Kenza eBookz

Auren wata ukku by sameena - Chapter 13

Auren wata ukku by sameena - Chapter 13

Auren wata ukku by sameena Chapter 13: Auren wata ukku by sameena Chapter 13. "Tashi kije Ummul direba yana jiranki. Ki sani bazan bari ki koma gidan…

4,500 words

"Tashi kije Ummul direba yana jiranki. Ki sani bazan bari ki koma gidan mahaifinki ba har sai ranan Aure gudun kar wani abu ya gifta. Kindai san matsalarki da abubuwan da mukaita fuskanta a baya na fashe fashen Aurenki. Wann karon ban shirya ba ma wani k'ofa ya lalata Aurenki ba. Naga Tani bata nan a nan, zan zauna wajen Abbanku Har Tani ta dawo. kuma zan karanto masa komai koda bazai bud'e idonsa ba na tabbata kunnuwansa da zuciyarsa zasu saurareni."

Ta murmusa tana duban Ummul "Na tabbata a yau mahaifinki ya farka ya ganki a d'akin Aurenki zaifi kowa farin ciki sann wann kad'ai Ya isa ya zama silan yaye damuwar dake k'unshe cikin zuciyarsa."

Dubanta kurum Ummul Tai ba tareda ta iya cewa komai ba. Har yanzu dai a idon Umma itace matsalar ahalinsu da k'addararta.

Ta kuma juyowa ta dubi Abba hawaye suka kuma gangaro mata. A hankali ta isa ta tofa masa addu'o'i kafin tasa kai ta fice jiki a mace. **

Abuja..

Zaune suke gaba d'aya a nan lambun dake farfajiyan gidan. Mommy Daddy harma da Anisa.

Mommy dai bata sama bata k'asa gaba d'aya kana ganinta zaka hango tsantsan farin cikin da take ciki.

Ta dubi Anisa tace maza ta sami one of the mades su shirya wajen cin abincin mutum guda.

Daddy ya dubeta "Are you expecting someone.?"

Mik'ewar da Anisa zatai ta hango shi ya nufo garden d'in. Looking handsome as always. Zuciyarta yai wani irin yankewa.

Mommy ta fad'ad'a murmushinta tana nuni da Haidar dake k'arasowa "Oh! He's here already." Ta maido da dubanta ga mijinta "Ya kamata mu rinka samun lokaci irin haka na musamman domin ahali. After all, amarya za'a kawo mana very soon."

Baice komai ba yaci gaba da abinda yake. Dan yanzu ya kula Kwaise batada zance sai na auren D'anta.

Haidar ya k'araso Mommy na masa sannu da zuwa. Sai nan nan dashi take. Wani sabon kula da soyayya take nuna masa abinda bata masa a baya ba. Kaman tayi ma wofi haka ya d'auki abun tinda yasan ba dan Allah take ba.

Koda Anisa ta kawo plate karb'a Mommy tai tana k'ok'arin serving d'insa sai haba haba dashi take tana tambayarsa me za'a zuba masa.

Cikeda k'osawa Haidar Ya rik'e hannunta Ya amshi plate d'in "Mommy please that's enough, I can do it myself. I've been doing it since childhood."

Jikinta ya d'anyi sanyi ta soma Tina ita dai tin tasowarsa tin yarinta bata tab'a tambayarsa yunwan cikinsa ko lafiyarsa ba. Masu aiki da Nannies Sune suka San lafiyarsa, cinsa ko shan sa. Har yayi ciwo ya gama bata san yayi ba kuma ba matsalar ta bane. The only abu da take tambaya ta kuma tada hankali akai shine karatunsa na boko da sakamakon da zai birge mahaifinsa. Idan kuwa bai kawo sakamakon da zai birge mahaifinsa ba ranan zai wuni ne a d'aki mai duhu kuma a kulle cikin tsananin horo.

Mommy ta gyara zama ganin table d'in Ya b'ata shiru sai sautin cutlery dake tashi cikin plates.

Ta d'an murmusa tana duban Haidar "Ya labarin aiki.. Ina nufin sabon project d'in naku.. Kun fara ne.?"

Yasan so take tai creating hiran da zai had'asa magana da mahaifinsa. Ya d'an girgiza kai kad'an "Still ironing out the details.." Ya d'ago yana dubanta sosai tinda yasan tasan komai "In a couple of months, Mommy. Let's say two to three months."

K'arasowar wata mai aiki rik'eda k'aton frame a rufe Ya katse Mommy. Mai aikin ta k'araso cikeda ladabi ta tsaya nan bayan Mommy rik'eda frame d'in tana sanar da ita security ne Ya shigo dashi.

Mommy ta jinjina Kai tana mai nuna mata yanda zata ajiye. Ta maidoda dubanta ga Ahalinta tana kuma fad'ad'a murmushinta "Na had'a mana wann cin abincin ne a tare domin na gabatar mana da wani mihimmin abu. Musamman gareka Haidar." Ta k'arashe tana mai isa jikin frame d'in.

Ta shiga bud'ewa sannu a hankali tana mai furta "Kyakkyawar Amaryar mu. Matar D'anmu Haidar. Sirkarmu wacce zata zamto silan dunk'ulewar ahalinmu."

Cak ya tsaya da abinda yake. Lokaci guda yana mai matse fork and knife dake rik'e cikin hannunsa. Bai iya janye idanunsa daga saman plate d'in ba haka nan bai dubi hoton da mommy ke nuna masa ba wacce ta ambaceta da matarsa.

Girgiza kai Daddy yai yana tunanin matarsa ta zauce da wann auren da take yunk'urin yima d'ansu. Ya d'auki tissue had'ida goge bakinsa. Ya dubi Mommy kafin yace "Are you in your right state of mind. What's the meaning of this Kwaise.?"

Mommy tace "Gani ya kori ji Engr. Matar Haidar ce. Idan ba a hoto ba nasan bazaije ya ganta ba har sai Randa aka kawo mana ita gidan. So kafin a kawota yak'i amincewa yace gaibu na auro masa. Gwara na samu dalilin kafa hujja. Look kalla kaga, zasu dace da Haidar.. Asshe ta iya zab'e." Ta k'arashe sai duban hoton take tana murmushi.

Daddy dai kallon wacce ta samu matsala yake mata. Lokaci guda ya girgiza Kansa "I'm done here." Yai maganar yana mai barin wajen.

Zuciyar Anisa yaci gaba da bugawa tana mai duban hoton. Cewa da Mommy tai Asshe ta iya zab'e shine keta yawo cikin kumnuwanta. Mai kenan hakan ke nufi.? Amminta ce ta zab'o wa Haidar mata.? Mahaifiyarta ta turota gidan ne dan taci amanarta ta nema ma Haidar auren wata daban a garin Kano.? Ko kuwa mai Ammi take nufi da ita.?

SameenaAleeyou📚 *AUREN WATA UKU.!*

*19*

*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*

Ruwa aka kawo za'a yayyafa ma Umma Asshe ta dakatar dasu ta bud'e bakin jaka ta shiga lik'a ma Umma kud'i had'ida umartan matan da ke gefe da su rangad'a ma Umma gud'a cikin kunne.

Aiko firgit Umma ta mik'e tana tambayan da gaske ne an d'aura auren Ummul, Ummul d'inta dai. Sai kuma ta fashe da kuka tana fad'in bata tab'a tsammanin zataga wann rana nan kusa ba.

Masu lallashi nayi masu tausayi nayi masu murna nayi harma da masu takaici.

Toh komai akace d'an lokaci ne, shi kuma aure baka tab'a yinsa sai lokacin da Allah Yace. No matter how hard you try or how many relationships make. Zai faru ne kawai a lokacin da Allah ya nufa. Yau dai Allah ya k'addari za'a d'aura auren Ummulkhairi bayan tulin fad'i tashi da mahaifiyarta taitayi dan dai taga 'yar tata tayi aure. Dukda irin kawo sadaki ana janyewa saka rana ana d'agawa harma da amshe lefe yau Allah ya nufa ya kuma k'addari za'a d'aura auren.

'Ya'ya musamman mata tamkar k'wai suke hannun iyayensu. Babu Iyayen da zasu so wani abu na k'i bisa tsautsayi ko tilastawa ya fasa wann k'wai da suke rik'e dashi cikin kula da kaffa kaffa. Tabbas burin ko wata uwa koma iyaye in general shine da zaran 'yarsu ta Kai gab'an aure su kaita d'akin mijinta cikin salama da aminci. Saidai wasu lokutan insecurity yakan rinjayi confidence da muke dashi akan yaranmu Wanda hakan ka iya zama babban threat a garemu. Tsoron zamansu a gabanmu babu aure, tsoron maganganun mutane da abinda ka iya zuwa yazo yakan sa mu mance wani b'angare mai mahimmanci Wanda yake tamkar foundation idan babu shi tamkar anyi gini bisa iska ne . Shine neman zab'in Allah da fawwala masa lamra. Idan tsoron ya rinjayi raunin har aka mance wann gab'a mai mahimmanci hakan ka iya jefa rayuwar yaran cikin had'arin da yafi zamansu gaban Iyayen. Wani auren death sentence ne iyaye suka jefa yaransu ciki ba tareda sunyi la'akari ba. Da yawa auren yayi ajalinsu. Wasu ma anyi tsafi dasu sabida ba'a nemi zab'in Allah ciki ba tun farko.

'Ya'ya amana ne hannun iyaye sann sunada hakkoki Akan iyayensu kaman yanda iyaye keda hakkoki Akan nasu 'ya'yan. Mu fara k'ok'arin sauk'e nauyi da hakkokin yaranmu Wanda shine tarbiya na farko da zamu basu ko dan nan gaba su sauk'e namu nauyin hakkin dake kansu. Bazai yuwu ka haifi d'a ka wofantar dashi ba kai tsammanin zai girma da tausayinka. Da yawan yaran da muke ji muke gani suna zama abin gudu cikin Al'umma mu bincika yaya tarbiyansu ya samo asali. Wasu tun suna yara iyayen sun d'ebe masu albarka da harsunansu. Wasu iyayen basu san cin yaran ba basu san karatunsu ba balle maganinsu Wanda duk nauyi ne da ya rataya kan iyaye. Ko a d'abi'ance Yaron da ya taso cikin kula da soyayya ba daidai yake da yaron da aka wofantar dashi ba. Akwai jarabawa. Idan kayi iya naka Allah ya jarabceka wann kuma jarabawa ce da yake jarabtar bayinsa dashi.

Ba'a yarda ka d'auki 'yarka ka bada aurenta ma ko wane irin mutum ne yazo Neman auren nata ba dan kawai kana hanzarin ka kauda ita gabanka. Shiyasa addini ya bada tsare tsare cikin Neman auren Kansa kafin aje ga auren. Uwa uba a nemi zab'in Allah cikin duk abinda ake nema. Allah ya shirya mana zuri'a ya azurtamu da yaranmu da samun abokan rayuwa na gari. Ameen.

Umma naku fah kan kace me ta ware. Har wani cakarewa tai cikin tsaddan leshi da Hajja Asshe ta kawo mata a d'inke. Kayan da Ummul zatai fitan biki ma Hajja Asshe ta kawosu a d'inke masu d'an karen kyau da tsada. Dik wani buk'ata da amarya zatai amfani dasu Asshe da k'awayenta Sun kawo.

Hajiya Hadiza k'awarta ta dubeta bayan Sun keb'e "Amma fah kawata kin bani mamaki, ko a mafarki ban tab'a hasashoki tsakankanin talakawa ana damawa dake ba. Wai fisabilillahi ya akai kuka amince da wann aure tinda nasan duk yanda tsiya yake ba'a ganinku wajen."

Murmusawa Asshe tai tana duban Umma yanda taketa shige da fice cikeda farin ciki. Ta kuma duban k'awarta Hadiza "Hadiza kenan, kin fad'a daidai. Duk yanda tsiya da talauci yake bana zuwa wajen. Toh amma babu yanda muka iya ne. Dole ce ta Kama sai anyi auren."

Hadiza ta girgiza Kai kad'an "Toh amma gida bai k'oshi ba yaya za'a kawo waje. Ina nufin ga Anisa 'yarki dan me baki had'a auren da ita ba tinda tana zaune itama ba mijin har yanzu.?"

Asshe ta kuma murmusawa "Tinda kikaji na Miki amfani da kalmar dole ki amince kawai dolen ne. Ni fah kaza ce Hadiza bani k'wai na saida zakara. Ke kinfi kowa sanin haka. Yanzu dai ki bari a gama hidiman nan idan mun natsu na sanar dake komai."

Hadiza ta jinjina Kai a hankali har lokacin mamaki bai saketa ba ganin yanda Asshe ta shiga cikin talakawan nan ana damawa da ita. K'awarta ce tun secondary school ta Santa farin sani. Asshe da zuri'arta worshiping money suke inji su Hadiza. Mutane ne da zasuyi komai Akan duniya da abinda ke cikinsa. Shiyasa ta sha mamakin ganin wann al'amari. Kaman yanda Asshe tace da ita akwai dalili ta tabbata akwai dalilin.

**

A can police station kuwa motar 'yan sanda na shigewa na Hilal ma ya sako kai.

Sauri sauri Hilal ya take mata baya ganin ta nufi hanyar da aka shige da Mama sai kururuwa Maman take tana fad'in wllhi bata ci kud'ad'en ba.

Mama taci gaba da fad'in "Wayyo Khulsum 'Yata ki cece ni ki ceci Mamanki kar a rufeni. Idan aka rufeni babu mai kula da Abbanku dake kwance gadon asibiti Khulsum."

Khulsum ta samu zarafin dakatar da 'yansandan ga bak'auye a gefe yana fad'in kwarankwatsa sai an karb'ar masa hakkinsa. Baici nanin ba nanin bazata cisa ba. Takardun bogi suka kawo masa ya saka hannun. Sarkin kasuwa yace baisan da zancensa ba. Idan sama da k'asa zasu had'e sai an fitar masa hakkinsa.

Police ya dubi Khulsum yace "Ke kuma fah.?"

Mama tai saurin bud'e murya tace "'Yata ce. "

Tsananin mamaki sai ya hana Khulsum furta koda kalma. Wai yau Mama ce ke kiranta da 'yarta. Ikon Allah, Ashe har akwai ranan da Mama zata danganta kanta da jinin Ummanta. Bata kaiga furta kalma ba ta hango Habib mijin Azeema da police woman d'in da kwanaki suka kawota nan police station d'in. Sai wani mannewa take jikinsa. Mama ganin Khulsum tayi shiru ya sanyata duban yanda Khulsum d'in ke duba.

Ta zaro ido waje tana kuma mutsukesu. Waye take gani haka.? Habibu ne mijin Azeema Sun fito daga wani ofishi yana faman gyara kwalan rigarsa sai washe baki yake ga wata 'yarsanda gefe sai kashesa da kallo take kaman zata shige cikinsa. Ta dafe k'irji tana furtawa da k'arfin gaske "Na shiga uku mai nake gani.! Habibu..!"

Hankalin Habibu da 'yarsandarsa ya dawo kansu.

Mama ta soma nunasa da yatsa "Habibu mai zan gani mai kake a nan..? Amanan Azeema kake ci da wann 'yarsandan.?"

"Madam ki iya bakinki police station kike ba Tasha ba." 'Yarsandan ta fad'a cikin dakatar da Mama wacce tai sokoko tana kallonta.

Habibu ya wayance "Haba Mama ya kike magana haka.? Nan fah police station ne. Zuwa nai inata fafutuka ina fad'i tashin yanda za'a samu a kamo mana Tasi'u mana Mama.."

Ya dubi mutanen dake wajen ya kuma dubi 'yansandan da suka kamota "Meke faruwa a nan.. ya na ganki da ankwa.?"

Sai Mama ta soma kuka "Habibu ka ceceni.. Kamo ni sukai.. Ka fad'a masu waye yaci kud'in shagon Malam. Kai shaida ne wllhi banci ba. Habibu kar ka bari a rufe ni."

Kaman daga sama suka sinkayo muryar Khulsum "Ni kuma zan bada shaidan kece kika sayar da shagon koda kuwa Kotu za'a je na shirya zuwa.!"

Mama ta kaikaito tana duban Khulsum "Fitsara zaki min a nan Khulsum.? Inji kin biyo ni ne dan ki taimakeni ki bada shaida kaina."

"K'warai kuwa Mama. Zuwa nai dan na bada shaida akanki na kuma tabbata kin biya abinda kika aikata wa mahaifina Wanda yake kwance baida ikon kare kansa balle dukiyarsa."

Mamaki ya cika Hilal. Ya dubi wann ya dubi wancan "Wait. D'an dakata, wai dama ba zuwa nan kikai dan ki taimaki matar nan ba.. I thought I heard you call her Mama or something.. Is she not your Mom.? Ba naji ta kiraki 'yarta ba. Ta ya kike bada shaida mai muni kan mahaifiyarki.. Are you going to let them arrest your mother just like that..? Don't tell me we came all the way here just for you to make sure anyi arresting Mamanki.."

"Malam kar ka sake kiran wann matar Mamata. Ni ba uwata bace. Kuma ka fad'i daidai zuwa nan nai na bada shaidan abinda ta aikata kafin wancan surkin nata yayi amfani da damarsa ya fiddata." Ta k'arashe tana nuni da Habib dake tsaye gefen budurwarsa 'yarsanda wacce ya kawo ta kama Khulsum d'in lokacin da ta mari Azeema.

"Amma nafi uwarki da ta saida 'yar Malam Isubu yana kwance. Gwara ni shago kawai na saida." Mama tace tana huci.

Hilal ya kuma duban Khulsum da mamaki Wanda kalaman Mama ya haifar mata da sanyin jiki.

Bakauye ya kafe sai an rufe Mama idan ba kud'ad'ensa aka lalo aka basa na. Haka dole aka jefata cikin cell Habib na kwantar mata da hankali da fad'in zai iya k'ok'arinsa yaga ta fita.

Khulsum kaw bata kuma fahimtar komai ba tun bayan maganan da Mama ta fad'a mata. Take taji wani irin kuka na zuwa mata. Tabbas Mama ta fad'i gaskiya gwara ita Akan Umma. Ita abun duniya kawai ta saida amma Umma fah mutum ta saida. 'Yarta da ya kamata ace ta zamto tamkar lu'ulu'u a hannunta. Abu mafi daraja fiyeda shago da abinda ke cikinsa Umma ta sayar. Ko kusa baza'a had'a laifin Mama da Umma ba. Bata San yanda take jefa k'afafunta ba tafiya kawai take tana kuka. Tana Jin wani abu mai kama da k'iyayya Wanda shine zata iya cewa iyakacin alak'arta kenan da mahaifiyarta.

Tana tafe gefen kwalta Hilal na biyeda ita cikin mota. Yaci gaba da fad'in "You know you are unbelievable.. Da nasan Akan wann dalilin kika taho all the way to police station da ban b'ata lokaci na na kawoki nan ba. Because of you na rasa d'aurin auren d'an uwana."

"Malam idan baka Kama gabanka ba duk abinda na maka Kai ka saya da kud'inka.. Da ace baka b'ata min jiki ba Watak'ila da ban tsaya na b'ata lokacina wajen ji da kai ba balle har nayi gamo da Mama. Watak'ila da na samu damar dakatar da auren zalunci da ake yunk'urin yima 'Yaruwata.."Ta fad'i tana ci gaba da sakin huci ga hawaye dake ci gaba da gangaro mata.

"Blame your step mother then." Hilal ya bata amsa Kai tsaye.

Khulsum taci gaba da tafiya tana hawaye.

Hilal yai parking ya fito ya tare gabanta "No I can't just leave you here. After all, Ni na kawoki nan. Idan wani abu ya sameki I'll blame myself for the rest of my life. Please get in the car. Ki bari na maida ke yanda na d'aukoki. At least."

Bata amsa shi ba sai kukan da take ci gaba da yi dan mugun takaicinsa take.

Ya d'an waiga yana duban mutane masu giftawa sai kallonsu suke.

Ya d'an kuma gyaran murya "Look, I don't want people to think that I hurt a girl. Dan Allah ki shiga.. At least ki bani dama na fitar dake daga nan.. Dare ya soma yi duba ki gani.. And is not safe for you to walk alone a babban kwalta irin haka."

Cikin kuka Khulsum ke dubansa "Na tsaneka.! Na tsani mugayen ahalinka da sukai amfani da raunin mahaifiyata suka sayi 'Yaruwata da sunan aure.!"

Hilal ya zuba mata ido "Look, bansan meke faruwa tsakanin ahalinmu ba. But the only abu da zan fad'a Miki shine my cousin is a good person.. He has his faults as human. But I can assure you he's a good person." Ya d'an tab'e baki "Idan yar uwarki ta kasance matarsa abun kiyi mata murna ne."

Takaici ya hanata furta koda kalma tasa kai tana ci gaba da tafiya. Hilal ya kuma tareta "Yamma yayi sosai ki shiga na kaiki gida. That's idan Kinaso ki cimma 'yaruwarki kuyi Sallama kafin a tafi da ita. Dan na tabbata kawo wann lokacin an d'aura auren. Tinda bakiyi nasaran dakatar da auren ba. Watak'ila zakiyi nasaran samun dama kuyi Sallama idan har kika shiga mota ta." Ya k'arashe yana nuni da motar.

Bata k'aunan abinda zai kuma had'ata da d'aya daga cikin wann ahalin. Toh amma gaskiya ya fad'a idan batai saurin cimma Addanta ba Watak'ila bazata samu suyi Sallama ba za'a tafi da ita. Saida ta rakasa da harara kafin ta nufi motar.

Hilal ya d'an tab'e baki yana bud'e mata marfin motar "Sorry to say a daidai yanda na d'aukeki zan ajiyeki. Kinga ko ba komai na rage Miki hanya."

Ta kula nema yake ya dad'a tunzurata hakan yasa bata kuma bi takanshi ba balle ta amsa shi.

Saidai suna isowa bakin babban kwalta da zai shigar da kai layinsu suka hango motocin amarya na ficewa. Alamun Sun makara amarya ta riga ta hau hanya.

Hilal ya tab'e baki kad'an "Looks like someone didn't make it on time. Unless zaki bi bayansu."

"Ajiyeni a nan." Ta fad'i tana k'ok'arin bud'e motar.

"Are you serious.?" Hilal ya fad'i yana k'ok'arin juya kan motar cikin k'ok'arin bin bayan motocin.

Da mamaki Khulsum ke dubansa ta kuma jan marfin motar ta jita a rufe alamun ya rufe daga wajensa.

"Malam ka ajiyeni a nan nace ko na maka ihun b'arawo.!"

"You and I both know this is what you want. Kiyi Sallama da 'yaruwarki. Just admit it." Ya d'an dubeta sai yai murmushi da gefen bakinsa "Don't worry, I'll do you a favor and take you to your sister. After all, Nima can na nufa.." Ya maida idanunsa ga kwalta "Kar ki damu ba sai kin biya kud'in abun hawa ba. A simple thank you will be okay."

Bai kuma cewa komai ba yaci gaba da tuk'a motan.

Izuwa lokacin ta rasa ma mai zatce ma wann d'an rainin hankali. Shiru tai tana duban titi yanda Hilal taketa fifila gudu da ita.

**

Abuja..

Zaune yai gaban mahaifinsa yana sauraronsa yanda Daddy yaci gaba da fad'in "I will be meeting with our international clients in Nairobi.. Daga can zan wuce Cape Town, southAfrica gameda business alliance da muka fara a can months back." Ya gyara zaman glasses d'in dake mak'ale idonsa kafin yaci gaba "Maybe it will take me two to three weeks before I return.." Ya k'arashe yana ci gaba da duba documents d'in dake gabansa.

Haidar ya jinjina Kai yana duban mahaifinsa "So why are you telling me all these Daddy.? Are you.. Do you want to hear from my own perspective.? I mean regarding the alliance.?"

D'agowa yai had'ida d'an zame glasses d'insa yana duban Haidar d'in sosai. "I did not send you to those expensive schools dan kawai ka dawo na saka ka a gaba naita kallonka. But unfortunately it is unfolding.. Watak'ila ba kai bane wann D'an da zanyi alfahari dashi. By now ya kamata ace na huta. Ya kamata ace Kai ke wakiltana a tafiye tafiye irin wann. Saidai Kai d'in banida k'warin gwiwa akanka. It is enough da na amince ka jagoranci project d'in cikin gida..!" Ya kuma dubansa sosai kafin ya k'arada "You are a complete failure to my name Aliyu!" Ya k'arashe yana maida glasses d'insa.

Haidar yai murmushi mai ciwo yana jinjina Kai "Is this the kind of legacy you wish to leave behind for your Son.?" Ya jinjina Kansa zuciyarsa na kuma masa d'aci kafin yaci gaba "I wouldn't be surprised of course. But You know what Daddy. No matter how insignificant you keep insisting I'm to you.. You can't deny the fact that your company needs me.. And you need me too.. Kuma shine dalilin da yasa ka kirani kake sanar Dani duka shirye shiryenka.. So Daddy, deny it all you want. But the truth is that I'm very much important to you.. And your company is nothing.! Absolutely nothing without me.!" Yana ida fad'in haka ya mik'e zuciyarsa na masa zafi.

A daidai k'ofan fita daga sashen ya had'u da Alhaji Gimba na shigowa. Alhaji Gimba na ganinsa ya fad'ad'a murmushinsa. Bai damu ba idan Haidar bai gaishesa ba. Shi dai bazai tab'a cire hope Akan Haidar d'in ba. Alhaji Gimba yaci gaba da fad'in "Congratulations to you and your team. Naji dadin wann al'amari kuma inada yak'inin company bazatayi danasanin zab'en gwarazan da zasu jagoranci wann aiki irinku ba..I trust you and your team." Ya d'anyi fasali kafin yaci gaba "Wann aikin kampani ne so ina shawartanka kar ka bari wani matsala da kake dashi tsakaninka da mahaifinka yasa kai ma aikin rik'on sakainan kashi ko ka yanke hukunci cikin fushi. Na yarda da Kai amma tunasarwa yanada kyau. The company's future relies on your hand Aliyu. And we have high expectations of you.. Let's set our differences aside so we can reach our common goal. Ko dan mu ba ma abokan Adawa kunya." Ya k'arashe murmushi saman fuskarsa.

Tinda ya soma magana Haidar da hannayensa ke sakale cikin aljihu yake dubansa lokaci guda yana nazarinsa "Trust me, it's just a matter of time before we find out who the real traitor is."

Murmushi Alhaji Gimba ya kuma sakar masa kafin yai nuni da parlorn "Baringa mahaifinka. Have a good evening." Ya fad'i yana mai shigewa cikin parlorn.

Lumshe idanunsa kad'an Haidar yai had'ida furzar da huci "Fake life fake people. Everything around this family is fake nothing is real." Lokaci guda yasa kai ya shige cikin sassarfa zuciyarsa na masa wani irin k'una.

Ya fito daga sashen mahaifinsa kenan ya hangi k'atuwar mota ta shigo cikin gidan shak'e da kaya ta nufi nasa b'angaren. Yabi motar da kallo kafin ya nufi hanyar sashen nasa. Nan ya hangi Mommy da Anisa sai nuna ma masu interior d'in yanda zasu jera kayayyakin suke. Ga tsaffin Kayan duka an fito dasu.

Yai tsaye yana dubansu da mamaki. Can Anisa ta hangosa. Sai ta matso kusan Mommy tai mata rad'a a kunne "He's here Mommy."

Mommy ta d'ago tana tambayan wane kenan. Ganin Haidar ya sanyata fad'ad'a murmushinta. Ta k'arasa da sauri ta kamo hannunsa "Haidar my son, today is the happiest day of my life.. An d'aura aurenka yau Haidar."

Sai yaji abun banbarakwai. Shi ya ma mance da wani batun aure da yarjejeniya. Wani irin duba yake mata irin na da gaske take.? Da gaske auren suka masa sabida son zuciya irin nasu.

Mommy taci gaba da fad'in "Wann shine Mafarin had'in kan ahalinmu da yardar Ubangiji. Cikin ikon Allah komai zai daidaita." Bakinta ya gaza rufuwa har mamaki Anisa take yanda Mommy ke matuk'ar d'aukin wann aure. Taci gaba da nuna ma Haidar kayayyakin "Look duba kaga. I know you have high taste so I ordered everything to your taste." Ta saka hannu ta tallafo fuskarsa "Yau d'in ina Jin na cika wani gurbi na zama uwa a gareka D'ana. Burin ko wata uwa kenan taga D'anta yakaiga cikan kamala."

K'ok'arin cire hannun Mommy daga fuskarsa yake Jin tana wasu irin sunbatu "Mommy will you please stop.! Enough of this drama." Ya dakatar da ita kafin yaci gaba "Quit the act already! Stop acting like you care.. Like you are responsible.! Like you are doing your motherly duties wad'anda kika makara bakiyi ba tun a baya. It doesn't suit you at all Mommy.!" Ya k'arashe jijiyoyinsa har fitowa suke.

"Haidar." Ta ambaci sunansa kaman mai shirin kuka.

Dakatar da ita ya kumayi "Mommy you and I both know ba auren tsakani da Allah bane. Ba don ci gaban rayuwana matsayina na d'anki kikai ba. You are doing all this for your own advantage." Ya d'anyi fasali "Mommy my day is bad enough, thanks to my Dad. bazan bari ki k'ara mun wani akai ba.!" Yana ida fad'in haka yasa kai ya fice daga gidan a gaggauce.

Jiki a matuk'ar sanyaye Mommy ta juyo. Anisa ta k'araso ta taddata.

"Mommy seems like ke kad'ai kike son auren nan a gidan nan. Shin bazaki hak'ura da auren nan ba kawai tinda Wanda akayi dominsa baya so. Kawai ki d'aga waya ki kira Ammi ki sanar da ita an fasa tin kafin a kawo matar cikin gidan nan. Dan na tabbata wann auren ba mai d'orewa bane."

Mommy ta harereta "Ke dalla rufe mun baki. Bansan shashanci, Wann aure da kika gani mutuwa ce kawai zata raba matar da Aliyu. Idan kinga auren ya Mutu ki tabbata matar ta Mutu ne.!" Tana ida fad'in haka tasa kai ta shige tana neman layin Asshe dan Jin mai ake ciki.

Anisa ta tab'e baki tana mamakin wann irin al'amari.

**

Kano…

Dik maganganun da Hilal keyi cikin motar ba sauraronsa take ba. Hasalima bazata iya tantance mai yake cewa ba da za'a tambayeta. Damuwarta kawai su isa ga 'yaruwarta tai k'ok'arin shawo kanta su gudu tinda babu idon Umma. K'aran bud'e gate ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da tai nisa ciki. Zuciyarta sai tsinkewa yake tana addu'an Allah ya bata ikon shawo kan Addarta Ummul cikin sauk'i. Tana ji a jikinta wann aure babu wani alheri cikinsa.

Hilal yana Ida parking tai saurin kama handle tana kokawan bud'ewa.

Ya tsareta da idanu "Easy kar ki balla min marfin mota bayan kin b'ata min da tab'o.."

Readers Also Read