Kenza eBookz

Auren katin kasa complete - Chapter 7

Auren katin kasa complete - Chapter 7

Auren katin kasa complete Chapter 7: Auren katin kasa complete Chapter 7. Washe gari da sassafe ummi ta shugo ta tashesu, wanka sukayi atare, wani simple…

4,240 words

Washe gari da sassafe ummi ta shugo ta tashesu, wanka sukayi atare, wani simple riga haifa ta bata ta saka, itama ta saka wani Ethiopian riga shigen irin nata, breakfast sukayi anan dakin haifa kafin ummi ta shugo tare da makeup artist wadda haifa tayi booking don yima amra kwalliya don su samu pictures, gaban haifa ummi ta karaso sannan tace "habibty get me glass of warm water," "okay ya ummi haifa fada tare da fucewa don taga kamar korarta ummi keson yi,zama ummi tayi gefen amra kafin ta kalleta fuskanta dauke da murmushi ta miqa mata wani abu kamar chocolate, hannu bibibyu amra ta karba kafin ta kalli ummi dake mata murmushi ''habibty eat this, yanada kyau sosai,''..ko ba a fada ma amra ba tasan aphrodise abu ne in form of chocolate da rubutun larabci ajiki, karba tayi tare da yi mata godiya sannan ta cinye tass, lokacin haifa ta shugo cikin daki da warm water ah cup, karba ummi tayi sannan ta bama amra tace ''warm water should be your hydrated water from now on''..godiya amra tayi mata sannan ummi ta fuce, wato wani abu da amra ta lura dashi shine, ummi batasan cewa wannan auren anyi shi ne saboda yarjejeniya ba, kuma suna samun abunda suke so zasu raba aure.

Masjid al abu dhabi… Babu mutane sosai aciki don duk an tattafi sbd an idar da sallah sai few mutane qalilan da bazasu wuce 30 ba, abuh ne zaune da jellabiya kundura irin nasu na larabawa sai hammam wanda shima yasha jellabiya kundura sai oga kwata kwata wanda shima kunduran ne ajikin shi saidai shi ya daura wata bakar riga kamar wadda yawanci haka duk wanda zaiyi aure yake sawa, rigar tana da hula ajiki, sai kayan ya fito da zallan kyawu da haiba irin tashi, fuskarnan babu yabo ba fallasa, Karfe 2 daidai hammam ya karbama abokinshi kuma amininshi auren amra daga wajen abuh akan sadakin 100,000 dirhams, saida aka gama komi abu yayi signing as waly dinta shima hammam yayi sannan aka fara musabaha suka firfito, suna fitowa hammam ya soma hotuna don hotunan ayanxu na da matukar amfani a wajen su, saida suka dauka su uku, shi da abuh da amar, sannan yayi ma amar da abuh sannan shima yayi ma kanshi da abuh. Chapter 69-70

Tun akan hanya hammam ya tura ma haifa hotuna, wadda tana gani wani dadi ya lullubeta saitaji dama nasu aka daura ita da hammam dinta. Kallon amra tayi wadda aka gama yima makeup wanda ya amsheta sosai, hancin nan ya futo dau sannan tace "let me get the dress", anatse taje wajen wardrobe inda ta aje paper bag din jiya,fuskanta dauke da murmushi ta tako har gaban amra sannan tace "get up mana madam, an daura fa, you're now the wife of our rudy general, the arrogant general''…tana kaiwa nan ta kalkale da dariya, amra ko banza tayi da ita kuma taqi tashi daga kwancen, saida ummi tazo ta shaida masu cewa abuh ya dawo dashi da groom din kafin ta miqe, zaro rigar haifa tayii, nan amra ta saki baki galala tana kallon ikon allah, wato wata irin haddaddiyar English gown fara tass tasha uban stones a jiki, tayi masifar haduwa, sai wani white lon veil agefen rigar, rigar duk duwatsu ne tundaga sama har kasa, sannan tayi wani flee kamar ta princesses, takowa haifa tayi har gabanta ta taimaka mata wajen saka rigar, aikuwa rigar tayi mata dam tayi wani irin masifaffan kyau kamar ka sace ta ka gudu, sai masha allah kawai haifa ke cewa,jawo hannunta tai ta zaunar da ita gaban dresser sannanta ta dauko wani siririn diamond necklace tace ''I know this wedding is not like every other wedding, but still its your wedding dear best friend, so this is my gift congratulation, allahumma bareek, and I've snap pictures of it as evidence also''…tana kaiwa nan amra ta rungumeta idonta na kawo ruwa tace ''haifa, ke mutuniyar kirkice, mai zuciyar alkairi, ina rokon allah a baki abinda kike nema duniya da lahira, I love you my best girl''…sarkan haifa ta sanya mata sannan ta sa mata dan kunnen Sarkar, anatse ta jawo veil din jikin rigar sannan ta fara nada ma amra akan coily hair dinta dayasha gyara sosai sai yayi kamar tayi mata mini hijab,yayi mata kyau sosai dukda bai rufe adon gaban rigan ba da boobies dinta sukayi flashing ta cikin rigan, wani haddaden hills haifa ta saka mata sannan tayi mata ruwan tsadaddun turare masu kamshi sosai, tana gama wa itama ta shirya cikin purple dress itama ta nadda veil din kamar hijab, ummi ce ta Kara shugowa ta umarce ta data yi sallah raka'a biyu don nuna godiya ga Allah wanda ya zama masu kamar tradition Duk bride saitayi, tana idarwa haifa ta rike hannunta suka fara sauko wa kasa anatse, tunda suka fara saukowa hammam ke kallon amra chan kuma ya kau da kanshi, shiko oga wayace ma akunnenshi yana Magana ahankali baibi ta kansu ba,suna karasawa haifa ta soma guda irin nasu na larabawa da yan wake tace ''marhaban mijin kawata, congratulations to you boths''..hammam ne kawai ya amsa ta sannan ta zaunar da amra gefenshi wadda itama ko kallo daya batayi mashi ba, suna nan zaune abuh da ummi sukazo, hotuna akayi masu kyau sannan sukayi congratulating dinsu suka wuce sama, suna tafiya haifa ta soma daukan ango da amarya, ganin sun zauna saroro yasa haifa saurin cewa ''haba kun wani babbata rai, ku dan matso mana sosai sbd evidence, idan muka gama saiku koma yanda kukeso''…amar baiko kalleta ba balle tasa rai ko zaiyi hakan, saima aje wayanshi ya yayi ya soma lumshe ido alamun gajiya, ganin haka yasa wani kuzari ya zoma amra ta miqe ta tako har gabanshi ta zauna dab dashi sosai, hannunta na rawa ta kamo hannunshi ahankali ta rike gam sannan ta sunkuyar da kanta kasa, jin alamun mutun gefenshi da wani irin dumin da yaji cikin tafin hannunshi ya sashi saurin bude idanunsa tarr akanta sai alokacin ma ya kalleta, dagowa tayi suka hado ido, ganin irin kallon da yake mata yasa ta sauke kanta qasa, shima dauke nasa kan yayi dukda bai cire hannun nashi daga nata ba, gashi wani irin kamshi takeyi sosai, wanda har cikin kirjinshi yake jin sa. Hotuna sosai haifa ta dunga zabga masu, dukda basuyi murmushi ba amma kyauwun da allah yayi masu saiya wanke hoton sosai. Ganin zaman yaqi karewa ya sashi mikewa tsaye zai kama hanya ya fuce, tunawa da abinda hammam ya fada mashi ya sashi tsayawa chak ''amar plesase be more serious dan Allah nasan halinka, kasan wannan kamar al'ada ne anan dole haduwarka ta farko da matar ka saika rungumeta so you have to do it''… dogon tsaqi yayi sannan ya juyo ahankali ya tako har gabanta, matsowa yayi sosai dab da ita sannan ya sanya hannunshi biyu ya tallabo kafadarta, ganin haka yasa haifa sauri saita camera ta fara video din moment din, anatse ya dagota har yanxu hannuwanshi na kafadarta, amra wadda tajita an dago ta sama yasa tayi sauri daga kanta, ganin fuskarshi dab da tata yasa kirjin ta ya fara dum dum, don shi dake kusa da ita yana jiyo yanda kirjinta ke bugawa, anatse ya matso daa ita gaban shi har tana cewa ''ahhh'' tayi gasping breath dinta, nokewa tayi don ko kafadarshi tsayinta baikai b, ahankali ya ranqwafo daidai goshinta sannan ya zame hannunshi daga kafadarta ya sanya a cute fuskanta, ahankali ya dora labbanshi masu taushi akan goshinta yayi kissing, take ta runtse idanunta wani irin sanyi taji tundaga tsakiyar kanta da kuma natsuwa ahankali ya cire bakinshi ya saqalo hannunshi ah kwankwason ta ya kara matso da ita gabanshi sosai, wani irin calm runguma yayi mata dukda ya qagu yayi yayi ya bar wajen, wani irin guda haifa tayi sannan tace ''masha allah, masha allah allahumma bareek'' saida ta dauka duk wannan moment din sannan ta kashe,shiko yana gamawa ya sa kai ya fice don ya gaji da kayan dake jikinshi, gashi komai kamar tilastashi akeyi don harga allah gani yake wannan ma raini ne kawai, amma tunawa da matsalarshi yasa kawai ya kawar da zancen.

Yana fita ya wuce motorn shi da m5 ya shigo da ita, shigewa ciki yayi sannan suka ja motor,kallonshi m5 yayi sannan yace ''congratulations sir''..dakyar yace ''thank you'' sannan ya kwantar da kanshi, don wani irin ciwon kai yake ji, duk wannan stress din shi bai saba dashi ba, aiki kawai ya sani, kallonshi m5 ya kumayi yace ''sir are we going to your penthouse or your apartment''…jin haka yasa amar cewa ''apartment'' direct apartment dinshi m5 ya kaishi, saida ya dauka wajen 20mins kafin ya futa daga cikin motar, duk wanda ya ganshi yasan ango ne sbd kayan jikinshi, anatse ya dannan pins din kofar yasa kai ya shige, wanka kawai yayi sannan ya fito daure da white towel a waist dinshi, bai tsaya saka kaya ba ya lafe kan gado sai bacci…

Amra kuwa ita ma wucewa sama tayi dakin haifa don cire wedding dress din jikinta, don ta dameta sosai, saidai tayi mata kyau, gaban dresser ta tsaya tana kallon kanta, ''masha allah'' ta furta.. ahankali moment din dazu ke tariyo mata, da sauri ta kawar da zancen ''no no, this is just like a contract marriage, kina samun abinda kike buqata amra shikenan its over, don't over think it amra''..duk wannan abun da take yi acikin zuciyarta take zancen zucin.. dakyar ta samu ta sabule rigar ta wuce toilet, wanka ta sakeyi sanna ta fito ta kwanta don duk ta gaji sosai.

Ganin duk sun tafi yasa hammam shima yayi ma haifa sallama ya wuce. Daki direct haifa ta wuce, tana shiga taga amarya na bacci daga ita sai purple towel na haifa don ta rasa kayan da zata sa don duk wardrobe din haifa bataga wanda zai shigeta ba, da sauri ta karasa kan gadon sannan ta dan bugi bayanta dan rub da ciki tayi, zannan henna din bayanta ya futo gwanin sha'awa, ''babeee tashi mana, kina matsayin amarya kina bacci, ay ko baki isa ba tashi we have a lot to do''…hararar ta amra tayi sannan ta wuce toilet don kuskure bakinta, baccin yayi mata dadi sosai ba kadan ba, tana fitowa haifa ta bata wani abaya, yellow color tasha stones itama, tayi matuqar amsar jikinta, anatse ta karaso ta shirya, tana gamawa ta wuce wajen da suke sallah, tana idarwa itama haifa tazo ta tada kabbara,tana idarwa amra tace ''yanxu kuma ina zamuje, ni bacci nakeji wallahi''..miqewa haifa tayi sannan tace ''idan mukaje zaki gani da idonki basai na fada maki ba''…tana kaiwa nan ta fuce daga dakin amra kuma ta biyota abaya, part din abuh suka wuce, saida suka kara gaggaisawa sannan haifa tace ''abuuh we need that your black card please zamuje shopping'', murmushi abuh yayi sannan yace ''okay kuje amma karku dade'', miqa masu card din yayi sannan sukayi ma ummi sallama suka fuce.

A daidai emirate mall motar haifa ta tsaya, amra dai kallon ikon allah kawai take, futowa sukayi suka shiga ciki, direct Joanna shop suka wuce, nan haifa ta judo mata kayan sawa English wears masu shegen kyau da tsada, saida suka dauka kusan awa biyu anan kafin su wuce wajen jesminé abaya's nan ma jidarsu haifa ta dungayi kamar ba da kudi za a biya ba don ita batajin zafin fitar su kwatakwata, saida suka gama da abayas sannan suka wuce modern sally wajen jakunkuna da takalma, at this point amra dai ta hakura kawai ta zubama sarautar allah ido tana kallon haifa, saida tayi mai isarta kafin suka fito suka wuce wajen lingerins, ganin inda haifa ke shirin shiga yasa amra tsayawa chak tace ''wallahi babu inda zani kuma, me zamuyi a wannan wajen''..dariya haifa tayi sannan tace idan na sayo karki saka''…ta wuce ciki abinta, wasu yan iskan lingering da bra da panies ta kwaso mata wajen kala ashirin, wasu abubuwan ma tana diba tana dariya ita kanta, saida ta gaji kafin ta futa, inda tabar amra nan ta sameta, janta haifa tayi suka samu waje suka zauna suka huta kafin su miqe don lokacin wajen karfe takwas yayi, haka suka samu helpers suka kwashe masu kayan har wajen da sukayi parking moton da sukazo dashi. Haka suka dawo gida da kaya nikki nikki, saida sukaci abinci sukayi sallah kafin haifa ta fara jawo kayan da suka sayo, don sun kusa cika tsakiyan dakin nata donma dakin yana da girma sosai. Miqewa haifa tayi ta jawo wani katon akwatin ta na delsy, ta bude sannan ta jawo na ciki wanda baikai na wajen ba, daukoshi tayi gaba daya ta kawo shi tsakiyan dakin sannan ta fara jera kayan da suka sayo, amra dai na zaune daga kan gado tana kallon iko ALLAH saida ta gama tsaf sannan ta mike da akwatunan ta ja su gefe sannan tace, "dare yayi ya kamata mu kwanta amarya sbd mu samu mu tashi da wuri gobe''.. shirin bacci sukayi kafin su kwanta. Wajen karfe uku na dare amra ta tashi, lokaci guda baccin nata ya qaurace mata, hakan yasa tayi saurin miqewa ta sakko daga kan gadon, direct toilet ta wuce ta dauro alwala, bayan ta futo ta gabatar da sallah atsanake, ta dade a tsaye tana rokon allah ya shiga lamarinta…anan zaune har akayi sallan subh daman haifa bata sallah so bata ma yi qoqarin tashinta ba, saida ta idar sannan ta zauna tayi azkhar, anan zaune bacci ya kwasheta mai dadin gaske. Sai wajen 10 suka farka kusan atare, wanka haifa ta fara shiga bayan ta futo itama amra ta shiga yin wankan, tana futowa ta wuce gaban dresser ta shafe jikinta ta mayukan haifa masu saka laushin fata, saida ta gama sannan ta feshe jikinta da turare, tana gama wa haifa ta shigo hannunta dauke da breakfast, ajewa tayi sannan tace ''babe baki shirya ba har yanxu, ga kayan dana fito maki dasu, ya kamata muyi sauri mu gama sbd hammam ya kusa zuwa, jin haka yasa amra cewa ''yau kuma ina zamuje?, nifa na gaji gaskia''..kallonta haifa tayi bayan ta miqa mata wata brown English gown tace ''lallai ma, keda ya kamata ace baki manta ba kece zaki manta haka, to yau zamuje for application,mudai yan rakiya ne''…jin abinda haifa tace yasata saurin cewa ''uhm ni harna manta ma''..kayan ta saka ajikinta, ay kuwa kamar daman don ita akayi kayan sai yayi mata kyau sosai, zama sukayi sukaci breakfast sannan suka zauna jiran hammam.

Har akayi sallan asr bai zo ba, hakan yasa amra cire rai kawai na fita, haka yasa tayi kwanciyan ta bayan tayi sallah, sai wajen magrib haifa ta tasheta sannan tayi sallah taci abinci ta koshi, abin zaqi haifa ta kawo mata mai suna kunafa ta kara ci ta koshi bam bam, mintuna kadan saiga ummi ta shigo dakin hannunta dauke da wasu packaging mai kyau, lokacin haifa ta shiga toilet don tayi wanka, kallonta ummi tayi sannan tace ''taso kizo nan''.. miqewa amra tayi sannan suka zauna gefen gadon haifa sannan ummi ta soma Magana ''abnati 'awadu 'an 'ansahak (my daughter I will like to advice you)'' nunfasa ummi tayi sannan ta cigaba ''shi aure da kike gani ba abin wasa bane, idan anyi yishi anyi Kenan ba a fatan rabuwa, ki zauna ki natsu sosai, ki kula da mijinki, karki sake ki nuna mashi bacin ranki akan komai, sannan komai zai faru kiyi kokari kiga auren ku yayi working out, karki bari misunderstanding yasa kiyi abinda zaisa kizo kina dana sani, at the end ina maki fatan alkairi da zuria dayyab'' kissing din goshinta ummi tayi sannan tayi mata kyakyawan runguma fuskanta dauke da smilying, anatse ta jawo wani park acikin kwali wanda ta shigo tare dashi da package din paper bags din, ta bude kwalin tayi ta zaro wani abu kamar chocolate sannan ta bata tace ''ungo kici wannan, ga sauran nan zan hada da kayanki, make sure you eat one pack everyday,'' sannan ta zaro wani pack din wani abun daban daga cikin packaging din tace ''make-sure every single night you take a shower,with this'' ta bude package din ta zaro wani abu da akayi rubutun larabci a roba mai kyau, sannan ta miqa mata wani turare tace ''this should be one of your scent collection habibty''…nan ummi ta bata komi wanda amra na ganin haka tasan aikin da uwa ya kamata tayi ma diyarta da zarar zata aurar ummi tayi mata, wani irin dadi ne ya lullubeta sosai, anatse ta dago ta kalli ummi tace ''shukran jazilan laki ya ummi''.. saida haifa ta futo daga toilet tukun kafin ummi tace ''haifa ga delivery ya karaso, naga sunanki ne ajiki, bari na sauka qasa nasan abuh ya dawo yanxu daga masjid''..fucewa ummi tayi sannan haifa ta kalli amra tace ''ki shiga kiyi wanka mana, zamuje mu gaida abuh zai maki nasiha ne''..tashi tayi kamar wanda aka zarema laka ta wuce toilet, wanka tayi sannan ta dauro alwala ta fito da brown towel din haifa mai laushi, anatse ta gyara curly gashinta wanda ya nannade sosai, cikanshi yasa dakyar take parking don tunda akayi mata wannan special treatment a spa da haifa ta kaita yasa gashin ya kara habaka sosai. Anatse ta wuce dresser tadan feshe jikinta da turaren haifa masu kamshi sannan ta juyo ta kalli haifa wadda tasa wata doguwar riga orange ta haskata sosai, rigar tayi`matuqar amsar ta, ''haifa kinga saida nace maki muje apartment dina na dauka kayan sawa kika qi, kika ce sabbin zan sa''..kallonta haifa tayi sannan ta jawo package din ta bude ta zaro wata milky doguwan riga, wadda tasha stones red, rigar har taso ta fi wadda tasaka jiya tsabar kyau, gashi sai wani kamshi bakhoor take, karasowa haifa tayi gabanta sannan tace, ''yanxu dai mubar maganar kayan nan ungo wannan kisa, kina matsayin amarya zaki saka tsoffin kaya, no noo… bazai yuwu ba ''…kallon rigar amra tayi sannan tace ''toh yanxu wannan rigar kikeso na saka muna shirin bacci''…kallonta haifa tayi sannan tace ''gurin abu zamuje kin manta na fada maki zai maki nasiha''..jin haka yasa amra ta amshe rigar, da taimakon haifa ta saka rigar….wooo masha allah, dakyar haifa ta dauke idonta akan amra tace ''masha Allah habibty, you look so stunning''..murmushi kawai amra tayi don tasan haifa akwai zuzuta abu, amma itama kanta data kalli kanta ajikin mirror tasan tayi wani irin kyau sosai, da taimako haifa ta saka sarkan kayan shima mai ratsin red, da dankunne sannan haifa ta nadaa mata mayafin sai ta fito kamar black Arabian, batayi kwaliyya ba amma fuskanta wani annuri yake sosai.wani dan flat shoe haifa ta bata ta sanya a kafafunta da suka sha dan red wine henna kadan. Kamo hannunta haifa tayi suka sauka qasa har main parlor na abuh, suna isa gabanshi suka zauna, basu ma lura da hammam dake zaune gefen shi ba don zuwanshi Kenan ko kiran haifa baiyi ba suka hadu da abuh ya dawo daga masjid,nan suka gaisheda da abu sannan ta dago suka gaisa da hamman, ita amra gashe sa tayi kafin abu ya soma Magana ''Alhamdullah, I'm so happy for you amra, may this beautiful knot last longer that we expect,''..godiya amra t tayi mashi sosai akan karamci da yayi mata sannan yace "kudin sadakin ki yana wajen mijinki don mu anamu aladar miji ne zai bama matarshi da hannunshi ranar farko data kwana a gidanshi" godiya sosai amra tayi mashi Harda yar kwallarta kafin suyi mashi sallama.

Futowa sukayi atare hammam ma yayi sallama da abuh sannan suka wuce, ganin ba hanyar stair zasuyi ba yasa amra kallon haifa tace ''ina kuma zamuje yanxu''..kallonta haifa tayi fuskarta dauke da murmushi tace ''hammam zai kaimu shan ice cream na fadi ma abu karki damu''..jin haka yasa amra bata bi ta kanta ba suka sa kai suka fuce, saida suka jira maids suka sauko da boxes din da haifa ta shirya kayan da suka sayo aka saka a boot din hammam kafin suka wuce, wanda duk wannan hayaniyan amra bata sani ba don ddanna wayanta take don trying number da salima ta kirata dashi wanda har lokacin a kashe yake, addua kawai ta soma yi don wani irin fargaba ta dunga ji sosai har suka kama hanya maidan nisa, tuni bacci ya kwasheta don ita ma'abociyar son bacci ce sosai. 71-72 Suna isowa haifa ta zagaya bayan seat ta bude don ta tasheta, anatse ta soma bude cute idanunta ashagwabe tace ''haif..gaskia wurin ice cream dinnan da nisa, mu koma gida inajin bacci sosai''…kallonta haifa tayi tace ''stop doing this cute face of yours and come down''..babu musu ta fito da kafafunta, wani irin sanyi ne ya buge ta, kallon building din ta soma yi, wajene babba sosai ga tsayi, ko ina na compound din flowers ne, ga wajen babu ko digon datti, sai tsirarrun mutane dake tafiya suna komowa harda masu yin jogging da running, wurin is so peaceful babu hayaniya. hammam ne ya futo daga cikin motar ya yi masu jagora, anatse ta fara takawa har suka shiga cikin building din apartment din, ko ina tsaftsaf, shuru amra tayi tana kallon wurin don ya burgeta don kwata kwata bai kai apartment din da take ba ko kadan, wannan daga gani upgraded apartment ne wanda yaci uwar nata, anatse suka hau lift su uku sannan hammam ya danna 7th floor,, suna isowa suka suka fito gaba dayan su, tafiya suka danyi mai nisa kafin tsaya gaban kofan da aka rubuta house number 55, anatse hammam ya soma dannan wasu pins jikin kofar sannan ya bude, tsayawa amra tayi tana muzurai, saida haifa ta jawo hannunta suka shiga, ko'ina haske wal wal, acikin apartment din, saida suka wuce walk way sannan suka karasa cikin sitting room din da kal kal yake, zama sukayi akan L shape chair din sannan hammam ya juya ya wuce ciki,cikin master bedroom din ya shige kai tsaye ko'ina dim babu haske hakan ya tabbatar mashi da yayi bacci already, baiyi kokarin tashinsa ba ya rufo mashi kofan sannan ya fito, yana fitowa yaji karar bell, anatse ya wuce ya bude kofan, nan helper din apartment din ya shugo da boxes din, nuna mashi wajen gaban sitting room yayi ya aje sannan ya rufe kofan bayan ya fuce, anatse ya kalli haifa sannan yace ''we've done our job so let's get going ko''…jin haka yasa ta miqe amra ta miqe itama, kallonta haifa tayi sannan tace ''habibty ya naga kin miqe, koma ki zauna, ay gidan mijinki muka kawo ki, kin manta dole ku zauna gida daya, so mu munyi namu, yanxu kune zakuyi abinda ya kamata, please amra karmuyi wani jayayya kinfa san komai so please just get back to your seat mu zamu wuce ''..bude baki amra tayi galala tana kallonta, abinma ya daure mata kai, ta kasa gane me taqa mai mai haifa ke nufi, har suka saka kai suka fice ta kasa koda motsawa, anatse tabi kofar da suka rufe da ido sannan ta fara bin apartment din da kallo, yanxu Kenan dole ta zauna da wannan mutumin da bata san waye shi ba, bata san halinshi ba,anatse ta koma ta zauna kan couch din ta doka uban tagumi, tunanin kanneta ta fara, chan siraren hawaye suka fara zarya a fuskarta, tausayi kanta take da kannenta, tunanin shin yaushe wannan matsalar tasu zata kare take, kodai basu da rabo ne agidan duniya, da wannan tunani bacci barawo ya kwasheta anan kan couch din.

Wajen karfe hudu na dare ta farka afurgice, wani irin ciwon mara ne ya taho mata gadan gadan, afurgice ta sakko kasan kujeran, runtse ido tayi hawayen wahala suna zubo mata, ahankali bayanta ya fara riqewa kamar zata zauce tunawa da maganinta yana chan apartment dinta yasa ta fashewa da wani matsanancin kuka mai ban tausayi, da sauri ta daddage ta miqe da kyar ta fara laluben hanyan kitchen dake hade da sitting room daga gefen corner row, kitchen ne tsaf harda kitchen island daya raba tsakanin parlor da kitchen din, anatse ta matsa gaban smart dispenser kusa da fridge freezer,neman cup ta fara yi, juyawa tayi ta hango glass cup da glass jug akan island, anatse ta jawo cup din ta fara deban ruwan zafi daga dispenser din, ahankali ta soma sha dukda yana kona mata baki, haka tasha wajen cup uku na ruwan zafi tana hawaye, ahankali ta soma jin relief din ciwon, saida ta dan ji maranta ya gasu da ruwan zafi ta samu ta lallabo ta karaso har can L shape chair din parlor, ganin zufa ya tsatsafo mata dukda ac dake aiki acikin parlor yasa ta saurin zame veil din data yafa, ahankali tayi rub da cikin kan kujeran tana furzar da nunfashi mai wahala, saida ta dauka kusan awa guda tana juyi kafin ta samu bacci ya dauketa. Lokacin sallan asuba nayi ya bude idanunshi, ahankali ya lumshe idanun nashi wanda sukayi lum lum kamar wanda bayason budesu, anatse ya fara karanto adduoi kafin ya yaye lallausan blanket din daya rufe jikin shi dashi, black and white pajama's ne ajikinshi masu santsi, anatse ya sauko da fararen kafafunshi masu kyan gani sannan yayi yar miqa, ya wuce toilet, wanka yayi don shi ma'abocin wanka ne sosai, sannan ya futo daure da farin towel dinshi, a gaggauce ya sanya jellabiya fara sannan ya shimfida karamin Turkish carpet din sallah, ya fara raka'a tainul fajr, kafin ya tada sallah fajr,anatse yake ibada ya dauka wajen awa yana azkar kafin ya miqe ya cire jallabiyan ya kwanta da shorts dinshi fari kal.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull