Kenza eBookz

Auren katin kasa complete - Chapter 16

Auren katin kasa complete - Chapter 16

Auren katin kasa complete Chapter 16: Auren katin kasa complete Chapter 16. Yana shiga dakin ya sauke nannauyan ajiyan zuciya, anatse ya tako gaban…

4,326 words

Yana shiga dakin ya sauke nannauyan ajiyan zuciya, anatse ya tako gaban gadonshi yana kallon koína yanda yake fess fess ga kamshin bakhoor daya gauraye ko'ina, kayan jikinshi ya soma tubewa ya wuce toilet don a gajiye yake daga airport yake ya taho apartment dinshi don ko penthouse dinshi bai leka ba saidai luggage dinshi dayasa m5 yakai mashi chan penthouse dinshi, daman tafiya yayi zuwa india na sati guda, wanda duk akan rashin lafiyanshi ne wanda doctor shi ya mashi recommending wani likita achan india doctor dirsham don ya duba shi idan da akwai yanda sauqi zaizo mashi, saidai kash kamar koda yaushe answer da yace bashida wani option, wanka kawai yayi ya dauro alwala ya futo, wani irin azabbaben ciwon kaine ke damunshi, saida ya idar da sallan dhuhur kafin ya miqe, duk yanda kanshi ke ciwo hakan bai hanashi jawo laptop dinshi bay a soma aiki har akayi sallan asr, daman bai cire jallabiyanshi ba hakan yasa ya miqe kawai yah au kana bin sallah ya tayarda sallah, yana idarwa ya zauna yayi azkar bai tashi ba har akayi sallah magrib da isha'I yana nan zaune, sai wajen karfe 8;30 ya mike ganin call din m5 na shugowa, miqewa kawai yayi baibi takan wayan ba ya fuce daga dakin, haryazo ya gitta ta a kitchen bai ce uppan ba, amra kuwa wadda kamshinsa ya mata sallama tun kafin ya doso hanyan hakan yasa bata juyo ba ta cigaba da dafa rice and stew din da take yi tana juya miyar dataji naman kaji zuqu zuqu aciki, bude kofar futa yayi ya karba basket din hannun m5 kafin ya rufe kofar ya tunkaro hanyar kitchen din, aje basket din yayi kan island kafin ya zauna akan chairs din yana latsa wayan shi, saida ya zauna na kusan minti goma still idanunshi nakan wayan shi kafin cikin nutsuwa ya soma Magana ''serve me'', tsayawa tayi da juye abincin da takeyi a containers sbd tana storing din su idan ta dafa dayawa don idan taji yunwa in bata son girki saita dumama taci kayanta, anatse ta aje container din da serving spoon din hannunta kafin ta juya bata ko kalli inda yake ba ta bude wajen plates da spoons da serving spoon ta kwaso ta dauraye ta goge kafin ya karasa gabanshi, bude warmer din tayi ta zuba mashi white soup din sai cheesy creamy pasta data gani agefe, tana gamawa ta tura mashi gabanshi ta bude fridge ta zaro mashi ruwa maid an sanyi kamar yanda yake sha, miqa hannunta tayi ta dauko pineapple and coconut juice din datayi, kamar ta aje don tsoron karya duzgata takeyi, da sauri ta maidashi ta wuce gabanshi ta aje mashi a gabanshi kafin tace ''bismillah'', dagowa ayi ya mata kallo daya kafin ya kauda kanshi ya dauka spoon din ya soma cokalawa cikin bowl din, wani irin zazzabi yake ji sosai wanda ya sashi loosing apetite dinshi, dagowa yayi ya kallet lokacin tana gama saka containers din cikin fridge bayan ta deba wanda zataci acikin plate ta jawo pincolada juice din datayi tayi kafin ta gitta ta gefenshi ta wuce duk agaban idanunshi, bata kaiga wucewa ba ta tsinkayo muryarshi ''wannan jagwalgwalon zakici?'' tsayawa tayi chak batace mashi komi ba haka zalika bata cigaba da tafiyanba ranta ne yadan sosu, tabe baki yayi ya jawo tissue ya goge bakinshi ya wuce ta gefenta yana yar tsuka da gefen bakinsa harya isa daki, toilet ya wuce dakyar yayi wanka don zazzabi harya soma rufe shi, idanunshi sunyi jaa sosai, wanda tunawa da maganar doctor ya kara tabbatar mashi da side effect din freezing din sperm dinshi da akayi ne wato zazzabin dare, don yaqi yaje ayi de-freezing don bai samu soluton ba har yanzu, yana fitowa ya jawo wandon pjs dinshi masu santsi da tsada, dakyar ya saka yanajin wani irin weekness na zuwan mashi sosai, ga wani irin abu da yakeji yana taso mashi tun daga yatsun kafafunshi zuwa kanshi wanda ke haifa mashi da tashin tsikar jiki da kasala, anatse ya lallaba ya karasa gaban gadon ya shige cikin duvet din nunfashinsa na sauya wa zuwa mai zafi sosai, runtse idanunshi yayi yana kokarin sanya kanshi bacci kozai samu salama, da kyar bacci ya fisgeshi, daga yanda yake fidda nunfashi da sauri ga zafi zaka gane yana jin jikinshi.

Tana gama cin abincinta da yake kirirari da jagwalgwalo ta tattara komai har wanda ya rage ta saka a frigde ta wanke kwanuka ta sha ruwa sosai don juice din data sha akwai madara wanda ya haifar mata da kishiruwa sosai, saida ta tabbatar ta gama komai ta kashe hasken kitchen ta koma sitting, wayanta tayi plugging a chargy kafin ta cire rigar jikinta ta saman ya zamana daga ita sai wandon rigar da yar vest din rigar kayan wanda ya zamana set ne, anatse ta soma karanto addu'oin kwanciya kafin ta kwanta.

Karfe biyu da rabi na dare ta miqe zumbur kamar wadda a tsungula, wani irin futsari ne ya matso ta, da sauri ta yaye dan blanket din da take lulluba dashi ta zuro kafarta kasa ta sanya fuffy bedroom slippers dinta, a gurgurje ta nufi dakin nasa, ahankali ta dora hannunta kan handle din ta bude, ganin dakin so dim don ko tsakiyan dakin ba a gani yasa ta fara tafiya ahankali don gudun tuntube har takai bakin kofar toilet, tana shiga ta rufe kofar ahankali ta kunna light din toilet din ta zauna kan wc, saida ta gama buqatunta ta wanke hannunta da handwash kafin ta nufi kofar ta bude ahankali ta futo, anatse take takowa harta zo gittawa gefen gadonshi, kunnuwanta suka fara jiyo mata sautin nunfashinsa wanda ke fita da sauri sosai kamar mai asma, jinkirta tafiyarta tayi don tabbatar da kodai ba lafiya ba, juyawa tayi saitin gadonshi, kanshi na cikin duvet din don ko alamun fuskanshi bata gani don da dan hasken bedside lamb, addua'oin neman sauqin wurin allah ne da yake yi ya tabbatar mata ba lafiya ba, cikin sauri ta karasa gabaon gado, daburcewa tayi sosai jin yanda nunfashin nashi ya tsananta sosai, cikin tashin hankali da rashin abinyi ya sata Magana ahankali ''uhm…are..you okay?'', jin shuru gashi ya fara jijjiga har gadon nashi na kara ya sata ta kara burkicewa, hankali atashe ta sake maimata tambayar datayi mashi ganin kamar ma ba jinta yake ba yasa ta daga hannunta cikin tsoro da fargaba ta janye duvet din daga kanshi gaba, arazane tayi baya don gaba daya hankalinta ya tashi da ganin yanayinshi, fuskarshi tayi jaa sosai kamar an shafa mashi barkono, ga zufa data gama wanke mashi fuska hade da tururin zafi dake futa daga jikinshi wanda daga tsayen datake tana jin yanda nishinsa ke fita da zafi zafi sosai, kallon fuskarshi da take a lumshe tayi kafin ta matso sosai gab da shi ta dan tsugunna daidai fuskarshi ahankali ta sanya hannunta akan goshinsa da sauri ta cire don wani irin zafi ne da shock ya hade mata waje daya, a razane ta kalleshi tare da dabbin fuskanshi ahankali ''yaya…yaya whats wrong are you? Youre burning up, innalillahi na shiga uku ya zanyi'', daburcewa tayi zata mike tsaye ya chafke hannnunta wanda yaji wani irin confort data saka akan fuskanshi don wani irin boiling jininshi keyi, kamar mahaukaci haka ya dunga jan hannunta akan fuskarshi yana gogawa, har zuwa kirjinshi, da sauri ta fara kokarin janye hannunta amma inaa,yayi mata wani irin damka kamar ranshi na hannunta, miqewa tayi don neman mafita wajen kwace hannunta don ta neman mashi magani acikin dakin, jin hanunta na neman kufce mashi yasa ya janyo gaba dayanta zuwa jikinshi, wani irin nannauyan ajiyar zuciya ya sauke don yaji kamar an zuba mashi ruwan sanyi a cikin jikinshi, da sauri ya kankameta sosai, amra kuwa wadda tayi suman tsaye dukta daburce da yanda yake maqalmqale jikinta, ga yanayin yanda dumin jikinshi ke shiga cikin nata, hankali atashe ta some kokarin Magana, dim tunaninta ya dauke jin gabadaya kanshi cikin rigarta wadda babu ko bra ajikinta sai yar shimin, yanayin yanda ya figota ta fado akanshi ya zamana tana kanshi yana kasa, da sauri da sauri yake fidda nunfashin neman salama wanda ke sauka akan fatar kirjinta zuwa wuyanta, hankali atashe idanunta ya fara kawo ruwa da sauri ta soma furta innalillahi wa inna ilaihi rajin, bat agama shiga tashin hankali ba saida tayi yanda ya farke rigar tata gaba daya ji kake qiiiiit yayi wurgi da ita, gaba daya ya futa hayyacinsa, wani irin sanyi ne ke shiga jikinsa wanda ya kasa gane menen akanshi shidai yasan kawai yana jin saukin zafin zazzabin da yake ji, kuka amra ta fara ciki ciki don ya damke kugunta sosai babu hanyar tsira ga yanda ya cusa kanshi tsakanin nonuwanta yasa tsikar jikinta tashi sosai, hankali atahse don wannan ne first time da jikin namiji ya sauka kan nata, body contact din yayi yawa sosai,saqalota yayi sosai a jikinsa kirjinta akan nashi sosai, ahankali nunfashinsa ya soma daidaituwa tare da sakin jikinshi sosai, sun dauke wajen awa biyu a haka, jikinta duk ya soma tsami da irin rukon dayayi mata da yanda ya saqalo da kanshi ta wuyanta yana sauke mata zazzafan nunfashinsa ya rungumeta sosai akan jikinshi, kirjinta tsam manne da nashi har baccin wahala ya kwasheta bata sani ba, shima baccin wahalan ne ya dauke shi mai zurfi sosai wanda ya danji saukin zazzabin dukda har lokacin baya cikin hayyacinsa, har kusan karfe shida suna kwance a hakan, ahankali ta soma bude idanuwanta akan fuskanshi wanda take dab da tata, runtse danunta tayi tare da budesu tar akanshi don tunawa da abinda da ya faru a cikin daren ranar, hamdala tayi da allah ya taimake ta ita ta fara farkawa, anatse ta soma janye jikinta daga nashi, jin yanda ya saqalo kugunta da hanneynshi yasa ta soma janye hannun nashi ahankali har ta samu ta cire hannayen nashi gaba daya, ganin yana juyi zai chafkota yasa tayi saurin yin wuf ta fado kasan gadon har tana buge bumbum dinta, ahankali ta furta ''ouchhhh'' da dan karfi, anatse ta dago ganin yana gab da da farkawa yasa tayi saurin rarrafawa ta fuce daga dakin don bata fatan ya ganta har tana mance rigarta don batabi takan rigar bama don hankalinta a mugun tashe yake idan ya ganta adakin nashi. Tana fita ya soma bude idanunshi wanda sukayi jaa sosai tare da kankancewa, addua yayi kafin ya mike ya sauka daga kan gadon yana dan tangal tangal kamar zai fadi don wani irin jiri ne ke debanshi, toilet ya fada saida ya sakarma kanshi ruwan zafi sosai kafin ya danji dama dama ya dauro alwala ya fito, gaban closet dinshi ya tsaya ya fiddo da farar jallabiyan shi ya sanya ya shimfida sallaya, saida ya dauka kusan awa yana zaune yana azkar, lokacin gari ya dan soma haske kadan, miqewa ayi ya nade sallayan ya koma kan gado yadan jingina da gadon, tare da lumshe idanunshi, ahankali kamshin da banashi bay a soma gaurayewa da nashi a dakin, ahankali ya dan bude idanunshi wanda suka danyi jaa sosai suka sauka kan duvet dinshi daya dan yamutse sai dan jan abu dake lekowa daga cikin duvet din, kauda kanshi yayi daga kan duvet din ba tare da wani dogon tunani ba ya jawo wayanshi ya danna kiran doctor shi, ringing biyu ya dauka ''good morning mr amar''.. anaste amar ya soma Magana cikin kamewarshi kamar koda yaushe ''morning doctor, Im coming to the hospital now, please book an appointment'', yana kaiwa nan ya kashe wayan tare da miqewa ya chanza zuwa kananun kaya masu laushi ya jawo wayanshi da keys dinshi ya fuce daga dakin, koda ya futo bai tsaya kallon parlor ba yasa kai ya fuce daga gidan gaba daya. Amra kuwa wadda saida ta futo daga daki tana fidda nunfashi tsira da sauri sauri ta samu waje ta zauna akan kujera, sai alokacin ta lura da shirmen datayi na barin rigarta a dakin, tashin hankalin data shiga bai barta ta tuna ba saida tabard akin, da sauri ta janyo hijab dinta ta fara kiciniyar sanya hijab din, idannta ta sauke akan boobs dinta da suka danyi jaa daga yanda ya yamutse ta har shati shati wajen yayi sosai, tunawa da yanayinsu na dazu ya sanyata saurin saka hijab din don bata son tunawa kwata kwata, zama tayi anan har akayi sallan subh, tana son yin shiga toilet don yin alwala amma ta kasa don wani irin tsoron shiga dakin ne ya darsu a cikin zuciyarta sosai tana nan zaune har ya fito, kanshi turarenshi ne ya mata sallama, har ya fuce bata dago ba haka zalika shima bai kalli inda take ba harya fuce, sauke nannauyan nunfashi tayi don ba karamin tsorata da futowanshi tayi da sassafe don duk a tunaninta ya gano wani abun ne ya mashi muguwan fassara, miqewa tayi ta wuce dakin domin dauro alwala don har kusan takwas da rabi saura. 92-93 Yana fucewa ya shige motar shi yaja bai tsaya ko'ina ba sai gaban private hospital din da yake zuwa, saida ya sanya facemask a fuskanshi kafin ya futo daga motar ya wuce ciki hannunshi rike da wayanshi, saida ya zo daidai da kofar shiga main entrance na cikin asibitin message ya shugo cikin wayanshi, dubawa yayi ya fara karantawa har ya buge da mutun wanda bai lura bama ya gifta ta gefen matar ya wuce, hankalinshi yayi gaba sosai wajen wayar da yake kalla bayan an sake tura mashi wani message din da same number, da sauri ya dago ya kalli ko'ina na harabar wajen daga karshe ya sake duba wayan nashi yana maimaita last message din da aka sake tura mashi ta cikin wata anonymous number da akayi hidden, ''I'm coming for you, I promise to destroy you'' maimaitawa yayi kafin ya sake karanta na next masseage na karshe da aka tura mashi wanda yafi bashi mamaki ''watch where you're heading too'' mamaki ne karara a fuskarshi wanda ba kowa ke gane hakan ba don yanayin fuskanshi abu ne mai wuyar tantancewa, tabbas wadda suka danyi clashing yanxu wanda ya kasa tantance macece ko namiji dan bai kalli fuskar wanda suka bige dashi dinba, tabbas shine ya tura mashi wannan message din, so bibiyar shi akeyi Kenan, tsaki yadan jaa chan kasan maqoshinsa don shi duk wannan threat baya daga mashi hankali, don ya wuce level din nan, babu abinda yake zaman mashi threat yanxu don shi jarumine da baya tsoron komai da kowa, tura wayan nashi yayi cikin aljihun wandonshi kafin ya karasa cikin asibitin, baima tsaya gaban reception bay a wuce office din likitanshi, azaune ya tadda likitan nasa dr stefen, zama yayi bayan sun gaisa ya fara kora mashi bayani akan zazzabin da ya taho mashi gadan gadan wanda ya sanya shi ficewa daga hayyacin sa, saida ya gama sauraron shi kafin dr stefen ya soma Magana ''mr amar, like a side last time, this is the side effect I'm warning you about, this is about more than 3 month of frezzing your sperm and desires, I will advice you get it un-frezz or you'll experience worse'' nunfasawa yayi kafin yadan shingida zamanshi ya kalli likitan ''doc this is not the perfect for it, I need more time'', sanin ba hurumin shi bane bin diddigin patients sannan dole saiya aminta kafin ayi mashi wani aiki saidai ya nuna mashi risk din rashin yin abinda zai kawo mashi sauki hakan yasa ya rubuta mashi pain killers kawai sukayi sallama ya wuce pharmacy ya karbo, bai tsaya komai ba ya wuce office bayan ya kira m-5. Yana isa office bai tsaya ko'ina ba sai cikin office din shi, zama yayi kan kujeran shi ya kwantar da kanshi dake mashi wani irin zafi, saida ya dauka kusan awa guda kafin ya dago kanshi ya kunna desktop din gabanshi ya soma wasu ayyukan, kurama desktop din idanu yayi yana kallo, ganin yanda yake kallo yasa na dan leka dan naga me yake kallo, files ne burjik wanda saida yabi daya bayan daya yana duba date da time kafin ya danna file din da lokacin dayayi tafiya wato 25th march budewa yayi saiga recorded video na dakinshi wanda ke nuna alamun akwai cctv camera a cikin dakin nashi, dan relaxing kanshi kan kujera ya fara duba video din, ganin babu wani movement yasa ya dunga forwarding komai wanda aciki ma yawanci amra c eke movement dinta na zuwa bandaki, ganin babu wani important abu cikin file din yasa ya futa ya shiga next day da baya garin, shima dai bai samu wani abunba saida ya shiga next file wanda ya kasance third day da baya gari,tun daga lokacin data shugo dakin ya tsaida forwarding din da yake har zuwa lokacin data shigo dakin ta gyara mashi ko'ina tare da saka mashi bahoor data saba koda yaushe, kanshi ya dauke wuta lokacin data gama komai ta soma tube kayan jikinta a tsakiyan dakin, da sauri yayi skipping wajen don bashida ra'ayin kallon wajen harta futo da dan towel dinta a kugunta da brush and sponge bag dinta, ta fuce daga dakin,skipping ya dunga yi har aka kwankwasa kofar office dinshi kafin ya bada umarni aka shigo, saida m-5 ya sara mashi kafiin ya soma Magana ''I have a very tight job for you, Ive sent some information to your mail, I want to know whos behind the contact, make sure you do a tough research okay? Da sauri yace ''yes sir'' Sara mashi yayi kafin ya juya ya fuce idanunshi ya maida kan cctv camera din ganin babu wani abu that is important yasa yadanyi tsaki yana tunanin wani tunani, ''what im I even thinking, tsaki yayi harzai kashe desktop din sai kuma yadan tsaya ganinta shugo cikin dakin sanye da doguwar riga mai roba roba wanda tayi mata kyau sosai pink color, kanta da hula pink kalar rigar headphones ne sakale a kunnenta tana tikar rawarta gwanin burgewa, shagala yayi da activity dinda take har saida ta fuce ya dan kwantar da bayanshi akan kujerar ya furta ''silly girl'' rufe idanunshi yayi yana tunanin abunda likita ke fada mashi nay a zama dole ayi unfrezzing sperm dinshi idan akayi kuma dole immediately ya kusanci mace yanxu shi damuwarshi ta ina sai kusanci mace, bayajin zai iya yin zina don bayason ya haifi danda bana sunna ba, gashi ita wannan da sauri yace hell no nooo, wannan yar yarinyar ina bazaiyuwu ba, infact bazai ma taba bari ba tsaki yayi kafin ya bude shanyaynyun idanuwanshi da sukayi jaa ya mike ba tare daya kashe desktop dinba harya dan yi taku daya yadan jinkirta ya juya yana kallon screen din, ganin hammam kwatsam cikin dakinsa, da farko harya basar don yasan haka yake sometimes yana zuwa gidan harya kwana but kamar bazai kalla ba chan kuma ya kurama screen din idanu, da farko zagaye dakin ya fara kafin ya kunna tv ya zauna kan couch din daki, cikin yan dakiku kuma ya mike ya fuce, fitarshi dayan awanni amra ta shugo tayi alwala ta fuce, mamaki ne karara a fuskanshi ganinta da kayan dazun wani irin daci yaji da baisan daga ina ya faro ba, shifa matsalanshi da yan mata Kenan basu san ya kamat ba yanxu haka ta zauna namijin da ba muharraminta baya ganta, shi yana kishin yaya mata musammam marayu bayansan yaga zsunyi hanyi haryan da ba madaidaiciya ba hakan yasa ya danyi shuru kafin ya dauka wayan shi ya keys din ya fuce daga office din, direct penthouse dinshi ya wuce ya danyi abubuwan sa kafin ya wuto apartment dinshi koda ya shiga kamar kullum a zaune ya taddata tana shan smoothie hankalinta kwance sanye take da rabian gown ta shan iska mai karamin hannu purple color fuskanta fayau babu komai sai sheki takeyi alamu hutu da jin dadi ya zauna a jikinta, mikewa tayi da sauri ganinshi gadan gadan akanta, da sauri ta soma Magana ''sannu da zuwa ina wuni'' baima tsaya jin abinda take fada ba bare kuma amsa gaisuwar tata azafafe yace ''daga yau kar ki kuma zama haka babu hijab koda kuwa ke kadai ce acikin apartment dinnan, bana son rashin hankali understood'' kallonshi tayi da yanda fuskanshi tayi jaa baka taba tantance fushi yake ko ranshi ne yayi mugun baci saboda yanda fuskanshi take da wani sihirtaccen annuri saidai kuma kwarjini da yake dashi zaisa ka gane da wani abun alamu ranshi a mugun bace yake da yanayin fuskarshi da bazaka taba tantance taqamaiman matsalarshi ba ko abunda ke damunshi, fuu ya wuce daki kamar walkiya yabarta cike da mamakinsa, tabe baki don inda sabo ta saba da wannan halayen nashi shidai baka gane gabansa da bayansa dukda ba shiga alamuranshi take ba don sai suyi kwanaki da yawa basuyi Magana ba saidai gaisuwa itama idan ya fito ko idan ta shiga dakin nashi, komawa tayi ta zauna ta cigaba da shan smoothie dinta da latsa waya. Shikuwa goga tunda ya shiga dakin kanshi bakhoor din da take sakawa ya mashi sallama, jingina yayi da jikin kofar yana furzar da numfashi kamar wanda yayi tsere, wani irin nauyi zuciyanshi ke mashi wanda ya kasa gane dalili saidai yana danganta komai da abubuwan dake faruwa daki cikin kwanakin wani irin zazzabi mai zafin ne ya fara zuwan mashi babu shiri, takowa yayi har gaban gadon nashi dake tsaf, kamar ba'a kai ya kwanta ba donta gyareshi tsaf har an sauya bedsheets din an sanya wasu daban farare tass, zama yayi ya dafe kanshi dake sara mashi, wayanshi ya zaro daga aljihun wando ya danna ma m5 kira, ringing biyu ya dauka, yace ''yes sir'' Cikin zafi ya soma Magana ''when did you stop updating me on anything when I travel? Ya fada a zafafe, yanda yake Magana kadai ya tabbatar ma da m5 yana cikin fushi sosai, saidai abin mamaki ya kasa fadan takamaiman dalilin fadan nashi dukda koda yaushe koda kuwa tafiya yayi kuma a ranar zai dawo sai anyi updating nashi akan komai don shi mutunne mai lura da taka tsantsan sosai akan abubwan da suka shafe shi duk wani abu da m5 yasan zaiso ya sani yana fada mashi bare idan har wani abu ya faru saidai this time around babu wani abu da ya faru saidai zuwan abokin nashi daya dunga yi cikin kwanakin shikuma wannan ya saba zuwa don an san tsakaninsu, babu abinda m5 yace tunda ya fara Magana harya gama yace ''im sorry sir'', shuru amar yayi yana nazari, why is he doing all this, sbd hammam yazo ne or what, ay bai kamata ace yana fada akan hakan ba sbd ay hammam ya saba zuwa gidan nashi koda kuwa baya nan, but why, shuru ya dan yana dogon nazari saida m5 yayi gyaran murya kafin ya dawo hayyacinci ya kashe wayan diff ya kwanta baima tsaya cire takalmin nashi ba. Amra kuwa ganin biyar saura yasa ta kira haifa, ''hey babe ya kike kwana biyu, bakizo office baya jikin abu?" Gyara zama haifa tayi akan kujeran patients guest wadda ke fuskanta gadon marasa lapiya nunfasawa tayi kafin ta soma magana ''hey babe ina nan lpy jikin abu ne yadan motsa amma da sauki munaa asibiti an kwantar dashi'' shiru ne yadan biyo baya kafin amra tace ''subhanallah yaushe aka kwantar Dashi baki fada min ba please ki tura min address zanzo anjima kadan ki gaishe da ummi please allah ya bashi lpy… ''nunfasawa haifata tayi kfin tace ''thank you babe zan tura maki yanxu zan aje waya don inda likitoci sunce yana buqatan hutu banda hayaniya see youu saikinzo''

Kurama wayan ido haifa tayi ta kalli ummi dake zaune kan sallaya tana azkar, kafin ta maida hankalinta kan wayan ta kara dialing number hamman yau kusan kwana uku Kenan rabon da suyi waya shida ita, hankalinta ba karamin tashi yayi ba don yawaci yana fada mata idan zaiyi tafiya gashi wayan nashi a kunne yake bawai ya kashe bane kuma tana rininging duk sanda ta kira, kamar koda yaushe message ta tura mashi kamar haka ''habibi ma bi, laqad atasalt bik'iinak la tastajib (habibi whats wrong ive been calling you, you re not responding) please reply me ass soon as possible, abu has been admitted.''.. tana tura mashi message din ta mike da sauri ganin abu ya bude idanunshi da yadan fada kadan, da sauri ta matso gabanshi ta rike hannunshi tana mashi sannu, murmushi kawai ya iyayi mata kafin ya lumshe idanunshi, da sauri ummi ta danna emergency bell ganin yanda ya lumshe idanun tsoro kar seizure din ne ya sake zuwan mashi, da sauri doctor ya shigo da nurse suka farad an dudubashi, saida doctor y agama kafin ya masu bayanin alluran da akayi mashi ne bai sake shi ba don jininshi daya dan hau ke sashi jikinshi mutuwa sosai. Bangaren hammam kuwa wani abu ne ya faru,wanda ya sashi daina daukan wayan haifa, wato akwai ranar da yakai wani proposal na wani business company din abuh wanda da farko abuh ya karbe shi da hannu bibiyu saboda yanda yaga da soyayya tsakanin shi da yarsa, saidai dan binciken da yayi ya gano kamshin rashin gaskia a tattare da hammam din da proposal din, saidaga baya ya gane daga inda proposal din ya fito wanda hammam yayi badda kama a zuwan da yayi ma abuh wanda hakan yasashi neman shi har office dinshi yazo, koda yaje abuh yayi kokarin bashi chance akan ya fada mashi gaskia daga karshe dai yace mashi yayi cancelling proposal din nashi, dukda bai fada mashi ko nuna mashi ya gano komai ba don lauje ne akayi shi cikin nadin, karshe ma dai abuh dariya kawai yayi mashi kafin sukayi sallama, koda hammam ya koma ma mahaifinshi da rejected proposal din yaji zafi sosai don dalilin wannan proposal dinne ma hammam ya tunkari haifa da soyayya duk dan ya samu shiga wajen mahaifinta sai abun yazo da sauki ba tare da neman taimakon nata ba da sukayi planning tun farko wannan dalilin yasa mahaifinshi ya sashi yanke alakarshi da ita don amfaninta ya kare sai kuma next plan.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull