Kenza eBookz

Auren katin kasa complete - Chapter 17

Auren katin kasa complete - Chapter 17

Auren katin kasa complete Chapter 17: Auren katin kasa complete Chapter 17. Hammam's res Kallon wayan nashi yayi dake ta ringing harta katse message ya…

3,552 words

Hammam's res Kallon wayan nashi yayi dake ta ringing harta katse message ya sake shugowa, dubawa yayi ganin message din haifa yasa, ya aje glass cup din hannunshi ya bude message din yadan jima yana karanta message din kafin ya dago jin gyaran muryan da akayi mashi kura mashi idanu tayi sosai babu kaya jikinshi sai gajeran wando, dagowa yayi ya kalleta kafin ta karaso gabanshi sanye take da farar riga har gwaiwanta da alamu kayanshi ne ma cikin rausaya ta zauna kan laps dinshi, ''young man are you affected if you are then call her up don't be a bastard?''ta daga mashi gira daya, dagowa yayi ya kalleta kafin ya soma Magana ''no need, I don't need her anymore'' Ahankali ta fara shafoshi hartazo kan nippy dinshi tadan murza kafin ta matso da fuskanta daidai kunnenshi kallonshi take tabbas shima wannan zata iya rage zafi dashi saidai inaaa general ya wuce shi nesa ba kusa ba, kishirwarta ta general ce sosai takawa tayi tace'' so whats the next plan now?'' ganin ya soma shiga yanayi yasa tadan matsa mashi nipple din da karfi tare da furzar da numfashi cikin kunnenshi ahankali tace ''I need your friend so badly, not only I want him to suffer I want him so badlyyy to my coreee'', wani ririn gauran nunfashi ya furzar kafin yadan tunkudeta gefen kujera ya mike yace ''get ready, for office tomorrow, kinsan yanda muka tsara komai bana son kuskuren, keep your hunger aside first'' yana kaiwa nan ya wuce cikin dakinshi yana sauke nunfashi, zama yayi kan lafiyayen gadonshi ya higa tunani, anya wannan hanya madaidaiciya ce, lallai ya cika butulu, saidai baya jin yanda ya faro komai zai iya tsayawa, tsaki kawai yayi ya kashe wayanshi baki daya ya shiga tunanin irin rayuwar da yayi achan baya. Hammam haifanfan dan Iraq ne, mahifinshi asalinshi dan kasar Iraq ne mahaifiyarshi kuwa anan uae aka haifeta, tun tasowarshi ya taso yana ganin irin ukubar da mahaifiyarshi ta shiga sanadiyan mahaifinsa, iyayenta masu kudi ne sun mutu sun bar mata dukiya wanda sanadiyan mahaifinsa ta salwanta sbd shaye shaye da yakeyi da chacha, tun suna gidansu na kansu har suka yawo kan titinan da gidaje da akayi abandoning suna kwana, mahaifinshi kuwa acikin shaye shayen nashi ya mutu dalilin zuciyarshi data buga don giya tayi mashi illa sosai a wulaqance ya mutu, shida mahaifiyarshi basu wani damu ba don dama chan babu abunda yake tsinana masu saiya zamana mutuwar tashi ma sauki tazo masu dashi don dukan da yake ma mahaifiyarshi idan ya bugu yanzu an rufe shafin wannan, ya taso babu ilimi kwata kwata saidai bara, bashi da burin da daya wuce ya kula da mahaifiyarshi sosai, lokacin da yanada shekaru goma sha shida shiff a duniya cikin wannan rayuwa dai ta rashin gata ta cikin kasakanci allah ya kawo masu alif bin shuraim, babu zato babu tsammani, alif yana daya daga cikin manyan dake diban yara irinsu irinsu mabarata yana basu aiki a cikin business din da yake wau yana turasu wata kasar wasu kuma anan uae yae basu aikinda babu wanda yasan wani irin aiki ne saidai, shima hammam ya ganshi ne lokacin da aka kawo record din beggers, ganin yanda yaron keda wayo da hazaka yasa ya karbeshi shida kanshi amimakon ya bashi aiki koya tura shi wani wajen, saidai yayi alwakawri zai maidashi weapon din da zaiyi amfani dashi idan lokaci yayi, ba karamin dadi mahaifiyar hammam taji ba ganin rayuwar hammam na chanzawa, don bashi kadai alif ya dauka nauyi ba harda ita kanta mahaifiyar tashi, akwana a tashi alif ya sanya hammam a makaranta yayi dogon karatu inda ya hadu da amar suka shaqu sosai har alif ya saka shi cikin uae armed force wanda shima tare sukayi shi, akwai lokacin da hammam yayi dogon training wanda wannan ne training din dayayi wanda dawowan shi ya tadda mummunan labarin mutuwar uwarshi haka kawai kwatsam, ko lokacin daya zo din alokacin alif ke shaida mashi tayi wata hudu da rasuwa, hammam yayi kuka kukan baqin ciki sosai, yayi alqawarin bama mahaifiyarshi gata, gatanda bazaima kanshi ba don tasha wahala dashi sosai, she protected him, yana rayuwa ne sbd ita saidai mutuwa tayi masu Katanga shida ita, kokadan baiji haushin alif ba naqin fada mashi mutuwar mahaifiyarshi sbd yana daya daga cikin mutanen da yake girmamawa sosai, kuma shine wanda ya maidashi mutun kuma yayi alqawarin zaiyi duk abunda alif keso zai kasan ce mai halacci don abunda mahaifiyarshi ta raineshi dashi Kenan, duk wanda ya dago ka ya maidakai mutun ka dage kayi mashi halacci karkayi butulci. Hammam bai fara karantar alif ba saida y agama makaranta tsaf ya karanci alif da kudururrukansa, wato alif babban mutunne mai connection, yana dealing da illegal jobs a uae, aiki na farko da alif ya saka hammam shine akan babba ogan su wato general ashraf wanda shine babban general mai hazaqa a shkarar 2014, lokacin suna officers shida amar, da farko aikin yaso bashi wahala don yana officer ne a lokacin saidai abun mamaki shine wanda ya daure ma shi kanshi hammam din kai shine, da yawa cikin manya manyan armed force dake cikin headquater mutanen alif ne, tun daga lokacin duk wani wahallaen aiki ko wani aikin da zai kawo mashi fargaba sai yazo mashi da sauqi, dukda shima dan sako ne, instruction kawai ake bashi saiya gudanar da komai, wanda duk aikin da yake yima alif din cikin kulli yake don shi kanshi ya kasa fayyace komai, duk sanya akayi sauyin manyan headquarters shike zuwa ya da mutanen baban kodai sukawo karshen lokacin generals din ko kuma ayi masu kulle kulle da zaisa subar aikin gaba daya shima idan basu amince da abinda suke tafe dashi ba, lokacin da suka fara tasowa shida amar, sun taso cikin kwarewa cikin aikinsu sosai, wanda amar ya wuce hammam a kwazo sosai da komai ma, amar yana aiki cikin ilimi da zurfin tunani, duk sanda zasuje operation amra ke dawo wa da rank, don da haka ake promoting dinshi, sannan duk wani important operation yana ciki domin he is very tough, ganin halayyansu ya banbanta yasa hammam tsorata sosai da amar saidai bai barshi ba don ance, makashinka na tre dakai, alif wato mahaifin hammam ya kwallafa rai akan hammam saidai ganin hazakar amar yasa yaji yana son yaron ya shugo hannu, saidai kashh amar yayi masu nisa sosai, tun alif na saka ran hammam ya zama shugaban armed form wato general har ya kawo yanxu bai kaiba, wanda amar ne ya amshe wannan rank din. Ayanxu alif bashida wani buri daya rage ya kawar da amar daga mulkin da yake don sauran generals din yanda yake da power yana tunkarar su har ya samu yanda yake so saidai shi wannan tun kafin ya zama abunda ya zama ya kasa tunkarar shi, don uae militriy ke rike da kasar ba sarauta ba ko government saidai mu'kami. Sauke gauran nunfashi hammam yayi bayan y agama dogon tunanin kafin ya gyara kwanciyarshi har bacci ya daukeshi anan wajen.

KANO STATE. Tun bayan ya Muhammad ya kaisu salima asibiti suke samun kyakyawar kulawa sosai, har salima ta farfado saidai salim da yake cikin coma, daki daya ya muhammada ya hadasu, wanda kullum salima tana gefen dan uwanta dukda itama da sauran waraka a jikinta hakan bai hanata kula da kanninta ba, ita ke sauya mashi kaya, ita ke wanke mashi wasu kanannun abubuwan buqatunsu anan asibitin, duk wannan zaman da sukayi da kusan wata guda babu wanda yazo duabasu daga nan gida sai Muhammad wanda shima yadan dauke kafa cikin kwanaki biyu da sukayi a asibitin saidai shi ayyuka ne suka mashi yawa don yana da aikin gaggawa akan Jordan da yake shirin komawa, daman aikin da yaxo yayi anan ba dadewa zaiyi sosai, bangren abinci suna samu cima mai kyau dukda salima ce kawai mai cin don shi salim saidai drip da Karin jini, gaba daya salima ta sauya tayi kyau sosai, ta murmure, dama chan cutar tata harda yunwa ma sosai a jikinta, rana daya tana zaune wajen karfe goma salim ya soma bude idanuwanshi har ya bude su tarr akanta, lokacin tana zaune gefenshi bacci nadan fusgarta,jin alamun motsawa yasa ta farkawa idanunta suka sauka akan kaninta da da ya raege mata a duniya, da sauri ta mike tana hamdala, kallonshi tayi sosai ta kamo hannunshi tace ''salim ka tashi, wayyo allah nag ode maka alhamdullillah, bari na kira likita karka rufe idanunka salim gani nan zuwa kaji'' Futa tayi ta kira likta yazo da hanzari ya duba shi, jikinshi yayi kyau sosai saidai yan abubuwan da baza'a a rasa ba, cire mashi drip akayi da jini kafin nurses suka taimaka aka kwantar dashi akan kujera, gaba daya ya dawo kamar wani dolo dolo don yanda jikinshi yayi tsami, saidai hawaye da yake yi, da sauri doctor ya kalleshi yace ''meke damunka yanxu?'' runtse idanunshi yayi yanason Magana amma ina ya kasa, da sauri doctor yace ''calm down boy, its okay youre healing, now nod your head idan kana jin abinda nake fada'', gaba daya zuba mashi idanu sukayi har salima da nurses din wajen ahanakli ya soma juya kanshi, murmushi lilkitan yayi yace ''hes perfectly fine now, the operation is successfully,'' hamdala salima tayi kafin likta ya futa nurse ta tsaya ta zare mashi sauran drip din tare da bama salima daman kula dashi sosai, mikewa salima tayi ta debo ruba a rober da dan towel ta dawo gabanshi ta soma goge mashi jikinshi, murna take sosai, ganin dan uwanta daya rage mata a gabanta ya warke, saida ta gama tass kafin ta maida rubber toilet ta wanke towel din ta futa, yanda ta barshi haka ta same shi anan, zama tayi ta kura mashi idanu fuskarta dauke da murmushi shime kokarin maida mata yake saidai ya kasa don komai nashi yayi sanyi saida taimako, wunin ranar suna zaune ita da kaninta, salla kawai ke miqar da ita shi kuma saidai ya bita da idanuwa don har lokacin jikinshi bai saki ba, saida nurse ta dawo ta sanya mashi drip don bazai soma cin komai ba sai washe gari, ana saka mashi kuwa bacci ya daukeshi, sai a lokacin salima ta samu taci abinci tayi sallloli tare da godiya ga allah kafin ta kwanta a nata gadon gefen nashi, wani irin kuka ne yake ciyo ta, shikenan yanxu adda ta manta mu, wani ririn hawaye ne mai zafi ke sauka a fuskanta, ''adda kina ina kika barmu cikin kunshi, adda baki kyauta mana ba kin saba alqawari, kece gatan mu allah allah gatanmu shi kadai ke sonmu, shima ya Muhammad ya tafi ya barmu, kuka ne sosai ke ciyota kafin babci ya kwasheta mai nauyi sosai. 94-95 Abuja Nigeria taura estate… Alhaji kabiru dake zaune hannunshi rike da news paper ya kalli ammah yace.. "Kin tsaya min aka cirko cirko lafiya," kallonshi tayi daga sama har kasa kafin tace ''kabiru what's the meaning of this, menene wannan nake gani?, over 200 million has gone missing? How, kana menene haka acikin wata hudu, amanar dana barmaka Kenan, yanxu idan magajin wannan dukiya ya tambaya me zance mashi?"" innalillahi wa inna ilaihi rajiun… kallon ta yayi dakyau kafin ya soma Magana ''maryam karki manta ni mijinki ne kuma wannan dukiya da kike Magana akai ta dan uwana ne qanina, me kike nufi Kenan,ke koda ninayi amfani da kudin duk ban a gyaran companying bane, kinada hankali kuwa ko kin manta ni mijinki ne?, da kike Magana magaji magajin dukiyar shi ya damu ne da dukiyar da uban nasa ya bar masa ne? ya tattara ya zabi aikin ma kasar da ba kasar data haifesa ba, gaskia bansan ke butulu bace ba sai yau, duk crises din da company ya shiga da nasarorin da company ya samu ta dalilina duk baki gani ba sai qalilancin miliyan dari biyu da suka bace cikin hidimar kamfanin, maryama ki fta min a cikin daki bana son sake maimata magana''…shuru Ammah tayi wani irin hawayen baqin ciki na zubo mata, juyawa tayi da sauri tabard akin nashi zuwa nata, koda ta shiga wayanta ta zaro ta soma kiran amar, yau kusan kwana biyar Kenan basuyi way aba kuam wayanshi baya shiga, hankalinta ne ya tashi kafin ta soma kiran account manager da lawyer company, cikin yan mintuna kadan ya dauka,'' good afternoon madam ya gida ya iyali,'' bata tsaya amsa gaisuwan sa ba kafin ta soma Magana ''tun yaushe kudade suka fara bata daga cikin ccount din company ba tare da sanina ba, yanxu badan naje company ba bazan san ha;lin da ake ciki ba whats the meaning of all this, am I not the next kin of this company?'' cikin tashi hankali lawyer ya soma Magana ''im very sorry ma, wannan matsalar badaga mu bane daga cikin gida ne sanda abubuwan suke faruwa yallabai yace basai mun kai maki record ba sbd karki damu but komai is written akwai hard cop da soft copy of the slush fund, akwai waenda oga ne da kanshi ya buqa….'''bata tsaya sauraron sa bat ace send all the copies through my email, and let me warn you this should be tha last time, imform me on every transfersion don't leave a penny out of this, and don't do any transactionwithout my approval '''yess maa…, kashe wayan tayi wani irin baqin ciki na tunkaro ta what going on, meke faruwane, cikin watannin nan komai tabarbarewa yake, aman y agama lalacewa, ya koma wata turba daban wanda ta kasa gane mashi kwata kwata, baya dawowa gida sai wajen karfe uku kamar yanda ubanshi yake yi wanda da farko bata damu ba don haka yakeyi tun farkon aurensu wanda ya nuna mata duk sbd aikin da yake ne na ganin cigabansu gaba daya, wannan abu baya damunta kwata kwata don ita kanta bata sha awan kadaicewa da shi balle suyi wata doguwar rayuwar aure,saidai lamarin aman ne ke tsorata ga shima amar ta kasa gane mashi duk sanda sukayi waya tanaji a jikinta yana cikin damuwa yaqi fada mata kwata kwata gashi duk yanda takeso tayi ta dawo dashi kasarshi ta haihuwa yaqi, daman abunda take gudu Kenan gashi yanxu abubuwa sun fara sauyawa, innalillahi kawai take maimatawa, yanxu miliyan 200 sun fice haka kawai an rasa ta yaya,da sauri ta bude wayan ta ta shiga email dinta, da sauri ta danna official email din daga accountant din company kasa tsaywa tayi kwata kwata, da farko ta soma ganin yanda ribar kampanin take sauka duk karshen shekara kafin farkon shekara ya dago, duk shekara kusan shekaru bakwai, sannan a wannn shekara maqudan kudade ke fita daga cikin account din company, hankali tashe ta soma lissafi cikin wannan shekarun anyi asarar kusan 48% din kudin kamfanin, hankali tashe ta wurga wayan gefe, whats going on ne, dama chan kamfanin baya gaba ne ko akwai wata a kasa ne, don ita tabbas bata shiga alamarin company don komai yana hannun kabiru wato kanin mahaifin amar wanda take aure yanxu, kuma ya nuna yana kula da company sosai saida yana ina akeyin duk wanna abubuwan, ganin duk wannan zulumin babu inda zai kaita yasa ta miqe ta wuce toilet ta dauro alwala tayi sallah, tana idarwa tayi adduoi sosai akan sallaya sai wajen karfe biyar ta sauko kasa ta soma shirya abincin dinner data saba koda yauseh don bata bari yan aikin suna yi mata idan har mai gidan yana nan dukda sun samu sabanin hakan baya sakata tauye mashi hakkinsa a matsainsa na mijinta, da taimakon lantana ta shirya komai akan dining, nan ta zauna a kan lumtsatsun kujerun sitting room din gidan tana dan lazimi akayi sallama, da fara arta ta tace ''ah ah kodai anyi batan hanya ne mlm labaran,'' murmushi yayi harya karaso gefen parlor ya tsugunna har kasa ''hajiya ina wuni mun sameku lpy ya alamura,'' lpy lau malam labaran, yau kusan wata rabon mu dakai, ya kasuwanci ''…alhamdullahi hajiya ay akwai cigaba sosai, babu abinda zamuce saidai muyi maku godiya, allah ya kara daukaka ya kara arziki mai albarka '''ameen malam labaran bari akawo maka abinci kaci, lantana'' da sauri lantana ta fito sanye da riga da zanin ta wanke abinka ta daurin kallabinta irin nay an kauye ta kalli labaran kafin ta sauke kanta kasa cikin kunya tace ''ina wuni'' bai kalli inda take ba yace lpy sannu da aiki'' yauwaa ta amsa mashi tare da kunshe murmushin dake subuce mata, kallonta Ammah tayi tsaf ta karanci lantana da yananyin da take shiga da zarar labaran yazo saidai shi kwata kwata babu wannan yanayi a tattarare dashi, murmushi kawai amma tayi kafin tace ''kije ki zuboma mlm labaran abinci a kula ki hado mashi da ruwa dajuice mai sanyi'' da sauri ta miqe tace ''tohm hajiya''.. juyawa tayi tana dan satar kallonshi kafin ta wuce kitchen, juyowa hajiya tayi ta kalleshi kafin ta soma Magana ''ya wajen noma kuwa? Ina ta so naje naga yanayi wajen?'' Ay hajiya noma tayi kyau, yau insha allah zan tsinkayi fruits din da suka nune sai a kawo nan, masarace dai bat agama tsura ba amma ana samu san harharda akai akawo sosai, ni ina ganin ma har kiwo idan babu damuwa za ah dungayi hajiya''.. murmushi tayi don labaran mutun ne mai qima da mutuntawa dasanin ya kamata sosai, ''ay babu komai labaran zaka iya yin kiwo ma idan kana so ay babu damuwa, allah ya taimaka ''ámeen hajiya allah ya kara karfin ido nagode sosai.. Shuru ne yadan biyo baya kafin ta kalleshi ta soma Magana cikin dabara ''ni kuwa labaran baka sha'awar yin aure ne, gashi dai ka manyanta, inma kana tunanin muhalli ne, bakada matsala da wanan, indai zakayi ay babu damuwa'' dariya ya danyi kafin yace ''ay hajiya, allah bai kawo wadda ta dace bane, bayan wannan ma ina tsoron irin rayuwar da nayi abaya don har yanxu bansan ni wanene bane, ina gudun matsalar rayuwa, a rayuwar yanxu ma babu wanda zata iya auran wanda baisan kanshi ba balle yan uwanshi ko dangin shi, hajiya banida kowa ayanxu sai ku, amma ina rokon allah ya kawo ranar da komai zai zo min da sauqi har na samu komai ya dawo min''.. dariya tayi irin ta manya kafin tace ''toh allah ya akwo mana mafita'' ameen yaa amsa, cikin yan mintuna kadan lanatan ta dawo rike da plates shake da abinci da ruwan sanyi da lemo shima mai sanyi, miqewa hajiya tayi kafin tace ''zaka iya cin abincinka anan bari nace zama nadan huta'' godiya ya mata sosai kafin ta hau sama, ganin ta wuce sama yasa lantana saurin dawowa gefenshi tace ''malam labaran meysa kake tunanin babu wanda zai aureka,'' kallonta yayi tsaf ya tsuke fuska kafin yace ''ki koma wajen aikinki nagode da abincin'' mikewa tayi jiki a sanyaye ta wuce kitchen, tausayinta yakeji sosai, don tana da hankali sosai saidai bazai bata fuska ba don harga allah idan har ba tunaninshi ne ya dawo ba baya tunanin kara wani aure ko soyayya don baisan irin rayuwar da yayi a bay aba, kila yana da yaya ko mata, ko masoyiya dake jiranshi achan, saida yaci ya koshi ya kora da ruwa, yana nan zaune aman ya shugo gidan cikin shigarshi ta ta kakken yan iska, bai tsaya kallo ko wanenen a wajen ba ya soma kiran lantana ''ke yar aikin gidan zo'' da sauroi lantana ta zo cikin sauri tace gani alaji, kallonta yayi cikin kaskanci yace tattara abubuwan wajen nan, nan ba wajen mabarata bane bana son karikicen mutane anan parlor, labaran naji haka ya miqe salin alin yana mai allah ya shirya da halayya irin da aman, to shi wannan Kenan da yake gaban iyayen nasu inaga dayan kuma da baya kasar ma Kenan shi nashi iskancin qila yafi na wannan saidai allah ya shirya kawai, wucewa yayi wajen mai gadi suka sha hira kafin yayi mashi sallama ya wuce wajen gidan gona chan gangare y agama duk wani abu da yake kafin ya wuce gida, gida ne dan karami mai daki daya da bandaki, wanka yayi ya sauya zuwa riga yar shara shara ta san iska lokacin an kira sallan magrib yana idar da salla aka kawo wuta, futa yyi ya sayo biredi ya dawo zama yayi bakin yar katifarshi,tunani ya shiga yi cikin yan kwanakin nan yana yawan mafarke mafarke ya kasa fuskantar komai, jawo buredinsa yayi ya ci ya kora ruwan pure water kafin ya mike jin an fara kiraye kirayen sallar isha'I, janyo sallayan shi yayi kusada yar bakkwon kayanshi kafin ya tada kabbarar sallah, yana idarwa ya ninken sallayan, ya tura cikin bakkon kayan sa, ya shingida kan yar katifar janyo littafin da yake yawan zane zane yayi ya soma dubawa, yawanci zanen gida ne ya soma yi kafin yakai karshen zanen da yayi na mutane uku a zaune bakin bishiya sun juya baya hannunsu ruke da juna ta yanda ya zana sub aka tantance yanayin fuskansu don bayansu kawai yake iya zana wa, zanen ya tsaya mashi arai sosai, ya kasa gane komai game da zanen, yayi ne sanadiyan mafarke mafarken da yake yi kwanakin kusan kullum kuma mafarki daya ne akan hannaye da suke rike da junan shekara bakwai Kenan da loosing memory da yayi tun lokaci baya jin akwai abun daya rasa amma yanxu yana ji a jikinshi akwai abubuwan da yake missing sosai yana rike da littafin nashi har har bacci ya kwashe sa.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull