Kenza eBookz

Auren wata ukku by sameena - Chapter 12

Auren wata ukku by sameena - Chapter 12

Auren wata ukku by sameena Chapter 12: Auren wata ukku by sameena Chapter 12. Hawaye sukaci gaba da gangaro ma Ummul. Cikin rawar murya take furta "Umma…

4,474 words

Hawaye sukaci gaba da gangaro ma Ummul. Cikin rawar murya take furta "Umma gidan da za'a cika mana buri fah kikace… Umma Ashe har akwai mahaluk'in da zai cika ma wani mahaluk'i burinsa..? Umma idan kinga burin d'an adam ya cika ya bar duniyar nan ne.."

Bata Kai aya ba Umma ta hanb'are mata baki "Ke ke meye haka.. Daina kira mana mutuwa a nan.. Nidai bazan Mutu ba sai burina ya cika in sha Allahu. Shiyasa nace da yardar Ubangiji. Kuma burina shine na ganki a d'akinki dik rintsi.. Koda k'arshen abinda zan aiwatar kenan a rayuwana.."

Jikin Ummul ya kuma yin sanyin Jin kamar mahaifiyarta ta riga ta zauce. Cak tai tsaye tana duban mahaifiyarta, ta rasa tausayin kanta ne ko tausayin mahaifiyarta take. Muryar wata mata ce ya dawo da Ummul daga duniyar tunanin da ta tafi "Ummul d'inmu ta iso..!" Ta fad'i kyakkyawan murmushi saman fuskarta.

Ummul ta karkato tana duban matar wacce keta faman fad'ad'a murmushinta. Kafin tai wani aune ta k'araso ta rungumeta tana fad'in finally sun had'u. Lokaci guda kuma ta shiga janyo Ummulkhairy tana fad'in maza ta shigo ta shirya mai hoto yanzu zai iso bada jimawa ba.

Tambayarta kanta take Wacece wann matar..? Ina Umma ta santa..? Hoto kuma..? Wane irin hoto..? Meke faruwa ne wai..? Anya zata iya jurewa..? Anya batai gangancin biyo Umma ba kaman yanda Khulsum tace.. Amma idan mutanen suka cutar da mahaifiyarsu fah.. Zuwanta shine daidai ko dan tasan wani hali Mahaifiyarsu ke ciki.

Jikin Ummul sai rawa yake yayinda Asshe taci gaba da janyota Har suka shige cikin gidan Umma na biye dasu baki har kunnenta.

* A b'angaren Khulsum kaw tinda ta shigo gidan ta rasa wani b'angare suka shige. Nan ta hangi wani section daga farko. Ganin k'ofan wajen a bud'e Ya sanyata nufan k'ofan cikin tunanin nan su Umma suka shige. Saidai tana shiga wayam bataga kowa ba. Shiru alamun babu kowa. A hankali cikin sand'a ta soma jada baya zata fice. Saidai tana cikin sand'an da baya da baya taji ta bangaji mutum. A tsorace ta juyo zuciyarta na tsinkewa dukda bata bari tsoron Ya nuna saman fuskarta ba saima sauk'e huci da take.

Wani matashin saurayi ta gani ya zuba mata ido, hannayensa hard'e. Yana binta da kallo mai d'aukeda alaman tambaya.

Taci gaba da huci tana hura hanci basu daina duban juna ba.

"Ina 'yaruwata.. Mai kuka mata.. Su waye ku.?"

Hilal ya girgiza kai kad'an "Excuse me, what are you talking about..? Wait, Who are you..? And what exactly are you doing in here.?"

Gajeren tsaki tai had'ada sa kai zata shige. Hilal ya kuma tare gabanta Yana girgiza yatsa alamun bazai barta ta fice ba har sai ta amsa masa tambayoyin sa "Oh wait. Dakata dakata. Ai bazaki fita ba sai kin sanar dani wacece ke. Daga ina kike..? Kuma mai ya shigo dake b'angare na.?"

Ya d'an girgiza kai ganin har lokacin hararsa kurum take. A tunaninsa sabuwar mai aikin Amminsa ce a gidan. Ya katse shirun da fad'in "You must be new here? Basu fad'a miki masu aiki basa shigowa b'angarena ba saida izinina.?"

Kallonsa tai daga sama zuwa k'asa jin ya kirata da mai aiki "Kaga Malam ka bani hanya na wuce. Banida lokacinka balle na tambayoyinka. Watak'ila ba kai nazo nema ba.!" Ta k'arashe kaman zata bangajesa ta shige.

Ya d'an matsa Ya bata hanya ganin da gaske bangajesa zatayi. Lokaci guda yabi bayanta da kallo "Who's she.? She doesn't sound like mai aiki." Ya d'an girgiza kai har lokacin yana duban k'ofan "She's so tough." Ya fad'i yana mai tab'e baki had'ida girgiza kai. *

Suna shigewa d'akin Ummul ta juyo ta dubi matar amma bataga Umma tareda ita ba. Nan fah tsoronta Ya ninku.

Asshe ta murmusa ganin har lokacin jikin Ummul bai daina rawa ba "Ki kwantar da hankalinki Ummulkhairi. Ki saki nan gidanku ne kinji.. Ga bathroom ki shiga kiyi wanka duk abubuwan buk'ata zaki samu cikin band'akin."

Asshe tasa kai zata fice kenan Ummul tai saurin kamo hannunta "A'a dan Allah kar ki cutar dani.. Dan Allah kar cutar da mahaifyata.. Na San tanada nata irin matsalar amma ita d'in ba mai kwad'ayin abin duniya bace.. Bansan mai ya sameta ba har ta mance damu da mahaifinmu dake kwance gadon asibiti ta zab'i wann rayuwar.. Kiji tsoron Allah kar ki cutar damu.. Na rok'eki..!" Ta k'arashe tana mai duk'awa gaban Asshe tana kuka sosai.

Tallafota Asshe tai ta d'agota cikin k'ok'arin kwantar mata da hankali take fad'in "Ki kwantar da hankalinki Ummul banida wani k'ulli cikin zuciyata taimakonku nai niyya.. Kar ki min mummunan fahimta.."

Ummul taci gaba da kuka har lokacin jikinta rawa yake "Dan Allah kar ki cutar damu kar ki cutar damu.."

Ganin gaba d'aya ta birkice yasa Asshe daka mata tsawa da fad'in "Ke ki mun shiru.. Yi mun shiru dallah.. Kar ki mun shashashanci a nan.. Shige maza kiyi wanka kafin masu kwalliya da mai hoto su iso.." Tai maganar tana k'ok'arin tura Ummul cikin bathroom Ummul tana tarjewa tana fad'in "A'a dan Allah.. Dan Allah a'a..!"

Daidai lokacin Khulsum ta k'araso ta finciki hannun Ummul daga rik'on da Asshe tai mata "Sakar mun 'Yaruwata.!" Ta fad'i da k'arfin gaske tana fincikan Ummul.

Asshe tai tsaye tana duban Khulsum wacce tuni ta soma tambayar Ummul koda abinda ya sameta "Adda sun Miki wani abu ne.. Muje zo mu gudu.. Zo mu tafi..!"

Kaman daga sama suka sinkayo muryar Umma tana fad'in "Babu yanda zaki kaita.. Sakar mun 'ya..!"

Da mamaki Khulsum da Ummul suke dubanta.

Khulsum tace "Umma Allah bazai baki damar cutar da 'Yaruwata ba sabida tin tasowarta biyayya take Miki. Dani da 'Yaruwata zamu tafi.. Zamu fice daga rayuwarki Umma idan Har haka kike so.." Muryar Khulsum ya soma rowa sosai "Umma me ya sameki..? Su waye wad'ann..? Menene gaskiyan rad'e rad'in da mutane suke akanki.. Umma shin kin manta da k'alubalen da ahalinmu suke fuskanta..? Shin har akwai abinda Yafi Miki ahalinki mahimmanci..? Umma Abba yana kwance a asibiti tsakanin mutanen da suke mafarki da burin ganin bayansa.. A daren da kika zab'i ki tafi ki barmu Har kusan kwana nayi a police station.. Duk ina kike Umma.. Ina kike sanda mahaifinmu yake tsananin buk'atarki kusan shi.. A kullum muna fita mu fuskanci mutane da maganganun da suke jifanmu dasu.. Yanzu kin zagayo kin d'auke 'Yaruwata kin kawota nan ayi tsafi da ita.!"

Bata kai aya ba taji sauk'an mari a k'uncinta. Ta d'ago tana duban Umma dake sakin huci.

Lokaci guda take nuna Khulsum hawaye na gangaro mata "Ke baki san komai ba.. Baki san abinda ke faruwa ba.. Zo ki fice… Shiyasa tin farko ban gayyatoki ba dan nasan ke dai kam ba'a k'ulla alkahiri dake.. Zo ki fice.."

Muryar Asshe ne ya katse su. Ta dubi Khulsum tace "Kar ki Fad'i abinda baki Sani ba yarinya. Duk fad'i tashin da mahaifiyarku keyi akanku ne da mahaifinku. Ina kuke a lokacin da kishiyar mahaifiyarku ta koreta tace taje ta nemo kud'ad'en da za'ayi ma mahaifinku jinya..?"

Khulsum ta kaikaito tana mata wani irin duba "Wacece ke..? Me kike nema daga wajen mahaifiyata..?"

"Ki kirani Sirkar 'yaruwarki Ummul.. Domin kaw nan bada jimawa ba Ummulkhairi zata zamto matar D'ana.!"

Da mugun mamaki dukansu suke duban matar da kuma Umma.. suka kuma juyowa suna ma Umma wane irin duba Wanda su kansu basu san duban me suke mata ba a halin yanzu.

"Sirka..! Matar D'ah..!" Khulsum ta nanata tana duban Asshe da Umma kafin ta kuma juyowa ta dubi Ummul wacce ita kanta cikin rud'ani da duhu take.

Umma ta jinjina kai "K'warai kinji da kyau.. Wann matar da kike gani k'anwa take wa mahaifiyar mijin Ummul d'ita.. Wnn karan bazan bama wani k'ofa Ya lalata auren Ummul d'ina ba, ba ke ba Khulsum ba Tani da 'ya'yanta ba ba kuma sauran munafukan mutanen layinmu ba.. Dan haka zo ki fice..!"

Ta k'arashe tana k'ok'arin rab'a hannun Khulsum dana Ummul amma sai taji wann karon Ummul ta rik'e hannun 'yaruwarta k'am tak'i saki hawayen dake idanunta sun kafe sun daina zuba.

Ummul ta girgiza kai tana duban mahaifiyar tasu cikin rashin yarda "Har yanzu wann ne damuwarki Umma.. Ki aurar Dani kota halin k'ak'a..? Shin Umma rashin aurena ne kawai k'alubalen da muke fuskanta a rayuwa..?" Muryarta Ya soma rawa sosai "Abba yana cikin wann yanayi.. Ahalinmu suna cikin wann jarabawa amma ke damuwarki har yanzu guda d'aya ne Umma.. Shin Umma bakida sauran matsaloli na rayuwa ne sai wann..? Umma iyakacin kiman da nake dashi kenan a wajenki a matsayina na 'yarki..? Iyakacin kiman da mahaifina yake dashi kenan a wajenki matsayinsa na mijinki.. Umma ina zaki kai girman hakkin Abba.. Ta Ya zaki shirya aurar da 'yarsa yana kwance cikin wann hali."

Khulsum na hawaye ta katseta "Ta Ya zata shirya sayar masa da 'Ya dai.. Adda dan Allah kizo muje.. Muje mu nemi agaji daga hukumar hisba wllhi Umma bata a hayyacinta.." Ta k'arashe tana kuka sosai.

Ummul na hawaye take girgiza kai "kiyi hak'uri Umma.. Ki yafe mun amma.. amma Bana tunanin wann karon zan iya Miki biyayya.. Kiyi hak'uri zanbi 'Yaruwata mu tafi.!" Tana ida fad'in haka ta janyo hannun Khulsum "Muje Khulsum..!"

Umma ta dubi Asshe hawaye na k'ok'arin ciko idanunta "Kin gani ko kinga abinda nake fad'a Miki.. Wann 'yaruwar tata ta kora mata mazan aure sunfi abinda suka fi da wann bak'ar Zuciyar nata. Kin gani hassada take da ita.. Toh wllhi wann karon ban shirya jin kunyan duniya ba.!" Tana huci take duban su Ummul da k'iris Ya rage basu fidda k'afafunsa daga cikin d'akin ba.

Umma ta bud'e murya tace "Ummulkhairi.! Idan kika saka k'afa kika fice daga d'akin nan.. Ki mance kinada mahaifiya Suwaiba..! Wllhi wllhi idan Har ki kai sanadin da mutanen nan zasu ce sun fasa auren nan toh Babu ni babu Ke kuma ke ba 'Yata bace daga wann lokacin.. Ki nemi wata mahaifyar amma ba ni ba..!" Ta k'arashe tana sakin huci.

Cak Ummul ta tsaya ta kasa koda motsa k'afarta guda.

Gani haka yasa Asshe bud'e murya "Ba sai kin mata baki ba! Baza kuma a mata dole ba. Yardarta da amincewarta shi zaisa ayi wann Auren." Ta maidoda dubanta ga Ummul "Har yau ba'a biya kud'in surgery da za'ayi wa mahaifinki ba. Anyi masa komai, an canza masa d'aki. Yana samun duk wani kulawa saidai kud'in aiki ne kawai yai saura.. Kinsan dalili..?"

Ummul ta dubeta cikin tsananin sanyin jiki "Sadakin ki shine kud'in da za'a biya ai ma mahaifinki aiki Ummulkhairy.."

Asshe taci gaba da takowa gaban Ummulkhairy, su duka biyun suna duban juna "Nasan za'a iso wann gab'ar. Shiyasa ban bari an biya kud'in aikin ba. Har sai nida Ke mun gana da juna. A halin yanzu, ki sani Aurenki shi kad'ai ne zai ceci mahaifinki. Domin kuwa sadakinki da zamu biya shine kud'in da za'a masa aiki a ceci rayuwarsa.. Wuk'a da nama na hannunki... Yanzu idan kika ce baki amince ba. Ni kuma zan janye komai ku nemi wani hanyar da za'ayi wa mahaifinki aiki.."

Umma ta kuma bud'e murya ganin Asshe tayi nasaran dakatar da Ummul.

"Wacece matsalar ahalinmu Ummul. Kece matsalar mu. K'addararki shi yai silan kwanciyar mahaifinki.. Idan Har akwai wacce tafi cancanta tai sadaukarwa mai girma wa mahaifinku.. Toh ki sani kece kika fi cancanta Ummul.!"

Khulsum ta soma girgiza kai tana duban Ummul "A'a Adda, dan Allah karki amince.. Akwai na gari da yawa. Na Allah basa k'arewa.. Dan Allah kar ki amince da wann auren na rashin galihu Wanda ko sanin mijin bakiyi ba." Ta k'arashe tana ci gaba da janyo hannun Ummulkhairy alamun tazo su tafi. Amma sai taji Ummulkhairy ta doge. Lokaci guda take girgiza kai tana duban Khulsum "Kiyi hak'uri Khulsum.. Na zab'i ceto rayuwar mahaifina koda shine abinda zanyi na k'arshe a rayuwata. Zanyi auren.. Zan auri ko waye Umma ta kawo dan na ceci rayuwar mahaifina.. Gaskiyar Umma ne. Watak'ila idan nayi auren komai zai zo k'arshe. Watak'ila matsalar ahalinmu zai k'are. Watak'ila ni ce matsalar kaman yanda Umma tace."

Khulsum na hawaye take girgiza mata kai alamun a'a.

Cikeda k'osawa Umma ta dubi Khulsum. Kinji abinda tace "Ita d'in 'ya mai biyayya ce ba irinki ba. Sakar min hannun 'ya kafin ki mata sanadin abun alheri da ya sameta."

Khulsum ta girgiza kai tana duban Umma. Lokaci guda ta soma jada baya. Tana duban Ummul hawaye na gangaro masu su duka biyun.

**

A can gida kaw Mama tana zaune tsakar gida ta rapka tagumi ga su Azeema da Badia sai dadd'age Kayan masarufin da Suwaiba ta kawo suke. Yaran Salima suna gefe an had'asu da Kayan mak'ulashe. Babu yanda Mama batayi ba kar su tab'a Kayan Suwaiba Kayan Shan jini amma babu wacce ta kula mama cikinsu sai Salima wacce ta tayata da tagumi. Gashi Salimar ta basu labarin irin kud'ad'en da Umman ta kashe a asibiti. Amenity ma aka maida Abba executive room kula ake basa na musamman. Su Azeema kam har so take washe gari yayi ko Umma zata sake zuwa ta rok'eta Aron tufafin kece raini taje bikin dangin mijinta da suke dashi a satin.

Mama ta kuma sauk'e kakkauran ajiyan zuciya tana tuna Suwaiba a baya Suwaiba fah data maidata bora cikin gidan farkon aurota wai itace yanzu duniyar nan ta juya akeyi da ita. Gashi har 'ya'yanta na cikinta sun fara son Suwaiba da tarayya da ita. Ikon Allah Lallai ta yarda babu mayaudariyar aba irin duniya. Yanzu zata rud'eka ka zata tanayi dakai anjima kad'an ta sake ta Kama wani a Barka bakin Tasha. Ita yanzu haka tanaji tana gani Suwaiba zata ci gaba da zuba mata bariki a gida. Lallai bataci ta zama ba. Ya zama dole ta san abinyi.

**

Abuja

Saukowa yai cikin shirin fita waya manne kunnensa "Family dinner?"

Ya d'an girgiza kai yana ci gaba da sauk'owa "This is not part of the agreement Mommy. You know we can't stand each other."

Shiru yai alamun yana sauraro daga mahaifiyarsa "Fine, I'm on my way there. Amma wann zai zama na k'arshe." Daga haka katse kiran yai.

Dareen ta k'araso tana dubansa "Going somewhere.?" Tace tana mai kamo hannayensa murmushi saman fuskarta.

"To my Mom's" Ya fad'i a tak'aice sai kuma ya k'ara da "Don't wait for me for dinner.. Maybe I'll be back late." Ya fad'i yana shafan b'angaren fuskarta guda.

Ta d'an jinjina kai "Haidar, don't you think it's high time you introduce me to your family. After all, we've been married for months now."

Hannayenta ya kamo cikin nasa "I don't think it's necessary. Those people mean nothing to me. I don't even consider them family.. Na rubuta yarjejenyar rabuwa dasu. Rabuwa ta har abada."

Tai masa k'uri tana dubansa, Ya d'an janyota cikin jikinsa suna fuskantar juna sosai "You.. And only you.. You are the only family I have."

Murmushi ta saki zuciyarta zallan k'aunarsa. Ta shafi gefen fuskarsa tana fad'in "And I'll love you till my last breath."

Ya murmusa had'ida manna mata light kiss. Lokaci guda Ya kuma mata Sallama kafin ya fice.

Tabi bayansa da kallo cikin d'aurewar kai. This is not like him. Ya canza gaba d'aya. Mutumin da ya tsana ai masa zancen iyayensa shine yanzu yake zuwa wajensu akai akai.. Sann mai yake nufi da ya rubuta yarjejeniyar rabuwa dasu..? Shin Wai meke shirin faruwa ne..? Haidar ya canza gaba d'aya wani sabon kusanci na neman shiga tsakaninsa da ahalinsa.. At the same time yana cewa ya kusa datse duk wata alak'ar dake tsakaninsu. What exactly is going on..? Kasa nemo amsar da Tai ya sanyata k'arasawa saman kujera ta zauna tana kuma fad'awa duniyar tunani.

**

Ita dai tana Jin yanda makeup artist d'in keta faman zuzuta kyaun da tai amma bata tanka ba. Dan physically ne kawai take wajen amma tinaninta da hankalinta basu a wajen. Duban fuskar nata take cikin madubi Wanda dukda makeup d'in ba mai tsanani bane. Amma abinka da wacce bata saba ba sai take ganin kaman an canza mata kamanni ne . Dama tin can ita ba gwanar kwalliya bace balle yanzu da take tsaka mai wuya. Bata tab'a tsammanin Umma zata tafi da nisa har haka ba. Tana jin sanda su Umma da Aunty Asshe suka shigo sai faman zuzuta kyaun da tai suke. Lafaya ne Wanda kallo guda zaka masa ka tabbata Ya amsa sunansa kalan peach Wanda Ya dace da skin color d'inta da bai cika haske ba haka nan kai tsaye baza'a kirata bak'a. sai black long sleeve shirt daga ciki, an kwantar da lallausar bak'ar sumarta da Ya sha gyara daga gefe.

Asshe ta k'araso da sauri ta mik'ar da ita tsaye "Wow! lallai za'a haifo mana Fulata shuwa. Yauwa 'yar albarka Uwar alkhairi.. Maza muje masu hoto suna parlor suna jiran fitowarki."

Ummul ta d'ago ta dubi Umma amma sai taga Umma ta kauda kanta gefe alamun bazata saurare ta ba. Cikin sanyin jiki ta soma jan k'afafunta tana biyeda Asshe wacce ke rik'e da ita. Can k'asar zuciyarta bata komai sai ambaton Allah domin ya shiga lamuranta.

Suna fitowa parlorn suka tadda masu d'aukan hoto har kusan mutum uku. Tai tsaye tana duban masu hoton wanda k'arasowarta kawai suke jira komai nasu ya zama ready. Ji tai kaman kar ta k'arasa wajen amma sai maganar Aunty Asshe ya fad'o mata "Kud'in Aurenki shine kud'in aikin mahaifinki" Ta d'an d'aga k'wayan idanunta sama cikin k'ok'arin hana hawayenta zuba. Tamkar kazar da k'wai ya fashe ma a ciki haka take takowa cikin parlorn. Ta k'arasa ta zauna yanda masu d'aukan hoton ke nuna mata. Lokaci guda zuciyarta na karanto mata 'Komai da kike gani na faruwa akwai dalilin faruwarsu Ummulkhairi.. Ita rayuwa jarabawa ce gaba d'ayanta. Allah yayi tanadi wa masu hak'uri kaman yanda yayi alk'awari.. Watak'ila kasancewar Umma a matsayin mahaifiya a gareki shine babban k'alubalenki a rayuwa.. Kiyi hak'uri kiyi mata biyayya.. Har abada bazaki tab'e ba.' Da wann batu na zuciyarta taji k'warin gwiwa na d'an zuwa mata.

Umma ce mai nuna mata styles d'in da zatayi har gyara mata zama take tana fad'in tai murmushi kyaunta ya bayyana. Kuji fah.

Izuwa lokacin Ummul ta daina mamakin Umma sai addu'a da take wa mahaifiyar nata cikin zuciyarta.

Aka d'auki hotuna aka gama dikda cikin idanunta akwai alamun hawaye a duka hotunan amma kam tayi kyau TabarakAllah ma sha Allah inji Aunty Asshe. Fad'i take d'ansu yayi dacen mata.

Bayan Asshe da Umma sun keb'e Umma tace "Toh yanzu meye abu na gaba Hajja Asshe.?"

Asshe tace an tura ma mutumin da zai wanke hoto can Abuja ya kai ma 'yaruwata. Yau zasuga Amaryarsu Ummulkhairy a hoto kafin su ganta a zahiri.

Umma ta lumshe idanu had'ida sauk'e ajiyan zuciya. Lokaci guda ta d'aga hannuwa sama "Ubangiji kasa an dace.. Allah yasa Ummul d'ina ta dace.. Allah na rok'eka ka jefa k'aunarta cikin zukatansu a kallon farko.."

Asshe ta murmusa ta dafa Umma "Anma dace in sha Allahu. Kinsan dai ance wai gani ya kori ji Shiyasa za'a aika masu hotunan Ummul su gani su shaida amma 'Yaruwata da D'anta basuda matsala. Yanzu Abu na gaba sai maganan kai lefe da saka rana.. Inaso duka ayi su a gobe ne. Amma kafin nan dole mu samu magabatan Ummul ayi magana.. Kinaga dangin mahaifinta zasu amince su bamu aurenta.?"

Umma tai shiru kaman mai nazari. Cikinta ya bada wani sauti k'uuu.! Ita sai yanzu ma ta Tina da za'azo wann gab'ar. Ta soma 'yan kame kame. Sai kuma ta nusa tace "'yanuwansa basa jituwa dashi abinki da gidan da 'yanubanci ya raba kai. Yaruwarsa mace ce guda d'aya tak, kuma itama Sun raba gari tinda jimawa. Kuma mace ai bata bada aure. Kaf 'yanubansa ne gidan Wanda ba wani ganinsa da gashin ido suke ba.." Idanun Umma suka kawo ruwa murna na Neman komawa ciki take duban Asshe "Toh.. toh.. Yanzu mai zai faru idan suka k'i amincewa su bada auren Ummul..?"

Saurin katseta Asshe tai "Haba Suwaiba kin faro abu da zafinki kar ki badani mana… Keda kike da babban makami.. Bakiga yanda kika aje Kishiyarki a yanda ya Kamaceta bane..? Ai kud'i Sune jigon rayuwar nan Suwaiba. Idan kud'i na aiki toh na tabbata Miki zasu bada auren Ummul ba tareda wani b'ata lokaci ba dan nayi imani kaf d'insu fama suke da rayuwar nan ta yau.."

Umma ta jinjina Kai "Kuma fah kince wani abu dan ko yau d'in nan da naje nai rabon kud'in ina ganin Baballe ya amshe Wanda na bawa D'ansa ya soke a aljihu.. Kunya ce ta hanasu nasan suma da Sun shiga layin rabon kud'in.."

Asshe tace "Ah toh kin gani ko. Ke fah yanzu sai abinda kika ce a wann gidan." Ta k'arada "Ita kuma Ummul zata zauna a nan a mata 'yan gyare gyare na amare.. Mai gyara na musamman na d'auko daga can gida Maiduguri.Kuma kinga dai yaro ne d'an gayu Wanda rabin rayuwarsa turai ne Ya saba cin karo da matan turawa da wayayyun mata da suka goge. Kinga kuwa dole duk wacce zata je matsayin matarsa ta wanku da kyau ta kuma k'ara samun gogewa gudun kar a samu matsala dukda ko a haka aka kai masa Ummul na tabbata baza'a samu matsala ba amma kinsan ance idan kanada kyau ka k'ara da wanka. Kinsan sha'anin d'an yau." Ta d'an gyara tsayuwarta "Sann zamanta a can gidan naku wani tsautsayin na kuma giftawa Wanda bazamuyi fata ba. Kinga Har kawo wann lokacin kishiyar ki batasan abinda ake shiryawa ba."

Umma tai karaf tace "Ai Kinga wann 'yaruwar tata da ta fice ko bala'inta kad'ai Ya isa ya iya jawo wani matsalan tinda kinga a nan take ce mata su gudu. Toh kafin ta koma can na shafa cikin dare naji sun gudu gwara ta zauna a nan asiri na a rufe a kula da ita idon masu ido bai ganta bakin masu baki bai tofa ba."

Asshe ta jinjina kai "Cikin kwanaki k'alilan komai zai kammala da yardar Ubangiji Ummul d'inki ta shige d'akin aurenta mafarkin ki ya zama gaskiya."

Umma sai ta fara hawayen farin ciki tana fad'in shikenan burinta yana gab da cika. Allah zai cika mata wann buri nata daga k'arshe.

Asshe ta girgiza kai kafin ta fice ta bawa Umma waje tai mai isarta.

A haka Ummul ta k'araso ta tadda Umma wacce itama hawaye ne kwance saman fuskarta.

Ta k'urawa mahaifiyarta ido. Sai kuma tasa bayan hannunta ta share hawayen dan taji kaf tattaunawar da su Umma sukai.

"Alfarma d'aya zan rok'eki Umma." Ta fad'i cikin rawar murya.

Umma ta dubeta wann karon hawaye ne saman k'uncinta.

Ummul taci gaba "Ki kaini wajen Abba na gansa nai masa Sallama kafin ku killaceni a wann gidan."

Umma ta jinina mata kai tana sakin murmushi ta kamo hannayen Ummulkhairi "Zamuje Ummul. Zamuje kiga mahaifinki. Sann zan baki labarin duk abubuwan da suka faru dalla dalla tin daga lokacin da Tani ta fatattake ni naje na nemo kud'ad'den jinyar mahaifinku."

Bayan Umma ta labarta komai dangane da had'uwarsu da Asshe da irin duk wani taimako da Asshe Tai mata. Da buk'atan Asshen na nema ma d'ansu aurenta. Jinina kai Ummul tai ba tareda tace komai ba dan kalamai sun k'are saman harshenta. Abinda yai mata saura hawaye ne Wanda suma d'in batada tabbaci idan basu kusan k'arewa ba.

Driver ne ya d'aukesu Ya kaisu Har asibiti wajen Abba.

Mama dake zaune a haraba tana hangosu ta mik'e cikin sauri ta nemi wajen b'oyo ta b'uya yayinda Ummul da Umma suka shige d'akin.

Umma ta dubi Ummulkhairy tace "Zan barki ki gana da mahaifinki Ummul. Ku biyu."

Ummul ta jinjina mata mai tana goge hawayen da suka kwararo mata.

Ummul zaune gaban gadon mahaifinsu Wanda idanunsa ke lumshe, ta saka bayan hannunta ta share hawayen da suka gangaro mata, abubuwan da suke faruwa da ahalinsu sai gifta mata suke a k'wayar idanu. Ta d'aura hannunta guda saman na Abba. Cikin rawar murya take furta "Abba tinda ka kwanta komai bai k'ara daidaita ba.. Umma ta canza Abba.." Sai kuma tai shiru tana share hawayenta "Abba koda bana nan… Ban sani ba ko zamu sake had'uwa ba ko bazamu sake had'uwa ba. Abba ka yafe wa mahaifiyata a bayana. Dan Allah ka yafe ma Umma.!" Kuka ya hanta ci gaba da magana.

Da k'yar kukan nata Ya tsagaita kafin taci gaba "Abba bazanso wani wanda ba kai ba ya aurar dani. Watak'ila Umma ta hana maka wann damar ne domin ceto naka rayuwar."

Muryarta yaci gaba da rawa "Abba banida wani zab'i.. Rayuwarka na kan gab'a a nan.. Watak'ila wann shine maslahan ahalinmu. Watak'ila komai zaizo k'arshe. Watak'ila ni ce matsalar. Watak'ila idan nayi nesa daku zaman lafiya da kwanciyar hankali zai wanzu tsakanin ahalin. Abba zanyi duk wata sadaukarwa sabida ahalina. Ka yafe mun Abba. Kuma ka yafe wa mahaifiyata ." Ta k'arashe tana mai kifa kanta gefen Abba hawaye na kuma kwararo mata.

Mama dake lab'e bayan window ta waje taji duk abinda Ummul tace. Wato Suwaiba ta shirya aurar da Ummulkhairi ne a sirrance..? Shin wann shine dalilin canzawan Suwaiba..? Aiko idan haka ne sai taga ta yanda za'ayi wann aure.. Idan Suwaiba tasan wata bata San wata ba. Toh amma ta ya zata b'ata auren tinda Suwaiba bata nuna masu mijin Ummul d'in ba.? Kar dai Suwaiba ta samo attajiri ne ma Ummul d'inta.. Idan har al'amra sukaci gaba da tafiya a haka kenan fah Suwaiba zata zamto sarauniya a gidan. Sai abinda tace. Harta 'ya'yan cikinta su Azeema sai Sun gagareta. Tin yanzu ma komai ya canza balle abubuwa suci gaba da tafiya a haka.. Uwa uba Har kawo wann lokacin basu saka Tasi'u a idonsu ba... Dawowan Suwaiba dik shi ya karkata masu hankali ta kasa aiwatar da komai gameda b'cewan Tasi'u. Toh inaga Abubuwa sunci gaba da tafiya a haka.? Yanzu ita fah zata tashi a tutan babu kenan ga Suwaiba ta dawo da sabon sauyi..

Mama ta koma gefe saman benci ta zauna had'ida buga uban tagumi. Kallo d'aya zaka mata ka fahimci duniyar tai mata atishawan tsaki. Sai faman sauk'e tagwayen ajiyan zuciya take tana canza salon tagumin ta. Babu babban abinda ya bata takaici kaman da ya kasance yanzu dik abinda suke ci daga wajen Suwaiba ya fito.. Shikenan Suwaiba fah ta amshe girman nata. Abinda yai saura kawai shine Suwaiba ta umarceta ta soma kiranta da Yaya.

Saiga Mama na hawaye tana fad'in har abada bazata bari Suwaiba tai nasara akanta ba. Idan abinda zata aiwatar k'arshe shine hana yuwan auren Ummulkhairi ta shirya yi. Da dai ta bari Suwaiba tai galaba akanta gwara tai komai dan nasara nata ne da yaranta ba na Suwaiba da nata 'ya'yan ba. Da wann tunani ta mik'e tagajan magajan domin kaw zama bai ganta ba.

* Kan Ummul na kife gefen mahaifinta tana ci gaba da cazgan kuka mai ban taisayi.

Umma ta k'araso ta dafata.

Ummul batace komai ba Har Umma ta ta k'araso wajen.

Readers Also Read