Kenza eBookz

Auren katin kasa complete - Chapter 37

Auren katin kasa complete - Chapter 37

Auren katin kasa complete Chapter 37: Auren katin kasa complete Chapter 37. Kamar daga sama suka fara jin karar helicopter na yawo a zarar yin samaniya don…

4,123 words

Kamar daga sama suka fara jin karar helicopter na yawo a zarar yin samaniya don kamar an wullosu, da sauri ogan ya kalli gabas kafin ya cije lebenshi yace "an tarfo mu, kowa ya gudu" Haka suka dunga gudu, dayake mugaye ne haka suka dunga harbin mutane da suka mimmike don neman hanyar guduwa, tun daga sama sojajin suka so su fara Harbi ganin suna neman guduwa saidai babu hali don zasu iya hallaka mutane, haka sukayi landing wasu suka bi hanyar dajin da sukabi sauran kuma suka tsaya,tunda sukayi landing ya Kasa motsawa don tun daga sama ya hango yanda mutane ke kwance, asad ne daya rigada ya fita ya ga situation din wajen kafin yayi saurin tura health team da suke cikin daya daga cikin helicopters din don su duba masu taimakon gaggawa, mutane biyar ne kawai suka rasa rayukansu ciki Harda driver Sai kuma mace daya ta suke tunanin kamar zuciyarta ce ta kusa bugawa, asad baisan wacece amra ba don hotonta ya gani kawai, sannan cikin mutanen wajen bai kura da itaba don Har gaban inda take kwance bayan an daura ta kan emergency bed, dalilin hijab dinta dake kan fuskanta data jawo Har hancinta yasa bai Lura ba, takowa yayi har gaban Amar dake zaune fuskanshi tamm bazaka taba tantance a wani yanayi yake ciki ba, dago da rinannun idanunshi yayi yana kallon asad tare da sauraron bayanan shi "oga mutane biyar ne suka mutu, sauran mutane babu wanda ya samu rauni, Sai mace daya da Muna kyautata zaton kamar zuciyarta taso bugawa don Har yanxu she's not responding Muna bata taimakon gaggaw…." Bai tsaya sauraron asad ba ya fito a gaggauce ya fara wucewa, mutane kamar sun san waye shi suka fara bashi hanya Duk tashin hankalin da suke ciki bai hana sun zuba mashi idanu ba ganin yanda yake tafiya cikin izza da qasaita. Saida ya duba ko ina bai ganta ba, da sauri ya fara bin motocin wajen da kallo daya bayan daya kusan guda goma ajere, nan take idanunshi suka sauka kan motar driver da suka karbi number shi da plate number na motar tashi, dan waigowa yayi wajen mutanen dake zaune yace "waye driver motar nan" Daya daga cikin mazan da suke cikin motar ne yayi saurin cewa "yallabai gashi nan Akwance shima an kashe sa" Saurin runtse idanu yayi sosai yace "Duk wanda yake cikin motar ya miqe tsaye" Nan duka suka mike su kusan shida saidai babu amra a cikin su kuma baiyi tunanin itace matar da asad ke magana akai ba, wani irin zazafan numfashi ya sauke idanunshi sun sake yin wani jaaa sosai, ganin haka yasa asad saurin zuwa gabanshi ahankali cikin rada yace "I think bata cikin motar nan," Kwata kwata baya Ma jinMaganar da asad ke mashi, saida ya dauka kusan minti ashirin kafin daya daga cikin health team tace "sir Mun samu pulse din wannan, I think she's alive" Dago da idanunshi yayi ya dubai matar kafin ya sauke idanun nashi kan matar da take magana akai, idanunshi ya bude sosai, ya kasa koda motsawa, tabbas hijab din da ya gani ne a jikinta lokacin data fito daga gidan ta cikin cctv camera, kamar zaki haka ya dunfaro wajen ya yaya chak ya kura mata idanu, jini Duk ya bata gaban hijab din nata, cikin sauri ya sa hannu ya zame hijab din daga Bakinta, yana yin arba da fuskar ya runtse idanunshi ya budesu sosai, ya kasa cewa komai ganin haka yasa asad shima matsowa Har inda take ya kafa mata idanu Sai a lokacin ya gane itace suke nema. "Oga she's the one" Shuru asad yayi baice qala ba don kamar tunani yake kafin ya kalli health team din yace "what's her condition?" Da sauri wata soja budurwa ta kalleshi tace "she's stable sir, shock ne ya kamata wanda yasa zuciya ta ya kusa bugawa, she needs somewhere peacefuly da rest zata dawo daidai" Bai kalli budurwa ba ya sake tambaya "and this blood stain?" Da sauri daya daga cikin mutanen yace "Jinin driver ne don shi aka harba maimakon ita lokacin da tayi ihu" Nan take jini shi ya sake boiling inda Ana measuring zafin zuciya za a gane yanda yayi high sosai babu abunda yake fada aranshi sai "hmmm" Ya rasa mema zaiyi mata yaji dadi aranshi, zuciyar shi ta hasala sosai, yayi warning dinta bataji magananshi ba. Kallon asad yayi yace "ka sa akawo available motoci daga kusa su tafi da mutanen nan inda zasuje,let's move with those that got injured" Asad najin haka yasan me yake nufi don haka yasa manyan sojoji guda goma su tsaya don kula da lafiyar mutanen wajen sauran waenda suka mutu aka debesu zuwa helicopter din health team, saida akazo tafiya da amra yace su dakata, nuni ya masu da su sakata a helicopter sun da yake, haka suka gurgura emergency bed din zuwa cikin helicopter din suka saka ta tare da likitoci biyu daga cikin health team, shi dai asad bai bisu ba ya tsaya tukunna saboda motocin da zasu zo su dauki mutanen wajen. Tunda ya suka Tashi sama bai sake kallon ko inda take ba, saboda yanda yake jin wani zafi ganin yanayin da take ciki,tunanin yanda zaiyi dealing da ita yake yanda bazata sake tunanin taka umarnin daya bata ba, kamar wanda aka tsungula ya zaro wayanshi ya soma kira, yana gamawa ya kashe ya kira landline din gidan shi na larrics, Nadine dake zaune hankali tashe tayi picking call din kafin ta saka a kunnenta, "go and bring her few clothes and pack your belongings," damm gabanta ya fadi da jin abunda yace bata gama tunani ba ya cigaba, "driver will be waiting for you outside, come along with your passport" Yana kaiwa nan ya kashe wayar, da sauri ta miqe ta tattara kayanta Harda kukanta don tunaninta korar ta yayi saidai tayi mamakin jin yace driver na jiranta a waje, agurguje ta fito da yar jakar kayanta ta shige motar driver ya jasu, Agaban headquarters driver ya dire ta, cikin Yan mintuna qalilan helicopter su ya dira a field din headquarters, ahankali ya soma saukowa kafin a sauko da amra wadda Har lokacin bata dawo hayyacinta ba, dan asibitin dake cikin headquarters aka wuce da ita aka cire mata kayan zuwa wasu wanda Nadine ta taho dashi kafin a mata allura don zuciyarta ta samu relive din shock din data shiga. Takowa Nadine tayi Har gaban gadon da aka kwantar da ita ta kare mata kallo, fuskarta tayi fayau Har wani yar rama tayi, dukda bata san wani hali take ciki ba tausayinta ya gama dabaibaiye zuciyarta take tayi alqawarin koma menene damuwarta zata taimaka mata. Manyan ambulance ne suka shigo cikin headquarter aciki aka saka ta tare da Nadine, kowa dake cikin headquarters saida ya shaida qila yar governor ce aka ceto ko kuma yar wani minister din, baibi motar ambulance ba ya shige cikin Tashi ya figi motar, wayarshi dake Kara yayi saurin picking yana dauka ya saka a hands free, daga chan baba garen aka soma magana "sir the visa is ready, and the private jet also" "Okay" kawai yace ya kashe wayan kafin ya Kara ma motarshi speed sosai. Agurguje dai saiga amra a airport ita da Nadine, dayake ya rigada yayi proceeding komai in less than an hour suna zuwa airports aka wuce dasu wajen private jet Har aka shige da amra wanda ke kwance kamar gawa, kallon Nadine yayi don shi bazai bisu ba tukunna saiya gama abunda ya kawo shi "When you arrive my personal guard will be there to pick you up," Kallon agogon shi yayi ya juya harzai tafi ya dawo yace "take care of her" Yana kaiwa nan ya fuce suna suka hau jirgin, abun mamaki Nadine na ganin jirgin tana an rubuta Taura baro baro, tasan sir yana bearing sunan saidai bata kawo ko nashi bane ko ba nashi bane saidai taga abunda ake kira da luxury lokacin da ta shiga cikin jet din gashi sak nan nan ake da su. Bangaren Amar kuwa wata zuciyar nashi na mashi fadan yin hakan don yasan zai sha wahala idan bata kusa don ya fara sabama kanshi da abubuwan da Allah ya albarkaceta dashi, saidai kuma yana ganin wannan opportunity ne da zai tabbatar idan Har cikinshi ya shiga jikinta ko bai shiga ba bayan wannan plans dinshi da yake akanta na nan yanda ya tsara tun farko kafin ta dawo Nigeria.

Gida ya tafi direct don wani irin ciwon kai ne ya addabeshi sosai, yana zuwa ya wuce dakinshi ya watsa ruwa ya kwanta don ya samu ya danyi barci kozai ji saukin abunda yake ji, saidai kuma barcin gaba daya ya kaurace masa, tunanin da baya son yin ya tsaya mashi arai, zuciyar shi nayi mashi wani irin nauyi ganinta da yayi a wannan yanayi, runtse idanunshi yayi sosai aranshi yace "why won't you get out my mind" Tsaki ya danyi ya sake juyawa tare da kure ac din dakin ya janyo duvet Har ya samu barci ya nasarar daukanshi.

Dubai United Arab Emirates Uae 🇦🇪….. Jet dinsu na sauka a uae international airport akayi masu Duk wani arrangement na shiga kasar ba tare da sun motsa ba, Nadine dai tana ganin rayuwar manya, don gaba daya ta gama tsurewa, Duk rayuwar a Cameroon bata taba shiga jet ba, amra dai tana daga chan wani bangare na cikin jet din da masu bata kulawa don Har lokacin bata farfado ba, minti bayar da landing din wata ambulance din ta karaso, m5 ne ya shigo Har cikin jet din ya jagoranci Nadine din suka sauka kasa zuwa motar dake harabar filin jirgin, iska ce mai dadi ke kadawa sosai. Ahankali aka saka amra cikin ambulance din itakuma Nadine ta shiga wata haddaiyar motar daban wanda m5 yazo da ita suka wuce gida tare da special doctor din Amar don shi zai kula da lafiyar amra. Tafiyar minti talatin suka iso tafkeken penthouse din general Amar,inda tundaga shigarsu Nadine ta soma bama idanunta hakkinsa, tunda take harkar aiki wayo house keeping bata taba ganin gida makamancin wannan ba, Har m5 yayi parking bataji ba don ta Lula tunani, saida ya bude mata kofa kafin ta dawo hayyacinta ta fito daga cikin motar, already motar data shugo da amra tayi parking itama Har an sauko da ita daga cikin motar, m5 ne yayi gaba suka bishi abaya dukkansu, doorbell ya dannan pablo dake expecting dinsu yayi saurin budewa kafin su saka kai cikin main parlor din, Nadine dai ta zama kamar jaka don da kyar ta shiga cikin gidan, direct wurin suka wuce kafin m5 ya Danna floor 2 don nan ne masaukin su, fadar haduwa floor dinnan Ma bata lokaci ne don dakuna ne ajere Sai babban cozy sitting room tamkeke da yasha kayan duniya na gani na fada, babban dakin aka wuce da amra nan Ma ba a cewa komai Sai Masha Allah don an zuba duniya ba kadan ba, akan wani hadadden English bed aka kwantar da ita da taimakon nurse din dake tare da doctor din kafin su fara dubata don Har lokacin barci take sakamakon allurar da akayi mata. A Last floor m5 ya nunama Nadine dakinta wanda yaci uwar na wanda aka bata a larrics don itama harda dan coffee table and chairs aka aje mata da tv Sai tamkeken bed dinta.. [7/11, 11:17 PM] +218 92-2035171: Update Unedited page Bai dawo gidan ba saida ya tsaya akayi sallar isha'I dashi kafin ya shugo gidan, lokacin daya shigo main sitting room babu kowa a kasan don haka ya wuce bedroom dinshi direct don hes not in a good mood. Bangaren amra tun bayan fitar ammah wani irin zazzabi ya rufeta, babu wanda yasan da situation din da take ciki, don ko sallar magrib kasa tashi tayi don ta samu tayi, tana nan kudundine cikin blanket akayi knocking kafin a shugo, lantana ce ta shigo hannunta dauke da tray da ammah ta zubama amra abinci, da sallama ta karaso dakin ta aje a kasan carpet, ganin amra a duqunqune tana rawar sanyi yasa ta karaso gaban gadon tace ''anty baki da lafiya ne?'' kasa Magana amra tayi don gaba daya ta zama very weak, sai karkarwa da jikinta keyi, ganin haka yasa lantana fucewa daga dakin zuwa part din ammah, da sallama ta shiga sitting room din ammah don bata shiga cikin bedroom dinta kai tsaye, tundaga bedroom ammah taji sallamanta don haka tace ''shugo'' Ahankali lantana ta bude bedroom din ta shugo daga bakin kofa ta tsaya tace ''hajiya nakaima bakuwar abunci saidai na ga kamar bata jin dadi,'' Ammah dake zaune gaban dresser ta juyo ta kalli lantana tace ''subhanallah, bari nazo dakin'' Futa lantana tayi ammah ma ta miqe tabi bayanta, amar dake shirin hawowa part din yana ganin ammah da yanda ta rude yayi saurin kallon inda take shirin shiga,ammah ma bata lura dashi ba don yana tsaye wajen stairs, dakin amra ta shige direct cikin sassarfa, lanatana na biye da ita,kai tsaye gaban gadon ammah ta tsaya ganin yanda amra take rawar sanyi, idanunta na neman rufewa, hankali atashe tace ''daughter meke damunki subhanallah'' tallafota ammah tayi ta janye duvet din data qanqame a jikinta kallon lantana ammah tayi tace ''jeki dubamin ko Muhammad ya dawo akaita asibiti'' Lanatana na juyawa don kiranshi sai gashi ya shugo dakin shima kai tsaye, sanye yake da doguwan jellabiya fara har kasa, hannunshi cikin aljihun rigar ya zuba masu idanu, juyowa ammah tayi ganin shi tsaye tace ''yaka tsaya anan, shugo mana ka dauketa Mukai ta asibiti'' Kasa daga kafafunshi yayi, ranshi ya a dagule, ganin ya tsaya kyam ya qi motsawa yasa ammah juyowa ta kalleshi tace ''muhammad? Kana jina kuwa'' Anatse ya bude baki yace ''I will call doctor yazo ya dubata'' yana kaiwa nan ya janyo wayarshi yayi dialing contact din family doctor dinsu, doctor na daga ya fuce daga dakin. Kauda kai kawai ammah tayi tana mamakin hali irin nashi, me Kenan yake nufi? Badai yana kan bakarshi na sakin yarinyar ba, tasan shi da kafewa akan abu saidai wannan karan zata nuna mashi ta isa dashi don ita ta haife shi bashi ya haifeta ba, kallon lanatana ammah ta sakeyi hannunta rike dana amra dake karkarwa ''shiga bathroom ki kawo min luke warm water da towel'' ''toh hajiya'' lanatana ta fada tare da shigewa bathroom din dakin, agurguje ta debo ruwa a cikin bowl da towel ta karaso gaban ammah tare da dukawa, karwan towel din ammah tayi ta jiqashi kafin ta fara gogama amra a fuskanta da wuyanta,ta dae sosai akan amra tana shafa mata ruwan don taji dadin jikinta saidai kamar ma kara mata zazzabin akeyi don jikin yayi zumm sosai, nunfashinta ma kanshi da zafi yake futa daga bakinta, ganin haka yasa ammah tace ''wannan wani irin zazzabi ne oh ni Maryam, yarinya daga dawowa'' kallon lanata ammah tayi tace ''ke rage min ac nan'' Mikewa lanatana tayi don itama a furgice take ta kashe ac, suna nan zaune after like 20mins saiga doctor, amar ne ya shigo dashi har cikin dakin, ammah na ganin haka ta bashi waje ya fara dubata, futa lanatana tayi don ta basu waje shima gogan bai tsaya bay a fuce ganin irin kallon da ammah take jefanshi. Cikin gaggawa doctor ya dubata harda drip ya saka mata ganin ta zama weak, kafin ya mata allurai da zai saukar da zazzabin, saida ya tabbatar shes stable kafin ya kalli ammah yace ''hajiya bamu gaisa bama ina wuni'' Murmushi ammah tayi don tana zaune daga bakin gadon tace ''lafiya kalua doctor, ya jikin nata?'' ''alhamdullah its just a fever, nayi mata allurai da zai saukar dashi sannan ga drip nan na saka mata zuwa anjima idan yak are sai a cire mata'' Godiya sosai ammah tayi mashi kafin ya ta rakoshi har kasa, doctor na tafiya ta wuce dakin amar kai tsaye, tana knocking kofar tace ''muhammd'' Amar dake kwance daga shi sai shorts yayi saurin miqewa ya janyo jallabiyanshi ya saka ya bude kofar bedroom din, ganin ammah tsaye fuskanta babu walwala yasa ya sauke kanshi kasa, kallonshi tayi cikin fada tace ''muhammad lafiyanka kuwa?matarka na chan kwance babu lafiya kai kana nan zaune hankalinka kwance? Waye zai kula maka da ita ni? '' ''im sorry ammah ba haka bane'' ya fada kanshi a kasa ''okay menene then? Don't tell me kana kan bakar ka saika saki yarinyar nan? Look bari kaji, Muhammad baka isa ka saki yarinyar nan ba saina baka umarnin haka, don sainaji daga bakinta idan tana raayin haka'' ta karashe rai abace Dan dagowa yayi ya kalli ammah zuciyanshi na mashi zafi sosai yace ''but ammah….'' Katse shi tayi ta hanyar cewa ''but what?'' Sunkuyar dakanshi yayi don bazai iya kallon cikin idanunta a wannan yanayi ba, ganin haka yasa ammah fucewa daga bedroom din nashi gaba daya, tana fucewa ya cije lower lips dinshi, saida wajen yayi jaa sosai amar zai fashe, dakin ya koma ya zauna bakin gadonshi ya dafe kanshi, ahanakli ya soma Magana ''ya allah, ammah please karki hanani abunda nayi niya, babu wani amfani aje mace arayuwana, bana buqata'' Ranshi a dagule haka ya kwanta, abubuwa sunyi mashi yawa.

Ammah na fitowa daga bedroom dinshi ta nufi hanyar stairs, salima dake zaune a dining tana cin abunci ta hango ta, da sauri ta karasa cin abuncin don daman kadan ya rage a plate din,kafin ta miqe zuwa wajen ammah ''ammah naaa tun daxu nake zuwa dakinki ban ganki ba'' Murmushi ammah tayi mata tace ''ina dakin daughter ne bata jin dadi'' Shuru salima tayi kafin ta dan tabe baki, kallonta ammah tayi tana karantar ta, kafin tace ''ina salim?yayi dinner?'' ''eh yayi tun daxu, har yayi bacci mah,'' ta bata amsa fuskanta dauke da murmushi ''ammah kinci abunci?'' salima ta tambaye ta cikin kulawa Murmushi amma tayi mata kafin tace ''nayi dinner tun daxu, kune dai da kuke son cin dinner late'' Dariya salima tayi suka hau sama atare har daki salima ta rakata kafin tayi mata sallama ta fito, tunda ta fito daga part din ammah ta kafa ma kofar dake chan gefen dakin su kallo, tunani kala kala na yawo aranta, tana son shiga saidai wata zuciyar na hana ta yunqurin shiga. Jiki a mace ta taka zuwa bedroom din tayi knocking, jin shuru babu response yasa ta dan bude kofar ta shiga, a kwance ta tadda amra hannunta da drip, kasa daga kafa salima tayi, hawaye ne ya soma bin kuncinta take tausayin amra ya fara dabaibaye ta, takowa tayi har bakin gadon ta tsaya ta kafe fuskar amra da kallo, ta chanza mata sosai, tayi kiba da cika, ta zama wat babbar mace a fuskanta, kallon yanda take barcin wahala salima tayi, tana jin qaunar yar uwar tata na ninkuwa hade da tausayinta lokaci guda, nan take ta fara tunanin da bata son yi,ganin amra na kokarin juyi da hannunta dake dauke da canula zata danne hannun yasa tayi saurin rike hannun nata don har yadan kumbura kadan, ahankali salima ta taimaka mata ta gyara mata kwanciyar kafin ta janyo mata duvet ta lulluba mata ta juya gaban switch ta rage mata haske kafin ta fuce..

The next morning… Wajen karfe takwas amra ta bude idanunta da sukayi mata nauyi sosai,kallon dakin ta fara yi daga kwance, kafin ta miqe zaune dakyar, cije lebenta tayi jin yanda bayanta ya rike,tace ''arshhh'' da muryarta da baya fita sosai,kallon rail din dake dauke da drip tayi kafin ta maida kallonta ga hannnuta dake mata zugi dauke da canula,anatse ta cire canula din ta kafin ta sauke kafafunta kasa ta wuce bathroom, wanka ta farayi da ruwa mai dumi sosai don jikinta yayi tsami sosai kafin ta wanke bakinta ta dauro alwala, dakin ta dawo ta maida kayan data cire kafin ta shimfida sallaya don gabatar da sallolin da ake binta, tana idarwa ta jingine da bangaon dakin tana tunani, da sallama ammah ta shigo dakin, da sauri amra ta miqe muryarta chan ciki ciki tace ''ina kwana'' Takowa har inda take ammah tayi ta riko hannunta zuwa gefen gadon ta zaunar da iat kfin ta zauna gefenta tace ''morning daughter kin tashi lafiya? Ya jikin ki?'' Anatse amra ta sunkuyar da kanta tace ''alhamdullah da sauqi,'' Murmushi amma tayi mata tace ''bari akawo maki breakfast ko akwai abunda kike so adafa maki'' kasa cewa amra tayi kanta a kasa jiki a mace tace ''ah ah!!'' nunfasawa ammah tayi ganin har yanxu taqi sakewa yasa tace ''toh bari akawo maki saiki samu ki karya,babu abunda ke maki ciwo ko?'' ''ah ah babu nagode ammah'' amra ta fada tana dan murmusawa Wani irin dadi ammah taji kafin ta fuce daga bedroom din, cikin yan mintuna kalilan lanatana ta shigo da lafiyayyan breakfast ta aje mata bayan sun gaisa, lanatana na fita ta tako har inda ta aje mata breakfast din, zama tayi ta deba yanda zai zauna a cikin ta. Nan zaune lantana ta sake dawowa hannunta dauke da kaya doguwar riga mai mayafi mai kyau cuttons,gabanta ta karaso tace ''gashi hajiya tace akawo'' Karba amra tayi tare da yin godiya, kafin ta juya. Anatse ta gama cin abuncin ta mikew ta sauya kaya, rigar ta zauna mata ciff ciff don bubu ce, mai hade da mayafi, tana gama shiri ta dan fesa turaren dake kan dresser, cikin nastsuwa ta kwashe plates din data gama cin abunci da tray din ta futo daga dakin, waige ta fara yi don parts din dake saman suna na da yawa, chan gefe ta hango stairs, cikin natsuwa ta bi hanyar ta fara saukowa, babu kowa a kasan don haka ta fara waigen hanyar kitchen, gashi bata san ko''ina a gidan ba, tana cikin waige waige ta hango hango wani dan sako da sautin cokula, takowa ta farayi don duk tunaninta nan ne hanyar kitchen din, shiga wajen tayi kai tsaye bakinta dauke da sallama, duk atare suka waigo suka zuba mata idanu banda amar dake facing hanyar shugowa dining din, dago tayi idanunta ya suaka akanshi, nan take hannunta ya soma karkarwa don kirish ya rage plate din ya fadi, saurin sauke kanta kasa tayi, kallonta amma tayi tace ''daughter kin sauko?kina buqatan wani abun ne?'' tayi tambayar fuskanta dauke da murumshi, anatse amra ta dubi bangarenta don tana daga gefen amar tace ''daman kitchen nake nema zan aje wannn'' ''ay da kin barshi kin kwanta kin huta lanatana zata kwashe,lantana lantana'' ammah ta fada tana kallon hanyar kitchen, daga chan kitchen lantana ta amsa Aman dai kasa tauna abuncin dake bakinshi yayi don yana ganinta yaga kammaninta da su salima sosai,don badan yaga tana da kiba bama zaice wannan ay salima ce, amar kuwa ta wutsiyar ido ya kalli inda take tsaye kafin ya kauda kanshi gefe, maida hankali da yayi wajen cin abuncin sa cikin kamewa, ba tare da yace tak ba, amra dai kamar ruwa ya cita ta kasa cewa komai saida lanatana ta karaso ta karbi plate din kafin ammah tace ''daughter kije ki huta ko'' Sunkuyar dakai amra tayi kafin ta juya, har zata tafi ta dawo tace ''ina kwanan ku'' Aman ne kawai ya amsa ta fuskanshi dauke da surpise, Batare da ta tsaya sanin wanda ya amsa ba ta juya ta wuce sama gabanta na faduwa don wani irin kunyar amar take ji sosai.

Tana fucewa aman ya kalli amma yace ''ammah whos she?'' Murmushi amma tayi ta cigaba da cin abuncinta tace ''your sister inlaw ga mijinta nan a gefenka'' Da sauri amar ya dago ya kalli ammah, itama shi take kallo don ganin reaction dinshi, saurin kauda kanshi gefe yayi ya miqe yabar dinin din, aman kuwa da tambayoyi suka mashi yawa ya sake cewa ''itace matar shi da yayi aure?'' ''yes itace'' ammah ta bashi amsa kai tsaye, jinjina kai kawai yayi

Amra na wucewa sama ta shige daki ta zauna gefen gado ta doka wani uban tagumi, gaba daya jikinta yayi sanyi, tunawa da yanda ko kallon inda take baiyi ba, ahankali wani hawaye mai dumi ke xubowa a fuskanta, tana regretting abubuwa sosai akan shi, yayi mata abunda duk duniya bazata taba ganin laifinshi ba, takaicin kanta takeyi akan yanda ta dunga judding dinshi, ashe gata yake mata, she can clearly recall lokacin data gudu daga gidanshi, ashe all this while shike protecting kannenta shine ya taimake su shine ya inganta rayuwarsu, saurin runtse idanunta tayi tana jin takaicin kanta da yanda ta dunga behaving.

Yana shiga daki bathroom ya shige after few minutes ya fito daure da towel,agaggauce y agama shiryawa cikin kananun kaya, saida ya feshe jikinshi da turarukanshi masu sanyin kamshi kafin ya fuce daga dakin, yana fitowa sama ya wuce zuwa dakin ammah, yana shiga bai jima ba ya fito ya sauka kasa ya fuce daga gidan gaba daya.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull