Auren katin kasa complete - Chapter 32
Auren katin kasa complete Chapter 32: Auren katin kasa complete Chapter 32. "Shiyasa nazo Ma, ga kayanki Ma nazo dasu" "Yauwa daman inata tunanin wanda…
4,304 words
"Shiyasa nazo Ma, ga kayanki Ma nazo dasu" "Yauwa daman inata tunanin wanda zansa,thank you nadine " Shuru duka sukayi kafin nurse ta shigo "amarya mai kuka" ta fada tana dariya don itake kula da ita wajen yin gashi Har sun saba "Nurse beauty kin dawo" "Na dawo amarya ya kikeji yanxu?" Dan kauda kanta gefe tayi tace "I'm feeling much better all thanks to you" "Ah haba, that's my profession, doctor ya rubuta maki sallama, an gama all necessary arrangements, ga billing papers, jiya da oga yayi signing na manta ban bashi ba,Allah ya Kara sauqi sai kinzo scanning" Gabanta ne ya bada daram kafin ta dago ta karba paper din ta dan tabe baki a ranta tace "allah ya tsare ni, ni aisha" Sallama nurse din tayi mata kafin ta fuce da gefen idanu ta kalli Nadine wadda tayi gum kamar bata san suna yi ba saidai kunnenta tass ya nadi komai, mamaki ne karara a fuskanta saidai sanin babu huruminta yasa ta yin gum. Saurin maida idanunta tayi kan papers din kafin ta soma karantawa, paper bill ne wanda aka shigar cikin file dinshi na nan asibiti akayi registering sunanta under nashi as her guardian, kurama bill din kasan idanu tayi dan kwanakin da tayi Har taci Rabin miliyan, runtse idanunta tayi tana mai jin wani irin sauyin yanayi haushinsa na raguwa cikin ransa, dama chan bata kullace shi ba saidai tayi alkawarin barin rayuwarshi gaba daya.
Karfe goma suka ta gama kimtsawa cikin abayar da nadine ta kawo mata, bata saka hijab din nata ba ta saka mayafin abayar suka fito Nadine na biye da ita da basket din data taho Dashi, daidai wajen motar da driver ya kawo Nadine suka tsaya ya bude masu suka shiga yaja motar sukabar asibitin.
A cikin dakin kuwa bayan fitarsu amra mai shara da goge goge na zuwa Gyaran dakin taga ledaji a kasa, da farko tama dauka trash ne saida ta bude taga kayan zaqi Kala Kala Harda wanda bata taba gani ba a rayuwarta dasu cakes kusan Kala biyar different flavour, chocolate masu tsada da sauransu ledoji biyu ne tam a cike da su a ciki, tana ganin haka kuwa ta qulle abunta ta karasa gyara ta fuce daga dakin.
Tafiyar minti Talatin suka karaso gida saboda traffic daya dan tsaida su don Safiya ce kuma Akwai masu zuwa office da wuri, driver na parking ya bude mata baya ta fito tadan tsaya tana karema gidan kallo kamar mai nazari kafin ta karasa ciki nadine na biye da ita a baya.
Tana shiga cikin parlor ta wuce sama zuwa dakinta ta zare mayafin abayar ta zauna gefen gado ta doka uban tagumi, ta dauka kusan minti goma a zaune kafin ta miqe ta wuce toilet jin futsari ya matsota, da kyar ta samu tayi futsarin tana cije lebe don Har yanxu tana jin zugi a wajen, tana gamawa tayi tsarki da warm water don yanxu likita yace mata komai da warm water zata yi har bayan ta warke ma. Tana fitowa daga bathroom din nadine na shugowa dauke da ledan magungunanta tace "ma gashi jin manta a mota" Ta aje mata tare da juyawa ta nufi kofa "Oh thanks nadine" ta fada tare da wucewa kan gado ta janyo duvet ta lullubama kanta, barci take son yi saidai tunani ya hanata ayanxu ta yanke shawarar yana zuwa zata shaida mashi zata bar gidan ta koma kano wajen Yan uwanta don zaman ta anan batada guaranteed din abunda zaije ya biyo baya, bayaga wannan Ma babu amfani sannan zata nemi ya saketa ta kama gabanta. Lokacin daya shigo gidan wajen karfe sha daya kamar kullum, tsayawa yayi a sitting room ya qare Ma ko'ina kallo babu kowa a parlor,kallon inda take yawan zama ta jirashi yayi kamar mai tunani wani abu kafin ya kauda kanshi gefe ya wuce sama, koda ya hau second floor tsintar kanshi yayi da tsayawa gaban dakinta, cikin natsuwa ya bude kofar, ganin duhu babu haske Sai dan hasken bedside lamb ya tabbatar mashi tayi barci don haka ya karo mata kofar ya haura sama zuwa dakinsa. Kwanan ta biyu da dawowa daga asibiti, cikin kwanakin nan koda wasa bata yarda ta hada hanya dashi ba, Duk wani abu da tasan zai hada ta dashi kauce Kasa take yi, cikin Yan kwanakin nan ta warware sosai don gaba daya ta daina jin zafin da yake ji, kullum Nadine ke kawo mata abinci daga na safe zuwa na dare, daga daki Sai bandaki babu inda take zuwa Har zaman ya fara gundurar ta, gashi wayanta bashida wani amfani don bata da masu kiranta ko ta kira, daman haifa ce, itama yanxu kusan wata guda kenan rabon data sameta a waya.
Thursday morning… Tun bayan data Tashi sallar asuba bata koma ba, wanka kawai tayi ta shirya cikin English gown mai dan tsayi don ta wuce gwiwarta sosai ta shan iska ta feshe jikinta da turarenta masu sanyin kamshi kafin ta zauna kan gadon ta soma latsa wayan ta don kwana biyu Instagram na debe mata kewa sosai, Tana nan zaune Nadine ta kawo mata breakfast, fada da murmushinta tayi don daman harda yar yunwarta ta Tashi, Har gabanta nadine ta karaso ta aje mata a gefen gado tace "Ma ga breakfast" karban abincin tayi tace ", thank you so much nadine daman yunwa nakeji sosai" Murmushi kawai tayi mata ta fuce Janyo tray din tayi ta bude plates din abunci ta fara ci hankali kwance.
Tana gamawa nadine na shigowa dakin, hannunta dauke da bottle water tace "sorry ma, na manta zaki buqaci ruwa zai yanxu na tuna" " thank you daman yanxu nake tunanin saukowa da plates din" "No ma'am Zan sauka dasu kasan" Murmushi kawai tayi bayan fitar Nadine tana yaba irin mutuntuwa da take dashi, batada damuwa kwata kwata, aikin ta ne kawai a gabanta.
Uae Haifa's res…. Kusan wata guda kenan tana neman line din amra bata samu, ta shiga damuwa sosai na rashin jinta cikin kwanakin. Bude kofar toilet dinta tayi ta fito da sauri jin karar wayanta alamun kira na shigowa,da sauri ta daukan wayar ganin tana neman yankewa, ganin sunan Hammam kan screen ya sata yin yar tsuka ta aje wayan tare da komawa toilet ta cigaba da abunda yake,daman wanka ta gama tana cikin yin skincare dinta karar wayar ya cika mata kunne. Saida ta fito ta shirya fess kafin ta janyo wayan nata ta soma kiranshi, ringing daya ya daga Wayar tare da yi mata sallama, saida suka gaisa kafin ya tambayeta ummi da abuh, mamakin shi take sosai, abubuwan da baya yi mata achan baya wanda a lokacin take son haka yake mata ayanxu, sama sama ta dunga amsa shi don garashi take yi sosai shi kuma yana lallabata. "Uhm how's your friend?" "You mean amra?" Tayi saurin bashi amsa "Yes" "Tana nan lpy, but I'm not sure don tun bayan banning dinta a akayi daga uae akan auren katin kasa ta koma nigeria ban sake samunta ba, I'm sure ka san zancen tunda Harda abokinka akayi suspending" Dariya ya danyi Har tana jin sautin dariyar tashi Shuru ta danyi tana sauraron sa don ya dan daure mata kai, don maganar da yake mashi ba abun dariya bace Da sauri adan qule tace "I'm I making a joke here? Da sauri yace "sorry dear" "Then why are you laughing" "It's just that….." A harzuke tace "let me just end the call" Da sauri ya ce" it's just a fake scandal," "I don't understand, what do you mean by it's a fake scandal" "I can't tell you everything, but it's a fake scandal, no one Is banned,not even the general, it's just a plan"
Shuru tayi tama rasa me zatayi murnar abunda ya fada mata ko haushinsa,"you mean it's all a plan?, and you didn't even bother to…" da sauri taja Bakinta tayi shuru Tunawa da lokaci da abun ya faru basa tare, "hold on a sec" Tana fadin haka ta kashe wayanshi ta shiga Kiran amra ba qaqautawa stil baya shiga, burinta yanxu kawai ta samu amra ta daga wayanta ta bata wannan kyakyawanan albishir,saurin sake kiranshi tayi tace "do you know a way that I can reach some one that is in nigeria?" "I've been trying to reach her out"
Da sauri yace "kina da contact dinta na chan ne?" " eh ina dashi but it's useless , don ina kira baya shiga" ta bashi ansa Gyara zaman wayan yayi a kunnenshi don yana office nema "What does the number start with" "It's start with zero" Da sauri yace "hold on a sec" Sauke wayanshi yayi ya shiga contact din Amar na nigeria. Sake kiranta yayi yace "I don't know if this will work but you have to add 3 more digit before the first digit, let me send you an example through sms" Da sauri ta sauke ijiyar zuciya tace "thank you so much" ta kashe wayan Yana tura mata ta saka tare da saurin dialing, nan take wayar ya shiga Har ya fara ringing, da sauri ta miqe fuskanta dauke da murmushi farin ciki. Amra dake zaune tun bayan sallar la'asar bata motsa daga inda take ba tana tunani duniya da makomar rayuwar ta sanin cewa yanxu ita baza a saka kanta cikin jerin budurwa ba hawaye na saukowa daga fuskanta tayi saurin goge wa, tunani ta shiga yi da zuciyarta inda ta yanke samunshi don suyi magana akan rabuwar su don bazata tafi da auren wani ba gida koda wasa, bala'in da zata tarar a gidan uncle na banning dinta da akayi babu karatun ma ya isheta. Tana cikin wannan tunanin wayanta yayi ringing……. [7/11, 11:17 PM] +218 92-2035171: Update!!!! 13/05/2023 Da sauri ta dauka wayan ganin contact din haifa akan screen din, Har jikinta na bari "Hello….haifa, is that you" Cikin murna da farin cikin samun kawar Tata tayi saurin cewa "habibty Ina kika shiga,I'm so sorry, bansan yanda Zan sameki ba saida hammam yam min bayanin yanda Zan kira ki" cikin mamakin abunda haifa ta fada tayi saurin cewa "hammam? Are you guys back together? Sauke nauyayyan numfashi haifa tayi tace "it's a long story,and what I will tell you now will shock you even more" Shuru amra tayi cikin damuwa da daurewar kai tace "haif, so much has been going on in my life recently, na shiga damuwa sosai na rashin samunki" cikin farin ciki da zumudin abunda zata fada mata tace "babe abunda Zan fada maki yanxu zai kawo karshen damuwarki I promise" "Haif na…" saurin katseta haifa tayi tace "babe you've not been banned from uae 🇦🇪 all that scandal is fake infact your marriage has been proved legal by the marriage consent group and I'm sure zasu baki katin kasar" Da sauri amra ta miqe tsaye idanunta tap da qwalla kanta ya gama qullewa da abunda haifa take fada mata "babe what, what are you talking about, ban gane ba kimin bayani yanda Zan gane" "Yea babe, abunda na fada maki gaskia ne, Duk abunda ya faru a lokacin it's just a plan made by general for some certain reasons,dazu hammam ya fada min," "Then that means he used me?,haifa you mean all That has happened kwanakin Duk karya ne?innalillahi wa inna ilaihi rajiun, haif Im so stupid" Tana karashewa ta fashe da kuka, tsagaitawa haifa tayi hankali tashe jin kukan da amra keyi tace "babe what wrong, na dauka you'll Be happy with the good news"
Cikin dacin rai da baqin ciki tace "no…noo haifa," Ta sake fashewa da kukan, abunda take son fada mata ma ya maqale, sanin halin amra yasa haifa yin shuru, saida ta dauka kusan minti ashirin tanayi kafin ta tsagaita don kanta, hankalin haifa ya gama Tashi gaba daya saidai ta Kasa gane dalili kukan kawar tata "Babe" ta kira amra ahankali cikin natsuwa "What's wrong? Why are you crying?" "Haifa he lied to me, he used me" dan kukan data tsagaita ta cigaba "Amra pleas explain to me yanda Zan fahimta, who used u?" "He played with my innocence, shine ya kawoni gidansa don ya samu cikar burinsa, yanxu ne Ma komai ya gama dawowa kaina" Da sauri haifa wadda ta gama kufuluwa da zancen tayi saurin cewa "kin saka ni a duhu, kimin bayani" Nan take amra ta fara zayyano mata bayanin tundaga lokacin da m5 ya dauko ta ya kaita airport zuwa lokacin da aka kawo ta gidan, shuru haifa tayi don itama kanta ya gama daurewa "you mean, kina zaune a gidanshi? And bai fada maki gaskia ba? What's his motive kenan, to protect you?" Cikin bacin rai amra tace "to protect me? He lied to me because all this while ya nuna min saboda ni da taimakon da yayi min akayi banning dinshi shima Har yayi affecting all his achievements,I was so stupid, I've been blaming my self all this while, what did I do to deserve this?" Da sauri haifa ta tari nunfashinta tace
"Babe if that's the case then why would he do that?,maysa zaiyi haka" "Saboda yaga I'm helpless, saboda yaga banida kowa, haifa he slept with me, forcefully" tana kaiwa nan ta Kara fashe wa da kuka mai shiga rai
"Wahttttt!!" Haifa ta fada da dan karfi tayi saurin gyara zaman wayar a kunenta ta cigaba "he slept with you? How did you let that happen" Nan take amra ta sake fashewa da wani kukan da zaka gane abun ya taba zuciyarta sosai tace "I don't want to stay for a second in this house haif,I'm in pain" "Babe calm down, ki kwantar da hankalin, karki yi saurin yanke hukunci,mubi komai a hankali" Da kyar haifa ta tausasa ta tare da bata shawarwari, sun dauka kusan awa guda suna magana kafin suyi sallama. Aje wayan tayi a gefenta ta wuce toilet ta dauro alwala,kafin ta fito ta tada sallah, ta dade sosai kan sallaya tana adduoi da neman taimko wajen Allah, babu abunda yakai tsayawa gaban Allah kakai kukanka, wannan zaman da tayi sai Tashi kashi 50 cikin damuwarta ya ragu, daman batada riko a ranta, saidai wannan ya tabbata sosai, mikewa tayi ta ninke sallayan ta zauna gefen gado, abincin da Nadine ma ta kawo mata bata kalleshi ba kwata kwata, tagumi ta tafka na tausayin rayuwar data tsinci kanta, tawakkali tayi tare da fawwala Ma Allah komai saidai tafiya kam Saitayi ta babu fasawa. Shawarar da haifa ta bata ta dauka, cikin kwarin gwiwa ta mike shiga tattara kayanta tsaf babu abunda ta bari ta saka acikin akwatinta.
Karfe Tara na dare daidai ta sauko kasa, fuskanta a kubure idanunta yayi jaa sosai, samun waje tayi ta zauna akan kujeran sitting room ta rafka uban tagumi, zaman awa uku tayi anan zaune, idanunta kyam babu alamun barci tana zaman jiran dawowan shi, karfe sha biyu daidai da Yan mintuna taji karar horn hakan ya tabbatar mata ya dawo, gyara zamanta tayi tare da saurin cire tsoron daya durar mata lokaci guda don tayi alqawarin cire tsoronshi daga ranta. Bude kofar yayi kai tsaye ba tare da tunanin komai ba ya iso Har sitting room din baima Lura da ita ba zaune, Har ya wuce sitting room din tayi saurin miqewa ta fuskanceshi tace " sannu da dawowa" Tsagaita tafiya yayi hannunshi duka na cikin aljihun wandonshi, fuskanshi na nan babu yabi ba fallasa Sai zallan gajiya shimfide a kan fuskar tashi, kamar bazai ce komai ba ya dan juyo kadan yace "yau..wa!" A rarrabe kafin ya juya yana shirin Taka stairs tayi saurin bin bayanshi ta tsaya dan nesa dashi tace "inason magana dakai" Dakatawa ya danyi bai juyo ba haka zalika bai ce mata komi ba, ganin haka ya sata saurin cewa "daman ina…." Bai bari ta karasa ba ya wuce sama "idan magana kike kiyi dani ki sameni a sama" bin shi tayi da idanu harya kauce Ma ganin ta kafin ta sauke wata nauyayyan ajiyar zuciya, ba tare da tunanin komai ba ta dake tare da tattaro Duk wani kizarinta ta hau saman,tunda ta tsaya bakin kofar dazai sadaka da sitting room gabanta ya soma faduwa, tana jin yanda heart dinta ke racing, saurin danne wa tayi fuskanta babu alamun fara'a ko murmushi Sai damuwa, saida ta fara knocking kafin ta bude kofar, a zaune ta taddashi ya daura kafa daya kan daya idanunshi na kan wayar yana dan latsawa, takowa tayi dan nesa dashi ta kauda kanta gefe don ko kallonshi bata son yi don abubuwa ne da yawa ke dawo mata a cikin zuciyarta data kalleshi ciki kuwa Harda tsiraicin shi data gani mura ran. Kasa cewa komai tayi yanda shima baice mata Kala ba don kwata kwata bai dago ya kalleta ba tun bayan kallo daya daya mata saidan kallonta da yake ta gefen ido ganin yanda ta kauda kanta gefe idanunta sun dan kumbura sunyi jaa, ganin tana shirin dagowa ya sashi kauda nashi idanun gefe "Zan tafi gida, Ina buqatar rabuwar auren mu" Dan dagowa yayi ya kalleta don yayi mamakin futowa daga zancen daga Bakinta saidai baice komai ba ya kura mata idanu yana son karantarta "Da izinin za zaki tafi?" Rai Adan bace ta kalleshi ido cikin ido, kafin ta sauke nata don yayi mata mugun kwarjini tace "bana buqatar izinin kowa, zama na anan bashi amfani" "And who told you that?" Yayi saurin tarar nunfashinta Baki a sake ta dago ta kalleshi, wani irin abu na tsaya mata a makoshi, saurin runtse idanunta tayi ta bude su yar akanshi tana kokarin tattaro courage dinta tace "bana buqatar aure a kaina tunda anyi banning dina daga uae babu amfanin auren, daman anyi shi ne saboda yarjejeniya da mukayi, tunda ban samu abunda na nema ba Ina son ka sake ni" Yanda take fada adan fada fada ya bashi mamaki sosai, wannan yar yarinyar ce ke mashi magana haka lallai ya jama kanshi raini, saidai zai koya mata hankali, rai Adan bace ya kike gadan gadan yayo kanta, saurin jaa baya tayi har tana turgudewa gabanta na bugu fat fat don koshi daya karaso gabanta saida yaji bugun zuciyar, saurin runtse idanunshi yayi idanunshi sunyi jaa sosai yace "how dare you talk to me like that? Bakya bukatar auren? Babu macen data isa ta kalli cikin idanuna ta fada min abunda zanyi, now open your ears ki saurare ni, you are going no where, zaki bar gidan nan only if I say so, and I will only free you when I'm pleased" Da sauri ta dago ta kare mashi kallo, kallon kama raina kin hankali, shima ita yake kallo kuma tsaf ya gane ma'anar kallon, saurin hana kanta kukan da take shirin yi tayi, tana son bude Bakinta saidai mamakin shi ya hanata, kallonta yayi sama da Kasa kafin ya juya ya wuce dakinshi ya barta a sandare, wani irin haushi da takaicin shi yake ji, me yake nufi kenan? Ai kuwa zata nuna mashi ita ba yarinyar yake kallonta dashi ba. A zafafe ta fuce daga dakin ranta ya mugun sosu sosai Kalaman shi sun mata zafi,koda ta karasa daki zarya ta fara yi acikin dakin "I will on free you when I'm pleased!!!!" Me yake nufi kenan, ta fada da dan karfi wannan kalaman sunyi mata zafi sosai. Da kyar ta lallaba kanta taga Safiya ranar don hancin Ma qaurace mata tayi, kuka kam saida tayi shi don idan batayi ba bazata samu sassauci ba, Sai bayan sallar asuba barci ya kwasheta akan sallaya.
Karfe sha daya daidai ya fito cikin shirinsa kamar kullum na kananun kaya, sunyi mashi masifar kyau Sai kamshi yake, wayar shi ce kawai a hannunshi Sai laptop bag dinsa ,saukowa kasa yayi ya bi hanyar dazai kaishi zuwa bedroom dinta, hankali kwance ya danyi knocking ya bude kofar, a zaune ya taddata ta gefen gado ga akwatinta dake gefenta ta dafe kanta, ta dade da Tashi ta tayi wanka ta shirya tana tunanin yanda zatayi, gashi ta kira haifa yafi sau Nawa, idan ta kira baya shiga kwata kwata, knocking din da taji baisa ta dago ba don Duk tunaninta Nadine ce ta shigo dakin, ahankali kamshinsa ke shiga cikin hancinta wanda ke sa zuciyarta racing sosai, saurin dagowa tayi ta mashi kallo daya kafin ta kauda kanta gefe, takowa yayi dan nesa da ita kadan ya kura Mata idanu, saida ya dauke kusan minti biyar a tsaye baice mata qala ba itama bata ce mashi ci kanka ba,rai a bace ya fuce daga dakin ta bishi da kallo harya bace mata daga gani. Breakfast kawai yayi ya fuce daga gidan, saida ya tsaya wajen masu gadi kafin yaja motar ya bar anguwan gaba daya. Yana fita daga dakinta ta janyo mayafin abayar jikinta tayi rolling akanta tare da janyo wayarta, taba shirin fita saiga Nadine ta shigo hannunta dauke da tray na abinci data saba kawo mata, da ido Nadine ta bita ganin ta janyo akwati, bata shiga hurumin da ba nata ba shiyasa tayi saurin cewa "ma'am ga breakfast" Ba tare da ta kalli Nadine dinba tace "thanks Nadine baba buqata I'm okay" Tana kaiwa nan ta janyo akwatin nata ta fito daga dakin, tana shirin sauka dashi Nadine ta karaso tace "let me help you ma"
Kasa suka sauko tare ta karbi akwatin tace "thank you Nadine" ta fuce daga parlor, ahankli cikin natsuwa take tafiya Har tazo bakin gate, da sauri security ya futo daga dakinsa don ya hangota ta cctv camera da aka saka a kusa da gate, "good morning ma'am" Morning tayi saurin amsa mashi, ganin baiyi yunkurin bude kofar ba kuka tasan smart gate ne yasa ta juyo ta kalleshi shima ita yake kallo tace "ka bude gate Zan fita ne" "I'm sorry ma, but sir yace Kar abar kowa ya fita daga gidan nan" Kura mashi idanu tayi ta sake cewa "what do you mean?" "I'm so sorry ma'am I can't let you out" Rai abace ta sake kallonshi tace "lub yaushe yace maka Kar abar kowa ya fita" "Dazu ne ya bada umarni I'm sorry ma" Rai abace kamar ta shakeshi take ji, wani irin kuka ne yake neman kufce mata, ta wuce cikin gidan rai abace, Nadine da taga shigo wants saitayi makakon ganinta sosai Har ta wuce sama, da sauri gate man ya janyo akwatin nata ya shige dashi Nadine ta karba ta wuce mata dashi sama, koda ta hau sama kuka ta fashe akan gado, ta rasa wani tunani satayi, mai yake nufi da ita kenan, wannan wani irin masifa ne,a dake ka a hanaka kuka, ranta a bace yake sosai, haushin sa ya ninku a zuciyarta. Koda Nadine ta shigo mata da akwatinta ta tausaya mata ganin irin kukan da take yi "I'm sorry ma'am bansan meke damunki ba but ba kuka ya kamar kiyi ba, try and fine d solution to your problem" Dago da jajayen idanunta tayi ta kalli Nadine tace "Nadine please help me out, Ina don barin gidan nan, bana son zama" Takowa Nadine tayi Har gabanta ya zauna gefenta tace "Bana son shiga hurumin da ba Nawa ba, kuka bazan tambayeki ba, but inaso kiyi hakuri ki daina kukan" "Nadine Wallahi bana son zama acikin gidan nan, ko Inuwa daya bana son hadawa dashi" Shuru Nadine tayi don kanta ya gama rikidewa tace "na taba shiga irin halin da kika shiga na tsabar wani abu lokaci guda lokacin ina kamar shekaru ki, saidai na tabbatar matsala ta da taki ba daya bace don bansan menene matsalarki ba" Nunfasawa tayi kafin tace "you need to be strong and believe in your self, kuka ba solution bane karshe Ma zai Kara maki ciwo ne don kuka ke tunzira mutun, ki gode ma Allah you have everything in life, baki rasa ci ba Baki rasa sha ba, you have a family you can turn to, kinada yayanki wanda ya dam…." Da sauri amra data kura mata idanu bayan ta tsagaita kukan ta kalleta jin abunda ta fada, saurin kauda kanta tayi tace "how can I calm down bayan bana da kowa bana tare da family's nawa, banma san a wani hali suke ciki ba" Cikin mamakin kalamanta Nadine ta kalleta. Ta Kasa dago zancen amra din "But ma'am you have your brother, you can talk to him" Dago da jajayen idanunta tayi tace "he's not my brother, he's my…husband" Nan take Nadine ta dago zancen, tayi mamaki sosai, don bata taba tsammanin Akwai aure tsakaninsu ba, Toh indai mata da miji ne maisa babu alamun haka a tattare dasu ta tambayi kanta. Nadine ta dade sosai a wajenta ba tare da ta tambayeta matsalarta ba ta bata shawarwari wanda ya sata jin sauqin zafi da ranta keyi mata harta samu tayi breakfast ta kwanta don kanta dake mata ciwo sosai.
Bangaren Amar tun bayan fitarshi bayan ya jama driver kunne akan Kar yabar kowa ya fita daga gidan ya wuce wajen da suke haduwa da asad,sun dade sosai suna tattaunawa, ya dade sosai waje shi don har sallar juma'a tare sukayi.
Karfe takwas daidai ya Koma gida, lokacin daya shiga cikin gidan babu kowa a parlor direct ya wuce bedroom dinshi yayi wanka ya sauya zuwa wasu kayan daban wanda suka amshesa kafun ya fito rike da keys dinshi da wayanshi, baibi takan dakinta ba don yaga alamu zatayi kafiya akan abu don haka shi kuma baya son haka don yana ganin hakan kamar raini ne gashi yanxu yaga kamar tayi growing wings don ko gaishesa batayi, abunda ya bata mashi rai kenan daya sashi takaicin…. Saurin kauda zancen yayi don zuciyar shi ta fara masa hasashen moments din su tare, cije lower lips dinshi yayi, ya runtse idanunshi daman kwana yake da tunanin abun a ranshi, don gaba daya Duk Safiyar asuba Sai manhood dinshi tayi kuka alamun how healthy he is,don shi Ma buqaci ne sosai don tunda yayi testing abun ya fara loosing home training dinshi shiyasa ya qaurace Ma ganinta cikin kwanakin bayan dawowar ta daga asibiti.