Auren katin kasa complete - Chapter 38
Auren katin kasa complete Chapter 38: Auren katin kasa complete Chapter 38. Haka amra ta wuni a daki ita kadai, time to time ammah ke shigowa dakin tana…
3,891 words
Haka amra ta wuni a daki ita kadai, time to time ammah ke shigowa dakin tana dubata, su salima kuwa daman sun tafi school, karfe biyu daidai suka dawo ita da salim, daki suka wuce direct suka sauya kaya, salim ne ya fara fitowa yabar salima a daki, direct dakin amra ya wuce yayi knocking kafin ya bude kofar, amra na ganin shi tayi saurin miqewa tsaya, kallonshi ta soma yi tana mamakin yanda ya kara girma, miqewa tayi da saurin ganinshi tsaye shima ya kafa mata idanu, har gabanshi ta tsaya ta mashi murmushi tace ''salim kaima kana fushi dani ko?'' Hannunshi ta janyo fuskanta gwanin ban tausayi tace ''forgive me kaji salim, bazan taba abandoning dinku ba kaida salima'' Saurin rungumeshi tayi tana hawaye shima rungumeta yayi yana hawayen kewar ta, yanxu wannan addar su ce, yana jin abun kamar a mafarki, da kyar amra ta janye jikinta daga na salim, yana ganin haka ya soma goge mata hawyen fuskanta yana mata murmushi, itama murmushin take mashi, kallonshi tayi tana nazari don tunda ya shigo baice mata kala ba don haka tace ''bazaka kulani ba ko salim? Kana fushi dani har yanxu?'' ta fada tana marairaicewa , kallonta yayi ya girgiza mata kai alamun ah ah, daga chan bakin kofa salima data fito daga dakinsu ta hango su tayi saurin karasowa inda suke, kallon yanda amra ta kafe salim da idanu tayi, cikin sauri salima ta karaso dakin ta janyo hannunshi waje ranta a bace tace ''meka tsaya yi anan, wuce mu sauka'' juyawa tayi tare da salim, amra na ganin haka tayi saurin cewa ''salima…' Tsayawa salima tayi ba tare da ta waigo ba, amra na ganin haka tace ''salima dan allah….' Katseta salima tayi ta hanyar cewa ''don allah ki rabu damu adda, na fada maki bama buqatar ki yanxu, alokacin da muka buqace ki ay baki waigo mu ba'' Tana kaiwa nan ta jaa hannun salim suka bar wajen,ammah dake jinsu daga kasa tayi mamakin yanda salima ke Magana da amra, tasan dole suji zafi saboda ta tafi ta dauka shekaru acahn wata kasa ba tare da ta waiwaye su ba saidai sanin cewa basu san halin data shiga sanadinsu bane yasa suke jin haushin ta, Suna saukowa kasa salima ta kalli salim tace ''duk sanda na kara ganinka a dakin nan saina mareka wallahi'' Kallonsu ammah dake zaune a sitting room tayi kafin tace ''salima zo nan'' Karasowa salima tayi don bata lura da ita bama a sitting room, bin bayan salim yayi shima yana gunguni har suka karaso gaban ammah. Zama salima tayi a gefen ammah kanta a kasa, kallonta ammah tayi in a calming tone tace ''why zaki hanashi zuwa wajen yar uwarshi?, nasan kuna jin haushinta but that doesn't give you the audacity kiyi ma addan ki Magana haka,kin tsaya kin saurari dalilinta na qin dawowa da tayi?'' Jiki a mace salima ta girgiza kanta, nunfasawa ammah tayi ta shafa kanta cikin dabara ta manya tace ''haba dearest, bai kamata kina mata Magana ahaka ba kinji ko, kamata yayi ki sameta kuyi Magana ta fahimta, babu yanda za ayi dan uwanka na jini yayi abandoning dinka, listen to her with open ears kinji ko?'' Hawaye ne ya zuboma salima tayi saurin sharewa tace ''toh ammah'' ''yauwa ko kefa, kuje kuci abunci kafin lokacin islamiyya yayi'' ''tohm ammah'' salima ta fada tare da miqewa, dining suka wuce ta zuba masu abunci ita da salim.
Bangaren amar direct headqauters ya wuce inda suka hadu hardasu m5 da sojojin da suka karso suka shiga helicopters kusan guda uku, tafiyar awa hudu ta fiddasu daga Nigeria, daidai inda bunciken su ya tabbatar da nan ne factory din alhaji kabiru suka tsaya, wajen gaba daya daji ne gaba da, suna landing duk suka fifito harda asad da mukarrabban shi,gaba daya kowannensu hannunsu dauke da bindigu, tun daga bakin gate suka fara harbi, agurgije suka shiga cikin factory din, nan take yaran alhaji kabiru suma suka fara don zuwan bazata sukayi masu, nan take wajen ya kacame da karar harbi, an kama kusan mutane talatin da suke cikin factory din, waenda sukayi yunkurin guduwa ma saida aka kamosu, daga bayan factory din kuwa katon gida ne da dakuna inda maaikatan ke kwana, nan take suka farabinciken ko ina, akallah sun samu kudi a cikin factory din akallah kusan billion goma, bayan wannan harda kwayoyin da sukayi sealing, abunda yafi bama su amar mamaki shine suna yin production din drugs din professionally harda batch number da seal din nafdac alamun shaidar drug din an tantance su, nan take suka fara fidda drugs din daya bayan daya, da chemicals din da suke amfani dasu wajen hadawa, harda waste din drugs din komais aida suka dauka saboda evidence, asad dai tsayawa yayi yana kallon yanda ake ainihin bincike, ba kmar yanda sukeyi baa nan Nigeria, don nan idan an kama mutun kotu kawai ake kaishi a yanke mashi hukunci, suko su amar da sauran sojojin dake karkashinsa daga uae aiki sukeyi tukuru wajen tattara komai babu abunda suka bari, saida suka gama komai suka tattara komai kafin su rufe wajen gaba daya.
Basu suka dawo ba sai wajen karfe sha biyu na dare, daga headquarters gida ya wuce direct, yana shugowa ya wuce dakinshi direct. Washe gari da sasafe ma haka ya shirya ya fuce daga gidan tun kafin kowa ya tashi.
Bangaren Aman ya natsu sosai, ya daina shaye shaye ya zama natsatse sosai da taimakon salima, wanda yanxu sun fara jonewa dukda har yanxu bata karbi tayin soyayyar shi shiko kullum nuna mata yake yanda yake qaunarta, yanxu ya maida hankali sosi wajen aiki a company don gayara abunda mahaifin ya lalata, relationship dinshi da amar ya gyaru sosai don yanxu baya mashi irin kallon da yake mashi a baya, don ya gano da taimakon aman aka gano duk wani ayyukan da alhaji kabiru yayi.
Salima ma tun bayan Magana da ammah tayi mata akan amra, tayi kokarin danne abunda ke zuciyarta, saidai har yanxu ta kasa daina fushi da ita, don ko hanyar da take bata bi,salim dai kullum yana zuwa wajen amra don hanashi da salima keyi yanxu ta daina. Bangare amra har yanxu ta kasa sakewa da gidan,yau kwanan ta hudu da suwa gidan kullum tana kunshe a daki,zuwan da salim keyi ne ke debe mata kewa, abunda yake tayar mata da hankali shine yanda kwata kwata salim baya Magana, gashi salima taki bata dama zuyi Magana don tsoron tambayarta ma take yi, haka zaizo idan tayi Magana yayi shuru sai ta fashe da kuka.
Saturday morning…. Tunda ta tashi take fama da ciwon kai,tun bayan datayi wanka ta zauna bakin gado ta doka uban tagumi, tan nan zaune lanatana ta kawo mata breakfast, tana futa salim ya shugo, kallonshiamra tayi harya karaso inda take ya zauna agefenta,kallonshi amra tayi tace ''salim ka tashi?'' girgiza mata kai kawai yayi yana murmushi Tana ganin haka tace ''salim baka Magana ne?'' Nan ma girgiza mata kai yayi, jiknta ne yayi sanyi ta kara tambayrshi ''meysa baka Magana?'' Sunkuyar da kanshi yayi kasa tana ganin haka tace ''kaci abunci?'' Girgiza mata kai ya sakeyi alamun baici komai ba tana ganin haka tace ''zo muci tare'' Da murnarshi ya zauna gefenta ta jawo masu abunci sukaci atare, tana kallonshi tana jin dadi aranta. Suna gamawa ta kafa mashi idanu tana kallonshi babu uhm babu uhm uhm.
Baibar dakin amra ba saida lokacin islmiyya yayi ya koma dakinsu don ya shirya, yna shigowa salima ta waigo ta kalleshi kafin ta kauda kanta tace ''kaidai wallahi kana da naci, harka manta wahalar da muka sha a gidan uncle, shine kake..'' Juyowa tayi ganin ya wuce bathroom baima tsaya ya saurareyta ba yana fitowa ta kalleshi tace ''banza kurma kawai'' Juyowa yayi ya galla mata harara, banza tayi dashi ta saka hijab dinta tace ''inkaga dama ka sauko mu tafi'' tana kaiwa nan ta fuce daga dakin. Dakin ammah ta fara zuwa tayi mata sallama kafin ta sauka kasa wajen driver. Driver dake zaune da maigadi suna hira ya hangota daga nesa kallon ta yayi kafin yace ''baba mai gadi yarinyarnan gaba daya zubinta na Fulani ne, yanda kasan gari daya suka fito da mlm labaran,'' juyowa baba mai gadi yayi yace ''naji ance yayan kanin hajiya ne, kasan itama bafullatana ce saidai basa kama da yan gidan kwata kwata'' Miqewa driver yayi yace bari naje na saukesu a islamiyya'' Yana kaiwa nan ya karasa ya bude motar, tana ganinshi ta gaishesa ta shige motar, cikin yan mintuna salim ya fito shima suka fuce daga gidan.
Bayan fitarsu ammah ta fito cikin shigarta da kamala,riga da zani na atamfa, dakin amra ta wuce direct tana shiga ta hangota gefen gado ta doka uban tagumi, murmsuhi amma tayi ta karso har bakin gadon ganin gaba daya tunaninta yayi nisa, ''daughter, lafiya dai tunanin me kikeyi'' Da sauri amra ta kalleta kafin ta sunkuyar da kanta kasa tace ''ina wuni ammah'' ''alafiya lau daughter'' ammah ta masa ta fuskanta dauke da murmushi Shuru ne yadan ratsa tsakaninsu kafin ammah ta nunfasa tace ''menene asalin sunanki?'' Atsanake amra tace ''Aisha'' ''masha allah'' ammah ta fada tana murmusawa kafin ta cigaba ''''aisha ina son ki daukeni a matsayin uwa kamar yanda su salima suka daukeni, inason ki cire kunya ki saki jikinki anan gidan kinji ko?,''
''insha allah'' amra ta fada tana sunkuyar da kanta fuskanta dauke da dan murmushi ''masha allah, yanxu inason naji ta bakinki, ki fada gaskia karki boye min komai, wani irin zama kukayi keda Muhammad achan dubai'' Gaban amra ne ya fadi dammm,samun kanta tayi da kasa cewa komai har saida ammah tace ''karkiji tsoro kinji ki fada min komai, shin zamanku da Muhammad bayan yarjejeniya da kukayi babu komai tsakanin ku?'' 'girgiza kai kawai amra tayi ta kasa cewa komai saida ammah ta sake cewa ''yace kin buqaci ya sakeki?,har yanxu kina son ya sakeki ne?koda kuwa shi baya son yin haka?'' Kasa motsi amra tayi balle ta dago ta bata amsa sai , ammah na ganin haka ta gane tana da matsanancin kunya don haka kai tsaye ba tare da wani kwana kwana ba tace ''kina sonshi?''
Shuru amra tayi hawaye na gangarowa akan fuskanta, koda ace bai dauki kannenta bay a kula dasu ba bazata taba iya kallon mahaifiyarshi tace mata bata son zama dashi ba, Ammah na ganin haka ta sauke ajiyar zuciya tace ''bazanyi forcing dinky ki fada min ba aisha, but kiyi tuanni akai kinji, zan dawo anjima zamu sake maganar nan, '' Tana kaiwa nan ta fuce daga dakin…
Daki ammah ta wuce tayi mata order kayan sawa ready made, dukda bata san size dint aba haka ta bayar ayi mata kafin ta zuwa dan wani lokacin idan komai ya lafa sai suje a dauka size dinta, tana gama waya da designer dinta wato zetatelia fashion house, wayar amar ta soma kira, don tana sane dashi kwana biyu yanda yake doging dinta,ringing daya biyu ya daga wayar yana dagawa tace ''kana ina?'' Magana yayi daga chan bangaren kafin tace ''ina son ka dawo da wuri inada Magana dakai'' tana kaiwa nan ta akshe wayar,mikewa tayi ta shiga dakin closet dinta, abubuwan amfani daga kan sprays, mayukan shafawa masu tsada turarruka, haka ta kwaso ta wuce dakin amra dasu, akwance ta taddata don haka tana shiga tace daughter ga wannan ki fara amfani dashi kafin zuwa nextweek saimuje shopping ko'' Sunkuyarvdakai amra tayi ta mata godiya kafin ta fuce. Kallon abubuwan amra tayi, wani irin dadi taji aranta son dama taba buqatar su sosai.
Karfe shida takwas daidai ya shigo cikin gidan saida ya fara tsayawa a masallaci yayi sllah kafin ya wuce cikin gida, direc t dakinshi ya wuce bai tsaya komai bay a watsa ruwa ya sauya kaya kafin ya fuce daga dakin, hawa stair ya fara yi ya tunkari part din ammah, bai kaiga karasawa ya jiyo muryar amra ''salima don allah ki kulani, wannan silent treatment din da kike bani is killing me, wallahi azeem bazan taba abandoning dinku ba kiyi hakuri ki yafe min'' Kallonta salima tayi don daman tazo kiran salim ne don suje suci dinner shine amra ta tare ta da tambayr meysa salim baya Magana, tambayar ta bata mata rai sosai, don idanda tana tare dasu ay zata san dalilin rashin maganar nashi, abunda yafi bata mata rai Kenan, don haka cikin kuka ta soma Magana harshly ''wallahi adda bazan taba yarda da maganr ki ba, shekara hudu fah?tunda kika tafi baki waigo mu ba sai yanxu, lokacin da muke buqatarki ay baki zoba sai lokacin da bama buqatarki,yanxu dan allah bakiji kunyar tambayar dalilin rashin Magana da salim keyi ba?are you not feeling ashamed?, tunda tun farko baki damu da sanin halin da muka shiga ba maysa yanxu zaki damu, kibarmu yanda kika ganmu'' ta karaseh tana kuka wiwi, itama amra kukan takeyi tana jin zafi da kunan rai, amar dai daga nesa yake hangosu don suna bakin kofa, tsaki kawai yayi ya shige dakin ammah, yana shiga ya taddata tana sallah kan sallaya, karassawa yayi cikin dakin ya zauna kan ottoman harta idar ta shafa, kallon inda yake tayi kafin ta miqe tsaye ta karaso inda yake ta zauna bakin gado, cikin nastuwa yace ''barka da dare ammah'' kallonshi tayi a kamilance tace ''kaga dam aka dawo gida da wuri yau?, ko ince k agama kauce kaucen naka?'' shuru yayi ya kasa dagowa, ''muhammad'' ammah ta kirashi Dan dagowa yayi ya kalleta yace ''naam'' ''da wayonka da hankalinka basaina fada maka maanar hakki ba, na lura da kana son ka nuna min kai ka girma ko?,'' Ta fada tana kallonshi, saurin dagowa yayi yace ''ammah ba haka bane…'' Kallonshi ta sakeyi tace ''so? Gardama zakayi min Kenan?'' Sunkuyar da kanshi yayi kasa ya kasa cewa komai, saida tace ''maysa kake son sakin ta?'' Kamar jira ko yake tayi tambayar yace ''ammah babu amfanin auren, aside from that wannan auren wallahi ban daukeshi a matsayin komai ba, yarjejeniya ne kuma its over, wallahi ammah bana buqatar mace a rayuwana, I have a lot on my he…'' Kasa karasawa yayi ganin yanda fushi ya bayyana a fuskanta karara azafafe tace ''ta gama maka amfani Kenan muhammad wato bari ka sake ta baka buqatar mace arayuwarka, to bari kaji, wallahi wallahi ka roki allah kada yarinyar nan tace itama batason auren don wallahi youll regret it, kai ina tunaninka, im not trying to be selfish over here don zan tambayeta dakaina idan har tace batason auren zan barku kuyi abunda kukeso but inason ka sani, a zamanin nan babu macen da zata zauna da namijin da baya haihuwa duk kyawunka da arzikinka da mukamun ka da kake takama dashi , maysa bazakayi wannan tunanin ba?'' Hade rai yayi ranshi adan bace aranshi yana jin zafin abunda ammah tace wai babu macen da zata iya zama dashi Kenan saboda baya haihuwa duk ajin shi da arxikinshi, shi abunda yafi bata mashi rai shine yanda ammah ke mashi fada akan wannan yarinyar' Dan dagowa yayi idanunshi yayi jaa ya kalli amma muryarshi a kasa yace ''ammah please….you have to understand, nine bana buqata, I don't mind nayi rayuwana a haka, bayan wannan ma ita da kanta ma ta buqaci sakin koda kuwa bata buqata ba ma zan bata dakaina saboda batada wani amfani a wajena, shes not my type, yarinya ce karama ammah, shes just 22,'' Rai abace ammah ta miqe don kwata kwata kamar ma bai gane maganganun da yakeyi ne suke hasala ta ba ''muhammd idan kai ka haifeni zan sani idan kuma nice na tsugunna na haifeka to dole kayi abunda nace, now get out my room,'' ''ammah please I don't mean to upset you, don allah karkiyi fushi'' Ya fada anatse ''muhammd get up, karna kara ganin fuskanka'' ta fada idanunta a rufe don ranta ya baci, daman ance mai hakuri bai iya fushi ba Yana ganin haka gabanshi ya fadi hankali atashe ya rike hannunta ya zaunar da ita cikin sanyin murya yace ''ammah na, please calm down, don allah kiyi hakuri wallahi zanyi duk abunda kike so dan allah kar kiyi fushi dani please, me kikeso ayi yanxu?bakya son na saketa right? Shikenan zanyi abunda kike so'' Bata kalleshi ba tace ''zan kwanta'' Yana jin haka ya miqe jiki a mace yayi mat sallama ya fito rai abace, azafafe ya wuce dakin amra yana zuwa ya bude kofar a zafafe, a durkushe ya taddata ta rike ciki tana kuka, rai abace ya karaso dakin ya kalleta yace ''keeeee!!!'' Yanda ya fada saida dakin ya amsa, da sauri ta miqe tana muzurai gabanta na faduwa,kallon fuskanshi tayi ganin yanda ya karade yayi jaaa kamar bashi ba yasa gabanta faduwa,bata ankare ba ta ganshi gadan gadan yayo kanta, kan kace me nan take ta sulale a sume, dan tsaywa yayi yana kallon ikon allah, yama rasa abunda zaiyi yana huci kamar zaki, juyawa yayi ya doka tsaki yabar dakin, kasa ya wuce zuwa dakinshi wuce ya zame kayan jikinshi ya shige bathroom, cold shiwer ya sakarma kanshi don hot temper dinshi yah au sosai, ya dade sosai saida yaji zuciyarshi ta lafa kafin ya fito anatse kugunshi daure da towel, closet dinshi ya shiga ya zaro kayan barci kafin ya shirya, gadon shi ya hau yayi rub da ciki, ya dauka kusan minti talatin ahaka hanakli ya soma jin yunwa don haka ya miqe ya zura bedroom slippers dinshi ya fuce daga dakin, fitowa yayi daga dakin cikin kamewa yawuce dining, nan ya tadda salima zaune da plate din indomie agabanta, kallonta yayi tana ganinshi itama tayi saurin miqewa tace ''ina wuni ya muhammad'' Ataqaice ya amsa ta ''lafiya'' kafin ya janyo kujera ya zauna, kallon wall clorck din dake gaban dining din yayi ganin kusan goma da rabi yasa yace ''why are you eating late'' Sunkuyar da kanta tayi tace ''dazun ne kaina ke ciwo saina kwanta'' Shuru ya danyi yana wani nazari kafin yace ''bring me coffee'' Da sauri ta miqe ta hado mashi coffee cikin coffee maker tana gamawa ta kawo mashi tace ''bismillah ya muhammd'' Karba yayi yace ''thanks'' Tana ganin haka ta dauke plate din indomie ta wuce kitchen dashi ta karasa tana gamawa ta fito hannunta rike da bottle water,''good night ya muhammad'' Dagowa yayi ya kalleta azafafe yac e''zo nan'' Anatse ta juyo gabanta na faduwa ta karaso wajen dining din tace ''gani'' Yana sipping coffee din ba tare da ya kalleta bay ace ''why where you talking to your elder sister harshly? Ita sa'arki ce?'' Shuru salima tayi hawaye na zubo mata ta kasa cewa komi saida yace ''clean those tears and answer me, ita sa'arki ce?'' ''ah ah'' salima ta fada ahankali tana goge hawayen ''who told you tayi abandoning dinku?you better get your head staright, you don't owe her explation saboda I recall na fada maku cewa saboda ita nasan ku, I don't have to repeat my self duk halin da kuka shiga ita kinsan wani hali ta shiga ne? kince kunsha wahala tayi abandoning dunku lokacin da kuke buqatarta right? Ita kinsan halin da ta shiga saboda ku day and night? kinsan abunda ta jefa kanta saboda ku?'' ya karashe a fadace yana kallonta har saida tadan furgita ''im sorry ya muhammd'' salima ta fada tana shesheka, ''bani zaki bama hakuri ba, you should be ashamed of your self for being selfish, and this should be the last time da zaki sake mata Magana babu respect understood'' Da sauri salima ta daga kai jiki na bari tace ''insha allah yaya'' ''go and sleep'' ya fada yana aje empty cup din, da sauri kuwa ta juya ta wuce sama. Tana tafiya shima ya miqe ya wuce dakinshi hankali kwance….
The next morning…. Sai wajen karfe biyar amra ta farfado, bakinta dauke da salati t miqe, duk jikinta ya gam tsami, saida ta zauna ta tuna da abunda ya faru, kamar a mafarki, mikewa tayi ta wuce bathroom tayi wanka ta dauo alwala, tana fitowa ta dora bayarta data zo da ita gida ta saka hija ta tada sallah tana idarwa tayi azkar, sai wajen karfe shida ta miqe ta koma kan gado ta kwanta, bacci ne ya dauketa sai wajen karfe tara ta tashi, tana tashi ta wuce bathroom ta wanko bakinta ta fito, gaban dresser ta tsaya tana karema kanta kallo, ta dan rame, duban kanta tayi dake buqatan gyara sosai don har tsinkewa ykeyi, nannadeshi tayi daga daurewar datayi da ribbom,ahankali ta tura annunta cikin gashi kafin ta fiddashi, hankalinta ne yadan tashi ganin gashi ya biyo hannunta,saurin annnade gashin tayi jin anyi knocking, salima ce ta shigo kanta a kasa tace ''good morning adda'' Da mamki amra ta jyo ta kalleta, murmushi tayi ta tako har inda salima take tace ''salima, good morning kin tashi lafiya'' yanda take Magana kamar itace kanwar salimar, ba tare da ta kalleta ba salima tace ''ammah tace ki sauko muyi breakfast'' tana kaiwa nan ta juya ta fuce daga dakin. Jikin amra ne yayi sanyi sosai, haka ta jawo veil din abayr tata ta maidashi kanta tayi rolling kafin ta sauko kasan, direct wajen dining ta nufa tana zuwa daidai hanyar gabamta ya soma faduwa, runtse idanu tayi ta karaso cikin dining din tace ''sallam alaikum'' gaba daya juyowa sukayi suka kallet hara mar dake zaune kafin ya hade rai wanda hakan akan idanunta yayi,saurin sunkuyar da kanta tayi ta karaso wajen dining din, ammah na ganinta tace ''zoki zauna nan kusa dani daughter'' Gaban wajen da ammah ke nuna mata ta karaso don dayan side din da mar ke zaune ne sai ya zamana sun sakashi a tsakiya, anatse amra ta zauna kanta kasa tace ''ina kwana ammah'' da sauri ammah tace ''lpy lau dota how was your night'' ''alhamdulillah amra ta amsa Murmushi ammah tayi ta kalli salima tace ''yan mata na a fara serving dinmu tunda kowa ya zauna'' Mikewa salima tayi ta fara serving sai alokacin amra ta lura da wanda kekusa da ita, daga chan gefe, ahanakli ta kalli aman tace ''ina kwana'' murmushi yayi mata yace ''lafiya kalua sister inlaw'' Da sauri salima t dago ta kalleshi ta galla mashi harara don duk a tunaninta yaa referring to her ne amatsayin yayar budurwarshi nan ko bata san shi ya fadi hakan ne saboda matsayin amra na matar amar, kallon gefen amar tayi daya hade rai yayi kamar ba a yi ruwanta a wajen ba, kanta a kasa tace ''ina kwana'' Banza yayi da ita kamar baisan dashi take ba wanda hakan akan idanun ammah, ''muhammd bakaji ana gaisheka bane?'' ammah ta fada Dan waigowa yayi ya mata wani irin mugun kallo ataqaice yace ''lafiya'' Kauda kai amma tayi ta basar, ba tare da tace komi ba.
Lantana ce ta karso dining din ta ajema ammah green juice dinta kafin ta koma kitchen. Anaste suka fara cin abunci har kowa ya gama amra dai kasa ci tayi sai juya cokali takeyi, ammah na ganin haka tace ''daughter ko kina buqatan wani abun ne?'' Saurin girgiza kai amra tayi tace ''ah ah wannan ma yayi'' Murmushi kawai ammah tayi ta cigaba da cin abuncinta, amar ne ya fara miqewa yace ''ammah zan fita'' ''ókay adawo lafiya'' ta bashi amsa yana fucewa aman ma ya wuce office,suna gamawa salima ta mike ta fara kwashewa, amra na ganin haka itama ta mike suka kai plates din kitchen atare, murmushi kawai ammah keyi tana kallonsu su biyu.