Auren katin kasa complete - Chapter 55
Auren katin kasa complete Chapter 55: Auren katin kasa complete Chapter 55. Anatse kowa kecin abunci sai karar cokali, amra dai tunda ta fara da cokali…
4,434 words
Anatse kowa kecin abunci sai karar cokali, amra dai tunda ta fara da cokali taga kamar baya shiga tayi saurin ajiyewa ta wuce kitchen ta wanko hannunta ta dawo ta zauna ta fara loma, duk motsinta akan idanunshi harta wuce kitchen ta dago, saidai bai yarda sun hada idanu ba sabod idonta na affecting dinshi sosai yanxu, dan wani duk yanda ta lumshe su sai tsikar jikinshi ta tashi. Suna gama cin dinner suka dawo parlor kowa ya baje ana hira banda amra da amanr da sukayi tsit sua zaune opposite din juna ita hankalinta nakan tv ma tana shan agwaluma idan anyi Magana takan dan jefa bakinta a cikin hira while shi kuma idanunshi nakan wayarsa saidai duk hirar da sukeyi yanaji and time to time yakan dan dago ya kalleta.
Salima ce ta maido dashi daga tunanin daya fada ''ya muhammd gobe zamu gama exam fa kuma ranar Tuesday zamuyi graduation' Dan dagowa yayi ya kalleta ''masha allah allah yasa asamu result mai kyau, and congratulation, wani gift kikeso'' Gyara zama tayi don a kasa take zaune ta tankwashe kafa ''ya Muhammad digital drawing book nake so'' Da sauri amra ta dago ta kalleta tana mamaki kafin ta jefa mata harara, ''shine baki fada min graduation din ba? ''toh ay adda kullum kina daki, idan nazo dakinki ma korata kikeyi shiyasa ni nama manta ban fada maki ba'' ''ay shikenan saikije grad din naki ke kadai'' amra ta fada ranta adan baci
Kallonsu ammah tayi tace ''ayi hakuri yaya babba, mantawa tayi'' Sauke kai amra tayi tace ''toh shikenan ammah,'' Kallon salima ta sakeyi ta gallo mata wata hararar ''saboda ammah kawai na hakura'' Amar ne yadanyi gyaran murya, salima najin haka tace ''sorry yaya, adda ta kaste mu, digital drawing board nake so'' ''okay'' ya amsa ta kai tsaye yana latsa wayarshi Cikin murna salima tace ''ammah ki tayani godiya thank you yaya'' ''allah ya saka da alkairi'' ammah ta fada tana kallon, kowa amsawa yayi da ameen, ''toh yarinyar kirki ni me kikeso na baki?'' ammah ta tambayeta tana kallonta, Hannu salima ta saka akan habarta tana nazari, amra dai bat ace komai ba tana sauraronsu aranta tana cewa ''oh su salima an samu waje''
''ammah, basai kin bani komai ba, kawai inason ki kasance a wajen idan akazo bani certificate dina'' salima ta fada tana murmushi ''toh shikenan dear sai kuma me kikeso?'' ammah ta sake tambayarta yayin da take shafa kan salim daya kwantar da kanshi kan cinyarta ''babu komi ammah na, wannan ma ya wadatar'' Dariya duk suka danyi, kafin a kalli aman, ''toh su yaya aman me bazama a tambayi me za a bani ba'' Hararar ta ya danyi kafin yace ''anqi tambaya din,'' Dariya duk sukayi gaba daya harda amra don inkaga yanda suke kamar wasu tom and jerry kwata kwata girmanshi faduwa yake idan har suna magana da salima. Karfe goma daidai kowa ya fara waste wa, amar ne yafara mikewa, ''ammah ina son coffee'' ya fada baima tsaya sauraron response dint aba ya wuce bedroom dinshi, bayan tafiyarshi aman yayi masu sallama shima ya wuce kafin amra ta mike itama tana hamma, ''ammah saida safe na fara jin barci'' Kallonta ammah tayi kafin tace '''ki fara kai mashi coffee din saiki kwanta daughte'' ''tohm ammah'' ta fada kanta a kasa don kwata kwata bataso zuwa part dinshi ba don wani irin barci takeji sosai. Sama ta fara wucewa ta watsa ruwa a gaggauce ta sauya kaya zuwa doguwar rigar bacci cotton wadda ta dan sauko mata har kasa don ta gifta gwaiwarta, sai yar hula data saka same color da rigar. Tana gama shiryawa ta sauko kasa direct zuwa kitchen.
Kitchen ta wuce ta hada mashi lafiyayyan instant coffee sai kamshi ke tashi ta zuba mashi a cup ta futo daga cikin kitchen din, lokacin data futo duk sun wauce sama har ammah ta rage hasken parlor don haka kai tsaye ta wuce part dinshi, da sallama ta shige cikin bedroom dinshi kai tsaye bayan tayi knocking daya. Tana shiga ta rufo kofar kafin ta juyo, a zaune yake kan gado ya rufe kafafunshi da duvet sai laptop kan cinyanshi yana typing cikin kwarewa sanye yake da pjs dinshi milk color, takowa tayi ta karaso inda yake zaune ta ajiye mashi gefen bedside ''ga coffee din'' Bai kalleta bay ace ''thanks'' yana typing. Juyawa tayi zata fita ya katseta ''come back here '' Ya fada in a commanding way babu wasa, wanda yasa gabanta dan faduwa ta dawo ta tsaya dan nesa dashi ''gani'' Banza yayi mata ya cigaba da aikinshi, saida ya dauka kusan minti goma yana aiki, ganin haka yasa ta zamu waje gefen gado ta zauna kusa da kafashi, saboda kafanta da baya juran tsayuwa. Saida ya shafe awa guda yana aiki yana shan coffee harya gama kafin ya rufe laptop din, sai a lokacin ma yaji nauyi akan kafafunshi ashe hartayi barci abunta ba tare da snainta ba, ajiye laptop din yayi ya janye kafafunshi ya sauke su kasa ya mike tsaye, bathroom ya shige cikin mintuna kalilan saigashi ya futo, direct gaban switch ya wuce ya rage haske kafin ya kaarso bakin gado ya rankwafo ya gyara mata kwanciyanta gefe kafin shima ya kwanta dayan gefen ya lulluba masu duvet bayan ya masu addua…. [7/11, 11:17 PM] +218 92-2035171: Update Unedited page Kasa motsawa yayi daga tsaye da yake bayan ammah ta katse wayar, gaba daya baima gane kan zancen ammah ba kwata kwata, meysa ammah zatace yaje ya nemo waennnan abubuwan da baima sansu ba? Ya tambayi kanshi, dan shuru yayi tunawa da wadda tace tana son abubuwan, ranshi ne yayi mugun baci lokaci guda, may yarinyar nan ke nufi kenan? Saboda ya saukar mata yanxu shine take neman kawo mashi raini? Inba raini ba Har tana da guys din da zata hadashi da ammah? Wani abun ya sake tunawa kafin ya danyi yar tsuka ya wuce cikin motarshi azafafe, yana shiga motar ya kunna yayi reverse, already securities sun bude mashi gate don haka ya fusgi motar ya fuce da high speed. Tunda ya hau kan titi ya rasa tunanin da zaiyi, babu abunda yake sai cije lebe yana tunanin kalaman ammah, Ina take cewa "Duk inda za kaje Ka nemo su na baka nan da 30mins" Haka ya dunga nanata kalaman ta a zuciyarshi yana tunanin meysa ammah ke bama yarinyar nan too much attention, yanxu abun Har yakaiga sai abunda take so za a sayo kuma ma babu wanda ta raina da zai sayo mata useless abubuwan nan sai shi saboda ta gama rainashi, and she's shamelessly asking for too much, shi kalaman ammah ne sukafi tayar mashi da hankali yanda take nanata mashi akan dole saiya nemo abubuwan da baima taba ganinsu ba baima sansu ba sai avocado kawai alya sani, haka nan dan dolenshi ya fara tunanin yanda zaiyi karshe sai gashi a wani babban grocery mall anan cikin guzape, yana karasowa yayi parking, saida ya danyi jim a cikin motar kafin ya fara kokarin tunanin abubuwan da ammah tace ya siyo, wayarshi ya fara janyowa ya fara kokarin browsing abubuwan, "what is agbalum" ya fara searching, haka ya dunga browsing dinsu daya bayan daya yana duban sunayen su da turanci, yana gamawa ya fito daga motar ya saka dark shade dinshi don Ana kwala rana sosai, cikin mall din ya shige atsanake cikin kamewarshi,Duk wanda yazo wucewa cikin mall din saiya juyo ya kalleshi.
Kai Tsaye ya shige cikin mall din yabi direction din wajen groceries, yana zuwa ya dan tsaya yana duban wayanshi, haka ya zagaye wajen nan baiga ko daya daga ciki ba, yanda yake zagaye wajen shi kanshi mamakin kanshi yake, don saida yaga 30mins sun da ammah ta deba mashi ya kusa karewa hankalinshi ya Tashi sosai, wani attendee ne dake kula da harkokin kayan lambu a wajen ne ya karaso inda yake don yana daga zaune yana kallon yanda yake zagaye wajen, "good day sir" mutun ya fada yana karasowa inda yake,kallonshi Amar yayi ganinshi da uniform din workers din wajen yayi saurin cewa "thanks" "Sir kana neman wani abu ne?" Mutumin ya tambayeshi yana kallonsa, Sauke glass din fuskanshi yayi ya kalli mutumin yace "yauwa, kunada uhm… agbalum, gunji and uhm…" ya dan tsaya yana nazari, Yalo" Dariya mutumin ya danyi kafin yace "yallabai Ay bazaka samu agwaluma anan ba da su data, saidai irin kan hanya haka," Shuru Amar yayi yana tunanin wani kan hanya kenan, " inane kan hanya kuma? I mean wani direction kenan?" Gaskia oga bazan iya cewa ga inda zaka samu saboda yawanci masu baro ne zakaga suna yawo a hanya haka, abunda na sani shine bazaka samesu a presidential root ba saboda basa bin irin manyan hanyoyin nan" Kallon agogo Amar yayi ganin 30mins din ya cika, baima kaiga gama tunanin ba wayar ammah ta shugo wayarshi, cikin sauri ya dauka yakai kunnenshi, "Muhammad kana Ina ne? What's the meaning of this?" "Ammah please ina nema ne, nazo mall Babu," Amar ya fada yana kokarin yi mata bayani "Yanxu ina Ka taba ganin Ana saida irin waennan fruits din a mall? Kaje kasuwa fruits Ka nema, na baka nan da 1hr, Wallahi son karka bari na sake kiranka baka dawo gida da wannan fruits din ba, kuma duka zaka sayo mata karka bar ko daya" Ahankali ya soma magana "tohm" Bata ma amsa shi ba ta kashe wayar, sauke wayar shima yayi daga kunnenshi yana cije lower lips dinshi, "pack those avocados" Kallonshi mutumin tayi jin abunda yace "sir duka??" A harzuke Amar yace "yes all" Shuru mutumin yayi ya fara packing duka avocados sun wajen don yakai kusan katon kwado daya, saida ya fara weighing kafin ya daukar mashi suka wuce wajen cashier, tunda suka tsaya mutanen wajen suka bisu da idanu dashi da wanda ya dauko avocado din niki niki,, Kallonshi cashier din yayi "sir 50k ne balance dinka" Ba tare da tunanin komai ba ya zaro wallet dinshi daga aljihun sa ya ciro black unlimited card dinshi ya miqa mashi, da mamaki cashier din ke kallon card din don bai taba ganinshi ba kafin yau I inserting cikin pos, yana gama payment ya fito wannan mutumin na biye dashi Har wajen motar shi, boot ya bude mutumin ya saka mashi uban tulun avocado din da sukayi mashi packaging a manya manyan kwalaye kafin ya rufe. Cikin motar ya shige ya zaro kudi daga cikin dash board dinshi da baima san adadin su ba ya miqa mashi, cikin jin dadi mutumin ya karbi kudin yana godiya don kudin yakai kusan albashinsa koma yafi haka, yana bama mutumin kudin ya zuge glass din motarshi yayi baya da motar ya fuce daga mall din.
Haka ya dunga zagaye akan titi yana tunanin ko maybe zai ga masu sayarwa saboda mutumin yace mashi akan hanya ake samun su, haka ya kusa cinye Rabin awa, ganin yana Jan lokaci sosai gashi yana tsoron bacin ran ammah yasa yayi parking gefen titi ya soma dialing number asad don shi kadai ne abokinsa anan Nigeria.
Ringing biyo asad ya daga wayar tare da sallama, gaisawa suka farayi kamar yanda suka saba kafin amar ya danyi jim yace "Ina san zamu wasu fruit anan abuja?" "Wani irin fruit kenan oga?" Asad ya tambayeshi "Uhm Wai abaluma da data da guji da sauransu" Shuru asad yayi kafin yace "Toh fah, gaskia bansan inda ake samun su ba, saidai maybe fruit market Koh ya tsaya irin su hanyar waje wajen garin abuja zaka samu, yawanci dai nafi ganin irin Abubuwan nan a buari" "Ina ne buari?" Amar ya tambayeshi "Hanyar fita daga abuja, zaka dauka wajen awa daya kafin kaje wajen",asad ya bashi amsa "No it's urgent, Ina ne fruit market din?" Amar ya sake tambayarshi "Akwai a garki2, Ka duba map" asad ya sake bashi amsa "Okay thanks" "Zan zo gaisheda hajiya anjima da daddare " asad ya fada yana sauraron amsarshi Kai tsaye yace "okay" yana kaiwa nan ya kashe wayar ya bude map,
Yana saka wajen a map ya kunna motar ya hau titi a guje, haka ya dunga wuce motoci yana kutsawa Har yakai fruit market, koda yake da kyar ya samu Yalo da agwaluma nan ma saida ya saya kusan kwando kwando, kafin yayi payment ya koma motarshi hankali atashe, haka ya juya akalar motar ya bar wajen, haka ya dunga bin hanya yana fatan samun masu saidaga akan hanya, yana cikin driving kuwa ya hango wani mutumi yana tura baro, da sauri ya gangara motarshi gefen titi wajen da mutumin ke tsaye da baronshi a tsaye, sauke glass din motar yayi ya kalli mutumin "barka dai malam" "Barka yallabai" Kallon abubuwan da yake sayarwa yayi kafin yace "menene wannan kake sayarwa?" "Wannan gurji ne yallabai sai kwakwa" Hamdala Amar yayi ya kalli mutumin ba tare da bata lokaci ba yace "Nawa ne duka?" "Dubu goma ne yallabai" ya bashi amsa "Hada mun duka" Amar ya fada yana kwaso sauran cash din dake cikin dash board din, baima taaya irgasu ba ya Mika ma mutumin, karba mutumin yayi kafin ya Mika mashi duka Gurjin da kwakwar "Nagode yallabai bismillah" Karba Amar yayi ya ajiyesu agefen seat din gaba, baima tsaya sauraron mutumin ba da yake cewa "kudin sun haura yallabai" ya fuzgi motar yabar wajen. Haka ya dunga zagaye, baiga wasu ba don haka ya wuce gida kawai jiki a mace, cikin minti biyar saiga shi a gida, yana shugo wa wayar ammah ta sake shigowa, saurin dagawa yayi yace "ammah gani nan na iso," Kashe wayar tayi tana kallon amra dake faman kelayar da amai, ta kasa cin komai, avocado dinma ta cinye shi tass tana neman kari gashi babu. Cikin minti biyu sai gashi ya shugo cikin sitting room security's na biye dashi da da ledoji, anan parlor ya basu umarnin ajiyewa, nan suka jera komai anan parlor, ammah ne ta fara saukowa kasan bayan ta ajiye wayarshi don tabbatarda ko ya dawo, kallon ledojin da ake ta shugowa dasu tayi kafin ta maida kallonta kan Amar, karasa takowa tayi parlorn ta tsaya daga nesa ta kalleshi "Muhammad wannan fah? Kanshi a kasa ya amsata "abubuwan ne" Sakin baki ammah tayi tana kallonshi tana kallon ledojin, "yanxu son Ina zata shanye wannan abun duka?" Sunkuyar da kanshi ya sake yi yama rasa mai zaice "daman na sayo da yawa ne saboda bansan ya ake amfani dasu ba, and I thought maybe zata buqata nan gaba" "Fruits ne fah? Zasu iya lalacewa yanxu ina zamu kai wannan" Yar tsuka kawai ammah tayi ta soma bude ledojin, saida ta bude duka tace "ya banga dataa ba?" "Ammah Wallahi babu na duba ban samu ba" Ya fada ranshi a hade kamar an sashi dole, dukda kanshi na kasa, "Ay kuwa saika nemo shi Wallahi, kaje wannan dinma yayi" Tana kaiwa nan ta deba ko wanne guda biyar ta wuce dashi kitchen, nan ta zuba su cikin sink ta wanke mata su tass kafin ta yanka mata yanda zataji dadin sha, yana nan tsaye ammah ta fito hannunta rike da tray harta wuce sama batabi ta kanshi ba, shiko binta yayi da idanu yana mamakin abubuwan da suke wanzuwa. Kasa daga kafafunshi yayi har saida ta bace mashi daga gani kafun ya dan cije lebe nshi ya wuce bedroom dinshi don watsa ruwa.
Ammah na hawa sama dakinta ta wuce direct inda ta tadda amra harta koma wani barcin wahalar, cikin tausayinta ammah ta kalleta, ciki, haihuwa,goyo , ba abu bane mai sauqi ko kadan shiyasa take tausayinta sosai, Nunfasawa tayi kafin ta karaso bakin gadon ta ajiye mata tray sun kan gado, anatse ta soma tashinta "daughter daughter" Bude jajayen idanu ta tayi da suka koma ciki sosai, ramar datayi ta futo sosai a fuskanta, "sorry dear gashi an kawo maki" ammah ta fada cikin lallami Ahankali ta soma gyara kwanciyar ta mike tana cije lebe, "sannu dear it's not easy, allah ya raba lafiya" kasa dagowa amra tayi kanta a kasa, turo mata tray din ammah tayi gabanta "gashi nan an kawo daughter" Cikin sauri ta dago idanunta ta sauke su akan tray din, da sauri takai hannu ta dauki agwaluma hannunta Har yana karkarwa takai Bakinta ta soma sha, har wani lumshe idanu take yi na samun abun da take so, she has been craving for it sosai, saida ta shanye kusna uku kafin ta ajiye ta dauka kwakwa, guda daya kawia taci ta ajiye ta janyo yalo, haka ta dunga ci hannu baka hannu kwarya, saida tasha da yawa ta ture, "ya isheki daughter?" Ammah ta tambayeta, "eh, Nagode ammah" "Alhamdulillah bari na ajiye maki, Akwai wani abun da kikeso again?" Girgiza mata kai kawia amra tayi tana lumshe idanu saboda barcin da bai gama sakinta ba , ammah na Ganin haka tace "shikenan dear kwanta abinki" Kwanciya amra tayi ammah ta janyo mata duvet kafin ta fuce da sauran zuwa kasa, tana sauka salima na dawowa daga school agajiye, tundaga bakin stair ammah tace "yarinyar kirki Har an dawo" Hammar gajiya salima tayi ta kalleta tace "barka da rana ammah na, Wallahi yau nasha wahala,maths mukayi and it's so hard but Alhamdulillah" Karasowa inda take tsaye ammah tayi tace "sannu dear, Allah ya taimaka, kije kiyi wanka saiki sauko ki diba abunci" "Tohm ammah na, yau adda ta barki da aiki ke kadai ko? Ni na kasa gane wani irin barci ne wannan takeyi kullum" Murmushi kawai ammah tayi kafin ta juya zuwa kitchen da tray din hannunta "yarinyar kirki basai surutu ba, Ina ruwan Ki da barcin ta" Tabe baki salima tayi cikin shagwaba tabi bayan ammah tace "Toh Ay ammah barcin ne ya wuce normal barci wannan, Allah ya kamata take asibiti a duba ta" Ajiye tray din ammah tayi a gefen kitchen island kafin ta maida duba ta ga salima "Toh naji, kije ki wanka saiki sauko kici abunci" "Tohm ammah," Juyawa salima tayi ta fuce daga kitchen din.
Amra bata Tashi ba sai wajen karfe biyar na yamma, tana mikewa zaune ammah ta shugo dakin, gefen inda yake zaune ta zauna tana kallon ta fuskanta dauke fa murmushi "daughter kin Tashi? Ya jikin? Daman yanxu nake shirin zuwa na tasheki kiyi sallah" Muryanta a kasa tace "Alhamdulillah da sauqi ammah, bari naje daki" Miqew amra tayi ta fuce daga dakin, tana fitowa taci karo da amar, bata ma dago ta kalleshi ba kanta a kasa ta wuce daki don wani jiri jiri take ji, shiko saida ya tsaya ya kare mata kallo, fuskanshi tam babu fara' a,harta shige daki bai daina kallonta ba yana waya tunani. Yar tsuka yayi kafin ya wuce dakin ammah. Yana shiga ya same ta a zaune, hira suka danyi inda ta tambayeshi maganar Gyaran gidan nan ya nuna mata abubuwan daya sauya na gidan, ba karamin dadi ya gani a tattare da ita ba lokacin da yake nuna mata abubuwan, "Allah yayi albarka son, gida yayi kyau sosai, Allah ya saka da alkairi" Da mamaki ya dago yana kallonta jin yanda take zabga mashi godiya sosai,baice komai ba sai sauke kanshi da yayi kasa. "Asad zaizo anjima, bai samu zuwa dubiya ba kwanaki saboda ayyukan da mukeyi tare" Kallonshi ammah tayi fuskanta dauke da murmushi don batayi tunanin suna zumunci sosai ba kamar yanda iyayensu sukayi, "Masha Allah asad dan gidan Alhaji abdallah abokin marigayi?" Girgiza mata kai amar yayi yace "uhm shi" "Ahh to Masha Allah, Allah ya kaimu" "Ameen" ya amsa kai tsaye
Kallon agogon dake maqale a bango ammah tayi kafin ta miqe "Bari na dubo daughter ko zata buqaci wani abun" Tana kaiwa nan ta fuce daga dakin ta barci a zaune sakeke. Ammah na futa daga bedroom dinta dakin amra ta wuce, a zaune ta taddata ta hada kai da gwiwa, saurin karasowa inda take zaune kan sallayan ammah tayi kafin Tayi saurin miqa da ita "daughter Yadai? Ko zamuje asibiti? Akwai abund ake damunki?" Ammah ta jero mata tambayoyin, fuskanta dauke da damuwa don saida ta dagata taga yanda idanun ta yayi jaa sosai alamun kukan da tayi, hankali atashe ammah ta riko hannunta ta zaunar da ita bakin gadon tace "muje asibiti ne dear?" Kanta a kasa ta kasa dagowa ta kalli ammah,"ah ah basai munje ba kaina ne ke dan ciwo" "Subhanallah Allah ya sawaqe, now tell me me kikeso kici ko akawo su agwaluman ne?" "Wainar fulawa" amra ta fada anatse jiki a mace, kanta a kasa "Tohm Bari ayi maki,Kinsha magani kuwa?" "Ah ah ban sha ba ammah, amai yake saka ni" amra ta amsata "Daughter haka zakiyi hakuri kina sha saboda ki samu kuzari keda babyn okay?" "Tohm" amra ta amsata kanta a kasa. Mikewa ammah tayi ta fuce daga dakin ta sauka kasa, nan ta tarar da salima tana diban abunci a kitchen, kallonta ammah tayi tace "Har an sauko ni kam Ina Salim ne?" " yana chan yana game,Ay Wallahi Saina fada ma ya Muhammad ya kwace game din ammah," dariya ammah tayi tana kokarin diban flour tace "ki kyaleshi ya huta, anyi hutu ay" Kallonta salima tayi Ganin tana kwaba kulli "Ammah ne zakiyi? Kawo nayi maki" "No dear kici abunci, kafun ki gama ma na soya mata daughter ke son cin wainan flour" ammah ta fada Ajiye abuncin salima tayi tace "Toh fa yanxu kuma har wahalar dake takeyi ammah, hmm nidai Wallahi ammah Kin fison adda Wallahi," Dariya ammah tayi ta kalleta "inason ku duka kowa da irin son da nake mashi, kinga bata jin dadi shiyasa dole na tausaya mata"
Turo baki salima tayi ta karbi kulli tace " shikenan Ay, kawo nayi Wallahi bazan iya tsayawa ina Ganin kina aiki ba, daman bana jin wani yunwa sosai, kawo nayi" Karba salima tayi ta karasa hada komai kafin ta fara so yawa ammah na tsaye harta gama soyawa tass daman bashi da wani yawa don baifi guda uku ba, tana gamawa ta zuba akan plate tace "bari na kai mata" Tana kaiwa nan ta fuce ta wuce sama zuwa dakin amra.
Da sallama salima ta shiga dakin, ahanakli amra dake jingine bakin gado, har lokacin towle ne a jikinta ta amsa mata sallaman da tayi. Karasowa cikin dakin salima tayi hannunta duake da plate din wainar, zama tayi gefen amra kafin ta ajiye plate din a gefenta "barka da yamma addah ya jiki? Ammah tace bakya jin dadi" Dan dagowa mara tayi kafun ta kauda kanta gefe jin turaren dake Tashi daga jikinta na danunta tace "Alhamdulillah!!, kije bana son wannan scent din" Da mamaki salima ta mike tsaye tana kallonta tana wani nazari, dukda tana da kananun shekaru hakan baisa ta Lura da changes a tattare da yar uwar Tata ba "kije banson scent dinki pleas" Da sauri salima ta mike ta fuce daga dakin, tana futa ta mike ta wuce bathroom a guje tana kelayar da amai m, saida ta fidda komai kafin ta dawo agalabaice, kallon wainar tayi, ranta naso saidai tana tsoron amai, haka nan ta janyo plate din ta tsakuri kadan ta kai bakinta, haka ta dunga tsakura tana ci tana tsoron amai harta ci guda daya kafin ta ture plate din ta kwanta kafin a kira Sallar magrib. Tunda ta kwanta take juye juye don ta hana kanta yin barcin.
Salima na fitowa ta sauko kasa zuwa kitchen lokcakin ammah ta wuce bedroom dinta, abuncin data ajiye ta dauka kafin ta koma sitting room ta kunna tv ta fara kallo.
Tana nan zaune Har aka kira sallan magrib tana kallo saboda she's off bata sallah. Kitchen ta mike ta wuce ta Dora simple dinner, stir fry noodles, saida ta gama ta jera akan dining kafin ta dawo parlor ta cigaba da kallonta
Ahankali yake takowa bayan ya hangota daga nesa don daga masjid yake, a bayanta ya ya tsaya ya sauke kanshi saurin kunnenta daga bayan kujeran murya shi chan kasa ya soma magana "my beautiful wifey to be" Da mamaki salima ta juyo don ta tsorata kafun ta dan turo baki "haba yaya Ka bani tsoro" Zagayowa yayi ya zauna gefenta " sorry baby kinyi sallah?" Sunkuyar da kanta kasa tayi ta kasa cewa komai "uhm I guess mun tafi off kenan," Saurin rufe fuskanta tayi tana jin kunya, hira suka shiga yi ta masoya anan zaune.
Ammah ne ta sauko fuskanta dauke da murmushi ta kallesu "son abarmin yarinya haka Kar a cikata da surutun karya na sama din zamani" Dariya ya danyi yace "barka da dare ammah" "Barka my dear," karasowa parlor tayi ta zauna, nan suka shiga hira gaba dayansu anan zaune.
Karfe takwas daidai saiga Amar ya shugo shida asad don, da sallama suka shugo atare, har zuwa parlor, su ammah dake zaune ne suka amsa sallamansu, kallonsu ammah tayi fuskanta dauke da murmushi tace "lale maraba yau PA alhaji ne a gidan namu" Saurin sunkuyar da kai asad yayi don baiyi tunanin zata tuna da sunan ba saboda sunan ne dada ke kiranshi dashi Duk sanda suka zo gidan.. Karasowa sukayi, Har kasa asad ya tsugunna ya gaisheta, da fara'a ta amsashi tana tambayar mutanen gida da hajiyarsa. Amar na daga zaune ya hakimce ya Dora kafa daya kan daya, salima ce Tayi saurin dukawa ta gaisheda da asad, kallonta tayi fuskanshi duake da murmushi ya amsa, maida kallonta tayi ga amar shima ta gaishesa, fuskannan Tashi a hade ya amsa ta. "Kunzo a daidai, bari a kawo dinner" Da sauri asad yace "Wallahi hajiya akan hanya nake, daman ayyuka ne sukayi min yawa shiyasa ban samu nazo ba" "Ahh Toh ko dan lemo Ay Ka tsaya kasha" ammah ta fada tana murmushi kafin ta maida kallonta ga salima, "yarinyar kirki a kawo ma baqo juice ko" Mikewa salima tayi ta fuce daga parlor asad ya bita da kallo wanda Aman ya ga hakan, take ranshi yadan sosu saidai bai nuna ba harta dawo da tray a hannunta, serving dinshi ta fara yi kafin ta miqa mashi. Godiya ya mata in a calming tone kafin ya karba yana mata wani irin kallo mai wuyar fasaara da alamu dai asad ya kamu.
Saida ya gama sha yace "Alhamdulillah Zan wuce hajiya Allah ya Kara lafiya" "Tun yanzu PA? Baka tsaya Kun gaisa da matan abokin naka bama bari a kirata" Da mamaki asad ya kalli Amar daya hade rai yana latsa waya Har lokacin baice qala ba,
Kallon salima ammah tayi tace "Kira min daughter" Mikewa tayi asad ya sake binta da kallo harta wuce sama, tana zuwa ga taddata zaune kan sallaya ta idar da sallar isha'I, daga nesa salima ta tsaya ta soma magana "adda kizo inji ammah" "Okay" amra ta fada jiki a mace, saida ta dauka kusan minti biyu kafin ta mike tabi bayanta don harta fuce.