yayi yawa sosai, tana idar da sallah ta miqe ganin yanda salim ya takure yana rawar sanyi da sauri ta arsa gabanshi ta tallabo shi sosai izuwa jikinta ta daura shi kan gado wani irin tari ya soma yi kamar ranshi zai futa, zama tayi gefenshi tana mashi sannun, ganin tarin yadan lafa yasa ta gyara mashi fuskarshi daya toge da gadon, tana zare hannunta idanunta ya sauka akan jinin dake Malala daga tafin hannunta, kallonshi tayi da sauri, jikinta na bari ta soma furta ''innalillahi wa inna ilaihi rajiun'', kai salim tashi mene, wannan jinin na mene''..afurgice ta janyoshi sosai don ganin daga inda jinin ke futa, kurama fuskarshi ido tayi bakinta na karkarwa '''na shiga uku salim, me nake gani innalillahi wa inna ilaihi rajiun'', jijigashi ta soma yi ammam ina kamar nunfashinsa ya tsaya, da sauri ta miqe ko ganin gabanta batayi wani irin juyawa da kanta keyi yasa ta kwala ihu ta fice aguje, har tsakiyar parlor rabonda ta fito harabar wajen harta manta, kallon ta daya bayan daya waenda ke zaune a parlor sukeyi, ya Muhammad wanda daga ya Ibrahim saishi wanda saukarshi Kenan kowa yazo tarbarshi don tafiya yayi ma tsayi sosai don ya shafe shekara kusan bakwai rbonshi da gida, su hajiya kareema da yayanta, khady dasu amina da jabir da jalal kananun duk suna zazzaune suka juya jin wani irin wari na doso parlorn, kallonta ibrahim yayi wanda shima warin jikin nata ne ya mashi iso zuwa hancinci anatse ya soma Magana cikin kamewa da nutsuwa sannan ''mummy ina kuka samu masu tabin hankali a ckin gidan nan, kudai da kwashe kwashen yan aiki'', tabe baki haj kareema tayi tace ''yar badaru ce fah'', gwalo idanu yayi yace ''wani badarun?'', bata bashi amsa ba ta miqe ta haye sama abinta bayan ta tattara kananun yayanta suka wuce sama,don kar warin salima ya cutar mata da yaya. Kallonta muhammad yayi da kyau sai a lokacin shima ya wani tuna da yayan kawun su daya rasu, hankali atashe ta dora hannu aka a fara sambatu, kallonta yayi lokaci guda ya fuskaci bata da lafiya don karatun likitanci da yayi, ''keee ki nutsu'' ya dan fada da karfi, juyawa tayi idanunta na dishi dishi ta kalleshi don bata shaida fuskarshi da sauri ta karasa gabanshi har yana dan matsawa gefe ta durkusa tace ''dan allah ka taimaki dan uwana zai mutu na shiga uku'', saida tayi Magana ya tabbatar ba mahaukaciya bace da yayi tsammani ''ina kanin naki'', da sauri ta miqe tace ''yana daki hancinci da bakinshi suna fito da jini, da sauri ya miqe tayi gaba ya bita abya suka shige dakin, wani rin kura da datti asa shi toshe hancinsa, da sauri ta yaye labulensu wanda yaji jiki sannan ta nuna mashi salim dake kwance kamar gawa har jinin ya fara bushewa akan gado, da sauri ya karasa gaban gadon ya taba wuyanshi don neman pulse dinshi, jin yanda pulse dinshi yayi weak sosai ya sashi tsayawa akanshi sosai cikin yan mintuna pulse din ya tsaya, shuru ya mhammad yayi yace ''I thik hes gone'', salima na jin haka wani irin hajijiya tahau kanta, atakae a wajen ta anke jiki ta fadi itama wanwas, akidime Muhammad ya mike yana kallonta da kanin nata, da sauri ya karasa gabanta jin pulse dinta yayi weak hankalinshi ya tashi da sauri ya mike ya fuce daga dakin, yana zuwa daidai hanyar futa ya kwala ma masu gadin gidan kira da driver daya daukoshi daga airport da gudu suka karasa cikin yayi masu jagorar cikin dakin tare da masu nuni da yaran yace, ku futo dasu akaisu asibiti, mai gadin baba dan ladi wanda shima rabon da ganin yaran kusa shekar biyu Kenan, don tun yana tunanin suna gidan har yazo ya yarda da zancen hajiya kareema na cewa duk wanda ya nemesu ace basa nan, da sauri suka sungume su, Muhammad na biye dasu aka saka su cikin motar daga salim din har salima, da sauri driver ya shiga gaba shima Muhammad ya shige baya gaban owner coner suka ja motar suka fuce daga gida, duk wannan akan idon hajiya kareem wadda tun daga window dakinta take hangensu, karshe ta tabe baki tace ''zaka dawo ka sameni ne, sometimes I wonder ko nina haifeka, don jinina bazai tsaya bata lokaci akan walqantattun yayan nan ba,''…. Cikin wani babban private hospital suka tsaya inda nan ne muhammd sai fara aiki, yana karasawa ciki ya miqa id card dinshi a chan kasar daya baro as professional health personel receptionalist din na ganin sunanshi ta kira nurse da babban likitan dake duty aka dauko gado suka wuce waje, yanda aka kwasosu daga gida haka nan suke kwance babu chanji, da sauri nurses din da taimakon driver aka fito dasu aka kwantar akan gadon aka shiga dasu cikin emergency, Muhammad kuwa office dinshi ya wuce wanda aka tanadar mashi tun kafin a iso kasar don part time job zaiyi a cikin asibitin kafin wasu yan watanni ya koma jordan don achan yake aiki, agajiye yake ga gajiyar tafiya ga wanda ya tarar a gida, mamaki ne ya cikaci sosai, nazari ya fara ya akayi yarannan suka wulqanta haka, bayan lokacin daya tafi ma suna kananu sosai cikin gata, kuma lokacin iyayen sun a raye, do mutuwar kawun nashi ma bai sani ba sai bayan yan shekaru cikin Magana daddy ke fada mashi, runse idanunshi yayi tausayinsu na ratsa shi. Dakyar likitoci suka samu nunfsashi salima ya dawo, kafin suka fara bata treatment sosai, karshe dai harda operation aka kare ayi mata don hantarta guda daya ta lalace saida aka cire, salim kuwa sun dauka kusa awa shida ana fama, dank iris ya rage zuciyarshi ta buga wanda hakan yasa komai ya tsaya chak ajikinshi, wannan dalilin yasa Muhammad yayi tunanin yam utu don baisan yana da ciwon zuciya ba, shima dai saida aka kare da operation an samu komai ya daidaita saidai kuma ya fada coma. Hankalin ya Muhammad ba karamin tashi yayi ba lokacin da manya manyan likitocin da sukayi operating dinsu suka mashi bayanin matsalolin yaran, wato bayan ciwon zuciya da ya salim ya kamu dashi wanda yanda tayi mashi mugun kamu don gab take da bugawa a kananun shekarunshi da ciwon kidney da salima take dashi wanda itama badan an cire wanda ta lalace dinba zai jawo dayan da ya rage mata yayi affecting, hankalinshi ba karamin tashi yayi ba, wani irin tausayi suka bashi kamar ya masu kuka don duk gidan bayan ishaq saishi waenda suke da tausayi da jin qan marayu duk yaya alhaji Mustapha. Daga asibiti ya barsu cikin kulawar likitoci da nurses din dake da duty din daren ranar, sai wajen karfe takwas yabar asibitin ya wuce gida direct, yana isowa bai tsaya ko'ina ba sai bangaren sun a samarin gidan, dakinsa ya wuce wanda yake kusa dana wahab, shiga yayi ciki ko'ina fess fess, kayan jikinshi ya rage ya wuce toilet don yin wanka, saida ya tsaftace jikinshi kafin ya futo ya wuce bakin gadon sa, saida ya kira asibitin yaji yanayin lafiyar su kafin ya aje wayan, sallolinshi da ake biyanshi ya rama, yana idarwa ko abinci bai nema ba don baya jin zai iyaci don wani irin bacci yakeji sosai. Haka hajiya kareema tayi zaman jiranshi har kusan karfe goma bai leko bangarenta ba ganin haka ta yanke shawarar neman shi washe gari, damuwa tayi mata yawa, business dinta yana neman yin kasa sbd itama saida ta fitar daga cikin savings dinta wajen fitar da Ibrahim.
Washe gari karfe goma ya ibrahim ya shirya fess cikin manyan kaya jumper skyblue, yana gama shirinsa yafuce daga gidan don da alamu yawanci babu wanda ya tashi sai rita dake kai kawo na abinci tana leken shi kamar munafuka aranta tace ''chineke, this guy fine dieee, ahhhh'', baima san da mutun a wajen ba ya futo wajen garage din motocin gidan ya kira haladu driver daya kaishi asibiti jiya, suna gab da juya kan motar zasu fice motar haj labiba ta danno kai, yana ganin haka yasa ya tsaida driver ya sauka, domin su gaisa, tana ganinshi cikin fara a ta futo daga bayan mota, takowa yayi har gabanta yace ''good morning mummy, na sameku lpy'', cikin fara'ar ta ta amsa mashi tare da yabon shi don duk gidan babu wanda ya kaishi daraja na gaba dashi ba kamar sauran ba, wucewa tayi daman tafiya ce ta taso mata zuwa niger don abbanta dake jinya tsawan wata Kenan sai ayanxu kannenta suke fada mata ganin kamar yana gab da rasa ranshi kuma yana nemanta, bayan tace airport dinne jirginsu yayi delay har ta kaiga akayi cancelling flight din saina karfe biyar shiyasa ta dawo gida kawai, tana hawa sama ta wuce dakin hilma don ganin kota tashi don da safe ta shiga dakinta taga tana barcinta hankali kwance, ganin baccin take hankali kwance yasa ta wuce dakinta tana mamakin yawan baccin da hilma takeyi yanxu, gashi yanxu sun shiga 100 level amma kota kota taqi maida hnaklinta wajen yin karatu yanda ya kamata, Ibrahim kuwa bayan wucewar haj labiba ya wuce cikin mota haladu ya danna horn driver ya wangale masu gate suka wuce da gudu, malam audu na rufe gate ya koma kan bencinsa da yake zama a bakin gate a waje yana shan iska, nan yan abokanan sa suke zuwa susha hira suna tsaida masu talle suna sayan gyada da rake, malam audu irin masu gadin nan ne da tsegumi baya wuce bakinsu, yana nan zaune abokinshi iliya ya karaso kamar kullum hannunshi rike da ledar shayi da burodi harda soyayyan kwai da yake sayo musu suna ci, ganin shi yasa mlm audu wangame baki yace ''ah ah abokina iliya, yauma ganimar zamu kwasa, kaidai baka gajiya da hira, kullum saikazo hira,'' dariya wanda aka kira da iliya yayi ya zauna gefen bencin suka gaisa kafin audu ya dakko masu kofi suka rama shayin suka kora da burodi da kwai saida sukaci sukayi nak kafin audu ya soma Magana ''kai abokina wallahi mutanen gidan nan basu da Imani ko kadan'', da sauri iliya ya soma maganar irin ta mutanen da sukayi zaman legas don kwata kwata ba bahaushe bane amma zama da yan arewa yasa hausa ta zauna radau a bakinshi, kallonshi iliya yayi kamar wanda yake jiran zancen yace ''mazaa ya akayi bani labara maisa kace haka don ni ina ganin masu gidan nan kamar sunada mutunci''..tsaki kawai audu yayi yace ''wallahi a fuska ne amma waennnan da kake gani mugaye ne na karshe wallahi, nan ya fara bashi labarin yanda suka shiga dakinsu saluma suka gansu kamar gwawawwaki da irin bakar wahalar rayuwa da suke ciki, kai karshe harda rayuwar da su amra sukayi tun farkon zuwan su har zuwa lokacin da ta tafi karatun har labarin fyade itama da wahab ya mata da yanda itama salima Ibrahim yaso yi mata amma allah ya kubutar dasu da yanda alhaji ke wulaqantar da rayuwar su kamar ba yayan qaninshi ba, sannan ya kora mashi da hakkin yaran bazai bar alhaji mustapha ba da iyalanshi don tun a gidan duniya shima iyalanshi sun fara shiga cikin babbar matsala gashi yanxu an kama danshi dake safarar miyagun kwayoyi zuwa manya manyan kasashe daban daban har kawo yanxu babu wanda yasan inda yaran yake yana kaiwa karshe iliya ya karbe da ''kai amma mutanen nan anyi azzalumai, allah ya saka masu, dana dam babu tabbas, duk wannan abun ace yayan dan uwanka jininka don kasa ta rufe mashi ido shikenan sai jinisa da ya kamata a basu kyakyawar kulawa su ake walaqantarwa, yana kaiwa nan ya zaro wayarshi ya danyi yan latse latsen shi kafin ya miqe yace ''to abokina sai gobe idan na dawo, Allah ya basu lpy akwai aikin da zanje nayi, kasan talaka bawan allah saida nema''..yana kaiwa nan sukayi sallama ya wucewarshi. Iliya na wuce hanyar gidan ya cire mustache din daya manna a gaban bakinshi ya cizge gashi daya manna cikin facing cap, wipes ya zaro ya goge yan pente pente da yayi ma fuskarshi saida y agama ya dago kanshi, wani mutumin ne daban ba iliyan da audu suka sha hira dashi ba, wannan kana ganinshi kaga tantiran yan legas, kanshi ma sol yake babu digon gashi, wayarshi ya daga yayi yan typings sannan ya tura komai da yayi recording lokacin da suke Magana da audu da duk wani information daya samu daga wajen shi,yana sending ya tari mai mashin ya wuce abinshi.
Kano private hospital…. Muhammad na isa asibitin da kanshi yaje ya duba su, bakamar jiya ba har sun dan marmare don kuwa salima harta dan watsake saidai itama bata farfado ba amma an gyara ta, an wanke kanta dake da muguwar dauda har waka saida nurses suka mata a kwance, shima salim an gyara shi saidai shi yayi wani irin haske kamar gawa jikinshi yayi wani irin sandarewa don har lokacin bai yana coma, ammma ana fatan ya tashi anytime soon, anan asibitin ya wuce shida ya kamat ya fara aiki Monday sai gashi yayi reporting tun ranar friday, wunin ranar shine ke dubasu da assistant dinshi, every 2 hours saiya dubasu har aka cire drip din salima sai jiran farfadowarta ita, Karfe tara daidai na dare ya koma gida agajiya, saida yayi wanka ya saka jellabiya ya rama sallar da bai samu yayi ba kafin a wuce dakin mama kareema, yana shiga tana zaune gaban gadonta ta rabka uban tagumi, gefen khady ce wadda take ta rafka uban bacci kamar wadda tayi maye, abugen take saidai karyar data zagba ma maman nata na cewa ciwon kai takeyi wanda ya jawo mata jin juwa akanta, tana nan zaune har barci ya kwashe don tayi high sosai, haj kareema wanda tunanin duniya ya mata yawa na rashin Ibrahim yasa batama gane cewa khady a buge take ba, saida tashi muryarshi kafin yta dawo nutsuwarta, ''mama is everything okay?akwai wani abu dake damunki ne''…gyara zamanta tayi tace ''daga ina kake tun safe muhammad''…atakaice yace ''naje asibiti'' na dauka sai Monday zaka koma duty maisa ka koma yau?,…''inada patients ne shiyasa na fara yau''.. nunfasa tayi kafin ya sake kallonshi '' yayan badaru kakai asibiti ina yayan badarun suke, waima tukunna ina ruwanka Muhammad da rayuwar wasu,'', mamaki ne karara dauke a fuskar shi don baiyi tunanin ta haka zatayi tambayar ba ya dauka zata tambayi ya lafiyar dasuke ciki, jinjina kanshi yayi aranshi yace ''lallai akwai matsala, what going on in this house meke faruwa ne'', bai amsata ba yace ''mama abinci fa, 'im hungry,'', ganin bai amsata ba yasa ta bar zancen kawai don batason karama kanta matsala kan wadda take ciki ta rashin jin labarin Ibrahim kamar an shafe babin rayuwar sag aba daya, abinda yafi damunta yanda dady ya nuna bai damuba kwata kwata. Anan yaci abinci sukayi sallama ya koma dakinshi ya kwanta abinshi. 90-91 Dubai uae….. Satinta biyu da dawowa daga asibiti ta koma office inda suka samu zama sosai ita haifa wanda sun kwana biyu sosai basu hadu ba, murna sukeyi sosai dan yanxu aiki ne sosai a gabansu ita da haifa, don yanxu har time din tashinsu ya chanza daga 4 zuwa 5:30 wanda general ne ya chanza haka, oga kwata kwata sir general amar Kenan, tun bayan sun koma aiki ganin juna ya zame masu abin wuya don ita dadin haka take ji don yanxu ta koyi kama kanta bata shiga sabgarshi sannan tana kokarin danne tsoranshi da take ji idan ta ganshi, babu abinda ke hada ta dashi sai gaisuwa bayan wannan kuwa ko kallo basu damu dayi ma juna ba, yanxu tayi settle da zaman apartment dinshi harta saba, wataran idan ya fita baya dawowa ma saiya kwana biyu uku har biyar bainshugo ba kuma bata damu da hakan ba don kowa rayuwarshi yake, duk lokacin office kuwa baya neman ya rage mata hanya itama kuwa bata buqatar haka kullum da safe tana shiryawa zatayi requesting ride azo a dauketa ta ta wuce lokacin tashi nayi ta dawo, yanxu kusan watansu daya da komawa office kuma duk wata saitaje ta diba blood sample dinshi kamar yanda ta saba a baya anan ne ma kawai take samu ganinshi a office, cikin headquarters kuwa few mutane sukasan oga general yayi aure don yawanci daga asibiti ne gossip din ya fara wanda haifa ce ta haddasa shi kuma tayi hakan ne da gayya don idan anzo investigation ko an biyo ta hanyar headquater za a samu shedu cewa akwai aure tsakanin sir general da intern amra, tun gossip din na damu amra har yazo ya daina damunta, yaxu haka ma wasu basa kiranta yanda suke kiranta ada wato intern mss badaru saidai ma, ko'ina ma tun tana dauke ido harta saba ahankali ahankali gossip ke shigewa har cikin headquarters wanda yawanci daga ma'aikata mata wanda suke kishi da ita don general ya zama kamar secret crush din kowa harda sojoji mata dake cikin headquater zuqa zuqan mata kyawawa sosai, ayanxu hankalinta yadan kwanta sosai don aiki takeyi sosai har allah allah take su gama haousemanship ta koma school ta karashe duk wani abunda zatayi daya rage mata don ta samu tabar kasar dukda har yanxu tana kwadaituwa da samun katin kasar don yanxu fargabarta day ace, kudin da daddy yace zata biyashi, don ayanxu ya daina tura mata upkeep daya saba dole saida savings dinta take amfani, yawan idan damuwar tayi mata yawa in haifa ta lura da ita tayi mata tambayar menene matsalarta saidai ta boye mata don haifa tayi mata abubuwa da dama wanda ahakan ma tana gode mata. Yau watan auren su biyar cur, wanda kullum cikin lissafi take don tun bayan da suka cike form din citizenship da take nema tun farkon watan auren har yanxu shiru ba a nemesu ba, ganin haka yasa duk suka sakankance itada shi, itadai burintaa kawai ta samu katin kasar inhar kuwa bata samu ba harta karasa makaranta tofa zata tafi ne kawai don bazata zauna ba, zaman shekara uku da tayi duk tayi shi ne cikin kunci da zulumin halinda kannenta suke ciki. sati guda Kenan rabonshi da gidan wanda hakan yasa ta sake sosai tana tashi daga bacci ta wuce dakinsa kamar koda yaushe idan baya nan haka ta gyara mashi dakin fess fess saidai a kiyayi hannunta daga taba mashi duk wani abubuwan amfaninshi, har wani haushi take ji idan yana kafafa akan taba mashi abubuwan, da yanda yake magan ''yen yen yen don't you dare touch my belongings amma ya iya barin abokinshi ya shugo dakinshi dukda baya nan, ta gama fadi tana tabe baki bayan ta kwaiwayi yanda yake Magana da gunguni irin yanda yake Magana, tunawa da yanda hammam ke zuwa gidan cikin yan kwanaki dukda yasan cewa baya gidan kuma ta fadi mashi amma haka zaizo ya wuce dakinsa ya dade kafin ya futo ya mata sallama ya wuce, akwai ranar da yazo ya kafeta da wani irin kallo wanda samm ta kasa gane ma'anar kallon karshe ma dai miqewa tayi ta koma kuryar kitchen ta zauna tana dafa abincin da bata shirya ba nan ma bai kyaleta ba har ta gaji ta juyo tace mashi ''uhm bana tunanin yanxu zai dawo amma zaka iya tafiya gobe saika dawo koka kirashi kaji idan zai dawo anjima saika dawo'', murmushi kawai yayi still yana kallonta yace ''okay alllah ya aimu goben'' yasa kai ya fuce, ..bata son kawo wani tunani aranta don tasan yanda haifa ke qaunar hammam sannan bata son yi mashi muguwar fassara shiyasa tabar maganar a cikin ranta, washe gari ma dai ya dawo kamar yanda ya saba kai tsaye ya shigo byan ya danna pin saijin budewar kofa tayi don ko knocking baya yi, azaune ya tadda ta saida suka gaisa kafin ya wuce dakin amar still yasan cewa baya nan, zama tayi tana tunani idan zata kirga yau kwana biyar Kenan yana zuwa ajere sannan da salo daban daban saidai ta hana kaanta da mashi mumunan fassara don tare ta gansu kuma taga yanda suke tsakanin su, dukda haka zuciyarta azalzaalarta take amma ta dage ta hana kanta yin abinda zuciyarta ke saka mata na ta shiga cikin dakin taga me yake gudun sharrin shedan gashi dagashi sai ita a gidan yasa taki zuwa duba me yake yi acikin dakin hakan yasa tayi zamanta harya futo bayan 30mins da shiganshi sannan yace ''uhm zan tafi na jira bai dawoba, if ya dawo ki fada mashi nazo''..cikin harshen larabci ya gama kafin sukayi sallama ya fuce, yana fuce ta shige dakin, da safe ta share dakin so zata iya tantance idan akwai abinda aka sauya mashi guri, ganin duk inda ta gyara daga gadonshi zuwa tsakar wajen yasa ta kawar da zancen kawai har zata fuce ta tsaya ta juyo ta zubama gefen bedside dinshi ido tachan dayan barin gefen gadon, takowa tayi har gaban wajen kafin ta tsaya, idanu ta kurama wajen wanda files ne nashi da laptop dinshi wanda yake yawan ajewa a gidan, hannu takai wajen daidai kan laptop din kafin kuma ta dauke hannunta kawai don tuna gargadinshi akan kayanshi amma tana mamaki don kamar da tayi gyaran gado ta danyi goge goge ba a juye ta hango laptop dinba ganin ta kasa gane komai yasa ta juya kawai ta fice. Firgigif ta dawo daga dogon tunanin hammam da chanji da ta gani daga wajen shi dukda ta tsame kanta kuma babu ruwanta, hakan yasa ta wuce cikin toilet saida ta gyara fess kafin tayi wanka ta mulka mayukanta wanda ta kwaso su da sabulanta da skincare dinta duka, mulka scrup din tayi a jikinta sannan ta wanke kanta da shampoo masu shegen kamshi na l'orel wanda ya sanya gashin nata santsi sosai, tana gamawa ta wanke duk wani lungu da sako na jikinta wanda a yan kwanakin nan take jin sanyin zuciya da kwanciyar hankali haka kawai, don tana jin kamar kannenta na cikin kwanciyar hankali, ta dauki hakan ne sbd yanda ta dukufa da addua akansu har allah ya sanyaya mata zuciyarta, tana gama wanka ta nado kanta cikin towel mai laushi peach color, babban kuma nade a kirjinta wanda yadan rufe mazaunanta, santala santalan cinyoyinta abayyane sai shek sukeyi don har wani walwali takeyi sosai, yau kusan wata biyar Kenan ta zaro sabulun da ummi maman haifa ta bata ta soma amfani dashi shima acikin kayanta ta gano shi, sabulun wani rirn secret ne kunshe a cikinsa, wanda ke sa jikinta sulbi da taushi kamar fatar jariri, ita kanta idan ta shafa jikinta wani ririn dadi take ji, ga hutu ya zauna sosai a jikinta da dan nutsuwa data samu, har wani irin cickowa kirjinta yayi wanda tudun kirjin nata ya bayyana ta sama dan yanda ta daura towel din sai yayi kamar ta buntsuro su gaba gwanin birgewa, tattara duk kayan wankanta tayi ta saka acikin bath bag dinta ta futo tana dan waqa tare da juyi saida ta zo tsakiyan dakin ta dan wani rankwafa in a stylish way ta juya mazaunan ta tana fadin ''oh baby let me whine my waist'', wannan ce favourite waqanta sosai shiyasa koda yaushe takan dan taka idan tana y, takawa tayi gaban socket din dakin ta kashe burner din da ta kunna a dakin kafin ta fuce, tana zuwa tsakiyan parlor ta jizge towel din kanta curly gashinta suga zubo har kafdunta, ruwan gashin na diga a kafadarta zuwa kirjinta, bata tsaya shafa mai ba jin kaurin abinci data dora yasa a guje ta karasa gaban gass cooker ta kashe ta sauke tukuyar don abincin har ya fara kamawa, saida ta sauke ta dawo natsuwar ta don duk ta daburce har kauri ya fara mamaye parlor ta juya ta fara takowa zuwa parlor tsayawa chak tayi bata juyo ba jin kamshin sa wanda ya kama duka gidan sosai itama kanta ya kama jikinta,girgiza kai tayi azuciyarta tace ''oh yaya badai kamshi ba'', buge bakinta tayi tace ''wai yaya yaushe ya zama yayan naki, kalan dangi'' tabe baki ta kuma yi tana gunguni tace ''wannan mafadacin hmm Allah ya hadaka da daidai kai''……anatse ta daga kafarta ta cigaba da wakanta ta juyi left and right, amar wanda bai dade da shugowaba jin kauri yasa yaja ya tsaya bai tako ba harta zo ta tsaya tsakiyan walk way din tsakanin kitchen da parlor, runtse idanunshi yayi wani irin bugawa kirjinshi nayi, gwalo idanu yayi jin furucinta na karshe ''waye ne mafadacin'',,,,ay da sauri ta tsaya kirjinta ya bada dammmm, da sauri ta juyo tana fuskantar, don harya tako yazo dab da bayanta, yana shaker kamshin bady wash dinta da tururin zafin hot bath din da tayi sai abin ya bada wani succulent serene a wajen, tsit kake ji nunfashin ma da kyar take fuddawa harta karasa juyowa ta fuskanceshi, ''ya allah'' ya furta chan kasan maqoshinsa, yanda gashin ta ke dripping zuwa wuyanta har kirjinta ya zubama idn=anun, lokaci guda idanunshi suka soma lunlumshewa runtse idanun yayi ya sake cewa ''uhmm??'' alamun ta bashi amsa, baki na karkarwa dukta daburce ta soma Magana, kafinma ta karasa don baya baya takeyi santsi ya kwashe saura kirish ta fadi, da sauri ya cire hannunshi daya dake cikin aljihu dayan kuma yana ciki bai cire bay a saqalo da hannusnhi around her tiny waist, da sauri ya fusgota ta bugi kirjinshi, har saida ta dago kanta yanda yafita tsayi sosai yasa ta saukewa, wani irin shock ne ya ziyarcesu daga shi har ita, matseta yayi sosai a kirjinshi yace ''answer me now kafin ranki y abaci bana son yawan magana'', ya fada idanunshi na sauka akanta da yake daidai kafadarshi don har tsakiyan kanta yana hangowa ahankali inadunshi suka sauka kan curly gashinta zuwa wuyanta dake dripping ruwan gashi zuwa tsakiyan mulamulan kirjinta da tudunsu suka buntsuro gaba, yanda ruwan yabi tsakiyan tsakannin bobbies dinta ya sashi saurin rufe idanunshi, wani irin sanyi da tsikar jiki na taso mashi tun daga makoshi, da sauri ta soma janye jikinta ta kasa, riko ya mata bana wasaba kamar za akwace mashi ita, kallonshi tayi anatse tace ''let……..gooo of …..me pls' lebbanta ya zuba ma idanu ya rankwafo da kanshi daidai saitin fuskarta wani irin bugawa kirjinta keyi, nunfashinsa da breath dinsa mai kamshi mint na dukan nata dukta daburce, kwata kwata shes not confortable, jin saukar labbanshi daidai kunnenta da saukar zazzafan numfashinsa ya sata kankame gaban towel dinta sosai don kanta ya fara kwancewa, ánatse ya furzar da nunfashi cikin kunnenshi in a harsh sexy tone wanda baisan yayi ba yace '' "Haka kike yawo yanxu idan Nace bakida kamun kai nayi laifi? Ahankali ya gangarar da kanshi zuwa wuyanta kamshin body wash dinta na fita azafafe, wani irin Zazzafan nunfashi ya sauke mata akan wuyanta zuwa kunnenta da sauri ta runtse idanunta tare da damko towel din nata da kyau don kiris ya rage subuce daga hannunta ya fadi tsabar kidimewa datayi shikuwa yana kaiwa nan ya hankada ta gefe ya tabe baki kamar yaga kashi yace "kina yar kwailarki,ki bari saikin zama cikakkiyar mace kafin ki dinga tallata jikinki" yar tsuka ya ja ya wuce ya barta anan tsaye sakeke ta sandare a tsaye, itama wannan mutumin mamaki yake bata kamar hawainiya mai chanza launi, saida ya gama kafeta da idanu kafin ya Gaya mata baqaqen maganganu Wai kwaila, gakiya ya cuceta Wai ita zai cewa kwaila meyake nufi kenan, bata da komai kenan wani irin kukane mai ciwo ya zo mata yanxu laifinta ne donta tsaya ta kashe gas baima tsaya ya saurare ta ba yayi mata muguwar fasaara wani irin maququn baqin cike ne ya turniketa tana kumbure kumbure tayi hanyar dakin kamar zata shiga Sai kuma ta juya wata zuciyar tata na ingizata "ashe ke matsoraciya ce" ta fada aranta, tabe baki tayi ta share hawayenta ta koma wajen sitting room ta bude box din kayanta ta saka riga da wando masu santsi sulub blue color, wanda ya danyi buje ta kugunta saiya fidda shape dinta sosai saidai bai dameta ba while rigar takai daidai kasan cikinta, sai tayi kyau sosai cikin kayan, wayan ta ta dauka ta kira haifa ta bata labari, dariya kawai ta dunga yi mata karshe dai ta fara tsokanarta ''babe tunda ya kiraki da kwaila ya kamata ki koya mashi hankali, kinsan wasu mazan idan sukaga kana da kananun shekaru saisu dinga maka kallon raini, ko su dunga maka kallon kamar ke yarinya ce babe ni wallahi gani nake kinfi karfinshi ma,''gwalo idanu amra tayi kamar haifa na gabanta tayi saurin cewa ''kaii haifa karkiyi sabo fah, wannan mutumin yafi karfina ko a mafarki kekam bare ma ni banson maza irinshi, masu masifa da miskilaccin ga girman kai badani ba'' shuru amra tayi tana sauraronta da zugar data fara mata akan wallahi ta nuna mashi itafa ba yarinya bace kuma itama tana da class, saida haifa ta zuga ta sosai kafin sukayi sallama, da farko dai ta watsar da zancen, saidai tunawa da kwaila daya kirata dashi abun ya tsaya mata arai kuma yana baqanta mata rai sosai, watsar da zancen kawai tayi kafin ta miqe ta deba abincin datayi wanda ya soma kone wa saida taci tayi nak anan kitchen din kafin ta wanke hannunta ta plates din ta koma sitting room, ganin karfe 1:30pm yasa ta zumbula hijabinta ta fuskanci kibla, tana idarwa tayi addu'oin data saba na nemawa kanneta kariyar allah da kanta kafin ta nannade ta aje ta koma kan couch tana kallon tv har barci ya kwashe ta anan.