Kenza eBookz

Auren katin kasa complete - Chapter 33

Auren katin kasa complete - Chapter 33

Auren katin kasa complete Chapter 33: Auren katin kasa complete Chapter 33. Daidai gaban gate din Taura estate yayi horning, securities na ganin plate…

3,556 words

Daidai gaban gate din Taura estate yayi horning, securities na ganin plate number shi sukayi saurin bude gate din jikinsu na bari don babu wanda yayi expecting sir general zai iso, yaa shiga katafaren estate din yayi parking wajen parking lots dinshi dake shake da motoci kusan guda goma, gefe kuma na kowa ne, shi nashi daban ne daman, yana parking ya fito hannunshi rike da wayanshi Sai briefcase dinshi, da sauri securities suka karaso gabanshi tare da mashi barka da zuwa, kamar koda yaushe rafed daya ya zaro ya basu ya nufi hanyar cikin gida ba tare da ya saurari godiya da suke zabga mashi ba. Gaban entrance door ya tsaya ya Danna door bell, cikin Yan mintuna kadan lantana ta bude tana hamma don barci ne ya kwasheta ita dasu salima suna kallon wani series anan kasa, tana ganin shi ta watsake tare da rarraba idanuwa tace "barka da dawowa yallabai" jiki na bari ta matsa mashi ya shige ciki kamar basarake, parlor ya karema kallo, kusan shekara uku kenan rabon shi da kamshin gida, wani irin dadi ne ya ziyarce shi, maida idanunshi yayi ga parlor ganin su salima yashe a parlor suna barka barci yasashi juyowa ya kalli lantana dake karasowa gaban shi tace "Ina wuni yallabai an iso lapiya" Kamar an mashi dole yace "lafiya, yaran nan fah maysa suke barci anan" Da sauri ta karaso gabanshi tace "kallo sukeyi ne barci ya dauke su" Tattara books dinsu tayi tare da fara tashin salima, bai tsaya ba ya wuce bangarenshi daban dake gefen na aman saidai nashi yafi girma sosai don parlor ne da daki Sai bathroom. Yana shigewa salima na bude idanunta "anty lantana kinga barci harya daukeni" Kallonta lantana tayi dake shirin tashin tace "Nima barcin ne ya daukeni saida naji karar door bell na Tashi"

Tabe baki salima tayi kafin tace "yanxu haka hala wannan shugaban Yan yawon ne" Shuru lanatana tayi tana dariya ciki ciki tace "kedai salim keda mutumin nan Allah ya kawo ranar da zakuyi mutunci" Da sauri ta kalli kanta tace "anty lantana ni ba haushinsa nake ji ba kawai bana son halinshi ne, baya girmama na gaba dashi ga girman kai mteww" "Ahh lallai wannan fada Sai ku, bashi bane ya dawo dan uwanshi ne yallabai na dubai" Da sauri salima ta Tashi zaune dakyau farin ciki bayyane a fuskanta tace "ya Muhammad ne ya dawo? Laaa wayyo Allah yana Ina?" "Eh yanxu ya dawo ya shige dakinsa ma" Cikin murna da farin ciki ta kalli lantana "kai naji dadi sosai zabga ya Muhammad nasan mammah zataji dadi sosai daman tun dazu take jiran isowarshi Yanxu haka nasan tayi barci ma" Sama suka wuce kafin lanata tayi masu sallama ta wuce nata dakin don kusan karfe sha biyu saura.

Yana shiga daki ya bi ko'ina da kallo, an gyara shi tsaf tsaf babu ko dogon datti sanin shi mai tsafta ne yasa ammah tasa lantana ta gyara mashi, dakin nashi bai kai na chan gidansa girma ba amma yasha kayan alatu na duniya Har parlorn shi ma,aje briefcase dinshi yayi akan gado Ya wuce cikin changing room dinshi, daki ne babba sosai wanda yasha wardrop daya zagaye dakin na glass kaya shake a ciki. Saurin tube kayan jikinshi yayi ya sauya zuwa pjs dinshi kafin ya fuce ya dawo daki yabi lafiyar gado don ya gaji sosai bayan wannan Ma yasan ammah ta rigada tayi barci don tana Shan maganin ta na diabetes da take dashi.

Washe gari murna baibar su salima ba saida suka shiga dakin ammah da sassafe don babu schools an shiga hutun weekends, samunta suka yi tana azkar don haka suka samu waje suka zauna Harda salim, salima dai zumudi ya hanata rufe baki, ammah na shafawa kuwa tayi saurin dawowa gefenta ta zauna tace "good morning ammah ya jikinki" Da murmushi ta bisu da ido daya bayan daya tace "morning, Alhamdulillah jiki da sauqi Kun Tashi lafy" ta fada tana shafa fuskar Salim dake mata murmushi shima Salima ce tayi saurin cewa "Lafiya Lau ammah albishirinki ammah" yar dariya ammah tayi tace "Toh fah, goro"

"Ammah yaya Muhammad ya dawo jiya da daddare" Fuska a sake tace "waya fada maki? Jin ganshi ne?" Da sauri salima tace "Wallahi anty lanatana ta fada min ya dawo, lokacin muna barci a qasa" Da sauri ammah ta kalleta don bata yarda ba da farko tace "kira min lantanar" Da sauri ta mike ta fuce daga dakin cikin Yan mintuna kadan ta Sai gata tare da lantana, Har gaban ammah ga karaso ta duka ta gaisheta "Lantana jiya Muhammad ya dawo?"

Da sauri lanata ta dago tace "eh ya dawo jiya wajen karfe sha daya da rabi" Da sauri ammah ta mike tsaye tace "shine baki fada min ba," Ayi hakuri hajiya daman naga inkin sha magani kin kwanta ba a tashin ki" "Muje kasan" Saukowa sukayi su duka cikin zumudi kafin su shige bangarensa, ganin ko"Ina a kashe yasa ammah cewa mu koma da alamu bai Tashi ba, haka suka koma yuuuu zuwa parlor, breakfast suka fara yi kafin ammah tasa a dafa mashi favourite dinshi, anan parlor suka ya da zangon zaman jiran, salima na gefenta tana mata tausa,

Karfe goma daidai ya fito cikin shirinsa, cikin kamewa ya tsaya daga gefe don basu Lura dashi ba ganin su a zazzaune ya sashi kallonsu daya bayan daya, idanunshi ne suka sauka kan salima, take gabanshi ya fadi ganin kamannnin ta da amra wadda ya kwana da ita a ranshi, saidai ita batakai amra kyau ba sannan ita siririya ce, salima dake gefen ammah ya kalla, kanshi akan cinyarta salima kuwa tana Kasa tana matsa mata kafa sai suka burgeshi sosai, Gyaran murya yayi gaba daya suka maido da hankalisu kanshi, fuskanshi Adan sake ya karaso parlorn da sauri salima ta miqe, fuskanta dauke da murmushi don tana ganinshi ta tabbatar da ya Muhammad dinsu ne, salim ma da sauri ya Tashi ya tsaya gefen salima, ammah kuwa wadda tun fitowarshi ta karfe shi da idanu, murna da farinciki tare da kewar danta yasa ta miqe itama tare da bude mashi hannunta kamar baby, da sauri ya tako ya karaso yayi hugging dinta, "welcome son, Alhamdulillah nayi kewar ka sosai, ka iso lapiya ya hanya" Yana cikin jikinta yana jin kaunar mahaifiyarshi na ninkuwa sosai a ranshi ya dago yace "nayi kewarku sosai nima, na sameku lafiya," Janshi tayi Har kujeran da take zaune suka zauna, da sauri su salima Ma suka karaso suka tsugunna Har kasa "barka da dawowa ya Muhammad, ya hanya an iso lafiya" Kallo su yayi fuskanshi dauke da murmushi yace "Alhamdulillah how are you? Ya school Ana kokari dai ko?" Bakinta a washe tace "Alhamdulillah Muna yi" Hannu ya miqa Ma Salim ya tako Har gabanshi ya zaunar dashi gefen shi sanin baya magana, shafa kanshi yayi yace "how are you dude" Girgiza mashi kai Salim yayi bakinsa a washe, ba qaramin dadi amra taji ba ganin su a zaune, nunfasa tayi tace "son breakfast is ready" Dining suka wuce shida ammah ta zuba mashi abunci da kanta kafin ta zauna gefenshi tana kallonshi, suna yar firar yaushe rabo. Suna nan zaune Aman ya shigo cikin parlor, da masoyiyar shi ya fara cin karo wadda ta zabga mashi harara kamar idanunta zai fado kasa, dariya kawai yayi kafin ya maida idanunshi kan dining, mamakin ganin Amar yayi sosai, kafin yayi dariya ta gefen baki ya wuce wajen dining din, kallo daya amar ya mashi ya kauda kai shima baice mashi Kala ba saika kallon ammah yayi yace "ashe manyan baqi mukayi, barka da dawowa" Amar bai kalleta ba yace "thanks" Akufule yabar dining din don baya qaunar attitude irin na amar. Yana gama breakfast ya koma daki ya shirya cikin kananun kaya ya fito cikin kamewa ya hau sama zuwa dakin ammah, yana shiga ya taddata zaune kan gado, karasowa yayi ya zauna gefenta "babana zaka fita ne ko hutawa baka gama yi ba kayi doguwan tafiya" Kallonta ya danyi kafin yace "I have to go ammah, harda fitan da zanyi a cikin dalilin zuwa na Niger, ina buqatar addua ki" Hannunshi ta kama ta rike tace "Allah yayi maka albarka, ya baka zuri'a mai albarka ya tsareka kuma ya baka sa'a" Da sauri ya amsa da Amin fuskanshi a sake don yana jin dadi adduoin ta agareshi. Sallama yayi mata ya fuce daga gidan, direct gidanshi ya wuce, koda ya shigo a parlor y yasa zango, ya dauka kusan minti talatin a zaune yana kallon stairs kafin ya miqe ya wuce sama, dakinta ya wuce direct, bai tsaya knocking ba ya bude kofar ganin babu haske a dakin Sai duhu duhu ya sashi shigewa ciki ya rufe kofar ya kunna switch din dakin, nan take dakin ya dai haske bauuuu, idanunshi ya sauke kan gadon da take kwance ta qudundune bargo a jikinta ,fuskanta a waje, karasowa yayi gefen daidai gadon ya nannade hannayenshi a kirjinshi ya kura mata idanunshi, waigowa yayi ganin akwatinta agefe ya sashi maido da idanunshi kanta ahankali ya furta "stubborn girl" Kamar tajishi kuwa ta fara bude idanunta ahankali jin turarenshi na shiga cikin hancinta yana kaiwa ziyara kwakwalwarta, arazane ta mike zaune tama manta da yanayin kayan jikinta, saurin kauda kanta tayi shiko ganinta da yayi ahakan yasa ya baka idanunshi abuncin da suke marari, farar singlets silky night gown ce a jikinta, tayi laping a jikinta tayi Ma fatarta kyau sosai, maido da idanunta data kauda gefe tayi ta kalleshi ganin ya kura mata idanu yasa ta duban jikinta da sauri ta janyo bargon ta lullube jikinta da kyau ta bata rai tammm. Gungunita soma yi "mutun Sai kallon tsiya " "What did you just say?" Bata daga ba haka zalika bata ce mashi Kala ba saima Kara hade rai datayi Ganin haka ya sashi hasala yace "karki sake ina maki magana kina kauda min kai" Kamar bata jishi ba haka tayi banza dashi saima wani abu daya shiga a zuciyarta, kokarin cire tsoronshi tayi kamar bata san yana existing a wajen ba ta janye bargon kyawawan cinyoyinta suka bayyana, wata irin miqa tayi cikin yauki daya sashi danyi tagal tagal kamar zai fadi idanun nan Har wani ruwa ruwa suke fiddawa, sauke kafafunta tayi ta miqe tsaye, yar rigar ya karema kallo don ko gwiwarta kadan ta karasa, ta gefen shi ta rabe kamar batasan yana wajen ba cikin tafiyarta ta natsuwa ta wuce toilet ba tare da ta kalleshi ba, haka ya raka ta da idanu harya shige cikin bathroom din don ko kallon yanayin daya shiga batayi ba, wato tun bayan tsyauwarta ya kame kamar soja anyways daman chan sojan ne, gaba daya tsikar jikinshi ta tashi m, saida ya dan dawo daidai ne ya soma jin kunyar kanshi baiyi wata wata ba ya fice daga dakin. [7/11, 11:17 PM] +218 92-2035171: Update!!! 14/05/2023 Unedited❌

Tun bayan fitarshi daga cikin dakinta motar ya shige ya fice daga gidan rai abace. Bayason komawa gida don haka yayi saurin Kiran asad a waya, "kana Ina ne?" "Morning oga, Ina gida asad yayi saurin amsa shi, Azafafe yace "meet me at the resort,inaga hanyar daka kawo shawara ita zamubi," Sauke nunfashi asad yayi yace "okay ba damu zanzo yanxu. Juya akalar motar shi yayi da mugun speed, yana isa resort saida ya jira isowar asad kafin su shige tare. Babban wurine babu hayani kwata kwata, mutane qalillan ke yawo, bangaren zama suka samu suka zauna kafin asad ya soma magana "ka koma gida ne?" Cije baki yayi ya kalli asad yace "Yea na koma jiya" Kallonshi asad ya sake tare da tattara nutsuwarshi "Oga are you sure akan batun nan kuwa," Tabe baki ya fuskanceshi da kyau yace "Dude in banyi da kaina ba wazai yi, I'm the only closer person to them, ta haka Zan tattara Duk wani evidence akansu" Girgiza kai asad yayi alamun gamsuwa zancen sa kafin yace "okay then, amma you have to be careful, this man is dangerous,musamman yanda familyn ka ke tare dashi, idan bamu zama very careful ba zai iya yin abunda bamuyi tsammani ba" Runtse idanu Amar yayi don maganar kadai ma zafi yake mashi a zuciyarshi "Akwai abunda ke daure min kai, I don't even want to think about it,", Kallonshi asad yayi yana son Karin bayani "It's about dada,I'm beginning to suspect kasheshi akayi" Saurin runtse idanunshi da sukayi jaa yayi Ganin haka yasa asad dan dafashi yace "meysa kake zargin kashesa akayi?" Da saurin cikin bacin rai yace "Saboda alamu sun nuna, Akwai wani secret information daya turamin a day before rasuwanshi, and Duk abunda yake buncike akai yayi ya danganci wannan empire din, da wannan nake ji ajikina there are a lot behind the doors" Shuru asad yayi yana sauraronshi kafin yace "kabi komai a hankali, yanxu mu jira muji daga wajen hammam Idan Har Mun samu wani abu daya danganceshi to tabbas yana cikin kungiyar" Dafe kanshi yayi dake mashi ciwo sosai, baya son tuna komai ayanxu, basu wani dade ba sukayi sallama kowa ya hau motarshi.

Taura estate… Yana parking ya fito ya wuce cikin gidan, ganin babu kowa a sitting room yasa ya wuce dakinshi, wanka kawai yayi ya kwanta kafin lokacin sallar asr yayi. Karfe 3 daidai karar wayarshi tashesa, rai Adan bace ya bude idanunshi ya dubai wayar, ganin I know called yasa ya danyi tsaki ya aje wayan,ringing din na katseta wani call din ya shigo, ranshi Adan bace ya dauka wayan ya saka a kunnenshi, shuru ya danyi na Yan mintuna jin ba ayi magana ba sauke huci yayi mai zafi ya doka tsaki zai zare wayan kenan muryar mace ta katse mashi tunani "pleas don't hang up," Bai bude idanunshi ba saidai yayi mamakin mai Kiran don bai dago muryar koma waye ba, cikin yauqi meeda tace "Dan Allah spare me just 5mins" Baice mata qala ba haka zalika bai cire wayan ba idanunshi still a lumshe " uhm nasan bazaka ganeni ba,sunana hamieda, Mun taba haduwa a airport, Ina magana ne da Muhammad Amar?" Mamakin tsagerancin ta yayi, baya kaunar mata marasa aji kwata kwata Jin yayi shuru yasa ta cire wayan kafin ta maida kunnenta ganin bai kashe wayan ba ta cigaba "Sorry ko na kira lokacin da bai daceba?"

Tsaki ya buga yace "whoever you are, karki sake kirana, rubbish" Yana kaiwa nan ya kashe wayan yayi wurgi da ita gefen gadon ya miqe ganin lokacin sallah har yana neman giftawa. Yana dawowa daga masallaci ya wuce sama wajen ammah, a zaune ya taddata, cikin kamewa ya tako Har gabanta yadan duka kasa "son harka dawo" Murmushi ya mata yace "na dawo tun dazu nadan kwanta ne,"

Shafa kanshi tayi tace "abinci fah? Kayi lunch?" Kallonta yayi cikin kyaunar ta da kulawarta a gareshi "Alhamdulillah Sai zuwa anjima,ya kafar kinashan magani kuwa?" Fuskarta dauke da murmushi tace "ay naji sauqi alhamdlh, girma ne yazo mana" Yana jin haka ya dago inda zancen ta zai nufa saurin kauda zancen yayi ta hanyar cewa "yarannan fah?ban gansu ba" "Sun tafi islamiyya Ay, yauwa son inata so muyi maganar yarannan, baka taba hadani da mahaifinsu ba, haka zalika nan taba jin sunyi magana akan iyayen su ba,nima ban tambaye su ba" Hannayenta ya rike ya sumbace su ya kalli cikin idanunta yace "ammah, lokaci zaizo very soon Zan maki bayani daga baya in sha Allah" Sanin halayyanshi yasa ta daga kai alamun gamsuwa tace "Allah ya nuna mana" Chan kasan makoshi Ya amsa da "Ameen" Shuru ya danyi yana san tambayarta abu saidai yana tsoron tambayoyin da zatayi shi kuma baya son ta shiga rudu da tunani, cikin da bata ya soma tambayarta" daddy fa? Yayi tafiya ne" Mamakin tambaya akan dady tayi sosai don Idan yazo ko shekara zaiyi Idan basu hadu da dady ba baya damuwa kuma baya tambayar da, dalilin ne Ma take yawan yi mashi fada tare da nuna mashi mahimmacin dadyn a matsayin shi da wa in mahaifinshi kuma uba a wajen shi saboda aurenshi da take. Murmushi ne shimfide a fuskarta don taji dadin tambayar da yayi, tace "baya nan yayi tafiya zuwa china, Yau wata guda kenan" Da sauri ya kalleta yace "yaushe zai dawo" Ba tare da tunanin komai ba tace "yace min business trip ne, Sai Mun ganshi kawai" Nazari ya soma yi kafin ya kauda zancen ganin yanda yake mashi kallon tuhuma, "uhm ya company kuwa?hope komai is under control" Take fara'a r fuskarta ta dauke, yana ganin haka ya fuskanci Akwai problem, saurin kauda tunanin daya zo kanta tayi ta saki fuskarta tace "kwanaki an dan samu problem but everything Is under controlled," Miqewa yayi ya mata sallama ya fuce, yana fucewa wasu hawaye suka sauko kan idanununta, tunanin dada ne ya fado mata Idan Har ya kalli Muhammad komai nashi irin na babanshi, tsayuwanshi da yanda yake miskilancin sa magana Ma wuya yake mashi, idan zaka zauna dashi a wuni daya bazaice Tak ba, ahanklai ta furta "Allah ya jiqanka dada"

Yana futowa daga wajen amma ya sauko kasa, anan kasan ya riski aman zaune kan kujera yana waya, kallo daya ya mashi ya kauda kai ya wuce dakinshi, da harara Aman ya bishi. Kafin ya cigaba da wayanshi.

Karfe shida da rabi daidai su salima suka dawo daga islamiyya,ammah ce kawai a zaune a parlor tana kallon tashar sunnah tv hannunta rike da charbi, da gudu Salim ya zo jikinta ya zauna gefe, salima na biye dashi tace "kai karka balla mana ammah" Dariya ammah tayi ta kallesu su duka tace "Yan islamiyya, Yau Ansha hadda" Dariya salima tayi tace "Wallahi ammah dakyar Allah ya taimake ni na biya"

"Kinyi kokari Ma my dear, kuje sama ku chanza kaya lokacin sallah ya kusa" Suna cikin magana kamshin turaren shi ya sanar da isowanshi wajen, ya fito daga bedroom dinshi sanye cikin jallabiya, takowa yayi har inda suke zaune, da sauri salima ta tsugunna Har kasa tace "barka da fitowa ya Muhammad ina wuni" Hannu ya miqa Ma salim alamun ya taho kusa dashi, kallon saliman yayi aranshi yana yaba halayyanta yace "ya karatu?, ana dagewa dai ko" Da saurin ta cikin zumudi tace "Alhamdulillah munayi sosai" Murmushi ya danyi ta gefen baki ya shafa kan salim yace "jeka chanza kaya mu tafi masjid lokacin sallah yayi" Da sauri Salim ya hau sama salima Ma ta bishi, maida idanunshi yayi kan ammah itama shi take kallo fuskarta dauke da murmushi tace "za aje masjid ne son" "Uhm kawai yace mata ya zauna gefenta Har salim ya futo suka wuce masallaci,itama saman ta wuce. Zama sukayi a masallaci Har akayi sallan isha'I dasu, suna idarwa hannunshi rike dana salim suka wuce cikin motarshi, wani katin mall suka tsaya yayi parking suka wuce tare, hannunshi hade dana salim suka shiga ciki, kallon yanda Salim yake murna yayi yace "dauka abuna kake so and don't forget your sister okay" Salim najin haka yayi tsalle,janyo trolly yayi suka shiga zagayen wajen, yana kallon yanda Salim ke tsalle tsallen shi, saida suka gaji kafin su fito da ledoji niki niki, yana son zuwa gidanshi dake larric, tuna wani abun ya sashi wucewa gida kawai.

Sai wajen karfe Tara suka iso gida, babu kowa a sitting room sai tv dake aiki, kallon Salim yayi yace "kake sama ku taba kaifa sister ka" Girgiza mashi kai Salim yayi kafin ya wuce sama da gudu don murna. Dakin ammah ya wuce shima ganin tana shirin kwanciya yasa ya mata sallama ya sauko kasa. Koda ya sauko babu kowa a kasan, dining ya wuce ya tsaya ganin flask da ammah ke dafa mashi coffee, Harda mug din flask din, murmushin ya yi yana yaba kulawa da ammah kw nunawa a gareshi wanda Duk duniya bayan dada babu wanda ya taba mashi, coffee din ya deba ya wuce dakinshi,kayan jikinsa ya rage daga shi Sai inner shorts dinshi, janyo laptop dinshi yayi ya hau kan gado ya fara aiki, yana Shan coffee din, ya dauka kusan awa kafin ya gama, janyo remote din tv dake aiki yayi ya kashe ya kwanta, tunanin da yake son hana kanshi ya kasa, lumshe idanunshi yayi tare da forcing kanshi ko zai samu yayi barci har kusan karfe daya, ganin haka yasa ya zauna rai Adan bace yace "maysa kake yawan saka ta aranka Well its because she's so important now," runtse idanunshi yayi bayan ya gama bama kanshi amsa, ahankali ya furta "dude focus" Komawa yayi ya kwanta da kyar mararshi na dan murda mashi yana jin haushin abun sosai, da zarar ya rufe idanu moments dinsu na dawo mashi, kokari yake yi sosai don ganin bai saka kanshi zancen da tunanin ba saidai ya kasa hakan, baya son yanda zuciyarshi ke ingiza shi don yayi alqawari bazai dake neman ta ba, ko last da ya nemeta yayi regretting hakan sbd ganin wahalar datasha da dinki da yaji anyi mata sai yayi tunanin saboda kananun shekarun ta ne, kwata kwata bai kawo daga shi bane, don shi cikakken namiji ne mai ji da lafiyar buqata.

Bangaren amra tayi mamakin kanta sosai da yanda ta fuskanceshi, daman zata iya, koda ta shiga toilet din gabanta bai daina bugu ba sosai, don ta dauka hakan da tayi zata jama kanta, Sai jin fucewar shi datayi don haka ta dauko damarar yin abunda yafi haka Ma tunda kiri kiri ya hanata tafiya saboda wani. Dalili nashi chan daban wanda bata gane ba.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull