Auren katin kasa complete - Chapter 39
Auren katin kasa complete Chapter 39: Auren katin kasa complete Chapter 39. Karfe biyu aka kawo kayan da ammah tayima amra order na ready made, da kanta ta…
4,125 words
Karfe biyu aka kawo kayan da ammah tayima amra order na ready made, da kanta ta shiga dakin don kai mata, tana shiga dakin lokacin amra na toilet, saida ta jira har ta fito. Da sauri amra ta karaso inda ammah take zaune kanta kasa tace ''barka da rana ammah'' Murmushi ammah tayi tace ''thank you dear, ga kayanan kafin mu samu time mu shiga kasuwa,allah yasa suyi maki daidai,'' Kallon inda ammah ke nuna mata tayi kafin tace ''allah ya saka da alkairi ya kara budi'' ''ameen ya allah'' ammah ta fada tana kallonta kafin tce ''zoki zauna nan daughter muyi magana'' Anatse amra ta tako har inda ammah ke zaune dan nesa da ita bakin gadon ta zauna kanta a kasa, nunfasawa ammah tayi tace'' daughter fatan kinyi tunani akan abunda na fada maki,'' anaste amra tace ''eh'' Kallonta amma tayi kafin tadan nunfasa tace ''kafin naji daga bakinki ina son nayi wata mahimmiyar Magana dake saboda bana tauyema kowa hakki, muhammd ya fada min auren yarjejeniya da kukayi inda kika buqaci citizenship wato katin kasa ta karkashinsa don ki kawo qannenki kusa dake yanxu dai inason naji daga bakinki shin kinsan dalilin da yasa shi Muhammad ya aureki'' Shuru amra tayi don bata kwata kwata all this while tunani daya ke zuwan mata akan dalilin aurenta da yayi which is saboda jikinta ya aureta,batayi yunkurin tambayrshi ba ko jin ta bangarenshi dalilin aurenta da yayi, itadai tayi concluding saboda yana shaawar jikinta ne shiyasa ya aureta har ya kaita asibiti aka gwadata don ya tabbatar da bata da ciki don ya saketa, runtse idanunta tayi ta nunfasa tace ''ah ah ban sani ba'' Shuru ammah tayi don tayi tunanin hakan, saida ta danyi wani nazari kafin tace ''kinsan oligospermia?'' Ammah ta tambayeta tana kallonta, Dagowa amra tayi tadan aklleta kafin ta sauke kanta kasa tace ''eh na sani'' ''masha allah, Muhammad yana da oligospermia 3rd stage ya aureki ne saboda he has last chance of producing a child'' Dan nunfasawa ammah tayi muryanta na breaking ta cigaba,''wannan ne dalili da yasa ya aureki saboda daga wannan last chance din idan bai samu haihuwa ba bazai taba haihuwa ba'' Da sauri amra ta dago idanunta fal da hawaye, innalillahi ta wa inna ilaihi rajiun ta fara maimaitawa aranta, maganar ammah ce ta katseta ''wannan ne dalilin dayasa nace kafin naji daga bangaren inason muyi Magana, duk abunda kika yanke daughter shi za ayi, don anytime muhammd zai iya sakin ki indai kina so,idan kuma bakya ra ayin hakan, ni an tsaya mashi'' Anatse ammah ta share hawayen fuskanta daya zubo mata tace ''my dear babu macen da zata zauna da namijin da baya haihuwa shiyasa bazanyi forcing dinky akan ki zauna dashi ba, idan har bkyaso zai sakeki kinji ko?'' Kallonta amra tayi hawaye na zarya a fuskanta, tama kasa cewa komai, tausayin ammah y agama dabaibaiye ta sosai, idanunta sunyi jaa sosai wato all this while tayi mashin muguwar fassara, bait aba shaawar jikinta ba ko sau daya, hasalima ya aureta ne saboda that was his lat chance of haihuwa, hawaye ne ya soma yi mata zarya a fuska, sai yanxu take regretting magan ganun data dunga fadamashi, da yanda take cewa ta gode ma allah daya bata dauki cikinshi ba, yanda take jinshi aranta yanxu ya wuce musali, ya samu wani babban gurbi a zuciyarta, dashi da mahaifiyars. Ammah na ganin haka ta miqe tace ''daughter zan barki kiyi shawara kinji ko'' Tana kaiwa nan ta fuce tana goge hawayen da take boye, salima dake labe bakin kofar su tayi saurin komawa da baya ta boye gefen flower vase, tana ganin ammah ta wuce daki ta fito, idanunta itama ya cika da hawaye she cant believe abunda kunnuwanta suka juyo mata, adda matar ya muhammd ce? Auren yarjejeniya sukayi saboda ta samu katin kasa ta kawosu kusa da ita? Sulale wa tayi anan wajen ta fara hawaye, daman ya Muhammad yace she will regret it idan taji abunda ta jefa kanta a ciki saboda su, kamar wadda aka tsugula ta miqe ta wuce cikin dakin amra, amra dake kukan zuci dana fili bataji kararbude kofar da salima tayi ba sai ganinta da tayi akanta, kura mata idanu amra tayi don tadan tsorata da ganinta tana hawaye, ''adda what did I just hear? Auren yarjejeniya kikayi saboda mu?'' Salima ta fada tana kallonta, kauda kai amra tayi tace ''ian kikaji wannan'' Zama salima tayi gefenta kanta akasa don wani irin nauyin amra ta fara ji tace ''adda im so sorry im sorry for blaming you'' Kuka ne ya kufce mata ta cigaba ''wallahi adda ban taba tunani kema kin shiga wani hali ba saboda mu, im so srry addaa'' Janyota amra tayi a jikinta tana hawaye tace ''salima ya za ayi na manta daku, daku nake kwana daku nake tshi, na shiga babban tashin hankali lokacin da kika kirani, don har lokacin nayi niyar dawowa saidai nayi laakari da idan na dawo komai zai iya wargajewa don daddy yace karna sake na dawo ba tare da na biyashi kudinshi ba bayan wannan ma banida wani option daya wuce na san aynda zanyi na kawo ku kusa dani har allah ya hada ni da ya muhammad'' It was an emotional moment for amra and salima a wannan lokacin, kuka dai har suka gaji babu wanda ya iya hana dan uwanshi suna rungume da juna, saida suka gaji dan kansu suka rarrashi kansu kafin salima tace ''adda, ina neman wata alfarma a wajenki, bansan irin zaman da kukayi da ya Muhammad ba but bana jin akwai abunda shida ammah zasu nema a wajen mu muqiyi masu, adda mutanen nan basu san ba sun karbe mu hannubibiyu, ya muhammd yayi mana abunda iyayenmu ne kadai zasu iya yi mana don yayi mana gatan da waenda ya kamat suyi mana basuyi mana ba,shi ya biya mana kudin aikin da akayi mana lokacin da muka kusa mutuwa shine yayi protecting dinmu lokacin da aka watsar damu akan titi, shine wanda dora mu kan ilimin da aka hanamu yi aka tauye mana, shi ya samu a school nida salim ba tareda yasan asalin mu ta sanadiyarki, ke karan kanki bakisan yayi hakan ba,adda babu abunda zasu nema a wajen mu da zamu gagara yi masu shi har karshe nunfashin mu don komai zamuyi masu bazamu taba biyansu da abunda sukayi mana ba'' hannunta salima ta rike looking very very serious tace ''adda rokeki da allah, karki rabu da muhammd don lalurar shi, yau ko bashi da kafa nasan zaki zauna dashi adda, idan har kinason haihuwar ma ni idan nayi aure zan baki duka yayana kyauta, kimin alqawarin bazaki taba barinshi ba adda promise me'' Amra na hawaye take bin salima da idanu, shes so speechless, wannan yanxu kanwarta ce, salima tayi hankalin da ayau ko bta raye zata kula da kanta da kaninta sannan tasan me ake nufi da halacci, Murmushi amra tayi danyi tare da yar dariya ta kalleta ''basai kin roke ni ba salima, yau koda ace baya iya amfani da jikinshi zan zauna dashi, har abada bazan taba complain ba'' Saurin rungumeta salima tayi tace ''tahnk you adda na, ni zan baki duka yaya na idan nayi aure'' Kallonta amra tayi tace ''soyayya kikeyi ko? Har kinsan wani idan aure zaki bani yaya'' Dariya salima tayi tace ''kaii add aim 19 years fa yanxu'' Bugu amra takai mata tace ''karya kike youre 18 ay a lissafe yake akaina, next month'' Dariya itama salima tayi tace ''wow ni harna manta fah, kuma next month ma graduation dina''
Hira suka sha sosai ta kewar juna har suka shagala, kiran sallar magrib ne yasa salima fucewa ta barta a daki, murmushi amra tayu sai taji 50% din damuwarta ta raguwa, nauyin da zuciyarta keyi ma duk ya ragu.
Bayan sallar ishai salima tazo ta kirata don suci dinner, tare suka sauko gwanin ban shaawa, anra sanye take da doguwar rigar material da amma tasa akayi mata na bubu, suna karasowa suka tadda ammah da salim akan dining, da murmushi ta tarbesu ganin yanda suka rike hannu suka karso, har kasa amra ta tsugunna tagaishe da amma kafin ta samu waje ta zauna, su hudu kawai sukayi dinner don amar da aman basu dawo ba.
Karfe tara daidai amra ta fito daga dakinta sanye da hijab, cikin natsuwa ta tako zuwa part din da take tunanin na ammah ne don yafita daban a saman, da sallama ta shiga part din, babu kowa a sitting room don haka ta kara kwada sallama, daga ciki ammah tace ''bislillah'' anatse amra ta tako har cikin dakin bakinta dauke da sallama, kanta a kasa ta shigo amma na ganinta tace ''daughter shugo mana ya kika tsaya kamar bakuwa daga kofa'' Anaste amra ta karaso ta tsugunna har kasa ta gaishet kafin ta samu waje ta zauna tsakiyan carpet, ammah na ganin haka tace ''haba daughter ki zauna kan gado mana'' Kai akasa amra tace ''nan ma yayi ammah'' Murmushi amma tayi ta kalleta, kai akasa amra ta soma Magana cikin kunya ''uhm daman….'' Murmushi ammah tayi tace ''kinason ki fada min shawarar da kika yanke ne'' Kai a kasa amra ta girgiza mata kai tace ''ehhh'' ''okay inajinki daughter, duk abunda kika yanke haka za ayi'' Dan nunfasawa amra tayi tace ''ammah bana son ya sake ni'' Runtse idanu ammah tayi cikin farin ciki da jin dadi tace ''are you sure daughter, karkiyi deciding kodan abunda yayi maku keda kannenki, inason kibi abunda zuciyarki ta raya maki kinji'' Girgiza kai amra tayi tace ''badan haka bane, babu abunda zan iyayi da zan saka mashi da wannan saidai na roki allah ya biyaku da aljanna, kune gatanmu, duk duniya babu abunda zai chanza wannan'' ta karashe tana hawaye, kanta ammah ta shafa tace ''thank you so much daughter, allah ya maki albarka, allah ya baku zuriyya dayyaba, inda rai akwai rabo, allah mai jin qan bayinshi ne, insha allah zaku dawwama cikin farin ciki har abada'' Wani irin dadi ne ya ziyarci amra jin kalamin da ammah tayi da adduó ta. Bata dade ba tayi ma ammah saida safe ta wuce dakin su salima, a zaune ta tadda salima tana zane while salim nab arci, karasowa amra tayi fuskanta dauke da murmushi tace ''har yanxu kina zanen'' Juyowa salima tayi cikin murnar ganinta tace ''addaaaaa naa, yau tare zamu kwana ko'' Kallon book din hannunta amra tayi ta ga zanen nata, kafin tace ''kin tuna min da abba, allah ya jikanshi da rahama da mami'' Hira suka sha sosai kafin su kwanta tare…… [7/11, 11:17 PM] +218 92-2035171: Update Unedited page Karfe shida saidai salima ta shugo dakin, sanye take da kayan islamiyya, kallonta amra tayi tace ''har kun dawo'' karasowa salima tayi fuskanta dauke da murmushi tana kallon amra tace ''waiii adda yanaga sai kyalli kike yi'' Murmushi karfin hali amra tayi mata tare da matsa mata gefen gadon donta zauna ''babu wani kyalli, kedai akwai zuzuta abu'' Zama salima tayi agefenta tare da janyo hannunta tace ''wallahil azeem kyalli kikeyi adda, kinji fatar hannunki kuwa kamar auduga'' Dariya amra tayi ta dan harareta ''kedai da zuzuta abu wallahi, kije ki sauya kaya saimu sauka kasa tare'' Cikin zumudi salima ta miqe ta fuce daga dakin nasu, tana fita amra ta sauke ajiyar zuciya don har lokacin tana fargabar haduwa dashi, da kyar ta samu ta danne abunda ke ranta ta miqe tsaye, gaban dresser ta tako ta tsaya tana karema kanta kallo cikin mirror, tundaga kanta zuwa shafaffen cikinta dake cikin doguwar rigar data sauya take kallo, ita kanta tasan kyan datayi yau naturally na dabanne don ya fito sosai, sauke ajiyar zuciya tayi kafin ta juya ta nufi hanyar kofa, tana fitowa salima na fitowa itama, atare suka sauko kasan suna hira kasa kasa, tunda suka shiga kitchen suka fara preparing dinner salima ta lura da yanda jikin amra yayi sanyi, bata kawo komai aranta ba don haka ta dunga janta da hira har suka gama abunci suka jera a dining table, sama amra ta wuce don ana gab da kiran sallar magrib, salima kuma kitchen ta koma don ta karasa kwaso plates da za ayi amfani dashi. Shogowa kitchen din aman yayi ya kafa ma bayanta idanu, yanda take goge plates da rag anatse, murmushi yayi ya tako har cikin kitchen din, bataji motsin shugowarshi ba saida yadan rankwafo daidai kunnenta yayi mata whispering wasu words daya sata dan razana har plate din hannunta na neman faduwa, saurin juyowa tayi ta kura mashi idanu fuskanta dauke da murmushi ''yaa aman, ka bani tsoro'' ta karashe a shagwabe, dariya yadanyi yace ''I missed you baby, yau gaba daya da tunaninki na wuni ah office'' Dan harara tayi mashi kafin ta gifta ta gefenshi ''babu wani nan,'' saurin riko hannunta yayi don tana gab da wuce shi, shima cikin shagwaba yace ''baby sal, dan allah ki karbi soyayya na, ni wallahi kina wahalar dani sosai,zan hadaki da ammah ko sister inlaw wallahi'' Kallonshi tayi da yanda yake shagwaba kafin ta kyalkyace da dariya ''yanxu shagwaba ka koyo kuma?'' Dariya shima yayi ya kara shagwabe fuska yace ''wallahi da gaske nake sonki zai kasheni baby sal'' Banza tayi dashi tana murmushi ta wuce dining, haka ya dunga binta daga dining zuwa kitchen, karshe dai guduwa sama tayi ganin yana neman shagaltata da shagwabarshi, wani irin son shi da kaunarshi take ji a jininta, hes so good with words, duk sanda ya fara mata Magana tsintar kanta take da blushing kamar wata zautacciya.
Amra na shiga daki ta wuce bathroom ta dauro alwala, tana fitowa ta zura hijab, ta tada sallah, tana idarwa ta zauna saida aka kira sallan isha'I, tana nan zaune salima ta shugo dakin da sallama kafin ta kalli inda amra ke zaune kan sallaya, ''adda mu sauka kasa, naga ammah ta sauka already'' Juyowa amra tayi ta kalleta ''bana jin yunwa, kije kawai sai zuwa anjima zanci'' ''okay,'' salima ta fada tana bude kofar futa daga dakin. Tana fita amra ta mike tsaye ta cire hijab din,baking ado ta zauna gabanta na faduwa sosai, wayarta ta janyo tama rasa abunda zatayi da wayar,sai a yanxu take missing din haifa sosai, aje wayar tayi a gefe ta kwanta tana tunani, gabanta na faduwa sosai.
Bayan fitar salima kasa ta sauko direct zuwa dining, ammah ce kawai a zaune sai salim a gefenta don harsun fara cin abunci, basu hangota daga cikin dining dinba don haka ta sulale ta juya zuwa dakin aman, anatse tayi knocking, jin shuru yasa ta bude kofar ta shige, babu kowa a sitting room dinshi don haka ta wuce gaban bedroom din tayi knocking, shuru har kusan minti biyu, wani knocking din ta sake jin shuru yasa ta bude kofar tadan sako kanta, kafin ta shige ciki gaba daya, bin dakin nashi tayi da kallo, ko'ina very neat babu datti, ahanakli idanunta ya sauka kan kwalabe dake gefen bed dinshi kusan guda biyar, idanu ta zaro sosai jikinta na bari ta karaso gaban kwalbar, anatse ta tako ta dauka guda daya ta fara karantawa, koba a fada mat aba tasan kwalaban giya ne don haka taji wani abu ya daki ranta, fuskanta ya soma jaa kamar zatayi kuka. Bude kofar toilet aman yayi daure da towel a kugunshi ya fito daga bathroom din, saida ya karaso dakin ya lura da ita a tsaye rike da kwalbar giya, gabanshi ne yadan fadi cikin hanzari ya karaso kusa da ita, dan dagowa tayi ta kura mashi idanu kafin ta maida idanunta kan bottle din ta aje shi a kasa inda ta dauko shi, ba tare da tace mashi komai ba ta juya zata bar dakin, da sauri ya kamo hannunta ya damek yace ''babeee wait'' Azafafe ta juyo ranta a bace ''let go of my hand''..hankali atashe aman ya rike hannun nata gam ''babe please listen to me, karkiyi saurin yanke min hukunci please'' Fusge hannunta tayi ya sake riko hannun nata, tana ganin haka tace ''ka sake min hannu na, I hate you, daman baka daina shan giya ba? Alkawarin dakayi min Kenan,'' Hankali atashe aman ya rungumota ta baya gaba daya ya susuce ''babe dan allah ki saurare ni, wallahil azeem na daina, don't hate me please ki saurare ni'' Saurin runtse idanunta tayi jinshi a bayanta da yanda ya kankameta, hawaye ne ya soma sulalo wa afuskanta, ''I said let go of me, ka daina taba min jikina kai ba muharramina ba, anyways daman ay kai baka san da hakan ba tunda ko wani jack and jill tabawa kake yi'' tana kaiwa nan ta fusge jikinta ta fuce daga dakin tana hawaye, saida ta tsaya a sitting room dinshi ta goge hawayen dake fuskanta kafin ta fuce kanta a kasa, bata tsaya wucewa dining ba ta nufi hanyar sama.
Ammah da salim ne kawai sukayi dinner, ammah dai mamakin rashin saukowan su tayi daga salima har amra don haka tana gamawa ta wuce sama, dakin amra ta fara shiga ganinta kwance tana barci yasa ta fito ta barta, dakin su salima ta wuce, anatse ammah ta shiga bakinta dauke da sallama, da sauri salima ta goge hawayen da takeyi kanta akasa, ammah na ganin haka ta karso gefen gadon su da take zaune tace ''my dear kukan menene wannan?'' ammah ta fada tana kallonta ''are you okay?, baki da lafiya ne'' Dan dagowa salima tayi tana kokarin danne hawayen dake shirin zubo mata tace ''barka da dare ammah na, kaina ne ke ciwo'' ''shine kike kuka? Kodai an maki wani abun ne?'' ammah ta shefeta da tambayar tana kallonta don gano abunda ke damunta, kauda kai salima tayi tace ''babu komi wallahi, ciwon kai ne ammah'' Murmushi ammah tayi ta kalleta ''kodai kunyi fada ne keda mutumin naki'' ammah ta fada tana kallonta tana murmushi, da sauri salima ta kalli ammah don tayi mamaakin jin abunda ta fada, saurin sunkuyar dakanta tayi kasa, ba tare da ta amsa tambayar da ammah tayi ba, mikewa ammah tayi kafin tace ''zaku shirya ne ma,'' ''kinsha magani?'' ammah Ta sake tambayarta Girgiza kai salima tayi tace ''ah ah, amma zan sha yanxu, inada panadol'' ''okay, ki fara cin abunci kafin kisha maganin, allah ya sawaqe'' ammah ta fada tana futa daga dakin zuwa dakin ta.
Karfe tara da rabi daidai ya shigo gidan,babu kowa a sitting room, sai karar tv dake aiki, direct ya wuce bedroom dinshi kai tsaye, kayan jikinshi ya fara ragewa kafin ya wuce bathroom, anatse yayi wanka ya fito daure da towel cikin kamewa, yan sahfe shafen shi yayi, kafin ya wuce cikin closet dinshi, short ya zaro da jellabiya, agaggauce ya shirya ya janyo wayarshi daketa faman ringing babu kakkautawa ya fuce daga cikin bedroom din, hanyar stairs ya bi ya fara takawa cikin kasaita, har ya hauro saman, ya wuce dakin ammah,da sallama ya shuga bedroom din ammah, a tsaye ya taddata gefen wardrobe tana shirya kayan wanki da aka kawo daga laudry, juyowa tayi ta kalleshi fuskanta dauke da murmushi ''har an dawo babana,'' Kallonta yayi cikin so da kaunarta ya karaso dakin ya zauna bakin gadonta ''barka da dare ammah,'' ''barka son, ya aiki? You look stressed kardai ka wahalar da kanka fa'' Ammah ta fada cikin kulawa tana karasowa inda yake zaune, kallonta yayi yana tausayinta sosai yace ''ammah bakice komai game da daddy ba'' Fuskanta ne yadan chanza tayi shuru, saida ta dauka yan seconds kafin ta soma Magana cikin natsuwa''toh me zance son?, duk abunda ya faru shiya jefa kasha a ciki, ni na dade da zargin yana miyagun ayyuka,'' Murmushi amar yayi ya riko hannunta ganin tana neman shiga damuwa yace ''please ammah karki sama kanki damuwa, daman na tambaya ne don naga baki ce komai ba akan zancen sa'' Riko hannunshi tayi cikin nasa itama tace ''bazan saka damuwa araina ba akan mutumin da bai san damuwar kowa ba saita kanshi, ni yanxu kaine damuwa ta son'' Yasan inda ta dosa don haka yayi saurin kauda zancen ta hanyar cewa ''inajin yunwa'' da ammaki ammah tace ''yau da kanka kake neman abunci?''….dariya ya danyi yana mahaifiyar tashi cikin kulawa yace ''im craving special coffee dinky ammah na '' ''oh kaida dada bansan waye yafi wani son coffee ba, allah ya jikanshi da rahama'' ammah ta fada still fuskanta dauke da murmushi, jikinsa ne yayi sanyi sosai, tunawa da wani abu, anatse ya miqe yace ''ammah kisa yarinyar nan ta kawo min bedroom,I will be so busy this night, zanyi rounding up duka investigation dina nan, I have to report back to office soon'' Murmushi kawai ammah tayi tana wani tunani kafin tace ''bari za a kawo maka yanxu'' Yana fucewa yaci karo da salima da plate din abunci a hannunta tana shirin shiga bedroom dinsu, kallonta yayi suna hada idanu ta sauke nata don ta tuna lokacin da yayi mata Magana akan cin abunci late, ''babu gaisuwa'' ta tsinkayo muryashi don yana gab da sauka kasa, anatse tace ''sorry ya muhammd, ina wuni ya officee'' ''lafiya'' ya bata amsa ataqaice kafin ya sauka kasan zuwa bedroom dinshi, yana wucewa salima ta sauke ajiyar zuciya tana hamdala, kafin ta shige daki.
Karfe goma daidai amra ta bude idanunta kamar wadda aka tsungula, mamakin yanda akayi tayi barci a wannan lokacin tayi, tarr ta bude idanunta ta fara bin da kallo kafin ta miqe zaune bakinta dauke da salati, mikewa tayi ta wuce bathroom jin jikinta yayi weak sosai, wanka ta fara yi ta wanke bakinta kafin ta fito anatse, wani irin yunwa ne ya nuqurqusota, aggauce ta bude wardrop ta janyo doguwar riga mara nauyi ta barci ta saka, rigar takai mata har kasa tana da hula a baya, bata tsaya komai ba ta futo daga bedroom dinta ta sauka kasa don neman abunda zata sakama cikinta, hanyar dining tabi ta karasa, ganin an kwashe warmers dake kan dining din yasa ta wuce cikin kitchen anatse, bin ko'ina ta farayi da kallo neat, tunanin abunda zata sama cikinta ta farayi, kafin ta yi deciding, bread dake ajiye a gefe rak ta jawo ta saka cikin toaster, cikin yan mintuna kalilan ta fidda toasted bread din ta bude fridge ta janyo avocado tayi mashing, tana gamawa ta hada da toasted bread din ta fito dining, zama tayi ta fara ci anatse, nan kasan shuru babu sound din komai. Tana nan zaune tana tura toast a bakinta tana tunani harta cinye kusan slize biyar, saida tajita dam kafin ta mike ta maida plate din kitchen ta dauraye kafin ta wuce sama. Bata dade da shiga daki ba saiga ammah, da sallama ta shugo cikin dakin sanye da hijab har kasa fuskanta dauke da fara'a ''daughter harkin tashi? Na shigo ay naga kinata barci'' Murmushi amra tayi kanta a kasa tace ''barka da dare aammah, daxun ne kaina ya dan soma ciwo shine na kwanta banma san lokacin da barci ya kwashe ni ba'' Murmushi itama ammah tayi mata ganin ta fara sakin jiki da ita ta karso cikin bedroom din, ''zauna daughter'' Zama amra tayi gefen gadon itama ammah ta zauna gefenta ''baki manta da abunda na fada maki ba daxu ko?'' Dan sunkuyar dakai amra tayi tace ''eh ban manta ba'' ''yauwa, ungu wannan'' ammah ta fada tana miqa mata wata kwalbar turare mai shegen kyau ''ki shafa kafin ki tafi, yana da kyau mace ta kasance tana kamshi koda yaushe,'' Sunkuyar dakai amra tayi ta karba hannu bibiyu tana jin kunya sosai, ammah na ganin haka tace ''daughter ki daina jin kunya ta, karki daukeni a matsayin sirika, ni uwa ce agareki, kuma zanyi kokarin ganin kin samu matsayi mai girma a wajen mijinki kinji,'' ''in sha allah, allah ya saka da alkairi'' amra ta fada ''baki daukeni uwa ba Kenan tunda kika godemin'' saurin dagowa amra tayi kafin ta sauke kanta kasa tace ''ba haka bane ammah'' ''karki godemin daga yanxu, duk abunda uwa zatayi ma diya shi zanyi maki'' murmushi amra tayi mata tana jin kaunar ammah sosai aranta, wannan itace uwa ta gari, mai jan kowa a jiki, ita kowa nata ne, bata kallon amra kwata kwata a matsayin suruka sai ya, shiyasa wayewa take da dadi.
''yanxu kije kiyi wanka ki shirya saiki tafi ko, akwai coffee daya buqata yana kan dining ki kai mashi, karkiji tsoron komai, ki cire tsoronshi a ranki'' ammah ta fada tana shirin miqewa, ''tohm'' amra ta fada ahankali ''saida safe'' amra ta fada ahankali kamar wadda aka zarema laka, ''Allah ya tashe mu lafiya daughter'' ammah ta fada tana fucewa daga bedroom din fuskanta dauke da murmushin jin dadi.
Tana fita amra ta sauke wani nauyayyan ijiyar zuciya, gabanta na faduwa tama rasa me zatayi, wani irin tsoro ne ya durar mata, kwata kwata shes not ready to face him saidai bazatayi jayyaya da maganra ammah ba, tasan cewa ammah tayi hakan ne saboda ta daidaita.