Kenza eBookz

Auren katin kasa complete - Chapter 9

Auren katin kasa complete - Chapter 9

Auren katin kasa complete Chapter 9: Auren katin kasa complete Chapter 9. Washe gari, ana sallan subh ya tashi yayi sallah, yana idarwa yayi azkar kafin ya…

3,824 words

Washe gari, ana sallan subh ya tashi yayi sallah, yana idarwa yayi azkar kafin ya koma ya kwanta, bai tashi ba har wajen kar 12, yana tashi yayi wanka ya shirya tsaf abinshi cikin riga da wando yana son zuwa gida yayi break sannan yana son yin workout don kwana biyu jikinshi yayi tsami sosai, yana gama shirinshi ya dauka wayan shi ya futo yana gyara wrist watch din hannunsa, anatse ya futo har wajen sitting room saida ya tsaya ya gama saka wrist watch din,yana nan tsaye daddaden muyar ta ta doki kunnen sa ''INA KWANA?''….baiko tsaya ya kalli inda take ba yace ''fine'' yana kaiwa nan yasa kai ya fuce abinshi. Saida taji karar rufe kofan da yayi ta sauke wani nauyayyan numfashi, daman ta qagu ya tafi donta samu ta gyara jikinta don period dinta ya tsaya, mikewa tayi ta wuce bedroom din, sanyin kamshinsa da na ac duk ya bade wajen, saida tadan lumshe ido kafin ta wuce bathroom tayi wanka tare da tsaftace jikinta sannan ta zumbulo hijab dinta ta fito ta wuce parlor, agurguje ta saka kayanta riga da wando masu kyau, wandon yana da fadi sosai kamar fela, akan kayan ta zumbula hijab dinta ta koma bedroom din, Gyaran da ba a sata ba ta soma yi, dauke laptop din kan gadon shi tayi ta aje kan center table din bedrrom din, kafin ta gyara mashi gadon tana gamawa toilet ta wuce nan ma dai ba gyara yake buqata ba amma haka ta gyara shi tsaf sannan ta futo ta wuce parlor lokacin har ayi sallar dhur saida ta idar kafin ta fara neman abinda zata ci, tunawa da pizza da suka sayo ita d haifa yasa ta dauko daga cikin fridge sannan ta saka a plate tayi microwaving tana gamawa ta debo ruwa a cup sannan ta samu waje ta zauna don babu ruwanta da daukan mashi ruwan bottles don tana ganin ya dauka jiya ta kauda kanta daga daukan Abubuwan shi don gudun kartayi laifi.

Tana nan zaune taji knocking, maida hijab dinta tayi ta mike zuwa kofar don ganin wanda ke knocking din, sanin cewa tabbas bashi bane don shi kai tsaye zai saka pin ya bude kofan, yasa tayi saurin budewa, ganin m-5 tsaye yasata saurin sauke kanta, da sauri yace ''good afternoon ma, dagowa tayi don ita kunya ma taji yanda yake gaisheta, anatse taje ''good afternoon sir,'' da sauri yace ''my name is m5, ga wannan oga yace a kawo maki'', kallon wani haddaen food packaging dayake miqa mata tayi sannn tasa hannu ta karbe, godiya tayi masa kafin ya wuce itama ta rufe kofar ta dawo sitting room ta kalli ledan, hadaddun packs ne guda hudu masu kyau, budewa ta soma yi don ganin abunda ke ciki,abunci ne sai buga kamshi yake,shuru tayi tana tunanin wanda yace ya kawo, ahankli ta furta ''noo it can't be him, wata zuciyar ce tace mata saidai hammam don shine ya tambaye ta maganar abinci jiya,'' ahankali ta lumshe idanunta sannan ta aje pizza din ta fara cin abinci atsanake.

Amar na kan thredmill dinshi jikinshi sanye da workout outfit na brand din under armour, fuskanshi duk yayi zufa don yayi workout sosai, wayan shi yayi ringing, da sauri ya sauka ganin m5 ne ke kiran, daga wayan yayi, daga chan bangare m5 yace ''sir nakai sakon, yanxu zan wuce, I will be back on Monday, and I've received the alert thank you so much''…''uhm'' kawai amar yace sannan ya aje wayan ya cigaba da workout. 75-76 Bangaren amra Ana kiran sallan asr ta mike, alwala ta dauro kafin ta fito ta wuce parlor tayi sallah, anan kan sallayan bacci ya kwashe ta.

Sai wajen karfe goma ya shugo gidan yauma, saida ya dan kalli gefen sitting room, kwance ya tadda ta lullube da hijab, ba a ganin komai nata sai hijab dinta,kauda kanshi yayi ya karasa cikin bedroom dinshi, ganin ko'ina tsaf tsaf ya sashi karasawa gaban gadon, kayanshi ya cire ya wuce cikin bathroom ya watso hot bath, saida ya gama yayi feshe feshen sa sannan yahau kan gado, ahankali ya fara laluben laptop dinshi, don yawanci yana gama aiki yake barinta kan gadon ganin bai gani kan gadon ba yasa ya miqe zumbur, da sauri ya sauko daga kan gadon don baima duba gefen couch ba, duba gadon yayi tsaf bai gani ba, azafafe ya wuce parlor, tana nan kwance rub da ciki kamar yanda ya shugo ya ganta, gadan gadan ya tsaya gabanta, hannunshi na cikin aljihun wandon sa, kamar karya tada ta, chan kuma yace ''keeee tashi''…ay kamar a dodon kunnenta ya ambaci kee din nan, afurgice ta tashi har tana fadowa kasa, ass dinta na bugun wooden tiles din kasan, ahankali ta fara goga wajen tace ''washhh bumm''…..bata karasa ba ta toshe bakinta ganinshi tsaye gabanta kamar zaki, wurwura idanunta ta fara, kamar wadda za a kama, jikinta harya fara kyarma, kaff kaff.. a dan zafafe yace ''did you touch my bed''…jin haka yasa ta dago da sauri ta sauke kanta kasa tace ''eh''…nunfasawa yayi kamar bazaiyi magana ba yace ''where did you keep my laptop''..hankalinta ne ya tashi don ita bata ma son wani laptop yake Magana ba, shuru tayi na kusan minti biyu, jin shurun yayi yawa yasashi saurin cewa ''I hate repeating my self''..da sauri ta dago kamar wadda ta tuna abu tace ''uhm dana gyara gadon ne saina aje maka akan center table''…tana kaiwa nan a dafe kirjinta kamar zai fado…kawar da kanshi yayi daga kanta yace ''don't ever touch my belongings again, ki tsaya a matsayinki, bana son rawar kai''..yana kaiwa nan ya juya ya wuce bedroom, anatse amra ta sauke ajiyar zuciya, wani tukikin baqin ciki ya tsaya mata a rai, maima ya dameta da harkarshi da har take gyara mashi gado, gashi yanzu ya gaya mata Magana akan tayi abin arziki, share hawayen ta tayi sannan tayi kwanciyanta. Washe gari tun karfe biyar ta tashi, tanason shiga toilet tayi futsari da alwala ta kasa shiga bedroom din sbd tana tsoron mai zai kuma ce mata, ganin wajen karfe bakwai yasa ta miqe sadaf sadaf ta bude dakin, ganin dakin is dim gashi ko'ina arufe babu haske yasa tayi tunanin ya koma bacci, ahankali ta tako tana laluben kofar toilet, har takai gaban kofar ta bude ta shiga ciki saida ta fara futsari sannan ta dauro alwala anatse ta futo tana tafiya sadaf sadaf don kartayi motsin da zai tashi, saida tazo tsakiyan dakin nashi ta tsaya chak jin kakkausar muryarshi ''kee me kikeyi acikin dakina?, and why are you walking like that kamar wadda zatayi sata''..gabanta ne yabada dam, ashe ba bacci yake ba, amar kuwa bacci ne yadan fara dibanshi, amma sakamakon bude kofar da tayi tun shigowarta yasashi saurin bude idanunshi, don yana sensing kara ko yaya ne, yana nan kwance kan gadon, ya lullube jikinshi da bargo fuskanshi ne kawai a bayyane, idanunshi tar yana facing din inda ta futo, runtse idanunta tayi ta dake tace ''uhm daman alwala nake son yi kuma naga babu wani toilet din Shiyasa na shiga wannan''..anatse ya soma Magana ''jeki yi sallan ki zo nan''…gabanta ne ya fadi jin abinda yace, ahankali ta bude kofan dakin ta fuce, saida tayi sallah tana idarwa tayi addu'oi sannan ta miqe da zumbulelen hijab dinta ta koma dakin nasa, this time around ya kunna light don ko ina haske ne dau, kanta akasa tayi sallama sannan ta tsaya daga gefe gefe tace ''ina kwana, gani''…baiko kalli inda take ba yana nan zaune gefen gadon shi ya dafe kanshi, sanye yake da riga da wando white pajamas, dagowa yayi ya mata kallo daya sannan yayi tsaki yace ''bana using toilet din da mutane sukayi using, so duk sanda kikayi min amfani da toilet ki tabbatar kin wankeshi sau biyu''..amra wadda ta sunkuyar da kanta qasa, ranta adagule da wannan wulaqanci nashi, kallon qasa kawai take tana wasa da yatsunta tace ''I'm sorry''..hawaye ne suka sauko masu dumi daga fuskanta bai kalleta ba ya sake cewa "what are you standing for? Go and wash the toilet now" Kamar wanda aka cire Ma kaya a jiki haka ta wuce toilet din nashi, duk wannan motsin nata akan wutsiyar idonshi, fuskewa yayi kamar baimasan tana yi ba kafin yayi tsaki. Saida ta wanke mashi toilet har sau biyu sannan tayi mopping ko'ina kamar ba'a taba amfani dashi ba kafin ta dauka hijab dinta tana kokarin maidawa jikin ta ta juyo, ganinshi a tsaye yasa ta saurin jaa da baya tayi saurin karasa saka hijab din jikinta, takowa yayi har wajen wash hand basin sannan ya soma wanke bakinshi, anatse, ganin haka yasa ta raba ta gefenshi ta fuce da sauri, don kwata kwata batason tsayuwa agabanshi, ga fargabar abindazai fada mata ga kwarjini da yake mata.

Shiko saida yayi wanka sannan ya futo ya shirya cikin kayan shan iska, ya feshe turare ajikin shi sannan ya jawo laptop dinshi saida ya danyi danne dannen yagama lokacin wayanshi yayi ringing, jawo wayan yayi ya kara akunnenshi, baima ce komi ba ya sauke wayan sannan ya sauko da kafanshi kasa ya sanya bathroom sleepers dinshi masu laushi sannan ya fuce, kai tsaye ya wuce sitting room ya bude entrance door, ya futa ya rufo kofar sannan ya fuskanci m5 wanda ke gaishesa, baima amsa ba ya karba packs din guda biyu sannan yace ''Thanks'', rufe kofar yayi sannan ya dawo ciki, ganin bata sitting room yasa ya juya, wajen kitchen ganinta a gaban fridge yasa ya kawar da kanshi ya aje mata pack daya a kan kitchen island ya wuce ciki abinshi.

Juyawa tayi don daukan cup din data aje wanda zata hada cereal dashi kafin ordern abincin da tayi ya iso, ganin leda yasa ta kawar da kanta don tasan ba ita kadai take zaune agidan ba, kamar yasan bazata kalla abin daya aje ba ya yujo ya mata kallo daya yace ''it's yours'' yana kaiwa nan ya sa kai ya shige dakin shi. Dawowa tayi kamar mara gaskia ta dauka, don duk atunaninta yauma hammam dinne ya aiko mata, anatse ta zauna kan chairs din dake gaban kichen island din sannan ta fara budewa, lafiyayyan Senegalese food ne wanda yaji grilled lamb sai kamshi, wanke hannayenta tayi kafin ta wanko spoon sannan ta debo ruwa a cup daga dispenser ta dawo ta zauna, murmushi ne ya kubce mata bayan ta zaro spoon din daga bakinta anatse ta furta ''abincin akwai dadi hmm'',..saida taci ta koshi kafin ta tattare wurin tsaftsaf sannan ta koma kan couch ta zauna tana latsa wayanta, tana nan zaune ya futo cikin shirinshi, sanin bayason ana shiga harkarshi yasa tayi kamar bata ganshi ba ta cigaba da latsa wayan ta harya fuce abinshi.

Zaman ta tayi ita kadai, karshe ta kira haifa suka sha hira koda ta tambaye ta any update akan amar, kamar kullum ta shaida mata yana nan babu sauyi ita tsoronta ma kar yazo ya jawo ta rasa abinda take nema ta dalilinshi wanda duk sun kasa ganewa, haka ta karaci weekend din nata kunshe ita kadai, daga wanka sai sallah sai cin abinci da latsa waya.

Yauma tunda ya fucewanshi bai dawo ba sai wajen karfe goma, har yazo ya wuceta tana zaune kan sallaya tana lazimi, batako kalli inda yake ba, shima baibi ta kanta ba ya wuce ciki, saida yayi wanka ya chanza zuwa kaya masu laushi marasa nauyi kafin ya futo sitting room din, direct kitchen ya wuce saida ya dauka ruwa ah fridge sannan ya zauna kan kujeran dake table din kitchen island din yana fuskantar parlor, amra kuwa batama san yana wajen ba don hankalinta yayi nisa wajen latsa waya tun bayan ta nade sallayan nata tayi shirin bacci, yanxu tunda ta fuskanci lokacin futanshi da dawowanshi ta daina bari suna hada hanya dashi don bata son yanda yake treating dinta. Anatse ta miqe tana dariya ta aje wayan nata sannan ta tashi ta tube hijab din jikinta, duk wannan abin da take akan idonshi, ganin tana shirin daga riganta yasashi sauri kau da kanshi yayi gyaran murya, afurgice ta juyo ta kalleshi, harta daga doguwan rigan nata, santala santalan cinyoyinta sun bayyana, da sauri ta sauke rigar adaburce, don batayi tsammanin ganinshi a wajen ba gashi ya bata tsoro sosai, ahankali ta sauke kanta kasa tana shirin zama kan couch tajiyo muryarnshi ''ke come here''…kunkune ta fara tana turo baki wanda duk hakan akan idonshi tayi batama san tana yiba, ahankali ta furta ''shi wai sai ya dunga cemin ke kamar mara suna'' duk wannan abin da take akan idonshi kuma ya gani sarai azaffafe yace 'kina Magana ne?''…da sauri tataho ta tsaya dan nesa dashi sanan tace ''ina wuni''…kallo daya ya mata sannan yace ''sake abinda kikayi yanxun nan''..dagowa tayi idonta zuru zuru akanshi tace ''wallahi banyi komai ba fah''..tsaki yayi sannan yace ''shekarunki nawa'', ahankli bakinta ya furta ''21''.. tsaki ya danyi aranshi yace ''how can I even…mteww wannan idanma nace zan abun nan ay raini zai janyo min, no it's like a child abuse ma''…hade rai yayi kamar bazaiyi Magana ba yace ''be sure you get ready by 10am tomorrow morning,I hate delays idan kika bata lokacin zanyi fucewata kuma babu ubanda ya isa ya sani na koma wajen karban application na abinda kike buqata, so be warned I don't repeat my self, and when ever I call you make-sure you distance your self from me understood''..anatse kamar marainiya ta girgiza mashi kai, juyawa tayi zata tafi yace ''ke na baki izinin tafiya ne'' juyowa tayi anatse idonta na kawo kwalla a shagwabe tace ''kayi hakuri''…tashi yayi fuu ya wuce ta gefenta. Yana shiga daki ta lallaba ta wuce ta tube kayan jikinta ta sauya zuwa doguwan riga mai dogon hannu, saida ta saka alarm na karfe biyar sannan ta kwanta abinta.

Karfe biyar daidai wayanta yayi alarm dinta yayi kara, tana jin karar alarm din ta miqe zumbur, da sauri ta fara laluben hanya dukda bacci bai saketa ba, ahankali ta karasa gaban kofar saidata leka taganshi kwanshe kamar bai tashi ba, ahankali ta shiga tayi wankanta sannan ta dauro alwala, saida ta tabbatar ta wanke mashi toilet kafin ta futo, tana fitowa ta ganshi a zaune dukda dakin is dim, tana iya hango yanda ya dafe kanshi yana runtse ido, ahanakli kamar wanda batason Magana tace ''good morning''…bai amsa ta ba yanda tayi tsammanin hakan ya miqe ya wuce toilet din, anatse yabi toilet din, ganin ribbom dinta agefen sink, ya jawo ribbom din kamar tsumma, tunawa da wani abun yasa kawai ya aje, ya wuce gaban basin ya janyo brush dinshi yayi brush ya dauro alwala ya futo,cikin wajen closet dinshi ya shiga ya jawo jallabiyanshi fara wadda kamshi ke tashi daga jikinta, ya shirya, sai yayi wani irin kyau, gashin bakinsa da suka cuko sosai ya shafa kafin ya fito ya shimfida sallaya a tsakiyan dakin ya tada kabbara, anatse yake sallah saida ya idar ya zauna yana azkar, ya dade hannunshi a sama yana rokon allah da ya shiga alamuranshi, ya dade sosai sai wajen 7 ya tashi, cire jallabiyan nashi yayi ya bar shorts sannan ya kwanta, wani irin bacci ne mai dadi ya fusgeshi, bangaren amra kuwa batayi baccin safiya ba, tun wajen 8 ta gama shirin ta don tana tsoron bata mashi lokaci hakan yasa ta shirya tun wajen 8 dukda tasan sai 10 yace zasu fitan, shiryawa tayi cikin abaya baqa mai shegen kyau, kana ganin rigar kasan mai shegen tsada ce, don duk tasha stones, anatse ta dan goga kwalli a idonta, da dan lip glosss, shafa kanta tayi wanda ya nannade sosai sbd rashin gyara dabai samu ba, jin babu ribbom din kanta yasa ta tsaya nazarin inda ta aje shi, tunawa da lokacin da take wanke mashi toilet yasa tayi saurin miqewa kamar zata je daki chan kuma wata zuciyar ta gargadeta, ahankali ta koma ta zauna jiran futowanshi kafin ta sulale taje ta dauko, don gashin nata yayi buzu buzu sosai daman ga yawa ga tsayi ga cika gashi coily, wayan ta ta jawo tana duba Instagram, time to time take duba lokaci, har wajen 10:20 shuru bai fito ba yasa ta miqe tsaye ta fara zaryar tsakanin kitchen da parlor, jin ana kokarin bude kofar dakin yasata saurin zama waje daya ta natsu kamar mai karbar karatu, kallo daya yayi mata yana gyara agogon shi na diamond rolex a hannunshi yace ''go and get that you thrash out of my bathroom, I thought I warn you, the next time na kara gani belongings dinky a toilet dina zaki daina shiga''..yana kaiwa nan ya wuce kitchen ya deba ruwa yasha yace, ''na baki 10mins ki sakko, I repeat 10mins idan kika wuce''…kwafa yayi yasa kai ya fucewan shi. Da sauri ta wuce dakinshi, tana shiga ta fada toilet ta dauko ribbon dinta, yanda ta barshi haka ta dauko shi, da sauri ta futo gudun karta wuce lokacin daya bata, saida ta tsaya ta tamke gashin nata da kyar kafin ta daureshi tam ta yafa gyalan, tana gamawa ta jawo wayanta ta saka takalmin ta ta futo, ahankali ta dannan lift din apartment din, ganin yana 10th floor yasa taga bazata iya jira ba don kusan minti biyu ya rage mata, da sauri ta wuce stairs, haka ta sakko daga 7th floor zuwa last floor, ga haki ga gumi daya fara tsatsafo mata wanda ya kwantar da edges din gaban gashinta, tana futowa gaban compound din wajen ta daburce don motocine da yawa pake a wajen, karar horn da taji yasa tayi saurin kallon wajen da take jin sound din, da sauri ta karasa wajen hadaddiyar motar shi lambor, saida ta tsaya dab da motar ta fara nazarin yanda zatayi, shin ta shiga baya kota zauna agaba, jin ya kara danna horn yasa tayi saurin bude gaban motor kanta a kasa, ta shige ciki muryarta kasa kasa tace ''salam alaykum'' kamar yanda tayi tsammanin bazai kulata bahakan ce ta kasance, da sauri ta sunkuyar da kanta ta rufe kofar, ''alayk salam'' ya fada chan kasan makoshinsa, shima don sallamar musulunci ce shiyasa ya amsa sbd shi Magana ma bata cika damushi ba, fusgar motar yayi suka fuce daga compound din suka kama hanya, karatun alqurani da yake sauraro ya kunna muryar sudais ce kawai ke tashi sai sanyin ac, hankalinshi kuwa yana kan tuqin da yake, yayi wani irin kyau sosai kamar ka sace shi ka gudu, kallon shi tayi ta wutsiyar ido, tana son tambayar shi inda zasuje amma kuma tana jin tsoron sa sosai karya fada mata Magana ko kuma yayi banza da ita. Da sauri ta kame kanta ta kalli window tana appreciating view din kasar, don inda yake tafiar ma bata taba bin hanyar ba. Adaidai wani babban building inda aka rubuta UAE NATIONALITY CITIZENSHIP suka tsaya saida yayi parking ya kashe moton kafin ya lumshe kyawawan idanunshi kamar bazaiyi Magana ba saida ya dauka wajen minti goma kafin ya soma Magana anatse ''you know what to do, and mind you bana son kaudi, muna zuwa duk abinda na fada kice yes kawai, and behave banason shirirtar yara''..yana kaiwa karshe ya mata kallo daya ya kauda kanshi….amra kuwa wadda kamar ya watsa mata garwashi haka ta tsaya kyam, daurewa kawai tayi don har ta fara jin saukar hawaye masu dumi daga fuskarta, ganin ya bude kofa yasa tayi saurin budewa ta fara takowa anatse tazo dan nesa dashi, saida ya danyi gaba kafin ta buyo bayanshi anatse, yanda yake tafiya da yanda take binshi kamar bazasu taka kasa ba, jin alamun kamar ana binsu abaya kuma ana kallonsu yasa tayi saurin juyowa, ahankali idanunta ya sauka akan wata mota wadda ana ganin ta juyo aka zuge glass din motor,..jin sautin gyaran muryanshi yasa ta saurin juyowa, wani irin kallo ya mata tayi saurin kauda kanta ta biyo bayanshi, saida sukazo dab da shiga wajen ya dan tsaya wanda bata ma san ya tsaya ba tadan bugi bayanshi da kanta, juyowa yayi kadan kamar bazai motsaba chan kuma kawai ya sanya hannunshi anatse ya kamo nata, da sauri ta daga kai tana kallonshi daidai shikuma yasa kai ya shige cikin babban building din, sauke kanta tayi kasa don yanda takejin hannunshi cikin nata dumin hannunshi na ratsa ta, shima dai saida yaji wani abu don zai iya cewa wannan ne first time daya taba rike hannun mace da sanin shi bawai an sashi ba, anatse suka shiga wajen duk wanda ya gansu sai sun bashi sha'awa gwanin burgewa, da an kallesu sai an sake don sun dace sosai. Cikin wani office suka shiga, suna shiga kamar bashine mai daure fuska ba cikin faran faran ya gaisa da mutumin dake zauna kan kujera, wani farin balarabe ne sanye da jellabiya, waje ya nuna masu suka zauna, anatse amra ta gaishe da mutumin cikin harshe larabci, sannan ta sunkuyar da kanta. Magana sukayi mai tsayi tsakanin amar da mutumin kafin mutumin ya futa. Juyowa yayi ya mata kallo daya sannan ya kauda kai ya fara latsa wayanshi ganin yanda ta rakube waje daya kamar bazaiyi Magana ba chan kuma yace ''zai kawo application form yanxu zakiyi signing application''..anatse ta dago kanta wanda yake sara mata sosai don duk wani motsinshi har cikin ranta takejin hakan gudun kar tayi wani laifin yasa tayi saurin cewa ''tohm''..mintuna kadan saiga balarabe ya dawo, kallon amar yayi sannan yace ''kunyi shuru kaida matar taka kamar bakwason Magana, jin haka yasa amar tunawa da wani abun, murmushi kawai yayi baima bama mutumin ansa baya juyo ya kalleta yace ''Haa..bib..ty.. are you still not feelin okay''..da dabara yayi mata tambayan Yana kamo hannunta cikin sigar lallashi, yayi hakan ne don tunawa da inda suke, jin sautin muryarshi da lausassan hannunshi cikin nata yasata saurin dago kanta ta kalleshi fuskanta dauke da mamaki hannunta har yana karkarwa, shima kallonta yake, anatse ya sauke wani dan guntun murmushi yana mata alamu da ido akan tayi abinda yace tayi dazu a mota, tunawa da abinda ya fada akan duk abinda yace tace yes yasata saurin cewa ''yess ha..bi..bi'' in a slow and shagwaba tone din da batama san tayi ba. Kallonsu mutumin yayi sannan yayi gyaran murya yace ''lets begin with the application''..har suka gama rubuce rubuce hannunshi na cikin nata, yana jin yanda hannunta ke fidda wani ni'imantaccen zufa da dumi, suna gama application din mutumin ya mike shima ya miqe tsaye sukayi musabaha. Ganin ya miqe da hannunta yasa ta miqe itama kanta a kasa, ahankali yake takawa tana biye dashi har suka futo daga wajen, saida ya tsaya gaban motar shi kafin yayi saurin cire hannun shi daga daga, itama batayi gigin dagowa don kallonshi ba ta sauke kanta kasa tana wasa da yatsun ta, tsaki yayi sannan ya bude motar ya shiga, ganin haka yasa itama ta zagaya ta shiga ta zauna, anatse ya tada motar suka fice daga wajen, koda suka fito motar dazu ta kuma gani, da yanda aka zuge glass din motar, bata kawo komai a rantaba ta kawar da zancen.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull