Kenza eBookz

Auren katin kasa complete - Chapter 2

Auren katin kasa complete - Chapter 2

Auren katin kasa complete Chapter 2: Auren katin kasa complete Chapter 2. Yana nan zaune karar emergency ta fara cika mashi kunne nan take aka fara…

4,493 words

Yana nan zaune karar emergency ta fara cika mashi kunne nan take aka fara announcing, ''everybody evacuate now!! Fire fire.''…ahankali ya dago kanshi wanda ke sara mashi sosai saida ya dauka wajen minti goma kafin ya miqe babu wani fargaba ko tsoro a tattare dashi, bude kofar office dinshi akayi wanda m-5 ne yazo domin yayi escorting dinshi, futowa sukayi atare shida m-5 har suka sauko qasa, wanda kowa ya fuce babu kowa tundaga office dinshi, anatse ya futo daga headquater ya tsaya ah harabar inda sauran sojoji kowa ya tsaya don jiran fire fighters wanda qa'ida ne su fito don ba aikinsu bane kashe wutan saidai fire fighters, saida kowa ya tattaru gaban tapkeken compound din lokacin wutan ta fara ci sosai ah floor din da ta fara ci, yan medical team wanda suma karasowarsu Kenan suma suka tsaya gefen sojojin, amar wanda ke gefe kamar baisan da mutane a wajen ba sai faman latsa wayar shi yake, chan ya dago ya kalli ko'ina da kowa na wajen, ahankali idonshi ya sauka kan yan medical, kawar da kanshi yayi kamar wanda ya tuna wani abu, ahankali ya fara nazari kamar mai tunanin wani abu sannan ya kalli m5 yace ''call the medical team here'' da sauri m5 ya isar da saqon shi sannan ya dawo tare dasu, daya bayan daya suka gaidashi cikin girmamawa sanin koshi waye, babu wanda ya amsa cikinsu saima kallon hafiza da yayi yace ''where's your assistant?'..kallonshi tayi cikin mamaki sannan tace ''sir tunda ka aiko a kirata bata dawo cikin hospital ba''.. jin hakan yasa amar kallon m-5 wanda shima ya kalleshi lokaci guda kuma yaji hankalinshi yadan soma tashi, da sauri ya fara tafiya zai shiga bulding din, nan fa sojoji suka taho gaba dayan su suka mara mashi ba, shiko baimabi takansu baya wuce gaban lift, ganin sun biyoshi gadan gadan yasa ya daga masu hannu hakan yasa duk suka sha jinin jikinsu suka tsaya curko curko don babu halin hanashi don su saidai ya basu order badai su bashi ba ciki kuwa harda m5, hammam ne kawai daman zai iya tsaidashi shima badon rank dinshi ba sai don shi abokinshi ne wanda kowa ya sani. Da sauri ya fara taka matattakalar benen azafafe har ya iso 4th floor wanda wuta ta fara cin abubuwa sosai, ahankali ya fara kutsa kai wajen roll din floor din, daya bayan daya ya dunga bin kofofin da kallo, har yazo daidai wata jar kofa da aka maqalama tag din health record room, da sauri yasa hannu don ya bude handle din, tunawa da handle din karfe ne yasa yayi sauri cire hannun nashi, yayi baya, da sauri ya taho gadan gadan ya buga kofar da kafa daya tashin farko ta balle, wai maza fa akwai karfi, da sauri ya kutsa kanshi ciki wanda duk hayaki ya dabaibaye ko ina, ko haske ba'a iya ganin, ahankali ya zaro mask din aljihunshi ya saka sannan ya fara dube dube, ganin babu alamun mutun ya sashi fara Magana ''hey hey anyone here'' chan ma dai shuru yaji, hankali atashe yama rasa me zaice don baima san sunanta ba, ''keee keee''!! ahankali amra wadda sumanta na biyu kenan ta soma jin Magana sama sama, ahankali idonta ya soma budewa, bakinta wanda ta shaqi hayakin harya cika mata baki yasa ta kasa Magana ko neman agaji, ahankali ta fara motsa hannunta har tadan bugi wani abu kamar dusbin, da sauri ta dunga jan hannunta harta tabo dusbin din sannan ta hankadashi da duk karfinta, jin motsi ta wajen wani sako yasashi sauri zuwa wajen, aikuwa yana karasawa yaji yadan bugi hannun mutun da kafarshi, da sauri ya tsugunna ya tabo ta don tabbatar da mutun ne, ahankali ya soma cewa ''ke tashi let's go''.. ganin kamar bata motsi ya sashi saurin jawo hanunta, da sauri ya taro ta don ta koma zata fadi, ganin idan ya kara mintuna a wajen rayuwar ta zai salwanta ya sashi runtse idonshi ya rankwafo ya sabota gaba daya in a bridal way, amra kuwa wadda ta fita hayyacinta jin wani kamshi da dumi yasa ta fara tura kanta a haukace cikin faffadan kirjinshi, gaba daya saida ta cukwikwiye mashi rigar jikin nashi har buttons din sun fara fita, jin nunfashinta na dawowa yasa ta kara bada himma ta zagayo da hannunta wajen qugunshi ta nade su tsam sannan ta cusa kanta cikin kirjinshi wanda farar shirt din ciki ta hanata samun access to bare skin dinshi, da sauri ya futo daga sakon ya fara shirin ficewa, yana karasowa daidai kofar kuwa inda ya dauketa gefen bangon wajen ya fara ruguzowa, da sauri ya kauda kai ya fuce, haka ya dinga kaucewa wutar nan ya fara taka stairs,har suka sakko last floor, hankalinshi bai kwanta ba saida ya fito nan m-5 ya taho da gudunshi gabansa sannan yace ''sir are you alrigt''… baiko bashi amsa ba yace ''take her to ER she'has lost her conscious,''.. da sauri m-5 ya mika hannu zai cicibeta..kallonsa amar yayi kawai sannan ya kauda kai yace ''just lead the way''.. fita sukayi tare wanda m-5 har ya isa gaban health team da suka tsaya cirko cirko yace su kawo gadon patients, da sauri aka kawo nan amar ya sauketa, dakyar ya banbare jikinshi daga hannunta don duk ta fita hayyacinta, duk wannan abin akan idon hafiza wadda idon ta tap da kwalla ita bama ta rashin lafiyar amra take ba, a a kawai dana'sani take, yanxu da tuni ita zai dauko a precious hannun nan nashi… Toh fah hafiza abin nata ya fara yawa fah………

Saida aka karama amra ruwa kafin ta dawo daidai, karshe dai harda allura akayi mata don ta samu bacci ta huta, allah ma ya taimaka an yi rescueing din ta da gaggawa da saidai a dauka gawarta don babu wanda yayi tunanin da mutun acikin floor din.

Duk wannan drama da akayi haifa bata sani ba don sun fita wani restaurant ita da babyn ta hammam ba tare da an sani ba, sai wajen karfe uku suka dawo wanda ganin lokacin tashi yayi yasa suka dawo. Abakin gate ya sauketa don kar aga sun dawo tare, itakuma ta tako har ciki, ganin mutane cirko cirko da kuma motar fire fighters manya manya yasa ta saurin karasawa ta fara tamnbayan meya faru, nan kuwa wani yayi mata bayanin wuta ce ta kama a 4th floor har an kusa rasa wata black African girl, jin haka yasa hankali haifa tashi don tasan amra ce kawai black African acikin headquarters da asibiti gaba daya hakan yasa da sauri ta wuce ER nan taga amra kwance tana baccin wahala, tausayinta ne ya dabaibayeta, nan take kwalla ta zubo mata ta fara Magana ''I'm so sorry babe, bai kamata na barki ba har kika shiga cikin halin nan,'' tana kaiwa nan ta kamo hannun amra ta fashe da kuka sosai, jin taushin hannu yasa amra dan bude idanunta da bacci bai ishesu ba ta sauke akan haifa wadda ke zubda kwalla, da kyar ta dago ta zauna ganin hakan yasa haifa taimaka mata ahankalin bakinta ya soma furta ''water please''…ruwa haifa ta debo mata ah dispenser ta kawo mata gabanta saidata shanye wajen cup uku sannan ta tsagaita ta kalli haifa tace ''babe waye ya fito dani daga cikin hayaqin nan and maysa kike kuka ''..jin hakan yasa haifa saurin rungumeta tace ''I'm so sorry babe ki yafe min na barki cikin wannan halin ban sani ba I'm so sorry''..lallabata amra tayi sannan suka tattara domin shirin tafiya gida, saida haifa ta cire mata Karin ruwan sannan ta deba mata magunguna a pharmacy sannan suka wuce wajen moton haifa, anatse take takawa sbd jirin da take ji kamar zata fadi, saida sukazo daidai wajen parking din staff suka ganshi shida m-5 suna takowa zasu wuce wajen motorn su, kallonshi amra tayi shima kallo daya yayi mata ya dauke kanshi sannan ya shige cikin moton shi, suka ja, sunkuyar dakai amra tayi tunani iri iri sunyi mata yawa, gida suka wuce inda haifa takira abuh ta Sanar dashi cewa zata kwana wajen amra, baiko hanata ba ya barta don ta fada mashi abinda ya faru ah asibiti kuma ya gani ah news.

Kula da ita sosai haifa tayi kamar yar uwarta ta jini, duk wani motsi sai haifa ta tambayi ko tana buqatan abu, har suka kwana uku tana kula da ita hartaji sauqi sosai, saidai yanxu ta rage Magana sosai sbd damuwa tayi mata yawa sosai akan batun su salima.

Haka suka karaci wannan kwana ukun sannan washe gari suka shirya suka koma aiki, babu wani aiki sosai sbd ana shirin yi hutun karshen wata, haka yasa basu wani dade ba suka dawo gida, washe gari ma haka suka karaci zamansu sannan suka fito, ganin shuru shurun amra ya fara yawa yasa haifa ta jata zuwa yawo, saida suka zagaye wurare da dama wanda yasa tadanji dadi sosai don damuwarta tadan ragu sosai. ✍️✨***Auren Katin Kasa ***✨✍️ (Unexpectedly falling❤️🇦🇪)

Story and written by: QueenMarh👸🏼

Paid book 📚 52

Salima kuwa azaman da sukayi ita da salim rashin lafiya sosai suka dunga yi, don sunyi wata irin rama sosai, salim kuwa kamar wanda ya samu qanjamau, don yanxu mama rabi ta daina aiki dalilin danta daya samu aiki a wani company babba ya saya mata gida da duk wani abunda zata buqata, haka yasa yace tabar aiki tunda girma yazo mata sosai.

Hakanan badan taso ba tabar aikin, don zataso ta zauna kodan su salima da salim wanda ta kasa fahimtar meysa ake wulaqanta su aka maidasu kamar prisoners agidan.

Dalilin tafiyar mama rabi yasa aka kawo wata rita, wadda ta sha rayuwar bariki ganin rayuwa ta juya mata yasa ta nema aiki kuma ta samu acikin gidan.

Rita irin mugayen yan iskan gari ce, ita ba musulma ba ita ba Christian ba, kuma baqar muguwace ita hakan yasa tasu tazo daya da khady don ta iya tafiya da yanda mutane sukeso, haka yasa khady ta bata umarnin daina bawa su salima abnci sau uku saidai sau daya arana, ganin hakan khady keso yasa taga banza ta samu, duk wani abu da ake basu na buqatu saita hana su irinsu sabulun wanka, da maclean wanda ake ajewa don yan aiki.

Yau kusan watanni Kenan rabon da suyi wanka da sabulu, duk sunyi baki sun dawo kamar aljanu, babu wani kuzari ajikinsu, wannan wahalar tasa cutar salim tashi gadan gadan, gashi babu magani ita kanta salima ciwon cikin nan dai qara gaba kawai yake, duk dare saidai tayi kuka ta godema Allah, yanxu basuda wani gata sai Allah, an raba su da yar uwarsu da karfi da yaji.

Abuja Nigeria….. Hankali atashe Amma ta mike ta fara zaryar tsakanin dakinta da parlor, jiran fitowar aman kawai take, kusan rabin awa kafin ya fito hannunshi rike da kwalba da alamu abuge yake, gabansa ta karasa tana kokarin kama hannunsa ya buge shi yace ''uban waye wannan zai taba ni'' hawaye ne suka cika idon Amma hankali atashe ta fara Magana ''aman meysa kake son salwantar da rayuwarka, aman wannan ba rayuwa bace mai kyau..tana kaiwa nan hawaye na zuba akan kyakyawar fuskarta wadda take sak da amar, matsowa yayi dab da ita zaiyi Magana Kenan sai amai sharr ajikinta, runtse ido tayi ta tallabeshi tana bubuga bayanshi harya gama sannan ta kwala ma yar aiki kira tazo, ahankali lantana tazo sannan ta umarceta data share wajen, ahankali ta dagoshi daga jikinta sannan ta jashi har dakinsa ta kwantar shi, toilet ta shige ta debo ruwa a bowl ta fara share mashi jikinshi da towel saida ta gama tsaf sannan ta tashi, cikin layi ya jawo hannunta ya rungume kamar za a kwace mashi hannun ya fara sambatu ''mummy karki tafi, mummy ki yafe min, wallahi banida karfin ikon abinda ya faru dake, daddy daddy….'''da sauri kuma ya lumshe idonshi bacci ya daukeshi.. zare hannunta tayi ahankali sannan ta mike ta rage mashi sanyin air con ta fito aranta tana mamakin me aman ke nufi da abinda yake shirin fada don da alamu abu na damunshi sosai don harda kwalla yake zubdawa, ganin bata da mai bata amsa yasa ta kawar da zancen kawai ta wuce kitchen.

Amar's….. Kwance yake, da laptop agefenshi, tunda ya tashi da asuba ya kasa komawa bacci anatse ya fara kallon laptop din wanda tun bayan asuba yake kallon screen din ya kasa gano clue kwata kwata, sake maimaita word din yayi MKS da sauri ya rufe system din kawai ya kasa gane me abin ke nufi amma yayi alqawarin duk abinda zaiyi saiya nemo ko wacce hanya ce don exposing wannan kungiyar ta mutun uku…..mutun uku yana fadin haka aranshi da sauri ya dawo gaban laptop din ya bude sannan yace ''m..k..s I got it now, da sauri yayi murmushi sannan ya wuce toilet, kamar kullum yauma saida yayi bubble bath sannan ya futo ya wuce closet dinshi ya fiddo da kayan da zaisa don yau baya tunanin saka kakin shi.

Anatse ya shirya cikin kayanshi farare tass riga da wando, kayan sunyi matuqar amsarshi, sai yayi wani irin kyau, anatse ya shiga lift ya sakko sitting room, kiran Pablo yayi a kawo mashi breakfast, bai wani ci da yawa ba ya fito ya wuce cikin white color ferarri shi wadda itama sai kyalli take don tsafta, anatse m5 ya fito ya sara mashi sannan ya bude mashi ya shiga suka kama hanya, haka kawai ya tsinci kanshi cikin farin ciki, har suka isa cikin headquarters, koda ya fito ya shiga ciki kowa mamaki yake yanda idan aka gaisheshi baya amsawa amma yau gashi yana masu murmushin da yake melting zuciyar matan wajen da yawa ciki kuwa harda hafiza wadda ta shigo domin diban sample din blood din senior officers, ganin yanda yake cikin farin ciki yasa ta yi alqawarin komai zai faru yau kam saita bayyana mashi sakon zuciyar ta, fucewa tayi zuwa asibiti fuskarta dauke da murmushi, tana shiga office dinta kuwa lokacin amra bata nan taje second patient check up, anatse ta samu waje ta zauna sannan ta cire dan kunnenta ta chanza zuwa na diamond sannan ta shafa red lipstick , daman abayane ajikinta mai budewa wanda tayi buttoning din ta sanna ta daura lapcoat, batako saka mayafin abayan ba saita riqeshi ahannunta , wayan ta kawai ta jawo sannan ta fito bayan ta dan feshe jikinta da turare mai kamshi, ahankali ta fara fita harta shiga cikin headquater sannan ta shiga lift zuwa office din general. ✍️✨***Auren Katin Kasa ***✨✍️ (Unexpectedly falling❤️🇦🇪)

Story and written by: QueenMarh👸🏼

Paid book 📚 53 Knocking ya fara yi saida aka dauka kusan 5mins kafin taji yace come in, ahankali ta bude kofan ta kutsa kanta ciki, azaune ta tarar dashi hakimce, waya maqale a kunnenshi, baiko kalli wanda ya shigo ba but yajiyo kamshin turarenta, ahankali yake motsa bakinshi kamar mai shagwaba yace ''Amma I promise insha Aallah zanyi kokari ko kwana biyu ne zanzo nayi but for now aikin yayi min yawa'' shuru ya danyi ya lumshe idonshi saida ya gama lallaba Amman shi kafin suyi sallama sannan ya kashe wayan.

Baiko kalli inda hafiza ke tsaye baya soma gyaran murya yace ''how may I help you?" jin bai yi mata fada ba akan zuwa mashi office daya hanata ba yasa tayi saurin gyara tsayuwar ta sannan ta soma Magana cikin kwarkwasa ''sir daman akwai wani Magana da nakeso nayi maka mai mahimmacin''..jin hakan ya sa shi tsagaita abinda yake ya dago ya mata kallon ke har kin isa kizo gabana kice kinason Magana mai muhimmanci dani, shi mamaki ne ma ya cikashi sbd babu abinda ya taba hadashi da ita in banda lokacin da tayi mashi kallon da bayaso hakan yasa ya soma magana cikin harshen turanci da muryanshi mai dadin sauraro ''okay go ahead''..babu wani bata lokaci ta soma bayani ''harga Allah nifa sonka nake sir, babu wani kwana kwana, kuma duk abinda kake buqata zan iya yi maka koda kuwa bada rai na ne'' dariya ce taso kufce mashi anatse ya guntse ta sannan ya tamke fuska kamar baitaba dariya ba ''so you even have the guts to come in my office without my consent and you think akwai abun da zanso a wajenki sannan kin tsaya agabana kina fadamin maganganun banza huh!........ya buga table din, ganin haka yasa hafiza saurin karasowa gaabanshi da sauri ta sanya hannu jikin lap coat dinta ta sabule ta sannan ta fara kokari cire rigar jikinta, baiko ankare ba ta yasar da rigar ta tako har gabanshi daga bra sai pant ajikinta, amai ne ya fara kokarin kakaro mashi, yama rasa mey zaiyi, wani irin azabben masifa ce ta tunkaro shi, runtse ido yayi don karta gane, itako duk atunaninta haqarta ce ta cimma ruwan don haka ta fara takowa daidai gabanshi ta duqo daidai saitin fuskarshi ta soma hura mashi iskan bakinta tace ''harda wannan ma'', ta girgiza mashi yan nonuwanta kananu kamar ta roka aka sammata , bude idonshi yayi wanda masifa ta ciyoshi sannan yayi sauri hankadata wanda hakan yasa tayi tangal tangal ta fadi, da sauri ya miqe yace ''get out before na illataki'' hafiza da taurine kai kuwa tana miqewa kamar zata wuce sai ta dawo da gudu ta rungumeshi, azabure ya tsaya yana kallon ikon Allah, kankameshi tayi sosai tana shafa mashi kirjinta sannan ahankalin hannunta ya fara yawo a kasanshi ganin abun ya fara wuce gona da irin yasa ya jawo gashin kanta sannan yayi baya da ita ya kwasa mata maruka zafafa guda uku ajere tass tass…lokaci guda hafiza ta tayi hutun wucin gadi, saidata dawo sannan ya karan hankadata da table din shi, nan take goshinta ya fashe, ganin zai mata illa wanda shi sam cikin tsarin rayuwarshi babu dukan mace yasa yayi sauri jawo landline dinshi yace ''get the car ready now!!'' yana kaiwa nan ya kalli hafiza wadda fuskarta harta kumburo hawaye shabe shabe yayi saurin cewa ''ki tattara qazantar jikinki da kayanki ki fice daga office dinnan, zan kyaleki ne kawai sbd ke macece badan haka ba da saina illataki don girman laifinki ba wanda zan iya yafewa bane, sannan kisama ranki cewa aiki anan kin gamashi har abada, I don't ever want to see your face," yana kaiwa nan ya fuce daga cikin office din nan ya wuce gida.

Hafiza kuwa takaici bakin ciki duk yagama cikata ga disgin da yayi mata hakan yasa ta tattara tarkacen ta, sannan ta shirya ta fuce fuu kamar iska, batama tsaya shiga office ba ta wuce motarta ta fusgeta tabar premises din gaba daya, tunda ta shiga mota take huci, bata taba tsammanin zai mata haka ba, ga dizgi ga wulaqanci babu abinda take cewa sai ''you'll regret this, I will surely make u regret what you did amar yunus tauraaaa…

Amra kuwa tana cikin aikinta wayanta ya dunga ringing, saida ta gama duba patients kafin ta fito ta wuce office, zama tayi sannan ta fara kallon missed call din, ganin number Nigeria yasa tayi saurin kira don tunaninta kawai ya kawomata su salima ne, saida ta kira kusan sau biyu kafin adauka, anatse ta soma Magana cikin harshe turenci ''hello please dawa nake magana''…rita kuwa ganin number kasar waje yasa tayi saurin cewa wrong number, kune masu kiran mutane mu dauka daga kasar waje ne ashe yan scamming ne'' tana kaiwa nan ta kashe wayarta, amra kuwa cikin rashin jin dadi ta aje wayan gefenta sannan ta doka tagumi, babu wanda take tunani saisu salima, ko a wani hali suke, yanxu idan tace zatayi kokarin komawa gida karatun ta zai salwanta barema bazai yuwu. ✍️✨***Auren Katin Kasa ***✨✍️ (Unexpectedly falling❤️🇦🇪)

Story and written by: QueenMarh👸🏼

Paid book 📚

Chapter 54 Bangaren rita kuwa tana aje wayan ta cigaba da wanke wankenta, Allah Allah take ta gama ta tafi wajen khady domin kai mata sakon molly data bata ta sayo mata, wato itama yar hannu ce shiyasa take kokarin siyeta da abubuwan mayen, ita kuwa khady sauqi ne yazo mata har gida don yanxu rita ce aminiyarta don itake kawo mata komai kuma ita ke mata introducing abubuwa sabbi wanda hakan ba karamin dadi takeji ba.

Saida ta gama gyare gyare sannan ta aje wayan nata a daki tayi wanka sannan ta shirya cikin casual dressing dinta na kafirai, riga da mini skirt sannan ta fito ta wuce sama wajen dakin khady, saida kwankwasa mata kafin ta shige ciki, akwance ta tarar da ita, ganin rita yasa khady mikewa tana fadi ''my girllll, hope todays molly is powerful'' murmushi rita tayi sannan ta zauna gefenta tace ''ma, todays molly is so powerful but the money high o,'' jin haka yasa khady miqewa ta wuce wajen da take aje hand bag dinta, anatse ta zaro yan dubu dubu guda biyar sannan ta dawo gaban rita, hannu rita ta miqa ta karba, saida ta kirga kafin ta zaqulo yar takardar daga kwankwasonta ta bata, hannu na rawa khady ta fuzge sannan ta fara kokarin budewa, tana ganin molly tayi maza ta bude ta shaqa, wani irin bari jikinta ya fara sannan ta afka abakinta, ko minti biyar batayi ba ta lula, ruf ta fadi don wannan mai shegen karfi ce, ganin khady ta jeme yasa rita dariyar mugunta tace ''shegun yara kunfi kowa iya kananun iskanci, iyayenku na daki kuma kuna daki kuna naku iskanci,'' ahankali rita ta fara bude jakar khady, saida ta yasheta tass sbd tasan cewa idan har ta farka bazata tuna duk wani abu data aje ba, saida ta kwashe yan zobinan gold dinta sannan ta wuce drower dinta ta kwashi English wears dinta wanda suka mata sannan ta tattara komai waje daya ta dawo gaban khady ta kuma kecewa da dariya sannan tace ''tunda har kin lula nima saina kwashi rabona,''

Saida rita ta kwakuleta tass kafin ta fice daga dakin, khady wadda azaba ta fara dawo da ita daga cikin hayyacinta yasa ta fara aman wahala.

Bayan fitar rita kuwa salima tana ankare da ita hakan yasa tayi saurin wucewa cikin dakinta ta dauki wayanta sannan ta dawo dakin su, ahankali ta soma laluben number amra wadda ta rubuta acikin paper kafin akwace masu wayan data bar masu, hakan yasa tayi saurin lalubar number tayi dialing, kusan sau biyar wayan ba'a dagawa hakan yasa salima ta fashe da kuka, tana cikin kukan taji karar kofar rita, hankali atashe ta mike tana labewa jikin kofar har saida rita ta rufe kofar dakinta, hankali atashe ta jawo wayan ta kashe wayan sannan ta wullata cikin drower, rita kuwa agajiye ta dawo daki bata bi takan wayanta bama ta kwanta abinta.

Washe gari duban duniya rita tayi ma wayan ta, amma bata samu ba hakan yasa hankalinta tashi sosai, ta koma dakin khady koda ta shiga bata sameta ba, haka yasa ta juya zata fuce jin kakarin amai yasa ta tsaya sannan ta wuce toilet din khady, zaune ta tarar da ita tana kwara aman wahala, saida rita ta taimaka mata tayi wanka sannan ta futo, ta kwanta. Rita kuwa tsabar dariyar mugunta dake ciyo ta yasa tama manta da batun waya.

Kwana hudu Kenan rita na neman waya harta gaji ta shirgama khady karyay cewa saida wayar ne zata samu ta dunga karba mata molly, haka yasa khady ta shiga dakin mummyn su haj kareema, ta kwaso kudi masu yawa acikin drower ta lokacin haj kareem ta shiga toilet, saida ta diba mai isarta sannan ta futo ta wuce daki, nan ta tarar da rita tana jiranta. Duka kudin kuwa khady ta bata, batama tsaya kirgasu ba. Rita kuwa dadi kamar zai kashe ta, tana komawa daki ta kwashi dubu biyar sannan ta boye sauran daman ranar zataje sayan groceries don haka tayi shirin tafiya da dubu biyar dinta don ta sayo sabuwar waya.

Salima kuwa saida ta jera kwana biyar tana kiran amra bata samunta don duk sai dare take samun yin wayan don tsoro takeji sosai kar akama ta tana wayan. Bangaren amra kuwa duk cikin dare sai an kirata da wannan number da matar tace wrong number, ganin hakan yasa tayi tunanin qila mistake suke suna kiranta, wanda yawancin kiran sai dare ake mata kuma lokacin tayi bacci.

Bayan kwana biyar salima kullum saitayi kiran number amra, yanxu tashin hankalinta charging wayan da yake neman mutuwa gashi tana tsoron zuwa dakin rita dauko charger don karta gane cewa itace da dauka wayan ta gashi jikin salim yayi wani mugun tsanani don yanxu abin nashi harda seizure idan ya fara saiya dauki wajen minti ashirin kafin ya dawo daidai. ✍️✨***Auren Katin Kasa ***✨✍️ (Unexpectedly falling❤️🇦🇪)

Paid book 📚

Chapter 55

Tunda salima ta tashi yau take tsoron daukan wayan don charging bazaikai mata dare ba zai mutu haka yasa tayi dialing number amra, lokacin da kiran ya shugo amra na tare da haifa suna duba patients, jin kiran yayi yawa yasa ta zaro wayan sannan tadan koma gefe ta daga ta fara Magana ''hello who's this?".. jin an daga wayan yasa salima fashewa da wani matsanancin kuka tace ''addaa adda nice ki kirani'' jin muryar salima yasa amra saurin cewa ''salima salima kece salimaaa'''da sauri ta kashe wayan sannan ta sake kiran layi, da sauri salima ta dauka ta fashe mata da wani matsanancin kuka tace ''adda nice, adda muna cikin mawuyacin hali, adda ki taimake mu, ciwon salim ya dawo, adda kizo ki daukemu ki dawo damu wajenki dan Allah'' jin hakan yasa amra tsugunnawa anan mutane kuwa me zasuyi banda kallonta don duk ta furgice, cikin shesheka amra tace ''salima meya faru daku, meya sameku innalillahi,'' kittt wayan yamutu sakamakon chargi daya kare, hankali atashe amra ta soma cewa ''salima say something salima!!!!! Jin shuru yasa ta duba wayan taga call din yayi ending hakan yasa tayi sauri sake kira amma me switch off, hankali atashe ta daura hannu aka ta fashe da kuka, haifa wanda sai yanxu hankalinta ya dawo kan amra yasa tayi sauri zuwa gaban ta tace ''amra what's wrong'' innalillahi kawai amra ke furtawa dakyar haifa ta jawo ta suka wuce office suka zauna, saida ta bata ruwa sannan ta fara dawowa dai dai, anatse ta soma Magana ''haifa siblings dina, suna cikin mawuyacin hali, ashe sune suketa kirana da wani line over a month now, I'm so stupid for not recognising them, bazan taba yafema kaina ba idan qannena suka shiga cikin matsala, innalillahi wa inna ilaihi rajiun, na shiga uku haifa"…saida haifa ta kwantar mata da hankali tukunna ta dawo dan daidai, babu abinda kwakwalwarta ke tariyo mata sai maganan salima da take cewa ''adda kixo ki taimake mu ki tafi damu, muna cikin matsala, ciwon salim ya dawo gadan gadan, runtse idonta kawai tayi don bazata iya jurewa ba kwata kwata.

Aikin da basuyiba a ranar Kenan ba, koda ta koma gida number ta dunga kira amma switch off, aranar dai amra batayi bacci ba kwata kwata. Bangaren salima hakan ta kasance, tayi kuka harta godema Aallah, karshe dai alwala kawai tayi domin kai kukanta wajen Allah, salim kuwa da yanxu rabin rayuwar shi kamar mattace kullum sai barci yake ta kalla, tausayinsa duk yagama lullubeta.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull