Auren katin kasa complete - Chapter 40
Auren katin kasa complete Chapter 40: Auren katin kasa complete Chapter 40. Kamar wata munafuka haka ta aje turaren kan dresser ta janyo zumbulelen hijab…
3,616 words
Kamar wata munafuka haka ta aje turaren kan dresser ta janyo zumbulelen hijab dinta akan rigar ta nufi hanyar futa, dan tsayawa tayi jimm ta juyo ta koma gaban dresser din, bude cover turaren tayi ta dan shaka a hancinta, turaren yana da wani irin karfi sosai at the same time yana da dadi sosai,beneath her breath tace ''uhm akwai kamshi'' tunani ta soma yi ko me yasa ammah tace ta saka kafun ta tafi part din, bata kawo komai aranta ba don haka ta dan zuba a tafin hannunta daya dan jan lalle a yatsun, tana zuba turaren taga its oily don haka tayi saurin murzawa a hannunta ta dake hijab din ta goga a jikinta, tana gamawa ta aje kwalban ta fuce daga bedroom din. Kasan ta sauko ta wuce kan dining, nan taga flask din coffee dinshi akan tray da mug agefe sai zuma, daukan tray din tayi anatse ta wuce hanyar part dinshi gabanta na faduwa, knockin ta fara yi, jin shuru yasa ta bude kofar ta tsaya bakin kofar, sanyin ac ne ya daketa, da sauri ta fara bin parlorn da kallo,wayanshi ne kawai da laptop a kan couch sai wani dan décor blanket a gefe da alamun bai dade da barin wajen ba, ta dade a tsaye ta kasa yin komai sai sake sake take aranta tana tunani, tana nan tsaye sai gashi ya futo kai tsaye sanye yake da classy pjs dinshi riga da wando nabarci, farare tass, baima lura da ita ba daya futo don kanshi a kasa yake yana kokari buttoning rigarshi, saida ya dago idanunshi ya sarqe cikin nata, mamakin ganinta ya soma yi don ba ita ya buqaci ta kawo mashi coffee din ba, jiki na bari amra ta kauda idanunta daga nashi ganin irin kallon da yake mata,kauda idanunshi yayi daga kanta ya karasa inda ya tashi daga kan couch din' Yana zama ya dora kafanshi dake dauke da black sock kan daya ya janyo laptop dinshi ya daura kan cinyashi, ta gefen idanu take kallonshi, saida ta tsaida natsuwarta waje daya jiki a mace ta karaso har inda yake zaune ta aje tray din akan center table, tana ajewa ta danyi baya gefe tace ''barka da dawowa, ina wuni ya aiki?'' Da mamaki ya dago ya kalleta, he's so surprise, shi mamakin ta ma yake ji, lokaci guda ta chanza from that stubborn girl to soft girl, murmushi ya danyi ta gefen baki tunawa da dalilin chnzawan nata, ''mata are fake'' ya fada a zuciyarshi Wani irin banzan kallo ya mata yace ''meya kawo ki dakina?'' Ya fada babu wasa a fuskanshi, sauke kanta kasa tayi murya chan kasa tace ''ammah tace na kawo maka coffee'' Bai ce mata komai ba ya maida hankalinshi kan aikinsa, ya dauka kusan minti talatin yana aiki, tana tsaye a gefenshi ta kasa motsawa, kamar daga sama ya tsinkayo melodious muryanta ''na saka maka coffee din'' Cire idanunshi yayi kan laptop din ya maida kanta yana kureta da idanu, tana ganin haka ta sauke nata kasa ''wowww,… ashe kema baki da banbanci da sauran mata, youre so fake, why are you acting up?na buqaci abu daga wajenki ne?'' Kasa dago kanta tayi tana sauraron abunda yake fada, idanunta yayi jaa sosai hawaye na shirin zubo mata daman tasan haka zata kasance, shiyasa kwata kwata bata shirya ma fuskantanshi ba, saidai babu yanda zata iya daman tasan zai fadi hakan. Shiko mamakin ta y agama cikashi don yasan duk wannan sauyin nata saboda ta gane shine ya taimaki yan uwanta, aduniya babu abunda ya tsana kamar mutun mai faking abu, ba haka ya santa ba, saidai yanda ta sauya lokaci guda abun na bashi mamki. ''what are you still waiting for?,'' ya kafeta da idanunshi dake tayar mata da hankali, kasa cewa komai tayi sai hawaye, yana ganin haka yace ''youre dismiss, zaki iya fita'' Ararrabe ta soma Magana '' anan zan kwa…'' Kasa tsayawa ya ji me zatace yayi ya zabga mata wani kallo daya sa zancen nata ya maqale, ''are you deaf?, you knw how I hate repeating my self right?'' Da sauri ta juya ta bude kofar parlorn nashi ta fuce tana hawaye, samun kanta tayi da zama a sitting room din kasa tasha kukanta harta gode ma, zuciyarta ta karaya sosai da alamarinshi, saidai ko sau daya bata kawo cewa zatayi giving up ba, ko me zaiyi mata da duk maganganun da zai gaya mata haka zata zauna dashi, wannan alkawari ne ta dauka ma kanta, da dade sosai a zaune tana saka wa tana warware har barci ya kwashe ta anan sitting room. Shiko goga tana futa ya tabe baki ya cigaba da aikinshi, coffee dinma baisha ba saida yaji barci na neman dibanshi ya fara sha don hana barcin, sai wajen karfe biyu da rabi ya samu ya wuce bedroom dinshi ya kwanta. Da asuba ammah ta futo ta wuce bedroom dinta, don hankalinta bai kwan taba data turata part dinshi, don definitely zai iya korota, saboda tasan halinshi, ganin bata dakin yasa ammah yin hamdala, ta wuce dakin su salima ta tashesu kafin ta fito, tana fitowata nufi hanyar bedroom dinta, bata kaiga karasawa ba ta juya zuwa stairs ta sauka anatse har zuwa kitchen, ganin koi a a kashe ya tabbatar mata da lantana bata tashi ba, bottle water ta deba guda biyu kafin ta fito daga kitchen din, kamar ance ta dago kuwa ta hango amra na yi miqa tana salati, baki abude ammah take kallonta don ita batabhango taba, ammah na ganin haka ta wuce sama ba tare da ta bari ta ganta ba, tana shiga bedroom kuwa ta zauna gefen gado tana mamakin ganin amra a kwance a sitting room din kasa, daman tasan za ayi hakan indai muhammd ne kafiya tayi mashi yawa sosai, girgiza kai kawia ammah tayi ''zanyi maganinka kuwa, indai korar yarinyar nan kayi'' Ammah ta fada tana janyo ledar magungunan ta ta bude tasha na safe don daman dalilin saukanta kasa Kenan don ta dauka ruwan da zata sha magani, yawanci lantana ke kawo mata da asuba, saigashi saukanta yanxu da tayi yayi amfani don ba lallai ta gane cewa ya kori amran ba haka zalika tasan amra bazata fada mataba.
Karfe goma kowa ya fito breakfast, jiki a mace amra ta sauko salima na gefenta suka karaso har dining suka gaida ammah, kafin kowa ya zauna, gaba dayansu daga salima har amra dukkansu jiki a mace kowa da abunda ke damunshi, ammah duk ta lura dasu don haka ya kauda kanta gefe batace komai ba don duk tasan damuwar su. Aman ne ya fara karasowa dining din shima jikinsa yayi laasar saboda baya samun barci kwata kwata, damuwar salima tayi mashi yawa don ta daina kula shi kwata kwata, bata ma saukowa kasan don shi baya hawa sama saidai idan zaije ya gaida ammah, kiri kiri take avoiding dinshi taki bashi chance din fada mata side of his story. Dagowa salima tayi idanunta ya sauka akan nashi,kauda kanta gefe tayi rai abace, shiko haka ya karaso kamar wani mara lafiya ya zauna agefe. Duk ammah na lura dasu su duka, don taga yanda suka kalli juna kafin su kauda kai. Anatse salima ta mike tayi serving din ammah kafin ta zuba ma amra da salim, tana gamawa ta nema wajen zama, dan dagowa yayi ya kalleta itama ta kalleshi tare da galla mashi harara, fuskan tausayi yayi yana dan daga hannunshi alamun bada hakuri, ammah na ganin haka tace ''dear yau baza a zubama yayan bane?'' Dan dagowa salima tayi ta kalli ammah tace ''shi yace karna zuba mashi''… da mamaki ya dago ya kalleta jin irin karyar da tayi, ammah najin haka ta dan murmusa ta maida hankali wajen cin abuncin ta, Akarshe dai aman da kanshi ya zuba ma kanshi abunci, amra dai hankalinta baya kansu kwata kwata, sai juya cokali take a abunci ta kasa ci tana tausayin kanta. Kamshinsa ne ya maidota daga tunanin data shiga,nan take hancinta ya shaida mata yana tafe don tundaga nesa ta jiyo kamshin, qin dago kanta tayi ta kalleshi har ya karaso ya jaa kujera ya zauna ya gaisheda ammah, su salima ma gaishesa sukayi ya amsa. Kallon ta ammah tayi ganin yanda ta sauke kanta kasa ''daughter bismillah'' Ammah ta fada tana kallonta, sanin abunda hakan ke nufi yasa ta mike ta jawo plate mai kyau ta zuba mashi, saida ta gama atsanake ta tura abuncin gabanshi, muryanta chan kasa kamar mai jin barci tace ''ina kwana, bismillah'' Bai amsa ta ba haka zalika hart aje abuncin bai kalli wajenba, jiki a mace ta juya ta zuana a mazauninta. Gaba daya breakfast din was awkward, don kowa yayi jugum sai karar spoon ne ke tashi, amar ne ya fara miqewa ya wuce bedroom dinshi follow by ammah, ammah na wucewa amra ta sauke ajiyar zuciya ta ture abuncin don tunda ta saka abuncin agaba tayi loma daya taji ya fita akanta, mikewa itama tayi ta wuce abunta, salim ma bai wani dade bay a mike, ya rage daga salima sai aman, itama bata san kowa ya watse ba don ta lula tunani, aman na samun chanze dinnan kuwa ya mike ya zagayo inda take zaune ya zauna, bata ji sanda ya zagayo ba saijin muryanshi tayi a gefenta ''baby sal dan allah ki saurare ni, wallahi zuciyata zata buga, I cant take this silent treatment da kike bani,youre ingnoring me I cant take it please my loveee'''ya karsehe fada cikin sanyin murya, samun kanta tayi da waigowa ta kalleshi tace ''hmey zakayi explain bayan na kama ka red handed?, me zaka cemin yanxu? Haba niba karamar yarinya bace ba da zaka kawo wa wani excuse daban bayan abunda na gani da idanu na'' Anaste ya kama hannunta bata hanashi bay a soma Magana ''babe a cikin daki kika gani ko? Shin a hannuna kika gani inasha? Shin ki shigo taddani ina maye ne?'' girgiza mashi kai tayi tana sauraronshi idsnunt sunyi jaa don bata jin akwai explanation din da zaiyi mata ta yarda, katse mata tunanin yayi ''love, wallahil azeem ba abunda kike tunani bane hasalima a cikin closet dina na tsinto su, shine na fidda su zan zubar, tunda na rantse maki kan cewa na daina wallahi na daina for the sake of all, believe me'' yanda yake mata Magana cikin sanyi saiya bata tausayi sosai, wani iri taji aranta, saidai shes finding it hard to believe him saida taji ya rantse tukunna ta yarda saidai bata nuna mashi ta yard aba saboda tana son ta tabbatar da gaske yake, kwace hannayenta tayi ta miqe ba tare da tace mashi komai ba ta wuce sama, yana ganin haka ya dafe kanshi ya furta''ya allah ka akwo mun sauqi'' kafin ya mike jiki a mace ya wuce dakinsa ranshi adagule. Amar kuwa yana shiga daki ya shirya agurguje ya fuce daga gidan baima tsaya yima ammah sallama ba saboda kiran gaggawa da asad yayi mashi.
Akwance take idanunta akan ceiling tana tunanin abubuwa da dama, knocking akayi a bakin kofa dayasa ta maida hankalinta ga wanda ke shirin shugowa, salima ce fuskanta gwanin ban tausayi kana ganinta kaga wadda take cikin damuwa, kallonta amra tayi harta karaso bakin gadon ta zauna ''salima are you okay? Naganki yau kwata kwata babu walwala'' amra ta tambaya tana gyara zama akan gadon, kallonta salima tayi tana kokarin danne abunda ke zuciyanta don tabbas tana buqatar abokin shawara saidai bazata taba iya fada ma amra cewa aman na shaye shaye ba don hakan kamar zata zubar mashi da kima ne a wajen yayarta, ta gwammace karta san da hakan kwata kwata, sauke ijiyar zuciya salima tayi ta kalleta ''babu komi adda kawaii m not in d mood ne'' Hannunta amra ta rike tace ''kodai period ne, nasan haka mood dinky ke chanzawa idan zakiyi'' Girgiza mata kai salima tayi tace ''nop bashi bane, munyi fada ne da ya aman'' Gyara zama amra tayi ta fuskance don jin abunda ya hadasu ''meya hadaku?'' amra ta tambaya tana kurama salima idanu ''I just feel like yamin karya ne akan abu'' ''kinyi confronting dinshi'' ama ta tambay aba tare da taji karyar da yayi matan ba ''yes adda, he explained and I believe him saidai zuciyana bata gama aminta da hakan ba'' Murmushi amra tayi tace ''okay…let me advice you, life is so short salima,if he sincerely apologies and explain, don't waste time wajen cire komai ki aje zargi, aikin shedan ne kawai'' Wani irin dadi salima taji da shawarar da amra ta bata don haka tace ''shiknan adda, na cire komai araina,'' Shuru ne yadan ratsa kafin salima ta bude baki tace ''au laa, king azan manta, ammh ne ke kiranki, kinga na zauna ban isar maki ba'' Mikewa amra tayi tace ''shine baki fada min ba'' Cikin sauri taja hijab dinta ta fuce daga dakin zuwa dakin ammah, da sallama ta shugo kanta a kasa tana gyra abayar dake jikinta, ''daughter karaso mana'' Ammah ta fada tana kallonta, karsowa amra tayi har zata zauna a kasa ammah ta hanata, ''yauwa dear, akwai fashion designer zatazo anjima zata dauka measurement dinki, saiki mata bayanin dinkin da zatayi maki'' ''tohm ammah'' amra ta amsa ta cikin sanyi ''daughter?babu dai abunda ke damunki ko? Muhammd bai maki komai ba ko?'' ammah ta fada tana sauraronta don jin me zatace 'yaqe amra tayi ta dan dago fuskanta da dan murmushi tace ''babu abunda yace min'' ''hmmm'' ammah ta fada chan kasan maqoshi, don tasan bazata fada mat aba, wani irin dadi take ji aranta, wannan ita ake kira da mace ta gari mai kare mijinta, murmushi kawai ammah tayi tace ''toh shikanan, ammah duk sanda ya maki wani abu da baki so ki dinga fadamin kinji'' Kasa dagowa amra tayi ta kasa ce mata komai, ammah na ganin haka tace ''dear saikinyi hkuri da halayan sa, haka yake, ni kaina mahiafiyarsa fama nake da miskilanci da kamewar muhammad'' Dariya kawai amra tayi batace komai ba don kunyar maganrsa takeyi agaban ammah, ammah kuwa janta ta dunga yi da hira harta dan sake, nan cikin dabara ta soma nuna mata yanda rayuwar aure ke tafiya da mahimmancin miji a wajen mata, itadai amra kanta a kasa don kunya saidai tana jin duk abunda ammah take fada mata kuma tayi alqawarin amfani da hakan..
Nigerian Army Headquaters…… Tunda ya iso headquarters na Nigerian army, bai tsaya ko''ina ba sai dakin sirri da suke ajiye manya manyan criminals kafin a kaisu prison, dakin ana kiranshi da dark room,dakin yana dauke da securities jiga jiga da suke guarding kai tsaye amar ya shiga dakin, asad na ganin shugowarshi yasa aka kunna lights, takowa yayi har inda asad ke tsaye da wani mutumi da akayi hanging hannayenshi da karafuna, ruwan sanyi asad ya dauka ya watsa ma mutumin, furfugi ya tashi ya dago kumburarren kanshi, alhaji kabiru ne kammaninshi duk sun chanza, kanshi ya kumbura idanunshi sunyi suntumm,badan yanada taurine raiba da tuni an shafe zancenshi, yana ganin amar a soma surutan da ya fara tun safiya wanda yasa asad kiran amar don yazo yaji da kanshi ''nine alajinsu su duka hahahahah'' alhaji ya fada kamar wani zautacce, ''tsinannan yaron Nan, saina kasheka yanda na kashe ubanka, wallahi yanda ka tarwatsa achievement dina na shekaru ashirin saina tarwatsa farin cikin ka, hahahah ay nama tarwatsa, hahahah'' Da sauri amar ya taho azafafe ya bashi wani blow daya sa hakoranshi zubewa duka tass, da sauri asad ya taro amar don inya barshi zai kasheshi ne da duka daya don amar nada wani irin karfi sosai ''oga calm down'' asad ya fada yana rike hannun amar, fusgewa amar yayi yace ''let go'' dagowa alhaji kabiru yayi yana tangadi don yaji bugun nan ba kadan ba yace ''ku kasheni, banida asara tunda zan mutu da cikar burina, wallahi wallahi saina tarwatsa farin cikin ka, hahahaha ina kan tarwatsa wa mahhh mark my words,just wait for the timeeee'hahahahah'' asad na ganin yanda idanun amar sukayi jaaa jijiyoyin kanshi sun fito,yasan abunda zai faru next don yakai high da yawa don haka cikin sauri ya janyo shock ya saka a wuyan alhaji kabiru nan take ya kwala kara ya sume saboda shock din. Amar na ganin haka ya fuce azafafe zuwa office din asad,asad na biye dashi yana shiga ya ganshi ya dafe table ranshi abace, ''oga ka kwantar da hankalika, don't take his word…'' Katseshi amar yayi ta hanyar cewa ''anya bai samu tabin hankali ba? Ko dai bakwa purnishing dinshi ya kamata? Yanda bakinshi yaqi mutuwa dinann I thout kuna aykin daya kamata, why is it taking so long na samu approval din tafiya dashi ne uae, mtewwww'''ya karseh yana dukan table, zama asad yayi a kujera ya kalleshi yace ''oga ka zauna muyi magana'' Da sauri amar ya zauna yana sauraronshi ''nifa ina ganin wannan mutumin fah yana da wata kirsar a kasa,yanda yake maimaita saiya tarwatsa ka anya bashi da wata kungiyar aboye ko mutanen da suke mashi aiki'' Shuru amar yana nazari kafin yace ''but munyi clearing duk mutanenshi, kana tunanin akwai abunda mukayi missing ne?'' amar ya fada yana kallon amar ''nidai I will advice ka zama very careful, zai iya yi maka wani abun'' Asad ya fada looking so concern about it ''and you think akwai uban wanda nake tsoro a duniyannan'' amar ya fada yana kallon asad kamar yanda shuma yake kallonshi ''ay ba sai lallai kai ba,'' Shuru amar yayi yana nazari kafin yace ''yanxu ya maganar approvai din, kace I should clam down zaka nema, if zai dauka time haka zan samu president din dakaina, its just a matter of one call'' Dariya asad yayi yace ''gaggawar me kake yi ne oga, zanyi kokari zuwa end of month'',,,,,,Sun dade suna tattaunawa, sai wajen karfe tara ya dawo gidan, kai tsaye ya karso cikin sitting room, azaune ya taddasu su duka banda ammah, salim na gefen cinyan amra while salima na zaune a kasa aman ma na zaune saitinta ya kafa mata idanu yana kallo, anatse ya fara takowa ya karaso parlor, gaisehsa duk suka farayi harda amra wadda baima lura da it aba don kwata kwata bata gabanshi yanxu,kalloni aman yayi yace ''can we talk'' ''yes sure aman ya fada jikinshi a mace, su salima na ganin haka duk suka miqe harda amra suka wuce sama don su basu waje, suna haurawa sama amar ya kalli aman yace ''I need your help'' da mamaki aman ya dago ya kalleshi don yayi mamakin jin haka daga bakinsa saidai tunda yaji haka yasan abu ne babba don haka yace ''okay, how may I help you'' Nunfasawa amar yayi yace ''uhm… bayan mutanen daka yi mana bayani da suke aiki da daddy akwai wata kungiya ne da yake dashi bayansu?, I mean kun taba Magana makamancin haka'' amar ya fada yana kallon aman seriously, shuru aman yayi yana nazari kafin yace ''I doubt that, bait aba yimin maganar wasu kungiya ba bayan wannan da yake dashi, kana tunanin yana da wata kungiyar ne ko kungiyoyin nashi biyu ne?'' ''no im just curious, inajin kamar we have miss something, baka tunanin akwai waenda suke mashi aiki bayan wanda muka kama?'' Amar ya fada yana karantar aman ''gaskia babu, iyakacin mutanen dana sani kenan'' aman ya fada kai tsaye Mikewa amar yayi yace ''okay thanks for the help'' Da mamaki amar ke kallonshi harya miqe yana mamakin yau amar ne ke mashi godiya.
Yana shiga daki ya rage kayan jikinshi yayi wanka ya shirya cikin kananun kaya, saida yayi sallah ya idar ya zauna, yana nan zaune wayarshi dake kan gado tayi ringing, mikewa yayi hannunshi rike da charbi ya zauna bakin gadon, ganin number ammah akan screen yayi saurin daga wa yakai kunnenshi, ''assalam alaikum'' ya fada kai tsaye Saida ta amsa sallamanshi tace ''ka dawo ne?'' ''yes ammah'' ya amsata kai tsaye ''okay kazoo inason ganinka'' ba tare da tunanin komai bay ace ''okay ammah'' Ajiye wayan yayi da charbin hannunshi yayi stretching jikinshi kafin ya mike,kwana biyu baiyi gyming ba duk sai yaji jikinshi is becoming weak.
Sama ya wuce bedroom din ammah direct, yana shiga ya zauna gefen couch din da take zaune, cikin kulawa yace ''barka da dare ammah na'' Ataqaice ta amsa shi ''barka'' Yana jin haka yasan yayi mata laifi Kenan ko tana fushi dashi, ''ammah na nayi laifi ne'' Dan dagowa tayi ta aje wayar hannunta tare da glass din dake kara karfin ido ta kalleshi babu wasa kwata kwata tace ''bakayi min komai ba, daman inason na shaida maka aisha zata dawo part dinka, muhammd muhammd muhammd sau nawa na kira ka'' Ta fada tana kallonshi, kanshi a kasa ya kasa cewa komai ranshi na kuna sosai, ''yarinyar nan amana ce a hannunka, tana da hakki akanka, saboda haka bana son jin wani zance daga wajenta, I don't have to tell you to treat her right, wallahi Muhammad akan yarinyarnan zamu samu sabani dakai kana jina ko'' Ranshi yayi mugun baci sosai, don babu abunda yazo ranshi sai maybe korarta da yayi jiya shine tazo ta fada ma ammah Kenan, cije lower lips dinshi yayi yana ayyana abubuwan da zai mata, lallai dole yayi maganinta don babu macen da ta isa ta hadashi da mahifiyarshi ''ka dai jini ko'' ammah ta kaste mashi tunaninshi Anatse ya dukar da kanshi kasa yace ''yes ammah'' Sallama yayi mata ranshi adagule ya fuce daga dakin zuwa bedroom dinshi, shifa harga allah ya amince ne bai saketa ba saboda ammah, saidai kwata kwata bashida niyar zama da ita a matsayin mata, babu yanda ya iya dole haka zai lallaba ammah ya nuna mata baya raayin wannan auren. For now dai saiya koya mata hankali sosai, don baya son rawar kai. Haka y agama bambaminsa aransa ya shige bedroom dinsa.