Kenza eBookz

Auren wata ukku by sameena - Chapter 11

Auren wata ukku by sameena - Chapter 11

Auren wata ukku by sameena Chapter 11: Auren wata ukku by sameena Chapter 11. Cikeda zak'ewa Habibu yaci gaba "Wann ai zancen banza kenan.. Ta Ya za'a ce…

4,460 words

Cikeda zak'ewa Habibu yaci gaba "Wann ai zancen banza kenan.. Ta Ya za'a ce kun kira shi Tasi'u kun dank'a masa ragamar komai irin haka. Mai zai hana baku tuntub'i ita Azeema ta kirawo nata mijin matsayin shaida ba..Wann ma ai ba magana bace tinda kud'in nan ba kud'in Bad'ia bane ita kad'ai.. Ehe kud'i ne na magada.. Kuma shago da ba shagon sata ba ya ma za'ace an sayar cikin rahusa haka. Nawa kowacce zata samu cikinku.?"

Badi'a dake aika masa mugun kallo tace "Toh wai kai Malam naka a wanne.. Ko harda kasonka ne cikin gadon.?"

Azeema ta katseta "Ai naga gadon na uban Tasi'u ne da kika gayyatosa Ya kwashe kud'ad'en Ya gudu. Toh wllhi na ranste da Allah bazata tab'a sakuwa ba wai bindiga a ruwa. Wllhi yanzu zan kirawo Yaya Salima tinda duk abinda ake itama bata sani ba. Na ranste da Allah sai an mana kashin hakkinmu ehe. Ko kuma wllhi na gayyato maku hukumar hisba nace Kun saida gadon mahaifinmu dake kwance gadon asibiti.!" Ta k'arashe sai huci take.

Habibu sai bud'e hannaye yake yana kuma ingiza Azeema. Fad'i yake Ahtoh magana kenan a fito masa da hakkin matarsa.

Azeema ta Ciro waya da zummar kiran Salima kenan suka sinkayo kukan Mama. Ta kamo bakin mayafi tana matse idanunta "Ni Tasi'u zai tona ma asiri a garin nan.. Na rufa masa asiri yana d'an wiwi na d'auki 'ya na basa a tunanina zaiyi hankali ashe ni ce 'yar wiwi."

"Mama ba fah kuka zakiyi ba, nemo Tasi'u Ya kamata kuyi yanda ya shiga Ya fita dan wllhi muddin Tasi'u baizo ba daga nan ofishin hukuman hizba na nufa na zayyane masu komai. Kun raba gadon mahaifinmu da ransa.!" Azeema tace tana huci.

Habibu yai saurin shiga tsakiya kaman wani alk'ali "A'a a'a baza'ayi gaggawan gayyato hukuma ba tinda abin duka na gida ne. Kamata yayi a binciko yanda Tasi'u yake duk rintsi. Yanzu zan tafi yanda shi Tasi'un ya cika zama na tuntub'i abokansa tinda dai baza'a samesa a gida ba. Na tabbata baiyi nisa ba." Ya k'arashe yana mai wucewa cikin sauri.

Ummul da Khulsum suka dubi juna cikin tsananin shock. Mama da Badi'a saida shagon Abba sukai kenan ko mai hakan yake nufi.? Innalillahi wa inna'ilaihi raji'un.

Suna a haka aka zo neman kud'in magungunan Abba wanda kusan kwana biyu kenan yana skipping wasu treatments d'in masu matuk'ar mahimmanci.

Mama sai ta hayyayako ta soma bala'i tana fad'in ta gaji da zaman asibiti ma jinyar da yak'i ci yak'i cinyewa.

Nurse yace "Yanzu babu kud'in da za'a masa jinyar.?"

Azeema tace "Kurma ne kai baka ganin tashin hankalin da muke ciki ne.. Damfararmu fah akayi.."

K'arasowan su Ummul suna tambayan mai ake nema gameda jinyar mahaifinsu yaja hankulan su Badi'a. Ita kam Mama har yanzu fah bata wani gane mai ake ciki ba hankalinta kacaukam naga Tasi'u da kud'ad'enta.

Badi'a tace "Kud'in jinya ake nema ko zaku biya ne tinda wancan karan ma ku kuka biya. Sai aje a sake saida jiki a kawo kud'i. Ko mazan ne babu.?"

Khulsum ta dubeta Har lokacin mamakinsu bai saketa ba "Da dai a kiramu b'arayi marassa imani masu saida k'addaran mahaifinsu da ransa gwara ace jikinmu muka saida muka biya kud'ad'en jinyarsa. Kin fahimta B'arauniya matar b'arawo.!"

Badi'a ta nufota a zafafe tana fad'in "Ke ni sa'anki ne dan ubanki.. Sai na gurje bakin ki yanzu a nan..!"

Saida aka shiga tsakanin Khulsum da Badi'a.

Nurse yace "Yanzu haka Dr zaizo babu abinda aka buk'ata.. Shin ba hanyar da za'a bi a samu a saya magungunan..?"

Kaman daga sama suka sinkayo wata murya "K'warai akwai hanyar da za'a saya!"

Mama dake shirin barin wajen dan batada lokacin cecekucen rashin kudin jinyar Malam da malaman asibiti burinta kawai ta isa ta cimma Tas'u. Nan tai birki jin wann murya dai tai ma me muryar farar sani. A hankali take k'ok'arin juyowa har dai ta karkato gaba d'aya.

Mama ta daskare. Ta shiga mutsuka idanunta tana duban wacce take gani gaba gareta "Suwaiba.!" Ta furta cikin tsananin mamaki.

Suwaiba ce fah.. Suwaiba Amaryar Malam Isubu nata take gani sanye cikin tufafi na alfarma. A gidan Uban wa Suwaiba tayi arziki dare d'aya. Karfa hausar nan da ake cewa dare d'aya Allah kan yi bature ta tabbata kan Suwaiba. Ta kuma mutsuke idanunta dan har lokacin gani take kaman gizo ne ba gaskiya ba. Wai Suwaiba shashashar matar Malam Isubu ce haka kaman wata matar shugaban k'asa ko gwamna.

Khulsum da Ummul ma da mugun mamaki suke duban mahaifiyar tasu wacce kaman an canzata. Suka dubi juna suka kuma duban Umma shaye da tsananin mamaki, cikin tsananin shock suka furta "Umma.!"

Umma taci gaba da takowa gaba garesu. Azeema da Badi'a ma da mugun mamaki suke duban Umman.

Kai tsaye nurse d'in Umma ta nufa tace "Nawa ake nema..?"

Nurse d'in Ya d'ago takardan na list d'in abubuwan da ake buk'ata Ya soma karantowa.

Kafin Ya gama karantowa Umma ta d'aga masa hannu alamun dakatarwa lokaci guda ta bud'e tsadadden handbag d'in dake rik'e hannunta ta Ciro sabbin kud'ad'e 'yan dubu dubu sai walk'iya suke. Mama ta zaro ido waje ganin dubabe bugun habuja suna walk'iya suna kashe mata ido. Wai Suwaiba ke fiddosu.

Ko k'irgawa batai ba ta mik'a ma nurse d'in "Ungo nan.. A saya duk abinda ake buk'ata, idan yayi canji ka rik'e canjin idan kuma akwai abinda bai isa ba ka sanar Dani.. Ko menene.." Ta k'arashe tana gyara zaman tsadaddan mayafin dake bisa kanta.

Nurse ya murmusa "A'a Hajiya saidai na Miki jagora ki biya da kanki."

Umma ta jinjina kai yayinda Umma ta take masa baya.

Tin daga k'afafu Mama ke dubanta Har zuwa tsadadden leshi da yan kunne da sark'a dake kwance wuyanta. Wann ko taron manyan matan gwamnoni Suwaiba taje a haka ai ta cinye taro.

Akan idonsu Umma ke gudanar da komai da taimakon nurse d'in kafin daga bisani ta amso receipts ta dawo yanda ta baro ahalin mijin nata Wanda kowa shock Ya hanasa aiwatar da komai. Baga Mama da yaranta ba baga Yaran Umma ba wanda zasu iya cewa Har yanzu basu tabbatar idan mahaifiyarsu bace.

Ko takan Mama batabi ba ta dubi su Ummul wacce suma kansu ta koma masu tamkar bak'uwa. Kallon rashin sani ne ko na mamaki suke bin mahaifiyar tasu dashi. Tsakiyan yaranta ta shiga wato Ummulkhairi da Ummukhulsum ta kamo hannayensu tace "Mujenku kuga mahaifinku.."

Tamkar rak'umai da akala haka Umma ke janyo su Ummul da Khulsum. A haka suka zo suka shige gaban Mama da yaranta wanda suka koma kaman an dasa su.

Har suka shige cikin ward d'in Mama da yaranta basu daina binsu da kallo ba.

Suna shigewa Mama ta dubi Azeema tace "Ke wanke ni da mari dan ubanki."

Azeema ta dubeta a yatsine "Ban gane na wanke ki da mari ba Mama.."

"Nace ki mareni na tabbata ba mafarki nake ba.. Ba Suwaiba bace Ke min gizo ba. Inji ba itace yanzu ta shige gaba na ba ko.? Ku amsa min mana.. Na shiga uku ni Tani.."

Bata kai aya ba taji zafi Ya tsunkuri 'yar yatsarta na k'afa. Badi'a ce ta take mata 'yar yatsar cikin k'ok'arin dawo da Mama hayyacinta.

Mama ta saki k'ara tana d'ingile k'afarta "Wayyo kunama ta cijen.!"

Badi'a tace "Ba kunama bane ta cijeki, take maki k'afar nai ki tabbata ba mafarki kike ba.."

Azeema tace "Mama wllhi Umman su Ummul ce. Amma nima nafi zaton canzata akai.. Mama ina ta samo kud'ad'e irin haka dare d'aya.. Kinga Har fari da shek'i ta k'ara dare d'aya. Mama kin kaw ga suturan dake jikinta. Wllhi iriinsa matar Gwamna ta saka ranan da za'a rantsar da mijinta.. Mama Ina matar nan ta samo kud'i haka wai.?"

"Yo Ina zan sani ina tareda ke a nan.." Mama tace tana kuma lek'en bayan Umma a tsarace.

Badi'a ta tab'e baki tace "Kar canzawarta ya zautar daku. Abu ne a bayyane matar nan dama barikinta kawai take son yi auren mahaifinmu ya taka mata burki.. Yanzu da take ganin zai Mutu shine ta baje kolinta da kyau zatai barikinta mai dalili.."

Azeema tace "Kai wllhi amma fah ta mun kyau, kinga shegen mayafin da ta watsa. Irin mai walwalin nan fah da ake talla online.. Inama ta bani aro naje dashi Bikin k'anwar Habibi na yak'i shegun danginsa."

Bata kai aya ba Mama ta hamb'are bakinta "Kud'in shan jini da tsafin zakije a baki.. Toh Idan shaye shaye kike kije Azeema.. Kije Suwaiba ta shanyeki.. Ni nayi imani itace ta asirce Ummul mazan dake nemanta ke gudu sabida Allah Ya rufa masu asiri da sauran kwanakinsu. Shi Fa'izu dake kwanansa Ya k'are gashi ta lashe kurwansa. Yanzu kuma abun yazo kan Malam Shiyasa data mik'a sa gashi a kwance kafi gawa.. Kuma yanzu ba sai anjima ba zan fiddata daga cikin asibitin nan.."

Fiuuu Mama ta shige ta nufi ward d'in yaranta na biye da ita.

Bata damu da majinyata dake kwance wajen ba Mama ta shiga kururwa tana fad'in Suwaiba mayyace yar K'ungiya asiri ne na shan jini.. Ta tsafe 'yarta Ummul tana amfani da ita tana cinye mutane kaman yanda Fa'izu d'an 'yar uwan Malam Isubu ya mutu. Bai isheta ba yanzu ta mik'a mijinsu zata cinye.. Sai dukan k'irji take tana fad'in wllhi bazaayi ma mijinta amfani da dukiyar 'yar shan jini irin Suwaiba ba.

Sauri sauri wasu nurses da cleaners suka tafi kiran securities. Hango securities d'in da Mama tai ya sanyata had'iye kalamanta.

Securities suka k'araso suna muzurai suna fad'in waye zasu fidda.

Take Mama ta shiga masu nuni da Umma tana fad'in "Ga Suwaiba ita zaku kama ita zaku fidda.. Yar shan jini ce.."

Ai sai Mama taga securities sun isa gaban Umma suna duk'awa suna kwasan gaisuwa lokaci guda suna tambayar ko da abinda kike so a miki Hajiya.

Mama sai ta saki baki tana duban ikon Allah. Suwaiba.? Suwaibar ne Hajiya..?

Umma ta murmusa tana gyara zaman mayafinta "A'a babu komai Kar ku damu. Haukar wancan Matar ne Ya motsa inaga b'allewa tayi daga b'angaren masu jinyar hauka."

Mama jin an ambaceta da Mahaukaciya ya sanyata kuma hayyak'owa. Jikinta Har rawa yake.

Sauran mutanen dake wajen Wanda dama fitinan Maman a ishesu sukace da gaske ne batada saiti kullum fama ake da ita.

Aiko nan take securities suka fidda Mama da k'arfin gaske sai ihu take tana tsine ma Umma. Yaranta suka bi bayanta a guje suna ambato sunanta.

Umma ta zuba masu idanu har aka fice dasu kafin ta sauk'e ajiyan zuciya ta juyo tana duban yaranta Khulsum da Ummul Wanda Har lokacin kallon mamaki ko muce kallon tsoro suke binta dashi musamman bayan da Mama ta gama fad'e fad'enta.

Umma ta kuma dubansu sai ta k'arasa ta rungumesu. Basu iya maida mata martanin rungumar ba.

"Ummul, Khulsum.. Ni ce fah mahaifiyarku Ummanku.. Meyasa kuke dubana kaman bak'uwar fuska. Shin ko baku shaida mahaifiyarku bace.?"

Girgiza mata kai Ummul tai "Mun shaida kamanninki Umma amma yanayi ki yafi kama da bak'uwar Fuska.. Umma mai ya canza ki cikin kwanaki k'alilan..?"

Murmushi Umma ta saki kafin ta dafa Ummul "K'addararki itace ta canza ni cikin kwanaki k'alilan Ummul.. K'addaranki Wanda a baya naita Allah wadai dashi shine ya zamto mabud'in Alherinmu.."

Girgiza kai Ummul tai cikin tsananin sanyin jiki "Umma ban fahimceki ba.."

Umma ta kuma murmusawa "Kar ki damu 'Yata da sannu zaki fahimci komai.. Kuzo muje.." Ta shiga janyo hannuwansu suka nufo waje yanda suka hangi Mama har lokacin huci take bayan an tilasta mata yin shiru.

Mama ta zabura zata nufo Umma amma sai taga wata jibgegiyar jeep taja tayi parking gaban Umma. Mama taja wani wawan birki tana dafe k'irji.

Mamaki da sanyin jiki Ya kuma sauk'ar masu Ummul.

Umma ta dubesu "Toh yarana ni zan tafi, in sha Allah zan kuma dawowa nan bada jimawa ba."

Da tsananin mamaki suke duban mahaifiyarsu. Tasa kai kenan zata shige mota Ummul tai saurin kamo hannunta. Hawaye na gangaro mata take girgiza kai "Umma.. Ina zakije ki bar Abba cikin halinda yake ciki..? Umma ina kikaje kika barmu mu nata nemanki.. Shin Kinsan abubuwan dake faruwa a nan.. Umma wai meke faruwa.. Umma meke faruwa ne..?"

Dafata Umma tai "Da sannu zaki fahimci abinda ke faruwa Ummul.. Zan rok'i alfarmarku. Kar ku bar kusan mahaifinku.. Ku zauna ku kula dashi.. In sha Allah daga yanzu duk wani abinda za'a kashe sabida jinyar mahaifinku bazai zama matsala ba. Na barku lafiya yarana.."

Ummul na kuka ta kuma kamo hannunta "Umma shin kinsan kalan tashin hankalin da muka shiga na rashin ganinki.. dan Allah kar ki tafi ki barmu.. Umma.." saidai tuni Umma ta cire hannunta daga rik'on da Khulsum tai mata ta shige mota. Ummul ta kuma yunk'ura tana ambato Umma amma saiji tai Khulsum ta rik'on hannunta had'ida dakatar da ita "K'yaleta Adda.. Wann ba Umman mu bace.. Idan ma itace banida haufi an canzata dare d'aya."

Fad'awa jikin Khulsum Ummul tai wani irin kuka na kufce mata.

Mama kaw zuba masu idanu tai tana mai kuma tabbatar da zarginta cewa Suwaiba dai K'ungiyar asiri ta fad'a.

Umma tana shigewa cikin motan ta dubi Asshe dake zaune gefe. Ta d'an yi adjusting mayafin "Hajja Asshe Ya kikaga k'warewata..? Kinga kaw yanda na razana Tani na haukata ta na gigitata.? Gaba d'aya fah ta birkice.."

Asshe ta murmusa tace "Ai ma fah bama ayi komai ba, wann ai sharan fage ne. Sai randa aka kai lefen Ummulkhairi, ranan ne zaki kashe kishiyar ki da k'unci. Dan ina mai tabbatar miki sai ta had'iyi ranta. Kaf abinda ta miki kan Ummulkhairi sai kin rama. Ranan biki kuma a fice da gawarta."

Umma ta zaro idanu "Na shiga uku, bazan so Yaya ta Mutu ba ai…"

Asshe ta d'an murmusa kad'an had'ida dafe kafad'ar Umma guda "Bazata Mutu ba ma sai taga Nasaranki da na Ummul. Kuma ko yanzu kin tauna tsakuwa aya kuma taji tsoro.. Ni so nake ki kece raini a kamfatanin layinku.. Duk masu aibata Ummul d'inki sai Sun shaida auren gata da za'a mata.."

Nan fah Umma ta shiga wage baki zuciyarta na mata dad'i. Karfa ku mance mijin Umma na kwance gadon asibiti tsakanin rayuwa da mutuwa. Amma Har yanzu burin Umma shine Ummul d'inta tayi aure kota halin k'ak'a ko ba dan komai ba sai dan ta birge Mama da sauran jama'an unga sabida abinda suka jima suna mata kan Ummul.

**

A b'angaren su Ummul kuwa tinda Umma ta shige bak'ar Jeep d'in nan mai lullub'e da tint suka kasa komawa cikin asibiti wajen Abbansu dan haka su Mama da Azeema sukai caa a haraban asibiti suna nunasu suna cewa ga 'ya'yan mayya. A dole suka fice daga asibitin suka dawo gida.

Ummul ta zuba tagumi Khulsum ma da kalan nata tagumin.

"Adda anya ba gaskiya Mama take fad'i kan Umma ba.. Anya Umma ba wani k'ungiyar asirin ta shiga ba..!" Tai maganar kaman mai tsoron furtawa.

Ummul tai saurin d'agowa tana dubanta "Haba Khulsum ta ya zakiyi irin wann tunanin..?"

"Adda abinda idanun mu suka gane mana fah kenan… Ina Umma ta samo dukiya irin wann tsakanin kwanakin nan..? Sann meyasa ta tafi ta k'yalemu..? Meyasa bata damu ta bar Abba cikin halinda yake ba.. Adda kifa duba kiga yanayin da Abba yake ciki amma Umma tana a matsayin matarsa ta saka k'afa ta tsallake shi har da shigewa shirgegiyar Jeep d'in nan. Ga ado da tayi irin wanda bata tab'a yi ba. Wata matace zatayi wad'ann abubuwan alhalin mijinta na kwance cikin tsananin jinya. Wllhi ko baki fad'i ba Kema kanki nasan zuciyarki bai kwanta ba Adda kuma akwai irin tambayoyin da nakeyi kwance cikin zuciyarki."

Sauk'e wani irin ajiyan zuciya Ummul tai sai kuma ta jinjina kai tace "Kinyi gaskiya… Akwai tarin tambayoyi k'unshe cikin zuciyata Wanda zanso Umma ta amsa min su.. Amma ko ma menene kar muyi gaggawan yanke hukunci da abinda idanu mu ka iya gani.. So tari abubuwan da idanun mu ke iya gani a zahiri ba haka suke a bad'ini ba.. Mu tsaya Har muga gudun ruwan Umma mu kuma ji abinda ke faruwa."

Khulsum taja wani irin gauron numfashi ba tareda ta kuma furta komai ba.

**

Abuja.

Laptop ne gabansa waya manne kunnensa yana duban wasu sketches na manyan bridges iri daban daban. Ko ba'ace ba da Hisham yake wayan. Da alama shi ya turo masa sketches d'in da suke tattanawa akai. Bayan Sun gama magana shiru yai yana nazarin abinda ke gabansa. Sai kuma ya rufe laptop d'in ya k'ura ma waje guda idanu.

Dareen da waya ke mak'ale kunnenta ta kuma lek'ensa kafin ta koma da baya tana rage murya had'ida matse wayar jikin kunnenta sosai "How would I know.. He's been acting strange lately.."

Daga d'aya b'angaren muryar mutumin ya katseta "What are you there for idan har bazaki iya karantar yanayin da yake ciki ba..?!"

Ta d'an rausayar da idanu had'ida furzar da huci "Look, I see him everyday but I can't grasp his mood. Ba ko yaushe asiri yake tasiri ba. Kar ka mance Shi mutum ne Wanda tun kafin sihiri ya jefesa yakeda wahalan sha'ani."

Mutumin yace cikin tsawatarwa "Kalla Dareen. Ban kawo ki cikin rayuwar Haidar dan kiyi holewarki dashi ba. Kinfi kowa sanin dalilin da yasa kike tare dashi. Idan Har bazaki min amfani ba. Zan tarwatsaki da kaina.. Kinsan inada makamin da zan tarwatsaki a hannuna tinda har yau baki san yanda na bisne sirrin da Ya rufe Aurenki da Haidar ba."

Lumshe idanunta tai had'ida bud'esu "Fine, zanyi iya k'ok'arina na fahimci mai yake shiryawa. Amma karkayi gangancin rabani da Haidar domin zan tashi wutan da kaima baka isa kashewa ba.!"

Ya murmusa "Kar ki mance I'm the one calling the shots here. Kibi umarnina ki zauna lafiya.!" Yana ida fad'in haka ya katse kiran.

Furzar da huci ta kumayi kafin tai k'ok'arin kintsa kanta ta fito parlor yanda Haidar ke zaune.

Murmushi saman fuskarta ta zauna gefensa "Love.." Ta fad'i tana shigewa jikinsa. Sai kuma ta d'ago fuskarta tana dubansa "Is something bothering you..? You seem preoccupied… Is it about work..? Ko kaje duba Mommy ne..?"

Tambayan da ta masa na k'arshe yasa ya dubeta sai kuma ya maida dubansa wani b'angaren "I'm fine.." Ya fad'i a tak'aice ba tareda ya kuma cewa komai ba. A 'yan kwanakin ta kula magana ma sai ya zama dole yakeyi. Ya koma mata tamkar bak'o cikin gidan dukda dama a iya zamansu bata isa tace ta sansa kaman yanda tasan tafin hannunta ba dukda kuwa Auren sihiri da tayi dashi. Mik'ewa yai ya nufi sama ba tareda ya kuma ce mata komai ba. Hannayensa sakale cikin aljihun sweatpants d'in dake jikinsa.

Tabi bayansa da kallo har ya haye sama kafin tai saurin janyo laptop d'in ta bud'e. Sannu a hankali take bin duk wasu abubuwan dake fuskan computer d'in tana karantawa. Aiki yake sosai kan project d'in da takeda masaniya yanata fad'i tashi akai. Toh kodai mahaifinsa ya basa go ahead ne.? Idan har mahaifinsa ya amince ya jagoranci aikin dole akwai wani abu a k'asa. Ba yanda za'ayi mahaifinsa ya amince masa cikin sauk'i.. She needs to find out meke faruwa.

** Yau kwanaki biyu kenan Umma bata kuma waiwayowa ba. Hankalin Mama kaw gaba d'aya ya gaza kwanciya. Damuwarta kawai shine tasan yanda Suwaiba ta samo irin wann arziki da ta gani tareda ita. Gaba d'aya ta ma mance da batun Tasi'u da halinda kud'ad'en shagon Abba ke ciki.

Yau d'in ko asibiti wajen Abba ta gaza komawa. Tare take da yaranta Badi'a da Azeema yayinda suka baro Salima can wajen Abba. Tunanin Mama d'aya idan ta fice Suwaiba na iya zuwa gidan wajen 'ya'yanta Shiyasa ko k'ofa ta gaza fita.

Mama da yaranta Azeema da Badia Suna tsaka da aibata Suwaiba 'yar k'ungiyar asiri gaban su Ummul suka soma jiwo hayaniya daga waje. Wann Ya dubi wancan wancan ya dubi wann.

Azeema tai saurin tare wani yaron cikin gidan da ya shigo a guje rik'eda gudan dubu a hannunsa yana ihun murna. Azeema ta rik'esa tana tambayarsa meke faruwa waje.

Yaron yace "Umma ce.. Umman su Khulsum itace tazo da k'atotuwar mota tanata rabon kud'i a waje.."

Mama dasu Azeema suka dubi juna. Babu shiri suka nufi waje a fujajan yayinda su Ummul ma duban junan sukai itada Khulsum. Take suma suka take ma su Mama baya.

Mama da yaranta suka wani irin birki Har saida ya rage saura k'iris Mama bataci tuntub'e da wani yaro da ya nufo gida a guje yana ihu yana d'aga kud'insa sama.

Daskarewa Ummul da Khulsum ma sukai suna duban kayan al'ajabi. Ikon Allah. Da gaske Umma ce ta fito cikin wann bak'ar shirgegiyar mota tana rabon kud'i ma Al'umman unguwar. Mutane kaw sai fitowa suke kusufa kusufa daga lungu da sak'o suna amsan kud'ad'en da Umma ke rabawa.

A haka Umma ta k'araso gaban Mama. Ta murmusa tana dubanta "Tani ya muka sameku.."

Mama ta kuma bud'e baki tana duban Umma jin irin gaisuwan rainin da tai mata. Wai Tani ya muka sameku.. Tani fah.. yau Suwaiba bata kirata da Yaya kaman yanda ta saba ba. Tani fah ta kirata dashi gatsau. Waima Yaushe Suwaiba ta sami 'yanci cikin gidan. Dan lokacin da aka aurota daga rugarsu babu kalan uk'uban da bata gallaza mata ba ga wauwauta ga shashashanci had'ida mugun k'auyanci da sukai mata dabaibayi.. Wai har Suwaiba ne ta waye yanzu.. Lallai ta yarda da hausar nan da ake cewa Shege na k'auye.. Idan bak'auye ya samu faraga yafi d'an birni iya shege.. Eh Tabbas yanzu ta shaida wann da idanunta.. Dan barikin da Suwaiba take a yanzu ko goggan d'an birni Wanda aka haifesa tsakiyar wayayyu bazai ba. Ko ita kanta bata tasa k'afa ta tsallake mijinsu dake kwance yana jinya ta tafi ta barsa ba. Sai yanzu take ganin ashe ita jaririya ce a bariki tinda ita saida shagon Isubu kawai tayi, tanata kumfan baki tana fad'i tashi ta raba gadon Isubu tun yana raye dan kar Suwaiba da yaranta su samu. Ashe Suwaiba kallon k'aramar 'yar iska take mata. Ita a daidai wann gab'ar ma ta baje Rumfar barikinta.

Muryar Umma ne Ya kuma dawo da ita daga duniyar tunanin da yai nisa ciki "Yauwa Tani nace ba ga wann ki kula da Abban Ummul sosai.. Naga Salima wajensa. Bansan mai kike a nan ba da har yanzu baki tafi wajensa ba. Idan akwai abinda ake buk'ata kina iya sanar Dani dukda dai duk wani abinda ya kamata a bayar an bayar. An canza masa d'aki ma ya koma b'angaren kud'i. Kira Salima zata sanar dake komai tinda tareda ita akayi duk wasu sauye sauyen. Tai maganar tana mai Ciro kud'ad'en cikin hamshak'in jakanta. Yacce kasan matar gida na bawa 'yar aikinta sak'o.

Mama tai sakare tana duban Suwaiba.

"Ungo amshi mana..!" Umma tace tana mai kamo hannun Mama had'ida damk'a mata kud'ad'en ciki.

Lokaci guda Umma tasa kai tana taku d'add'aya sai juya ma Tani mazaunai take.

Kusan silalewa wajen Mama tai har saida Azeema ta tallafeta.

Kasa motsawa Khulsum tai har Umma ta shige ta nan gabanta rik'eda hannun Ummulkhairi wacce ke biye da ita tamkar rak'umi da akala. Bata iya dawowa hayyacinta ba saida ta sinkayo muryar Mama na fad'ida Azeema ta rik'eta sosai bata iya tsayuwa kan k'afafunta.

Cikin sauri Khulsum ta nufi bayansu Umma k'afafunta Har hard'ewa suke.

Tana shigowa ta sinkayo muryar Umma dake rik'eda hannun Ummulkhairi tana fad'in "Ba sai Kin d'auki komai ba.... Maza tashi muje direba yana jiranmu.."

Katseta Khulsum tai da fad'in "Ina zaki Kai 'Yaruwata Umma..?"

SameenaAleeyou📚

*AUREN WATA UKU..!*

*17*

*©️Sameena Aleeyou…✍🏽*

Katseta Khulsum tai da fad'in "Ina zaki kaita Umma..?" Muryarta Ya soma rawa sosai sanda take ci gaba da furta "Umma shin abinda mutane ke fad'i gaskiya ne..? Umma dan Allah wacece ke..? Ina asalin Ummanmu da muka sani..?"

"Banida lokacin Miki bayanin komai a yanzu Khulsum.. A halin da ake ciki 'yaruwarki nazo d'auka.." Ta k'arashe tana mai janyo hannun Ummulkhairi.

Cikin azama Khulsum ta rik'e Ummulkhairi tana girgiza mata kai tana hawaye "A'a Adda kar ki bi Umma.. Adda dan Allah kar kije.."

Dubanta Umma tai a yatsine kafin direba ya bud'e mata owners corner saida ta dubi yaranta na d'an lokaci kafin taceda Ummul idan kin gama kya shigo muje." Daga haka ta fad'a mota kayanta.

Khulsum ta kuma share hawayen da suka gangaro mata. Hannayenta cikin na Ummul take fad'in "Adda dan Allah kar ki bi matar nan.. Bamu san Ina zata kaiki ba.. Watak'ila rad'erad'in da mutane suke da gaske ne Adda.. Kinga Umma dai an canzata gaba d'aya bamu San Wacece ita ba a halin yanzu."

Khulsum na hawaye take girgiza kai lokaci guda taci gaba " Adda Ummul, Mai zai faru idan da gaske wajen matsafa zata kaiki.. Mai zai faru idan wani abun ya sameki.?"

Ummul ta zame hannunta daga cikin na Khulsum tabi bayan Umma aka bud'e mata mota ta shige. Tana kallon Khulsum dake tsaye wajen hawaye na gangaro mata yayinda itama Ummul d'in hawaye ne ke gangaro mata. Ta rintse idanunta cikin zuciyarta take furta 'Kiyi hak'uri 'Yaruwata. Ya zama dole nayi wann. Babu abinda zai sameni face Allah ya k'addari faruwan hakan.. Dani dake mun San yanayin Umma a d'abi'a da halayya. Munsan matsalan mahaifiyarmu, Abu ne mai sauk'i a rud'eta.. mahaifiyarmu ce, ya zama dole na bita na gano hak'ik'anin abinda ke faruwa da ita. Domin kaw bazamu bari ta auka ma halaka ba munaji muna gani. In sha Allah komai zai daidaita K'anwata..' Ta k'arashe tuanin nata wasu hawayen na kuma gangaro mata.

A daidai gate d'in wani gida mai matuk'ar kyau da tsari motar tai horn.

Khulsum da tuni ta d'ale acab'a tabisu a baya ba tareda saninsu ba. Tana ganin gidan da akai parking tace ma me mashin ya ajeta daga can nesa dan sai ta karanci gidan kafin ta danna kai ciki. Allah ya gani bazata bari mahaifiyarsu ta bada 'yaruwarta ayi tsafi da ita ba.

Driver na Ida parking Ya fito ya bud'e masu k'ofofin. Zuciyar Ummul sai tsinkewa yake tana duban Umma wacce ta koma mata tamkar bak'uwa.

Umma ta dafata tana murmushi "Ki saki jikinki Ummul d'ita. Ban kawo ki yanda za'a cutar dake ba. Domin kaw ni mahaifiyarki ce. Tin haihuwarki burina shine rayuwarki ya cika da d'imbin alkhairai kaman dai yanda sunanki yake." Ta d'an numfasa kafin taci gaba "Kinga nan gidan.. Gidan da za'a share mana hawaye ne.. Gidan da za'a cika mana burinmu da yardar Ubangiji. Kukanmu yazo k'arshe Ummul.. Taho muje.." Ta k'arashe tana mai janyo hannun Ummul. Amma sai Ummul ta tarje.

Umma ta juyo tana dubanta "Ummul ya kika ja kika tsaya, kinga nasan damuwarki bai wuce tafiya da mukai muka k'yale 'yaruwarki Khulsum ba. Sanin halinta, sanin duk abinda aka saka da ita sai ya lalace shisa bamu taho da ita ba.. Shige muje kinji."

Readers Also Read