Auren katin kasa complete - Chapter 3
Auren katin kasa complete Chapter 3: Auren katin kasa complete Chapter 3. Washe gari, kwata kwata amra ta susuce, bata cikin nutuswarta, koda taje aiki…
4,420 words
Washe gari, kwata kwata amra ta susuce, bata cikin nutuswarta, koda taje aiki babu abinda ta iya yi kwata kwata, gashi ayyukan sunyi mata yawa don hafiza tunda ta tafi bata kara dawowa ba, haifa ce kwai ke taimakonta sosai wajen wasu abubuwan, yanxu kam ta yanke hukuncin duk yanda za ayi saita san yanda tayi ta kawo qannenta kusa da ita kuma zatabi ko wace irin hanya ce.
Zama sukayi ah café, wanda kwata kwata amra ta kasa cin komi sai haifa ce take dan turawa itama bata cikin kwanciyar hankali ganin yar uwarta cikin damuwa, hakan yasa ta zuba mata ido kawai sannan tace ''ámra I have a solution but I don't know if its going to work,(inada shawara saidai bansan ko zata yiwu ba), kinga dai visa ki saura shekara biyu kuma kince baki gama tara bashin uncle ba ko?..girgiza mata kai amra tayi tana fuskantarta da nutsuwa .. anatse haifa ta cigaba ''babe why not ki nemi katin kasar nan sbd ki kawo kannenki kusa dake'' jin wannan batu yasa amra yin shuru chan tace ''wannan ce kadai hanyar da zan iya kawo su kusa dani haifa??'''girgiza mata kai haifa tayi sannan ta cigaba ''but babe samun katin kasa ah uae shine abu mafi hatsari musamman ma ke mace yar Africa domin hanyoyin da akebi asamu are not legal, kuma akwai risk babba''..kallonta amra tayi don a yanxu kam bata jin akwai abinda bazatayi ba akan qannenta, gyara zama tayi sannan tace ''haifa all the risk are not important to me now, ni yanxu damuwa na qannena ne, so I can go to any extent don na taimaka masu, kuma wannan katin kasar shine kawai solution ayanda nayi tunani yanxu.
Nunfasawa haifa tayi sannan tace ''okay idan har kinga zaki iya ni kuma zan taimaka maki, akwai wata secretary data tabaa aiki karkashin abu na, itama kusan issues dinku daya saidai ita iyayenta ne wanda suke cikin mawuyacin hali wanda hakan yasa tayi AUREN KATIN KASA…''jin haka yasa gaban amra faduwa ana wata ga wata, dakewa kawai tayi ta cigaba da sauraron haifa, ''yanxu zan kira abu don ya bani number nasan yana dashi har yanxu, idan na sameta zan roki ganinta sai muyi fixing date between yau da gobe don mu ganta yanxu dai ki kwantar da hankalin ki komai zaizo da sauqi kinji'' Saida haifa ta gama tukunna tadanji sauqin zafin da ranta keyi mata sannan sukaci abinci suka koma office. ✍️✨***Auren Katin Kasa ***✨✍️ (Unexpectedly falling❤️🇦🇪)
Story and written by: QueenMarh👸🏼
Paid book 📚
Chapter 56-57
Amar kuwa satinshi guda a asibiti, tun bayan abinda ya faru tsakaninshi da hafiza likitanshi ya sashi on a bedrest.
Wato bayan fitarshin nan dakyar ya shiga motor sbd wani irin masifar dripping da ya dinga yi, gashi yana da low sperm count, hankali atashe ya shiga yace ma m5 ya wuce dashi asibiti, bayan sun isa likita yayi mashi scanning ba karamin asara ya samu ba don kwayayen haihuwanshi duk kusan masu amfanin sun zube, aranshi kamar yayi kuka, dama already doctor yace ya dinga lura sosai, yanxu gashi dan sakacin da yayi ya jawo mashi asarar mai yawan dai zai iya jawowa bazai taba haihuwa ba harya mutu, wanda haka ba karamin tashin hankali bane agareshi domin yana qaunar yara sosai ba kadan ba.
Ganin yanda result dinshi ya fito with bad news yasa likita ya bashi bed rest, wanda yau kwanan shi biyar cur kuma ayau za a bashi sallama. Zaune yake gaban likitan nashi wanda ya soma bayani kamar haka ''mr amar I'm so sorry to say this, but this time around your condition is worse and I'm afraid you may not be able to …but we did a second test after your bed rest so we''ll see how it turns out,..kwankwasa kofar akayi wata nurse ta shigo hannunta dauke ta file ta mikama doctor sannan ta fice, amar kuwa wanda tunda doctor ya fara bayani yayi resting kanshi wani irin azaban sara mashi yake ga wani sabon bad news ya sashi kasa cewa komai, saida yaji muryan doctor tukunna ya bude idanunshi ya kallesa..''íncredible, mr amar,nayi mamaki sosai, wannan bedrest ya taimaka yayi stabilizing jikinka sosai, and ina maka albishirin din cewa kana da 10% chance na samun da ko ya, so ina baka shawara yanxu ya kamata kasan yanda zakayi,because daga wannan bana tunanin zaka samu chance kamar haka, sanan akwai medication da zan baka ka dunga amfani dasu,'' godiya kawai amar yayi mashi sanan ya wuce motor …tashin hankali, koda ya shiga motor kanshi ya kulle ya rasa tunanin da zaiyi, ya rasa mafita, dole yasan yanda zaiyi don bazai taba yarda yayi loosing wannan 10 percent dinba,ahankali ya zaro wayanshi yayi dialing hammam, yana picking ya soma Magana ''hamman I need you now, please come to my pent, its urgent.'' Yana kaiwa nan ya kashe yaja motor har penthouse dinshi. Yana parking motor hammam itama tana parking, saida suka yi musabaha sannan suka wuce cikin penthouse din atare.
Zama sukayi a kan daya daga cikin set of chairs din sitting room din suna facing juna, Pablo ne ya shigo cikin parlorn ya gaishesu atare sannan ya aje masu abubuwan sha masu sanyi, godiya hamman yayi mashi, shiko amar ko kallon wajen shi baiyi ba, saida Pablo ya fuce kafin hammam ya kalleshi yace ''dude what's the problem, duk hankalina ya tashi, menene matsalar?'' runtse idanu amar yayi yana jin zafin abin sosai aranshi sosai saida ya dauka almost 2mins kafin ya fara Magana cikin natuswa'' I just came back from the hospital,akwai abinda ya faru last week, I don't even know where to start, but that's not important now,'' kallonshi hammam yayi sbd ya qagu yaji mey ya faru sannan yace ''dude just say it anyhow''…komawa amar yayi ya jingina da kujera sannan ya jawo file din daya aje gefenshi ya miqa ma hammam, da sauri hammama ya karba ya fara budewa, saida ya bude file din ya karanta tsaf sannan ya soma Magana ''amar I don't understand, 10 percent kuma, explain it to me so that I can understand you better''…bude idanunshi yayi wanda sukayi jaa sosai, jijiyoyin kanshi duk sun fito sosai yace ''yess hamman I have just 10 percent in me, and I can't have children if I loose those percentage,''…magana hammam ya soma da fada fada yace ''what!! Oligospermia!!!!!kaga matsalarka Kenan, tun last year nace maka, we should find solution tun kafin abin ya zama worst, shin kasan male infertility yayi destroying mutane da yawa, naka da sauki ma tunda ance zaka iya haihuwan, amma yanxu with 10 percent chance idan kayi loosing komai fah, gashi kana da saurin feelings, waima tsaya how did dis happen? I thout last time da mukaje kaga doctor ya baka magani kuma naga dai kai ba neman mata kake''……..runtse ido yayi baya ma son tunanin abunda yayi causing duk wannan matsalar tashi, kallonshi hammamn ya kumayi yace ''amar talk!!...dagowa amar ya sakeyi ya kalleshi yace, ''dude I just don't want to talk about it, yanxu solution kawai nake nema, I don't even want Amma to know about this because she will be so disappointed, cos tun ba yanxu ba take so nayi aure ta samu jikoki but na hana hakan faruwa,'hammam please tell me what to do, kaina duk ya kulle''….shuru hammam yayi yana nazari sannan yace ''solution daya ne kamar dai yanda na fada maka last time, you just have to get married tunda dai bazaka haihu ta hanyar zina ba,'' shuru amar yayi yana nazari sannan ya kalleshi dakyau yace ''but..but..'' katseshi hammam yayi da cewa''but you don't want to get married outside your culture ko?, I knew that's what you want to say, well wannan kuma ya rage naka, solution dai daya ne, get married fine.'' Gyara zama amar yayi yana fuskantar hammam ''kai maysa kake haka ne, kasan cewa niba kula mata nake ba'' yatsine fuska yayi sannan ya cigaba ''kuma kasan cewa bazan iya auran wadda ba culture na daya da nata ba, I mean ni bana son auren larabawa irin ku, kai kasan yanda auren culture ku yake, complications din akwai yawa, on top of that ma, kai kasan bakwa auren bare and bayan wannan ma,kuma karkayi tunanin Nigeria, don I don't know how on earth you expect me to find someone in just couple of days to bear child for me, bama wannan ba kasan yanda nake da kyankyanmi I cant just share bed with anyone''…kallonsa kawai hammam yake baki galala yana mamakin amar da yanda yake magan yana tabe baki kamar bayason maganar ma, girgiza kai kawai hammam yayi ya miqe yace ''you are not serious dude, ni zan tafi duk sanda ka shirya then call me, ina nuna maka gabas kana yamma, inaga baka fuskanci me 10percent din nan ke nufi ba, inda ka gane tashin hankalin cikin haka da ko begger ka samu zaka aura ka dura mata sauran abinda ya rage maka''..yana kaiwa nan ya sa kai ya fice, takaici ne ya turnike amar, tabbas abinda ya fada hakan ne ba karya yayi baa, saidai baya tunani zai iya yin haka, dakinsa kawai ya wuce ya watsa ruwa mai dumi sannan ya saka shorts da farar tight vest ya kwanta.
Tunda amra sukayi maganar katin kasa da haifa hankalinta yaqi kwanci, duk tunani ya dabaibayeta, abu daya ne ya tsaya mata rai, auren da taji haifa tace secretary din abu tayi, wanda batajin zata iya wannan. Wunin ranar adaki tayi shi, babu abinda take sai zullumin jiran call din haifa.
Haifa kuwa tana komawa gida ta kwanta baccinta dukda damuwar amra ta saka ta a gaba , saida tayi baccin kafin ta yi wanka ta shirya cikin kayan shan iska sannan ta wuce wajen abu, nan ta sameshi yana zaune yana riqe da newspaper, gaishesa tayi sannan suka dan taba hira, daga bisani ta tambaye shi secretary dinshi, kallonta yayi da mamaki yace wace secretary din, bata boye mashi komi ba ta kwashe duk labarin amra ta fada mashi, jinjina kai yayi da tausayin amra sannan yace ''gaskia na tausaya mata don qawar Kirkice a wajen ki haifa, but ina son ku sani nemen katin qasa is a long process and it takes years kafin mutun ya samu, but zan baki contact info na secretary jemima tunda itama tana daya daga cikin wanda sukayi applying kuma suka samu sai tayi maku bayi''..godiya sosai haifa tayima abu kafin ya bata number. Bayan ta koma dakinta ganin dare yayi yasa ta fasa kiran jemima a lokacin saita bari sai gobe da safe.
Washe gari kuwa Sunday, da matsanan cin ciwon kai haifa ta tashi, bayan tasha magani ta kwanta sai wajen asr ta tashi, koda ta tashi kan nata ya lafa, abinci kawai ta nema sannan ta lalubi wayanta domin kiran jemima,tana bude wayan taga missed calls birjik a wayan, daga wajen amra da hammam, saida ta fara kiran hamman tukunna suka sha hiransu ta masoya sannan sukayi sallama. Amraa na ganin call din haifa wadda daman tunda ta tashi take zullumin kiranta yasa tayi sauri daga wa tace "haif, ina kika aje wayanki, inata kiranki baki dauka.'' Da sauri haifa ta soma mata Magana ''I'm so sorry habibty, yau da ciwon kai na wuni,'' shuru amra tayi tana sauraron bayani, jin hakan yasa haifa cewa ''yauwa ban fada maki ba,na samu contact din secretary din abu jemima, yanxu haka ma muna gama waya dake zan kirata,''murna fal ciki amra tace ''bari na kashe saiki kirata, please duk yanda kukayi ki kirani immediately'' kit ta kashe.. murmushi haifa tayi don ta ji yanda amra taji dadin wannan batun samun contact din jemima.
Zama tayi gefen gadonta sannan tayi dialing contact din jemima, saida tayi mata kira biyu ana uku tayi picking ''hello, this is jemima how may I help you'', jin haka yasa haifa saurin cewa ''hii jemi this is haifa abdul-samad shuraim,'' jin sunan haifa yasa jemi saurin cewa ''ohh hy haifa, how are you?, how's sir abdulsamad, and family?''……gaisawa sosai sukayi ta mutunci kafin haifa ta soma mata bayanin kiranta da tayi, jimm kadan jemi tayi sannan tace ''I really don't want to ever talk about my own experience but I can't say no to abdulsamad family, so fix a lunch day and forward the details to my sms, lets meet up tomorrow by 4pm,'' jin haka yasa haifa saurin cewa thank you so so much jemi, I will surely booked and send you the details, nagode sosai''.. sallama sukayi sannan ta kashe wayan, tana kashewa kiran amra na shigowa don duk ta kosa,dagawa haifa tayi cikin murna da farin ciki ta shaida mata komai sannan sukayi sallama.
Washe gari da safe da wani irin dadi da farin ciki amra ta shirya cikin shigarta ta kamala abaya ce kalar burnt orange har kasa, tayi rolling veil din fuskarta fa'yau babu komi sannan ta fito domin zuwa wajen aiki.
Tana sauka daga motor direct cikin asibiti ta wuce lokacin haifa ma bata karaso ba, saida tayi round checkup kafin ta koma office din haifa don jiranta, batafi minti goma da zama ba haifa ta dira, tana shugowa suka rungume juna sannan suka fara aiki atare, lokacin sallah nayi suka wuce masallaci, suna idawa suka dawo asibiti don rounding up komai don yau da wuri zasu tafi sbd appointment dinsu da jemi.
Amar kam, abubuwa sunyi mashi yawa, don yanxu akwai sabon policy ta yake shirin budewa a cikin headquarters akan staff da dama, duk aiki yasha mashi kai, anatse yake komai cikin office dinshi, hankalinshi nakan system, jin knocking din kofa yasa shi dago kanshi, ganin hammam yasa ya tamke fuska, sai yanxu ya tuna da matsalar da yake ciki, don kwata kwata yama manta gaba daya, takowa hammam yayi ya samu waje ya zauna wajen da aka tanada don baqi sannan ya fuskanceci yace ''dude whats up, daga fada maka gaskia sai shariya kuma, anyways hope yanxu ka samu naka solution din tunda wanda na baka which is the fact that I stated baiyi maka ba huh??'''amar baiko kalleshi ba yace ''muje muyi salla lokaci yayi'', atare suka sauka domin zuwa masjid,saida suka idar sannan aka kira hamman wani office don zaiyi wani aiki, nan sukayi parting ways shi kuma amar ya wuce office dinshi don ya kammala aikin nashi da wuri.
Karfe uku daidai suka fito, ko wannen su dauke da handbag dinshi maqale a hannun, direct moton haifa suka wuce, bayan sun shiga suka fuce daga premises din wajen.
Adaidai lushrose restaurant suka tsaya bayan haifa tayi parkin suka fito ajere, direct table din da haifa tayi reserving suka zauna, restaurant din is so peaceful, babu wani hayaniya sannan ko ina is private, zama sukayi a sit din mai dauke da kujeru uku, anatse haifa tayi masu ordern cool smoothie bayan an kawo masu suka fara sha kafin jemi ta karaso.
zaman minti talatin sukayi saiga wata ta karaso table din, tana zuwa tace ''heyy girls, I'm so sorry for being late'', murmushi haifa tayi don ta santa sosai tace ''hey jemi, welcome'' zama jemi tayi ah empty kujeran gefensu wadda itace ke facing dinsu sosai, jemi black African ce, kana ganinta, batada wani qiba sosai doguwace kuma akalla zatayi shekaru talatin aduniya, saida itama aka kawo mata dan abin sha kafun ta kallesu su duka sannan ta soma Magana ''so how may I help you ladiess'…. Kallonta haifa tayi sannan ta koro mata bayanin amra, da dalilin neman taimakon ta don tayi masu bayanin yanda ta samu katin kasa.
Nunfasawa jemi tayi sannan ta fara magana "naji duk bayanin ku kuma na tausayama wannan qawa taki don nima na shiga irin halin data shiga saidai nida ita akwai banbanci, don ni alokacin na fiku shekaru sosai,'' nunfasa tayi sannan ta cigaba ''ábout katin kasa, nidai ta nawa bangaren, aure na zaba don shine mafi qanqancin shekarun da zanyi na samu katin kasar nan har na cimma burina, but akwai wani secret agent da aka hadani dasu ban sani ba ko an kamasu ko sun daina aikin nan, sune wanda suka yimin hanya da taimakonsu sosai na samu nawa katin, yanxu zan baku contact din matar data taimakenin daga nan zata maku bayanin yanda application din yake da kuma yanda abubuwan suke gudana, don samun katin kasar hanyoyi ne daban daban sai kun zaba wanda yayi maku. ✍️✨***Auren Katin Kasa ***✨✍️ (Unexpectedly falling❤️🇦🇪)
Story and written by: QueenMarh👸🏼
Paid book 📚
Chapter 58-59
Saida ta basu contact din matar sannan sukayi mata godiya sosai sukayi sallama ta tafi abinta. Zama sukayi anan sannan suka fara kiran layin, kusan sau biyar suna kira ba a dagawa, ganin haka yasa haifa cewa su bari sai gobe saisu sake kira ko za a dace, amra kuwa wadda tun lokacin da jemi ta karanto masu number ta haddace akanta.
Gida haifa ta sauketa sannan itama ta wuce gida, donta huta, saida tayi bacci sannan taje dakin ummi, hira sukayi Tsakani ya da uwa cikin raha, suna nan zaune wayan haifa yayi ringing, ganin wanda ke kiranta yasa tayima ummi sallama sannan ta fuce ta koma dakinta, tana shiga gadonta ta haye sannan ta fara kokarin kiranshi back kafinma ta danna lock saiga wani video call din ta facetime yana shugowa, saida ta gyara zaman rigar ta sannan ta amsa call din, yana nan kichingide akan kujera hannunshi rike da grapes yana tauna anatse yana kallonta yana admiring beauty irin nata, duk yan matan da yake haifa ce kawai yake jinta ajininsa sosai, dukda yana tsoron lokacin da zata san manufarsa akanta.
Kallonshi tayi cikin sanyin murya tace ''habibi hammam, how are you today?''..kallonta yayi sannan yayi mata murmushi yace, ''habibty haifa I'm fine how are you today, naje office dinki dazu don naga kyakyawar fuskanki ko zanji dadi, saikuma na tararda bakwanan keda best friend din naki''…murmushin jin dadi ne ya bayyana afuskarta sannan ta soma mashi magana cikin larabci ''habibi, kwana biyu bana cikin nutsuwa sbd best friend amra, sbd…..nan ta kwashe duk labarin amra ta fada mashi, jinjina kai yayi da tausayin amra sosai sannan yace ''I'm so sorry for what shes going through, may Allah ease her pain''…yana kaiwa nan sannan yace so yanxu menene solution din da kuka samu''…shuru tayi na yan mintuna tana lumshe ido alamun bacci sannan tace, ''yanxu bamu samu solution ba, kawai dai na bata shawara ta nemi katin kasar nan idan ta samu saita kawo kannen nata nan abu dhabi saisu zauna tare don hankalinta bazai taba kwanciya ba suna chan gashi she has additional 4years now da dole saitayi ma government aiki sbd ilimin data samu anan, kaga ko bazata iya zama har 4years babu su kuma suna shan suna wahala'' girgiza kai kawai yayi cikin gamsuwa da kalamanta sannan yace ''well that's a good idea, but kinsan samun katin kasa it takes years sosai, saidai idan tana da arab wanda suke soyayya kozai aureta donta samu shima dai nasan it takes years kafin asamu saidai idan trick zakuyi which nasann kunsan is not legal, kuma Duk wanda aka kama prison yake tafiya and career dinshi is at stake yana kaiwa nan a jefa grapes abakinshi, kallonshi haifa tayi sannan tace''Allah dai ya taimake mu ya kawo mana solution mai amfani''….hira suka danyi sannan sukayi sallama tayi kwanciyanta….
Hankali atashe amar yake kallon shorts dinshi, wannan ne third time daya cire shorts ya chanza zuwa wani, sbd bacin da yakeyi, hankali atashe ya kira doctor, koda ya kirashi same bayani dai yayi mashi kan cewa percentage dinshi ke raguwa, sbd haka ya rage stressing kanshi, ya dinga zama hydrated sannan ya samu bacci sosai da kuma shan maguguna nan shi akai kai, yana jin haka ya kashe wayan sukayi sallama sannan ya fada bathroom ya sake sabon wanka. Yana fitowa Hankali atashe ya kira hammam, almost 3 calls baiyi picking ba, hammam kuwa yana gama waya da haifa ya wuce toilet lokacin call din amar ya shugo kusan sau uku, dayake wayan yana silent hakan yasa bai samu yaji shigowar call din ba kwata kwata harya fito ya kwanta, saida ya jawo wayan yaga call amar 30mins ago, yana ganin haka yasan da wani abun, da sauri ya fara dialing number amar. Amar kuwa wanda ya dafe kanshi damuwa tayi mashi yawa, jin karar wayanshi yasa yyi saurin dagawa ya aza wayan a kunnenshi, gyara kwanciya hammam yyi sannan ya soma Magana ''sorry dude, ka kira lokacin na shiga toilet, so what's up? Ka samu naka solution din tunda nawa baiyi mka ba?''…tsaki amar yyi sannan ya soma cewa ''hammam ka daina min haka fa, nakiraka don nayi sharing matsala na yanxu kana kara min wata matsalar akan tawa''…..tausayi ya bama hammam hakan yasa yyi saurin cewa ''okay dude, I'm sorry, so what the issue now?,menene matsalan yanxu''..nan amar ya mashi bayanin yanda sukayi da doctor..tausayin shi ne ya lullube hammam, wato kowa da irin jarabawar da allah yake mashi a duniya, shikuma tashi jarabawar Kenan, tunda suka hadu yake fama da wannan ospermia din tun baisan itace matsalar dake damunsa ba har ya soma ganin likitoci daban daban, gashi har yau babu sauqi, abin fargabar ma kar yazo yakai to the extent din da bazai taba haihuwa ba,don wannan masifa ce babba, gadai shi nan babu abinda ya rasa, arziki, lafiya, wadata, ilimi,ga kuma uwa uba kyau don babu abinda amar bashi da shi. Jin hammam yayi shuru yasashi saurin cewa ''dude, kana jina kuwa''..gyaran murya hammam yayi sannan yace ''sorry ina tunanin mafita ne''..anatse ya fara tausasa amar don yasan idan yabishi da zafi zafi to fa bazai tsaya ya saurare shi ba, hakan yasa ya soma Magana cikin nutsuwa ''Amar inason ka tsayar da hankalinka waje daya ka saurareni, yanxu kaga shekarunka talatin a duniya,babu abinda baka mallaka ba ciki kuwa shine iyali da zaka kira naka,wannan shawara da zan baka itace kadai zata taimake ka, shawara shine kayi AURE, nasan cewa baka da wadda kake so ko kake tunani aure but I want you to sit and think, nasan kana da babes dake yawan bibiyar ka saboda suna sonka, ka zauna kayi tunani sosai cikinsu idan akwai wadda zata iya bearing maka child, I will also help you out, nidai bazan baka shawarar surrogacy ba, don a addinance ma babu kyau kaika sani, kuma nasan idan Ammah tasan da haka it will break her heart, so yanxu wannan ce shawara ta karshe da zan baka, kayi kokari kayi tunani akai saika min bayani''…sallama sukayi sannan ya kashe wayan nashi.
Kwanciya yayi rub da cikin sa, saida ya kwashi wajen minti ashirin yana jin dripping din da yake kafin bacci ya daukeshi.
AMRA's apartment…. Tunda haifa ta sauketa a gida, tayi wankanta sannan ta shirya cikin riga da wando na baccinta, ruwa ta debo a glass cup ta zauna a bakin gadonta wayanta a hannu tana jujuyawa, tunani takeyi akan abunda zatayi, saida ta shanye ruwan sannan ta aje cup din a bedside.
Hayewa tayi gaba daya kan gadon sannan ta gyara zamanta ta soma danna wayan, ..rubuta number tayi sannan tayi saving da agent, tana gamawa ta bude message sannan ta fara typing kamar haka ''good day to you, i and my best friend called you earlier today around 4;30pm,mun kira ne sbd muna neman taimakon ku, mun karba contact dinne wajen jemima wadda kuka taimaka wa ta samu katin qasa, dan Allah idan har kunyi receiving message dinnan kuyi responding, ina buqatar taimakon ku cikin gaggawa, nagode'' tana gama typing tayi sending message din sannan ta aje wayen agefenta ta kwanta, sai wajen karfe uku na dare taji karar vibration, bacci ne mai nauyi ya dauke ta hakan yasa batako san ma an turo message dinba.
Lokacin sallar subh nayi wayanta yayi vibrating, hakan yasa ta mike don yin sallah, tana idarwa ta fara karatun qur'ani, sai wajen 6 ta tashi sannan ta wuce toilet don yin wanka, tana fitowa ta zauna kan dresser tana shafa mayukanta cikin nutsuwa, kallon kana tayi cikin mirror, girma yazo mata fah, don sai yanxxu ma budurcinta ke futowa sosai, ko ina na jikinta ya bude tayi kyau sosai sai sheqi takeyi skin dinta na glowing. Anatse ta gama komai sannan ta shirya cikin wani English gown mai kyau red color, rigar mai kamar flow sai ta zauna dam tayi mata kyau, dukda bata dameta ba, shirin ta tayi a tsanake sannan ta sha tea da pancakes. Saida ta gama tsaft ta tattara duk wani abu da zata buqata sannan ta wuce parlor ta zauna don tayi requesting ride din da zai kaita, wayan ta bude daman bata wani damu da saka password ba, tana dannawa taga message yayi popping akan screen din da sauri ta bude ganin number da tayi saving da agent, hannunta har karkarwa yake wajen danna message din, da sauri ta miqe ganin reply din da suka mata, wani irin farin ciki ne ya lullube ta, da sauri ta shiga typing ''thank you, thank you so much, let's meet later by 5 as you requested '…. Tana sending ta fara kokarin kiran haifa, haifa wadda harta kama hanyan zuwa office jin karar rining tone dinta yasa tayi saurin picking tace ''babes how far?" cikin murna tace Haifa tayi responding " wowww hamdullah let's meet at the office ni ina kan hanya na kusa''…..
Ride din amra na karasowa ta wuce don allah allah take kawai ta ganta a cikin hospital don ta hadu da haifa. Tana isowa direct office din haifa ta shige wadda itama wayanta a hannu, murmushi dauke fuskanta tace ''babe agent dinnan sunyi reply, gashi sunce mu hadu a rosalle private loung eatery by 5, jin haka yasa amra cewa ''babe nima sunmin message, kinsan jiya na kasa hakura shine nayi masu message, ashe sunmin reply tun wajen 3 na dare, sai dazu nake ganin reply din, yanxu bari muga zuwa anjiman sai muje ko''…cikin farin ciki da murna suka dunga aikinsu har wajen karfe 2 tayi, tsabar zumundi amra tace ''haifa kodai mu tafi tun yanxu mu jira su ne, nifa I can't wait wallahi'' dariya haifa tayi mata sannan ta kalleta ''babe calm down, ki bari 4 yanayi saimu wuce gaba daya,. ✍️✨***Auren Katin Kasa ***✨✍️ (Unexpectedly falling❤️🇦🇪)
Story and written by: QueenMarh👸🏼
Paid book 📚
Chapter 58-59
Saida ta basu contact din matar sannan sukayi mata godiya sosai sukayi sallama ta tafi abinta. Zama sukayi anan sannan suka fara kiran layin, kusan sau biyar suna kira ba a dagawa, ganin haka yasa haifa cewa su bari sai gobe saisu sake kira ko za a dace, amra kuwa wadda tun lokacin da jemi ta karanto masu number ta haddace akanta.