Kenza eBookz

Auren katin kasa complete - Chapter 23

Auren katin kasa complete - Chapter 23

Auren katin kasa complete Chapter 23: Auren katin kasa complete Chapter 23. Tana nan kwancewa galabaice aka kira sallar azahar, muke wa tayi ta wuce toilet…

4,335 words

Tana nan kwancewa galabaice aka kira sallar azahar, muke wa tayi ta wuce toilet ta dauro alwala ta fito ta tada sallah tana idarwa ta miqa kukanta gurin Allah. Tana shafawa ta fito tama rasa abunda zatayi, parlor ta sauko ganin Nadine na jera abunci ya sata tsayawa gefe guda, sosai Nadine tayi mamakin saukowanta don haka tace "Ma kina buqatan wani abu ne"? "No thank you" Rasa abun cewa tayi don haka ta hau sama, cire hijab dinta ta fara yi kafin ta zaune gefen gado ta doka uban tagumi. Tana nan zaune Nadine ta shugo dakin tace "Ma na gama lunch akawo abinci yanxu Ko zakici a kasa"

Da sauri amra tace "barshi zanzo kasan" Nadine na fita kuwa ta mike zumbur ta sauko kasa don dama neman damar sauka take, tana sauka kuwa ta zauna a dining Nadine tayi serving dinta, raraba idanuwa tayi tana kallon stairs saidai ganin babu alamun saukowanshi yasa ta maida hankalinta kan abunci dake gabanta don ko cokali daya bata kai baki ta ba, Haka nan ta dunga tura abuncin badon tanaso ba don daci Ma abuncin yake mata, tana gamawa ta wuce parlor ta zauna idanunta kan stairs din shuru shuru saida aka kira sallah asr ta mike ta wuce sama.

Amar kuwa tun bayan fitar ta ya chanza kaya ya fuce daga gidan sai wajen karfe 10 ya dawo gidan yana shigowa yazo giftawa ta sitting room ya hangota shingide kanta yadan karka ce alamun barci ya kwashe ta a wajen, kauda kanshi yayi ya kalli Nadine data bude mashi kofa yace " wake her up taje ta kwanta, and bring me just coffee" Yana kaiwa nan ya wuce sama, amra dake jin maganganunshi da Nadine sama sama cikin bacci, Tashi ta nadine ta soma yi tace "Ma kije ki kwanta" Cikin bacci amra tace "ya dawo ne?" "Yes ma" Shuru amra tayi takaici barcin daya kwasheta ne ya turniketa donta dade a zaune tana jiran zuwanshi, bata gama tunanin nata ba nadine ta fito hannunta dauke da mug da saucer, ganin tana nufa hanyar stairs yasa amra saurin cewa "ya buqaci coffee ne" Kallonta Nadine tayi tace "eh" Takowa amra tayi gabanta tace "kawo Zan kai mashi" Mika mata nadine tayi kafin ta mata sallama ya wuce nata dakin, saita natsuwarta tayi kafin ta tunkari hanyar sitting room din saman, Sai a lokacin ta karema parlor saman kallo, kayan alatun parlor yafi na kasa kyau sosai, gashi da girma sosai, an kawata shi da kayan zamani masu tsada, hanyar dazai sadaka da dakin tabi saidai tana zuwa daidai kofar gabanta ya soma faduwa, runtse idanunta tayi tare da cije lebbanta ta kwankwasa, saida ya dauka mintuna kusan biyar kafin yace "yea come in" Anatse ta soma bude kofar harta wangale ta shugo tare da rufe kofar ta tsaya daga bakin kofar kamar mai neman gafara tunda ta dago ta mashi kallo daya yana sanye da kayan barcinsa masu santsi, Riga da wando, wandon Ma bai Halle boturanba dan tana hango kwantaccen gashin kirjinsa, jin shuru yasashi dagowa, karar idanunshi suka sauka akanta, sanye take da kayan daya ganta da gamma dog uwar Riga saidai yanxu ta saka hula ta nade gashin nata saidai yana iya hango edges din sumar gaban gashinta, kauda idanunshi yayi gefe ba tareda ya sake kallonta ba ya tsuke fuska tam ya zauna kan gado ya wulla mata idanunshi da take jinsu suna yawo a jikinta. Dagowa tayi charaf idanunta suka sauka a nashi, da sauri ta janye nata, yanda ya tsura mata idanu ya sata jin tsayuwar na neman gagarar ta, dakyar ta tartaro sauran jarumtarta ta soma magana cikin sanyi "uhm, ga coffee din" Jin Shuru yasata dago kanta saidai this time around idanunshi a lumshe suke ya nade hannayenshi a kirjinsa, ganin yana shirin dago nasa idanuwan yasata saurin sauke nata kasa

"Nace maki Ina buqatar wani abu daga wajen Ki ne?" Da sauri ta dago jin tambayar da yayi mata, idanunta ne ya soma taro ruwa Bakinta na karkarwa tace "daa…man..naga zata kawo ne shine Nace ta bani na kaw….." wani irin mugun kallo ya Willa mata tare da tarar nunfashinta yace "Bana buqatan abu daga wajenki, now get out with that trash" Ya karashe yana nuna mata coffee dake hannunta

Hawayen ta dai basu daina ambaliya ba haka zalika bata fitanba saida ya daka mata tsawa arude Har tana harde kafafu ta fuce, tare da rufo mashi kofar, kukane sosai ya kufce mata, ta rasa wani tunani zatayi, ganin batada wani mafita yasa ta wuce kitchen, aje coffee din tayi ta sulale kasan tiles din ta fara kuka sosai mai ratsa zuciya

Goga kuwa tana futa yayi kwanciyar sa hankali kwance. Update!!!!!! Unedited

Tun bayan zuwan da yayi bayan ta farka bai sake lekowa ba Nadine ce ke kula da ita sosai ganin tana Shan wahala, gashi ta Kasa cin komi Sai ruwan tea, karshe Ma dai saida Nadine ta taimaketa wajen jika mata towel a cikin ruwan zafi tana gasa wajen daga kwance.

After an hour wani doctor ya sake shigowa saidai wannan babban mutun ne sosai, lokacin da yazo Nadine ce ta je dakin general don shaida mashi zuwan doctor, nan take yacemata ta kaishi dakin madam ya dubata, ba tare da bata lokaci ba ta koma ta shigo da doctor din tare da mashi jagora zuwa dakin amra koda suka shiga dakin tana kwance Duk ta galabaice sosai ta ji jiki ba kadan ba don haka ya samu damar tambyanta yanda take jin jikinta,dakyar ya samu tayi mashi explanation, nan take shima ya gano menstrual pain ne na mata saidai yayi mamaki yanda ta mashi bayani yanda take Shan wahala Harda suma ,duban ruwan da aka sa mata yayi ganin harya kare ya cire mata kafin ya rubuta mata magunguna ya bata tare da nuna mata yanda zata sha kafin yace ta samu ta watsa ruwa mai zafi sosai zataji dadin jikinta don alamu sun nuna she's weak, saida ya tabbatar she's stable kafin yayi masu sallama ya tafi. Da taimakon Nadine ta yaye mata bargon dake lullube a jikinta da Harya soma dan baci ta taimaka mata zuwa toilet, ruwa mai dumi sosai ta tara mata a cikin bath kafin ta futa don gyaran dakin, Nadine na fita a daddafe ta karasa gaban wc ta zauna tayi tsarki kafin ta shiga cikin bath tube din,ta dan dade sosai cikin bath tube din kafin ta futo ta sake watsa ruwa mai zafi, da taimakon Nadine ta dawo dakin daure da towel, lokacin har Nadine ta gyara ko'Ina Harda kan gado, ta cire duvet din da Zanin gadon ta sauya zuwa wasu sabbi ta kunna diffuser da oils masu kamshi sosai.

Ganin mikewa Ma dakyar takeyi yasa Nadine bude closet ta janyo mata wata rigar bacci daidai gwiwanta mai santsi pink color, hannun rigar bashida kauri dan siriri rigarma ba lallai takai kasan gwiwa ba, saida ta shafa mata turarenta dake kan dresser data gani kafin ta aje mata a gefenta,kallonta Nadine tayi Ganin ta dafe kanta "sannnu ma, ga kaya nan ki saka bari ba kawo maki tea ki samu Kisha tunda kin Kasa cin abunci."

Dagawa tayi idanunta sunyi luhu luhu sunyi ja dakyar ta iya furta "thanks Nadine" Nadine na futa ta janyo rigar ta saka, kamar Nadine tasan bata son kaya masu nauyi idan tana period, tafison ta dunga jinta freely babu takura.

Koda Nadine ta dawo hannunta dauke da tea saida ta zuba mata idanu, ganin wani extra ordinary kyau da take dashi, tana da irin kyau din da Duk kyan fuskanta jikinta yafi daukan hankali. Karasowa tayi tare da mata sannu ta bata tea din da zafin sa, dakyar amra takai tea sun bakinta tayi sipping, bata wani sha da yawa ba kadan tasha jin amai na zuwan mata yasata ajewa.

Wajen karfe sha biyu na dare Nadine na tare da ita tana bata kulawa, ganin bacci ya kwasheta yasa nadine rufa mata bargo ta rage mata gudun ac tare da rage hasken fitilar dakin ta rufe mata kofan ta wuce daki don ta samu ta huta itama, don wunin ranar tana tare da ita a dakin, wasu daga cikin ayyukanta ma bata samu ta karashe ba donma babu wani ayyuka masu yawa, abunci ne wanda yawanci ma basu fiye ci ba, idan anyi ma ba a ciba securities ake kaiwa,Sai kuma dan gyare gyare wanda takeyi safe da yamma, ayyukan ma Allah ya taimaka tayi na safen na yamma ne bata samu tayi ba dalilin rashin lpy madam wanda takema kallon kanwa a wajen oga don alamu basu nuna matarshi ce ba.

Dakin ta na masu aiki ta wuce wanda zaka rantse dakin baqi ne, daki ne babba da gado Harda carpet da wardrobe sai toilet shima dayasha abubuwan zamani, koda ta shiga dakin kwanciyarta tayi itama.

Karfe daya daidai ya aje laptop dake kan cinyanshi tare da janye duvet din daya rufe kafafunshi dasu, mikewa tayi tsaye tare da yin miqa, ciki natsuwa ya zura bedroom slippers dinshi tare da gyara riganshi da buttons din suka bude, fitowa yayi daga dakin cikin kamewa ya sauka kasa, tunda ya sauko second floor ya rasa dalilin saukowan nashi, maida idanunshi yayi ga kofar dakin ta kafin ya juya ya sauka kasa, hanyar kitchen ya nufa wanda ya zamo mashi rana ta farko daya tako ya shigo kitchen din, ko ina tsaf tsaf babu kazanta, sai kamshin freshner dake Tashi harma da dan sanyi sanyin ac dake kune a cikin kitchen din, kunna duka lights din kitchen din yayi don guda daya ne a kunne, bin ko'ina ya soma yi da kallo, kafin ya tako gaban katon fridge freezer dake a hade ya cinye kusan Rabin bango daya, budewa yayi ya zaro bottle water guda daya mai sanyi, kafin ya rufe fridge din ya balle marfin ya kafa bottle din a bakinshi, yanda yake Shan ruwan Ma a gayance da natsuwa kamar basarake,ahankali ruwan ke sauka daga makoshinsa Har wani dan zufa ke sauka daga wuyanshi wanda yake looking so sexy a tsaye, amra dake saukowa kamar wadda aka zare Ma laka fuskanta gwanin ban tausayi lokaci guda Duk ta dan fada kadan fuskanta fayau, tun bayan futar Nadine bata wani dade ba ta farka jin ciwon na shirin dawowa, saukowan datayi Ma tazo neman ruwan dimi ne don tasha ko zata ji dan dama dama. Tun daga bakin stair ta fara jin kamshinsa saidai bata kawo zata ruskeshi ba a wannan lokaci, kai tsaye kanta a kasa ta karaso cikin kitchen,tan shiga kamar ance dago karaf idanunta suka sauka akan fuskanshi zuwa makoshinsa, yanda yake Shan ruwan Ma ya shagaltar da ita don mamakin ganinsa a kitchen din ta somayi, cikinta ne yadan murda daya sata damke kasan marar tata tare da dan dafe kan marble din kitchen island tayi yar Kara "arhhhhhshhh"

Yana nan tsaye bottle din na bakinshin Baiji alamun shugowanta ba sai yar kara data danyi, sauke idanunshi yayi akanta, tun daga sama Har kasa ya kafa mata idanu yana kallonta, idanunshi ne yayi magneting waje daya kyam kan nipple dinta da suka mashi hello daga nesa don sosai suka fito daga cikin rigar tata nan take ruwan daya sauka makoshinsa ya soma sarqe mashi a maqoshi Har idanunshi nayin jaa fuskarma ta soma jaa abunka da farin fata, sauke bottle din yayi ya kauda kanshi gefe kafin ya maida bottle din bakinshi ya shanye sauran with just a sip, shida kesha a natse Sai gashi natsuwar ta kufce ya kwankwade gaba daya lokaci guda ya rufe bottle din, tare da dan sauke nunfashi da huci mai zafi, cikin ranshi ya soma magana "uhmm damnnn" Juyowa yayi azafafe ya zuba sake zuba mata idanunshi kamar yaga abunci na farko yanason karantar asalin ciwon nata saidai bai gane ba koda doc yace mashi monthly menstruation da mata keyi takeyi, Yadai san period da mata keyi Duk wata saidai cramps dinne ya Kasa gane daga Ina yake, ta wani bangaren yake,da wannan yake kokarin son hana zuciyarci tunanin da take shirin bijiro mashi don tun kallon farko da yayi mata gabanshi yayi mugun bugu lokaci guda, kamar wanda ake fusga ya tako zuwa gabanta dan nesa da ita kadan ya tsaya tare nade hannayenshi a kirjinshi dake a bayyane don rigar a bude take, kallonta yayi tsaf irin kallon kurulla dinnan, tundaga kanta da babu hula, curly gashinta a bayyane sun kwanta lub lub sun nannade, gaban goshinta da edges din gashinta sun kwanta sakamakon zufa data tsatsafowa mata saboda jin zafin ciwon marar nata, Tunda ta dago ta mashi kallo daya bayan sun hada idanu ya kauda nashi gefe bata sake gigin dagowa ba don kallonshi, saidai har yazo gabanta tana jin takunshi har cikin xuciyar ta, runtse idanunta tayi gam lokacin da ya tsaya dan nesa da ita tana jin yanda idanunshi ke yawo a jikinta, lokaci guda taji gaba daya she's so uncomfortable don jikinta is expose gashi babu bra kwata kwata a jikinta,rigar ma is not helping the matter don tana da santsi sosai ta manne mata wanda ya sanya nipples dinta fitowa sosai don shatinsu a bayyane yake cikin rigar, Dayan hannunta dake gefe tayi saurin daurawa wajen kirjinta Dayan kuma data dafe island dashi kamar zata fasa marble din donta damqe shi sosai, idanunta a runtse yayi taku daya ya karaso gabanta saidai da dan tazara sosai tsakaninsu,tattara natsuwarshi tayi cikin kamewa ya soma magana fuskannan dai bazaka taba tantance ta, "How are you feeling now?" Babu zato taji tambayan nashi, don haka ta Kasa dagowa don gaba daya kunya ta gama lullubeta dukda rashin lafiyan da takeji hakan bai hanata jin kunyarba, don tana da kunyar jikinta sosai, Kanta a Kasa muryanta ma baya futa sosai tace "Alhamdulillah!!"

"Raise your head" yayi commanding dinta Dan daburcewa tayi don kusan bata gane me yake nufi ba still kanta na kasa " I don't want to repeat my self" ya fada adan azafafe, Kunqukuni ta soma yi,fuskanta adan shagwabe ta dago ta kalli gefe,hakan datayi kamar ta ingizashi ya sake magana a kausashe "Heyyyy look up here" Ya sake fada still hannunshi na nade a kirjinshi. Kamar yar maye haka ta maido da fuskanta kanshi tana dan kunkuni don bata son hada idanu dashi, ganin yana shirin magana yasata saurin kallon idanunshi saidai ko second batayi ba idanunshi suka rinjayi nata don gaba daya wani irin kwarjini yake mata sosai. Kokarin sauke nata idanun tayi saidai irin kallo daya zabga mata ya sata sallama mashi ta tsaida idanun akanshi, tunda ta zuba mashi manyan idanunta da ke nan kamar mai jin barci Har wani lumshesu takeyi tana budewa eyelashes din na kwanciya sun dan jike dalilin kukan datayi, take yaji tsayuwansa ma na neman gazawa, da sauri ya dauke nashi idanun daga kanta ya gyara tsayuwanshi kafun yace "me kika futo yi" Da sauri kamar wadda ke jiran tambayar ta bashi amsa "ruwa nazo dauka" Dan tabe baki yayi kafin ya raba ta gefenta ya fuce daga kitchen din cikin kamewa. Yana futa kuwa ta sauke nauyyayiyar ijiyar zuciya wadda saida ya jiyota kafin ya bar kitchen din gaba daya. Saida ta dauka kusan minti biyu kafin ta daidata natsuwarta ta wuce wajen da ake ajiye mugs, ruwan zafi ta deba daga diapenser dake jikin fridge din kafin ta fito ahankali jin yanda murdawan keyin gaba sosai, bata tsaya duban sitting room din kasan ba don ko'ina a kashe yake babu haske Saina wajen entrance dake hasko parlor kadan, stair ta fara takawa atsanake, taku daya biyu tayi bata kaiga taku na uku ba taji ciki ta ya Kara murdawa, cikin hanzari ta dafe handrail din stair din tare da da yin yar Kara don yanda ta razana dajin zafin ya sa ruwan mug din ya dan fantsala akan skin din hannunta duqawa tayi ta dafe mararta tana jin wani irin azaba, Amar dake tsaye nesa da ita don yana zaune a sitting room din harta fito yana hangota saidai ita bata ganinshi, harta hau stairs da tsayuwan datayi Duk akan idanunshi Har zuwa lokacin da tayi yar karar, tare da dan duqawa kadan. Har inda take ya tako ya tsaya dan nesa kadan kafin yace "get up" Adan furgice ta jiyo ta ganshi tsaye don batayi tsammanin ganinshi ba don Duk a tunanin ta ya wuce sama, miqewa ta soma yi ahankali kafin ta daga kafa daya ta kwala yar kara, tabe baki yayi don ganin kamar Ma abun nata da raki da shagwaba baiyi wata wata ba ya sungumeta gaba daya, Sai jinta tayi a sama, tsoron daukan da yayi mata a bazata ya sata saurin kankameshi sosai wanda hakan saida ya sashi dan tsayawa for a moment jin lafiyarshi ta dan motsa, daidai ta natsuwarshi yayi kafin ya haura saman da ita, Har bakin gadon ta ya sauketa bai tsaya kallonta ba ya juya ya fuce daga dakin, yana futa kuwa ta sauke ijjiyar zuciyar don tunda ya dauketa gabanta ke faduwa, bayan Yan mintuna kadan Sai gashi da wani mug daban a hannunshi, karasowa yayi gabanta ya miqa mata, bai ce mata komai ba ita ma tana ganin yana miqa mata ta karba tare da cewa "thank you!" Ganin ya tsaya bai motsa ba Sai nannade hannayenshi dayayi a kirjinshi gashi ya zuba mayun idanunshi dake sata jin wani iri ya sata kauda kai gefe ta soma kwankwadar ruwan ba tama jin zafin ruwan harta shanye tass ta sauke nunfashi still hannunta nakan kirjinta tana kokarin rufe kirjin, shi mamaki Ma yake tana da kananun shekaru take da jiki haka, tsaki yayi ganin yanda take kare kare kafin yace "what are you hiding?," ya fada yana hade rai tamau Saurin dagowa tayi ta zuba mashi idanu chan kuma ta sauke still hannunta na kan wajen, "babu komi" ta bashi amsa kai tsaye Wani irin kallo ya zagba mata mai wuyar fassara wanda ya sata daburcewa ganin yanda ya bata rai sosai. Kamar wata munafuka haka ta sauke hannun ta kadan ta kare wajen yanda bazai gani ba. Oga dai gyara tsayuwanshi yayi ya kura mata idanu ya cigaba da tambayarta "Ina kike jin ciwon" "Kasan mara ne" ta bashi amsa Adan shagwabe don tama manta dawa take magana, abunka da mara lafiya da neman attention Kamar ya karanenceta kuwa ya sake tambayan "wajen Ina ne let me see" Kamar doluwa haka ta mike tama manta da kare Karen kirji da take ta tako gabanshi tana turo baki a shagwabe ta daura hannunta kasan shafaffen cikinta wajen mararta ta sunkwi da kai tace "nan kasan" Tunda ta mike ta dunfaro gabanshi kamshinta ya bugeshi sosai Har cikin hancinshi, Dukda da yar tazara tsakanin su saida ya tako gab da ita sosai, itako da kanta ke Kasa tana kokarin nuna mashi Sai jin nunfashinsa tayi daidai fuskanta yadan duko gabanta sosai ya sauke mata lafiyayyen nunfashinsa mai zafi akan fuskanta, abunda yafi tada mata hankali shine jin saukan lausansan tafun hannun shi akan mararta dake cikin yaloluwar rigar da ita da babu Duk daya, da sauri ta daga idanunta tare da sauke wa kanshi, nan take tayi arba da tashi fuskar daidai tata Har hancinsa na neman gogar nata, tuni nunfashinta ya tafi wucun gadi, don kamewa tayi kyam ta Kasa motsi, hannunshi kam yana nan kan mararta shima ya Kasa daukewa don wani irin shock yaji ya durar mashi take ya gane cewa lafiyar ta dawo inma bata gama dawowa ba kiris ya rage, shafa wajen daya danyi ne ya maidota hayyacinta da kuma muryarshi dake dauke da kamshin mint daga bakinshi "Daidai nan ne?" Kamar wawuya ta bude baki tace "uhm" Kara dan matsa wajen yayi yace "uhmmmm" Jikinta ne ya soma kyarma Da sauri ta danyi Kara tace "zafi tare da saurin yin baya ta koma ta tsaya tana sauraron yanda zuciya ta ke racing sosai, tabe baki yayi Harda yar guntun tsuka yace "go back to sleep" Batayi wata wata ba ta hau kan gado ya bita da idanu harta janyo duvet ta rufa, jin alamun bai motsa ba yasata bude kanta tace "good night yaya" Bai tsaya amsata ba ya juya tare da janyo kofar ya rufe mata Yana futa ta sauke ijjiyar zuciya sosai tana mamakin yanda ya sauko yau, saidai bata sama kanta hope din haka zasu dinga tafiya ba don baka gane mashi kwata kwata. Dakyar barci barawo ya kwasheta dukda idan ciwon ya nuqurquso ta farkawa take yi idan ya lafa kuma ta koma.

Shima gogan yana shiga daki ya hau kan gadonshi ba tare da tunanin komai ba yayi kwanciyarshi saidai barcin baizo mashi ba Sai gab da sallar asuba tunani iri iri na yawo a kwakwalwarshi saidai yanda yake da dakewa yasashi kawar da komai kamar ba komai ba.

Washe gari Monday da sassafe ya fuce daga gidan saboda wani urgent investigation da zasuyi shida lieutenant asad, koda ya fuce Nadine ma bata fito ba,

Ahankali amra soma bude idanunta da sukayi mata nauyi sakamakon baccin data samu gab da sallah asuba, Mika tayi tare da adduar tashi daga bacci, ayanxu ciwon cikin nata ya dan ragu don sama sama take jinshi, gashi maganin datasha ya sata jin kwarin jikinta, kafafunta ta sauke kasa ta wuce toilet, bata tsaya komai ba ta fara watsa ma jikinta hot bath, tana gamawa a gurgurguje tayi brush ta fito don yunwa take ji sosai, Riga mara nauyi ta zaro doguwa daga cikin kayanta tare da set din bra da pant kafin ta fara shirywa ,saida ta feshe jikinta da turarenta,bata tsaya shafa mai ba ta nannade gashinta ta tura cikin hula ta fuce daga dakin, Kasa ta sauka ganin Nadine bata parlor yasata wucewa kitchen direct, tana shiga kuwa ta hangota tsaye tana goge gogen gas da alamu bata dade da gama amfani dashi ba, cikin girmamawa suka gaisa kafin ta tambaya jikin ta. " how are feeling now ma?" Nadine ta tambaye ta fuskanta dauke da murmushi "Alhamdulillah Nadine naji sauki" amra ta bata amsa "Na gama breakfast yana dining, daman na bari na gama ayyuka ne Saina duba ko kin Tashi don dazu wajen 7 bayan sir ya futa na leko don naga ko jin Tashi sainaga baki Tashi ba" Nunfasa amra tayi kamar bazatace komai ba chan kuma tace "uhm shi ya karya ne?" "No bai karya ba, lokacin daya futa ma ban dade da futowa ba, nima ban sameshi ba don saida naje kaima security da driver abunci naji sun futa shida driver da sassafe.

"Oh okay,Yau me kika dafa mana nadine" amra ta tambayeta fuskanta dauke da murmushi Murmushi itama Nadine tayi tace "ma, as asual dai chips ne Sai egg sauce da chicken pepper soup" Shuru amra tayi kafin tace "Bari naje dining din, sannu da aiki" Tana kaiwa nan tasa kai ta fuce nadine ta bita da ido tana murmushi tace "wannan yarinya badai kyauba ga fara'a saidai shi yayan nata baida fara'a kamar ita"

Zama tayi a dining ta zuba chicken pepper soup a bowl daidai cikinta kafin ta hada tea mai zafi, ba laifi taci da dan yawa, kafin ta sha tea din don shi tafi buqata, tana gamawa tayi handala ta goge bakinta ta wuce sama, magungunan da doctor ya bata ta ballo tasha kafin ta zauna gefen gado ta janyo wayanta, line din haifa ta soma kira, baya shiga tun last time da sukayi waya ta daina samunta, haka zata dinga kira amma baya tafiya kwata kwata.

Amar… Tunda ya karaso Nigerian army headquarters ya wuce direct office din lieutenant asad, tundaga gate kowa yasan anyi babban baqo,Duk zuwan da zaiyi Sai an zuba manyan securities wanda baya son haka sbd ba official zuwa yyi ba don cikin sirri suke yin aiki da taimakon asad saidai in Har zai shiga headquarters na sojoji dole Sai Ansan da zuwan shi, shiyasa yawanci idan zasuyi meeting akan investigation da sukeyi yake saka lieutenant asad ya nema masu waje mai sirri, wannan zuwan Ma da yayi zuwan gaggawa ne kuma dole ya shigo cikin headquarters don abun ya shafesu. Yana iso wa ya wuce direct office din asad, yana shiga kuwa ya miqe suka gaisa cikin girmamawa kamar yanda suka saba, shima asad office dinshi babba ne kamar ko wani office saidai kuma bazai taba Kamo na general gabaki daya ba lols.

Tunda ya fara ma asad bayani, baiyi wani mamaki ba don abunda yafi haka Ma za a samu anan nigeria, gashi sunada report dayawa akan human trafficking da akeyi da yawan futar haramtarciyar kwaya wanda an Kasa gano daga inda take, gashi tana kisa musamman wa kauyuka sbd yawanci waste din drugs din rafi ake kaiwa ayi dumping inda baza ayi tsammanin ,mutanen kauye kuwa basu damu ba shan ruwan rafin su sukeyi wanda daga karshe su dinga cututukan da ba a gano ta yanda suka samu.

Nunfasawa asad bayan ya gama sauraron bayanin shi hannun shi nade a kirjinshi yace "Oga nifa bazanyi mamaki ba,we have thousands of report akan human trafficking, yanxu haka da nake maka magana Akwai badge of yaranda went missing, Mun Kasa gano komai, amma yanxu ka kirashi muji idan zai samu turo mana evidence koda hoton yaranda aka tafi dasu tunda yace maka ya tabbatar Yan nigeria ne Sai muyi comparing mu gani daga nan zamu samu damar tracking ta inda yaran suka bace" Shuru Amar yayi kafin ya dauka wayanshi ya soma dialing number hammam.. Ringing daya biyu ya dauka " hey dude" amar ya fada yana relaxing a kan kujeran da yake zaune da take facing asad "I'm so surprised ka kira, bansan da wani baki zan baka hakuri ba, I'm so sorry dude" hammam ya fada daga chan bangaren Nunfasawa Amar yayi kafin ya saka wayan a speaker "It's okay dude, naji dadi da kayi uniting da mahaifiyarka" Murmushi hammam yayi yace "all thanks to you, ta dalilinka na gano komai and I promise you yanda na fada maka I will make sure Mun kawo karshe azaluman nan"

"Insha Allah" Amar yayi saurin fada mashi kafin ya cigaba "Now I need your help, naga email din da kayimin akan abubuwan daka gano"

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull