Kenza eBookz

Auren katin kasa complete - Chapter 56

Auren katin kasa complete - Chapter 56

Auren katin kasa complete Chapter 56: Auren katin kasa complete Chapter 56. Anatse ta futo sanye take da dogon hijab har kasa don towel ne kawai a jikinta,…

4,317 words

Anatse ta futo sanye take da dogon hijab har kasa don towel ne kawai a jikinta, gaba daya dagowa sukayi suna kallonta harta sauko Banda amar da asad, tana karasowa ta gamsu zazzaune, "ammah gani" Ta fada muryanta a kasa don bata tsaya ta tantance su waye a parlorn ba, Dagowa asad yayi ya kalleta, kasa dauke idanunshi yayi akanta, yana tunanin inda ya santa, aranshi babu abunda yake furtawa sai "waiii perfect match" Ammah ce ta danyi Gyaran murya "daughter ga abokin mijinki," Dagowa ta danyi suka hada ido kafin ta sauke "Ina wuni" "La..fi..ya.." ya amsa ararrbe Saurin dagowa amar yayi don haka kawai yaji yana son ya dago, kallon Ind a take tsaye yayi kafin ya maida kallonshi ga asad, Ganin yanda ya kureta da idanu yasa yaji wani irin abu ya taaya mashi a maqoshi sa [7/11, 11:17 PM] +218 92-2035171: Update!! Unedited page… Wajen karfe uku na dare ya farka saboda wani irin zafi dayaji a jikinsa lokaci guda, bude rinannun idanunshi yayi ya sauke su akanta, ta maqalqaleshi gaba dayanta ta sauke mashi nauyin jikinta tana rawar sanyi, ga wani irin turirin zafi dake fita daga jikinta, saurin lumshe idanunshi ya sakeyi yi ya budesu tarr akanta sosai bakinta na gab da nashi lebanta na karkarwa sosai, saurin mikewa yayi zaune ya gyara zamanshi ya kalleta da kyau saboda akwai hasken bedside lamb dake a kunne, kyawawan ya zubama idanu inda wasu siraran hawaye ke zarya akan fuskan nata, saurin taba wuyanta yayi ganin yanda ta fara kafewa bakinta har lokacin yana karkarwa sosai, wani irin zafi yaji daya sashi saurin cire hannunshi ''shes burning up'' ya fada ahankali yana kallon fuskanta, saurin janyeta yayi daga jikinshi ya mike tsaye yama rasa abunda zaiyi don ya mata taimakon gaggawa, tunawa da yanda ammah ke mashi lokacin da yake karami yayi don haka ya wuce bathroom ya jiko hand towel kafin ya dawo gefen gadon ya zauna ya soma goga mata a fuskanta. jikinta ne ya tsananta don har lokacin he can feel yanda take sauke nunfashi mai zafi sosai akan hannunshi, last option daya yake dashi wajen taimaka, kamar bazaiyi ba don yasan zaiyi affecting dinshi sosai, saidai ganin yanda take rawar sanyi ya sashi jin wani iri don haka ya mike tsaye ya kashe ac dakin ya wuce ciki closet ya dauko babban duvet mai nauyi sosai ya sauya da dayan, yanda yake yin komai a gaggauce zaka gane hankalinshi a tashe yake. Yana nan tsaye yana nazari kamar ana fusganshi haka ya soma zame kayan jikinshi ya rage daga shi sai dogon wando pjs dinshi. Ahankali ya hau kan gadon ya zauna kafin ya janyota jikinshi ya soma zame kayan jikinta, saida ya cire kayan barcin nata gaba daya kafin ya hade jikinshi waje daya ya rungumota, wani irin shock ya soma ji saboda yanda fatar jikinta ke gogar nashi don babu bra kwatkwata jikinta, runtse idanu kawai yakeyi jikinshi na vibrating saboda kusanci yayi yawa sosai, janyo duvet din yayi ya rufa masu gaba dayansu tundaga sama har kasa har lokacin tana cikin jikinshi tayi lamo. Ahankali zafin jikin nata ke transferring zuwa jikinshi don shi temperation dinshi is normal, shida idanunshi suke a bude kuma yana cikin hayyacinshi shi kadai yasan irin connection din da zuciyoyinsu suka shiga, don heart beat dinsu kusan a tare suke bugawa, at the point ya tabbatar zuciyarshi is beating for her don kwata kwata ba haka zuciyarshi ke bugawa ba, Bakinshi ya maotso saitin kunnenta ya soma karanto mata addu'oin samun sauki harta daina rawar darin da takeyi nunfashinta na sauka ahankali akan kirjinshi da gashi ke kwance akai.

Har aka kira sallar asuba bai runtsa ba ko kadan yana maqale da ita, sallar ma bai samu yayi ba don sai a lokacin barci ya fusgeshi saboda wani matsanancin ciwon kai daya fara kawo mashi ziyara.

Amra dai bata san wainar da yake toyawa ba saidai daren ranar taji wani irin sanyi a zuciyarta, daman duk dare saitayi wannan zazzabin wanda ayanxu ya zaman mata jiki don duk dare saitayi.

Basu suka tash ba sai wajen karfe goma na safiya, amra ce ta fara bude idanunta saboda wata irin yunwa data nuqurqusota, saurin bude idanunta tayi ganin duhu duhu yasa tadan razana don bata ma lura da ajikinshi take bay a lullubesu da duvet, mutsu mutsun da ta soma yi ne ya farkar dashi daga barcin, bude kyawawan idanunshi yayi ya sauke akanta, sai alokacin itama ta kalli fuskansa da kyau, janyota yayi sosai a jikinshi ya lumshe idanunshi da suka danyi jaa yace ''shiii go back to sleep'' Dauke idanunta tayi akanshi don yanda yayi mata maganar yasa ta soma jin wani abu chan kasan ta saboda whispering tone yayi using, dan turo bakinta tayi kafin ta soma Magana anatse '' ni yunwa nake ji'' Bai bude idanun nashi ba ya sake cewa ''baki isa ba fah, yanda kika hanani barci jiya sai kin koma'' Ashagwabe ta sake cewa ''wallahil azeem yunwa nakeji, cikina yana ciwo'' Banza yayi da ita, idanunshi a rufe to his surprise sai jin kukanta yayi kamar wata baby ashgwabe tana kuka tana gunguni tana Magana ''ni wallah yunwa nake ji'',ta fada tana harba kafarta har wani zungurinshi takeyi da kafafun nata wanda ya sashi runtse idanunshi ya danyi yar tsuka ya bude idanun ya saukesu akanta ''why are you so stubborn ne? ke ba'a isa a fada maki abu kiji ba'' ''toh nace maka inajin yunwa kaqi barina na tafi'' ta sae fada tana kauda kanta daga gareshi. Bai saketa ba haka zalika bai sake ce mata qala ba harta karaci kukan nata ta gaji ta rabu dashi, don kukan ma galabaitar da ita yakeyi sosai. Saida suka dauki kusan minti atalatin a haka, har lokacin bai saketa daman dalilin qin sakinta nata da yayi was erection din data tado mashi wanda bayason ta ganshi a haka ta samu kofar sake rainashi shiyasa ya ki sakinta saida ya bari komai ya dan lafa mashi.

Sauke duvet din ya farayi kafin ya sassauta rikon da yayi mata ya sauke kafafunshi kasa ya wuce bathroom anatse ba tare da ya waigo inda take zaune ba don har lokacin engine dinshi na nan a tsaye bai sauka ba, ya shiga bathroom ya soma zame kayanshi ya fara wanka.

Tana ganin ya shige bathroom ta mike zumbur, sai alokacin ta lura da babu komi a jikinta said an pants dinta, wani irin takaici ta danji a ranta don yanzu kiriri ta gane buqatarta yake sosai, wanda tayi alqawarin bazata taba bari ya kusanceta ba sai ya karbeta a matsayin mace kamar kowacce mace a wajen mijinta. Yar tsuka tayi ta zura rigar barcinta, bata ma staya saka hula ba ta fuce daga dakin aranta tana rokon allah yasa babu kowa a parlor, koda ta futo daga dakinshi ta karasa wajen kofar fita daga parlor nashi saida ta dan tsaya ta bude kofar ahankali ta zuro kanta, babu kowa a parlor kuma bataji wani hayaniya ba ko karar spoons don haka tayi maza ta bude kofar ta fuce fit tana dan sassarfa kamar munafuka. Batayi landing a ko'ina ba sai dakinta tana shiga ta sauke wata ajiyar zuciya tana haki, saida ta dan dawo daiidai kafun ta wuce cikin daki ta soma rage kayan jikinta ta wuce bathroom tayi wankanta.

Tana gama wanka ta fito daga bathroom tana tsane jikinta da hnd towel data ruko a hannunta, agurguje ta soma shiryawa ta saka wani doguwar riga wanda ta dan kamata kadan, tana gama shiryawa ta hau kan sallaya ta tada sallah, tana idarwa ta mike tsaye tana kokarin cire hijab din jikinta saiga sallamar ammah, cikin sauri ta sauke hijab din kasa ta wuce wajen dresser ta tsaya tana murmushin yaqe don bazata so ta ganta tana sallah yanxu ba don duk wand aya ga haka sai ya kawo wani abun, ammah dai ta kamata lokacin da ta bar wajen sallayar haka zalika taga fitowarta daga dakin nashi don tana tsaye tana shirin futowa daga kitchen ta hangota. Fuskan ta dauke da murmushi ta tako cikin dakin tace ''daughter yau kin Makara sosai'' Adaburce amra ta saukar da kanta kasa tana wasa da yatsunta tace ''ina kwana ammah?'' ''lafiya kalua daughter ya kwanan ki da na baby?,'' ammah ta sake tambayarta ''alhamdullillah'' ta amsata anatse muryanta baya futowa ma sosai. ''zo ga breakfast na kawo maki, na sanki da son dumame'' ammah ta fada tana karasowa baking ado ta ajiye mata akan carpet ''bismaillah, zoki zauna kici dear'' Cikin jin dadi amra ta karaso inda ammah ke tsaye kanta har lokacin a kasa fuskanta fayau said an murmushi da ya wanzu akan fuskanta ''thank you ammah, daman dashi na tashi wallahi'' Murmushi kawai ammah tayi mata kafin ta juya hanyar futa tace ''idan kin gama ki sauko kasa, yaudai kid an zagaya estate din, ga salim nan saiya rakaki'' ''tohm ammah'' amra ta bata amsa.

Ammah na fucewa ta zauna ta nadi tuwon nan sosai, saida taci ta koshi harda sude hannu kafin ta wuce bathroom ta wanke hannunta, tana wanke hannun ta fito ta dauki plate din ta fuce daga dakin. Kasa ta fara saukowa babu kowa a kasan don haka ta wuce kitchen kai tsaye ta ajiye plates din, gaban fridge ta tako ta dauka bottle of ice water kafin ta fuce daga kitchen din. Tunda ta gifta ta wuce kitchen ya dago ya kaleta harta futo daga kitchen din batama san yana wajenba, itako amra bata lura dashi ba kwata kwata kanta a kasa saida tazo daidai wuce hanyar dining din ta jiyo karar spoon, duk a tunaninta ma ammah ne a wajen don haka ta dan dago da idanunta, karaf idanun nata suka sauka akan nashi, hannunshi rike da toasted bread yana kokarin kaiwa baki, samun kanta tayi da galla mashi harara tayi wani farr da idanu tare da turo mashi baki kafin ta kauda kanta gefe tana kokarin amsa kiran da ammah dake zaune a sitting room takeyi mata ''daughter daughter, kin sauko ne?'' ''eh na sauko ammah, plate na ajiye ne a kitchen'' tana kaiwa nan ta sake mashi kallo daya ta dauke kanta ta cigaba da catwalk tafiyanta kamar wata tarwada,mazaunanta yabi da kallo har saida ta gifta ma kallonshi kafin ya sauke wata nauyayyiyar ajiyar zuciya ''ya allah,'' ya furta ahankali, tunani ya soma yi aranshi har lokacin bread din na hannunshi bai kai baki ba, ''yarinyar nan na neman haukatani'' ya fada aranshi kafin ya danyi wani murmushin da shi kadai yasan ma'anar shi ''zanyi maganinki ne'' Tura bread din yayi abakinshi, da farko kwata kwata bayajin cin komai saidai yanxu daya ganta da yanda tayi wannan abun da tayi mashi da fuskanta saiya tsinci kanshi da jin dadin cin abunci,.

Amra kuwa wani irin haushinsa takeji yanda yake kokarin maidata kamar wata toy dinshi, don sai ayanxu ta lura da take takenshi na neman coffee da daddare, saboda yasan ammah zata ce takai mashi, tun kafin ta karaso parlor ta soma Magana a zuciyarta ''ay kuwa bazan kara kai maka ba wallahi, daman na lura da take taken ka'' Kaarsowa tayi parlor har lokacin tana tunani aranta,muryar ammah ne ta katseta ''daughter kayannan baya damunki?'' Dan dagowa tayi kafin ta maida idanunta kan kayan ''ah ah ammah, baya damuna'' ''toh shikenan, ki dauko mayafi salim ya rakaki ku zagaya'' ammah ta fada tana maida kallonta ga tv ''tohm '' tana kaiwa nan itama ta wuce sama anatse, tana shiga daki ta dauka dankwalin doguwar rigar ta tsaya gaban mirror ta daura dankwali, ba karamin kyau daurin yayi mata ba dukda bata iya ba, tana gama daurawa ta dauka kohl ta sanya a idanunta da suka dan fada kadan, tana gamawa ta dan jaa baya ta karema kanta kallo, dan bumb dinta ya futo sosai don sai a lokacin ta lura dashi saboda yanayi rigar jikin nata daya fiddashi dan kiff, shafa cikin tayi tana murmushi, ''yanxu da baby anan wajen'' ta fada tana shafa cikin nata tana murmushi, ta dauka kusan minti biyu a tsaye tana shafen cikin nata kafin ta tuna da wani abu, take yanayinta ya sauya tana tausayin kanta, duk sanda ta tuna yanda ya Muhammad ke treating dinta tana jin rashin dadi aranta, ta rasa dalilin dayasa hes always cold to her, kowani aure tasan koda babu soyayya akwai mutuntawa da kulawa da juna saidai ita batayi sa'a ba, don ko fara'arshi baifi sau biyu ta taba gani ba, baya sake mata ko kadan, doguwar Magana ma bata shiga tsakaninsu saidai fada, har lokacin ta kasa gane wani irin mutunne shi, da farko bayan rashin lafiyar ammah har tana cewa ya chanza ashe ashe bai chanza, koda yake what did she expect? Baka taba chanza mutun daga yanda yake dlilin wannan yasa ta kasa tantance a wani matsayi ta sakashi a zuciyarta, bata jin zai taba sonta a duniya don haka bata daurama kanta bama saida ta kawo zancen soyayya aranta ta tuna da Haifa,ada chant un tana tunaninta sometimes harda kuka idan tayi missing dinta saidai yanxu komai ya chanza, but har lokacin tana ranta. Nunfaswa tayi ta janyo mayafin ta ta nada shi kan kafadarta ta fito daga dakin har lokacin bottle of ice din data dauko yana hannunta, natse take tafiya harta sauko kasa, dan dagowa tayi daga nesa ta hangoshi zaune kusa da ammah ya daura kafa daya kan daya, wayarshi maqale a kunneshi yana responding calls, ''har kin sauko?'' ammah ta tambayeta tana kallonta ''eh,'' ta amsa ta kai tsaye kanta a kasa ''toh tashi kuje salim, ku zagaya ko'ina ki danyi exercise kafin ku dawo'' ammah ta fada tana kallon salim dake zaune yana buga ball Mikewa salim yayi ya zagayo inda take ''ammah sai mun dawo'' amra ta fada tana bin hanyar futa daga cikin parlor hannunta rike dana salim suna tafiya ahankali. ''toh daughter saikun dawo'' ammah ta fada tana maida idanunta kan tv. Saida y agama wayar ya dan kalli ammah ta gefen idanu, kamar bazaice komai ba chan kuma ya hade rai yace ''ina zasuje da safen nan'' Yanda yayi maganar yana basarwa kamar bashi ba,ammah bata kalleshi ba ta bashi amsa kai tsaye ''zasuje strolling'' Dan tabe baki yayi kmar bai damu ba, yna son mikewa saidai kuma yana ganin kamar amma zatayi tunanin wani abun don haka ya soma latse latsen wayarshi. Tunda ta fuce yake kallon time din wayarshi don ya dauka suna fita zasu dawo saidai yaga akasin haka don kusan 30mins basu dawo ba, kasa sukuni yayi daga zaunen da yake dukda bazaka taba tantance hakan akan fuskanshi ba sai tsaki daya dunga jerowa har lokacin idanunshi nakan wayar, ganin tsukar tashi taki karewa yasa ammah juyowa ta kalleshi ''is everything okay son?'' dan dagowa yayi ya kalli ammahn kafin ya sauke kanshi ''wani aiki nasaka ayi shine akayi min shirme'' Ammah dai bat ace mashi qala ba don ta lura da yanda ya yanayin nashi bayan futarsu amra, babu abunda tke sai murmushi aranta ta so Magana ''zama ka saukar da wannan ego din naka ne''

Zumbur ya mike tsaye ya wuce bedroom dinshi, cikin yan mintuna qalilan sai gashi da key a hannunshi, don gaba daya hes anxious akan futan nata, gani yake kamar wani abu zai sameta ko kuma za a kalleta wanda hakan ke tayar mashi da hankali sosai, ganin ya nufi hanyar futa yasa ammah cewa ''futa zakayi? I thought kace yau wuni zakayi a gida'' ''akwai wani abu da zanje na karba ne'' ya amsata ''okay adawo lafiya'' ammah ta fada tana dauke idanunta daga gareshi tana dan murmusawa irin nasu na manya.

Yana futa ya wuce wajen zabgegeiyar benz dinshi ya budeta ya shige ciki, cikin hanzari ya kunna motar yayi reversing, wani irin mahaukacin horn yayi don gab daya securities din suna cikin cctv room sai karar horn dinshi sukeji. Da sauri daya daga cikin securitis din ya futo ya bude mashi gate din, a harzuke ya karaso da motar inda securities din yake ya zuge glass din motar ya soma Magana cikin fada ''what the hell is going on with your head? Kana son loosing job dinka ne? Da sauri secuty yace ''no sir sorry sir'' ''so you better do your job properly, this is your last warning'' ya karashe yana fuzgar motar aguje kamar zai tashi sama, bin kan titin estate din ya farayi don street kusan uku ne a cikin estate din, haka yabi first street baiga alamunsu ba, gaba daya ranshi a dagule yake shi kanshi ayanxu kasa controlling kanshi yakeyi akanta, haka ya dunga bin street din estate dinnan yana zagayesu yana dawowa tass bai samesu ba, saida yazo dab da last street ya hangosu daga chan nesa, rage gudun motar tashi yayi ya soma tafiya ahankali, nan ya soma hangosu da kyau, tana daga zaune kan wani dakali wajen kofar gate din wani apartment salim na daga gefenta shima a tsaye yana wasa da wani farin cute kare, itama idanunta nakan Karen tana kokarin shafa kanshi, saurin taka burki yayi kiii lokacin da wani mutumi ya fito daga cikin apartment din yana masu Magana, dan jim yayi yana kallonsu zuciyarshi na boiling sosai, abunda ya kara harzuka shi shine ganin tana murmushi tana shafa kan Karen wanda mutumin ya janyo ring din da ake kama Karen dashi da alamu nashi ne, amar dai idanunshi sunyi jaa sosai, ranshi yayi mugun baci sosai har baisan lokacin daya karaso inda suke da mot aba ya zuge glass din motar fuskanshi babu annuri yace ''get in'' Tunda ya tsayar da motarshi amra ta dago ta kalli motar,baka hango na ciki don saida ya zuge glass din ta ganshi, gabanta ne yadan fadi haka kawai ba tare da sanin dalilin ba, ganin yanda fuskanshi ta hade sosai yasa ta danji wani iri, ''do I have to repeat my self'' Mikewa ta soma yi ahankali tana kokarin mikewa, kafanta da ya dan sake mata ya jaaa jinni ne yasa ta danyi baya ta danyi kara ''washh'' da sauri mutumin ya mika hannu zai taimaka mata karta fadi kasa, aamar da yaga haka yayi saurin buga mashi tsawa ''don't you dare, don't you dare touch my wife!!!!! Are you insane!!!'' Yanda yake fada a cikin motar da yanda gaba daya a susuce yasa gaba dayansu suka sha jinin jikinsu harma da mutumin, kallonshi mutumin yayi in a calming tone yace ''sorry yallabai, naga zata fadi ne shine!!!'' ''shut the fuck up ka wuce cikin apartment dinka ko na koreka daga..'' Kallonshi mutumin ya dunga yi tun lokacin daya soma Magana, sai a lokacin ya lura da koma waye, ''the owner of the estate,'' ya fada aranshi, cikin sauri ya akste amar daga abunda yake shirin fada yace ''dan allah kayi hakuri sir, tsautsayi ne'' yana kaiwa nan ya wuce cikin apartment dinshi da dan Karen sa a hannu. Amra dai komawa tayi baya ta zauna saboda zugin kafarta, idanunta sunyi jaa sosai, ''keee'' amar ya sake fada yana kallonta, bata dagoba don at this point dayace kee dinnan ya hasalata sosai ''idan kika bari na sake repeating kaina saina…'' ''saikayi me?'' tayi saurin katseshi ranta a bace, itama idanunta yayi jaa sosai, mai ciki da jaraba, lokaci guda idanunta ya rufe ta soma Magana ''nace me zakayi min? dukana zakayi?, ehhh?' da fada da dan karfi daya salim matsowa kusa da ita yana jan gyalenta alamun tayi shuru, saurin ture hannunshi tayi ta hankadashi gefe idanunta yayi jaa sosai bata ji bata gani ''matsamin a waje kai kuma,'' Tana fadin haka ta maido da idanunta kana amar ''ina ruwanka dani yaya? Naga dai baka damu da alamarina ba? Baisa yanxu kake shiga cikin rayuwata?, '' Ranshi ne yayi mugun sosuwa don haka ya mata wani irin kallo mai wuyar fassara, cije lower lips dinshi yayi ya fusgi motarshi yabar wajen yana jin haushin kansa da yanda ya sauke kanshi har tana iya fada mashi Magana, gaba daya maganganunta basu bashi haushi ba sai Kalmar dukana zakayi datace, abun ya bata mashi rai sosai, me take nufi Kenan? Hes not that ruthless, bazai taba koda bugun hannunta ba saboda tana da wani matsayi babba a zciyarshi.

Yana barin wajen ta sauke wata ijiyar zuciya don batayi tunanin zasu wanye da sauqi haka ba don duk a tunaninta da sanin da tayi mashi da zafin rai bazaiyi shuru yayi walking out haka ba, salima e daya rakube gefe ya tako inda take ya rike hannunta ya taiamaka mata ta mike suka bi hanyar dazai maidasu gida. Cikikin yan mintuna kalilan suka karaso gida, babu abunda take sai haki har suka karso cikin gida, ammah suka tadda a zaune yanda suka barta ''sannu daughter kinyi kokari'' Murmushi kawai amra tayi ta samu waje ta zauna ta mikar da kafarta ''washh ammah na gaji anya zan iya kuwa'' ''zaki iya mana daughter, sannu haka zaki dage harki saba' ammah ta fada tana kallonta ''dauko min ruwa mai sanyi salim'' amra ta fada tana kallonshi Mikewa yayi tsaye ya wuce kitchen kallonta ammah tayi tace ''ku hadu da son akan hanya kuwa yanxu shima ya futa'' Hade rai amra tayi tadan tabe baki kafin tace ''eh munga fucewarshi lokacin muna dawowa''….. [7/11, 11:17 PM] +218 92-2035171: Update Unedited page Hade rai amra tayi tadan tabe baki kafin tace ''eh munga fucewarshi lokacin muna dawowa'' Shuru ne ya biyo baya bayan dawowar salim da ruwan data buqata, tunda tayi resting bayanta ta soma jin barci barci sama sama, ammah na dake duban ta jefi jefi tana ganin yanayinta tace ''dear kije ki kwanta kafin anjima da yamma saiku sake futa ko?'' Kamar daman jira take ta mike tsaye tana dan yin nishi sama sama ''toh ammah,'' Tana kaiwa nan ta wuce hanyar stairs zuwa dakinta, datayi dan taku daya biyu saita huta kafin ta cigaba, ammah na kallontta daga zaune, fadin irin farin cikin da take ji idan ta kalli amra dake dauke da cikin Muhammad mara misaltuwa ne, shes so happy, kusan kullum sai tayi sadaka, duk dare kuwa bata barcin daya wuce awa biyu, haka zata tashi ta kafa goshinta akan sallaya tana godiya ga Allah daya basu wannan kyauta ta musamman, she's just waiting for the perfect time ta fada ma Muhammad, dalilin dayasa ta boye mashi kuwa shine, yanda ta lura yana qaunar amra sosai amma yaqi futowa fili ya nuna yana son ta, bayan wannan tafison sai ya nuna yana buqatar matarshi da kanshi kuma yayi accepting dinta da kanshi kafin ta fada mashi. Ayanxu ta zuba masu idanu tana karantarsu sosai, daya daga cikin abunda ta lura dashi shine, yanda yake pushing amra don duk hidimar datakeyi mashi akan idanunta ne shi kuma yana basarwa saboda ego dinshi daya kasa barinshi ya saukar da kanshi kasa, da farko taso ta barsu a yanda suke ko zasu dawo dan kansu saidai kuma amaimakon komai ya falling into places sai akasin haka, don yanda yake pushing din amra yasa take baya baya dashi, don da gayya ammah take aikata dakinshi don ta lura ta daina kwana anan dinma, bata takura mat aba haka ta kyaleta tana kwana inda takeso saboda yanayin ta. Nunfasawa ammah tayi tana tunanin, harga allah tana son tagansu kamar kowanne mata da miji, saidai hakan kamar bazai samu ba saboda kafiya irin ta amar, tunanin yanda zatayi dasu ta fara kafin takai kan decision dinta. Tana nan zaune salim na gefenta yana barcin daya saba a doguwar kujera akayi sallama, kallon inda yake shugowa ammah tayi fuskanta dauke da fara'a da bata barin fuskanta, ''malam labara maraba lale'' Har inda take zaune ya karaso ya zauna a kasa ya fara gaisheta ''nace ka daina zama a asa malam labaran, ga kujera nan manene amfaninta kenan'' Cikin girmama way ace ''hajiya nan ma yayi, ina wuni ya iyali?'' ''lafiya kalua alhamdullahi ya aykin gona?,ya kuma jiki'' ''da sauqi hajiya alhamdullahi, '' ya bata amsa ''toh madallah allah ya taimaka'' amma ta amsa shi tana kokarin kallon tv. Hannunshi ya zaro cikin aljihun shi yace ''hajiya ga wannan, kudin wannan shekarar ne, shine nace bari na akawo'' Kudin ya ajiye mata da paper a gefe ''wannan list din komai ne na rubuta a ciki, murmusawa ammah tayi ta kalli kudin daya nade a leda kafin ta maida idanunta kanshi, ''masha allah, ka rike a hannunka, duk wani abunda za a buqata a gonar saika saya dashi sai kuma amfaninka kaima'' Kanshi a kasa yace ''hajiya akwai duk wani abunda za a buqata, wannan…'' ''Toh ka rike kaja jari'' ammah ta kkasteshi, wasu ahwaye ne suka fara zarya akan fuskanshi, kafin ya dan dago ya soma jero mata adduo sosai. ''babu komai malam labaran ka daina min godiya? Yauwa daman inata so na tambayeka, ya maganra memories dinka kuwa, akwai improvement?'' nunfasawa ya danyi yana murmushi yace ''alhamdullahi, gaskia akwai, saboda yanxu idan na kalli wasu abubuwan wani shafi daga cikin rayuwata yana zuwanmin'' ''toh alhamdullah allah ya kawo sauqi cikin lamarin'' ammah ta fada tana murmusawa ''ameen hajiya, bari na wuce,'' ya fada yana mikewa, ''toh madallah malm labaran nagode sosai.'' Dan waigawa yayi ya kallli inda salim ke kwance ya juyamasu baya don baya fuskanta inda suke zaune, murmushi kawai malam labaran yayi ya fuce daga gidan yana jin yanda hajiyar take kara qima da daraja a idanunshi, ''oh ashe waennan ne yaran da ta rikesu, allah sarki samun mutane irin hajiya sai an tona, baka sansu ba basu sanka ba ka rike su amana kamar naka allahu akbar'' malam labaran ya fada yana tafiya shi kadai har yazo bakin wajen mai gadi, don shima maganar yara da hajiya take rikewa daga wajen baba mai gadi yaji zancen. Sallama yayi ma baba mai gadi kafun ya fuce daga gidan.

Bangaren amra kuwa tana shiga daki ta soma zame kayan jikinta ta wuce bathroom don jikinta har wani yami yami yake mata saboda dan zufar datayi, a gaggauce ta watsa ruwa ta fito daure da towel tayi kwanciyarta nan take barci ya debeta.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull