Kenza eBookz

Auren katin kasa complete - Chapter 8

Auren katin kasa complete - Chapter 8

Auren katin kasa complete Chapter 8: Auren katin kasa complete Chapter 8. Karfe 9 daidai ya tashi bakinshi dauke da salati sannan ya wuce toilet, saida…

4,812 words

Karfe 9 daidai ya tashi bakinshi dauke da salati sannan ya wuce toilet, saida yayi wanka yayi brush sannan ya futo daure da wani towel din white, wanda ya dan wuce mazaunan shi, hannunshi kuma rike da dan karami, wanda ya kaishi fuskanshi yana goge sajen shi wanda yasha mayuwan gyara. Karasawa yayi gaban katon mirror dresser din ya bude gaban dresser din ya fara futo da mayukan shafawan shi, anatse ya soma shafawa har yazo kan body sprays dinshi masu sanyin kamshi, budo kafar dakin da akayi ne ya sashi tsayawa daga shafa wani oil mai kamshi da walki a sajenshi, dan juyowa yayi yana kallonta, amra wadda ciwon maran ne ya kara farkar da ita daga wahallen baccin data samu ya dauke ta ne, ta rasa yanda zatayi gashi tana son zuwa toilet don wani irin futsari ne ya matsota sosai, gashi tana jin yanda ta fara staining dukda bai fito a riganta ba, afurgice ta fara duban parlor ko zata samu toilet ganin babu guest toilet yasa ta saurin bude dakin data gani daga gefe kawai ta fada ba tare da tunanin wani abun ba. Ganin mutun atsaye ya bata baya sanye da towel, iya gwiwa wadda iyakacin towel din kasan kwankwaso, ga faffadan bayanshi a bayyane da gashi lub lub a kwance kamar na jariri ya sata sauri komawa da baya tana gwalo ido harta rufe kofar bata ankare ba juyowa yayi yana fuskantarta, da sauri ta kawar da kanta, jikinta sai faman kyarma yake yi kamar wadda aka kama tayi laifi, da sauri ta soma tattaro kalaman bakinta tace ''I'm sooooo….so..rry wallahi bansan da mutun acikin dakin ba''..tana kaiwa nan ta juya har fuskanta na buguwa da kofan sannan ta saka hannu da sauri ta bude kofan ta fuce kamar iska, don tsayuwan nan datayi da yanda yake kallonta qiris ya rage batayi futsari a tsayen nan ba. Shiko amar mamaki ne yagama cikashi, yaushe tazo,me takeyi a cikin gidan shi, don shi bashida masaniya akan zuwanta, sanin babu wanda zai bude mata kofa koya bata pin sai hammam yasashi saurin wuce wa gaban bedside ya lalubo wayan shi ya soma budewa, ganin message din hammam ya sa yayi saurin budewa ya fara karantawa ''dude we came to your house last night naga kayi bacci, mun kawo maka bride dinka ne so enjoy your honey moon and remember yarjejeniyar nan, dole ta zauna tare dakai.'' Yana gama karantawa ya wullar da wayan yana furzar da huci mai zafi, shifa wannan takura ne awajen shi, ya za ayi ya zauna gida daya da mace, macen ma wannan yar abar salon ta gama rainashi, gashi shifa baya son sharing komai, dole ma kawai ya bar mata gidan ya koma penthouse dinshi, saida yagama tunane tunanen shi kafin ya wuce wajen glasswardrob dinshi na dakin ya bude ya fiddo kayansa riga da wando ash, rigar mai buttons ce, wandon kuma daga kasa wajen kafanshi mai kamawa, kayan kana gani kasan designer ne basai an fadaba, anatse ya shirya tsaf ya feshe jikinshi da turaren shi mai kamshi sannan ya zari wayanshi ya futo daga bedroom din, koda ya futo kallo daya ya mata don bedroom din yana facing sitting room, tana nan araqube kamar wadda tayi sata aka kamata, motsin kirki ta kasa tunda ya futo, kamshinsa ne ma ya fara kai mata ziyara, da sauri ta rumtse idanunta ta tamke throw pillows dake gefen kujeran, bai ma bi ta kanta ba ya wuce wajen kitchen island, anatse ya jawo glass jug din wajen da glass cup din ya deba ruwa daidai ya kai bakinshi anatse yaji muryan ta a dodon kunneshi "Good morning" saida yagama shan ruwan sannan ya juyo ya mata kallo daya suka hada ido tayi saurin sauke nata, tabe baki yayi sannan ya aje cup din ya wuce hanyar fita baiko bi takanta ba balle tasa ran zai amsa mata gaisuwan nata. Saida ya futa ta samu ta sauke wata nauyayyiyan ajiyar zuciya da numfashi, har tana shafa kirjinta dake bugawa pat pat, tashin hankali, wannan wani irin tsoro take ma mutumin nan, lokacin daya futo har cikin zuciyarta take jin takunshi har ya wuce wajen kitchen island, anatse ta sauke kanta wasu siraran hawaye na zubo mata, sai yanxu ma take tunawa dalilin shigarta dakin, wani irin zabura tayi, nan take futsarin ya taho gadan gadan, da gudu ta mike ta kama hanyar dakin, saida tazo daidai kofar kirjinta ya fara bugawa, har yanxu wajen kamshin sa yake kamar yana wajen, runtse ido kawai tayi ta fada cikin bedroom, bata ma tsaya kallon dakin ba idonta ya sauka akan wata kofa daga gefe, da sauri take takowa kafanta har hardewa yake, ga murdawa da cikinta keyi, da sauri ta bude kofan ta shiga ciki, bata ma tsaya duban dakin ba saboda yanda futsarin ya matsota sosai,tana shiga ciki ta soma tube kayan jikinta, saida tayi futsarin tukunna ta samu sauqi, ahankli idonta ya sauka kan wc din, duk jini ya bata hankali atashe ta karasa sabule kayanta, saida ta fara wanka a shower din, ahankali ta dunga bin gaban shower nashi da kallo, wasu hadaddun shower gels ne ajere kusan guda goma, kowanne brand daban daban janyo wani lavender gel tayi ta fara murzawa ajikinta, ahankli ta lallaba ta gama wankan sannan ta wanke mashi wajen data bata tass,neman abun da zata daura ta farayi kafin idanunta suka sauka kan towels dinshi wanda suke ajere jikin hanger kusan guda biyar, kawar da idanunta tayi daga wajen ta maida rigar ta sannan ta futo, fucewa tayi daga dakin gudun karma tayi wani abun da zai jawo mata Magana. Ahankali ta koma parlor ta bude kayan da haifa ta hado mata wanda suka sayo,budde box din tayi ta samu wata decent English gown mai kyau ta saka sannan ta samu waje ta zauna ta rabka uban tagumi, wayarta dake gefe ta jawo charging ma ya kusa sauka, duba location din da take tayi sannan ta shiga 24 hour online shop tayi ordern pads da sabbin toothbrush harda maganin pain killer, zaman kusan awa guda tayi kafin ordern ya iso,kafin ta tashi ta bude kofan don ganin house number na gidan kafin ta fada ma delivery man din, bayan yan mintuna kadan sakonta ya iso, koda ta bude kofan anan gaban kofanta taga delivery din, anatse ta jawo box din ta bude, ta fiddo komai ta koma dakin nashi, toilet din ta koma sannan ta sauya pants dinta wanda yagama baci sosai, tana gama kimtsawa ta gyara mashi toilet din ta fito, zama tayi a parlor ta sha maganin, nan take bacci yayi awon gaba da ita. Amar kuwa yana fita ya wuce penthouse dinshi, yana sauka ya wuce cikin main entrance din, kamar kullum gidan yana nan fess fes sanin shi ma'abocin tsafta ne yasa Pablo ke qoqari sosai wajen gyara ko'ina,wajen dining ya wuce don wata yunwa ce ta ciyo shi sosai,kujera ya ja ta luxury dining set chairs din ya zauna, fitowa Pablo yayi hannunshi dauke da wasu tsadaddun warmers masu kyan gaske, ganin oganshi yasa ya sara mashi sannan ya fara serving dinshi abinci, saida ya gama tsaf ya zuba mashi coconut drink mai sanyi sannan ya koma wajen aikin sa, anatse ya soma cin abinci, kusan rabi yaci don bai samu yayi dinner ba ya kwanta kwanan jiya, anatse yake cin abinci kamar wanda baison ci, saida ya gama ya jawo savage ya goge bakinshi kafin ya miqe ya wuce lift, yana shiga yayi resting kanshi ya danna floor din part dinshi, sama ya wuce bedroom dinshi, yana shiga nanma fessfess sai kamshin freshners mai dadi,gaban light switch ya karasa ya maida light din dakin zuwa dim, kwata kwata kwanakin ya rasa mey zaiyi tunda suka samu hutu karshen shekaran nan, anatse ya wuce closet ya chanza kayanshi zuwa masu sauqi, dan short ne da farar armless top,yana gamawa ya dawo ya zauna gefen gadonshi ya dafe kanshi, duk wannan abin auren yana tariyowa akanshi, yanxu shi aure yayi bada sanin Ammah ba dukda auren ba wai auren dindin din bane, amma dai still aure baa bin wasa bane don yana da ilimi, amma bayajin zai iya fada ma ammah dalilin yin haka, sbd bazata taba jin dadin yin aurenshi ta wannan hanyar ba. Dafe kanshi yayi wanda ya soma mashi zafi, sai yau tunanin dada yake dawo mashi kanshi ''amar ka kula min da Amman ka, komai ka gani arayuwar nan yana da dalili, ciki kuwa harda mu gaba daya, duk wandaka ganshi haka, ba haka allah ya barshi ba, kayi kokari ka zama mutun na gari, mai tausayin alumma, ka zama gatan marayu karka bari ayi rashin adalci agaban idonka.''… dago kanshi yayi yana kallon sama, idanunshi sunyi jaa sosai, ahankali ya kwanta bacci yayi awon gaba dashi. Amra kuwa bacci ne sosai ya dauke ta sai wajen asr ta farka, shima wata masifaffiyar yunwa ce ta farkar da ita, ahankali ta tashi ta koma dakin ta sake wani wankan ta futo, sai alokacin tayi ma toilet din kallo mai kyau, komai fes fess kamar ba'a taba amfani da wajen ba,kana ganin designer towels dinshi zaka san yana da bala'in tsafta da gayu, futowa tayi sannan ta tsaya tsakiyan dakin, dagakan gadon zuwa couch din dakin zuwa ga bedings din tabi da kallo, ahankali ta furta ''masha Allah''..murmushi ne ya kubuce mata, arayuwar ta tana kaunar taga komai organise kuma mai kyau, haka yasa ta shagala sosai wajen kallon ko'in ganin kamar gadonshi yana buqatar gyara yasa ta karaso gaban gadon, ta gyara shimfidar, wani irin kamshi ne ke tashi mai sanyaya zuciya, saida ta gama tukunna ta futo ta koma parlor, kayanta ta kuma sauyawa zuwa masu sauqi, zama tayi ta lalubo wayanta ta soma yin ordern abinci, pasta tayi order aka kawo mata taci sannan ta kwanta tana tunanin rayuwa da su salima.

Dare nayi wani irin tsoro ya dirara mata, kwanan gidan da bata tabayi ba babu mutane, afurgice ta miqe ta fara zarya, jawo wayarta tayi ganin charging ya sauka sosai yasa wasu siraran hawaye suka fara yi mata zarya, tama rasa yanda zatayi, tunanin kodai ta koma gida ne ya fado mata, ganin har wajen karfe goma yasa ta yanke shawarar tafiya kawai, ahankali ta jawo wayanta ta soma requesting mota, bata kaiga gamawa ba wayan yamutu dipp, kuka ne kawai ya kubce mata, yanxu dai bata jin yinwa amma ya zatayi idan wani abu ya faru da ita, ahankali ta koma ta zauna, har wajen karfe sha biyu idonta kwal babu mai gidan babu motsi ko kadan, tsoro ne ya dirar mata, tabbas lokacin da take apartment dinta ita kadaice amma yanxu ta rasa dalilin da yasa take jin tsoron nan, ko motsin mutane ba a ji, ganin babu sarki sai allah yasa kawai ta samu waje ta kwanta nan kan couch din har bacci ya kwasheta. Amar kuwa bai tashi ba shima sai gab da sallar magrib, yana tashi ya wuce toulet ya dauro alwala sannan yayi sallah yana idarwa ya jawo laptop dinshi ya fara aiki, bashine ya aje laptop dinshi ba sai wajen karfe daya, anatse ya tashi ya aje laptop din ya jawo landline din dakisnhi yayi dialing wasu numbers, Pablo yana daga wa yace"yes sir," lumshe kyawawan idonshi yayi wanda lashes din sukayi zara zara sannan yace ''bring me coffee''..aje landline din yayi, bayan yan mintuna pablo yayi knocking, kamar bazaiyi magana ba yace ''come in'' …anatse Pablo ya shugo ya aje mashi gaban side stools dake kusa da couch din bedroom din parlorsannan ya fuce.

Ahankali ya sauko ya ya zauna kan couch din, tunani iri iri aranshi, yanxu damuwan shi daya yanda zaiyi ya kawo karshen wannan empire din, sannan abinciken da yake akwai mutane da dama dake son ganin bayanshi dukda shi wannan ba matsalar shi bace he has ways of saving him self amma mutane fa da yayi swearing saiyayi protecting dinsu, sipping coffee din yayi, gaba daya ranshi adagule yake, ajewa kawai yayi ya wuce toilet don ya watsa ruwa, bayan ya futa pjs dinshi ya sauya sannan ya kwanta. 73-74 The next morning… Amra kuwa bata tashi ba sai wajen karfe goma, anatse ta tashi tana bude kyawawan idanunta kafin tayi adduar Tashi daga barci ta mike gaba daya ta wuce cikin bedroom din,sadaf sadaf ta bude kofan don duk a tunaninta ya dawo tana bacci, batayi gangancin kunna light din dakin ba ta wuce bathroom, agaggauceta fara yin brush, kafin ta zame kayan jikinta ta fara wanka, anatse ta fito daga shower sannan ta jawo rigarta ta maida tsayawa tayi ta soma bin bathroom din da kallo, very clean fess fess kamar ka zuba abinci akasan kaci, ga wajen wc din ma abin kallo ne, da wash hand basin din, yanda ya jera kayan wankanshi gwanin burgewa, yauma bata taba komai nashi ba in banda shower gels dinshi, anatse ta futo sannan ta sulale ta bude kofan dakin ta fuce, tana karasowa sitting room ta janyo boxes dinta tare da budewa, wajen bras da pants ta bude ta zaro wata hadadden cup bra da pant masu shegen kyau ga laushi, kana gani kasan masu quality ne da kudi sosai, ajewa tayi agefe sannan ta bude wajen mayuka ta dauko wanda zata fara amfani dashi dasu perfumes da body sprays, anatse ta fara shafawa tana karema sauran kayan kallo, saida ta gama sannan ta bude na kaya, wata abaya ta jawo mai kyau sosai hade da veil dinta purple color,cikin natsuwa ta shirya ta rufe boxes din ta janye su gefe, zama tayi don tunanin yanda zatayi gashi yunwa ya fara damunta, ga wayanta ya mutu bare tayi order, anatse ta tashi ta taka Har wajen kitchen, ko ina tsaf tsaf kamar ba'a taba amfani dashi ba, karema wajen kallo tayi sosai , dan kitchen ne daidai mutun daya, babu wani girma sosai, babban gas plate ne awajen sai dishes washer sai microwave da oven a hade cikin yar cupboard sai fridge freezer a hade shima babba sosai wanda har yaso ya wuce tsayinta, daga gefe kuwa wani sako ne da manya manyan shelves na pantries, anatse ta shiga, babu wani kayan girki na kirki,rasa abunyi tayi ta fara duba ko'ina ganin madara da hot chocolate da cereal yasa tayi saurin jawosu, harda zuma, kitchen ta koma ta fara duban cups, bude upper drawer ta fara yi ta dakko katon bowl da spoon, saida ta wanke kafin ta aje akan island sannan ta zuba madara yanda zai isheta da zuma da dan ruwa, gaba daya pack din cereal din ta kinkimo ta dawo kujera ta zauna ta fara hadawa, hannu baka hannu kwarya ta dunga turawa dake yunwa ta ciyota dayawa sai ya mata dadi sosai, dakyar ta shanye donta hada da yawa sosai, anatse ta miqe ta wanke bowl da spoon din sannan ta maida sauran ceareal din da madaran kafin ta dawo parlor ta rabka uban tagumi, gashi babu cash ajikinta da saita tafi gida kawai, ganin kuma hakan bai daceba idan tabar mashi gida abude yasa kawai ta zauna tana tunani kala kala har wani baccin wahala ya dauketa anan zaune.

Dai dai karfe uku na rana karar bell ya tada ta daga bacci, afurgice ta miqe don duk tunaninta mai gidan ne ya dawo, ahankali ta karasa gaban door din ta fara kokarin budewa, dake kofar is smart ajikin screen din gaban holder din taga wanda yake knocking, da sauri ta bude taja da baya kadan, da sauri haifa ta gifta gaban hammam ta shugo tana rungume amra tace ''babeeee nayi missing dinky, amarya how are you my dear?'' rungumeta tsaf amra tayi tana murnar ganinta, hammam kuwa kallo daya ya musu ya wuce ciki zuwa bedroom, bude kofar dakin yayi ganin wayam yasa ya tsaya ko zaiji saukan ruwa jin shuru yasa yayi saurin futowa yace ''baya gidan ne?'' sai alokacin amra ta kalleshi tace ''good afternoon ''..jin haka ya sashi yi mata murmushi ya sake tambayan dazu , shuru ta danyi tana nazari kafin tace, ''yau 2days baya gidan''..jin haka yasa hammam saurin cewa ''whatt ke kadai kike kwana anan?, abinci fah?'' duk atare ya jero mata tambayoyin, batako kalleshi ba tace ''inashan cereal ay, and besides badan wayana yamutu ba da dashi nake order,''…shuru kawai yayi sannan ya kalli haifa yace ''babezz bari na danje wani wuri zan dawo bada jimawa ba na dauke ki, yana kaiwa nan ya barsu zaune kan couch ya fuce. Juyowa haifa tayi sannan tace ''kai wallahi wannan mutumin anyi baudadden mutun, wai maima yake nufi kamar ba taimake ni in taimakeka bane wannan yarjejeniyar, I just hate mutun mai yawan ego,''..tana kaiwa nan ta miqe tace ''bari naga gidan naku best girl''..zagayawa sukayi ko'ina kafin su dan gyagyara ko'ina, daman gidan ba wani datti yayi ba. Kallon haifa amra tayi sannan tace,''babe muje gidana mana kafin hammam din naki ya dawo, inason daukan abubuwan buqatu na''..jin haka yasa haifa cewa to muje saidai kinsan bansan password din gidan ba but I will text hammam yanxu sai muje mu dawo kafin ya dawo. Atare suka futo daga gidan, sai yanxu amra ke ganin kyan wajen, wato apartment ne duk yawanku zai iya occupying dinku, don akwai apartment din room biyar, da mai room uku, daidai yanda kake so, anatse suka sauka ride din da haifa tayi requesting ya karaso, saida sukaje gidan amra suka kwaso kayan amfaninta sosai, wanda daga charger sai yan mayukanta da wasu kayan sawa sannan suka fito saida suka tsaya suka saya pizza da burger da Oreo smothies sannan suka kama hanyan dawowa wajen karfe 7 na dare.

Hammam kuwa Yana futowa ya wuce penthouse din Amar yana zuwa gidan ya wuce dakinsa direct, nan ya tadda amar kwance ,tashinsa ya soma yi yace ''dude wake up tashi akwai wani aiki da zamuyi a headquarters yanxu" Tsaki kawai Amar yayi don Hammam ne kawai ke iya yi mashi hakan don baya son Ana interrupting barcin sa, baice mashi komai ba ya mike zuwa bathroom saida amar yayi wanka ya shirya hammam na zauna na jiranshi kafin suka fito atare, nan yasa m-5 ya buyoshi da motorn shi don zasuyi partings ways da hammam idan sun gama da headquarters, ajere motocin suka tsaya acikin parking space na headquater, anatse suka futo gwanin burgewa, amar na sanye da jellabiya white kundura shima dai hammam casual dressing dinne jikinshi, ciki suka shiga wanda yawancin mutanen wajen yan apartment din dake cikin hedquaters ne wanda suke zaune da iyalansu ko su kadai, ciki suka shige inda ake private meeting na manya manyan seniors officers, zama amar yayi suka fara introduction akan private meeting din wanda is professionally private kusan awa uku suna cikin meeting sai wajen karfe biyar suka fito suna fitowa hammam yace ''inason magana dakai amar, ko zamuje office dinka'' anatse amar yayi leading hanya har suka isa office din amar, zama suka yi a kujerun guest kafin hammam yayi gyaran murya yace ''amar I thought you're matured enough but as for now I don't see that anymore, what's wrong with you ne dude?, munyi maganar nan ba sau daya ba, duk a tunanin na you understand what's going on here, Amma da alamu baka gane ba''…shuru yayi yana kallon amar dake kallonshi kamar yaga tv, yama rasa ina zancen hammam ya dosa, lumshe idanunsa yayi ya bude alamun bashida energy yin jayyay da hammam hakan yasa yayi saurin cewa ''you have to talk fah, bazakayi shuru ba, inason nasan dalilinka na acting this way,idan har bazaka taimaki yarinyar nan ba, ay da baka bari munkai har iyanxu ba,.'''……..nunfasawa hammam yayi sannan ya cigaba, ''waima tsaya, ka manta mai nace maka ranar ko, kai baka san kai zata taimaka ba, because taimakon da zatayi maka dukda nasan bata sani ba don wayon da muka masu na qin fada masu, yarinyar nan yarinya ce, marainiya ce, bata uwa bata da uba sai wan mahaifinta wanda he's wicked, bari kaji na fada maka, wannan abun da yarinyar nan take na neman citizenship wato katin kasa bawai don son zuciyarta zatayi hakan ba kodan ta zauna anan, no its because tana son taimakon kannenta wanda suke zaune wajen wan mahaifin nasu, rayuwar wulankanci ta fuskanta achan gidan har allah ya kawo nan, basu da kowa, itama kanta scholarship ta samu tazo nan din, ko kasan cewa upkeep dinta da uncle din nata ke bata saita biyashi don yace saitayi hakan inba haka ba cikin will dinsu zai dauka wanda shi kadai mahaifinta ya bar masu ita da kannaneta, …''ýa karashe da dan fada, lumshe ido amar yayi ya kwantar da kanshi jikin seat din zuciyan shin a mashi wani iri, anatse hammam ya cigaba, ''this girl needs katin kasar nan don ta kawo kannenta nan kusa da ita, which gaba dayan su ma basu cikin issashiyar lafiya, haba amar be matured mana''…jin haka yasa amar saurin bude idanunshi kan hammam yace ''do I look like I care about problems dinta, please I don't have time for this''..yana kaiwa nan ya miqe, da sauri hammam ya tsaidashi wajen cewa ''shin baka jini da kyau ba Kenan, YARINYAR NAN MARAINIYA CE, na dauka kafi kowa sanin rayuwar marayu yanda take kasan cewa dan you're one of them''..tsayawa chak amar yayi tunanin maganganun dada ya fara dawo mashi cikin brain dinshi ''my dear son duk inda kaga marayu ka taimaka masu please, guide them and protect them''….runtse idanunshi yayi wanda sukayi jaaa, jijyoyin kanshi duk sun fifito alamun ranshi abace yake, da sauri ya mike yasa kai ya fuce gaba daya daga building din, gaban motor shi ya tsaya sannan ya umarci m5 daya bashi key din motor shi, yana karba ya fuce bai tsaya ko na ba sai bar din da ya saba zuwa, kamar kullum tsaftaccen private loung aka bashi ya zauna yana jin kanshi na sauka, zaman kusan minti talatin yayi kafin ya jawo wayanshi ya fara dialing Ammah, anatse tayi picking da sallama abakinta ''hey son, ya kake ya aiki?'' anatse ya sauke wata nauyayyiyar ajiyar zuciyaa yace ''Ammah na I missed you so so much'',…jin hakan yasa ta tabbatar yana cikin damuwa, anatse ta soma yi mashi nasiha, kan ya rage sama kanshi damuwa sannan ta tambaye shi matsalan shi ''Amma babu wani matsala kawai na tuna da dada ne'' ya bata amsa…jin haka yasa tace ''idan ka tuna da mahaifinka addua zakayi mashi bawai kasa damuwa aranka ba, kasan he's up there and he's proud of you I'm sure of that, yaronshi is successful, yaronshi yana daya daga cikin masu taimakon alumma, you've helped the uae government and the record is there, bama su kadai ba, you've contributed a lot to your nation also, allah yayi maka albarka, kullum ina maka adduar samun nasara aduk inda kake da abubuwan da kake yi, I will always be proud of you son, allah ya baka mata ta gari ko bayan raina zata kula dakai sosai son''…..ba karamin kwantar da hankali kalaman ammin shi suke sashi ba, anatse yayi mata godiya sannan sukayi sallama, kallon wayan yayi kamar bazai danna ba sannan yayi dialing wata number ya kafa akunnenshi, ringing biyu aka dauka anatse ya soma Magana ''Hello james, whats up with the research?'' Magana akayi daga chan bangaren, saida ya nutsu kafin yace ''doesn't matter just send me what you've got, dukda haka ka cigaba sosai, da digging wasu imformation din akanta, yanxu ka tura min through email dina''..yana kaiwa nan ya kashe wayan yayi resting kanshi, kallon non alcoholic drink din da aka kawo mashi yayi sannan ya dan yi sipping yana latsa wayan shi, da sauri ya dannan email dinshi ganin message ya shugo sannan ya bude, shiga cikin document din yayi hoton amra ne ya futo da uniform din school din lokacin graduation kayan sunyi mata kyau sosai, tayi smiling har dimple dinta guda daya ya futo cute kananun hakoranta sun bayyana gwanin burgewa, samun kanshi yayi da kallonta tsaf daga sama har kasa, don atsaye akayi hoton, kallon dogon wandon jikinta yayi yanda hips dinta ya cika wandon har kana iya hango yanda shape dinta ya yi curvy da tiny waist dinta, da sauri yayi sliding jin abu na tunkaroshi ya watsar da tunanin sannan ya bude next page, sunanta ya gani complete Aisha Badaru (amra) 21 years, born and raised in Abuja and kano, anatse ya fara karanta tarinhinta da na kannenta da rayuwar da sukayi da mutuwar iyayensu lokacin da suka mutu, da rashin lafiyar da kanninta salim yayi da yanda ake banbanta su cikin yayan uncle din, da yanda shi uncle sun ke treating dinsu babu abunda ba a rubuta ba kaf saida ya gama karanta komai, ammam abu daya ne ya bashi mamaki, wajen mutuwar iyayen su, a binciken da james yayi iyayensu are not declared dead kawai an rubuta accident that causes them burning to death, anatse yagama karantawa sannan ya sake kiran james yace''I need everything I mean everything about her family don't let go of anything even if its an index finger of her's okay'' yana kaiwa nan ya kashe ya fuce daga wajen, lokacin it's around 9 na dare, har ya kama hanyan zuwa penthouse dinshi wani tunani ya zo mashi ya yi corner ya wuce mini apartment dinshi,anatse yake drinking cikin kwarewa harya iso cikin compound din apartment din, wajen yayi shuru alamun kowa ya wuce cikin gidansa, parking yayi wajen parking space dinshi sannan ya futo ya wuce ciki,don agajiya yake, yana zuwa daidai kofan apartment dinshi ya saka pin ya bude, shigo da kafanshi cikin walk way din sitting room, yayi ya fara takowa majestically ko ina tsaftsaf sai karan ac dake tashi, bai tsaya kallon gefen sitting room dinba ya wuce gaban kofan bedroom dinshi, wucewa cikin bedroom dinshi yayi direct ya tako har gaban shoe rack dinshi ya aje takalmin shi sannan ya wuce gaban gafonshi ya aje wayan sa kan bedside drawer sannan ya soma cire kayan jikinsa domin yin wanka, saida ya tube komi ya rage daga shi saidan shorts dinshi sannan ya sa kai ya wuce bathroom din,anatse ya saka hannu kan handle din kofar bude, karaf idonshi ya sauka kan gadon bayanta da take kokarin saka towel dinta data taho dashi daga gida dasukaje tare da haifa, juyowanta Kenan idanunta ya sauka kan nashi, ta sauri ta ja da baya ta rafka uban qara, kawar da kanshi yayi daga kanta ganinta na neman faduwa gashi ta runtse idanunta ta juya mashi baya da sauri ya sashi takowa har gabanta yace ''keee''…jin kamshinsa ya sata jikinta karkarwa, burinta akwai ta fuce mashi daga toilet din,sbd wani irin kunya data dirar mata, batasan shiko tunda yayi mata kallo daya ba ya dauke kanshi,ahankali ya soma magana babu wasa ''get out of m…'' bata bari ya karsa bama tayi saurin juyowa don fucewa, da sauri ta runtse idanunta don dab suke da buge juna sannan ta gifta ta gefen shi ta wuce aguje, har kafafunta na hardewa, saida ta iso sitting room tukunna hankalinta ya soma dawowa daidai, bata taba tsammanin ganinshi yanxu ba don duk atunaninta ba yanxu zai dawo ba don harta dan saba da zaman ita kadai dukda yanxu ta matsu a dawo hutun shekara da akayi masu ah a asibitin da duka staffs. Zaman kusan rabin awa tayi anan zaune, tunanin kar su kara yin clashin yasa ta tuna babu kaya a jikinta sai towel, da sauri ta jawo boxes dinta ta nemo silk pjs riga da wando sannan ta saka, tsam suka zauna mata kuma sukayi mata kyau sosai, jawo hijab dinta tayi ta rage light din parlor to dim lights sannan ta kwanta ta lullba da hijab dinta,har barci ya fara fusgarta ta tuna da pizza da burger da suka sayo ita da haifa wanda bata ci ba,mikewa ta yi ta tashi ta wuce kitchen ta bude fridge ta saka a ciki, ta jera su yanda bazasuyi kankara ba sannan ta rufe fridge din, glass cup ta dakko idanunta na neman rufewa alamun bacci ya na fusgarta sosai, ta taro ruwan daga dispenser din a cup tasha kusan sau biyu, jin bai isheta ba yasa ta aje cup din tana taran wani idanunta a lumshe kamar mai layi, jin tsayuwar mutun abayanta da kamshi mai dadi ya sata saurin juyowa, dim taji kirjinta ya bata don bata yi tunanin ganin shi ba, ga kamshin sa duk ya bade kitchen din, kallo daya ya mata ya dauke kanshi yace ''get out of the way''.. da sauri ta koma baya zata aje cup din kafanta ya harde, saura kiris ta fadi, da sauri ta bashi waje ta bada gab sosai tsakanin su sannan ta tsaya gaban tap ta juya mashi baya ta wanke cup din, shiko baima bi ta kanta ba ya tsaya gaban fridge ya zaro bottle watter dake jere kusan guda goma, daya ya dauka ya wucewan shi cikin bedrrom dinshi, saida ta taji giftawarsa kafin ta juyo ta lallaba ta wuce ta kwanta ta rufe jikinta dakyau.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull